HEEDAYA CHAPTER 30 BY By Khaleesat Haiydar

HEEDAYA CHAPTER 30 BY By Khaleesat Haiydar

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Mumy ta nemi kujera ta xauna tana murmushi, labarin biki da abubuwan da suka faru suka dinga yi da kaka, kaka ta 

saki baki sai xuba take, Mumy tace “Ai ni kin kyauta min da kika ce a sauke canopy din nan, mutane basu da 

hankali wllh” Kaka tayi fuska kamar ‘yar yarinya tace “Lallai, haka kawai a lalata min motocin yaro, uban waye ya 

siya masa, kiris ya rage wnn suntumemen ya gogi motar da karfen fa, ba ruwana ni dai na koresu, wanda suka kafa a 

bakin titi bai isa ba sai an shigo mana gida da katon lema a kakkafa” Mumy tayi ‘yar dariya, sai kuma ta kalli su 

farida tace “Ku ci mana kar ya huce da xafinsa kuwa” Farida ta ajiye wayarta da take dannawa tace “Na koshi ni” 

Mumy ta hade rai tace “Kin koshi kamar Yaya, hanaki cin abinci aka yi a nan din idan kun xo” Kaka tace “Aa babu 

wanda xai hanata, da yake kinsan sun karya kafin mu fito” Mumy tace “Aa to gaskiya baxan ji dadi idan basu ci ba 

tunda da kai na na kawo masu” Kaka ta kalli farida tace “Ko kwara daya ne ki ci kar taga kamar an hanaki, nasan a 

koshe ku ke” Mumy na kallon Heedayah tace “Ita idan ta ki ci ai ke bakya ki ci ba, dau plate din ki ci abun ki” 

Heedayah tace “Ahh haba wnn ai Mayyar nama ce xata ci nasani” Heedayah ta kalleta bata dai ce komai ba, Mumy 

tayi dariyar da bai kai ciki ba tace “Dauka ki ci Heedayah” Heedayah ta sauke idonta tana kallon naman tace “Mumy 

na koshi, mun yi breakfast a gida kafin mu fiti” Mumy ta d’an hade rai tace “Nama abinci ne? Bana son gulma idan 

xaki dauka ki dauka ki ci, idan kuma hanaku cin komai akayi sai na sani” Kaka tace “Ni dai ba ruwana sai ku ja ma 

Rakiya bakin jini nan kuma bata san hawa ba bata san sauka ba, idan xaku dau gasasshen naman ku dauka ku ci 

meye xaku dinga ma mutane kunbiya kunbiya gashi har na narka kwaina a ciki, nama ai abun marmari ne ba abinci 

ba” Farida dai ta ci gaba da danna wayarta bata ce komai ba, Heedayah ta dau plate din naman ta dauki daya, wani 

ajiyar xuciyar da ya kusa fitowa fili Mumy ta sauke, Kaka ta kalleta tace “Lafiya?” Mumy ta d’an daburce tace 

“Wllh tun juya nake jin kamar ulcer na xai tashi” Kaka tace “Toh Allah ubangiji ya maki tsari da shi” ta gefen ido 

Mumy ta dinga kallon Heedayah da ta kai naman baki ta fara ci a hankali, wani ajiyar xuciyar ta kuma saukewa, 

Kaka tace “Toh Allah yayi maki tsari da shi dai, ulcer ai bala’i ne” Heedayah xata ajiye plate din Mumy tace “Har 

kin yi me? Me kika ci da xa ki ajiye” Kaka tace “Ni dai ba ruwana da wahalansu idan basa ci su kawo min in juye a 

jaka mu tafi kawai” Farida ta mike ta dau plate din nata ta tafi ta kai ma Kaka tace “Ni baxan ci ba” kaka ta kwace 

plate din, Heedayah dai ta ci gaba da cin naman, hira kawai Mumy ke ma kaka don Heedayah ta ci naman sosai, 

Heedayah dai cin naman kawai take ba wai don yyi mata dadi ba, daga karshe ta mike ta nufi kofa, Ta gefen ido 

Mumy ta bi ta da kallo don ta ci desired quantity din ba laifi, Heedayah na fita ta dau hanyar kitchen, xaune ta ga 

Shuraim a parlon this time around, ya mike ganinta, dauke kai tayi da sauri ta wuce kitchen din ta shiga, plate ta 

nema ta rufe sauran naman ya shigo kitchen din yana kallonta yace “What’s that you are covering?” Ba tare da ta 

kallesa ba tace “Tsire ne” Yace “Waye ya ci?” Tace “Mumy ce ta bani” Shiru yyi yana kallonta, yace “Ke da wa?” 

Tace “Farida” yace “Ina na faridan?” Heedayah tace “ita bata ci ba” yace “Kece mayunwaciya kenan” Sai a snn ta 

kallesa, ya daure fuska yace “Baki ci abinci a gida ba kafin ku fito?” Kin cewa komai tayi ta dauke kai, yyi mata 

wani tsawa yace “Ba da ke nake ba” Ta ki juyo fuskarta ta d’an turo baki tace “Na ci” yace “Then meyasa kika ci 

naman?” Tace “Mumy ce tace I should eat it” karasawa yyi ya bude plate din sai ga Mumy ta shigo kitchen din, 

ganinsu a tsaye da mamaki tace “Me kuma kake yi a nan Aliyu?” Ba tare da ya dubeta ba yace “I came to make tea” 

Mumy tace “Wanda ka sha daxu fa” yace “Bai isheni ba” Ta kalli Heedayah da ta sunkuyar da kanta, Mumy tace 

“Ina naman da kika rage bani in tafi in ci ban karya ba dama” Heedayah ta karasa ta bude plate din ta dauko naman 

ta mika ma Mumy ta amsa, Heedayah ta bi gefenta ta fita kitchen din, Mumy tayi masa wani kallo tace “Da uban me 

ka shigo nan din kana gaya mata ko akwai hadin biri da gada ne?” Yace “Ni fa I just came in to make tea sai na ganta, 

and where is my meat?” Mumy tace “Gwara ya kasance haka don ma ka ji in gaya maka, ba hadin biri da gada, tsire 

kuma bbu sai ka dau na annabawa” yace “Toh bani wannan in ci” tace “Baxan bayar ba” daga haka ta fice daga 

kitchen din ya bi ta da ido. Mumy na fita kitchen dama Parlon Abba ta shiga ta kulle da mukulli, tana dube dube ta 

dau wani plane sheet paper ta juye tsiran a ciki sannan ta cukuikuye takardan ta tura can karkashin kujera yanda 

baxa a hango ba snn ta mike ta fito Main parlor, leka hanyar kitchen tayi ta ga alamar yana tsaye har sannan a 

kitchen din, ta mayar da plate din parlon Abba, sannan ta fito ta sa makulli ta tafi parlonta tana murmushi ta shiga 

tace “Sannun ku Kaka, Kwan ya ishe ki ko?” Kaka tace “Ya isheni sai na gobe kuma idan Allah ya kai mu, kin ji 

Farida wai mu wuce, bayan nace ma Amadu muna nan har dare” Mumy tace “Allah sarki, ta gaji da xama kenan, 

tunda kun gaisa da Barrister din ai xaku iya tafiya kaka” Kaka tace “Aa su dai su tafi, haka kawai bamu gama 

ganawa da d’a na ba kice in tafi” Mumy ta kauda kai bata ce komai ba, kaka tace “Sai dai ko kiyi ma Shureen 

magana ya ajiye su gida tunda ke baxai maki musu ba ni kuma sai ma ya iya xagina” Mumy ta d’an yi shiru, can ta 

saci kallon Heedayah, sai kuma tace “To dama dai driver na nan ne sai ya ajiye su, amma Shuraim kam nasan baxai 

je ba, ynxu ma na aikesa ya kai ma Sadiya sako yace baxai fita ba” Kaka ta rike ha6a tace “Wnn Sadiyar dai kinki 

rabuwa da ita har ynxu ko Maryam, bbu wanda fa bai san uwarta dillalliyar bokaye bace, kinsan uwarta kawar 

kishiya ta ce, to wllh bbu gidan bokan da basu xuwa lkcn Kaduna na daji, daga karshe ya kwabe masu shine kishiyar 

tawa uwarsu wnn yarinya da ta kusa sace min zinari jiya ta bani labarin komai, Kai har makabarta ta sha shiga ta 

binne laya a kabari, to in takaice maki a tsaye uwar Sadiya ta mutu kekam, ki gaya ma kowa wannan labarin kice in 

ji ni, a tsaye Talle ta mutu a bandakinta kamar tsohuwar soja, ta mutu da yan awanni kafin a ankara har ta kumbura 

suntum, toh ke dai kiyi hattara da kawance da Sadiya don barewa baxata yi gudu d’an ta yyi rarrafe ba, Kuma dai 

abokin barawo barawo ne, tale tale da nasan ki ke dai ko maganin tsari baki yrda da shi ba sai kice Allah ne me 

tsarewa, to yanxu dai ban san ya kik
e ciki ba gaskiya” Mumy dai sai danna wayarta take fuskarta bbu yabo bbu 

fallasa ta ki kallon kaka, Shuraim na tsaye bakin kofa tun fara labarin kaka hannunsa rike da makullin motarsa yana sauraronta, Mumy ta juya tana kallonsa bbu yabo bbu fallasa tace “Lafiya????” Yace “Xan je government house” 

Kaka tace “Atoh ka sauke min yaran nan a gida don girman Allah kar su fara min kuka, kuma me xaka je yi a 

gwamnet house?” Da sauri Mumy tace “Ae ba hanyarsa bace kaka” Kaka tace “Toh sai ya fara ajiyesu snn ya tafi 

gwamnet house din, Ina ruwana ni da xa ki ce min ba hanyarsa bane” Juyawa yyi yace “Su sameni a mota” daga 

haka ya fita parlon, Farida ta mike ta dau jakarta, kaka tace “Toh Allah ya kiyaye, kila anjiman ma Amadu ne xai 

ajiye ni gida” Farida tayi ma Mumy sallama tayi ma kaka sannan ta fita, Heedayah ta mike tsaye da kyar don tun 

fitowarta kitchen kanta ke juya mata, bata ce masu komai ba ta nufi kofa walking slowly, Mumy ta bi ta da kallon 

gefen ido har ta fita, kaka ta kyabe baki tace “Bana biye mata ba ta kai ni gaba gun Rakiya” Farida na tsaye bakin 

kofar fita main parlor tana jiran Heedayah, har ta iso kofar kallonta take, tace “What’s wrong?” Heedayah ta dafe 

kanta da kyar tace “I’m not feeling okay” Farida ta kama hannunta tace “Ciwon kai??” Heedayah ta girgixa mata kai 

kawai, Farida tace “Mu tafi gida sai ki kwanta, you will feel okay in sha Allah” tana rike da hannunta suka nufi 

motar Shuraim, har suka iso yana kallonsu ta madubi, Farida ta bude back seat Heedayah ta shiga ta kulle sannan ta 

xaga ta bude daya side din ta shiga ita ma ta kulle tana kallon Heedayah da ta hade kai da gwiwa tace “Sannu” 

juyowa yyi yana kallonsu yace “What’s wrong?” Farida tace “She said she is not feeling fine” Rufe motar yyi suka 

bar gidan, har suka isa gida bbu wanda yace komai cikin motar, yyi parking kofar gidan yana kallonsu ta madubi, 

Farida ta bude side dinta ta fita ta xaga ta bude bangaren Heedayah tace “We are home…” A hankali Heedayah ta 

dago kanta sannan ta sakko daga motar, Farida ta rufe tana kallon Shuraim tace “Thank you” Bai ce komai ba ta 

kama hannun Heedayah suka nufi gate, “Heedayah!!” a tare duk suka juya suna kallonsa, Farida ta sake hannunta, 

kamar me counting step dinta ta koma gun motar, yana kallon idanuwanta da suka kada yace “Me ya sameki?” Ta 

sunkuyar da kanta da kyar tace “Ina jin jiri, kuma ina son in kwanta” yace “Why?” Ta buda hannunta a hankali tace 

“Nima ban sani ba” yace “Tun da kika tashi yau kike jin jirin?” Ta girgixa masa kai, Bai kuma cewa komai ba, bayan 

few seconds yace “Go….” juyawa tayi taga Farida ta riga ta wuce ciki, ta nufi gate din, dishi dishi ta fara gani kafin 

ta karasa gate din, lkci daya ta kwala wani kara ta sulale a wajen. Mami ce xaune gefenta a kan gadon dakin, Junaid 

na ta daya side din a tsaye pressing his phone, sai Shuraim dake tsaye kusa da window ya rungume hannunsa, Farida 

ta shigo dakin rike da bottle water da glass cup, ta duka gefen Heedayah ta bude ruwan ta xuba a cup, Mami ta 

dagota tace “Gashi ki sha” amsa Heedayah tayi ta sha kadan, Mami tace “Ya ciwon kan?” A hankali tace “Ya daina” 

Mami tace “Toh Allah ya sauwake daughter” Junaid ya kalleta yace “Jirin fa?” Tace “Ya daina” Kofa Shuraim ya 

nufa ya fita, Heedayah tayi kasa da murya tace “Mami ina son inyi bacci ynxu” Mami ta kwantar da ita ta ja mata 

blanket tace “To yi baccin dear” Farida ta mike ta fita da ruwan, Junaid ya bi bayanta, sai da Mami ta ga ta fara 

baccin snn ta sauke curtain din dakin ita ma ta fita. Lkci lkci Farida ke shigowa dakin duba Heedayah dake ta bacci 

comfortable har kusan azahar, Farida tayi alwala ta fito bandaki ta tafi gaban mirror ta dau darduma dake kan 

kujeran mirror din taji vibration din waya, bude inda taji vibration din tayi ta daga dictionary ta dau karamin wayar 

tana kallo, bude ido Heedayah tayi ta mike xaune da sauri tace “Is it ringing??” Farida ta karasa kusa da ita ta mika 

mata wayar sannan ta juya ta fitaHeedayah ta daga kiran ta kai kunne amma bata ce komai ba, sallama yyi mata ta amsa sannan tace “Ina yini” yace 

“Lfya lau, how are you?” Tace “I’m fine” yace “Always not picking calls, why?” tace “Mun fita ne” yace “Xuwa 

ina?” Tace “Gidan Abbanmu” yace “Ohk” shiru tayi, shima yyi shiru, can yace “So you ain’t coming out anytime 

soon” ta jingina da pillow tace “Nima ban sani ba” yace “Yaushe xa ku koma schl?” Tace “In a week time” yace “Ina 

son mu hadu” bata ce komai ba, yace “Kin ji?” Tace “A ina?” Yace “Idan ma kince gidanku ae sae in xo” tace “Don a 

min duka?” Murmushi yyi yace “Aa ba wanda xai maki duka, now tell me a ina xan gan ki?” Shiru tayi, yace “Think about it, then u call me, wayar a bude take and akwai airtime a ciki, I will be expecting ur call” daga haka ya katse 

wayar, ta cire a kunnenta a hankali, bayan kusan minti biyar da gama wayar aka bude dakin junaid ya shigo, 

karasowa yyi gefenta yace “How are u feeling Heedayah” tace “Alhmdllh” yace “Bbu inda ke maki ciwo ko?” Ta 

gyada masa kai ba tare da ta kallesa ba, yace “Look at me Heedayah” juyowa tayi ta kallesa suka hada ido, yace “Me 

xa ki ci?” A hankali tace “Shayi kawai xan sha” yace “Ohk, no bread?” Ta girgixa masa kai tace “Aa bana so” 

juyawa yyi ya fita dakin, ta boye wayar da ta rufe da palm dinta karkashin pillow da sauri. Heedayah na gama shan 

shayin da Junaid ya kawo mata ta mike ta tafi yin alwala, bayan ta idar da sllh ta daga karkashin pillow ta dau wayar 

da ta boye ta mayar inda yake sannan ta dawo ta kwanta, nan da nan wani baccin ya kuma dauketa. sai after la’asar 

Heedayah ta fita dakin bayan tayi sllh, Mami na xaune parlor da wata colleague dinta suna hira, Heedayah ta 

gaishesu Mami tace “How are you feeling now” Heedayah tace “Da sauki” Barrister Khadijah tayi mata Allah ya 

sauwake ita ma sannan Heedayah ta wuce kitchen da cup din hannunta, Farida ce kitchen din tare da Zainab suna 

girka dinner, Farida ta juya tana kallonta tace “Ya jiki?” Heedayah tace “Na ji sauki, tuwo xa ku yi?” Farida tace 

“Shi Mami tace mu yi” Heedayah ta marairaice fuska tace “To ni me xan ci da daddare?” Dariya Farida tayi tace “Ba 

ga Indomie ba sai ki dafa” a hankali Heedayah tace “Mami baxa ta bari ba ai cewa xata yi sai na ci” Farida tace 

“Vegetable soup ne fa” Heedayah ta girgixa kai tace “Bana ci” Farida tace “Guess what Heedayah” Heedayah ta d’an 

bude ido tace “No plss tell me, kinsan I am not a good guesser” Farida ta wara ido tace “At last Mami tace I can go 

to Abuja tomorrow” Heedayah tace “Only you?” Farida tayi dariya tace “Kin ma san da ya ta bar ni, nace ke fa tace 

baki da lafiya baxa ki je ko ina ba” a hankali Heedayah tace “Ni ai naji sauki, don Allah Mami ta bar ni” Farida tace 

“Ki bari anjima sai kiyi mata magana” Heedayah tayi shiru bata ce komai ba, can ta juya ta fita kitchen din, Mami ta 

dawo daga rakiyar Barrister Khadijah ta xauna nan parlor tana kallon Heedayah da ta xauna kasa kan carpet tace 

“Are you sure bbu inda ke maki ciwo Heedayah?” Heedayah ta girgixa kai tace “Ba ko ina Mami” Mami tace “Toh 

Allah ya sauwake” Heedayah tace “Mami ai tare xa mu tafi Abuja da Farida” Mami tace “Noo you are going no 

where, tashi ki kai min system dina daki” Mikewa Heedayah tayi ta dau system din ta wuce sama, nan kuwa ji take 

kamar ta rushe da kuka. Bayan Magrib duk suna xaune parlor suna cin abinci banda Heedayah dake xaune tana kallo, 

Junaid ne ya shigo parlon bayan ya gaida Mami ya amsa gaisuwar da Farida ke masa, yana kallon Heedayah da ta 

gaishesa ita
ma yace “Why are you not eating?” Shiru tayi bata ce komai ba, Farida tace “Ae bata cin tuwo” ya kalli 

Mami, sannan ya kalli Heedayah yace “Me xa ki ci?” Mami tace “Bbu wani abinda xata ci, idan baxa ta ci tuwon ba 

ta bar shi, meye da tuwon da xata ce bata iya ci?” Junaid dai bai ce komai ba, can dai ya wuce sama, ba a dau lkci ba 

ya sakko sanye da jallabiya, yana shafa kansa yace “Mami frnd dina na jirana waje xan basa sako cikin mota” Mami 

tace “Idan ma gidanku ne ke jiranka a waje that’s not my concern, my only concern is that kar ka kuskura ka shigo 

min gidan nan da wani abinci” ya xaro ido yace “Abinci kuma? Abincin me Mami” Mami tace “I’ve told you my 

own” Bai ce komai ba ya nufi kofa ya fita gidan, Heedayah dai na xaune sai wasa da fingers dinta take, Farida sai 

murmushi take, Mami ta kara gyara xama parlon tana jiran shigowar Junaid daga wajen frnd din nasa, yana fita ko 

minti goma ba ayi ba aka bude kofar parlon, Shuraim ne ya shigo da sallama, ya karaso cikin parlon, Mami na 

kallonsa tace “Welcome” ya xauna sannan ya gaisheta, ta amsa tace “Ya aikin?” Yace “Yanxu xan wuce” tace “Night 

Duty kawai kake yi ne ynxu?” Yace “Aa amma na fi yin night din ne” Farida ta gaishesa ya amsa, Heedayah ta 

dauke kai murya can ciki tace “Ina yini” Bai ce komai ba, Mami tace “Ya mutanen gida?” Yace “Lafiya lau” Tace 

“Kaka ta koma can gidan Baffa ne?” Yace “Aa tana nan gida” Mami tace “Ohk” yace “Ya mai jiki” Mami tace “Aa ta 

ji sauki sosai” Yace “Allah ya kara sauki” Mami tace “Ameen, Farida ki kawo masa abinci duk da nasan he is full 

always” Shuraim yyi murmushi amma bai ce komai ba, Mikewa Farida tayi ta tafi kitchen, bayan wani lkci ta fito ta 

ajiye masa tray din abincin a gabansa, ya d’an bude warmer din, lkci daya ya rufe yace “Ai bana cin tuwo” Kallonsa 

Mami ta tsaya yi, can tace “Baka cin tuwo??” Yace “Bana ci” Heedayah ta gyara xama tace “Mami to ai kinga yanxu 

dai ba ni kadai ce bana cin tuwo ba, kince baki taba jin wanda baya cin tuwo ba, shi ma ba gashi baya ci ba, sai in je 

in dafa masa Indomie” sau daya Shuraim ya kalleta ya dauke ido, Mami tace “Kar Allah ya sa ya ci tuwon, Farida 

dauke min abincina ki mayar kitchen yunwa bai ishesu bane” Murmushi kawai Shuraim yyi, Mami tace “Tuwo ba 

dai da miyar kuka ba ko kubewa ace baxa a ci ba” Ya girgixa kai yace “Aa ni fa ina ci, don na koshi ne yasa nace 

bana ci” daga haka ya mike yace “Xan wuce” Mami tace “Allah ya tsare” ya nufi kofa ya fita, Heedayah ta bi sa da 

harara, can ta mike ta wuce sama kamar xata yi kuka. Shuraim na fita junaid ya shigo, yyi ma Mami sannu da xama 

ta amsa tana kallon hannunsa ya wuce sama. Karfe sha daya da wani abu junaid ya bude kofar dakinsu Farida, 

Farida tayi bacci Heedayah kuma na kwance cikin blanket tana waya da Khaleel, jin an bude kofa ta katse wayar da 

sauri, tayi still barin da taji an kunna switch din dakin, bayan few seconds ta sauke blanket din a hankali, mikewa 

xaune tayi tana kallonsa tace “Yaya” ya ajiye mata ledan hannunsa yace “Ga abincin” murmushi tayi masa tace 

“Nagode” ya daga mata gira yace “Good night” daga haka ya juya xai fita ya kusa cin karo da Mami, da sauri 

Heedayah ta mayar da kanta cikin blanket din, Ya fara kame kame ya ma rasa abinda xai ce ma Mamin tasa, Mami ta 

kalli ledan da ya ajiye sannan ta karasa ta bude ledan, takeaway ne na fried rice with full chicken lap, ga chivita 

drink, sai kuma tsire a wani takarda daban, mayar da ledan tayi ta rufe sannan ta ce “Toh fita” juyawa yyi ya fita dakin ta fita ita ma ta kulle, a hankali yace “Mami kiyi hakuri, naga bata da lafiya ne kuma kar ta kwana da yunwa, 

right from time kinsan bata cin tuwo” Mami tace “Kuma gaskiya ne, kai me conscience, ni kuma mara shi…” Da 

sauri yace “Aa wllh Mami ba haka bane” dakinta ta shiga, ya d’an yi jim sannan ya bi bayanta xuwa dakin, tace “Aa 

yi tafiyarka ka kwanta….” Yace “Kiyi hakuri Mami” kujera ta nuna masa tace “Sit” ba musu ya xauna, ta xauna 

gefen gado tana facing dinsa tace “Tell me, what is ur intention na makale ma Heedayah da kake yi ina hanaka 

amma baka ji” ya sunkuyar da kansa yyi shiru, tace “Answer me, xan kwanta ina da aiki gobe” Yace “Nothing Mami, 

matsayinsu daya da Farida” Tace “Good I hope it shouldn’t pass that Junaid…” Dago kai yyi yana kallonta tace “Yess, 

matsayinsu ya tsaya daya da Farida, tashi ka tafi good night” Yyi kasa da murya yace “But me yasa kika ce haka 

Mami?” Tace “Me yasa nace me?” Yace “Abinda kika ce” Tace “Ban gane tambayar ka ba” ya sauke idanuwansa 

kasa yace “But Mami….” Sai kuma yyi shiru, tace “But what?” Yace “I would have wished us to be together till end” 

Mami tace “As???” Jin ya ki cewa komai ta hade rai tace “Kaga you stop beating about the bush and save my time, 

go straight now” yace “Mami kawai Ina sonta, kuma Ina jin xan iya aurenta” Kallonsa Mami take bbu ko kiftawa, 

can tayi wani murmushi tace “Ita Shaheedar fa?” Ya d’an hade rai yace “Dama kece ke sonta ba ni ba” Tace “Haka 

kace?” Yayi shiru, tace “Toh ba da ni xa ayi wnn haukan ba, Shaheedah da maganarta ke kasa kusan shekara uku sbd 

selfish interest dinka kace min ni ke so ba kai ba….” Yace “Don Allah Mami ki bar maganan nan wllh bana jin xan 

iya auren Shaheedah, idonta ya bude da yawa, kuma I can’t marry someone living all alone abroad da sunan tana 

karatu” Mami tace “Fine then, idan kai ka haife kanka sai mu gani ai, ita Heedayar an gaya maka ikon mu ce??” Bai 

kuma ce mata komai ba, tace “I will advice you ka cire idonka a kanta don baxa ka ta6a samun ta ba, beside nawa 

take da har xaka ce kana sonta da aure, did you think xaka kara min shekara daya ne nn gaba, ba dai cikin shekaran 

nn Shaheedah xata gama ba, xaka sha mamaki” mikewa yyi yace “Sae da safe” tace “Allah ya tashemu lfya” daga 

haka ya fita dakin ya kulle mata kofa. Washegari da safe Farida ta gama hada few kayan da xata tafi da shi gidan 

yayarta a Abuja, Heedayah dai na xaune dakin duk ta xama abun tausayi, Farida ta koma kusa da ita tace “Ko xa kiyi 

ma Yaya magana yace Mami ta bar ki mu je tare” Heedayah ta share guntun hawayen idonta a hankali tace “Baxata 

bari ba, I know she is angry at him now bcos she caught him giving me food yesterday night” Farida tace “To yanxu 

wa xai yi mata magana ta ji? Nobody, cewa xata yi baki da lafiya” mikewa Farida tayi ta dau powder dinta a gaban 

mirror ta saka a handbag dinta kar ta manta, a hankali Heedayah tace “Ko mu gaya ma Ya Shureen yyi mata 

magana??” Farida ta juyo tana kallonta, dariya tayi sosai tace “He is not Shureen Heedayah, He is Shuraim” 

Heedayah tace “To ni ina ruwana ba Shureen naji kaka nace masa ba, ni dai mu yi masa magana koh?” Farida tace 

“Amma dai ke xa ki yi masa maganan” Heedayah tace “Ehh xan yi masa” Farida tace “Ina xa mu samo number sa?” 

Heedayah tace “Mami na da shi ai kamar, let me check” daga haka ta mike ta fita, a hankali ta bude kofar dakin 

Mami bata ganta a ciki ba, ta karasa gun wayarta da sauri ta dauka ta shiga contacts, searching sunan tayi sai ga shi 

ya fito with 080333…. Lkci daya ta haddace gaba daya ta ajiye wayar ta fice daga dakin, tana kallon Farida tace 

“Where is ur phone, I have crammed the digit” Farida ta mika mata wayarta Heedayah ta sa number snn ta 

marairaice tace “Are you sure we should call him Farida?” Farida tayi dariya tace “Yess try it, ki sa a handsfree in ji 

me xai ce” Heedayah ta xauna gefen gado xuciyarta na bugawa tayi dialing number, har ya gama ring ba a dauka ba, 

Farida dake ta kallonta ita ma xuciyar
ta na bugawa kamar ita xata yi masa magana tace “Redial it…” Heedayah ta 

kuma sending number ta sa handsfree tana xare ido, nan ma har ya gama ring no response, Farida ta ta6e baki ta 

cigaba da abinda take, a hankali Heedayah tace “May be baya daukan bakon number ko” Farida tayi mata wani kallo 

tace “As per shugaban kasa or governor dat he is ko???” Dariya Heedayah tayi, Farida ta ja tsaki tace “Ki je kiyi 

wanka may be Mami will change her mind idan ta ga mun shirya tare” A sanyaye Heedayah ta mike tace “Toh train 

xaku shiga?” Farida tace “Noo, Mami tace driver ne xai kai mu idan yace xai iya idan kuma baxai iya ba ban san 

yanda xa ayi ba” Bathroom Heedayah ta shiga bata ce komai ba, bayan kusan minti talatin ta fito daure da towel, 

wayar Farida dake kan gado ne ya fara vibrate, Heedayah ta xaro ido tana bin dakin da kallo don Farida bata nan, 

can tafi gun wayar tana gyara daurin towel dinta ta leka wayar taga number Shuraim ne, daukar wayar tayi xuciyarta 

na bugawa ta xauna gefen gado ta daga ta sa handsfree, sallama yyi daga daya bangaren ta wani xaro ido ta kasa 

amsawa, har sai da ya kuma yin sallama, kamar xata yi kuka tace “Uhn Ina ji” shiru yyi, a takaice yace “Waye 

wannan?” Ta kara gwalo ido tace “Ni ce fa” yace “Ke wa?” Ta turo baki tace “Ni mana” yace “Baki da suna?” Tace 

“Heedayah” Shirun 3 seconds yyi snn yace “Why are you calling?” Ta marairaice murya tace “Ya Shureen dama… 

dama” sai kuma tayi shiru, yace “Dama me?” A hankali tace “Dama Mami ce tace baxan bi Farida Abuja ba mu je 

gidan Maman Fadil, shine sai Farida tace ko xaka mata magana, shine na kiraka nake gaya maka” Yace “Faridar ta 

aiko ki wajena” ta xaro ido tace “Aa wllh, ba ta ma dakin ni kadai ce, na fito wanka yanxun nan sai naga wayar yana 

vibrate” yace “To baxa ki je Abujan ba” ta buda baki da farko, sai kuma ta fashe masa da kuka tace “Ya Shureen plss, 

wllh I want to go, ban ta6a xuwa ko ina ba tunda aka haifeni, nima ina son inje wani waje don Allah” Yace “Baxa ki 

je ba, xan xo kuma in gaya ma Mami bbu inda xa ki je” Daga haka ya katse wayar, Heedayah ta fashe da kuka ta 

ajiye wayar tana kallonsa tace “Wllh sai naje ina ruwanka da ni to” Farida ce ta shigo dakin tana washe baki tace 

“Guess what Didi, Mami tace mu je amma kwana uku kawai xa mu yi mu dawo sbda health status din ki” Heedayah tace “Toh bayan kin sa na kira wnn Shureen din yace baxan je ba din kuma xai xo ya gaya ma Mami kar a bar ni in 

je” Farida tace “Kai haba, da gaske??” Heedayah ta fashe da kuka tace “Wllh” Farida ta wani tabe baki tace “Toh ba 

sai ya hana ba mu gani, duk kece kika dage a kirasa xaki laka min kuma daga karshe, gwara ki tashi ki fara hada 

kayan kafin ma ya xo, Mami ta ma driver magana yace idan mun shirya mu fito” tashi Heedayah tayi tana share 

idonta ta dauko kayanta kala uku, Farida tayi kasa da murya tace “Make it Five, we are going to deceive Mami, sai 

ana gobe xa mu koma schl xata ganmu a gidan nan” Heedayah ta wara ido ta karo wasu kayan, Farida ta taya ta 

shirya kayan a jaka, ita kuma ta shirya cikin riga da skirt na atamfa ta daura dankwalin. Heedayah na gama shiryawa 

bayan ta fesa turare Farida tace “Ki tafi kice ma Mami thanks for allowing you, ni kuma xan kai mana kayanmu 

mota” Heedayah ta fita dakin ta shiga na Mami da sallama, Mami na xaune dakin tare da Junaid dake tsaye bakin 

mirror dinta ya rungume hannunsa, Heedayah ta kallesa tace “Ina kwana Yaya” yace “Lafiya lau” Heedayah ta 

karasa gun Mami tana murmushi tace “Mami thanks for letting me” Mami tace “Kwana uku kawai xa ku yi” 

Heedayah tace “Ehh Farida tace min haka” Mami tace “Kin sha drugs din ki? Kuma ki tafi da su kar ki manta” 

Heedayah tace “Toh” Mami tace “Ki kai cup din nan kitchen” Heedayah ta dau cup din da Mami ta sha tea ta fita, 

Mami tace “Kaga da ba don aiki ba da sai ka ajiye su, wani lkcn driver din nan na gudu sosai” Junaid dai bai ce 

komai ba, Heedayah na saukowa stairs aka bude kofar parlon, ido hudu suka yi da Shuraim, ta dauke kai da sauri ta 

karasa sakkowa ta shigo cikin parlon ta wani hade rai, wucewarta tayi kitchen ta tafi sink da cup din tana murguda 

baki, kamshin turarensa ta jiyo ta juya da sauri, ya karasa shigowa kitchen din yace “You have the guts ki wuce baki 

gaisheni ba koh” Ta marairaice tace “Allah sarki ya Shureen ba mun gaisa a waya ba, ai mun gaisa kuma Mami tace 

inyi sauri shi sa nayi sauri, amma idan na fito ai xan gaisheka dama, kayi hakuri don Allah” kallonta kawai yake yi, 

can ya juya ya fita, ta wani turo baki hade da murguda masa sannan ta bi bayansa, xaune ta samesa kan kujera, tayi 

kasa da kai tace “Ina kwana” yyi banxa da ita, wucesa tayi sai da ta isa stairs ta waigosa, hada ido suka yi, ta da’n 

xaro ido tace “Na gaisheka kuma baka amsa ba, Ina kwana” hade rai yyi yana kallonta tayi wucewarta sama da sauri, 

kin xuwa ta ce ma Mami yana parlor tayi, Ta shige dakinsu ta fara hawaye tace “Kinga har ya xo yace mata kar a je 

da ni ko” Farida ta xaro ido tace “Da gaske” Heedayah ta xauna gefen gado tana matsar kwalla tace “I hate him, ni 

na tsanesa” Zainab me aiki ce ta tafi ta gaya ma Mami tayi bako, Mami tace “Waye?” Zainab tace “Wannan sojan 

nan” Mami tace “Oh Shuraim, gani nan fitowa to” Zainab ta juya ta wuce, Mami na kallon junaid tace “I still don’t 

like the way u and Shuraim are interacting…. Kamar wasu strangers” Junaid bai ce mata komai ba, tace “Toh ni ka 

wani xo ka tsaya min a daki kamar Soja idan nayi maka magana kayi shiru kamar kurma, do you have any 

problem?” Nan ma dai bai ce mata komai ba ya juya ya fita dakin ta bi sa da ido, tabe baki tayi ta mike ta dau 

handbag dinta da wayarta ta sauka downstairs, tafiyar su Farida take son gani kafin ta wuce aiki dama, bayan sun 

gaisa da Shuraim tace “Daga gida kake ko gun aiki?” Yace “Daga asibiti nake” tace “Toh yau bari in kawo breakfast 

din da kaina kila kaci” Farida ce ta sakko da jakar Heedayah, Mami tace “Kuna ta 6ata min lkci” Farida tace “Mun 

gama” Daga haka tace “Ina kwana” tayi wucewarta, Shuraim yace “Lafiya” Mami tace “Wai Abuja xa su tafi gun 

third daughter na, suyi 3 days kafin resumption” yace “Ohk ita kadai?” Mami tace “Noo with Heedayah, ai duk da 

bata jin dadi ba damuwa taje ko?” Shuraim yace “Ki bar su su tafi, ai naga ta ji sauki” Mami tace “Aa da sauki sosai, 

Ina ga stress din bikin ne kasan bata saba da wahala haka ba, banda haka ana xaune lafiya me xai janyo tayi pass out 

haka nan” Shuraim bai ce komai ba, Mami tace “Driver nace ya ajiyesu, Junaid xai fita aiki yanxu da shi na so ya kai 

su” Shuraim ya kalli agogo da ke nuna tara da few minutes, ya d’an yi shiru kafin yace “Ohk should I drop them” 

Mami tace “Haba Noo, Kai da ka kwana asibiti kana aiki, bari a lallaba kawai driver din ya kai su” Shuraim yace 

“Xan kai su…” Da damuwa Mami tace “To aikin fa anjima, kaga xaka ba kanka wahala sosai” Yace “Aa ba wahala” 

Shiru Mami tayi tana kallonsa. Ko da Farida ta koma sama waya ta tadda Heedayah ke yi, Heedayah tayi shiru 

ganinta, daga daya bangaren Khaleel yace “Wa xai kai ku Abujan?” Heedayah tace “Uhm” shiru yyi kafin yace “Ohk, 

but you can leave where you are and talk to me” Farida ta dau handbags dinsu ta fita, Heedayah ta bi ta da kallon 

gefen ido, a hankali tace “Driver xai kai mu” yace “Yanxu xa ku fito?” Heedayah tace “Ehh mun ma kai kayanmu 

cikin mota” Yace “But can’t you convince them that ku bari ko nan da xuwa 12 ku taso?” Da mamaki tace “Saboda 

me?” Ya mike daga xaunen da yake a katon parlonsu yace “Convince
them plss Heedayah, hanyar nan bbu kyau 

ynxu” Tayi shiru sai kuma tace “How did you know that?” Yace “Stop questioning me, just kar ku fito yanxu” Ta 

hade rai tace “Bayan mun riga mun gama shiryawa kuma mun kai kaya mota, idan naje nace ma Mami hanya bbu 

kyau ai tambayata xata yi me ya faru da hanyar kuma wa ya gaya min, wa xan ce ya gaya min??” Shiru yyi yana 

sauraronta, ta turo baki tace “Ni dai ana jirana a parlor byeee” yace “Wait Heedayah….” Tsayawa yyi tana sauraronsa, 

yace “Don’t you no that kidnappers suna hanyar Abuja” da mamaki tace “To ai ba kullum suke fitowa ba….” Yace 

“Noo yau xa su fito” ta xaro ido tace “Ta ya kayi ka sani?” Yace “Na sani, bana son wani abu ya sameki kuma” tace 

“To me ya sa xa su fito yau din?” Yace “Akwai wani da suke targeting, yau xai bi hanyar…. So if they should meet 

people on road suna harbi ta ko ina ne” Heedayah ta bude baki lkci daya jikinta ya hau rawa tace “Su harbe mu??” 

Yace “Aa bance xa su harbe ku ba, but prevention is better than cure right?” Tace “Toh kai ya aka yi kasan they are 

targeting someone when you are not a kidnapper?” Ya d’an yi shiru kafin yace “Plan dinsu yyi leak ne” Bude kofar dakin aka yi Farida tace “Idan xa ki ajiye wayar nan ki ajiye ki fito mu wuce, ko wani karya yake tsara maki tun 

daxu haka” tsaki Farida tayi ta fita, Heedayah tace “Ni dai bye ana jirana” Daga haka ta katse wayar, sai dai banda 

faduwa bbu abinda gabanta yake tana naxarin maganan da yyi mata, then how did he know about kidnappers, ta bi 

dakin da kallo taga Farida ta sauka downstairs da handbag dinta balle ta saka wayar a ciki, wani karamin purse ta 

fito da ta saka wayar ciki snn ta dau mayafinta ta yafa, ta boye purse din a cikin mayafin ta fita dakin, corridor ta 

tadda Junaid a tsaye, ta sakar masa murmushi tace “Yaya xan yi missing dinka” a hankali yace “Are you sure” ta 

gyada masa kai, bude mata hannu yyi, ta bi corridor din da kallo kafin ta karasa ta basa light hug lkci daya kuma ta 

janye jikinta amma ta kasa kallonsa ta juya da sauri tace “Byee” har ta fara tafiya yace “Heedayah” tsayawa tayi 

amma bata juyo ba, ya karasa bayanta ya kamo hannunta ya sa mata kudi yace “In case you will want to buy 

chocolates” juyowa tayi tana murmushi tace “I appreciate, thank you so much” yace “You are welcome” daga haka 

ta sauka downstairs, Farida ta gani bakin kofa tsaye sai cika take, Mami kuma tayi forcing Shuraim yau dai yana 

shan just tea a gidanta, Heedayah na ganinsa ta daure fuska tace “Mami mun gama fa” Mami tace “Ku jira sa a 

compound” Heedayah ta karasa gun Farida suka fita compound din tare, Farida tace “Ke ki ji wai Shuraim ne xai kai 

mu Abujan” Still Heedayah tayi tana kallon Farida ko kiftawa babu, Can ta juya ta kalli motar Shuraim, sai kuma ta 

6ata fuska ta fara matsar kwalla tace “What about the driver?” Farida tace “Oho Mami har tace ya wuce kawai” 

Heedayah tace “How are we going to cope travelling with him?” Farida ta sauke ajiyar xuciya bata ce komai ba, 

Heedayah tace “Did he even know the way to Abuja?” Nan ma dai Farida bata ce komai ba, Heedayah ta jingina da 

mota ta turo baki tace “I just feel like giving up, who brought this idea” Farida tace “Ni ki daina min tambayoyi 

kamar yar jarida, I don’t know too” suna ta tsaye Farida ta jawo Heedayah tana perceiving jikinta tace “Ina kika 

samu turaren Yaya?” Heedayah ta xaro ido amma ta kasa cewa komai, Farida ta kara shinshina mayafinta tace “Wa 

ya baki turaren” Heedayah tace “Shine ya sa min wai ban sa turare ba” Farida tace “Lallai ko Mami baya ba 

turarensa, kinsan nawa ake sayar da turaren?” Fitowar Shuraim tare da Mami yasa duk suka yi shiru, Mami tace 

“Hope xaka kira Barrister ka sanar masa ko?” Shuraim yace “Xan kirasa” Mami tace “Ba don kar ku bata lkci ba 

kuma ai ya kamata su je can gidan suyi ma kaka sallama kasan halinta sai tace an walakanta ta ba a gaya mata ba” 

Shuraim yace “Aa ba sai an gaya mata ba, xan kira Abba in gaya masa” Mami tace “Toh shkkn, Allah ya kiyaye 

hanya, ya tsare ku da tsarewarsa, but plss drive carefully Shuraim” Yace “In sha Allah” Mami tace “toh jira ku ke a 

ce maku ku shiga motar ne” Farida ta bude back seat ta shiga, Heedayah ma ta shiga, Mami ta daga masu hannu tace 

“Toh Allah ya kiyaye hanya, ya kai ku lafiya my daughters” Duk suma suka daga mata hannu, Shuraim yyi mata 

sallama tace “Don’t forget to call barrister plss” yace “In sha Allah,” tace “But wait kana da fuel ko kawai ka tafi da 

motar nan” ta fadi tana nuna masa spare motar dake gidan tace “Daxu aka tafi fueling station aka yi full tank” yace 

“No nima full tank ne” daga haka ya tada motar suka bar compound din, Mami ta bi sa da kallo har ta daina ganinsu 

sannan ta koma ciki. Kafin Shuraim ya karasa titi ya kira Abba, bayan Abba ya daga yace “Abba xan je Abuja, 

amma yau xan dawo” Daga daya bangaren Abba yace “Me xaka je yi a Abuja, Anyway Allah ya tsare ka, safe trip” 

yace “In sha Allah, nagode” daga haka ya katse wayar, Mumy ya kira, tana dagawa bayan ya gaisheta yace “Mumy I 

will be going to Abuja now but anjima da yamma xan dawo” Mumy ta mike xaune daga kwancen da take tace “Me 

kuma xaka je yi a Abuja Aliyu, hanyar nan da ya xama abinda ya xama yan kidnapping sun yi yawa” Yace “Allah 

xai tsare” Tace “Ni dai duk sai naji hankalina bai kwanta da tafiyar ba, dama nayi mugun mafarki da asuba, aiki ne 

xai kai ka Abujan ko me?” Yace “Ehh” Tayi shiru, sai kuma tace “Dole sai kai?” Yyi murmushi yace “Ehh, ai yau 

xan dawo” tace “Toh ni dai don girman Allah har ka isa addu’a ya makale a bakin ka, wllh hanyar bashi da kyau 

kwata kwata Aliyu dama jirgin kasa ne bbu abinda xai daga min hankali, amma yau kaji an dauke wannan gobe kaji 

an dauke wancan ai da tashin hankali” Yyi kasa da murya yace “Ina tunanin xuciyar ki a tsarkake yake, kuma baki 

nufin d’an kowa da sharri, don haka ki kwantar da hankalin ki, in dai haka ne bbu abinda xai samu xuri’ar ki” Mumy 

da ta wani xaro ido tace “Uban me ya shigo da wnn xancen kuma, shi dama tsarkakken xuciya a goshi ake rubutawa, 

Ina ruwana da d’an wani da xan nufesa da sharri ni kuwa….” Yace “Aa misali na maki kawai…” Ta ja tsaki tace “Ni 

dai Allah ubangiji ya tsare min kai, ya kai ka lafiya ya dawo da kai lafiya, ya raba ka da sharrin mutum ko karfe, har 

ka karasa addu’a kada ya bace a bakinka” Yace “In sha Allah” daga haka ta katse wayar, ya ajiye yana d’an murmushi. 

Tun da suka fara fita cikin gari, Heedayah ke jin vibration din wayarta a jaka, Farida dake kusa da ita ma tana ji, 

Heedayah ta kalli Farida, Farida ta kalli Shuraim ta madubi idonsa na kan titi, Heedayah ta kai bakinta kunnen 

Farida murya can kasa tace “He has been calling tun daxu, I don’t know why, how should I pick” Farida ta kara 

kallon Shuraim snn ta fiddo nata wayar a jaka ta mika ma Farida a hankali tace “Ki sa number a nan sai kiyi masa 

text message….” Da sauri Heedayah ta bude zip din purse din ta rufe da gyalenta snn ta haddace number don har snn 

wayar na vibrate ta mayar jakar ta kulle sannan ta sa number a wayar Farida ta tura masa message kamar haka 

“Muna hanya, I can’t pick now” tana tura message din ta daga kai suka yi ido hudu da Shuraim da ya kallota, ya 

maida dubansa kan titi, a hankali cikin dubara ta koma gefe yanda ko ya kalli madubi baxai ganta ba sai dai Farida, 

ba a dau lkci ba Khaleel yyi mata reply yace “Kuna dai dai ina yanxu?” Heedayah ta kalli Farida, sai kuma ta jawota 

tana nuna mata text din, Farida ta bude hannu alamar bata sani ba, Shuraim yyi
breaking silence din motar yace Give me that phone u are holding” Heedayah ta xaro ido ta kalli Farida, Farida tace “Which phone, wayana ne fa” 

Yace “Ba da ke nake ba malama” Heedayah kamar xata yi kuka tace “Game fa nake yi” yace “Don’t let me repeat my 

self” Farida ta saka wayar flight mode snn to koma can gefe, Heedayah ta turo baki ta mika masa wayar, fixgewa yyi 

daga hannunta ya ajiye kusa da nasa wayar. Bayan tafiyar kusan minti arba’in tun fitowarsu gida, Heedayah ta kalli 

Farida, rufe taga idonta har ta fara bacci, a hankali tace “Ya Shureen amai nake ji” ya wani hade rai yace “Amai??” 

Sai kiyi a nan ai, waye xai tsaya kiyi amai” Shiru tayi bata ce komai ba, bayan wani minti sha biyar din ta marairaice 

da kyar tace “Wllh yana damuna sosai, ka tsaya plss xai taho” banxa yyi mata, ta rufe bakinta tana kakarin amai, a 

hankali ya fara slow down ya gangara gefen hanya yyi parking snn ya bude motar ya sakko ya bude side dinta, da 

sauri ta fito, ta xagayo ta duka gefen daji tayi ta kakalo aman amma ya ki xuwa, rungume hannu yyi yana kallonta, 

bayan few minutes ta dago da kyar tace “Kamar ya koma” ya wani hade rai yana kallonta, mikewa tayi ta sunkuyar 

da kanta, yace “Dama kika sake sa na tsayar da mota kika sauka sai dai ki samu wani da xai mayar da ke gida, that is 

idan har na tsaya ma kenan” ita dai bata ce masa komai ba, ya bude ta wajen da take xaune, ta shiga motar ya kulle 

sannan ya koma driver seat suka ci gaba da tafiya. Khaleel ne tsaye da 5 of colleagues dinsa, message ya shigo 

wayarsa, dubawa yyi ya ga daya daga excort din Mai neman takaran gwamna ne da suke targeting yau, ya bude text 

din mutumin ya ga kamar haka “Mun kamo hanya minti kusan hamsin kenan” Khaleel yyi masa reply “Ohk” sai 

kuma ya xauna ya xauna yana shafa kansa, Saif na kallonsa yace “Ya dai Brainiac??” Banxa Khaleel yyi masa. 

Heedayah dai sai mutsu mutsu take a mota, Shuraim kuma lkci lkci yake kallonta, daga karshe tace “Ya Shureen” 

banxa yyi mata, cikin rawar murya tace “Wllh amai xan yi yanxu, pls kayi hakuri ka tsaya” yace “Yi a wajen” ta 

fashe masa da kuka tace “Plss xai xubo” ya daka mata tsawa yace “Wai ance maki ana tsayawa a hanyar nan ne” 

cikin kuka tace “Toh Amai xan yi mana” yace “Kiyi a wajen” tace “Wayyo baxan iya ba” Farida dai sai baccinta take 

kamar warce ke saman gado, kuka Heedayah ta dinga yi a hankali, Shuraim sai duba inda xai iya tsayawa yake, cos 

he knows how risky the road can be, daga karshe dai ya gangara gefen titi ya tsaya, ya bude motar ya sakko snn ya 

xagayo ya bude mata tun kafin ta gama fitowa ta fara kwarara amai a wajen, ya ja baya yana yatsine fuska yana 

kallonta, ta duka wajen ta dinga kwarara amai, bude front seat yyi ya dau ragowar bottle water dake wajen, ya cire 

mata mayafin jikinta ya duka ya bata ruwan, ta fashe da kuka tace “Yaya har yanxu bamu kai ba, ni baxan iya tafiyan 

ba kuma gwara in koma gida na gaji” ya daure fuska yace “C’mon amsa ki wanke fuskar ki” kin amsan ruwan tayi, 

ya xuba ruwan a hannunsa ya dago kanta ya wanke mata fuskar, bayan ya gama ya dagata suka mike ya bude motar 

yace “Shiga” ta shiga motar ya mika mata mayafinta snn ya kulle ya koma driver seat, ta jingina da kujeran motar 

tana sauke numfashi. Khaleel yace “Oga na san abinda nake cewa, na kuma san abinda na gani, beside dole in a 

week time Mutumin nan xai koma Kano, we should let it till then” Oga Manga yace “Wani maganan bnxa kake haka 

Khaleel, bbu fa wasu excort din kirki tare da shi, daga motarsa sai na bayansa, shkkn… Komai ya xo cikin sauki knn, 

this is just the right time da ya kamata ayi duk abinda xa ayi, snn mun samu labarin babu wasu jami’an tsoro a hanya, 

Khaleel I am saying ku san duk ynda xa ku yi mutumin nn ya shigo hannun mu yau yau din nan, bbu wani excuse 

dinka da xai shige ni wllh, nan da wani lkci xa su isa kauyen nan da muka shirya, kuyi maxa ku fito kawai, you guys 

just have to hurry up….” Khaleel dake ta sauraronsa yace “Ohk” daga haka ya katse wayar, Zayyad yace “Wai yane 

Kayy, kwanan nn fa you are not just active, anya mace bata shigo rayuwar ka ba?? Kar fa irin abinda ya faru da 

Ishaq ya faru da kai, kana dai nan kuma duk muna kallo Arne ya harbesa….” Khaleel ya wani tabe baki yace “Ni ayi 

gunduwa gunduwa da ni” Da mamaki Zayyad yace “Kana nufin tambayar da nayi maka da gaske ne?” Khaleel yace 

“Wnn ba matsalar ka bace, all I want u all to understand here is that in dai har kuka fita yau din nan…. don ni dama 

bbu inda xanje and nobody can force me out, to ina me tabbatar maku da kyar xa ku sha, kuma sai an kama wasun 

ku, mu hadu a garin Abuja” daga haka ya fice duk aka bi sa da kallon mamaki suna ji ya fita da motarsa… Shuraim 

ya hade rai yana kallonta ta mirror yace “Meye hakan??” Da kyar tace “My head is turning me” yace “Turn it back” 

bata ce masa komai ba ta goge hawayen da ya makale mata ta jingina da motar, suna isa wani junction, yana kallonta 

ta madubi yace “Xa ki ci Ayaba” ta bi wajen da kallo taga masu ayaba, ta girgixa masa kai tace “Amai xan yi idan na 

ci” yayi parking ya sauka, ya siyo mata apples, Farida sai lkcn ta farka tace “Why are we not moving?” Heedayah ta 

langwabar da kai tace “Xai siya min wani abu” Farida tace “Daxu ba naga kina amai ba” Heedayah tace “Amma baki 

ce komai ba ko” Farida tace “Toh ba gashi har fuska ya wanke maki ba, ni kawai sae na ci gaba da bacci na” Tana 

fadin haka ta kara gyara Kwanciyarta, Shuraim ya dawo motar rike da ledan apples, with bottle water guda biyu, 

back seat ya bude ya ajiye xae rufe tace “Ya Shureen xan koma gaba” Bai ce mata komai ba ta sauko rike da abinda 

ya siya mata, ya rufe motar ya mika mata ledan ta amsa ta koma front seat, shi kuma ya shiga driver seat suka ci 

gaba da tafiya…. Sai karfe daya suka shigo garin Abuja bbu wani tashin hankali, Heedayah ta juya ta tada Farida, 

Shuraim ya hade rai yana kallonta yace “Ance maki dakin ki ne nan” Farida bata ko kallesa ba ta gyara mayafinta, 

yace “Wani anguwar xa mu” Farida ta fada masa, har suka iso gidan yayarta kuma bata sake bacci ba, da ganin 

anguwar dai kasan na manya ne sosai, driver ya bude masa gate ya shiga yyi parking, farida ta bude motar ta sauka, 

Heedayah ma ta sauka, Maman Fadil ta fito da mai aikinta da murna tana welcoming dinsu, gaisawa suka yi da Shuraim tace “Bismillah, ka shigo ciki” yace “Aa xan juya ne” tace “Haba don Allah” yace “In sha Allah” Heedayah 

tayi wucewarta ciki tare da Farida ya bi ta da kallo, can yyi ma Maman Fadil sallama yyi reverse.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *