HEEDAYA CHAPTER 31 BY By Khaleesat Haiydar

HEEDAYA CHAPTER 31 BY By Khaleesat Haiydar

Www.bankinhausanovels.com.ng 

House maid din Maman Fadil suka bari da shigo masu da kaya, Heedayah ta xauna babban parlon da ya kayatu da 

kayan alatu, Farida tace “Ta so mu wuce ciki” Heedayah tace “Ae ba mu gaisheta ba” Farida tace “Wlh I am so tired 

xata biyo mu daki” Ita dai Heedayah bata tashi ba, Farida tace “To sae ki sameni daki ni dai” daga haka ta wuce, lkci 

daya ta juyo tace “Innalillahi, baki amsar min wayata gun Shuraim ba” Heedayah ta bude ido tace “Lah, kuma gashi 

ya wuce” Farida ta hade rai tace “Why are you talking as if it’s normal, wayana ne fa da nake amfani da shi, kuma 

duk xaman da kika yi gaban motar xa ki ce baki kallon wayar??” Heedayah bata ce mata komai ba sae tabe baki da 

tayi, Farida ta ja tsaki ta dawo cikin parlon ta dau wayar yayarta ta nufi kofar fita, a bakin kofa suka hadu, Farida 

tace “Aunty don Allah ki bude min, I want to make phone call, Shuraim ya tafi da wayata” Maman Fadil tace “Ohh 

shi ne Shuraim din dama?” K’in cewa komai Farida ta yi, yayar ta amshi wayar ta bude mata lock, Farida ta karba ta 

juya ta koma gun Heedayah tace “Tunda har kin haddace number sa sae ki sa min ni dai” Heedayah tace “Toh da na 

haddace number akwai abinda nace xanyi da shi ne, ko amfanin me xai min” Farida tace “Oho” Heedayah ta tabe 

baki ta amshi wayar ta saka number Shuraim ta mayar mata, Farida tayi dialing, sae da ya kusa katsewa ya daga, 

tace “Ni fa amfani nake yi da wayata kuma ka tafi da shi” yace “So??” Tace “Ka dawo in amshi wayata kawai” Yace 

“I see, idan na baki wayar a kaduna kar ki amsa” daga haka ya katse wayarsa, Farida ta kalli screen din da sauri, 

Maman Fadil tace “Me yace maki” Kamar xata yi kuka tace “Maganan banxa fa yyi min” Da mamaki Maman Fadil 

tace “Maganan banxa kuma” Farida tace “Ehh mana ai haka yake, ni dai Aunty ki yi masa magana don Allah ya 

maido min da wayata tun bai yi nisa ba, ni wllh baxan iya xama gidan nan bbu wayata ba” Maman Fadil tace “To ke 

garin yaya wayar ki ya je hannunsa” Farida tace “Ba ga warce ke amfani da shi ba ya amshe” Maman Fadil tace 

“Toh don tana amfani da waya sai ya karba, an hanata rike waya ne?” Farida tace “Ina fa, shi dai ne ya hanata 

rikewa” Maman Fadil ta amshi wayar ta sake dialing numbersa ta kai kunne, yana dagawa tace “Haba Yaya Shuraim 

ayi hakuri da su pls, ynxu dai kana ina sai in tura driver ku hadu ya amso wayar kawai” shiru tayi tana sauraronsa 

sannan tace “Toh shkkn, ba damuwa, nagode” Daga haka ta katse wayar, Farida ta wani xumburo baki tace “Me ya 

ce” Maman Fadil tace “Yace bai ma tafi ba tukun, idan bai dawo ba xai kirani in turo driver din ya amsa wayar” 

Farida ta wani tabe baki tayi wucewarta daki, Maman Fadil na kallon Heedayah tace “Deedayar kaka an xama ‘yan 

mata, ya gajiyan hanya?” Heedayah tayi murmushi tace “Alhmdllh” sannan ta gaisheta, Maman Fadil ta amsa tace 

“Ya su Mami da Yaya” Heedayah tace “Duk suna gaisheku” Maman Fadil tace “Toh muna amsawa, ki shiga ciki kiyi 

wanka kiyi sllh, sai ku sakko ku ci abinci” Heedayah ta mike tace “To, ina Fadil?” Maman Fadil tace “Yana can 

neighbors dinmu” Heedayah tace “Ohk” snn ta wuce ciki ita ma. Heedayah na kwance dakin Farida ta fito daga 

wanka ta shirya ta dau darduma xata yi sllh, Heedayah ta mike xaune tace “You are taking it personal as if ni nace 

Ya Shureen ya amshi wayar ki” Farida bata tanka ta ba ta fara sallarta, Heedayah ta tabe baki ta mike tsaye ta cire 

kayanta snn ta wuce bandaki, tana fitowa wanka taga Farida ta fita dakin, ta shirya cikin doguwar riga mara nauyi 

snn ta saka hijab dinta ta shimfida darduma ta fara sllh. Bayan ta idar ta mike ta dau purse dinta ta bude ta ciro waya, 

miss calls din Khaleel ta gani da yawa, tayi dialing number, yana fara ring ya daga, tace “Ina yini” yace “Lafiya lau, 

kun isa Abujan ko?” Tace “Ehh mun kai” yace “Ya hanya” tace “Lafiya lau kuma bbu abinda muka gani a hanyar, ba 

wasu kidnappers din da kace” D’an murmushi yyi yace “Da gaske?” Tace “To kai so kayi ayi kidnapping din mu 

dama?” Ya girgixa mata kai yace “Idan aka yi kidnapping din ki ai ni aka yi kidnapping” Tace “Ban gane ba” Yace 

“Tun da dai you arrived safely shkkn” Ta tabe baki bata ce komai ba, yace “Ke da wa ma ku ka tafi Abujan??” Tace 

“Ni da Farida, da Ya Shureen, shi ya kawo mu” yace “Waye shi?” Tace “Ba na ta6a gaya maka ba, yaron Abbana ne, 

yayanmu ne” Ya d’an yi shiru, sai kuma yace “Ohk soldier din nan?” Tace “Ehh” yana gyada kai a hankali yace “I 

see… shi ma a Abujan xai kwana yau kenan?” Tace “Aa yana da night duty, he is going back to Kaduna” yace 

“When?” Tace “Yau din nan” yace “Nasan yau din nan , karfe nawa nufina xai tafi” tayi shiru snn tace “Nima ban 

sani ba” yace “Are you still together with him now?” Tace “Yess” yace “If he is going ki gaya min, Kar ki manta….” tace “Saboda me xan gaya maka??” yace “Nothing, bana son in kira ki yana nan ya gani, so idan kika ce min ya tafi i 

can call anytime” ita dai bata ce komai ba, yace “Heedayah” tace “Ina ji” yace “Me yasa kika yi shiru” tace “Aa ba 

komai” yace “Ohk, gidan wa ku ka je a Abuja” tace “Gidan yayar mu” yace “Toh ki bani address din wajen” tace 

“Sbda me?” Yyi kasa da murya yace “Baki son ganina kenan!” Ta turo baki tace “Toh ni fa I still don’t know why we 

are together, Ina ce parent dina xaka nemo min kace??” Murmushi yyi yace “Su xan nemo maki in sha Allah” Tace 

“You are not making effort, kawai dai kai kana son mu dinga haduwa ne” yace “Noo Heedayah, tunda ba tare muke 

dake ba ai you won’t see my effort, you are only desperate to meet with ur parent shi yasa kike ga I am not making 

effort, but trust me dear tunda nace xa ki ga iyayen ki, xa ki gansu” ta d’an yi shiru kafin tace “Ohkk” yace “Good 

gal, send the address via Sms now” tace “Toh” katse wayar tayi, ta mike ta fita daga dakin, Farida na parlor tare da 

yayarta sai Fadil da wata yarinya da baxata wuce shekara uku ba suna wasa da Fadil dake xaga parlon a kekensa 

tana biye da shi da katon doll dinta, Maman Fadil na duban Heedayah tace “Kinyi sllhn?” Heedayah tace “Ehh na 

yi” Maman Fadil tace “Toh ga abinci an kai maku dining area, na samu labarin baki cin tuwo ko…” Heedayah tayi 

murmushi ta sunkuyar da kanta bata bata amsa ba, ganin ta nufi kofa Maman Fadil tace “Ina kuma xa ki?” Heedayah 

tace “Ina xuwa” Bin ta suka yi da kallo da Farida har ta fita, Can gun mai gadi ta nufa tana kallonsa ya mike ya bude 

mata gate din gidan, fita tayi ta duba address dake manne daga gefen gate, ta bi anguwar dake dauke da manyan 

gidajen gaske da kallo, lafiyayyen titi ne malale anguwar, ko wani gida da flowers xagaye da shi masu kyau, 

tsayawa kallon katon gidan dake kusa da na su Mama
n Fadil tayi, don gidan har ya fi nasu girma da haduwa, taji 

muryar Farida a bayanta tace “What are looking for outside Heedayah?” Heedayah ta juyo da sauri tace “Nothing” 

Farida ta rungume hannunta tace “Hope you are not trying to give anyone address to this house?” Heedayah ta bi ta 

gefenta ta wuce ciki tace “Not at all pls” daga haka ta nufi entrance din gidan Farida ta bi ta da kallo. Heedayah bata 

wani ci abincin kirki ba ta wuce sama xuwa dakin da suka sauka ta dau wayarta ta tura ma Khaleel text din address 

din gidan snn ta kwanta ta rufe ido kamar me bacci tana nan a haka har aka yi la’asar snn ta mike ta shiga bandaki 

tayi alwala ta fito, da sauri ta dau wayarta kafin ya katse, tace “Have u seen it?” Daga daya bangaren yace “Sure, Ina 

ta jira baki gaya min ko Yayan naku ya bar Abuja ba” Heedayah tace “He is not leaving today” yace “Why?” Tace 

“Haka nan kawai, may be tare xa mu koma” Jin Khaleel yyi shiru tace “Xan yi sllh, sai anjima” katse wayar tayi ta 

mayar cikin purse dinta, bayan ta idar da sllh ta sauka parlor, bbu kowa parlon sai su Fadil, ta karasa gun su da sauri 

ganin fada suke, ta riko Fadil tace “Me tayi maka Fadil? What happened??” Muryar Mum dinsa taji daga sama tana 

cewa “You’ve started fighting her ko, to gobe in ji kace a kai ka wajenta, baka da kirki wllh” kamar xai yi kuka yace 

“Mumy she is pushing my bicycle, why will she? did i push her fat doll??” Heedayah dai na rike da hannun yar 

yarinyar dake ta kallon Fadil hawaye makale idonta, ta dau hularta da ya fadi kasa ta rufe mata dogon gashinta da 

shi tana bata hakuri, yarinyar na nuna sa cikin rawar murya tace “You are not my frnd any longer” Maman Fadil ta 

sakko ta karbe hannunta daga na Heedayah tace “Yi hakuri kin ji Islam, don’t cry” Farida ta shigo parlon tace “Aunty 

yarinyar waye wai, ban ta6a ganinta ba, yar me kyau da ita” Maman Fadil tace “Yarinyar makociyata ce, shi ke 

makale mata fa, amma idan ta shigo yyi ta mata walakanci, bini bini kya ji yace xai tafi gun islam” tuni Fadil ya 

wuce sama kamar Soja a dole yyi fushi, Maman Fadil tace “Heedayah ku kai ta gida da farida yanxu tana fara kuka 

bbu me iya lallashinta a nan” Heedayah tace “Wani gidan ne nasu?” Maman Fadil tace “Ku tambayi Mai gadi idan 

kun fita” Heedayah ta dau doll dinta ta mika mata yarinyar ta amsa sannan suka fita tare da Farida don kai ta gidansu, 

kiris din ya rage Islam ta fara kuka, bin su kawai take tana makale da doll dinta, suna fita gate Mai gadi ya nuna 

masu gidan nasu, suka kwankwasa gate Mai gadin gidan ganin tare suke da Islam ya bude masu yana kallon 

Heedayah suka shiga cikin gidan, shi ya nuna masu inda xa su bi, babban gida ne na gaske me dauke da duplex biyu, 

motoci ne a duk parking space uku dake compound din da ya kawatu da flowers ta ko wani angle, suka danna bell 

bayan few minutes aka bude kofar, gaisheta suka yi, ta amsa tana masu sannu da xuwa sannan ta amshi hannun 

Islam tace “Tana daya bangaren mamanta, Bismillah ku shigo yanxu xata fito” Farida tace “Aa, muna dai gaisheta, 

sai anjima” daga haka suka juya suka nufi gate suka bar gidan. Heedayah na xaune saman darduma ta idar da magrib 

jin wayarta na vibrate ta kalli Farida dake sllh, mikewa tayi ta bude purse din ta ciro wayar snn ta daga ta kai kunne, 

daga daya bangaren yace “Ina waje” ta xaro ido ta d’an kalli Farida, sai kuma tace “Ohk” katse wayar tayi ta ajiye, 

haka nan kawai taji kamar an cire mata tsoro a ranta, taji she is not even afraid of anyone, taji kuma she wants to 

meet with Khaleel, tana ta xaune dai har Farida ta idar da sllh ta mike ta fita dakin, sannan ita ma ta mike tana rike 

da gyalenta da ta linke ta sauka parlor, tsaye ta same farida inda take shiga ba nan take fita ba, yayarta dai na xaune 

tana feeding din Fadil tana kallonta, cike da fada tace “Kuma wllh idan ya koma da wayata baxan sake amsar wayar 

ba ko an bani, dubi fa yanda na wani xauna tun rana kamar marainiya ba waya, nasan kuma ana ta kirana, ba sai ya 

bari driver yaje ya amso min kayana ba dama idan ba niyyar tafiya yyi da shi ba” kamar xata yi kuka ta kare 

maganar, Maman Fadil tace “Toh bari a kara kiransa amma Ina jin bai tafi bane da xai tafi ai xai kira yace in turo 

driver haka muka yi da shi” Farida tace “Lallai baki san waye shi bane Aunty wllh da gangan ma sai ya iya tafiya da 

wayar don in ji haushi, ai kinga ita da ta janyo ya amshe wayar har yanxu bata ce min komai ba as if fault dina ne, 

kuma har komawa tayi gaban motar fa ban san me ya kai ta can ba ta xauna, kuma sai tace bata ga wayar ba a kusa da ita???” Heedayah dai ko kallonta bata sake yi ba tayi hanyar kitchen, Mai aiki ce ta fito kitchen din ta gama 

wanke wanke, Farida ta bi Heedayah da wani shegen kallo har ta shige kitchen din, Maman Fadil tayi kasa da murya 

tace “Ni gaskiya bana son haka Farida, xata ga kamar don ta biyo ki ne kike mata haka, tun rana sai masifa kike 

mata gashi ta ki kulaki, bata ce maki komai sai masifa kike, wnn bai yi ba dai” Farida tace “Wa?? Kin xata wai ta 

rasa abinda xata ce ne yasa tayi shiru, ai ko xan kwana ina yi baxata tanka ba kuma baxata bani hakuri ba, taurin kai 

ne da ita da kike ganinta haka, wllh nasan kila da gangan ta bar masa wayar dama naga sai wani shisshige masa 

take” Maman Fadil tace “Shisshige masa ta ya kuma?” Farida ta xauna fuska daure tace “Ohon masu” Murmushi 

kawai Maman Fadin tayi ta dau wayarta tace “Bari dai in sake kiransa” dialing Number Shuraim tayi ba a dau time 

yana ring ba ya daga, gaisawa suka yi tace “sai muka ji shiru Yaya Shuraim…” Ta gama sauraronsa snn tace “Toh 

shkkn ba matsala, Allah ya tsare” katse wayar tayi ta ajiye, Farida ta xumburo baki tace “Wai me yace??” Maman 

Fadil tace “Jarabbiya to yana hanya xai kawo maki ynxu” da mamaki Farida tace “Toh me yasa bai koma ba??” 

Maman Fadil tace “Kilan ya gaji ne, kamar ma bacci yake, Amma yace xai taho ya kawo ynxu” Farida ta tabe baki 

bata dai ce komai ba. A hankali Heedayah ta bude kofar dake kitchen da xai sada ka da bayan gidan ta fita snn ta 

jawo kofar very careful kar yyi making ko wani sound snn ta yafa veil dinta ta fara tafiya da sauri, ta jikin parking 

space ta raba har ta isa gate, ganinta mai gadi ya fito dakinsa da sauri yace “Fita xa ki yi Hajiya?” Ta gyada masa kai, 

ya bude mata gate din ta fita, tana fita ta juya ta kallesa don tsayawa yyi ya ki komawa ciki as if wanting to know 

where she is going, ta hade rai, sau daya ta kalli motar da ya tsaya shi daya a layin da hasken fitilu ya haska kamar 

ba dare ba, ta san Khaleel ne duk da ba motar da ta saba ganinsa da shi bane don wnn har ya fi wancan haduwa 

amma bata tsaya ba tafiyarta kawai take, can ta ji Mai gadi ya kulle gate din ta juya taga ya koma ciki, A hankali 

Khaleel ke tafiya har ya tsaya dai dai flowers din gidan da suka kai islam daxu amma ta opposite, Heedayah ta sake 

juyawa tana kallon gate din gidan da ta fito snn ta nufi motar, sauke tinted glass dinsa yyi ta xagaya ta bude front 

seat ta shiga ta rufe. Khaleel na kallonta murya can kasa yace “Hope u took permission before coming out?” Ta 

girgixa masa kai ba tare da ta kallesa ba, yace “Why?” Ta turo baki bata ce komai ba, yace “Heedayah” daga manyan 

idanuwanta tayi ta kallesa tace “Don a min fada?” Yace “Toh ai ba a gida kike ba, kuma yawanci xa ki ga aunties 

usual don’t have much problem, da yawa idan mace na son haduwa da saurayinta kuma ba a barin ta fita a gida, ta 

kan hada baki da yayarta ko aunt dinta sai ta xo gidan aunt din nata su hadu, kuma bbu wanda xa
i sani sai daga ita 

sai aunt din, so wnn ma da kin gaya mata baxata hanaki ba” Heedayah ta wani kallesa tace “To kai saurayina ne?” 

Shiru yyi yana kallonta, can yyi murmushi ya girgixa mata kai yace “Aa” ta dauke kanta, yace “Amma duk da haka 

da kin gaya mata, ko da yake naga kin fiye tsoro ke din” Tace “Not when Farida is there xan gaya mata, Beside it’s 

not as if mun saba sosai da ita, na fi sabawa da kanwarta Aunty Fatee” yace “Ohk wnn baki santa ba?” Tace “Aa na 

santa, tana xuwa once in many month tayi two days” yace “Ohk how about her husband?” Tace “Yana UK shi” 

Khaleel ya gyada kai bai ce komai ba, ya ciro wayarsa dake vibrate a aljihunsa, Zayyad ne ke kiransa ya mayar da 

wayar ya ajiye har ya katse, tun yana hanya Zayyad ke kiran nasa yaki dauka, ya kalli Heedayah yace “Hope kin ci 

abinci?” Ta nuna masa wayarsa da aka sake kira tace “Pick ur call” Ba musu ya daga ya kai kunne bayan ya rage call 

volume din, Daga daya bangaren Zayyad yace “You caused everything Khaleel, you just ruin everything, da ka bi 

mu wllh wllh duk wannan abinda ya faru baxai faru ba, and mind you Oga Manga na neman ka yanxu haka, just 

don’t show up anytime soon…” Calmly Khaleel yace “Me ya faru?” Zayyad yace “Abinda ya faru shine an harbe Saif 

and he is dead, mu hudu muka fita dama, kuma we weren’t early enough don har target dinmu sun wuce exact 

village din that’s conducive for the operation, and u caused everything, so muna dai tafiya not knowing an kafa wani 

check point a gaba sbda robbery da aka yi a wajen da asuba har an kashe wasu, da mun san da check point din da 

baxa muyi attacking dinsu ba a particular area din da muka yi attacking dinsu, everything wasn’t in our favor today, 

mun sha ne da kyar… It wasn’t funny Khaleel, kuma duk kai ne ka ja komai, Oga Manga na nemanka yanxu haka” 

Khaleel da yyi shiru yana sauraronsa yace “Tough day indeed” daga haka ya katse wayar ya sa flight mode ya ajiye, 

Wani mota ne ya shigo layin ya haskosu, da sauri Heedayah ta dukar da kanta, Khaleel ya dage glass din motarsa 

yana bin motar da ido, dai dai gidan dake opposite dinsu motar ya tsaya Mai gadi ya wangale gate, a hankali 

Heedayah ta dago kanta motar ya shiga gidan aka rufe gate din, kallonta Khaleel yyi yace “Kin taba xuwa layin ne 

da kike boye fuskarki?” Ta girgixa masa kai, xai yi magana wani motar ya kuma shigowa layin, Heedayah ta xaro 

ido sosai tace “Yaya Shureen” rufe fuskarta tayi da gyalen jikinta, Khaleel ya dinga kallon motar har ya iso inda 

motarsa ke tsaye, Heedayah ta dago kai ita ma a hankali ta bi motar da kallo, dai dai gate din gidan Maman Fadil yyi 

parking, Heedayah na kallon Khaleel kamar xata yi kuka tace “Did he see me?” Girgixa mata kai yyi yace “Tinted 

glass ne ai” Ta juya ta sake kallon motar Shuraim ta ga ya sakko daga motar sai da ya fara kallon motar Khaleel snn 

ya tafi ya kwankwasa gate din gidan, Heedayah ta marairaice tace “Kila ya gan ni fa” Khaleel yace “How? is he 

having tinted eyes?” Tace “Ni dai mu je gaba to” driving din motar yyi yana tafiya a hankali har ya bar layin gaba 

daya. Kallonta yyi yace “Ina xa mu je” tayi shiru gabanta na faduwa, sai kuma ta ji kamar an cire mata tsoron gaba 

daya, ta jinginar da kanta da kujeran motar a hankali tace “Anywhere

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *