HEEDAYA CHAPTER 32 BY By Khaleesat Haiydar
Shuraim na shiga gate din gidan ya hadu da Farida xata fita ita kuma, komawa baya tayi ganinsa, ya mika mata
wayarta, ta amsa kamar dai baxata ce komai ba sai kuma tace “Thanks” juyawa yyi xai fita, har xata yi magana sae
kuma tayi shiru sai da taga ya fita gate din sannan ta leka waje, da ido ta hau surveying din street din, mamaki ne ya
cikata ganin bata wani ga alamar Heedayah ba, to ina ta tafi, suka hada ido da Shuraim da ya bude motarsa ya shiga,
ta dauke kai ta shigo cikin gidan tana kallon Mai gadi tace “Don Allah warce muka xo gidan nan daxu tare ta fita
ne?” Mai gadin yace “Ehh ta fita” Farida ta fita gate din gaba daya tana sake bin layin tun daga saman sa har kasa da
kallo, banda motar Shuraim bbu wani mota dake waje a wajen bbu kuma alamar mutum a layin, ganin kallon da
Shuraim yake mata daga cikin mota ta juya xata koma ciki, taji yace “Come here, who are you looking for??” Shiru
tayi bata son ce masa Heedayah take nema ta ja mata, can ta kallesa a takaice tace “Nobody” bata jira cewarsa ba ta
shige ciki. Gun yayarta dake xaune parloe ta koma tace “Aunty ban ganta ba fa” Maman Fadil ta mike da mamaki
tace “Baki ganta ba kuma, to ina ta tafi?” Farida tace “Wllh ban sani ba kuma me gadi yace ehh ta fita gate” Kasa
cewa komai Maman Fadil tayi tana kallon Farida, Farida tace “And ni ban ga kowa a layin ba” Maman Fadil ta xaro
ido tace “Toh kar dai bin wani tayi tunda kince kinji tana waya da saurayi” Farida ta girgixa kai tace “Noo Heedayah
will neva follow him, ni na santa baxata yarda ta bi sa ba” Maman Fadil tace “Yau Naga ikon Allah, to idan ba bin sa
tayi ba guduwa yyi da ita? Waye shi din, ke kin san sa ne?” Cike da damuwa Farida tace “Ni ban wani san sa ba wllh,
kuma fa bbu wanda ya san ya bata waya, nima bata gaya min ba kawai gani nayi tana ta boyewa, I am just confuse,
ina Heedayah xata je da daddaren nan” Bude baki Maman Fadil tayi tace “Na shiga uku ace a gidana, ita Hadiyar
dama haka take? Daga xuwa garin mutane sai ki bi saurayi ku yi tafiyar ku, duka duka nawa take da xata aikata wnn
aiki, ko kece kika bi saurayi daren nan ba sai Mami ta kusa balla ki ba balle ita, ni yanxu matsala xa a ja min kawai
wllh, ta ina xan fara wani bayanin yanda aka yi, kamar wasa kawai a nemi yarinya a rasa” Fita tayi daga parlon
Farida da duk jikinta yyi sanyi ta bi bayanta tana tunanin anya mutumin nan ba guduwa yyi da Heedayah ba kuwa,
Banda haka ai duk abun Heedayah tasan baxata yarda ta bi sa da daddaren nan ba, tunanin hakan yasa xuciyarta ya
tsinke taji tsoro ya kamata sosai, Maman Fadil ta tafi gun mai gadi tace “Mukhtar ka ga fitar bakuwata da daren nan
kuwa?” Yace “Ehh nine ma na bude mata gate” a mugun fusace Maman Fadil tace “Don me xaka bude mata gate da
daddaren nan ba tare da izini ba” Yyi kasa da murya yace “Kiyi hakuri Hajiya naga ba yarinya bace shi yasa na bude
wllh, na xata ko tadi xata fita” Maman Fadil ta bude baki with much surprise, can tace “Toh da ta fita ina kaga tayi?”
Yace “Toh da ta fita naga dai kamar bata ji dadin kallon da nake mata ba, sai naga tayi can, nan kuma so nayi inga
inda xata ne, Amma dai da wata mota da naga anyi parking a kofar gidan Honorable, ni dai sai na koma ciki na
xauna sai da wnn bawan Allah ya xo na sake bude gate din to ko da na leka waje gaskiya ban ga motar ba kuma, ita
ma ban ganta ba” Maman Fadil tace “Innalillahi wa Inna ilaihi raji’un, haka dama Hadiyar take Farida, ki shiga
motar saurayi a garin da ba naku ba ki bishi kuyi tafiyar ku?? Yanxu me xan ce ma Mami” Farida dai ta kasa cewa
komai gaba ta tsorata ne sosai, Maman Fadil ta juya ta nufi hanyar shiga parlor tana cewa “Toh kuwa bari in kira
Mami bbu wanda xai ja min matsala gaskiya” da sauri Farida ta bi bayanta tace “Noo plss don Allah aunty kar ki
kirata, Mami won’t take it likely with her, mu jira sanda xata dawo sai kiyi mata fada ke, don Allah Aunty kar ki kira
Mami” Maman Fadil tace “Ya xa ki ce kar in kirata, wnn ai ba abinda ya kamata a boye bane, ya kamata a sanar ma
Mami, gaba daya nawa take? Ta wuce 17 wnn da ganinta, amma ita har tayi wayon bin saurayi da daddare ba ma da
rana ba, kai ko da rana ne hukunci me tsauri ya kamata ayi mata balle da daddare, samarin Abujan nan masu lalata
yan mata, a gidan ubanwa ta san sa ma, snn kince Mami ma bata san da waya hannunta ba, ni bbu wanda xai xo ya
ja min matsala daga ke har ita wllh” Farida dai ta ma rasa bakin magana, Maman Fadil ta xauna parlor sai dai bata
kira Mamin ba, hankalin Farida ya d’an kwanta sai kallon agogo take tana addu’a, tana fatan Allah ya sa Heedayah ta
dawo anytime from now, yanda duk ta tsorata sai kace ita tayi laifin ma. A wani tsadadden wajen shan ice cream
Khaleel yyi parking yana kallon Heedayah da idonta ke saman titi ko kiftawa bata yi, yace “Kina shan ice cream?”
sai a snn ta juya ta kallesa ta kalli gun siyar da ice cream din, tace masa “Uhn” yace “To mu je ki xabi flavor da kike
so” a hankali tace “Aa ni baxan fita ba” yace “Me yasa?” Ta langwabar da kanta tace “Ba komai, kawai bana son in
fita” yace “Ohk then, let me get you” bata ce komai ba ya dau face cap dinsa ya kafa a kansa, baka ganin komai sai dogon hancinsa da karamin bakinsa, ya bude motar ya sauka ya kulle, ta bi sa da kallo har ya shiga babban Ice
cream parlor din, bayan wasu mintuna ya dawo rike da leda me dauke da packaged ice cream har uku ya bude motar
ya shiga snn ya kulle ya mika mata ledan, amsa tayi ya tada motar suka bar wajen, ya kalleta ganin ta ajiye ledan a
gefenta yace “Toh ki sha” tace “Ni kadai?” Yace “Yess” tace “Ai baxan iya shan duka ba” yace “Toh sha wanda xa ki
sha” ba musu ta bude ledan ta dau vanilla flavor ta bude ta fara sha, a nutse yake driving din, just roaming round
FCT, sai bin manyan wurare take da kallo, you can’t say if she is happy or not, ita dai ga ta nan, suna isa wani joint
na shawarma yace “Do you take shawarma?” Ta girgixa masa kai alamar Aa, yace “Why?” Tace “Na koshi” yace
“Toh tsire fa?” Ta girgixa masa kai nan ma, bai kuma ce mata komai ba ya ci gaba da driving slowly, kallon agogo
dake nuna karfe tara saura minti sha biyar yyi yace “Are you sure baki son komai?” Ta gyada masa kai, tafiyar kusan
minti sha biyar suka kara ganin inda suka nufa ta kallesa da sauri tace “Ina xaka kai ni?” Yace “Home, its late kar a
neme ki, nasan yanxu ai so called yayan naku ya wuce ko?” Shiru tayi bata ce komai ba, ya ci gaba da driving,
girgixa kai tayi a hankali tace “Ni baxan je gidan ba” Da mamaki ya juya ya kalleta, yace “Baxa ki je gidan ba
kuma?” Ta gyada masa kai, yace “Why?” Kamar xata yi kuka tace “Ni dai kawai baxan je ba” Yace “Did you have&nb
sp;
any other guardians in Abuja” Ta kallesa tayi shiru, sai kuma tace “Ban san kowa ba” Bai kuma ce mata komai ba ya
ci gaba da tukin, Kuka sosai Heedayah ta fashe masa ganin sun kusa layin, hakan ya basa mamaki sosai ya samu
gefe ya tsaya yace “Are you alright Heedayah?” Cikin kuka tace “Plss kar ka mayar da ni don Allah” kasa ce mata
komai yyi yana kallonta, can yace “Me suka maki da baxa kije gidan ba” Tana share hawayen dake xuba idonta tace
“Ni dai ban so, don Allah kar ka mayar da ni” He was lost of words don sai kallonta yake, ganin yanda take kuka
yace “Talk to me Heedayah, sun maki wani abu a gidan ne?” Ta hade kanta da gwiwa tace “Ni basu min komai ba,
bana son in je kawai” ya jingina da seat dinsa yace “To ina xan kai ki yanxu?” Cikin rawar murya tace “Ka tafi da ni
kawai” yace “In tafi da ke ina?” A hankali tace “Inda xaka je” Jin shirun yyi yawa ya sa ta dago tana goge hawayen
idonta, kallonta taga yake yi, ya kamo hannunta a hankali yace “Noo Heedayah, you need to go back home, xa su yi
ta nemanki….” Ta fixge hannunta tana masa wani kallo tace “Ni baxan je ba nace maka, kuma ka ajiye ni a nan
kawai inyi wucewa na” Da mamaki yace “Ki tafi ina?” Kokarin bude motar ta fara yi tace “Ni ka bude min” ya
jawota yace “But Heedayah, what just came over you, Ina kike son in kai ki da daddaren nan, kince min baki san
kowa ba a garin nan banda gidan warce ku ka xo, to ina kike son in kai ki kuma” Kuka kawai take masa xata kwace
hannunta, ya jawota kusa da shi yace “Ki gaya min me aka maki a can gida” turasa tayi tace “Nothing I said, ni ka
bude min in sauka” Khaleel couldn’t stop looking at her, ganin ya ki bude mata motar ta hade kai da gwiwa. Har
karfe goma saura Farida da Yayarta suna xaune parlor sun yi jigum, Farida ta san kiris ya rage yayarta ta kira Mami
don ta cika daga xaunen da take, Farida ta dau wayarta duk jikinta yyi sanyi ba kadan ba, bude ido tayi tunawa da
tayi ai ta ba Heedayah wayarta suna tahowa a mota daxu tayi ma Khaleel din message, shiga message tayi da sauri
tana dubawa taga bbu message din sabon number, alamar Heedayah ta goge text din gaba daya, Number Shuraim ta
duba duk da bata yi saving ba amma ita ma ta so haddacesa tunda bashi da wahala, tayi dialing number har ya katse
bai dauka ba, ta sake kiransa, nan ma bai dauka ba, sai gashi ya kira, dagawa tayi ta kai kunne, da farko ta rasa
abinda xata ce sai kuma tayi masa sallama, ya amsa, shiru tayi, yace “Wacece?” Mikewa tayi ta mika ma Maman
Fadil wayar tace “Don Allah aunty kiyi masa magana ni ban san me xan ce ba” Maman Fadil ta jefa mata wani kallo
tace “Waye?” Farida tace “Ya Shuraim” amsar wayar tayi ta kai kunne hade da yi masa sallama, bbu bata lkci tayi
masa bayanin komai cikin few minutes, shirun da taji yasa tace “Hello” Shuraim yace “Ina ji, and she is not yet back
har yanxu?” Maman Fadil tace “Wllh kuwa, ni tunda nake ban ta6a ganin haka ba ma, har nawa take xata yi wannan
aika aikan, Ina ta bi sa suka tafi, ni gashi ko abinci na kasa ci har yanxu, ta ina xan fara yi ma Mami bayani, me ma
xan ce mata??” Shuraim gaba daya ya rasa abinda xai ce, don basu kai sa mamaki ba ma, can yace “Ba wa Farida
wayar” Mika ma Farida wayar tayi, Farida ta amsa ta kai kunne, Yace “All this while dama akwai waya a hannunta”
Farida ta koma ta xauna ta rasa abun cewa, yace “Baki ji na ne?” Tace “Nima ban sani ba….” a fusace Maman Fadil
tace “Munafuka kika ce baki sani b, wllh tana sane ita ma munafukar ce ai, kuma kema ta ja maki matsala tunda kike
boye abinda take yi” Shuraim yace “Waye shi Mutumin??” Farida tace “Ni fa ba gaya min komai take ba” Katse
wayar Shuraim yyi ya mike daga kwancen da yake, ya dau makullin motarsa ya fita. Khaleel bbu irin lallaba
Heedayah da bai yi ba ya mayar da ita gida amma kememe ta ki, har sannan suna tsaye gefen hanya a motarsa sai
kallonta kawai yake, ji yyi tace “To naji xan tafi gida, amma ka sauke ni in karasa da kafa kar ka kai ni street din”
Yace “But it’s late and they are dogs everywhere….” tace “Ni kuma a nan xaka ajiyeni nace” yace “In ajiyeki ki tafi
wani waje kenan?” Ta kallesa tace “Ehh, don baxan koma gidan ba” ya fi minti uku yana kallonta kafin ya tada
motar ya fara tafiya, har ya dau hanyar gidansa sae ya tuna abinda Zayyad yace masa daxu, can kuma kawai ya nufi
gidan nasa. A cikin motarsa ya ciro makullin gate din gidan, ya sauka ya bude gate din, Heedayah sai bin anguwar
that is so quiet ta ke da kallo har ya dawo cikin motar ya shiga, a parking lot ya tsayar da motar ya kashe ya sauka ya
koma gate din ya kulle da makulli snn ya koma gun motar yana kallonta yace “Are you satisfied now?” Ta gyada
masa kai yace “To sauko” bude motar tayi ta fito tana bin gidan da kallo tace “Gidansu waye?” Yyi shiru yana
kallonta, ganin ynda take kallonsa a hankali yace “Gidanmu ne” tace “Mum dinka da Dad and siblings suna ciki” Yace “No” tace “Why? Where are they?” Kulle motar yyi bai ce mata komai ba, ya nufi entrance din katon gidan, ta
bi bayansa tace “You are not saying anything?” Yace “Duk basa nan” tace “To ina suka je” Yace “Gobe xa su dawo,
they travelled” tace “To ni da kai kawai xa mu kwana gidan?” Bai ce mata komai ba ya sa makulli yana bude kofar
parlon, tace “Ehh??” Sai da ya bude kofar snn ya juyo yana kallonta yace “Aa da mutane” daga haka ya shiga parlon
yana haska fitila da wayarsa ta bi bayansa, a hankali tace “Ni tsoro nake ji, babu wuta?” Yace “xan kunna yanxu”
Ajiye wayarsa yyi da ya haska some areas of the parlor snn ya fita ta bi sa da kallo, ba a dau lkci ba haske ya
gauraye ko ina na katon parlon, ta dinga bin parlon da kallo don yyi mata kyau sosai kamar ba a Nigeria ba, parlon is
so neat don bai yi kama da wanda ba a amfani da ba, Khaleel ya shigo parlon ya kulle kofa snn ya dawo ya xauna
yana kallonta yace “Now tell me Heedayah, me aka maki a can gidan?” Ta girgixa kai tace “Aa ni ba a min komai ba,
kawai bana son komawa ne” yace “Noo, there must be reason for that, haka kawai baxa kice baxa ki koma ba” Tayi
shiru tana kallonsa, mikewa yyi ya nufi fridge dake dinning area ya bude ya dau drink din gwangwani me sanyi snn
ya dawo yace “I am tired, and sleepy… Mu je in nuna maki inda xa ki kwanta” Shiru tayi tana kallonsa, stairs ya nufa,
ta mike ta bi bayansa, ya bude mata wani daki yana kallonta yace “Here….” Bata ce komai ba ta shiga dakin ya kulle
kofar snn ya koma downstairs. Rai bace Maman Fadil tace “Baxa ki bude baki ba ana maki magana munafuka kawai,
Banda kukan munafurci meye wnn kike yi, baxa ki basa amsan tambayar da yake maki ba” Farida ta ki cewa komai
ta goge hawayen idonta da ya ki tsayawa, Maman Fadil ta kalli Shuraim tace “Don Allah da ta ganta da waya who is
first person da ya kamata ta fara sanar ma wa, idan ma baxata iya fada ma Mami ba tana ganin Mami won’t take it
likely ba sai ta gaya ma Yaya Junaid ba? To wllh bbu ruwana dubi karfe har sha daya saura bbu yarinya bbu
labarinta, me xan ce ma Mami daga xuwa gidana yarinya ta bi saurayi da daddare” sai ita ma ta fara kuka, Shuraim
dai na tsaye parlon just as the soldier he is, Farida ta saci kallonsa don tunda take bata ta6a ganin anger dinsa irin na
wnn lkcn ba, gaba daya idanuwansa sun sauya daga yanda ta san su, Maman Fadil na share hawayen dake kwarara
idonta tace “Ni kawai don kace kada a tada ma Mami hankali daren nan ne wllh da na kira na sanar mata Yaya
Shuraim, amma duk da haka bari in kira Yaya yanxu ya san abinda ke faruwa this is almost after eleven” tana bari
n
parlon shuraim ya juya yana kallon Farida fiercely yace “For how long wayar ke hannunta” Tayi shiru bata ce komai
ba, tsawar da yyi mata ya sa ta mike a hankali tace “Ni bata ce min ya bata waya ba, kawai boyewa take ta yi har na
gani” xaunawa yyi saman kujera ya sauke boyayyen ajiyar xuciya ya dafe forehead dinsa da ya ji yyi masa nauyi,
sake mikewa yyi yana kallon agogo dake manne parlon…. Khaleel ya gama duk abinda xai yi ya kashe wutan parlon
ya kwanta saman 3 seater wajejen karfe sha biyu da rabi, sai a sannan ya cire wayarsa a flight mode, bayan few
minutes sai ga text din Zayyad ya shigo masa har uku, ya bude ya mike xaune yana duba messages din…. Lkci daya
ya mike ya nufi kofar parlon ya bude ya fita da sauri.
Kashe wutan gidan yyi gaba daya snn ya dawo parlon ya dau wayarsa ya kunna fitila ya wuce sama, a hankali ya
bude dakin dake kallon wanda Heedayah ke ciki, ya shiga ya rufe, kusa da kofar bathroom ya isa ya duka ya daga
foot mat dake kasa ya daga tiles din da aka daura kawai a wajen, sai dai idan mutum bai lura ba baxai gane daura
tiles din kawai aka yi ba xa a iya dagawa, wani karamin under ground ya haska a wajen bayan ya bude wani box, ya
ciro bindiga guda daya cikin bindigogi biyar dake nan snn ya dura bullet dinsu dake wajen su ma, ya mayar da tiles
din ynda yake ya daura foot mat din ya mike ya saka bindigan a aljihunsa, ya fita dakin ya kulle kofar gently, har xai
sauka sai kuma ya kalli kofar dakin da Heedayah ke ciki ya dawo ya bude kofar shi ma gently yana kallon cikin
dakin, all with the aid of his phone flash, kwance ya ganta ta dukunkune waje daya tana bacci, ya karasa cikin dakin
ya bude press dake ciki ya fiddo babban blanket me laushi ya lulluba mata, still yyi sai kuma ya kashe flash din da
wuri ganin ta gyara kwanciyarta, sai da ya tabbatar ta ci gaba da baccin snn ya tafi gun curtains xai gyara ya hango
mota biyu sun tsaya dai dai gate din gidan don ta window din ana yi ganin wasu bangare daga surrounding din street
din, kallon motar yake har bayan kusan minti goma shi dai bai ga alamar an sakko daga ciki ba, wanda idan ma an
sakko din ma ba sani xai yi ba sbda jikin wall din gidan motar ya tsaya, nan kuwa mutane biyar har sun sauka
daga motar xuwa bakin gate din nasa, daya daga mutane biyar din da suka diro daga motar ya tafi ya durkusa bakin
gate din gidan yana haska fitilar wayarsa ko xai ga tambarin tayar mota da xai yi nuni da mota ta shiga gidan, mikewa yyi yana kallon sauran yace “Yes yana ciki” dayan cikinsu yace “Cikin darkness?? da yana ciki ai xa a ga
wuta a cikin gidan, but no light and akwai wuta a anguwar ai” Bindiga wanda ke kallonsa ya daura masa a fuskarsa
strictly yace “Ka raina kitabar Brainiac kenan? Tunda har baya gidansa na asokoro, baya can gida, to yana gidan nan,
coz he have no business with the other gender ballantana ace yana hotel, baya ma kwanan hotel, so now you guys
should just find a way da xa mu shiga gidan nan in hukuntasa” Mutumin yace “Talent dinsa na yanda yake shiga
gidan mutane in every operation xa mu yi amfani da yanxu” Tuni Khaleel ya fita dakin da Heedayah take ya sakko
downstairs ya fito compound, ta jikin bango ya dinga bi har ya iso gate ya manne da bangon pillar din gate din, nan
kuma duk ya dau muryoyinsu, A karo na farko Maska yace “We should bother our self not….. finding a way in, I
have his spare keys, stole them from Zayyad” Khaleel yyi grinning teeth dinsa bai kara second daya a wajen ba ya
koma cikin gidan da sauri, a karo na farka a rayuwarsa ya ji he is disturbed about something, ya ji gaba daya
hankalinsa ya tashi, baya son abinda xai tsorata Heedayah ko kadan, ya san kuma dole xa su shigo gidan ya san
tunda makulli na gun maska xa su shigo, da ma shi kadai ne xai sama ma kansa way out cikin few minutes but not
with Heedayah, yana shiga parlon ya ji suna bude gate din, ya sa makulli kofar parlon leaving the key jikin kofar
duk da ya san it’s of no use cos he knows all the trick, they knows all the trick, they are expert users of his talent and
experiences, sama ya haura ya tsaya nan corridor patiently waiting for them, yana jin suka bude kofar parlon bayan
wasu mintuna, haka kawai a sannan ya dinga jin faduwar gaba, and with just a blink of an eye sae ga wuta ya haska
ko ina, wato sun kunna wutan gidan yasan kuma aikin Maska ne, Fago na nuna ma Oga Arne takalman Heedayah
dake parlon yace “This is the root of the problem, mace ce ta shigo rayuwarsa shine take yaudararsa yake
misbehaving yake raina ku” Arne ya rike ha6arsa yana gyada kai convincingly yana kallon takalmin da mugun
mamaki, a hankali yace “Ohh I seeee, mace ce ta shiga rayuwarsa farat daya, abun ka da ba sabon ba” Fago yace
“He risked his colleagues life sbda matsiyaciyar mace da xan harbe yanxun nan” Arne yyi wani dariyar bossawa lkci
daya kuma ya daina dariyar yace “To wllh wllh a gabansa xa a aikata lahira, snn sai ya san yayi fatali da umarnin
manyansa yau, shi ya mance a yanda muka daukesa kenan, I am more of his father than Boss, ni ne uwarsa nine
ubansa ynxu haka a duniya” Khaleel dake jin duk abinda suke cewa ya manne da bango hannunsa rike da bindigarsa
ya saita dai dai gwiwar Fago cikin few seconds ya saki bullet din, bayan ya tabbatar ya samu kafar ya bude dakin da
Heedayah take ciki ya shige da sauri ya sa makulli, wani ihun axaba fago yayi ya xube kasa jini na malala daga
gwiwarsa ta dama, ko wannensu har Arnen suka samu bango duk suka manne suna xaxxare ido, A firgice Heedayah
ta mike xaune saman gado tana kallon Khaleel, ya boye bindigar hannunsa a bayansa, ya sakar mata murmushi da
iyakarsa lips, kokarin sauka ta fara yi daga saman gadon looking very afraid tace “Meye yyi wani karan, what’s that,
is that a gun????” Ya nufeta trying his best to calm her down yace “No sound, may be… May be… We have visitors,
probably armed robbers, bandit, kidnappers….” Ta wani xaro ido ta fasa wani shegen ihu ta mike tsaye, rikicewa yyi
ganin yanda ta tsorata ya isa gabanta not minding she will see the gun in his hand yace “Noo Heedayah, I will
protect you by all means bbu abinda xai faru dake, I promise you this” Ta wani xaro gaba daya idanuwanta ganin
bindigan hannunsa ta kara saka wani kara me karfi, jawota yyi jikinsa yace “I am protecting us with it, they have
guns also, I mean no harm Heedayah” ta kankamesa tace “Wayyo ni tsoro nake ji, plsss take me out of this house,
don Allah ka tafi da ni daga nan, tsoro nake ji” Jikin window ya nufa holding on to her tightly, ya bude window din
dakin ya saita bindigarsa up the sky ya saki bullets uku that sounds so loud a anguwar, Heedayah bata ta6a tsorata
irin na wannan dare ba tunda aka haifeta, tana son kwace kanta kuma amma ya ki saketa, ya kara harba bindigar, dai
dai nan Maska ya bude kofar dakin, sun kai su shidda ko wanne na nuna masa bindiga kamar yanda shi ma yake
nuna ma Arne, Duk ynda Heedayah ta so juyawa taga wa enda suka shigo Khaleel bai bata wannan daman ba sbda
yanda ya rungumeta, Arne ya dinga kallonta yana nuna mata bindigar hannunsa, shi kuma Khaleel na pointing dinsa
da nasa bindigar, Arne yace “Ka sauke bindigar ka ko in harbeta har lahira ynxu” Girgixa kai Khaleel yyi yace
“Same will happen to you right now” Arne yyi wani shegen kara yace “Genius dama sbda mace kayi disappointing
dinmu ka janyo mana rasa Salim????? Ka janyo mana asara da yawa, duk sbda yar kwailar nan? Wato a cikin
kankanin lkci ka gurbata rayuwarka ka fara harka da mataaa
, a kaf duniyar nan dama kana da sama da ni???” Cikin
tsawa ya kare maganar yana huci, sai kuma ya nufesa still pointing the gun to Heedayah, Khaleel ma na nuna sa da
gun dinsa fuskarsa a daure, lkci daya Siren ya cika anguwar Arne ya juya da sauri yana kallon yaransa yana xaro ido,
Maska sake xare ido shi ma yace “Policemen….” cikin daga murya Arne yace “Get set, back to the cars now, help
Fagoo out, immediately now” Duk suka juya suka fice daga dakin da sauri, Arne na komawa da baya bai fasa nuna
Heedayah da bindiga ba yana kallon Khaleel cikin kaushin murya ta mugunta yace “Wllh wllh idan baka dawo
hanya ba nine ajalin ka Khaleel, nine ajalin wannan yarinya, nine ajalinku ku biyu billahh, sae na yi maka kisan
walakanci, ita kuma in harbeta cikin ruwan sanyi, kasan wanene ni Khaleel, kasan wanene Manga, kasan wanene
Barau, kasan wanene Bala, forget you are a Genius idan aka hada mu hudu mun fi Genius, we will make life a dirty
miserable for you before sending you to ur early grave, yanxu muka fara harka da kai, baka isa ka kara bijira mana
lkci daya ka janyo mana matsala ba, Kai din namu ne” yana fadin haka ya fice daga dakin in a haste, har sannan
siren na tashi a anguwar loudly, Khaleel ya sauke wani ajiyar xuciya a karo na farko ya kalli Heedayah that he is holding so tight a jikinsa don ya san she passed out from the moment she heard their voices, kwantar da ita yyi
saman gado yana kallon kyakkyawan fuskarta cikin sanyin murya yace “Heedayah….” Su Arne da tawagarsa na isa
titi suka jiyo jiniyar yan sanda so far away alamar a lkcn ma Yan sandan ke tahowa, and they wondered wani siren
ne ke tashi a anguwar haka, not minding that…. a mugun guje suka yi wucewarsu da motocin su kafin bayyanar
motar yan sandan, Knocking Khaleel ya ji ana yi downstairs with voices, ya mike tsaye da sauri ya ajiye bindigar
hannunsa karkashin pillow ya fita, corridor din dakunan ya hadu da matasa just like him guda biyu sai dattijai guda
biyu, daya dattijon yace “Hope you are safe brother?” Khaleel ya kirkiro murmushi yace “Alhmdllh” Daya matashin
yace “Babu abinda dai suka yi ko, don naga pool of blood downstairs” Khaleel yace “Ni na caki daya daga cikinsu
da wuka, har suka gudu sbda karan Siren wukar yana jikinsa, I battled with them” A tare suka hada baki suka yi
hamdala, Dattijon yace “To matar taka fa?” Khaleel da kamar baxae ce komai ba sai kuma yace “Ta dai tsorata ne
kawai, and I think she passed out….” Daya daga matashin yace “Can I meet her in and check on her” Dattijon yace
“Ehh likita ne shi, either ya dubata ko kuma a wuce asibiti kawai” komawa dakin Khaleel yyi ya isa kusa da
Heedayah ya durkusa ya dau dankwalinta da ya fadi a kasa ya rufe mata gashinta da shi snn ya gyara mata skirt dinta,
ya koma gunsu yace ma likitan xai iya shiga, makotansa ne su din gaba daya, iyakarsa da su haduwa a masjid din
anguwar yyi masu gaisuwar mutunci yyi wucewarsa that is if yana Abuja, though a wata ya kan yi sati uku a Abuja,
xamansa a Kaduna lkci lkci ne, Siren din da ya dinga tashi a anguwar kuma daya daga matashin wanda ya kasance
soja ne ya kunna kuma yyi kiran office a turo masu yan sanda tun farkon harbin da Khaleel yyi sau uku, neighbors
din nasa na nan har yan sanda suka iso suka d’an yi investigation dinsu suka wuce, sae kusan karfe biyu da few
minutes duk neighbors din suka bar gidan Khaleel, bayan likitan ya tabbatar Heedayah is fine, kuma bacci take. Har
kusan asuba Khaleel na xaune gefen Heedayah bayan ya gyara parlon duk ya share blood stain din, ya jinginar da
kansa da gado yana kallon saman dakin, juyawa yaga tayi, ya sauke idonsa kanta da sauri yana kallonta, a hankali ta
bude idonta suka yi ido hudu da shi, mikewa tayi xaune tana kallonsa sai kuma ta bi dakin da kallo, ya kamo
hannunta kafin yace komai ta fashe masa da kuka tsoro karara a fuskarta tana komawa baya, yyi kasa da murya yace
“You are safe Heedayah, ‘yan sanda sun xo sun tafi da su” ta fashe da kuka sosai xata sauka saman gadon, ya riko
duk hannunta biyu yace “Nace maki yan sanda sun tafi da su, don’t cry plss” cikin rawar murya tace “I am still afraid,
why were they here?” Yyi kasa da murya yace “To Rob” ta dinga bin dakin da kallo tana hawaye, yace “Stop crying
plss” tace “Kaina na min ciwo” da damuwa yake kallonta, can ya mike don Dr Farouq ya dauko mata magani daxu
daga gidansa ya kawo kafin su tafi, Khaleel yace “I’m coming” sauka tayi da sauri daga kan gadon ta tsaya kusa da
shi tace “Nooo kar ka barni” kama hannunta yyi suka fita dakin xuwa downstairs ta makalkale masa don duk a
tsorace take, kitchen ya shiga tare da ita, ya dau bottle water a fridge ya xuba a kettle ya kunna, ya lumshe ido jin
yanda taki basa breathing space standing so close to him, Bai bari ruwan ya tafasa ba ya dauraye mug ya xuba kayan
shayi a ciki snn ya xuba ruwan ya dau spoon ya juya, kashe wutan kitchen din yyi suka fita, yana rike da cup din
shayin tana makale da shi suka koma sama, yana kallonta tana shan shayin bai san sarkin shan shayi bace har ta
shanye tass, yace “You need more?” Girgixa masa kai tayi, ya bata ruwan gora da paracetamol ta amsa ta sha, bayan
few minutes ta kwanta saman gadon tayi shiru tana kara tunanin abinda ya faru, she is still shock, kallon agogo dake
nuna karfe uku da few minutes yyi sai a snn ya fara jin bacci, ya lumshe idonsa ya bude yace “Did you need
anything Heedayah?” Girgixa kai tayi tana kallonsa, yace “Xan tafi in kwanta….” Da sauri ta mike xaune tace
“Where?” Yace “Dakina” kuka ta sakar masa tace “Noo kar ka barni ni kadai pls, wllh tsoro nake ji” Shiru yyi yana
kallonta, can ya mike ya bude press ya ciro wani bargon ya shimfida a kasa ya dau pillow ya ajiye snn ya kashe
wutan dakin ya kwanta kasan bargon yace “Good night” edge din gadon ta dawo ta inda yake kwance yanda xata
dinga ganinsa yana daga kasa tana daga sama tayi lamo gabanta na faduwa, ba a dau lkci ba bacci ya dauketa, shi
kuma duk baccin da yake ji sai ya samu kansa da kasa yi…. A idonsa aka yi kiran sllhn asuba, biyar da few minutes
ya mike ya shiga bandaki yyi alwala ya fito ya bude kofar dakin a hankali so careful not to wake her sannan ya fita.
Bayan ya dawo masallaci a parlor ya kwanta nan da nan bacci ya daukesa, cikin bacci ya ji ana tashinsa, ya bude
idanuwansa a hankali ya ganta durkushe kusa da shi tana kallonsa, murya can kasa tace “Babu Hijabin da xan yi
sllh” ya kuma lumshe idonsa snn ya bude ya mike xaune, ita dai kallonsa kawai take da idanuwanta da suka
kumbura, tashi yyi ya wuce sama ta mike ta bi bayansa, ya shiga wani daki sai gashi ya fito da hijab a linke, ya mika
mata, tace “Na waye?” Murmushi ya sakar mata yace “Pray Heedayah” daga haka ya koma downstairs, ta shiga
dakin ta dauko darduman ita ma ta dawo kasa, har ya koma bacci ta samesa a parlon, ta jima xaune saman darduman
bayan ta idar da slhn don har gari ya fara haske, daga karshe ta kwanta saman darduman nan da nan bacci ya dauketa.
Karfe takwas saura mintuna Mami ta shigo garin Abuja, tun hudu da wani abu na asuba hakurin Maman Fadil ya
kare ta kirata don tayi ta kiran Junaid wayarsa wasn’t going through a daren, nan dai ta sanar ma Mani halin da ake
ciki with tears, daren ranan daga ita har Farida bbu wanda ya rintsa, I don’t want to talk about shuraim cos he saw no
sleep too, ya kuma fi su shiga tashin hankali, Tun da Maman Fadil ta sanar ma Mami abinda ke faruwa, sllhn asuban
ma sai da Mami tayi consoling kanta na gaske snn ta iya yi, she h
ave never been down lkci daya kamar ynda tayi jin
news din nan ba, she felt so sick at once, ba training din da tayi ma Heedayah ba kenan, baxata taba tafiya tare da saurayi ba kamar yanda Dinar ta sanar mata, Mami was so confuse and shock to the highest, wanda bata san lkcn da
hawaye ya hau mata xarya ba gashi junaid baya gidan sai dai bata yi yunkurin kiransa ba, tana idar da sllhn Asuba
sai da ta sha magani ko xata d’an ji saukin abinda take ji, snn ta saka Hijab dinta har kasa ta dau hanyar Abuja, not
minding the road tare da driver dinta, she just can’t hold it anymore, a motar ma banda addu’o’i bbu abinda take ta yi,
tun auren Maman Fadil sae ranan Mami ta taka gidanta a karo na farko, daga Farida har Yayarta bbu wanda ya iya ce
ma Mami komai, sae Maman Islam makociyar Maman Fadil da ke parlon da wata neighbor dinsu Maman Safwan ne
suka iya gaisheta da yi mata sannu da xuwa ganin kamaninta da su farida, Mami ta amsa cikin sanyi, ta nemi kujera
ta xauna don bata jin xata iya ci gaba da tsayuwa tana kallon Maman Fadil tace “Deenar me ku ka yi ma Heedayah?”
Cikin sanyin murya Maman Fadil tace “Haba Mami me xa mu yi ma Heedayah, karfe nawa suka iso a jiyan ma balle
ayi mata wani abu, wllh bbu abinda aka yi mata” sae kuma ta fara kuka sosai, Mami ta dafe kanta ita ma hawayen
har ya kawo idonta, ta shiga kiran Allah a xuciyarta, Abba kawai da kaka suka fado mata a wnn lkcn, where is she to
start from now, Maman Fadil na share idonta tace “Abun da mamaki sosai, ko da ta fita gurin saurayi ae xata dawo
sai in wani abu ne ya faru, kuma gashi bamu san waye saurayin ba, wllh Mami sneaking tayi ta fita ni da Farida bbu
wanda yasan ta fita, da na sani ai babu abinda xai sa in barta ta fita waje, mu uku kadae ne gidan sae Fadil fa” Farida
dai hawaye kawai take ta kasa cewa komai, Mami ta daure ta mike tace “Nearest police station a ina yake?” Maman
Fadil tace “Aa tun asuba Shuraim ya kai kara can, he is still not yet back ma” Maman Islam ta sauke wani ajiyar
xuciya tace “Allah ubangiji ya takaita wahala da tashin hankali, ya bayyanata cikin aminci da yarda” A hankali
Maman Fadil tace “Ameen” Mami ta dau wayarta ta shiga kiran Shuraim. Karfe tara saura Heedayah ta farka, ta
mike xaune tana bin katon parlon da kallo, har sannan Khaleel na kwance saman kujera yana bacci, ta mike ta isa
kusa da shi ta durkusa tana kallonsa, hancinsa ta kafe da ido, can ta kalli dogon lashes dinsa snn lips dinsa, ta kuma
kallon hancinsa, sosai gabanta ya fadi, lkci daya ya bude ido ta koma baya da sauri har tana neman faduwa tana kifta
ido tace “Tell me who were those people of yesterday” ya mike xaune yana shafa kansa yace “Armed Robbers, good
morning Heedayah” shiru tayi tana kallonsa, ya lumshe idonsa ya bude yace “May be sun ga ina gari and they’ve
been targeting sae jiya suka xo” a sanyaye tace “How did they leave?” Yace “My neighbors helped, they alerted the
police” Tayi shiru tana kallonsa, sauke dogayen kafafuwansa yyi kasa yace “I’ve slept for so long, you need to get
back home Heedayah, kar ki ci gaba da daga hankalin wa enda suka rike ki da aminci, I am taking you back home
now idan kinyi breakfast” lkci daya mood dinta ya canxa tayi shiru tana kallonsa, ya mike yace “Ki tafi sama ke ma
ki shirya, take ur bath I will get you something to wear now” da kallo ta bi sa har ya wuce upstairs ba a dau lkci ba
ya sakko da makullin motarsa, yace “Toothpaste, toothbrush, sponge, soap towel duk suna nan na ajiye maki saman
gado, I will be back soon” ta mike da sauri kamar xata yi kuka tace “Ni tsoro nake ji wllh” yace “No harm Heedayah,
ba dadewa xanyi ba kuma, I will be back soon” daga haka ya fita parlon tana ji ya fitar da motarsa daga gidan,
xancen da yyi mata kafin na karshe ne ke yawo a kanta, she needs to get back home, but she never wants to go back,
shiru tayi tana tunanin kilan dole yace sai ya kai ta gida, ita kuma bata son ta je, hawaye ya kawo idonta ta wuce
sama da sauri ta dauko veil dinta snn ta sakko kasa, ta sa takalminta ta nufi kofa, gwara ta tafi kawai kafin ya dawo
ya ka ita gida. Murda kofar tayi ta ji a rufe, kamar xata yi kuka ta dinga kallon kofar, ta sake murdawa bai buduwa
ba, a hankali ta juya ta koma sama duk jikinta a sanyaye ta dau abubuwan da ya ajiye mata saman gado ta shiga
bandakin, ko da ya dawo bata fito ba ya ajiye mata ledan hannunsa kan gadon sannan ya fita dakin ya wuce nasa, har
ya sakko wajen karfe goma bayan yyi wanka ya shirya Heedayah bata sakko ba, sai kallon agogo yake don ya kagu
ya ga ya mayar da ita gida, daga karshe ya mike ya wuce saman, karo suka kusa ci xata sakko ya koma baya yana
kallonta, sosai bakin abayar yyi mata kyau kamar ya aunata kafin ya siyo, ya sakar mata murmushi yace “U look
cute” Ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, yace “Taho kiyi breakfast lkci na wucewa” bin bayansa tayi suka koma
kasa, ya hada mata shayi ya bata fried Irish with egg and ketchup da ya siyo, yace “Do you take bread?” Ta girgixa
masa kai, shayin ta fara shanyewa gaba daya, ya buda ido yana kallonta yace “Why?” Tace “Haka nake yi” yace
“You need more?” Ta girgixa masa kai, jawo plate din Irish din tayi ta fara ci a hankali, ya d’an yi murmushi ya hada
shayinsa da iyakarsa bai kai rabin cup ba ya fara sha, yace “Ina xa ki ce ma Guardians dinki kin tafi idan na mayar
da ke yanxu Heedayah?” Ta kallesa bata ce komai ba, lkci daya ta kasa ci gaba da cin dankalin, ganin hakan yace
“Why are you not eating” bata ce masa komai ba ta ci gaba da ci without appetite, har cikin ranta bata son xancen
gida, daga karshe ta tura Irish din ganin ya fice a ranta gaba daya, ta koma saman kujera ta xauna ta jinginar da kanta
da kujeran, da ido ya bi ta yace “What’s wrong Heedayah?” Ta girgixa masa kai tace “Nothing na koshi” Kafin yace
komai tayi saurin cewa “Wannan shayin ne xai isheka?” Yace “Baxan ma shanye ba” Tayi shiru tana kallonsa bata ce
komai ba, a hankali kuma tace “I saw u with gun yesterday, waye ya baka” kallonta yyi da sauri coz her question
came unaware, sai kuma ya sauke idonsa kasa cikin cool voice dinsa yace “My father, you know…. he is a soldier, da
naji barayin sun shigo shine na tafi dakinsa na dauko bindigar” Yana iya ganin tsoron da ya bayyana fuskarta lkci
daya, ya ajiye sauran shayin da ya rage ya mike yace “I need to get u back home Heedayah, nasan hankalin kowa ya
tashi yanxu, ki saka kayan ki da kika cire a leda ki sakko da shi mu tafi” Shiru tayi tana kallonsa ko kiftawa babu,
gabanta na faduwa kuma sosai, ganin jiranta yake tace “Na saka a leda….” yace “To dauko su” tayi narai narai da ido cikin tsigar shagwaba tace “Ni baxan iya xuwa sama ba kuma, my legs a paining me, ka dauko min” ya kai minti
daya yana kallonta can yyi murmushi ya wuce saman ta bi sa da kallo har ta daina hangosa, mikewa tayi da sauri ta
tafi ta saka takalminta ta fice daga parlon da ya bari a bude bayan shigowarsa daxu, kusan da gudu ta isa gate shi ma
lock kawai ta bude ta fice daga gidan gaba daya, mota ce tayi parking dai dai gate din gidan, tana kallo har wanda ke
cikin motar ya sakko, kallonta ya dinga yi, taki yarda su hada ido ta nufi hanyar da take tunanin xai fitar da ita daga
anguwan da sauri, da ido ya bi ta har tayi nisa snn ya shiga gidan, ya bude parlon ya shiga, daga kitchen Khaleel ya
fito yana neman Heedayah, ya tsaya kallon wanda ya shigo parlon, Zayyad yyi masa wani shegen kallo sai kuma ya
kyalkyale da dariya yace “I am happy for you frnd, ko ba komai kai ma xaka bada labarin wac
ece mace tunda ka
kwana gida daya da mace yau, sai dai you are in great risk Brainiac, Mu ma ba wai bama harka da mata ba, but we
still concentrate on our goals, kai kuma da yake sabon shiga ne, it’s causing you much distraction, ga mata iri ri sai
warce ka xaba ka darje a gari, don’t be afraid of loosing this one…..” Wani kallo Khaleel ya jefa masa xai koma sama
neman Heedayah and idan ma ya ganta baxai bari ta fito ba har Zayyad ya wuce, Zayyad yace “Na samu labarin
artabun da kayi da su Oga daren jiya, you chop liver Genius… and probably my text message helped, yanxu dai
tunda har gari ya waye har kuma yarinyar ta kama gabanta sai mu je ka bada hakuri, I don’t want to imagine
anything happening to you Brainiac….. But isn’t that girl I saw too young for u, anyway sweet sixteen, and she is
damnnn pretty with the perfect curves….” Har Khaleel ya fara hawa stairs ya dakata ya juyo da sauri fuska daure
yace “And where did u see her??” Zayyad yace “Mun hadu bakin gate xata wuce yanxu” Wani tsalle Khaleel yyi ya
duro maimakon sakkowa few stairs din da ya hau yace “Ta tafi Ina?????” Zayyad ya tsaya kallonsa, Khaleel ya
nufesa da sauri yace “Answer me plss Zayyad, Ina ta tafi” Zayyad yace “Wahala be like bicycle, I just met with her
outside ynxu da xan shigo and tayi hanyar titi how will I know inda xa ta” Khaleel yace “Nooo, why did u let her”
Zayyad ya saki baki yana kallonsa yace “Ikon Allah to nasan inda xa ta ko nasan me ya fito da ita” Khaleel ya warce
car key din hannunsa ya fita waje da sauri almost running, Zayyad ya bi bayansa with much surprise.