HEEDAYA CHAPTER 50 BY By Khaleesat Haiydar
Mumy ce xaune dakinta tana ma Shuraim wani kallon tace “Kai me yasa baka da mutunci ne Aliyu?” Da mamaki
yace “But Mum how do u expect me to know what happened bayan nace maki ni bana wajen, ni ban san me ya faru
ba, ki tambayi Abba” Wani kallo ta dinga yi masa, Bayan few minutes jin ta ki cewa komai yace “Kiran kenan
Mumy?” Ta jefa masa wani kallo ta nuna masa kujera tace “Xauna mu yi magana” Ba musu ya tafi ya xauna saman kujeran, tana kallonsa tayi kasa da murya tace “Aliyu ka gaya min tsakanin ka da Allah, ni dai nice na haifeka ba
wani ba….” Shi dai Shuraim kallonta kawai yake, tace “Tell me, do you have any feeling for Heedayah?” Kallonta ya
dinga yi da surprise, can yace “Wacece haka?” Tace “Auuu Heedayar ce baka sani ba?” Yace “Heedayah??” Ta hade
girar sama da ta kasa, can yace “Ohh, Wai Heedayah guda dai da na sani? Feeling na me kenan?” Ganin sai
hararansa take ya d’an yi murmushi yace “Idan ina da feeling for her xaki yrda wani tarayya ya hadani da ita ne?”
Tace “Why not? Ba ubanka bane yyi wahala da ita da rainonta? Ina ce a gidan nan ta taso? kuma ae nasan irin rainon
da aka yi mata ba wanda xai cutar da kai ko ni bane ko da wata alaka ta shiga tsakaninku” Shuraim yace “I don’t
have the feeling you are thinking Mum, ba gobe naji Abba yace xa a kai kudinta ba, Allah ya sanya alkhairi” Kasa ce
masa komai tayi, but she look shocked, ya mike yace “Allah ya tashe mu lfya” Daga haka ya nufi kofa as if babu
abinda ya damesa a lkcn, sai bayan da ya fita dakin nata ya kulle kofa ya ji kamar an axa masa abu me nauyi saman
kirjinsa, xaunawa yyi a hankali saman kujeran parlonta na few minutes, kafin ya mike da kyar ya fice daga parlon
gaba daya ya koma dakinsa. Washegari da safe Shuraim na kwance jin wayarsa dake vibrating a gefensa ya bude ido
a hankali ya jawo wayar yana kallon screen din, Number Mami ya gani, ya kalli wayar for few seconds snn ya daga
ya kai kunne, Mami tace “How are you doing?” Ya cire duvet din jikinsa ya mike xaune yace “Good morning” Tace
“Morning ya gida?” Yace “Alhmdllh” tace “Idan ba damuwa ina expecting din ka nan da anjima Shuraim” ya d’an yi
shiru har sai da tace “Are you there?” Yace “Alright, Amma yau xan koma Lagos ne” Tace “Ka xo din dai kafin ka
tafi” Yace “In sha Allah” daga haka ta katse wayar, ya ji kamar kar ya tafi gidan ya koma yyi kwanciyarsa still
claiming he is fine duk da yanda ya ga rana haka ya ga dare jiya. Karfe goma saura Shuraim ya shigo gate din gidan
Mami, Heedayah ta xagayo daga backyard din gidan kenan ta shanya ma ita da Farida Hijabs dinsu da ta wanke,
suna hada ido ya nufi balcony bai kuma kallonta ba, bin bayansa tayi kafin su karasa balcony din tace “Ina kwana ya
shureen?” Bai tanka ta ba har ya shiga ya kwankwasa kofar parlon, ta tsaya bayansa leaving a little distance between
them, a hankali tace “Ina kwana Yaya” juyowa yyi ta d’an koma baya da sauri, calmly yace “Ban sani ba” Tayi narai
narai da ido tace “Ya Shureen Mami ce ta kalleni jiya shi sa I couldn’t say anything, and I don’t want it to be like she
isn’t saying the truth to the officers….” Yana kallonta da kyau yace “So you both might have face the consequences,
don idan har da gaske ta gaya maki waye wnn mutumin ku ka boye a tare, then both you and her aren’t safe any
longer…..” Heedayah ta marairaice tace “Ni ae gobe xan wuce kano, I won’t stay here, sae in sa Ammina tayi
convincing Mami su dawo kanon su ma, Kuma Mami taji tausayinsa ne kawai kilan don yace mata bashi da iyaye”
Shuraim na kallonta yace “Shi kuma bai ji tausayinta ba yyi kidnapping dinta ko?” Shiru Heedayah tayi tana
kallonsa, ya d’an yi murmushi ya girgixa kai yace “Something is definitely wrong with Mami, coz a barrister won’t
do what she did yesterday” Bude kofar parlon aka yi, duk suka kalli kofar, Farida ce tsaye bakin kofar tana kallon
Shuraim tace “Good morning” yace “How are you” ta basa hanya tace “Alhmdllh” Shiga parlon yyi, Farida na kallon
Heedayah tace “Wankin Hijab tun 8:00 am, Heedayah bata ce komai ba ta shiga parlon ita ma, Shuraim na xaune
parlon suna gaisawa da Dinar da Amira da suka iso daga Abuja safiyar ranan, Dinar na murmushi tace “Ya aiki?”
Yace “Alhmdllh, yau ku ka iso?” Tace “Eh wllh, morning train muka biyo” Amira dai na ta danna wayarta tunda ba
sanin Shuraim tayi ba, Bayan some minutes Mami ta sakko downstairs ta xauna parlon suka gaisa da Shuraim, shi
dai yana wasa da Fadil dake xaune kusa da shi, can Mami tace “I am sorry about yesterday Shuraim, I just had to….”
Shuraim na kallonta yace “Me yasa kike tunanin you have to Mami?” Mami tayi shiru, sae kuma murya can kasa
tace “May be because I am a Mother, and because I never expect that… I never saw it coming” Dinar ta mike ta bar
parlon don bata ma son ci gaba da jin wnn abin dake bata takaici, Amira dai sae kallon uwartata take, Shuraim ma
kasa ce mata komai yyi, Kwankwasa kofar parlon aka yi, Heedayah dake dinning xaune tare da Farida dake shan tea
ta mike ta nufi kofar ta bude, ido hudu suka yi da Khaleel, ta wani xaro ido cikin few minutes ta bar wajen a guje ta
koma can hanyar stairs ta rakube a mugun tsorace, su Mami duk suka bi ta da kallon mamaki, Khaleel ya shigo
parlon da sallama, Farida ta mike da sauri ta bi bayan Heedayah, Mami da Amira kadae suka amsa sallamarsa, ya
karaso cikin parlon kansa a kasa, bai xauna ba ya gaida Mami a hankali bowing his head, Mami ta nuna masa kujera
tace “Morning how are you?” Xaunawa yyi saman kujeran yace “Alhmdllh….” Yana kallon Amira yyi kasa da murya
yace “Ina kwana?” Amira tace “Sannu da xuwa” yyi mata godiya, kallon Shuraim da ya tsiri danna wayarsa yyi yace
“Good morning” Bayan few seconds Shuraim ya dago yace “Morning” Mami tace “Ina abokin naka?” Khaleel yace
“Yana mota a waje” Mami tace “Let him in” Mikewa yyi ya nufi kofa, Amira ta bi sa da kallo har ya fita, Shuraim ya
mike ya mayar da wayarsa aljihu yace “Ni xan koma Mami” Mami tace “Aa ka d’an jira, ae ba mu gama magana ba”
Yace “Xan dawo kafin in tafi anjima in sha Allah” tace “No, sit back Shuraim, xa muyi magana kafin ka tafi din” Ba
musu ya koma ya xauna duk da ko kadan ransa bai so ba, Ba a dau lkci ba Khaleel ya dawo parlon tare da Zayyad,
Yana kallon Mami yace “Ana sallama a waje” Mami xata yi magana Dinar ta sakko ta mika mata wayarta dake
ringing, Mami ta amsa ganin Abba ke kiranta ta daga, bayan sun gaisa ya sanar mata he is outside tace “Toh gani nan
xuwa” Daga haka ta mike ta fita bayan ta sanar ma Khaleel and his friend she will be back soon, tun asuba ta tura
ma Abba message ya xo kafin ya tafi aiki pls, a compound din ta samesa xaune,
ta ja kujera tana kallonsa tace “Ya
gida?” Yace “Fine me yaron nan ya sake dawowa yi a gidan nan Barrister?” Mami tace “Ni nace ya xo” Abba ya girgixa kai yace “Rahinah ni ban san meye matsalar ki ba, all ur words at the station yesterday are nothing but lies,
do you have any agenda to do with this thug da kike rufa masa asiri? Tunda baki son a hukuntasa ba sai ki rabu da
shi ba ki daina basa fuskarsa xuwa maki gida, Why are u behaving this way pls Rahinah? Ba ma shi kadai ya shigo
gidan yanxu har da abokinsa sbda samun waje??” Mami ta sauke ajiyar xuciya tace “There is something I want to
know about him barrister….” Ya dakatar da ita yace “Me saninsa xai kara maki a rayuwa, why are you risking your
life and that of people around you?” Mami tace “Ba haka bane Ahmad, there is something about him that I feel I
need to know, from the little he said about him kamar ba son ransa bane harkan nan da yake yi” Da mamaki sosai
Abba ke kallonta, can yace “Ikon Allah, wato kawai kin ma san Kidnapper din ne shi, to ina ruwanki ko da son ransa
yake ko ba da son ransa yake ba, Jan sa ake su fita operation din ko da kafafuwansa yake tafiya, plss Rahinah stop
all this nonsense idan xa ki bari a hukunta Mutumin nan ki bari, is 30 million 30 thousand??” Mami tayi shiru a
sanyaye tana kallonsa can tace “Don Allah mu basa listening ears barrister, may be labarinsa xai mana amfani, ba
wai nace kada a hukunta sa ba but plss let know how he joined the gang, coz with tears in his eyes yace min he was
never opportune to know his parent” Abba ya dinga mata wani kallo, ta mike tayi kasa da murya tace “For my sake
plss Barrister ka tashi mu je parlon, I invited him and his frnd ba xuwan kansu bane” Barrister ya girgixa kai yace “I
have other important cases to look to Rahinah, dama wnn shine dalilin message din da kika min in xo??” Mami ta
dakatar da shi tace “Pls for my sake Barrister, I am saying plss” daga haka ta fara tafiya, ya bi ta da kallon mamaki
har tayi nisa, text ya shiga turawa a wayarsa yana gamawa ya mike ya bi bayanta xuwa cikin parlon. Bayan Abba
sun gaisa da su Dinar a parlon ya kalli Shuraim da yyi masa sannu da xuwa, Abba yace “You said you are leaving for
Lagos today” Mami tace “Ni na tsayar da shi xuwa anjima barrister” Abba yace “Alright” Mami na kallon Khaleel
da idonsa ke kan Tv tace “I am sorry Khaleel, ba ni kadai xan saurareka ba, ni da barrister will listen to you, if there
is any help we can render you from our discipline we will gladly do that… Amma fa we want nothing but the plane
truth from you, idan kuma muka sameka da laifi xa ayi maka hukuncin da yyi dai dai da wanda ya kamace ka”
Khaleel dai kallon Mami kawai yake, can ya sauke kansa kasa yace “Mami ni me laifi ne dama ae” Mami tace
“Allow us to decide that” Shi dai Zayyad na jin abinda Mami ta fada ya ji he just have to leave that parlor
immediately, Mami could see how uncomfortable he was, haka ma Shuraim dake ta kallonsa, ta d’an yi murmushi
tace “Ka kwantar da hankalinka Zayyad, I am assuring you this… ba abinda xai faru” Abba wayarsa kawai yake
dannawa, Dinar har xata bar parlon jin furucin da Mami tayi ma Khaleel na karshe yasa ta samu courage din xama,
Junaid ne ya sakko parlon rike da makullin motarsa ya shirya cikin white shadda kasancewar ranan Friday ne,
Heedayah da Farida dake jikin rack din stairs sun ki komawa parlon yace “What’s that?” Basu kai ga basa amsa ba
ya kalli parlon, karasawa ciki yyi, Amira ta sakar masa murmushi, Junaid ya gaida Abba, ya ba Shuraim hannu yyi
ma Khaleel da Zayyad ma haka, ganin fita xai yi Mami tace “You stay back Junaid” Ya juyo yana kallonta bai dai ce
komai ba amma ransa bai so ba ya xaga bayan kujera kawai ya tsaya. Mami na kallon Khaleel tace “Now tell us who
you are Khaleel” Khaleel ya kalli Zayyad, Mami tace “Ko shi xai gaya mana?” Khaleel yace “I can’t say daga yaushe
ne nake tare da su Ummi, sau da yawa yana attempting bani labarin dalilin kasancewata da su, amma nasan xuciyata
baxai iya daukan hakan ba sbda ailment dina….” Abba yace “Kwanciyar da kayi kwanaki a Abuja shi ne matsalar da
kake nufi a nan?” Khaleel yace “Eh shine” Abba ya gyada kai sannan ya kalli Zayyad wanda har lkcn ya ki sakewa,
Tun maganar da Khaleel yyi na farko Abba ya ji he is also interested to know him, as a barrister bai ga alamar karya
ko tsoro a tare da Khaleel ba, he is being just Frank, unlike his frnd that at anytime if care isn’t taking xai iya barin
parlon, Abba ya kalli Junaid dake tsaye shi ma yana kallonsu yace “Ka kulle kofar Junaid, we need privacy” Xaro
ido Zayyad yyi, Junaid ya nufi kofar ya sa makulli, Abba na kallon Zayyad yace “Tell us about ur frnd….” Zayyad ya
goge fuskarsa sannan yace “Amma Ina son alkawari daga gare ku na cewar bayan labarin mu da xa ku ji xa ku rufa
mana asiri with out involving hukuma” Abba yace “Don’t worry about that, there is always a reason for everything,
mu baxa mu tona maku asiri ba amma xa mu yi abinda ya kamata” Zayyad yyi shiru, Abba yace “Ka kwantar da
hankalin ka, muna sauraron ka” Zayyad ya sauke kansa kasa yace “Shekaru kusan talatin da hudu xuwa biyar da
suka wuce…..” Kallonsa duk occupant din parlon suke, Zayyad ya ci gaba “Oganmu ya taho da wani yaro da baxai
wuce shekara uku ba daga operation din da suka fita yi gidan wani attajiri, wnn mutumi na daya daga masu kudin
wancan lkcn duk da mu dai ba wasu manya bane don ba a fita da mu irin wnn operation din amma duk mun sani, shi
wnn yaron da oganmu ya kawo shine Khaleel, a ynda Oga Salahu ya sanar mana a lkcn sun kashe Mahaifin yaron
bayan sun kwashi kudade da zinarai masu yawa, bana mancewa daya daga ogannimu na ynxu da ake kira da Arne
wanda a lkcn shi ma yaronsu ne ya tambayi Oga Salahu me yasa ya taho da Khaleel, Oga Salahu yace xai yi mana
amfani nan gaba…. A nan ya bada labarin wai bayan sun harbe mahaifinsa tashi yyi daga jikin mahaifiyarsa dake
rike da shi ya gudu xuwa daki ya dauko bindigogin wasansa wai xai harbe su shi ma, wani oganmu a lkcn yyi niyyar
harbesa Oga Salahu ya dakatar da shi, wnn dalilin kuma ya sa oga Salahu ya daukesa yana rike da bindigar wasan
nasa da yake ikirarin xai harbe su, a ynda Oga Salahu ke bamu labari Mahaifiyarsa na kuka da xa su tafi da shi, sai
yake ce mata xai dawo anjima idan ya kashe su duka da bindigarsa, courage, fearlessness da zeal din dake tare da shi
yasa oganninmu suka ji they just have to go with him and raise him, he have to be their own, wnn shine mafarin dawowar Khaleel cikinmu tun yana shekara uku a duniya, sai dai bana mantawa sunansa a lkcn ba Khaleel ba, idan
ka tambayesa ya sunansa xai ce maka Aliyu Usman, Babban Oganmu na gaba daya at that time sunansa Oga Saminu,
to Oga Saminu na da wani yaronsa da yake ji da wanda ‘yan sanda suka kashe a wani operation… sunan yaron
Khaleel, yaron is also brave and intelligent….” Zayyad na nuna Khaleel dake ta kallonsa yace “Shi yasa ya mayar
masa suna Khaleel, kuma har yau idan ba ni ba sai wa enda suka jima tare da mu bbu wanda yasan sunan Khaleel na
ainahi, shi kansa Khaleel bai san sunansa ba ynxu sai da na fada….” Zayyad ya jinginar da kansa da kujera yace
“Khaleel is more than intelligent, wnda duk wanda ke tare da shi baxai so ya bar sa ba, wayonsa kuma ya fi karfinsa
as at then, till now…. ga rashin tsoro, tun yana shekara 7 ya iya harbin duk target dinsa, duk oganinmu na ji da shi ba
kadan ba barin oga Arne, mu da muka jima tare da su ma sai da Khaleel ya nuna bamu iya komai
ba, hatta bera idan
Khaleel yasa kansa xai kamo duk inda ya shiga sai ya kamosa cikin mintuna kalilan, da farko da aka kawosa duk
dare sai yyi kuka yana kiran mahaifiyarsa, amma as time goes on, shekara daya biyu sai ya watsar gaba daya, ba a
ta6a saka wani cikinmu makaranta ba, amma Oga Arne yyi convincing ogannimu sun saka Khaleel….” Shiru Zayyad
yyi yana kallon Mami da ta sunkuyar da kanta hawaye na sauka idonta sosai, Khaleel ma kansa na sunkuye yana
sauraron Zayyad don shi kansa bai san wnn bangaren na labarin nasa ba sai a ynxu, xamowa kasa yyi a hankali ya
xauna xuciyarsa na bugawa, Shuraim dai sai kallonsa yake kamar yanda Junaid ma ke kallonsa ko kiftawa bbu,
Abba ya sauke wani ajiyar xuciya underneath his breath yace “Innalillahi wa Inna ilaihi raji’un….” Bayan few
seconds Abba ya kalli Zayyad da yyi shiru yace “Go on….” Mikewa Mami tayi, Abba na kallonta da mamaki yace
“Ina xa ki kuma?” Bata iya tace masa komai ba ta nufi stairs hawaye na ci gaba da sakko mata uncontrollably…..