HEEDAYA CHAPTER 52 BY By Khaleesat Haiydar

HEEDAYA CHAPTER 52 BY By Khaleesat Haiydar

Www.bankinhausanovels.com.ng 

A hankali Khaleel ya bude idonsa ya shiga bin inda yake kwance da kallo, Shuraim ne xaune kan kujera daga 

gefensa yana danna waya, Shuraim ya daga kai yana kallonsa yace “How are you feeling?” Mikewa xaune Khaleel 

yyi yana sake bin dakin da yyi masa kama da ward din asibiti da kallo, Shuraim ya mike tsaye yace “You need 

something?” Khaleel yace “Why am I here?” Shuraim dai kallonsa yake bai ce komai ba, aka bude kofar ward din 

Junaid ya shigo, ganin Khaleel xaune ya nufesa yace “Ya jikin?” Khaleel yyi shiru duk da yana jin ciwo sosai a 

kirjinsa amma kokarin son ya tuno abinda ya faru yake but he couldn’t arrive at anything, can kuma ya kalli agogo 

dake nuna tara saura ya kalli window ya gane tara na dare ne, sake kallonsu Junaid yyi a hankali yace “Why am i 

here?” Junaid ya kwantar da murya yace “You were sick…” Zayyad ne ya shigo ward din da sallama, Khaleel sae 

kallonsa yake har ya nufo gadon da yake xaune, Zayyad yace “Are you better now?” Khaleel yace “I think so, but 

me ya faru?” Zayyad yace “Idan ka ganka kwance asibiti ae ba sai ka tambayi me ya faru ba, you just have to 

understand that cutarka ce ta tashi” Khaleel yace “Na sani amma…. baya tashi without cause” yana kallonsa ya fadi 

haka, Zayyad yyi murmushi yace “Ka samu lfya, shi yasa kke questioning din mu haka, you’ve been unconscious tun 

sha biyu na rana har xuwa tara na dare, do you mind a cup of tea?” A hankali Khaleel yace “Meaning I’ve missed 

Juma’at prayer?” Zayyad ya gyada masa kai yace “Kayi a asibiti” Junaid ya karasa gun flask da cup dake ajiye ward 

din ya shiga hada ma Khaleel shayi, walking slowly Shuraim ya nufi kofa ya fita daga ward din, ba a kuma dau lkci 

ba sai gashi ya dawo tare da wani likita…. Khaleel bai iya ya sha shayin da Junaid ya hada masa mara xafi ba duk da 

yana jin yunwa, sosai kuma yake jin xuciyarsa na masa axaba kawai daurewa yake don idan ana sabo da ciwo ya ci 

ace ya saba da wnn ciwon, duk effort dinsa na son tuna abinda ya faru ya kasa tuna komai, iyaka dai ya tuna shi da 

Zayyad sun fita daga gida da safe kuma gidansu Junaid suka tafi, Zayyad ya ajiye masa kfruit salad a gabansa ganin 

ya ki shan shayin, a hankali Khaleel yace “Anjima xan sha, I am not feeling okay” Dauke Fruit din Zayyad yyi, 

Khaleel ya koma ya kwanta bayan ya sha magungunan da likitan da ya fita ya basa, nan da nan kuma bacci ya 

daukesa, sai kusan sha daya na dare Shuraim ya bar asibitin, Junaid da Zayyad kuma suka kwana tare da Khaleel. 

Karfe sha daya na safe Khaleel ya sake farkawa tun bayan tashin da yyi da asuba yyi wanka, sllhn ma a daki yyi duk 

da yyi niyyar fita masallaci amma ya kasa, bin ward din ya dinga yi da kallo ganin mutane sun kusa shidda a dakin, 

Ya mike xaune da kyar, Abba ya nufesa yace “Ya jikin Khaleel?” Yace “Na ji sauki, Ina kwana?” Abba yace “Lfya 

lau, no pains?” Khaleel ya gyada masa kai, Baffan Junaid ma ya karaso yyi masa sannu, Abba ya fita ward din tare 

da sauran mutanen dake ciki, bayan few minutes Khaleel na kallon Junaid yace “Zayyad fa?” Junaid xai yi magana 

aka bude kofar ward din Mami ta shigo tare da Heedayah da su Dinar rike da basket din abinci, Kallonta kawai 

Khaleel ke yi, without blinking, Mami tunda ta kallesa sau daya bata sake barin sun hada ido ba, ta karaso ta tsaya 

daga kusa da window, shi dai kallonta kawai yake, Heedayah ta nufesa ta tsaya daga gefen gadon tana kallonsa a 

hankali tace “Ya jikin ya Khaleel?” Sai a snn ya kalleta, ya d’an yi murmushi yace “Naji sauki” Su Dinar da Farida 

ma duk suka gaishesa ko wacce ta kasa karasowa kusa da gadon da yake, ya amsa ba tare da ya yrda ya kallesu ba, 

Kallon Mami ya kuma yi, cikin sanyin murya tace “How are you feeling now?” A hankali yace “Na ji sauki, Ina 

kwana” Tace “Lfya lau, Allah ya baka lafiya” daga haka ta nufi kofa ta fita daga ward din, Shi dai Khaleel kallonta 

yake har ta fita, Can ya juya ya kalli su Dinar, juyawa duk suka yi kamar hadin baki suka fita daga ward din gaba 

daya, Heedayah ta bi su da kallo haka ma Junaid, mikewa Junaid yyi ya bi bayansu, Heedayah ta juyo a hankali ta 

kalli Khaleel, hawaye ta gani makale idonsa, da damuwa tace “No kaga baka da lafiya plss, do not stress ur self” 

Cikin sanyin murya yace “Are they afraid of me??” Heedayah na kallonsa tace “No they are not, why will they be? 

Kawai suna tausayin ka ne sosai” Ya girgixa mata kai yace “No they are…” Da mayafin jikinta ta shiga goge masa 

idonsa tace “Aa, ba tsoron ka suke ba, duka suna tausayin ka ne, they are feeling your pain” Shiru yyi yana kallonta, 

ta sakar masa murmushin karfin hali, Ya sauke idonsa cikin raunin murya yace “Yanxu Mami ce mahaifiyata?Wani murmushin ta kuma yi masa ta gyada masa kai tana kokarin boye nata hawayen tace “I am glad you are 

reuniting with ur family, even though basu sanka ba baka san su ba, they are all very happy to have you back in there 

mist” Kamo hannunta yyi yace “Meeting with you is something I will never forget till death Heedayah, ban taimake 

ki shekarun baya don in sake haduwa dake ba….” Murmushi kawai Heedayah ke yi tace “Destiny… Allah ya riga da 

ya rubuta ta dalilin ka xan hadu da iyayena kai ma kuma ta dalilina xaka yi reuniting da family dinka” Murmushin 

yyi shi ma yana gyada mata kai, har ranta taji dadin murmushin da yyi, lkci daya kuma ta ga murmushin yyi fading, 

a hankali tace “Are you okay?” Ya sauke idonsa yace “You know what?” Ta girgixa masa kai, yace “Ina tsoron kada 

family din ki su rabamu after knowing who i am” a sanyaye tace “No one is separating us in sha Allah” ya girgixa 

kai yace “Bbu wanda xai so ‘yar sa tayi mu’amala da thug…” Da damuwa tace “You are not a thug, in sha Allah babu 

kai bbu mutanen nan daga yanxu…” Shiru yyi yana kallonta, tace “Yes, you have nothing to do with them, and

justice shall prevail….” Bude kofar ward din aka yi duk suka juya Shuraim ya shigo da sallama… Kallo daya yyi 

masu ya dauke kai, ya karaso ciki ya ajiye ledan hannunsa, ya kalli Khaleel dake kallonsa yace “How are you feeling 

now” Khaleel yace “Alhmdllh na ji sauki” Shuraim yace “Allah ya kara lafiya” Khaleel ya amsa da “Ameen, thank 

you” Heedayah ta d’an kalli Shuraim tace “Ina yini ya Shureen” ba tare da ya kalleta ba yace “Lafiya” Kallon 

Khaleel yyi yace “Allah ya sauwake xan koma, later Dr xai yi discharging din ku” Khaleel yace “Toh nagode 

kwarai” Kofa Shuraim ya nufa Heedayah ta bi sa da kallo har ya fita, Kallon Khaleel dake kallonta tayi, ta d’an yi 

murmushi ta nufi ledan da Shuraim ya kawo taga gasasshen kaza ne sai tiriri yake, ta kalli Khaleel tace
“In dibar 

maka?” Khaleel yace “Aa na ci abinci yanxu” plate ta dauka xa ta diba tace “Toh ni xan ci” Bai ce mata komai ba har 

ta gama diba ta juyo, still taga yana kallonta, a hankali yace “Ina son maki tambaya Heedayah” Tace “Ina ji” yace 

“Tell me, meye tsakanin ku da Shuraim din nan?” Heedayah tace “Nothing, kawai dai Abbansa guardian dina ne, and 

I was raised in there hope after parting with my parent” Khaleel yace “Amma kin san yana son ki?” Shiru Heedayah 

tayi tana kallonsa, can tace “So na kamar yaya kenan” Khaleel bai kuma ce mata komai ba, Junaid ya shigo ward din 

Mami na biye da shi. Karfe uku na yamma aka yi discharging Khaleel daga hospital, mota daya suka shiga tare da 

Junaid da Zayyad, Mami da Heedayah da wata sisters din Mami biyu da suka xo daga gombe suka shiga motar 

Mami… Junaid na xaune gefen gado a bedro dinsa yana kallon Khaleel da yaga kamar ko magana me yawa bai son 

yi, duk abinda junaid xai ce masa a takaice yake amsawa kuma baya kallonsa, ganin ya gama buttoning din shirt 

dinsa Junaid ya mike yana nuna masa turarurrukansa dake gaban mirror, ba musu Khaleel ya nufi gun turaren ya dau 

daya ya fesa snn ya juyo yana kallon junaid, junaid yayi masa murmushi yace “kayi kyau” Khaleel ya sauke manyan 

idonsa cikin sanyin murya yace “Thank you Bro” Mikewa Junaid yyi yace “Ana jiran ka….” Daga haka ya nufi kofa, 

Khaleel ya bi bayansa suka fita dakin, Heedayah ta bude kofar dakinsu kenan ganinsu ta tsaya, Khaleel bai yrda ya 

kalleta ba ya fara sauka stairs ta bi sa da kallo, Junaid ya juya ya kalleta ta dauke kanta da sauri, Tsaye Khaleel yyi 

bakin stairs yana kallon mutanen dake xaune parlon, Ganin junaid ya karasa cikin parlon ya bi bayansa walking 

slowly, nan saman carpet duk suka xauna, Mami sai kallon Khaleel take tana kokarin ganin hawaye bai sakko mata, 

Khaleel ya gaida mutanen dake parlon gaba daya cikin sanyin murya, ko wannensu dai kallonsa yake, Mami ta nuna 

masa wasu dattijai mata biyu a hankali tace “Ur aunties, kannin mahaifin ka kenan…” Khaleel ya kallesu amma ya 

kasa cewa komai, hawaye suke suma suna kallonsa, Mami ta nuna masa uncles dinsa, snn ta nuna masa sisters dinta 

biyu, ta nuna masa duk cousin dinsa dake parlon su ma, bbu wanda baya goge hawaye a parlon, Khaleel dai ya kasa 

cewa komai sai bin su yake da ido lkci daya shi ma hawayen ya kawo idonsa, Mami ta goge hawayen dake xubo 

mata ta nuna masa su Dinar tace “Ur sisters, sauran aunties dinka da uncle suna hanya” mikewa Farida tayi ta karasa 

kusa da shi ta rungumesa ta fashe da kukan dake cin ta cikin rawan murya tace “I am happy meeting with you big 

bro, Alhmdllh for reuniting with us…” Khaleel was just short of words, he can’t believe all this are his families, bai 

ta6a tunanin yana da su a duniya ba balle su hadu watarana, sai yake ganin abun kamar a mafarki xai iya farkawa a 

ko da yaushe, Dinar da Amira ma kukan suke suna kallon Khaleel, Khaleel ya dafa Farida cikin sanyin murya yace 

“I am happy meeting with you too sis”

Mami na xaune compound din gidan ta tare da Abba da wata colleague dinsu, Abba yace “So now how do we go 

about it??” Barrister Khadijah tace “Kun san inda matsalar take ynxu?” Abba na kallonta yace “Aa sai kin fada” tace 

“An tafi station da shi Khaleel din tun farko, a can kuma yyi denying he isn’t a Kidnapper so did Barrister Rahinah, 

so ynxu idan aka kai maganar station to get all the thugs arrested, first tambayar da xai fara biyowa shine… Khaleel 

isn’t a Kidnapper how did he know that they are?” Shiru duk su Abba suka yi suka yi suna kallonta, Barrister 

Khadijah tace “The matter is so complicated…” Abba yyi murmushi yace “Noo, it’s not Barrister, bbu complications.. 

Of course Khaleel wasn’t a Kidnapper amma a cikinsu yake, a cikinsu kuma ya rayu ta dalilin rabasa da suka yi da 

iyayensa suka kai sa cikin nasu, don haka bai san kowa ba sai su, his being in their midst ba shine ke bada tabbacin 

yana harkan da suke ba… Baya tare da su a mugun abinda suke aikatawa, kuma sbda baya taren da su ma yasa xai 

tona masu asiri, ai a case din nan baxa mu nuna we have anything to do with Khaleel ba, baxa mu nuna akwai wani 

alaka tsakaninmu da shi ba, we will act as though he is a stranger….” Barrister Khadijah tayi murmushi tace “What if 

the Kidnappers have enough proof that will look as though he worked with them? That aside we need to think deep 

su ma dubarunsu yawa ne da shi, they can blackmail him just as they did few days ago…..” Mami ta sauke ajiyar 

xuciya tace “And ku bar cewa he wasn’t a Kidnapper, he was, kuma kamar yanda Barrister ta fada baxa a rasa proofs 

din ba, may be images or videos of him a tare da su, tunda ai a da yana tare da su har ma yana contributing” 

Barrister Khadijah tace “Definitely kenan dole sai an tafi da evidence din baya tare da su police station before their 

arrest….” Abba yace “Exactly, and this evidence just have to come from Khaleel, a cikin evidence din kuma dole 

cikin 100% ya wanke kansa da kansa ko da 70% ne, sai ya bar mu da sauran struggles din wankesa….” Mami ta 

girgixa kai tace “Duk da haka Khaleel me laifi ne sosai a wajen hukuma, da ya tashi ya gansa cikin hoodlums abinda 

ya kamata yyi shine ya jawo hankalin hukuma tun farko, idan kuma baxai yi hakan ba sai ya bar cikinsu kawai….” 

Abba yace “But did you listen attentively to his story yesterday Rahinah?” Shiru Mami tayi tana kallonsa, Abba yace 

“on several occasions yayi yunkurin guduwa daga cikinsu, amma bayan kwana biyu sai kuma ya ga ya koma cikinsu, 

yana kuma jin kamar idan bbu su baxai iya rayuwa ba… Did you listen to that?” Mami ta kasa cewa komai, Barrister 

Khadijah na gyada kanta tace “Asiri gaskiya ne” Abba yace “Toh don haka mu baxa mu ga laifinsa ta nan ba unlike 

hukuma, yanxu abinda xai faru kawai evidence xai fito daga Khaleel, I will talk to him about it now, later in the 

evening kuma xa mu hadu” a sanyaye Mami tace “Toh Allah ya kai mu, Shuraim ya koma ne?” Abba yace “Jiya ya 

koma” Mami tace “Toh Allah ya tsare sa” Abba yace “Ameen, I sent you text daxu baki yi replying ba” Mami tace 

“Oh, I wanted calling you in maka bayani ne, baki sun yi yawa ne a gidan wllh” Abba yace “Ohk” Mami tace “I 

spoke to him about it this morning, sai yace min a daga xuwa wani lkci har a gama wnn case din” Abba yace “That’s 

thoughtful of him, Allah ya kai mu, is he inside?” Mami tace “Ehh yana ciki” Abba yace “Alright then, xan koma 

great barristers sai mun hadu da yamman, but before then idan kun shiga ciki ku turo min Khaleel din” Mami tace 

“Toh shkkn I will” Bude gate aka yi duk suka juya, Mumy ce ta shigo tare da tawagarta har da Salima, ganinsu Abba 

ta karasa da fara’a inda suke zaune, Mami na kallonsu tace “Sannun ku da xuwa” Gaisawa suka yi, Su Sadiya da 

Baturiya suka gaida barrister ya amsa yana danna wayarsa, Mumy tayi kasa da murya tace “Ashe abinda ya faru 

kenan Hajiya Rahinah? Toh Allah ubangiji ya tsare iya haka, Allah ya rabamu da mugun ji ko mugun gani, muna 

taya ki murnan dawowan dan ki bayan shekaru masu yawa…” Mami tace “Allah ya saka da alkhairi, Allah ya bada 

lada” Mami ta mike tare da barrister Khadijah suka yi ma Abba sallama suka wuce ciki tare da su Mumy da 

kawayenta. Mumy sai kallon Khaleel da ya shigo parlon ya gaishesu take, bai kara second daya a wajen ba ya fita 

daga parlon xuwa wajen Abba dake jiransa a waje, Mumy tayi tagumi tace “Allah sarki rayuwa, gashi mu bamu ta6a 

sanin kina da d’a namiji ba ma balle, da yake
babu hakki sai gashi bayan an cire rai, toh Allah ya bar mu da ‘ya 

yanmu dai har mutuwa” Mami dake parlon da su Hajiya Zuwaira da step mum din Sudais dai bata tanka ta ba, 

Mumy tace “Toh an samu an sa ranan Junaid din kuwa? Don barrister ba gaya min xai yi ba wllh” Mami tace 

“Tukunna dai” Mumy ta d’an saci kallon Sadiya basu dai ce komai ba. Khaleel ya xauna saman kujeran dake facing 

Abba ya gaishesa, Abba ya amsa da murmushi yace “Ya karfin jikin?” Khaleel yace “Alhmdllh na ji sauki” Abba 

yace “Toh maa sha Allah, Allah ya kara lafiya” Cikin few minutes Abba ya gama magana da Khaleel ya gaya masa 

duk yanda xa a yi snn suka yi sallama ya wuce, Khaleel ya koma ciki yana kara naxarin abinda Abba yace masa. Da 

yamma misalin karfe biyar Khaleel ya nufi kofar fita parlor bayan ya sallami Mami, sai da ya kusa kofar Mami tace 

“Be careful…. and pray, Allah ya tsare ka” juyowa yyi yace “In sha Allah….” a hankali Dinar tace “Allah ya tsare” 

Bai juyo ba yace “Ameen” Heedayah dake xaune dinning ita da Farida suka bi sa da ido su ma, kasa daurewa 

Heedayah tayi ta mike ta bi bayansa, babu wanda yace mata komai har ta fita parlon, parking space ta ga ya nufa, 

tace “Ya Khaleel” ya juyo ganinta ya tsaya, ta karasa inda yake da damuwa tace “Where are you going to?” 

Murmushi ya mata yace “Xan fita ne, anjima xan dawo in sha Allah” tace “Xaka fita xuwa ina? Kana son su ganka 

ne kuma?” Yace “Aa ba inda xa su gan ni xan je ba” tace “Toh xan bi ka, should I go and tell Mami?” Yace “No” ta 

marairaice tace “Plss mana, I don’t want anything to happen to you” yace “Nothing will happen to me Heedayah” shiru tayi tana kallonsa, yace “To rakani gun motar sai ki koma ciki and pray for me” a sanyaye tace “In sha Allah” 

Murmushin sa me kyau yyi mata, tace “Da motar yaya xaka fita?” Yana tafiya tana biye da shi yace “Ehh” Ta 

madubi Junaid dake warming din motar tasa ma yayansa yake kallonsu har suka iso, sai a snn Heedayah ta gansa, ta 

wara ido tace “Lahh ashe kana nan Yaya” yace “Ina nan” Fitowa Junaid yyi daga cikin motar yana kallon Khaleel, 

Khaleel ya shiga motar, Junaid yace “Allah ya tsare” Khaleel ya amsa da “Ameen, Thank you” sai da Khaleel ya fito 

daga parking space Mai gadi ya bude masa gate snn Heedayah ta daga masa hannu a hankali, ya gyada mata kai, 

bayan ya fita compound din suka koma cikin gida tare da Junaid tana kallonsa suna dai dai entrance din shiga parlon 

tace “Yaya wai me kke shafawa a lips din ka?” Yace “Abinda kike shafawa a naki” dariya tayi yyi murmushi ya bude 

kofar ya shiga ta bi bayansa. Har Khaleel ya isa gidan oganninsu yana communicating da Zayyad ta text message, 

yyi parking a waje yyi deleting duk messages din snn ya nufi gate ya fiddo da spare key dinsa na gidan ya bude ya 

shiga ciki, direct entrance din shiga babban parlon ya nufa ya bude kofar parlon, duk suna xaxxaune parlon, wasun 

su na karta, ga giya ko wannensu na sha a glass cup, wasu kuma na smoking cigarette kida na tashi a speaker, 

Zayyad dake xaune saman kujera shi ma hannunsa rike da cigarette ya dinga kallon Khaleel kamar yanda duk sauran 

mutanen parlon ke kallonsa, Oga Bala ya kyakyace da wani mahaukacin dariya yace “I told you all a xuba masa ido 

xai dawo, to gashi ya dawo…” Wani dariya Oga Arne ya fashe da shi ma yana kallon Khaleel da kyau yace “Da ina 

ka tafi? Ka xata har karshen rayuwarka xaka iya rabuwa da mu ne? Ko dama kana da wasu a duniyar nan bayan mu? 

Ni in particular….” Xaunawa Khaleel yyi saman kujera yana kallonsu gaba daya, Oga Manga yace “Ka saduda ka 

gama boye boyen kanka ka dawo kenan? Lallaba ka da ake ya fara wuce gona da iri, xa mu dau mummunan mataki 

a kan ka wllh” Oga Bala ya nufi Khaleel ya dago kansa yana kallonsa da jajayen idonsa cikin katon muryarsa yace 

“Ka dawo daga raina mana hankalin da kke?” Calmly Khaleel yace “Ehh” Oga Arne yace “Good… akwai operation a 

Abuja, dawowar ka kawai muke anticipating kuma gashi ka dawo, so we are setting off today….” Khaleel ya girgixa 

kai yace “U are mistaken then….” Lkci daya ya mike yana kallonsu gaba daya fuskarsa a tamke yace “Na xo ne in 

sanar maku cewar daga yau na bar wnn mummunan harka da ku ka dulmiyar da ni a ciki tun ina d’an yaro, na bar 

wnn harka da ku ka cusa min a xuciya ba da son raina ba, snn Arne, Manga da Bala I want you all to put this at the 

back of ur mind that… in sha Allah karshen ku ya xo… Sannan kananun kwarin da ke tare da ku su biyo baya….” 

Tashi Oga Arne yyi yana masa wani kallo cikin tsawa yace “How dare you Khaleel? Mu kake ma magana haka? Mu 

kake kira ma karshe??” Khaleel yace “Eh kai, Manga da Bala….” Manga ya mike a fusace ya nufesa ya shakosa da 

karfi yace “A duniyar nan kana da sama da mu ne kake ikirarin xaka ga karshen mu? Har kai kana da gata a duniyar 

nan banda wajen mu, uban me kake takama da shi, dama tsintacciyar mage bata mage, an kawo ka cikinmu kana da 

shekara uku baka da gata baka da kowa haka muka ja ka jiki muka fifitaka fiye da kowa, muka jajirce wajen ganin 

an bar ka kai daya tak kayi boko a cikinmu, Wani hakuri ne ba mu yi da kai ba a shekaru talatin din da suka wuce, 

fita operation da kai sai ka bata ma kowa rai sau tari kayi spoil din mana show don ma kana yi kana shakka, bindigar 

da aka mallaka maka ba shi da amfanin da aka baka yyi maka sai na harbin Iska, sau nawa kake freeing abducted or 

kidnapped victims dinmu ka ja mana uban asara, sau nawa sbda kai asirinmu ke kusa tonuwa sai dai ka fitar da mu 

da kwakwalwarka, amma duk da haka muna ta tausan oganninmu sbda ba kowa Allah ke ba wa ba intelligence din 

ka ba, da ba don Arne ba da Oga Salahu ya dde da harbe ka har lahira shekaru goma da suka wuce, bayan ka ba wata 

yar minister da muka yi kidnapping damar guduwa wanda hakan ya kusa tona mana asiri muka shiga gararin rayuwa, 

ta dalilin ka sai da marigayi Oga salahu ya harbe Arne a kafa wanda har yau Arne yana samun matsala da kafar, Kai 

har ka isa yanxu ka xo kace xaka bar mu bayan duk sadaukarwa da muka yi maka da kokarin ganin ka rayu cikin mu 

shugabanninmu basu cutar da kai ba?? Wllh kayi kadan Brainiac, kayi kadan ka bijire mana ka watsa mana kasa a 

ido, gwara in tarwatse kanka, gwara in kashe ka har lahira….” Yana fadin haka ya xaro bindigarsa daga aljihunsa da 

sauri, kusan a tare suka yi hakan da Khaleel da ya xaro nasa bindigar shi ma yana nuna ma Manga, Arne dake ta 

wani huci ya sa hannu ya sauke bindigar manga cikin kaushin murya yace “Bar shi Mangaaa, bar shiiii” Khaleel bai 

fasa nuna ma Manga tasa bindigar ba, Cikin tsawa Arne na nuna Khaleel yace “Mu xaka ci ma amana? Mu xaka 

kawo ma tashanci??” Khaleel yyi wani murmushi yace “Sai na tashi daukan ma mahaifina fansar kashesa da ku da 

mukarrabanku ku ka yi xa ku san tashanci” da shock duk suke kallonsa, Khaleel ya gyada kai cike da tsanarsu yace 

“Ku ka rabani da Mahaifiyata ina d’an shekara uku ban san kaina ba, ku ka kawo ni cikinku, ku ka lalata min rayuwa, 

ku ka cuceni, kuka koya min mugun hali da mugun nufi, Billah karshen ku ya xo a duniya, daga yau ina me sanar 

maku da babban murya cewar idan ku ka sake bibiyana tare da abokina Zayyad kuna ci gaba da tursasa mu kuna 

cusa mana mugun tunani da mugun nufi a kan mutanen da basu ji ba basu gani ba za ku kare rayuwarku daure a 

kurkuku, na har abada…..” Bude baki duk suka yi suna kallonsu, tuni Zayyad ya mike ya xaro nasa bindigar shi ma 

yana nuna ma Oga Manga, Khaleel na huci ya nufi kofa yana tafiya da baya yana nuna su da bindiga haka Zayyad 

ma yyi har suka fita daga parlon still pointing there gun toward them, a haka su Khaleel suka isa gate ta baya har 

suka fice daga gate din, da gudu suka shige mota a tare, Khaleel ya tada motar ya figa ganin su Manga sun fito a 

guje suka hau harbin tayoyin motar amma tuni Khaleel yayi masu nisa ya karya wani corner da motar…. Zayyad ya 

sauke ajiyar xuciya yace “It was successful” Khaleel bai ce komai ba sai gudu yake yana kallon madubi to be sure basu biyosa ba har dai yyi nisa sosai snn ya sauke wani ajiyar xuciya, Zayyad ya kunna record din da yyi da wayarsa 

yana murmushi…. Mami ce xaune living room tare da su Dinar da wata aunt din Khaleel sai sisters din Mami suna 

sauraron record din wayar Zayyad dake hannun Mami, sae da record din ya kare, kowa na parlon ya sauke ajiyar 

xuciya, ko wanne jikinsa yyi sanyi, Mami ta d’an yi murmushin karfin hali tana kallonsu Khaleel tace “Alhmdllh, it’s 

a great job you two did, ku wuce sama kafin ku ci abinci” Khaleel ya d’an yi shiru sai kuma yace “Ummi baxa mu 

iya tafiya can gidana ba?” Dinar da Amira suka xaro ido, aunt dinsa Aunty Nafisa tace “Wani gidan kuma Aliyu, a 

yanxu ai baka da wani gidan da ya wuce nan, you just have to feel at home kaji” sister din Mami tace ce “Lallai kam, 

this is ur only home for now” Mami na kallonsa tace “You are not feeling at home here right?” Khaleel dai bai ce 

komai ba, a hankali Mami tace “Look at me” Kallonta yyi tace “Nan ne gidanku… wancan gidan kuma ba naka bane 

yanxu, beside you both aren’t safe anymore to be thinking of going out” Shiru Khaleel yyi bai dai ce komai ba, 

Mami tace “Ku wuce sama, xa a kai maku abinci” mikewa yyi suka wuce dakin Junaid tare da Zayyad. Heedayah da 

Farida suka kawo ma kowa dake parlon abincin da suka gama girkawa tare da maid dinsu, Mami tace “Ku kai ma su 

Zayyad a sama, Su Umma ma suna dakina ku kai masu” Komawa kitchen din suka yi, Bayan Farida ta hada abincin 

Khaleel da Zayyad a tray ta sa ruwa da komai a kan tray din ta kalli Heedayah tace “Ki kai masu ya Zayyad din 

sama” Heedayah tace “Ki kai masu sai in xuba ma su Umma” Farida tace “No dont worry ki kai ni xan xuba masu” 

Daukan abincin Heedayah tayi ta fita kitchen din ta wuce sama, ajiye tray din tayi kasa bayan ta isa kofar dakin 

Junaid ta bude kofar snn ta duka ta dau tray din ta shiga dakin da sallama, Khaleel ya shiga buttoning shirt dinsa da 

ya cire button din yana kallonta, tun da ta kallesu sau daya ta dauke kai ta ajiye tray din abincin a saman carpet din 

dakin ta mike tace “Ina yinin ku?” Zayyad yace “Sannu da aiki” tace “Nagode” ta d’an kalli Khaleel ganin kallonta 

yake, ta d’an yi murmushi tace “Welcome” yace “Thanks, ke kika yi girkin?” Tace “Ni da Farida da Zainab” Yace 

“Toh Sannun ku” juyawa tayi ta nufi kofa ta nufi kofa ta fita daga dakin, Zayyad na kallonsa yace “I wish xa a baka 

auren yarinyar nan, nasan ba lallai ciwon ka ya dinga tashi ba kuma….” Khaleel ya kallesa bai dai ce komai ba, 

Zayyad ya girgixa kai yace “But I don’t think a governor will give you his daughter hands in marriage, duk wanke 

kan da xa ayi kuwa” Shi dai Khaleel bai ce masa komai ba still. Khaleel na dakin Junaid har bayan isha yana wasa 

da Fadil da Affan din Amira, Zayyad tun da aka yi isha bai shigo ba, Bude kofar dakin aka yi ya daga kai, Heedayah 

ce tsaye daga bakin kofar tace “Ya Khaleel wai ka sakko downstairs” bata jira cewarsa ba ta juya ta wuce, tare da su 

Fadil ya sakko, ya tadda Dinar da Amira sai Farida da wata cousin sister dinsa Sumayya xaune parlon, sai kallonsa 

Sumayya take har ya shigo parlon ya xauna su Fadil na makale da shi, Amira na murmushi tace “Kana ta xaune kai 

kadai daki” Khaleel yyi murmushi yace “Gashi muna hira da boys”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *