HEEDAYA CHAPTER 56 BY By Khaleesat Haiydar
Karfe goma saura Heedayah ta farka daga baccin da ta koma da safe, kallon sabuwar wayan da Shuraim ya kawo
mata dake ajiye gaban mirror tayi, ta mike xaune, sai kuma ta tashi ta tafi ta dauko ledan ta dawo ta xauna ta ciro
wayar daga kwalinsa, ta dau sabon sim card da ya siyo tare da wayar tana jujjuyawa, can dai ta saka cikin wayar ta
duba ko da kudi a layin taga dubu biyar, number Khaleel ta yi dialing ta kira, har ya katse bai daga ba, can ta kara
kira ya dauka, tayi masa sallama, ya amsa yace “Whose line?” Tace “Nawa” Yace “Ohk okay, an kawo maki wayar
ki daga Kaduna?” Tace “Aa sabuwar waya ce” Yace “That’s good, ya mutanen gida?” Tace “They are fine, are you
still leaving gombe today?” Yace “Ina hanya” Ta wara ido tace “Amma ban ji hayaniya ba” Yar dariya yyi, tayi shiru
tana sauraronsa, his laugh was unique, bata ta6a jinsa yyi dariya ba, yace “Motar haya kike son ki ji na hau?” Tayi
murmushi tace “Aa ni bance haka ba” Yace “Ohk, motar kawu na ne… And i am together with his driver” Heedayah
tace “Toh Allah ya tsare, kun kusa?” Yace “Obviously” tace “Toh Allah ya kawo ku lafiya” Yace “But….” Sai kuma
yyi shiru, tace “But what?” Yace “Is it necessary sai mun tsaya kano?” Bata fuska tayi tace “Ni ba necessity dinka
bace ai… It’s not necessary” Ya wara idanuwansa yace “Sorry ba haka nake nufi ba, anyway in sha Allah xa mu tsaya
kano” Jin ta ki cewa komai yace “Kin yi shiru” Kamar xata yi kuka tace “Wato xa ma ka iya wucewa baka tsaya ka
gan ni ba” Yace “Noo, baxan iya ba” Tace “Toh Allah ya kawo ku lfya” yana murmushi yace “Ameen” Daga haka ta
katse wayar, Har xata ajiye sai tayi dialing number Shuraim da ta haddace, yana fara ring ya katse, sai ga shi ya
kirata, dauka tayi amma bata ce komai ba, yace “How was ur night?” Tace “Fine, good morning” Yace “Morning”
Tace “Ya Shureen me yasa baka ce min so kake in bar maka laptop dina gaba daya ba…” Shiru ta ji yayi, can yyi
murmushi yace “Saboda nace maki bani da nawa?” Tace “Toh ai ban sani ba” Yace “Toh xan kawo maki anjima” Ta
wara ido tace “Aa wasa nake, you can use it har lkcn da ka gaji da shi” Yace “Okay kin kira ne just to hear from me
kika fake da laptop?” Ta turo baki tace “Sbda laptop na kira ka” Yace “I see, ya kawarki?” Tace “She’s fine, why do u
ask?” Shiru yyi bai ce komai ba, ita ma tayi shiru, can tace “Ya Shureen me kake son gaya min da na raka ka jiya
kuma ka fasa?” Yace “Naga ke yarinya ce shi sa na fasa” Dariya tayi sosai tace “Yarinya?” Bai bata amsa ba, tace
“Meye ka sani wanda ni ban sani ba har yanxu??” Shiru yyi, can yace “Allah ko?” Tace “Eh mana, ni din ce
yarinya?” Murmushi yyi yace “Ohk, xan nuna maki abinda ni nasani wanda ke baki sani ba” Ta ta6e baki tace “Babu
wannan abun, nice ma nasan abinda kai baka sani ba” yyi shiru…. Can yace “Da yake ke har gidan da ba naku ba kin
ta6a kwana ko?” Shiru tayi ita ma kafin tace “Ban gane ba” Yace “Ohk leave it” Ta hade rai yace “Wani gidan ne na
kwana da ba namu ba?” Yace “Ni xa ki tambaya?” Tace “Toh ai dai naga ba gidan wani daban na kwana ba gidan
saurayina ne” Yace “Haka ne, dole ki san abinda ni ban sani ba kam, i will hang up now ina wajen aiki” daga haka ya
katse wayar, ta kalli screen din snn ta ajiye wayar tana hararansa, mikewa tayi ta fita dakin ta tafi bangaren Ammi,
ganin tana da baki ta wuce bangaren Mum Islam, Mum Islam na kallonta tace “Sai yanxu kika tashi?” Ta xaro ido
tace “Aunty sai karfe takwas da rabi fa na kara wani baccin bayan nayi wanka, mun fa gaisa da Abba tun sassafe”
Mom Islam tace “To xauna dama ina nemanki” Heedayah ta xauna gefen makeken gadonta tana kallonta, Mom
Islam ta xauna gefenta tace “Ki gaya min gaskiya Heedayah…” Sosai gaban Heedayah ya fadi ta dinga kallonta,
Mom Islam tace “Heedayah tell me, ke a xuciyar ki wa kike so, but kar ki manta xaman aure fa ba abinda xa ayi na
shekara daya ko na shekara biyu bane, xama ne na dindindin, xama ne na har abada, ba a fatan rabuwa sai in
mutuwa” Heedayah ta sauke kanta kasa, Mom Islam tace “Ina jin ki, wa kika ji xuciyar ki ya kwanta da” a hankali
tace “Aunty ni Khaleel nake so” Mom Islam tace “Kin tabbatar?” Ta gyada mata kai, Mom Islam tace “Me yasa baki
son kaninsa?” Heedayah tace “Aa ni bance bana sonsa ba, kawai baxan iya aurensa bane, Ya junaid is among the
people that did good to me, yana da kirki sosai, kuma ya nuna min kulawa yanda xai yi ma Farida, amma ni i can’t
marry him” Mom Islam tace “Shi kuma Khaleel me yasa kike sonsa?” Heedayah ta d’an yi shiru, Mom Islam tace
“Ina jin ki” A hankali Heedayah tace “Ina sonsa sbda shi ne mutum na farko da ya fara taimakona a rayuwa, Ina
sonsa sbda yana da hali me kyau if not of the situation he found himself, kuma na ga yana da rikon addini duk da
haka, kuma ina tausayinsa sosai, I don’t want anything to happen to him ta dalilina, Aunty ai kinsan condition dinsa”
a sanyaye ta kare maganar, Kallonta kawai Mom Islam take kafin tace “Anya ba tausayin Khaleel kike ba
Heedayah?” Heedayah ta kalleta tace “Ehh ina tausayinsa kuma Ina sonsa” Mom Islam ta girgixa kai tace “Aa
tausayin ya fi yawa nake kaga” Heedayah tace “Aa, bayan tausayinsa nasan ina sonsa, tun daga sanda muka fara
waya da shi, Aunty kinsan fa har gidansa na ta6a kwana, his ways of life is perfect, yana rikon addini sosai, kuma in
sha Allah nasan ya daina abinda yake har abada….” Mom Islam tace “Eh nasani” a hankali Heedayah tace “Wllh ina
sonsa Aunty” Mom Islam tace “Toh shkkn Allah ya tabbatar da alkhairi dear” Heedayah ta sauke idonta kasa tace
“Ameen, Yana hanya ma Aunty” mom Islam tace “Xai xo nan?” Heedayah ta gyada mata kai tace “Ya ma ce min ya
kusa” Mum Islam tace “Shine baki sanar ma kowa ba?” Heedayah ta kalleta tace “Yanxu muka yi waya da shi ya
gaya min, naje xan gaya ma Ammi naga tayi baki, shine na xo nan” Mom Islam tace “Toh Allah ya kawo sa lfya”
Heedayah tace “Toh Aunty me xa a dafa masa?” Mom Islam tace “Abinci ba matsala bane ai masu aiki suna can ma
suna yin na rana, kawai xuwa xa muyi ayi masa sabon snacks coz wanda ke da akwai aren’t fresh” Heedayah tace
“Toh Aunty” Mikewa Mom Islam tayi tace “Ki tafi nawa kitchen din Ina sakkowa yanxu” Heedayah tace “Aunty
kitchen nawa ne gidan nan?” mom Islam tace “Kitchen hudu ne” Heedayah tace “Ohk” daga haka ta fita. Sai da suka kusa gama snacks din da suke yi Mom Islam tace “Nasan bakin Amminki sun tafi yanxu ki je ki sanar mata”
Heedayah ta wanke hannunta ta fita kitchen din, bangaren Amminta ta tafi, Kawar Ammi daya ce a parlon, Ammi na
kallonta tace “Ya aka yi?” Heedayah t
ayi shiru bata ce komai ba, Ammi ta mike ta wuce bedroom dinta ta bi bayanta,
Ammi na kallonta tace “You want something?” Heedayah ta girgixa kai tace “Aa Ammi ya Khaleel ne xai xo?” Shiru
Ammi tayi tana kallonta, can tace “Daga ina?” Heedayah tace “Daga wajen relatives dinsa a Gombe” Ammi tace
“Toh ni bani xaki fadi ma ba ai, sai ki sanar ma Babanki” Daga haka Ammi ta fita daga dakin, Heedayah ta fi minti
biyar tsaye kafin ta juya ta fita, kitchen ta koma gun stepmom dinta, Step mum din na kallonta tace “kin sanar
mata?” Heedayah ta gyada mata kai tace “Amma tace ba ita xan gaya ma ba Abba xan gaya ma” Mom Islam tace
“Bari mu koma daki sai in kira private number dinsa yana gunsa idan ya daga sai ki sanar masa” Heedayah tace
“Toh” har suka gama jikinta a sanyaye yake suka fita kitchen din tare xuwa bangaren Mom Islam. Mom Islam ta kira
Abban Heedayah ta mika mata wayar bayan ya daga, nan Heedayah ta sanar masa Khaleel na hanya, Abba yace
“Yau?” Heedayah tace “Ehh” Abba yace “To maa sha Allah, Allah ya kawo sa lafiya” Heedayah tace “Ameen”
Amsan wayar Mom Islam tayi tace “Toh xaka sanar da xuwansa ne kar ya samu matsala wajen shigowa tunda bashi
da wani appointment?” Abban Heedayah yace “In sha Allah” Daga haka suka yi sallama ta katse wayar ta ajiye, a
sanyaye Heedayah tace “Aunty me yasa kamar Ammi bata son ya xo?” Mom Islam tace “Aa tana so mana, tunda
kince ya kusa ki tafi ki shirya sabbin kayanki na can wajenta da tailor ya kawo last week, ki kawo akwatin gaba daya
in xabar maki wanda xa ki saka” Heedayah tayi shiru, can tace “Nawa ni kadai Aunty?” Mom Islam tace “Aa ke da
Farida da kannin Shuraim biyu, amma bai kawo nasu ba tukun” Heedayah tace “Toh a ina aka samu measurement
dinmu?” Mom islam tace “Mami ce ta turo naku, kannin Shuraim kuma Uwarsu” Heedayah tace “Ohk” mikewa tayi
ta fita xuwa gun Amminta, nuna mata trolleyn kayan kawai Ammi tayi, Babban trolley ne sosai, ta ja sa har xuwa
bangaren Stepmom dinta, Mom Islam ta kwantar da akwatin ta bude, kaya ne duk a goge kala ashirin da biyar masu
tsada sosai ko wanne kuma da mayafinsa, duk laces ne da atamfa, mom Islam na duba kayan a nutse tace “Ba su
kenan ba ma, kilan basu gama ba tailors din” Wani ubansun lace me tsada ta fiddo ta ajiye mata, Heedayah ta dinga
kallon lace din, Mom islam ta dauko wani akwatin cikin press dinta ta kwantar ta bude duk takalma ne da jaka kusan
kala goma, Mom Islam tace “Naki ne, tun da aka kawo ban kai gun Ammin ki ba” Takalmi da jaka da xai tafi da lace
din ta fiddo ta ajiye gefen gadonta inda ta ajiye kayan, Heedayah na murmushi tace “Nagode” Mom Islam tace “Ki
shiga bandaki ki sake wanka ki fito” Heedayah ta cire doguwar rigar jikinta, ta shiga bandakin, ba a dau lkci sosai ba
ta fito daure da towel din step mum dinta, a nan dakin tayi sllhn azahar sannan ta shirya, kallonta kawai Step mum
dinta ke yi tana murmushi don sosai kayan su amsheta, Heedayah ta sunkuyar da kanta, Mom Islam tace “Kinyi
kyau sosai my daughter” Murmushi Heedayah tayi tace “Nagode Aunty” Mikewa Mum Islam tayi ta dauko kit din
kayan make up dinta, nan tayi mata very light make up, Heedayah ta dawo kamar ba ita ba, tayi kyau sosai kamar
wata amarya, Mum Islam ta kara fesa mata turarurrukanta iri iri sannan ta dauko mata wani dankunnen zinari da
zobe ta bata ta saka, mom Islam tace “Two month ago wata kawata ta kawo na daukar maki” Heedayah na murmushi
tace “Nagode Aunty” Mom islam tace “Toh kuma ina kika bar wayar kar yyi ta kira” Heedayah ta xaro ido tace
“Lahh yana dakina” daga haka ta fita da sauri ta tafi dakinta dauko wayar, miss call dinsa daya ta gani, ta shiga
kiransa, bayan ya daga tace “Sorry bana kusa wllh, kun iso ne” Yace “Ehh mun ma shigo” Tace “Okay no problem
ko?” Yace “Sure, tare da wani soja” Tace “Toh sai kun karaso” tafiya tayi da wayar ta koma gun Mom Islam, nan ta
sanar mata sun shigo, mom Islam tace “To mu je in hada maki abinda xaki kai masa kar kiyi shirme” Tare suka fita
xuwa kitchen dinta, dama ta sa yan aiki su debo duk abinda suka dafa a different cooler su kawo mata kitchen dinta
su ajiye, mom Islam taga warmer din a jere, ta shiga budesu one by one, shinkafa da miya with cow meat, sai tuwo
da miyar assorted egusi, da garnished cous cous da ya ji hanta, pepper soup na kaza sai xuba kamshi yake, last bowl
din ta bude taga coslow ne ciki, Mum Islam ta kalli Heedayah dake tsaye gefenta tace “What’s his favourite?”
Heedayah ta bude hannu tace “Nima ban sani ba” Mom Islam tace “Toh a kai masa shinkafa da miya da coslow da
pepper soup din, sai a debi cous cous kadan a plate a hada ko?” Heedayah tace “Toh” Nan Mom Islam ta fara hada
abincin a tray, ta dauko ginger and zobo drink da tayi tare da snacks tace “Shi xa ki fara kai masa” Heedayah tace
“Toh” kallon wayarta da ya fara ring tayi tace “Aunty kilan sun shigo” Mom islam na kallonta tace “Toh ki fita ki
shigo da shi” Heedayah ta koma ta dauko mayafinta ta sa takalminta snn ta fita, har wani walwali take kamar amarya
cikin kayan jikinta, a hankali take tafiya, ta gansa xaune inda suka ta6a xama tare da Shuraim, kallonsa take tun daga
nisa don kaftan ne a jikinsa da hula, bata ta6a ganinsa da manyan kaya ba sai yau, sai yyi mata kama da balarabe da
yyi dressing din hausawa, sosai kayan suka yi masa kyau, shi ma kallonta yake kamar yanda take kallonsa har ta isa
inda yake, murmushi tayi ta sunkuyar da kanta a hankali tace “Sannu da xuwa” Yace “Uhn baki gane ni bane?” Ta
boye fuskarta tace “Ya hanya” yace “Alhmdllh” Tace “Toh ka shigo ciki” Yace “Bari in huta kadan” Ta kallesa tace
“Toh a ciki ma ai xa ka huta” Mikewa yayi ta dinga kallonsa, a hankali tace “Kayi kyau” Yace “A’a ke dai kika yi
kyau” Murmushi tayi ta fara tafiya ya bi bayanta, parlon baki ta kai sa tace “Bari in kawo maka ruwa” Daga haka ta
wuce can kitchen din Mom Islam ta dauko tray din ginger drink da zobo sai bottle water da snacks ta fita ta koma
parlon, xaune ta gansa ya jinginar da kansa da kujera idonsa a lumshe, a hankali ta durkusa ta ajiye tray din hannunta tana kallonsa ya bude idonsa yace “Thank you” ta xuba masa ruwa a glass cup ta mika masa ya amsa, Mikewa tayi
tace “Ina xuwa” daga haka ta fita parlon, Bangaren step mum dinta ta tafi, tana kallonta tace “Aunty ya na parlor”
Mom Islam tace “Ohk to bari in je mu gaisa, ki je ki sanar ma Ammin ki” Heedayah tace “Toh” fita tayi ta koma
bangaren Amminta, cikin dakinta ta sameta, ta kasa kallonta gabanta na faduwa tace “Ammi ya iso yana parlor”
Ammi tace “Wa ya iso?” Heedayah tace “Khaleel” Ammi tace “Ohk…” Bayan few seconds Heedayah ta juya ta fita
dakin, a parlon da Khaleel yake ta tadda Mum Islam xaune suna gaisawa, Heedayah ta shigo ta xauna kasan carpet,
Mum Islam na kallon Heedayah tace “Ki kai sa ya gaisa da su Yakumbo” Heedayah tace “Toh” Mikewa tayi tace
masa sai anjima sannan ta fita daga parlon, Heedayah na kallonsa tace “Mu je yanxu?” Yace “Aa let me rest first”
Shiru tayi bata ce komai ba, bayan wani lkci tace “Toh baxa ka ci snack din ba” Xaunawa yyi kan lallausan Carpet
din parlon yace “Mun ci abinci a nan kano fa Heedayah, wllh I am not hungry” Lkci daya ta 6ata fuska, yyi
murmushi ya dau samosa daya yace “Ke ma xo ki dauka idan kina son in ci” D’an murmushi tayi ta mike ta koma
inda yake xaune leaving a little distance between them ta dau samosa daya, kallonta kawai yake har ta kai baki, sai a
snn ya ci na hannunsa, kadan ya ci yace “Ban iya cin abin nan ba, yau na fara ci sbda ke” Heedayah ta
xaro ido tana
kallonsa, ya dau ruwa ya sha, yace “Ya isheni wllh” Shiru tayi tana kallonsa, can tace “Me kafi so cikin abinci?”
Yace “fried rice, rice and stew, meat ko wani iri na halal Ina ci, I love pizza, shawarma, sausage, burger, milk drink,
tea…. I think that’s all” Xaro ido Heedayah tayi tace “Tuwo, wake, taliya, macaroni, egg, fish, different soups….”
Katse ta yyi yace “Hell No, abinda na lissafa maki kadai nake ci a duniya” da mamaki Heedayah ke kallonsa,
Sallama aka yi a kofar parlon, Heedayah ta juya da sauri, Ammi ta shigo parlon, Khaleel ya sauke idonsa kasa,
xaunawa Ammi tayi saman kujera tace “Sannu da xuwa” da ladabi yace “Ina yini” da murmushi fuskarta tace
“Lafiya lau ka xo lafiya?” Yace “Alhmdllh, ya gida” Tace “Alhmdllh, daxu mun yi waya da Barrister tace min tana
kano” Khaleel yace “Ehh tana nan” Ammi tace “Kun hadu da ita kenan?” Yace “Aa ba mu hadu ba” Ammi tace “Ohk
anjima xa mu je da driver sai in daukota in sha Allah” Khaleel yace “Allah ya kai mu” Ammi tace “Ameen, you are
welcome” D’an murmushi yayi yace “Nagode” Mikewa tayi ta fita parlon, Heedayah ta wara ido tana kallonsa tace
“Ashe Mami ma ta xo?” Yace “Ehh ta xo” Heedayah tayi murmushi tace “Xan bi ku mu koma” Ya wara ido bai dai
ce mata komai ba, tagumi tayi tana kallon dogon hancinsa, ya shafa kansa ya bude goran ruwan ya diba a glass cup,
a hankali tace “Zayyad fa?” Yace “Yana gombe mun hadu ma” tace “Wajen wa a Gombe?” Yace “Shi ma Yan
uwansa na can gomben” Heedayah tace “Ohkkk” wayarta dake hannunta ne ya fara ring ta kalla ta ga Shuraim ke
kiranta, a hankali tayi silencing wayar, Khaleel dake kallonta yace “Pick ur call” tace “Aa ban san waye ba” Wani
samosan ta dauka ta fara ci tace “Me yasa baxa mu je mu gaida su kaka ba yanxu?” Yace “Xan je anjima kadan” Mai
aiki ce ta shigo parlon ta gaida Khaleel da ladabi tana kallon Heedayah tace “Aunty tace ki je” Heedayah tace “Toh”
mikewa tayi tana kallonsa tace “Bari in je in dawo” Ya gyada mata kai ta wuce, tana Isa bangaren Step mum dinta,
tace “Abbanki ya kira yanxu yace yaje office ya samesa” Heedayah tace “A ina office din?” Aunty tace “Government
house” Heedayah tace “Toh wa xai karasa da shi?” Aunty tace sojoji suna waje suna jiransa, Heedayah tace “Ohk”
daga haka ta fita dakin, bayan ta sanar ma Khaleel abinda Aunty tace, ita ta rakasa har inda soldiers din suke snn ta
koma ciki. Sai bayan la’asar Khaleel ya dawo, Heedayah har ta canxa kayan jikinta xuwa wani sabon atamfar me
tsada, xaune ta samesa a parlor, ta xauna kasa tana kallonsa tace “Sannu da dawowa” yace “Thanks dear” mikewa
tayi tace “Bari in kawo maka abinci” yace “Na ci abinci” tace “A ina” murmushi yyi yana kallonta a hankali yace
“Wllh na ci” Tayi shiru, shi kam kallonta kawai yake, murya can kasa tace “Mami ta xo tana sama wajen Ammina”
Yace “Ohk…” Bude kofar parlon aka yi suka juya a tare, Shuraim ne ya shigo Heedayah ta dinga kallonsa, ya ja gefe
ya tsaya, Sudais ya shigo parlon, wara ido Heedayah tayi ta mike tana kallonsa tace “Ya Sudais” murmushi ya sakar
mata yace “Cutie…” Bata san lkcn da ta nufesa da gudu ba, saura kiris ta rungumesa lkci daya ta ja baya, sai kuma ta
fashe da dariya tana kallonsa, shi kam murmushi yake, Khaleel ya dauke kansa, Shuraim dama tuni yyi hakan…. Barin su Shuraim yyi a wajen ya karasa cikin parlon ya mika ma Khaleel hannu suka gaisa, Heedayah suka karaso
parlon tare da Sudais, Sudais na murmushi ya mika ma Khaleel hannu shi ma, Khaleel ya mika masa nasa suka gaisa,
Kofa Shuraim ya nufa Heedayah ta bi sa da kallo tace “Ya Shureen are you going??” Ba tare da ya juyo ba yace
“Yea” daga haka ya fita, Heedayah ta mike ta tafi ta kawo ma Sudais ruwa yana kallonta yace “Cutie shine kike gudo
kika bar mu a kaduna?” Murmushi tayi tace “Aa ya Sudais na xo hutu ne xan koma soon” yace “Toh ya su mama?”
Heedayah tace “Bari in kirata ku gaisa” Yace “Noo ba kina da bako ba kar ki damu anjima xan dawo, yanxu sauri
mu ke kawai nace bari in xo mu gaisa, xan wuce jigawa ne immediately” a hankali tace “Toh yaushe xaka dawo?”
Yace “Before Magrib idan Allah ya yrda” Daukan ruwan yyi ya sha yace “Let me get going don in dawo da wuri”
tace “Kai da ya Shureen xa ku je?” Yace “Aa nan kawai nace ya rakoni” mikewa yyi ya karasa gun Khaleel ya sake
basa hannu still smiling yace “Xan koma” Khaleel yace “Allah ya tsare hanya” Heedayah ta bi sa da kallo tace
“Allah ya dawo da kai lafiya ya Sudais” Yace “In sha Allah cutie” daga haka ya nufi kofa, Khaleel yace “Ki rakasa
mana” ta kallesa tace “In rakasa?” yace “Ehh” mikewa tayi ta nufi kofa da sauri ta fita, tsaye ta gansa inda Shuraim
ke xaune a karkashin thatched roofing, ta karasa inda suka Sudais na kallonta yace “Why did you leave him?”
Murmushi Heedayah tayi tace “Raka ka xan yi” yace “Noo, Kar ki damu ki koma kawai, amma fa kar ki ce da kaka
na xo” tayi murmushi tace “Baxan gaya mata ba” Ta kalli Shuraim dake danna wayarsa tace “Ina yini ya Shureen”
without looking at her a takaice yace “Lafiya” Mikewa yyi yana kallon Sudais yace “Toh mu je” Daga haka ya fara
tafiya, Sudais yace “Sai na dawo Heedayah” daga masa hannu tayi ya bi bayan d’an uwan nasa, sai kuma ya juyo
yana mata murmushi yace “Saurayin naki so handsome…. Kamar balarabe” Da sauri Heedayah ta juya ta koma ciki
tana murmushi, bayan ta shiga parlon ta xauna kasa kusa da Khaleel tana kallonsa da murmushi fuskarta tace “Ya
Khaleel kasan waye ne shi” Yace “I think xan xo in wuce yanxu, so that I can reach Kaduna early” Shiru tayi tana
kallonsa, ya mike yace “Erm kice da su Ummi na wuce, bana son night journey” Rasa abinda xata ce masa tayi, can
ta sauke idonta kasa, ya dau wayarsa yace “I bought you perfumes, suna mota, but bari in wuce da su kaduna
anytime kika dawo ki karba” Jin bata ce komai ba still yace “Ain’t you talking?” Hawayen dake makale idonta ya
sakko, shiru yyi yana kallonta, can ya koma ya xauna yace “To me na maki kuma kike kuka?” Ta rufe fuskarta da
kujera hawaye na sauka idonta, kallonta kawai yake, can yace “Hasbunallah, yanxu kukan me kike Heedayah?” Ta
share idonta ta mike tace “Allah ya kiyaye hanya” daga haka ta juya xata bar wajen ya fixgota, fadowa tayi gefensa
kan kujeran, ta fashe da kuka a hankali…. Ya kwantar da ita shoulder dinsa a hankali yace “Tell me plss me yasa kike
kuka” taki cewa komai yana jin hawayenta na sauka jikinsa, sosai jikinsa yyi sanyi, ya sa daya hannunsa yyi
wrapping dinta much closer to him, sai ta xama yar karama kusa da shi, lkci daya ta tsayar da kukan da take, ya
daura goshinsa saman kanta cikin sanyin murya yace “I am sorry Heedayah….” ita dai ta kasa ce masa komai, ta ji
gabanta ya hau faduwa, xame jikinta ta fara yi amma ta kasa kwace kanta sbda irin rikon da yyi mata, kamar xata yi
kuka tace “Ka sakeni” ya ki saketa, a hankali yace “Tell me kukan me kike?” Tace “Plss ka sakeni ya Khaleel” ya
dago kanta yana kallon kwayar idonta da idanuwansa da suka sauya launi lkci daya, ta ki yrda su hada ido gabanta
sai faduwa yake, a hankali yace “Me yasa kike son kula wasu mazan??” Xaro ido tayi ta kallesa, yace “Me yasa
kullum sai Shuraim ya xo wajen ki? And what stopped you from hugging the other guy??” Kamar xata yi kuka tace
“They are all my brothers fahhh….” Kauda kanta tayi ganin kallon da yake mata, bata ta6a jin xuciyarta na bugawa
irin haka ba, gaba daya jikinta yyi sanyi, xata kwace kanta still ya ki saketa, ta juyo ta kallesa kamar xata fashe masa
da kuka tace “Y
aya plss ka sakeni, kar wani ya shigo” sosai canjawar da idanuwansa suka yi ke bata tsoro, ya kamo
hannunta cikin taushin murya yace “Heedayah” bata yrda ta kallesa ba, ya juyo da kanta da damuwa yace “Don’t
break my heart Heedayah, Ina maki son da nima ban san irinsa ba, Ina maki son da bbu macen da na ta6a yi ma…”
Sauke idonta tayi kasa jikinta yyi sanyi ba kadan ba, ya daura forehead dinsa saman nata yace “Kin ji?” Muryarta na
rawa tace “I won’t….” Ya daura lips dinsa saman dogon hancinta ya lumshe idonsa, ta kwace kanta da karfi gabanta
na faduwa ganin abinda yake son yi, xamowa kasa tayi ta xauna, ya biyota kasan a hankali yace “I am… Am sorry”
kasa kallonsa tayi, shiru duk suka yi na kusan minti biyar, can yace “Xan shigo da daddare in sha Allah” Daga haka
ya mike tsaye da kyar ta saci kallonsa ta sunkuyar da kanta, ganin ya fara tafiya, a hankali tace “Don Allah da gaske
xaka dawo?” Ya juyo yace “In sha Allah, Mami tace in bari mu tafi gobe” Ta sunkuyar da kanta ya nufi kofa, a
hankali ta dago ta bi sa da kallo gabanta na faduwa har ya fita. Har Magrib Mami na can bangarensu Kaka, tun da
Heedayah ta je ta gaisheta bayan tafiyar Khaleel bata sake xuwa ba tana bangaren Step mum dinta, sai bayan da tayi
Magrib ta fita xuwa gun Amminta, Ammi na bedroom dinta tare da su Ashnaah, Xaunawa tayi ta gaida Ammi,
Ashnaah ta nufeta tana nuna mata takardan hannunta tace “Aunty Abba ne ya siya min da Ashfah” Heedayah ta
amshi takardan tana dubawa, Ammi tace “Bakon naki ya tafi?” Heedayah tace “Ehh tun da yamma” Ammi tace
“Kadunan ya wuce?” Ta girgixa kai tace”Yace min da Mami xa su koma gobe” Ammi bata kuma ce mata komai ba,
bayan wani lkci Heedayah ta mike ta fita tunawa da tayi Khaleel yace xae xo da daddare, dakinta ta tafi ta dau
wayarta ta xauna gefen gado tayi dialing number din Shuraim, har ya gama ring bai daga ba, ajiye wayar tayi tana ta
xaune gefen gado sai ga kiran Khaleel, Dauka tayi a hankali tayi picking ta kai kunne, daga daya bangaren yace
“Come out now…” Tace “Ohk baxa ka shigo ku gaisa da Mami ba?” Yace “Mun yi magana ta waya da ita” Heedayahta 6ata fuska tace “Aa ka dai shigo plss” ya d’an yi shiru snn yace “Ohk” katse wayar tayi ta mike ta d’an gyara
fuskarta ta feshe sabon hijab dinta da turare sannan ta fita dakin tana rike da wayar, parlon baki ta samesa, ta nufesa
tana murmushi ta durkusa gefensa tace “Ina yini?” Ya shafa kansa yace “Lafiya lau” ta mike tace “Mu je ku gaisa”
yace “Where?” Tace “Sama” Bai ce mata komai ba ya bi bayanta, tafiya sosai suka yi har suka iso bangaren da su
kaka suke, ta bude kofar a hankali tare da sallama, Kaka na xaune parlon da Yakumbo, Mami ma na parlon tare da
Shuraim, kaka na ta kallon Heedayah tace “Rakiya ba don iyayen Heedayah ‘yan halaq bane da shkkn mun
taimaketa a banxa ko bi ta kanmu baxa ta sake yi ba a rayuwa, Ina lura da ita bata wani farin ciki da xaman gidan
nan da nake yi, toh bata farin ciki mana tunda ba gaisheni take ba kwata kwata yanxu” Heedayah ta hade rai ta ba
Khaleel hanya ya shigo parlon da sallama cikin cool voice dinsa, Tsit kaka tayi, Yakumbo ta sunkuyar da kanta,
Heedayah na kallon Shuraim ta nufi Mami ta durkusa kusa da ita da murmushi tace “Mami good evening” Mami
tace “How are you dear” Xaunawa Khaleel yyi daga inda Shuraim yake, Shuraim ya basa hannu suka gaisa, Khaleel
na kallonsu kaka yace “Ina yinin ku?” A tare kamar hadin baki suka ce “Lafiya lau” ko wacce na kirkiran murmushi,
ya kalli Mami yace “Ina yini Ummi” Mami tace “Lafiya lau, how was the journey?” Yace “Alhmdllh” tace “Ka baro
su lfya?” Yace “Suna gaishe ku” Mami tace “Maa sha Allah” Kaka da Yakumbo dai kallo kawai suke a TV, Khaleel
ya mike yace “Xan koma” Kaka tace “Toh madallah, Allah yyi maka albarka, ina Junaidu?” Mami tace “Yana
Kaduna” Kaka tace “Atohh, shi dama ba mai son yawace yawace bane” Mami dai bata ce komai ba, Khaleel yyi ma
Mami da Shuraim sallama snn ya nufi kofa, Heedayah ta mike sai da ta ga ya fita parlon ta kalli Shuraim ta hade rai
kamar xata yi magana sai kuma ta fasa ta bi bayan Khaleel da sauri, Yakumbo ta bi ta da kallon damuwa. Khaleel bai
yarda ya xauna parlon baki ba wai ya fi son waje, bbu ynda ta iya masa kawai suka fita, tana kallonsa a inda suka
xauna tace “Toh abinci fa?” Yace “Naga alama kina da son abinci sosai, ke dai kawai aci abinci?” Dariya tayi ta rufe
fuskarta tace “Toh laifi ne don an ci abinci” Murmushi yyi bai ce komai ba, tace “Kayi shiru?” Yace “Na sha fruit
before coming” Tace “Just fruit?” Yace “Yea and am okay” Sun fi minti arba’in xaune wajen daga karshe ganin yanda
yake lullumshe ido tana basa labari, ta bata fuska tace “Wai bacci kake ji?” A hankali ya bude idonsa yace “Yes dear,
na gaji da yawa” Shiru tayi tana kallon kyakkyawan fuskarsa, Can tace “Toh ai Abbanmu yace ka kwana nan” da
sauri yace “Noo, I’ve already lodged a hotel” tace “Toh me yasa baxa ka kwana nan din ba” Yace “Nothing” Tace
“Toh shkkn, gobe ai xaka xo kafin ku tafi” Yace “Uhn xan xo” Ta rungume hannu ta hade rai tace “Ban yarda ba”
Yyi murmushinsa me kyau ya kai hannunsa a hankali kan hancinta yace “Ko mun yi auren wnn wahala kawai xaki
dinga bani, kin fiye rigima” Ta rufe fuskarta da hannunta, ya mike yace “Ai ni nace maki xan shigo idan Allah ya
yrda” A hankali tace “Toh Allah ya kai mu” tashi tayi tace “Bari in raka ka first gate din can” Yana kallonta yace
“Okay dear” a tare suke tafiya, taji ya kamo hannunta a hankali, ta kallesa bata dai ce komai ba har suka isa gate din,
tsayawa yyi yana facing dinta, ta sunkuyar da kanta, murya can kasa yace “Thanks for ur care sweetheart” Bata ce
komai ba ya kai hannunta bakinsa yyi pecking, sosai gabanta ya fadi, ta ki yarda su hada ido, ya saketa cikin sanyin
murya yace “Sleep tight dear” Ta gyada masa kai kawai ya fita gate din ta juya ta koma building din gidansu tana
tafiya a hankali….. Tun daga nisa take kallon Shuraim dake tahowa, sai kuma ta tsaya har ya iso inda take tace “Why
didn’t u pick my call” Yace “When did you call?” Tace “To ka duba wayar” Ya fiddo wayarsa a aljihu ya shiga call
log, kafin yace komai ta amshi wayar tana kallon call log din, taga bayan miss call dinta ya daga kira har uku, ta
kallesa tace “Kace baka gani ba” Yace “Ohk na gani, ban ga damar dauka bane” Ta tabe baki tace “Toh ai nima ba da
kai xan yi magana ba, dama naga ya Sudais bai dawo bane shi sa na ke son in tambayeka ko ya wuce ne, da ina da
number sa ma baxan kira ka ba” Tana fadin haka ta mika masa wayarta tace “Sa min number sa” shafa kansa yyi a
hankali yana kallon wayar da take mika masa, can ya sa hannu ya amsa, tafiya ta ga ya fara yi, ta xaro ido tace “Ina
kuma xaka da wayata” Bai juyo ba balle ya bata amsa, ta bi sa da sauri tace “Ya Shureen ina xaka tafi da wayata,
number ya Sudais nace ka sa min fa” ganin ya ki tsayawa kuma ya ki ce mata komai ta riko hannunsa kamar xata yi
kuka tace “Ni dai ka bani wayata, ba kawai sai kace min baxa ka bada ba….” Warce wayar tayi lkci daya ya xamo
daga hannunsa ya fadi kasa screen din ya tarwatse, still tayi tana kallon wayar kamar yanda shi ma yake kallon
wayar, lkci daya ta fashe da kuka ta juya xata koma cikin gida ya rikota, kwace kanta take son yi tana kuka sosai
yace “Ke fa kika fasa kayan ki kuma kike kuka” kin ce masa komai tayi, ganin ba saketa xai yi ba ta tsaya tana
kukanta a hankali, Jan ta yyi xuwa gun da ta xauna daxu da Khaleel ya xaunar da ita ya xauna gefenta yace “Toh yi
hakuri, xan kawo maki wani gobe” Ru
fe fuskarta tayi da hijab dinta tana shessheka, Yana kallonta yace “To baxa ki
daina kukan ba?” Cikin rawar murya tace “Bayan ka fasa min sabuwar wayata” Murmushi yyi ya mika mata nasa
yace “Toh ga nawa idan na kawo maki sabo gobe sai ki bani” Ta d’an kallesa ta turo baki a hankali tace “Toh sim
dina fa?” Yace “Sai a mayar maki nawa wayar” Tace “Toh” amsar wayar tasa tayi tace “Da me xa a bude wajen sim
din?” Yace “Ke xan tambaya” Ta bata fuska tace “Toh bani da pin” yace “Likewise me” shiru tayi ta sunkuyar da
kanta, yace “Ohk, let me see ur earring” Cire hannun Hijab din tayi ta bude hijab din tana nuna masa dankunnenta,
ya kai hannunsa ya cire earring din daya snn ya bude wayarsa ya cire sim cards dinsa, ya bude nata ya ciro sim dinta
ya maida wayarsa, nasa kuma ya saka a wayarta, daukan wayar tasa tayi ta kunna ta mika masa tace “Ka cire lock
din” amsa yyi, yayi yanda tace, yana kallonta yace “Shkkn?” Ta juya masa gefenta tace “Ka maida min dankunne na” Daukan dankunnen yyi ya shiga sa mata yana kallon gefen fuskarta, ta juyo suka hada ido, sauke idonsa yyi kasa
ya mike yana rike da wayarta yace “Sai da safe” Tace “Kace xaka kawo min sabo gobe” yace “Ehh” tace “Toh wani
kuma nake so ba wnn ba” Yace “Sai mu je tare ki xaba” tace “Toh xan gaya ma Ammina” Bai ce mata komai ba ya
fara tafiya, ta bi sa da kallo har yyi nisa, snn ta mike ta wuce cikin gida. Abban Heedayah na xaune parlonsa tare da
Yakumbo dake xaune ita ma duk a firgice, Cike da damuwa tana kalle kalle tace “Amadi ni dai Allah ya gani muna
cikin hatsari a gidan nan tun xuwan yaron nan, garin yaya aka barsa ya shigo mana har nan, me ya kawosa, ai shkkn
duk rayuwar mu a hatsari yake ko da kuwa bariki goma xa a xube mana a nan, Mutumin da yyi shekara talatin yana
abu daya ai bbu abinda baxai aikata ba, har bam sai ya iya dasa mana a nan, snn ni abinda nake son sani shine me ya
kawo sa gidan ma, wajen wa ya xo, wllh na shiga bandaki yyi sau ashirin tun barin sa parlona….” Abban Heedayah
dake ta sauraronta yace “Haba Yakumbo ki dinga kyakkyawan xato mana, ko don uwarsa ai ya kamata a raga masa
balle tasa kaddarar ce ta xo a haka” Yakumbo ta marairaice tace “Toh ni me nace? Ka ji na xagesa ne?” Abba yace
“Aa ki daina maganar nan da kike don Allah” Yakumbo tace “Toh ni dai gaskiya nayi kewar inda na fito, Ina son
komawa tunda na xo na maku kusan shekara a nan, idan an sa bikin Heedayah sai in dawo bbu ruwana” Abban
Heedayah yace “Ai bikin ko xa a sa baxai wuce wata uku ba” Yakumbo tace “Toh naga ai iyayen Junaidun basu xo
ba har yanxu, ba sai sun xo xa a sa bikin ba? Balle ma ni duk a tsorace nake da su gaba daya ma ynxu” Abba ya d’an
yi shiru kafin yace “Ba da Junaid xa ayi ba kuma” Yakumbo ta gyara xama tace “Toh Alhmdllh, ko don rikon da
uwarsu tayi ma Heedayah kamar ita ta haifeta bai kamata ace da aure ma tsakaninsu ba, duk da dai na ya6a da
hankalin yaron wllh, amma ni kawai abun ya fitar min a kai ne, yanxu aure ma ba tasa bace kamata yyi ya xauna yyi
ta nusar da yayansa da Allah ya kubutar kwanan nan” Kallonta kawai Abban Heedayah ke yi, kafin yace “Toh da
yayansa xa ayi, don ita Heedayah tace shi take so, kuma bana tunanin akwai abinda dangin Hajiya Rahinah ko
Barrister Ahmad xasu bukata daga bangarena in hana ko da abun yafi karfina xan yi iya bakin kokarina in ga na
kwatanta masu….” Yakumbo kallonsa take kamar bata fahimci abinda yace ba, can dai tace “Wani ne a dangin nasu
yace yana son Heedayar kake nufi ko me, ni ban gane ba” Abba yace “Shi dai Khaleel din ke sonta da aure, ita ma
kuma ta shaida min shi take so, Barrister ya kirani mun yi magana, Yan uwan mahaifinsa ma sun kirani munyi
magana jiya, kanin mahaifinsa ma na da wani mukami a nan gombe, gidansu ba kananun mutane bane, gida ne me
tarihi me kyau da usuli, ynxu xa mu jira ne a gama shari’ar da ake a kotu snn a sa rana wanda baxa a ja lkci ba idan
Allah ya yrda, ni na yrda da kaddara, me kyau ko akasin haka, kaddarar Khaleel ne sai yyi rayuwa cikin gurbatattun
mutane, kaddarasa ce sai sun gurbata masa rayuwa, amma ynxu Alhmdllh da Allah ya maidosa hanya madaidaiciya
ya shiryesa, ni baxan kyamacesa ba kamar yanda Uwarsa bata kyamaci tawa ‘yar ba, snn bana fatan wani nawa ya
kyamacesa, ba laifinsa bane don ya tsinci kansa a rayuwar da yyi a baya…. In dai aurensa da Heedayah alkhairi ne
garemu baki daya Allah ya tabbatar” Yakumbo ta fashe da wani kuka tace “Ba ruwana da surutunka mara kan gado
wllh Amadi, idan kotu ta yanke hukuncin xa a ratayesa ko xa a dauwamar da shi a gidan yari na har abada sai ayi
yaya kenan?” Abba ya girgixa kai yace “Dangin ubansa baxa su ta6a barin hakan ya faru ba, haka zalika
mahaifiyarsa da ta kasance babban lawyer, snn ga mijinta da shi ma babban lawyern ne, idan kuma an ajiye
batunsu… laifin Khaleel ba mai yawa bane tunda bai ta6a kisa ba” Yakumbo ta kara rushewa da kuka tace “Katon
mutumi ya xauna ya giggilla maku karya yace bai ta6a kisa ba ku yrda, dama an ta6a d’an ta’adda da bai ta6a kisa
ba? To wllh ni dai da ya auri Heedayah gwara kawai a kasheni” Tana fadin haka ta mike ta fice daga parlon, Abba ya
girgixa kai don darun Yakumbo ba matsala bace a wajensa, shi dai yasan bbu abinda xai hanasa bai ma Khaleel
auren ‘yar sa, sai in shi ya fito da kansa yace ya fasa. Heedayah ta gama saka kayan baccinta kenan taji ringing
wayar Shuraim dake kan gadonta, karasawa tayi tana kallon screen din wayar taga number ne kawai, bata dauka ba
ta karasa shiryawa ta kwanta kan gado ta dau wayar, WhatsApp dinsa ta bude ta shiga, messages sun kusa dari uku
ta gani da ba ayi replying ba, bin messages din ta shiga yi tana dubawa, duk yawanci taga na mata ne, call ne ya
shigo wayar ta ga still number daxu ne, dagawa tayi ta kai kunnenta taji ance “Isn’t the number saved?” Ta d’an yi
shiru kafin tace “Ehh no name” yace “Toh wani labarin ku ka yi da saurayin naki yau?” Tace “Me yasa kake
tambayata?” Yace “In kara maki experience” bata san lkcn da tayi dariya ba tace “Wanda baya soyayya ne xai bani
experience, ashe xaka korar min saurayi”