HEEDAYA CHAPTER 58 BY By Khaleesat Haiydar
Basu yi awa daya suna tafiya ba motar da Heedayah ke ciki ya gangara daga tsakiyar motocin da yake yyi parking
gefen titi, hakan yasa duk sauran motocin har da na gabansa suka yi parking, Heedayah ta bude motar ta sauka ta tafi
gefen ciyayi ta durkusa, Shuraim ya sakko daga motar da yake ciki ya nufeta yana kallonta, sojojin ma duk suka
sakko daga mota, lkci daya Heedayah ta mike da kyar tana kallonsa tace “Ya Shureen amai nake ji” Tsayawa yyi ya
jingina da motar ya rungume hannunsa yace “Toh kiyi” ta koma ta durkusa sai kuma ta dago kamar xata yi kuka tace
“Ya ki xuwa” gaba daya she’s restless alamar aman na damunta, bai ankara ba sai gani yyi ta duka da sauri ta fara
kwararo amai a kan ciyayi, ya tsaya yana kallonta, can ya bude motar ya fiddo bottle water dake ajiye kan kujera ya
bude ruwan, sai da ta gama sannan ya karasa ya mika mata, ta amsa da kyar ta wanke fuskarta ta mike tana maida
numfashi, ya bude mata motar yana kallonta, shiga tayi ta jinginar da kanta da kujera xai rufe motar a hankali tace
“Don Allah ka shigo nan Ya Shureen, ni kadai ce” yace “In shigo in maki me?” Da damuwa tace “Ka xauna, kuma
kace ma driver ya rage Ac din sanyi nake ji” Da kamar baxai shiga ba, sai kuma dai ya shiga motar ya rufe, sauran
sojojin suka koma motarsu, Shuraim ya umarce driver da ya rage sanyin Ac, drivern yyi haka nan suka ci gaba da
tafiya. Lumshe ido tayi daga haka bacci ya dauketa, sai da suka iso Zaria ta bude idonta a hankali, daga kai tayi ta
kalli Shuraim dake danna wayarsa, ta kalli shoulder dinsa da ta daura kanta, gyara xamanta tayi tace “Ba mu kai
ba?” Bai ce mata komai ba, ta karbi wayar hannunsa ya kalleta, tace “I am asking ko mun kai” yace “Ehh har mun
juyo” Yana fadin haka ya kwace wayarsa, ta turo baki ta koma can nesa da shi ta xauna, d’an murmushi yyi ya ci
gaba da abinda yake yi a wayarsa, bude handbag dinta dake hannunta tayi ta fiddo wayarta dake vibrate, ganin
Khaleel ke kiranta sai da gabanta ya fadi, ta dai daga ta kai kunne tayi shiru, daga daya bangaren yyi sallama, ta
amsa, yace “How are you?” Tace “I am fine” yace “Kun taso?” Tace “Ehh mun taso” yace “Okay, ya hanya?” Tace
“Alhmdllh” Yace “Ke da waye?” Ta d’an kalli Shuraim snn tace “Ba kowa, ni da driver ne” Yace “Ohk, Allah ya
kawo ku lafiya” A hankali tace “Ameen” snn ta katse wayar, satan kallon Shuraim tayi suka hada ido don shi ma
kallo ta yyi, ta dauke kanta ta gyara xamanta, har suka shigo kd wajejen karfe sha biyu. A hankali Heedayah ta bude
motar ta sauka bayan driver yyi parking compound din Mami, Farida ce ta fito ganin Heedayah ta taho da sauri ta
rungumeta, Kankameta Heedayah tayi tace “I missed you Farida” Farida tace “I missed you more Didi ya su
Ammi?” Daga kai Farida tayi suka yi ido hudu da Shuraim, yace “Ya kike?” Farida tace “I am fine” juyawa yyi ya
nufi gate ya ciro wayarsa dake ring a aljihunsa, Heedayah ta bi sa da kallo tace “Ain’t you coming in ya Shureen?”
Ba tare da ya juyo ba yace “Xan dawo” Daga wayar yyi ya kai kunne ganin Mumy ce ke kiransa, Ya gaisheta tace
“Shuraim ga ni a kano ka xo ka shigar da ni government house, ina nan kofar Nasarawa gidan ‘yar uwar Sadiya”
Shuraim dake sauraronta yace “Bana kano, Ina Kaduna ynxu” Da wani irin shock Mumy tace “Kaduna kuma? Me
kaje yi Kaduna, kuma wa ka gaya ma xaka je kaduna? To ni yanxu wa xai shigar da ni government house din?”
Shuraim yace “Ki kira kaka ta sanar masu xa ki shiga” A fusace Mumy tace “To wai ma uban me kaje yi Kadunan ne
baka gaya min ba?” A hankali yace “Aiki Mum” Mumy tayi tsaki tace “Toh kawai ka turo min number Maman
Heedayah, kaka mutum ce da xa a kira, ni ka ji da ni ina jira” Yace “To” daga haka ta katse wayar, ya tura mata
number Ammi da ta ce. Heedayah ta ja hannun Farida da ta bi Shuraim da kallo suka wuce cikin parlor, har bedroom
din Mami Heedayah ta shiga ta tafi da sauri ta rungume Mami cike da murnan ganinta tace “Mami good
afternoon….” Mami na kallonta tana murmushi tace “Afternoon My Daughter ya hanya?” Heedayah tace “Alhmdllh,
su Ammi da Aunty sun ce a gaisheki” Mami tace “Maa sha Allah ina amsawa hope baki yi amai a hanya ba”
Heedayah ta boye fuskarta jikinta tace “Nayi sau daya Mami” Mami tace “Allah ya yaye maki, ya Abban ki da su
Yakumbo??” Heedayah tace “They are all fine, they sent their regards, kaka ma next week xata dawo tace amma
kwana biyu kawai xata yi ta koma” Mami tace “To maa sha Allah, Allah ya kawota lfya” Heedayah tace “Mami Ya
junaid fa?” Mami tace “Yana gidan Baffansa, anjima xai shigo in sha Allah” Heedayah tace “Allah ya dawo da shi
lfya” daga haka ta mike tana kallon Mami tace “Xan yi sllh Mami” Mami tace “Toh kiyi wanka gaba daya, idan
kinyi sllhn sai ki ci abinci” Heedayah tace “Toh Mami” daga haka ta nufi kofa ta fita ta kulle ma Mami kofarta,
Tsaye ta tadda Khaleel bakin kofar bedroom dinsa yana sanye da kananun kaya ya rungume hannunsa yana kallonta,
sosai gabanta ya fadi ta sunkuyar da kanta a hankali tace “Ina yini” murya can kasa yace “Lafiya, why did you lie to
me?” Ta kallesa da sauri tace “Na me?” Shiru yyi yana kallonta, kamar xata yi kuka tace “What did i lie about?”
Yace “Kince ke kadai kika taho” da sauri tace “Ehh with… with Escort” Ya gyada kai yace “Good, Sannun ku da
xuwa to” Downstairs ya fara sauka ta bi sa da kallo, snn ta turo baki ta shiga dakin Farida ta kulle kofar, sai bayan da
Heedayah tayi wanka ta canxa kaya tayi sllh snn ta fito dakin ta sauka downstairs, Khaleel na xaune parlon da Farida
dake kusa da shi yana nuna mata abu cikin laptop, tsaye tayi bakin stairs tana kallonsu, ko lura da ita basu yi ba a
wajen, Farida ta wara ido tace “Waow yaya, you are an expert, ni ma ka koya min” ya kyabe baki yace “Xaki
shekara goma baki iya ba” Bata rai tayi tana kallonsa, dai dai nan ta ga Heedayah dake tsaye har lkcn, ta sakar mata
murmushi tace “Ga abincin ki can dinning na ajiye maki” Heedayah bata ce komai ba ta nufi dinning din, can
Khaleel ya dauke laptop din kafarsa ya ajiye kan kujera ya mike ya bi bayanta. Mumy na xaune parlon Yakumbo
tare da Ammi da Mom Islam bayan an gama gaggaisawa, Kaka na kallonta da kyau tace “Toh me ya kawo ki
Maryam??” Mumy ta yi yake tace “Aa biki muka yi, shine nace bari in karaso in kawo ziyara inyi xumunci snn inyi
Allah sanya alkhairi ranan da aka sa ma Heedayah tunda har na shigo kanon” Kaka ta rike ha6a tace “Su xumunci
manya, to amma kina da wasu yan uwa ne a kano wanda bani da labari Maryam?” Mumy ta sunkuyar da kanta tace
“A’a yar uwar Sadiy
a ce aka yi bikinta” Kaka ta kyabe baki tace “Toh sannu da xuwa, gwara kema ki xo ki d’ana
arxiki kar ayi ba ki” Yakumbo ta kyabe baki, Ammi ta mike tana kallon Mumy tace “Mu je can bangaren Hajiya”
Mumy ta mike tana murmushin karfin hali ta bi bayanta suka fita parlon kaka ta bi ta da kallo tace “Kiri kiri ta ki
rike Heedayah bbu irin walakancin da ba mu gani ba daga wajen matar nan, kawai dai a bar kaza cikin gashinta”
Yakumbo tace “Toh ba kanta tayi ma ba, yau ba arxikin Heedayar ta ci ta shigo gidan nan ba, Banda haka meye
hadin mu da ita??” Kaka tace “Kul…. Uwargidan Amadu ce, uwar Shuraim, da ba don Amadu ba kuma Heedayah
kilan sai dai kullum a dinga mata addu’ar gafara gun ubangiji, Kinga kuwa ai ba laifi don ta shigo Gwamnet house”
Ammi na komawa bangarenta da Mumy ta sa masu aiki suka kawo mata kayan ciye ciye da ruwa da abinci, Mumy
sai kalle kalle take tana duba inda xata ga Heedayah ta billo, duk wnn abun da aka cika mata a gabanta ba shine
damuwarta ba, can dai ta kalli Ammi murmushi dauke fuskarta tace “To ina Heedayar ta shiga ban ganta ba” Ammi
tace “Ayya ai yau suka wuce kaduna” Mumy ta gwalo ido da sauri tace “Da wa?” Ammi tace “Ita da Shuraim suka
tafi, taje yi ma iyayenta na can sallama, tunda bikin ba wani lkci me tsayi aka sa ba” Mumy taji xufa ya karyo mata
tace “Yaushe xata dawo kenan?” Ammi tace “Baxa dai ta wuce kwana uku ba ina jin, duk dai yanda Abbanta na
Kaduna yace” Mumy tayi wani murmushin karfin hali tace “Toh maa sha Allah, Allah ya dawo da su lafiya, nima din
dai yau xan koma dama” Da mamaki Ammi tace “Yau kuma Hajiya, ai yamma yyi, ki bari gobe” Mumy tace “Aa ba
mu yi da barrister xan kwana ba, in sha Allah yanxu xan wuce, dama kawai nace in xo inyi Allah ya sanya alkhairi
ne” Ammi tace “Da dai kin hakura gobe Hajiya, hanyar nan bai fiye kyau ba” Mumy ta sauko kasa ta dau snacks
daya tace “Aa Hajiya yanxun nan ma kuwa xan wuce, bari in d’an ta6a abincin” ko minti ashirin Mumy bata kara a
government house ba ta dau hanyar park wajajen karfe uku na yamma. Shuraim na xaune parlon Abbansa yana
sauraron maganan da Abba ke masa, Jin ya ki cewa komai Abba yace “Ka min shiru” Shuraim ya daga kai ya kallesa
yace “Abba ni fa ban san komai kan xancen nan ba” Abba yace “Kwana biyu da suka wuce kaka ta kirani a kan
batun, na kuma yi tunanin kai kayi mata maganan” Shuraim yace “Aa ni ba mu yi wata magana da ita ba” Abba ya
girgixa kai yace “Toh bayan bikin Heedayah ina son inji kace min ga gidan da xa mu tafi nema maka aure, naga
kamar baka san a sa maka ido ba” Shuraim dai bai ce komai ba, bayan few seconds Abba yace “Snn akan batun
mahaifiyarka….” Daga kai Shuraim yyi yana kallonsa, Abba yace “Wannan karan xan dau mataki me tsananin gaske
a kanta, tunda har na hanata fita gidan nan tayi disobeying dina tayi ficewarta, to ta tabbatar ba gidan nan xata dawo
ba” Wayarsa ne ya fara ring, ganin number isn’t saved ya dauke kai, Shuraim dai bai iya yace komai ba, Abba yace
“Ina raga ma Maryam wasu abubuwan sbda ku amma bata gani, duk ina sane da abubuwa da yawa da Maryam ke yi
ba wai bana sane ba, Maryam bata san annabi ya kafu ba, I am overlooking so many things a da, but today I am
done….” Abba ya kalli wayarsa da aka sake kira for the second time, daukar wayar yyi ya daga ya kai kunne tare da
sallama, Jin tambayar da aka yi masa a wayar yace “Ehh, who is on the line” shiru Abba yyi as if trying to comprehend the message passed to him kafin ya ajiye wayar bayan an katse yace “Innalillahi wa Inna ilaihi raji’un”
Shuraim dake ta kallonsa yace “Lafiya Abba?”