HEEDAYA CHAPTER 60 BY By Khaleesat Haiydar
Komawa baya Heedayah tayi, lkci daya tsoro ya bayyana fuskarta, cikin tashin hankali tace “Yaya me ya faru tell me
plss don Allah ka gaya min” Jin Shuraim ya ki bata amsa ta sakar masa kuka tace “Ka gaya min mana Yaya”
Gathering courage yyi ba tare da ya kalleta ba trying to be very strong yace “We just pray for her” Mikewa
Heedayah tayi tana dubansa gabanta na faduwa tace “Kamar ya?” Ya mike shi ma still ya ki kallonta ya kama
hannunta suka bar wajen. Kaka ce ta bude kofar parlon da mutane ke cike a xaune, cikin mutanen parlon Yan uwan
Abba ne na kusa da nesa, sai ‘yan uwan Mumy, Mami ma na parlon tare da Hajiya Zuwaira da su Hajiya Amina, duk
aka daga kai ana kallon kaka, kaka ta rushe da wani matsanancin kuka ta xauna nan bakin kofa tana nanata
“Innalillahi wa Inna ilaihi raji’un, na shiga uku ni Patuu, wai dama da gaske ake?? Da ma wnn mummunan labarin
gaskiya ne?” Bbu wanda ya tanka mata a parlon, Kaka ta daura hannu a ka tace “La ila ha illallahu muhammadur
rasulillahi sallallahu alaihi wassalam, yanxu da gaske Maryam ta rasu?” Ammi ta shigo parlon a sanyaye tare da
Mum Islam dake biye da ita, Yakumbo dama a nan balcony ta xauna tana sharban kwalla, Heedayah dai da Farida na
xaune kusa da Mami sun yi kukan har sun gaji, Hajiya Zuwaira ta mike ta nufi gun kaka ta dagota cikin sanyin
murya tace “Addu’a xa ki yi mata kaka Allah ya gafarta mata” Kaka ta kara rushewa da matsanancin kuka ta
rungumeta tace “Wllh matar kirki ce Maryam, duk abinda aka ga tayi bai kai xuciyarta ba xugar shegu ne, kaf
shekarunmu da ita bata ta6a tanka ni ba, bata ta6a min rashin kunya ba, duk tsiyata da fitinata shiru take min, kuma
anjima baxata fasa xuwa ta min magana ba, ita dai idan ka xauna wajenta cikinka ne xai gaya maka amma wllh ko
kallon banxa baxata maka ba balle maganan banxa, kaf surkaina bbu me raga min sai ita, kuma ba dai kaga ta canxa
fuska ba don Amadu xai yi maka abu ko xai baka abu, bbu ruwanta da wnn wllh wllh, ita dai kawai girki ne bata son
yi balle ta baka ka ci ka koshi, yanxu Maryam ta rasu?? Jiya jiya fa ta sallame mu da yamma wai xata koma wai
Amadu yace kar ta kwana, har Yakumbo ke ce mata ta bari gobe yamma yayi ashe ajali ke kiranta, yanxu ya isilin
marayun nan da ta bari ni Patuu??” Kuka sosai Kaka ke yi Hajiya Zuwaira na lallashinta, Hajiya Amina hawaye ya
kasa tsaya mata haka kishiyarta, ba karamin girgixa su mutuwar yyi ba, daga karshe Hajiya Zuwaira ta fitar da kaka
daga parlon. Sosai aka ji rasuwan Mumy, ba ‘yan uwa ba, ba makota ba, yawanci kuma duk kyawawan halinta ake
fadi, kaka dai ta dage a kan bata ta6a mata rashin kunya ba, ko kallon banxa bata ta6a mata ba, yunwar da ta barta da
shi ma ta yafe mata duniya da lahira, har kwana uku kaka bata daina kuka da jimami ba, ana xaxxaune parlor a
kwana na ukun, Hajiya Sadiya ta shigo tare da Hajiya Balarabe, Sadiya ta rushe da kuka tana rufe fuskarta da Hijab
din jikinta, kaka tayi mitsi mitsi da ido tana kallonta, Sadiya ta karaso tana goge hawayen idonta ta xauna kasa tace
“Innalillahi wa Inna ilaihi raji’un, Allah ya ji k’an Maryam, Allah ya gafarta mata, Allah ya yafe mata” Kaka na mata
wani kallo daga sama har kasa tace “Sai yau kika ji rasuwan kenan?” Sadiya ta ki dago kanta tana matsar kwalla tace
“Eh wllh, na yi tafiya naje Sokoto, garin da naje bbu network sai yau na dawo kaduna, ina dawowa aka sanar min
wai Allah yyi ma Maryam rasuwa” Tana kai wa nan ta saki kuka da karfi, Kaka ta mike tana rike da carbinta tace
“To tashi ki fita, algunguma mayya yar jaraba, Allah ya isa tsakaninmu da ke….” Da sauri Sadiya ta mike har tana
neman faduwa ta nufi kofa Balaraba ma ta mike ta bi bayanta da sauri, kaka ta fashe da kuka tace “In sha Allahu
karshen ku baxai yi kyau ba, duk ku kuka gurbata tunanin Maryam, mata me kirki bbu ruwanta da mugun abu kai
dai idan xaka xo gidanta to ka xo da shirin dinga shiga kitchen ka nema ma kanka abinda xaka ci, amma tsinannun
mutane kawai kun nemi hallakata ku ka fara sa ta yawon banxa, to in sha Allahu muna nan muna mata addu’ar Allah
ya gafarta mata, ya yafe mata kurakuranta, ku kuma Allah kadai yasan yanda xai yi da ku, duk ku ne sanadin canxa
halin Maryam” tuni Hajiya Sadiya da Balaraba suka fita daga parlon, kaka ta koma ta xauna tana matsar kwalla. Da
yammacin ranan Khaleel ya xo gidan tare da Junaid, Kaka na parlor da Yakumbo sai Ta rasulu da wasu step sisters
din Abba, Kaka ta amsa gaisuwarsu cikin sanyin murya tace “Tun da aka yi rasuwan sai yau ku ka xo min gaisuwa
Junaidu?” Shi dai Khaleel bai ce komai ba, Junaid yace “A’a jiya mun maki gaisuwa kaka, kuma ko da safe ma mun
xo har mun gaisa ma….” Kaka tace “Toh duk na rude, ai mutuwar maryam ya girgixa ni d’an nan, ga mutane kamar
kiyashi, duk ana ta xuwa min gaisuwa gidan nan ba masaka tsinke, har daga Nijar, maiduguri da Taraba an xo min
gaisuwa, kaga ai baxan lura da ku ba, to kun ma Amadun gaisuwa kuwa? Shi ma dai duk karfin hali yake, mutuwar
mata ai babban tashin hankali ne, shekaransu talatin da tara tare, sai da suka yi aure da shekara shidda marigayiya ta
haifi Shuraim d’an ta na fari” Junaid yyi kasa da kansa yace “Allah ya gafarta mata” Kaka ta goge kwallar idonta
tace “Ameen dai, Allah ya yafe mata kurakuranta, mu ma kuma Allah ya kyautata namu karshen” Junaid yace
“Ameen” Yakumbo dai sai satan kallon Khaleel take tana wuri wuri da ‘yan idanuwanta, Junaid yace “Shuraim fa?”
Da damuwa Kaka tace “Wa ma ya sani, ni dai nace da ma kukan yyi yanda duk muke yi ko xai ji dadi ya samu
salama, rashin kukan ya fi cutarwa, daxu dai ya shigo da d’an uwan, ban san ko ya fita ba” Junaid ya sauke ajiyar
xuciya yace “Allah ya kara hakuri da dangana” Kaka tace “Ameen, Rakiya na can parlon ku shiga ita ma ku kara
mata gaisuwa, yau kwananta uku a nan gidan ita ma” Mikewa Junaid yyi ya nufi parlon da Kaka ta nuna masa
Khaleel ya mike shi ma ya bi bayansa, Kaka ta bi sa da kallo kasa kasa tace “Yo ba sai ya sa6a xama cikin jama’ah
xai sake ba, mutum dai kamar bass din shirin Indiya, ko murmushi bai yi, naga yanda Deedayah xata xauna da shi
tunda tace ta ji ta gani, ba ruwanmu” Yakumbo tace “To ba dai ita da uban sun ji sun gani ba, har ynxu fa a dari dari
yake da mutane, abin ka da wanda ya saba xaman daji” Mami na xaune parlon tare da su Hajiya Amina da Zuwaira,
Heedayah ma na parlon da Farida da su Rabi’ah da su Zainab, Junaid ya xauna nan kasan carpet din parlon ya gaida
su Mami, Khaleel ma ya xauna ya gaishesu kansa a kasa, Gaba daya ‘yan matan parlon suka gaida su Junaid,
Heedayah dai na kwance idonta rufe ta juya ba, Junaid na kallonta yace “Bacci Heedayah take” Mami ta ta6ata a
hankali tace “Heedayah” da sauri ta bude ido ta juyo ta mike xaune ganinsu Junaid tace “Ina yini Yaya?” Yace
“Lafiya lau bacci kike yi?” Tace “Uhm” Kallon Khaleel dake kallonta tayi a hankali tace “Ina yini?” Yace “Lafiya
lau” Junaid yace ”
Ya karin hakuri?” Tace “Alhmdllh” Junaid yace “Allah ya gafarta mata” ta amsa da “Ameen”
kallon Mami yyi yace “Shuraim na gidan kuwa?” Mami tace “Ehh yana dakinsa with Sudais, you check” Tashi yyi
suka fita parlon tare da Khaleel. Washegari Mami suka koma gida gaba daya, gidan ya rage kaka da tawagarta da
sisters din Abba, har su Rabi’ah Mami ta wuce da gidanta, sosai yaran ke bata tausayi hakan yasa ta sa su debi kayansu su koma can gidan nata tare, tunda suka dawo gida Heedayah gaba daya bata da walwala kai kace
mahaifiyarta ce ta mutu, abinci sai tayi da gaske take ci, Suna kitchen tare da Farida da Maid din Mami suna serving
ma kowa abinci a gidan, Farida ta mika mata plate din abinci da ta xuba ma Khaleel d’an kadan sanin haka yake ci
tace “Ki kai ma Yayanmu” Heedayah ta jingina da cabinet tace “Ke dai ki kai masa, ba wanke wanke xan karasa ba”
Farida tace “Ba ga Zainab na yi ba, meye kuma idan kin kai masa abinci” Heedayah dai bata ce komai ba, can ta
amshi plate din ta dau wani plate ta rufe sanin ba a lkcn xai ci ba idan an kai masa ta juya ta fita kitchen din, sama ta
wuce ta bude dakin junaid taga baya ciki, ta karasa last room dake wajen don yawanci nan yake xama yanxu, ta bude
kofar amma ba gaba daya ba tayi sallama, sai da taji ya amsa snn ta shiga, xaune ta gansa yana danna laptop, ya
daga kai yana kallonta shi ma, har ta karaso ta ajiye plate din tace “Ina yini” Yace “Have u finish mourning?” Ta d’an
kallesa bata ce komai ba, yace “To Allah ya gafarta mata, naga kamar kun shaku da ita sosai ko?” Sake kallonsa tayi
still taki cewa komai, Ya ci gaba da abinda yake a laptop, ta juya xata fita yace “Heedayah” juyowa tayi ya nuna
mata kujera yace “Sit, let’s talk” Ba musu ta dawo ta xauna tana kallonsa, ya d’an yi shiru kafin yace “Kamar naga
baki son aure yanxu ko? Like… Karatu kike son ci gaba da” Ta kallesa, jin bata ce komai ba yace “Feel free talk to
me” Tace “Why did you ask me that?” Yace “Because I have noticed ur changes in behavior” Ta hade rai tace “Wani
irin changes?” Yace “Na baki son auren, may be u have other plans” Ta girgixa kai tace “I have no plans, kuma ni
bance maka bana son auren ba” Ya d’an yi murmushi cikin sanyin murya yace “Don’t worry Heedayah my heart have
been broken so many times nasan damuwar ki kenan, na saba da heartbreak kar ki damu da haka… kawai dai naki
will be different and may be more painful and difficult to endure, but all the same, ba a tilas a aure, I will help you
tell ur parent su bari ki ci gaba da karatun ki….” Heedayah ta girgixa masa kai hawaye na sauka idonta tace “Ni ban
ce haka ba, kai ma kuma kasan I so care about you bana son wani abu ya sameka, ni bance bana son auren ba…. just
that ina son kada ka dinga kokarin hanani mu’amala da yayanni na, and you just have to trust me….. I will never
betray you” Shiru yyi yana kallonta, ya mike ya isa gabanta yace “Baxan hanaki mu’amala da su ba, amma kuma ni
ma kada ki hanani kishin ki” Ta sauke idonta kasa bata ce komai ba. Da daddaren ranan Heedayah ta fito daki xata
kai cup din da ta sha shayi kitchen ta tadda Mami da Shuraim xaune downstairs, Kansa a kasa Mami na yi masa
magana cikin kwantar da murya, shi dai bai ce komai ba, tun rasuwar mum dinsa wnn ne ganinsa na biyu da tayi, ta
wuce kitchen ta ajiye cup din hannunta ta fito, bata karaso cikin parlon ba ta gaishesa cikin sanyin murya, ya daga
kai ya kalleta ya amsa, Mami tace “Ki kawo masa abinci” Ya girgixa kai yace “Aa, I am full” Mami tace “Aa sai ka
ci, you don’t even look like someone that is eating” Shiru yyi bai ce komai ba, Heedayah ta juya a sanyaye ta koma
kitchen din, Ko da ta fito da tray din abinci Mami ta riga ta bar parlon, ta karasa ta ajiye masa tray din gabansa tana
kallonsa a hankali tace “Ya karin hakuri ya Shureen?” Yace “Alhmdllh, how are you?” Tace “I’m fine” Bai kuma ce
mata komai ba, ta xauna nan kasa tace “Ya Shureen plss ka kwantar da hankalin ka, you don’t look okay, don’t get
sick plss” Ya d’an mata murmushi yace “I am okay” Tace “Nooo gashi ka rame” Yace “Katuwa kike son in xama
kamar ki?” D’an murmushin karfin hali tayi bata ce komai ba, yace “Ohk xauna, let’s talk” Ba musu ta xauna nan
kasa tana kallonsa, kamar baxai ce komai ba sai kuma yace “I want to ask for a favor Heedayah” Ta gyada masa kai
tace “Sure, ina ji” ya sauke idonsa yace “Forgive my Mum Heedayah….” Ji tayi xuciyarta yyi rauni sosai, ta girgixa
masa kai hawaye ya kawo idonta lkci daya, cike da karfin hali tace “Bata ta6a min komai ba ya Shureen” cikin
sanyin murya yace “No Heedayah, I wished she had the privilege to ask for ur forgiveness before leaving, my mum
was good, Just all of a sudden….. anyway just Forgive her for the sake of Allah and my father” ta goge idonta tace “I
have done that already, Allah ya gafarta mata” Yace “Ameen, I appreciate, ya shirye shirye?” Tace “Na me?” Yace
“Na bikin ki?” A hankali tace “Ba a fara ba tukun ai” Ya d’an yi shiru, ta daga kai ta kallesa, yace “Toh Allah ya kai
mu lkcn lafiya, ki turo min su Rabi’ah” Tace “Toh” daga haka ta mike ta wuce sama. Mami da iyayen Heedayah sun
so a dage bikin da ya rage saura sati uku yanxu sbda rasuwar Mumy amma Abba ya ki amincewa da hakan, wnn
yasa aka bar bikin lkcn da aka yi fixing, bayan sati biyu da rasuwar Mumy kuma aka hau shirye shiryen bikin duk da
ko kadan hakan bai ma iyayen Heedayah da ma Mami dadi ba, sai dai Abban Heedayah yace daurin aure kawai xa
ayi sai walima bbu wani event…. Biki saura kwana goma Heedayah ta koma Kano ta private jet tare da su Farida da
Rabi’ah…..