HEEDAYAH SHURIEM CHAPTER 4 BY Maryam sule koki {Maman khairiyya}

HEEDAYAH  SHURIEM CHAPTER 4 BY Maryam sule koki {Maman khairiyya}

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Kokarin kwace hannuna nayi Amma Ina nakasa, momy ce ta Fara fitowa sannan yayanmu, Ai bansan sanda wani karfi yazominba nafin cike hannuna nayi hanyar gida ba Ina isowa bakin kofa nayi turus, saka makon ganin Abba da carbi A hannu da alama masallaci zashi.

Shi kuwa Hamza Yana ganin Haka da sauri yatafi zai shige mota beyi auneba saiji yayi Ankai Mai naushi Akeyarsa jibgarsa Yaya yarinshigayi Kamar ba gobe, Abbane da momy suke janyeshi Amma Kamar dutse momy harda duka take hada wa shuriem Amma duk Abanza shibesan ma tanayiba saboda ran Yan maza yabaci.

Abbane yaga lallai inya kyale shuriem zai iyayin kisa da karfi ya angijeshi tareda Shan gabansa shi kuwa Hamza dayaga Abba yasha gaban shuriem mikewa yayi jikinsa duk jini yay gurin motarsa, key yaywa motarsa yabar layin dawani Azababben gudu.

Nikuwa Ina tsaye banda kuka ba Abinda nake, yayanmune yajiyo gurina idansa da suke farare tas sun juye sun zama jajaye Kamar garwashi, Abbane yakuma Shan gabansa tareda daka Mai tsawa wadda tadawo dashi cikin hankalinsa Abbane ya Fara magana cikin rarrashi, Yana cewa “son ba ayin hukunci cikin fushi, laifinmune da bamu gaya Mata matsayinka Agurinta ba shiyasa Haka ta faru yanzu kawuce muje masallaci mudawo inmun dawo saimu zauna muyi maganar”, kallan momy Abba yayi yace” Ashiga da motar gida Kuma kuje kujirani Haka Abba yakama hannun Yaya Kamar wani soko suka nufi masallaci.

Ban tsaya jiran momyba nawuce gida da saurina Ina shiga get natarar da ummi tana labe kallona tayi awulakance tace “ke dama Heedaya Ai Rayuwar data dace dake kenan shima Banda Abun Abba mezesa yadamu da Rayuwarki Haka Banda uwarki ta shanyeshi Aida tuni ya koreki shiya huta muma mu huta Kar kijawo Mana Abun kunya, yanzuma wayasan Abu Aboye.

Cikin gida nawuce tareda fashewa da wani irin. Kuka nabar ummi naci gaba da yabamin maganganu, sadiya. Natarar Afalo da sauri tataso tarungumeni tana kuka tana cewa Heedaya bakyaji kullum kece dag ki tsokalo wancan saiki Aikata wancan Bata karasa rufe bakintaba saiga iya tashigo tanata sababi domin ummi taje ta fesa Mata harda cemata Wai Aje aimin test din ciki Kar asami matsala.

Iya kuwa tas tawanketa domin duk masifar ummi iya ta dameta tashanye, ji nayi tana cewa Bari ubannaki yadawo yau Zaki tattara kibi mijinki mungaji da wannan magana dakike ja Mana, sallamar momy mukaji dukkan muka amsa zama tayi tagaida iya, iya ko amsa gaisuwar bataiba tafara shiwa momy Albarka tareda cewa nadade Banga mace me irin hakurinki da juriyarkiba Ammasu Heedaya ba’a dauko halin uwaba, sannan Ina nan Zaune ,kowacce taje tayi sallar Isha’i tadawo tasameni kafinnan ismailan yadawo, duk tashi mukayi momy tayi hanyar dakinta nida sadiya ma mukayi hanyar namu dakin Abunda ya farune ya Fara dawomin tiryan tiryan har nazo kan zancan iya dakin mijina wa kenan Amma iya tsufa yasa tafara rikicewa.

Bayan mun idar da sallah, Abbama yadawo, bayan sun tattauna da   iya, yasa Aka kirawomu,  yayane Zaune gefen momy Yana Danna waya momy ta kalleshi son bawa sadiya mukulli zataimin shara A part Dinka kafin mugama” dauko mukullin yayi ya mikawa sadiya hartayi hanyar fita momy takirata tace taje dakinta tadauko turaran wuta intagama sharar saita kunnah.

Komawa sadiya tayi tadauko tatafi dakin Yaya, Abbane yakallini yace heedaya  jeki ki kirawomin ummynku tashi nayi, nayi hanyar part dinta Ina zuwa bakin kofa naji ummy na magana da’alama wayatake, Kuma Kara kunnena nayi naji tana cewa Ai  maman meerah yadda muka tsara Haka za’ayi, idan meraah ta auri shuriem tayi kokari tasamu ciki, daganan saimu kasheshi, bayan yayi Arbain saimu Aika Alh. Ismail Sai Kuma naji momy tayi shiru da Alama wadda suke wayace take Mata magana, cannaji momy tace Aikar kidamu maman meerah 50-50 zamuyi karki damu nagode to shikenan sai anjima, inajin ummy takashe wayar natattaro nutsuwata, na kwankwasa kofar, waye yashigo naji tace, shiga nayi na tsugunna tareda fadin ummy Wai kizo Abba na kiranki Amma yace kitaho da mayafinki ganinan jeki zantaho tashi nayi nafita hankalina Atashe Dole nasamu momy muyi magana Adarannan basai gobeba, falon nakoma nacewa Abba tana zuwa momyce tacemin tahadamin ruwan wanka atoilet din dakinta naje nayi tashi nayi Zan tafi Naga momy Bata tasoba, kallanta nayi nace Momy, tashi tayi tace muje, bayan mun shiga dakin nace Mata momy nifa nayi wanka, nasani wani nakeso kisake tafada tana dauko wata Yar’ ubansun doguwar riga red me Adon stone ta ajiye kan gadonta kiyi maza kiyi wanka kisaka banason shirmen banza sainaga tajuya zata fita da sauri nace Mata momy Akwai maganar  dama danakeso muyi kallona tayi Rai Abace tace wato heedaya Dan Kinga nasake Miki shiyasa kikeyin magan ganunki Kai tsaye koh duk Abinda kikayi kin manta koh? Hakuri nashiga Bata can tacemin ya Isa duk Abinda Zaki fada fadeshi A minti 2 Dan bamuda lokaci da sauri  dasauri nashiga gaya Mata Abinda naji ummy na fada awaya, momyna ta firgita sosai tareda gargadin Kar nagayawa kowa, zata dau mataki, sannan tajuya tafita, wanka nayo nazo na shafa Mai NASA kayan da momy tadaukomin tareda fesa turare Masha Allah na fada tareda kallon kaina Amudubi Abinku da farar mace Sai rigar ta amsheni nayi kyau sosai, falon nakoma natarar

Ummi ma iso, wuri nasamu nazauna, Abbane yafara sallama sannan yay Addu’a bayan anshafa yace” Ina godiya ga ubangiji daya nunamin wannan Rana na hada ya’yana aure shuriem da Heedaya Kuma Ayau A yanzunnan zata tare da mijinta, mikewa nayi zumbur tare dafe kirji, ummyma mikewa tayi dagata nuna ni saita nuna Yaya shuriem….

Cikin firgici nanu na Yaya shikuwa ko kallo ban isheshiba, jinayi idona ya kafe kukanma yaki zuwa, magana na farayi kamar Haka ni bazan aureshiba ni bana Sansa wallahi mugunta zai tayimin maganganu iri naringayi Kamar bana cikin hayyacina, momyce ta kalli shuriem Rai Abace tafara magana Wai Kai shuriem wani irin sokon namijine kana kallon Abinda matarka keyi bazaka tsawatar mataba. Jinayi wani kuka yatahomin, Dede Nan Abba yace ya Isa kowa yay Mai shiru, Sai Kuma ummi ta bude babin nata rashin mutuncin maganganu iri iri taringayi kamar wata tababbiya Saida iya tamike tace keeeee rahanatu kikiya yeni indai baki yarda da wannan aureba Sai dai kikoma naki gidan uban, dan Auran shuriem da Heedaya hadine na ubangiji Kuma karyarki Tasha karya kisa awarware wannan aure ke Kuma momyn Yara Ahir dinki da shiga sabgar iyalin shuriem da kike cewa yadauki mataki dukanta kikeso yayi dame Akeso tajine.

Falon ne yayi tsit yayinda ummi takama kanta Dan inbatai wasaba tasan bakaramin aikin iya bane yau ta kwana agidansu.

Iyace tacewa ummy tatashi suraka Heedaya inaji Ina gani iya ta kamani muka tafi part din Yaya Ina kuka Ina komai Amma basuji tausayinaba har bedroom dinsa suka Kaini suka Ajiyeni gefen gadonsa ummi kuwa tazama hoto ganin Abun takeyi Kamar Amafarki zuciyartama taki Bata damar dazatayi tunaniba  saboda tana cikin rudani,   s
undan Jima zaune saiga sadiya da  Akwatin kayana Niki niki, kuka na Kuma runtu mawa, iyace tai saurin cewa Heedaya Kiki yayeni inkina wannan kukan ai angonnaki rainaki zaiyi Sha sha Shar banza, Sha sha Shar wofi, toki Kama kanki kirike mijinki inba hakaba Nanda wata daya za’a daura Mai wani Auran, Dan Haka inzaki dage ki dage ehe, taso mutafi rahanatu Allah yabaku zaman lafiya, ta fada tanayin hanyar fita.

Sadiyace ta matso tareda rike hannuna tanayimin nasihohi iri iri shiru nayi Ina saura ranta, can dai nace Mata sadiya gobe inzaki school kitsayani zanzo mutafi, ido tazubamin da mamaki ke Ina Kika taba ganin Amarya tafita washe garin da aka kaita nidai gaskiya bazan jirakiba, kallan tanayi nace ” to kibiyomin Dan Allah murmushi tayi tace sokike yayanmu yaymin dukan mutuwa kenan irin Wanda yaywa Hamza tafada tareda tashi ta ruga Aguje Aikuwa Nima na mara Mata baya muka fito kofar part din inata kokarin kamata, Yaya muka gani tsaye Agaban mu da ledodi biyu Ahannunshi Ajiye dayan ledan yayi ya wanke sadiya da Mari tareda nunata da yatsa yace idan na Kuma ganunki A bangarena saina babbalaki wace kibani guri da sauri tawuce nikuma Ina tsaye jikina natarawa kallona yayi yace ke Kuma wuce muje sakaryar banza.

Wucewa nayi muka shiga kitcheen din falon yawuce Sai gashida plate guda 2 da cups zama nayi na takure kan kujerar bedroom din shima guri yanema yazauna leda daya yamikomin da plate daya kin karba nayi, kallona yayi yace “Heedaya ko bakici darajar komaiba zakici darajar momy Agurina Amma bazan yarda da rainiba.

 

Karba nayi na Ajiye tabe baki yayi ya Bude ledar, wata katuwar Dan kwaleliyar kazar hausa  yadauko   Sai maiko take  yadora kan plate din ga kabeji ga Attaruhu ga Albasa  Abindai Sai Wanda yagani, sannan yadauko fresh yo! Dinsa ya Ajiye gefe Ahankali yafara ci Kamar me yanga nikuwa Araina nace shi yayanmu Kamar wani mace komai Sai yayi iyayi jinayi yace to ya sanranki.. yacigaba da cin kazarsa nikuwa nai maza na toshe  bakina Ashe maganar tafto bansaniba, bayan yagama Naga yatashi yashiga bayi cannaga yafito da tawul a kugunsa da wani yana goge kansa kasa nayi da Kaina dannasan Yaya bakaramin Aikinsa bane yazageni tas Acikin darennan Haka bayan yagama yashafa yaje ya shafa mansa Mai kamshin gaske sainaga yatashi yadauko jallabiya yasaka sannan Naga yadauko turare kala kala yanata fesawa nidai mamaki kawai na tsaya inayi se kace wata mace, tabe baki nayi, Sai Naga Kuma yahaukan dadduma yadade Yana nafila cankuma Naga yayi Addu’a yashafa sainaga yaje ya haye gadonsa yay kwanciyarsa.

Nima tashi nayi naje nayi Alwala nadawo kan kujerar na kwanta danaji Kamar garin da Dan sanyi Akwatina nabude nadauko hijab na rufa dashi.

Ummy kuwa Ai Aharabar gidan suka rabu da iya Dan tace kanta ciwo yake bayan Takoma part dinta kuka tasaka takirawo Aminyarta Haj. Amina tagaya Mata Abinda yafaru itama hankalinta yatashi sosai tace”  kibari zuwa gobe zanzo saimu samo mafita……✍🏻

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *