HEEDAYAH SHURIEM CHAPTER 7 BY Maryam sule koki {Maman khairiyya}
Bayan na idar da sallah Ina zaune Kan dadduma ina Jan carbi sainajiyo Ana guda gabanane naji yayanke yafadi Anty saudatce ta fuskanci halinda nake ciki, hannuna takama tarike Gam cikinnata hannun, mundan jima Ahaka saigasu sun shigo, Anty saudatce tajawoni muka fito babban falo, da fara’a takarbesu tanayi musu sannu da zuwa.
Bayan sun zaunane wata dattijuwace ta Fara magana acikinsu “ga Amarya nan munkawo Amana yarinyarmu munyi mata tarbiyya bazaku samu matsala daga garetaba.
Anty saudat ce takarbe zancen da cewa muma tamu yar’ batada wani Aibu kyawawan halaye gateta Dan haka muba San fitina kuma mun gode Allah yatayamu riko, hannun merrah suka Kama suka kaita nata falon, Ammafa sun raina gidan sosai, sunata gutsiri tsomar inda Aka ajiyeta bedace da itaba.
Hakadai suka gaji da cece kuce kkwacce ta nufi gidanta, Anty saudat ma saidata karayimin nasihq sannan Yaya taupiq yamaida ita gida.
Misalin karfe goma nadare gidan yayi tsit, jama’a duk sun watse naahiga tunani me zurfin gaske sainaji kamar Ana taba kofar babban falonmu tsorone yakamani saikuma Naga anturo kofar falona Ayda gudu nazabura zanyi bedroom Dina naji Andakamin tsawa aikuwa nakara firgicewa, najuyo dqsauri sainaga yayaunmu fuskarnan ba Annuri, yasha wankansa cikin shadda sky blue, gawqni sihirtaccen kamshi dayake tashi Ajikinsa Kai yayafa dangayune.
Dqsauri nagaidashi ko amsawa beyiba ya AJIyemin wata Leda sannan yace”kiyi Alwala inzaki kwanta kuma ki kashe fitila, niyanzu wurin Amaryata zan wuce” Yana Gama Fada yay wank makirin murmushi Wanda shi kadai yasan ma’anarshi, sannan yajuya yafita, ni kuwa na kame Agurin can kuma narushe da kuka kamar wadda Aka aiko ubanta ya mutu.
Bangaren shuriem kuwa yau cikin farin ciki yake saboda kasancewar ya mallaki masoyiyarsa meerah, da dokinsa yatura dakin meerah yahangota can tsakiyar gado da sauri ta Mike bawani Jan Aji tazo tarungumeshi shi kuwa da kallo yabita Yana mamaki Dan shi Ayadda Abokansa ke bashi labari Amarya najin kunya da kuma tsoro Adaren da,’aka kawota gidan mijinta, begama mama kiba kawai yaga takarbi ledar hannunsa tayi kitchen Sai gata dauke da Trey da Naman kaji Akai Sai gefe ruwan roba da lemuka guda 2.
Zuwa tayi ta Ajiye agabansa babbar rigarsa takama zata cire yace tabarshi ze cire da kansa, kwabe fuska tayi ta Fara magana cikin shagwaba haba dear wqnnan fa ranatace Dan Allah kabarni..
Murmushi yayi yadanganta Abun da tsananin sanda Meerah take masa, kallanta yay yace” kiyi komai meerah yau ranar kice da sauri tarungumeshi tana murna sosai, sannan takama rigar tacire masa, sannan ta debo masa ruwa ta wanke masa hannu nan tafara ciyar dashi, Shima Yana Bata, dadai yaga tafara shige masa, cikin Azama ya Mike yace mata taje tayo Alwala, badan ranta yasoba ta tashi tashige toilet, saboda ita Meera Atsarinta sallah batadameta ita irin mutanan nanne Wanda Asati insunyi tayini 2 cikakkiya to sunyi dayawa.
Bayan tafitone, Shima shuriem yashiga, bayan yafito yajasu limanci ya sukayi sallah raka’a 2 sannan yadora hannunsa Akan goshinta yay mata Addu’a, 🤔🤔🤔🤔🤔 oh ni maman khairiyya yau Naga Abinda yafi karfina, meerah nagani ta Mike takama cire kayanta yarage daga ita Sai undies, maman ibtihal da sister zainab ibrahim naji sun figoni🙄🙄🙄🙄 sunyo waje dani wai bazan dauko muku rahotoba🤫🤫🤫 da Alamu dai su fans din meerah ne, ja nai natsaya bakin kofa Suma suka ja suka tsaya, mun ta tsaye har 3:30am Naga bacci yadaukesu Sai nayi wuf na koma dakin😂😂😂😂……
Meerah ce kwance tana kukan wahala, yayinda shuriem yaketa sharar baccinsa.
Nikuwa haka nayi kwanan bakin ciki haka bacci yadaukeni A falo azaune Kan kujera ban farkaba Sai danaji Ana Kiran sallar Asuba, mikewa nayi, nayi Addu’ar tashi daga bacci, sannan nawuce toilet nayo Alwala nayi sallah, Alkur’ani me girma nadauko nakaranta suratul bakara, Agogo nakalla na 7:00am, tashi nayi nakama gyaran gida bayan nagama nashiga babban kitchen din babban falo na daura break fast, bayan nagama naje nacan cada wanka nayi kwalliya cikin doguwar riga dinkin zamani sannan na feshe jikina da turare, naje najera Abinci Kan dining.
Zama nayi nafara break fast ci nakeyi Amma kamar magani nake taunawa , haka nadaure naringa ci saboda Kar nazauna da yunwa, nakusa gamawa naji motsi Alamun tafiya, daga Kai nayi Naga me tahowa, yayaunmu ne shida meerah, meerah na hangoni tawani lafe jiknsa, nikuwa kasa nayi dakaina wani Abu naji ya soki kirjina, mikewa nayi zanbar gurin naji yayaunmu yace”heedaya koma kizauna, haka nadawo badan raina yasoba.
Yayane ya Fara Zama sanan yajawa meerah kujera tazauna, tea nazubawa Yaya da chips da wainar kwai Sai biredin Dana gasa hadeda girfa, daukan tea din yafarayi Yana sha, Sai kawai naga meerah tajanye filet din gaban yayaunmu tayagi wainar kwai zata Kai Bakinta, hannu nasa natan kwabe wainar tafadi Ajikita banyi auneba naji ta gauran mari.
Nima cikin Azama na daga hannu nawanketa da mari, Yaya shuriem ne ya Mike da sauri tareda daka Mana tsawa, sannan ya Fara magana kamar haka” gidanan ba filin danbe bane duk wadda tace zataimin Fada to wlh saina Saba mata kuji da kyau, ke heedaya kinsan halina banida kyau, innatashi fushi ban iya fushiba.
Meerace ta kalli yayaunmu tace yanzu dear kana kallo ta mareni bazakayi wani Abu Akaiba Sai kuma tafashe da kuka, nikuwa kallon 2 saura kwata nai mata kallan bakisan me kikeyiba, yayane yakalleni yace” heedaya Bata hakuri.
Kallansa nayi da mamaki nace Yaya inbata hakurifa kace, ko bazaki bataba yafada Yana kallon gefe, kiyi hakuri nace, ban tsaya jiran meze kuma cewaba nayi falon da sauri.
Shikuwa shuriem hanyar fita yanufa da sauri meerah tabishi tareda Shan gabansa tace” my love ina kuma zakaje be kalletaba yace zanje gurin momyne, yatsina fuska tayi tace wace ce wannan Babar waccan Abar ta Fada tana nuna dakin heedaya dahannunta haba dear Dan Allah kazo mu wuni tare.
Shuriem da ransa yagama baci, kallan merahh yayi yace” Arayuwata natsani Wanda bazega mutuncin iyayenaba kisani cewa saidata yadda na aureki, datace bataso da bazan aurekiba Dan haka kisani zaman momy kikeyi Agidann kibita kizauna lafiya zagayeta yayi yafice tareda rufo kofar da karfi domin ransa Abace yake.
Sashen momy
yawuce, Yana Isa yasamu momy Afalo kusa da ita yakarasa yagaisheta ta amsa cikin fara’a sannan tace son kanada mata har 2 Amma kafito da wannan safiyar shiru yayi tareda sunkuyar dakai, karadin iya suka jiyo zata shigo falon, momy ce tai saurin ce masa tashi tashi maza kashiga dakina kasan data ganka dagani harkai mun Banu Agunta, da sauri ya Mike yace” toh momy break fast din Akawomin ciki Yana Gama Fada yashige ciki da sauri,. Aikuwa saiga iya sallama tayi momy ta amsa tanai mata maraba, wuri tasamu tazauna tacigaba da fadanta, momyce tace kekuwa iya waya taboki, da sauri iya amshe wakuwa kikasani duk gidannan Baya kaunata Ai rahanatu tamaidani sa’arta yanzu fisabilillahi haryanzu Bata bani Abun Karin safeba, nace kubarni nadingayi dakaina kunki, keda isma’ila kun takura saina huta, momyce tashiga Bata hakuri sannan ta tashi ta nufi kitchen sadiya momy takira tabata na shuriem sannan tahadawa iya nata, sadiyace tazo zata wuce iya, nanfa iya tace dawa Allah yahadani inba keba, inzaki da Abinci Niki Niki, cewar iya, sadiyace ta kalleta tace Banda Abun iya Nene ke bbakyacin irinnamu naturawa kibari dai Akawo miki irrinnaki dakika sabaci nanfa iya ta hau ta inda ta shiga batanan take fita ba itadai sadiya dai Wucewa tayi takaiwa shuriem beak fast dinsa.
Ni kuwa Ina shiga falona wani kukane ya kwacemin batareda na shiryaba nayi kuka har na gaji na share hawayena nagaya Allah yay min maganin meerah.
Shuriem bedawo gidanba Sai bayan Azahar Koda yadawo yataramu A falo yafara magana kamar haka” zangaya muku dokokin gidana duk wacce kesan Zama Dani Acikinku dola ne tabi wadannan dokokin wadda kuwa taga bazata iyaba kofa Abude take……³⁷,³⁸