HIKIMA CHAPTER 5

HIKIMA





CHAPTER 5








“Na hakura! “

Kalmomi biyu ne amma sun girgiza duniya ta gaba daya, ban taba jin kalamai masu daci a rayuwata ba se wannan, sun dake ni, sun kunce min duk wani abu da nake Takama dashi. Da sauri na samu guri na zauna ina jikina ya Fara rawa nace

“Abdallah! Ka hakura? Dani? Da soyayya ta? Ka manta promises dinka? Dama yaudarata zakai”

Hawaye shar ya Fara gangaro min, se yayi Shiru na seconds kafin yace

Bai jira abinda zance ba ya kashe wayar, duk duniya a rabuwa da Abdallah regret dina guda daya ne, da ban cinye masa mutunci ba, da ban nuna masa Wacece real Hikzeey ba, da ban zagi uwarshi da ubanshi ba. Ajiye wayar nayi akan gado na nufi toilet na dauro alwala da yake banyi Sallar ishai ba. Ina fitowa na saka lock a dakin, na Nemo inhaler na aje a gefen praying carpet dina. Sallah na tayar Inata kokarin ganin conversation dinmu da Abdallah bai dawo ba, seda na kai sujjada ta karshe wadda daga ita na idar, a lokacin naji Ya kamata na fadawa Allah damuwa ta, nasan shi kadai zai amsa min, shi kadai yasan halin da nake ciki. Ina furta

“Ya Allah! “

In takaice muku ranar akan dandanyar tiles na kwanta duk sanyin da ake, idanuna suka kekashe banda kuka marar sauti babu abinda nake, abin ya kada ni, it was unexpected, I never expect such daga gareshi.

Wajen Karfe goma na dare, Mama Tazo tana ta buga min saboda ban ci Abinci ba, amma ko kokarin budewa banyi ba, se kuka daya Kara kwace min. Ni daya nasan abinda yake faruwa cikin zuciyata, ni kadai nasan wutar da ake rura min, se naji tamkar son Abdallah aka kara min

Karfe uku na dare bayan nayi sallah bacci me nauyi Yayi gaba Dani, bacci marar dadi da duk yawanci mafarkan Abdallah ne, wai yazo yace min wasa yake min, he never meant his words. Koda asuba kasa tashi nayi se wajen shida na safe nayi sallah nayi wanka sannan na duba mudubi, seda na tsorata saboda ganin yadda idanuna sukai jawur, fuskata ta Dan tashi, gefen idanuna saboda zubar hawaye duk wrinkles Sunyi forming a gurin. Kaina na dafe saboda bansan Wanne bayani zanyiwa Mama ta yarda ba. Sai na tuna weekend ne Zanje islamiyya, haka nayi sauri na saka uniform dina, koda na fito as usual kowa baccinsa yake Shara, haka nayi tafiyata ban nemi Abinci ba.

Da naje islamiyya babu kowa, haka na zauna na zabga tagumi inajin yadda zuciyata take zafi amma hawaye ko diso yaki zubowa. Na jima kafin students suka Fara zuwa akai Shara sannan muka shiga aji. Kowa ya ganni Se ya tambayeni ko lafiya? Hatta Najaatu kasa fada mata nayi, na fada mata nace me? Haka nayi Shiru Abuna, ina bada hadda naje can karshen class na zauna har kowa suka bada tasu. Adduoin cikin hisnul Muslim mukai sannan aka tashi. Tunda muka taho Najaatu ke cemin

“Yau Abdallah bazai zo bane? “Kaina na girgiza mata kawai saboda bakina yayi min nauyi, kuma Haka kurum bana son yawan magana idan ba dole ce ba. Da na koma gida Mama Tana dakinta Dan Haka can na sameta muka gaisa, ta kura min ido tamkar me son gano wani abin, Nidai mikewa nayi kawai na fita zuwa dakina.

Tundaga wannan ranar shikenan muka kulla da zaman daki, Kai ka rantse kace nan aka haifeni, na daina yawan surutu da nake a baya, Abinci baifi sau daya nake ci a Rana ba, duk nabi na rame na lalace. Mama se ta tambayeni Kamar sau biyar a rana meke damu na, amsa daya ce babu komai Se wani lokacin nace kaina yana min ciwo, kuma ba karya nake ba, kullum dashi nake wuni nake kwana, hakan ya Fara tsoratar da Mama , Baffa kam yasan dawar Garin, ya dai zuba min ido ne dukda wasan buya nake mishi saboda bana son mu hadu yace na tura mishi Abdallah, Haka yasa kawai na yankewa kaina shawarar daina zaman parlour, shima baya nema na. Hamma Mussadiq dif shi da matarsa tamkar Anyi ruwa an dauke, ni tashin hankalin da nake ciki bai barni na fahimci Anty Fadila fushi take Dani ba.

A Haka a daddafe nayi sati biu da faruwar abin. Idan kuka kalleni se Kunyi min kuka, saboda Ina cikin mutanen dake saka damuwa a ransu, Ina cikin mutane dake zafafa Abu, basu taking things easy kwatakwata.

Da daddare Kamar kullum ina dakina, Mama ta tafi dakin Baffa yana kwance yana kallon network news dake har Karfe Tara tayi. Zama tayi gefenshi cikeda damuwa tace

“Nikam Kamar Baka san halin da Hikmah take ciki ba a gidannan, ka tattara mu ka watsar. “

Gyara zamanshi Yayi yace

“To me zance muku? Kunyar Idanunta nake Maman Musbahu. Saboda abu take so, banda shi Bazan iya bata ba, inda Inada karfin Ikon aura mata Abdallah wallahi se na aura mata shi, amma Yaron gabaki daya bayada niyyar alkhairi Dan da yana sonta to zai turon Mahaifinshi muyi magana, amma yaki, kuma nayi niyyar idan Mahaifinshi yazo ko shekara hudu ne zan jira amma yaki, Kinsan har office din Babanshi naje, da ya kirashi se cewa Yayi baya sonta….. Ya zanyi? Bansan yazan lallashi Hikma ba”

Ajiyar zuciya me nauyi Mama ta aje, cikin damuwa tace

“To Yanzun ya zanyi kenan? Yazan mata, babu abinda na tsana Kamar ganinta a damuwa.”

Tashi Baffa yayi yace

“Muje na ganta. “

Banyi tunanin kowa zai shigo min daki ba shiyasa banyi jamming ba. Ina zaune saman praying mat din Dana idar da sallah, na fada kaina da gwiwa ta ina kuka, Nima na gaji da halin da nake ciki, inason na koma Normal self dina amma zuciyata taki bani Hadin Kai, kwatakwata na kasa cire wanna Kalmomi biyu da Abdallah ya fada min, na kasa tsayawa na rarrashi kaina.

Ji nayi an turo kofa, da sauri na dago tareda mikewa tsaye ina share hawayen idanuna da Hannayena, it’s too late dan sun rigada sun gani, Gabaki dayansu fuskokinsu babu walwala, babu wani annashuwa se Tashin hankali Mussaman ganina ina kuka.

Mama ta riko hannuna ta zaunar dani Kan sallayar Dana tashi akai, idanuna a warwaje saboda Ko Naki ko Naso yau dole zan fadi matsalata. Ga mamakina babu Wanda ya tambayeni se nasihohi da Baffa ya dinga min akan yadda da kaddara. Hakan nan se naji zuciyata tayi sanyi , na Rungume Mama na kankameta Inata kuka, amma Tundaga wannan ranar
Wani irin Murmushi na farin ciki Maina Ya saki yana zaune office dinshi Ya gama clerking patients na ranar, Sanye yake cikin tuxedo shirt da Armani jeans Wanda suka kayatar dashi, Maina is handsome and charming, badai Yayi shiga Ka kusheba, sake kallon system dinshi yayi yana Kara karanta email din da ya shigo na releasing dinsa da akai zuwa Russia dan Karin Karatu. Kanshi Ya shafa yana adduar bayannar Lulu kafin ya kammalla karatunnan, Dan idan ya gama bata nan to Bashida wani excuse kuma na rashin aure. Yasan dole ne ya auri ko Wacece, don Alhajin sama ya bashi last chance akan idan ya dawo shekaru hudu kenan to ko bai kawo Macen da yake so ba, Alhaji yace aure zai masa.

Duk satin duniya se yayi istikhara na neman Zabin Allah, amma for once bai taba jin jiran da yake yiwa Lulu bata lokaci bane, shidai kawai yana jin wani abu me girma yana jiranshi. To daya zauna bata lokacinshi yaga is more better yaje Yayi Neurosurgery (likitan laka) shekaru uku yake ganin Zaiyi tunda dama yanada exposure sosae kan aikin.

Ammiey na kitchen itada Rukayya da Nafisa suna hada burabiskon shinkafa, Gabaki daya gidan Ya turare da kamshin abincin. Ga wata lafiyayyar taushe da Amna ta hada. Suna kammallawa kowa ya fito Rukayya nata bacin rai Dan duniya babu abinda ta tsana Kamar shiga kitchen bata so bata kuma kaunar hakan, amma ya zatayi tunda Salima ta haife ta, gwara gwara gidan Hafsa idan kaje ita da kanta take girkinta, to Lokuta da dama can take guduwa. Dukkansu parlour suka zauna Nafisa na kara tambayar Ammiey Wasu abubuwan. Tana ta bata amsa Tana jin dadi, kafar ta tasa ta hauri bayan Rukayya ganin yadda take tura baki Tana canja canja channels 

“Aike kam Naga me tsautsayin da zai kwashe ki, yarinya bata son a more ta Se son jiki Kamar kasa. ” 

Dariya Amna da Nafisa sukai hakan ya kular da ita, dake ita ce karama, Alhaji Nafi’u ya bata da yawa, shiyasa ta raina kowa kuma basu shiri da Ammin tasu. 

“Tashi kije Ki cire Naman nan daga oven, ki saka cikin tray ki kawo dining. ” 

Tashi tayi Idanunta har sun kawo ruwa tace 

“To Ammiey amma kina ganin dariyar da suke min ko?” 

“Sunyi din, wuce kiyi abinda na saki” 

Ta fada tana hararar ta, kanta ta gyada ta wuce kitchen din tana tunanin irin sharrin da zatayi musu gurin Abba.  Ta nufi kitchen din se taji sallamar Maina ai da gudunta ta dawo tana ihu 

“Oyoyo Yaya! Oyoyo Yaya!! ” 

Gabaki daya suka mike kowanne farin ciki fal fuskarshi, rungumeshi Nafisa tayi tana ta ihu, kanta ya rankwasa yana cireta daga jikinshi yace

“See this girl, Bakisan kin girma bane? ” 

Turo bakinta tayi tana shafa kanta, se muryar Abba sukaji yana fadin 

“Maina daga zuwanka zaka fara dukar min ‘Yata” 

Sake shagwabe fuska tayi tana diddira kafa ta nufi gurin Abban tana fadin 

“Abba, Tun dazun Yaya Amna take ta duka na.” 

Bude baki Amna tayi cikeda mamakin Iskancin Nafisa, Abba ya dubi Amna yana doka mata harara yace 

“Ke zaki bar gidannan Yanzun nan ta mun rigada mun miki aure. No room for disturbance.” 

Baki Ammiey ta tabe tana fadin 

“Kai ta biyeta dai Tana hada Ku fada da Yayanka.” 

Dauke Kai yayi yana shigowa ciki suna gaisawa da Maina Wanda ke ta dariyar dramar gidannan. Dukkansu tare suka zauna dan cin Abinci se lokacin Ammiey ta tuna da wannan Nama da tace a ciro daga oven, cikin sauri ta Mike ta nufi kitchen din, Tana budewa Har ya Fara konewa, ranta a mugun bace ta fito rikeda tray, sede kafin tayi magana wayarta ta Fara ringing. Aje musu tray din tayi ta tafi gurin wayar. Kamar bazata dauka ba ganin Maman Fainusa ce amma Se ta dauka suka gaisa Kamar yadda suka saba. Sannan Maman Fainusa tace

Story continues below


“Hajiya Salima, ya Maganar mu kuwa? ” 

Dukda Ammiey tasan abinda take nufi, ce mata tayi 

“Wacce magana kenan? ” 

Dan dariya Maman Fainusa tayi tace 

“Zancen Hadin da zaayi na Fainusa da Doctor mana” 

“Na zata Maganar nan ta rigada ta wuce Hajiya Baraka, kinga Maina ba yaro bane balle nace zanyi mishi dole. Shi da kanshi ya fadamin babu wani zance makamancin wannan, just because yayi clerking dinta bashi bane sonta yake ba. Kullum ihunmu maza na Wulakanta mana yayanmu a gidan aure, bafa laifinsu bane duka, Muma akwai namu Laifin. Yanzun ki kalla yadda ake cusawa Maina Fainusa, yarinya me tarbiyya, kyakyawa me aji amma ace bin namiji ake Ya sota! Haba Hajiya” 

Ammiey ta Bata amsa don takaicin halinda muka tsinci kanmu a Yanzun muke, takaicin RAYUWARMU A YAU take, ai ita mace ita Zaa dinga bi ana so bawai ita ta dinga bin namiji ba. 

“Amma Hajiya Salima Karin zumunci ne fa” 

Cikeda mamaki Ammiey tace 

“Dan Allah Hajiya Baraka mu bar Maganar, ko kuma ki nemi shi Mainan kuyi magana dashi in person. Se Anjima ki gaida Fainusal” 

Daga Haka tayi hanging up ranta a bace ta karaso inda suke zazzaune ta zauna Tana musu bayani, dariya Abba yayi yace 

“Dan Hafsa, Yayi kasuwa zan kira Babarka na fada mata” 

Dariya Maina Yayi yace 

“Ai Abba iya wannan ka sani, shiyasa gwara na bar kasar kowa ma Ya huta. ” 

Tabe Baki Salima tayi tace 

“Kasan da ka dawo babu daga kafa ko Baka so dole kayi aure. ” 

Wani ihun murna Nafisa ta saki hakan yasa Salima Kai mata Duka tana fadin 

“Da ban dakeki akan kin kona Naman ba, shi ne zakiyi ihu to remind me of your existence ko? Zaki sani wallahi duk ranar da kika shigo hannuna. ” 

Abba ne yace 

“Haba Tawan babu kara? Ina zaune ana dukar min auta? “

Hararashi tayi tace 

“Ku kuka sani. ” 

Dariya yayi sosae su Amna na tayashi. 

A Daren Maina Ya koma gidansu Wato gidan Aminu. Bayan sati biu dukkan Wasu shirye shirye sun kammalla. Haka aka dunguma aka mishi rakiya airport Ya tashi zuwa Russia, sede muce Allah ubangiji ya bada saa ya kuma ida nufi. 

                                 **** 

Cikin lokaci kankani na Fara dawowa hayyacina, Tun ranar dasu Mama da Baffa sukai min magana naji zuciyata tayi sanyi amma har lokacin akwai burbudin takaici da zafi a ciki. Amma Haka nan kodan na faranta musu rai yasa na daina zaman daki, ina kuma kokarin ganin naci Abinci. A hankali a hankali na Fara fuskantar breakup is not the end of life, Wasu abubuwan a rayuwa suna faruwa ne to make you more stronger. Kwatakwata Abdallah bai cancanci hawaye na ba, bai dace na uzzurawa kaina saboda mutum daya yace baya yi da ni, to da wannan maganganun na samu na dawo normal self dina, dukda Baa Bari a kwashe daidai amma I tried kuma nayi kokari sosae. 

Yammancin lahadi ne, ina daki na gama jera uniform dina da aka kawo daga gurin guga a wardrobe, idanuna suna kan wata katuwar cardboard paper dana manna a jikin bango, ina countdown na graduation, Tundaga 200 days na Fara, Yanzun gashi baifi 50 days ya rage ba, daf muke da kammalla waec mu Fara neco. Wani farin ciki naji a raina tuna cewar Nima na kusa naji yadda akeji, mun kusa hannun riga da wahala don duk tunanina secondary school is the worst of all, bansan gashi irin na oven na ABU yana jirana, Musa Iliyasu aljanna ce. But we all have this mentality idan muna secondary tunani muke it’s the end of life not knowing komai yana gaba. Koda zaayi maka bayani you will never believe that Har se ka zama eye witness ka kuma yi experiencing wutar! 

Shigowar Mama yasa na jiyo fuskata da Murmushi nace 

“Mamata” 

“Zainabu ta!” 

Ta bani amsa Tana kallon gyaran da nayi, kanta ta gyada min tace 

“Hikmah Ko zancensu Fadila Bakiyi, sati wajen biyar zuwa shida Fadila bata zo ba se mijinta kawai” 

Nima cikeda damuwa nace 

“Nima Inata tunanin su Mama, kinga nayi ta kiranta Batai picking ba, nayi mata text amma ko daya batai replying ba” 

Yadda Mama ta kura min ido yasa naji may be tanada insight akan abinda ya faru. Girgiza kanta tayi tace

“Ki shirya kije gidan” _Jakadiyar kainuwa

Tunda na fito naji gaba na yana faduwa dan bansan me zan tarar gidan Hamma Mussadiq ba, Dan tabbas nasan akwai abinda ya faru Babba, idan ba Haka ba ta Yaya Anty Fadila zatayi kwanaki sama da Arbain bata neme ni ba? Ba kuma tazo gidanmu ba. Haka na cigaba da sake sake cikin zuciyata Har Nazo parking space, idanuna cikin na Aneeysa wadda ke tsaye da handbag hannunta, Tasha kwaliyya Kamar aljanna, se naji dariya na neman kubce min, amma nayi saurin maida ta saboda fitowar zaki. Tunda ya kalleni ya hade rai sannan yace 

“Ke zo nan” 

Babu musu naje inda yake, seda ya gama rufe seat dinshi sannan yace 

Kallonta Nayi tana ta wani bubbude hanci Kamar bauna ita a dole me saurayi sannan nace 

“Mama ta aikeni” 

Daga Haka na juya nayi ficewata, a raina Ina ayyana da da Yanzun ba daya bane. Idan da na dauki irin wannan rainin Yanzun Bazan dauka ba, gidan ubanshi ne Kamar yadda yake gidan Ubana. Tunanin hakan se naji Kamar na zake, Kamar abinda na ayyana din ba haka bane. 

Inata tafiya ran nan nawa a mugun hade, nayi kicin kicin a dole kada wani ya ganni Ya nuna interest dinshi a Kaina. A tunanina I want to cheat nature bansan cewa wani hakan da nake shi zai birgeshi a Kaina ba. 

Gefenta na zauna she was absent minded, deep in her thoughts da Har seda na tabata sannan tayi firgigit ta dubeni, muna hada ido ta dauke kanta tana kokarin mikewa. Hannunta na riko, amma Haka ta kwace ta shige dakinta ta kullo kofar. Mikewa nayi nai sororo Kamar doluwa. Meye nufin Anty Fadila? Me nayi mata? Shiru nayi Ina tariyo last encounter dinmu, to kodai ranar Hamma Mussadiq yayi mata wani abin akaina ne? Shiru nayi Inata tunanin possible abinda zai saka Anty Fadila yin fushi Dani, ganin babu ko abu daya dazan iya tunawa yasa kawai na cire veil dina na daura na shiga kitchen seda na toshe hancina saboda yadda yake tashi. Nade hannuna nayi na Fara wanke wanke, ina gamawa na hau share share da mopping, kafin wani lokaci kitchen din yayi tsaf Se na dakko tukunya na daura abincin dare tunda har biyar ta wuce. Ina cikin wanke shinkafa naji an rike Hannayena, dago idona nayi Ko ban kalla ba daga hannayen nasan Anty Fadila ce, kallon fuskarta nayi yadda take murtuk Kamar bata taba dariya ba, janyo ni ta dinga yi har seda muka zo kofar parlon ta sannan tace 

“Fita min a gida, munafuka kawai! ” 

Tirjewa nayi na kwace hannun nawa nace 

“Anty Fadila me yake damunki? Me ya faru? ” 

Hankade ni tayi, Ina iya hango hawaye yana taruwa a idonta, da yadda take battling dasu Dan kada su zuba, tayi nasara as a wannan lokacin ta maidasu, muryarta na rawa tace 

“Tambayata kike? Nace ki fita min a gidannan, munafuka, macuciya kawai” 

Zagin da tayi min ya bige ni saboda babu Wanda ya taba min irinshi, amma banma saka a raina ba, fatana kawai naji Meye matsalar, 

Story continues below


“Anty Fadila kiyi hakuri, duk na dauki sunayen da kika kirani dashi amma Dan Allah ki fadamin inda matsalar take. 

Kawai se ta rungumeni ta saki kuka, hannunta na kama na zaunar da ita kan Cushion sannan na dakko mata tissue box na aje mata gabanta ba tareda na furta komai ba. Ta jima tana kuka sosae Kamar dan shi aka halliceta, seda ta gama kukan me isarta sannan na mike na dakko robar cest Bon me sanyi daga fridge na mika mata, babu musu ta karba ta kwankwada sannan ta dinga jera Ajiyar zuciya. 

“Me Ya faru?” 

Kamar nace Fara kuka ai se ta Kara sakin wani kukan, amma shi bata dauki lokaci ba tayi Shiru sannan tace dani 

“Mussadiq yace aure zaiyi, aure zai Kara! ” 

Idanuna a waje cikeda mamaki nace 

“Aure? kai Anty Fadila, wanne aure ana zaune lafiya? ” 

Hawayenta ta dauke da tissue dake gabanta, ta gyada min Kai in confirmation sannan tace 

“Da gaske yake Hikma, Dama Tun ranar dana aureshi na shiryawa zuwan ranar nan amma ta zomin ba yadda nayi expecting dinta ba. ” 

Cikeda tausayawa da damuwa a muryata nace 

“Kiyi hakuri Anty Fadila, ban hango wani aure da Hammana zai kara ba, Kinsan waye Mama da Baffa Kinsan su Kinsan halinsu, Kinsan bazasu taba Bari ki wulakanta ba. Amma Kamar akwai wani kuskure guda daya da mu mata muke making a rayuwarmu. Allah Ya hallata maza su auri mata daga daya zuwa hudu matsawar zasui adalci, ni bansan aure ba, bansan Meye a ciki ba, kishi halitta ce a wani bangaren Ina daukar kishi tamkar jarrabawa ce daga Allah akanmu, we’re tried with kishi kuma more than 60% na matan duniya Basu cinye wannan jarabawar. In your case, Kalli jikinki Anty Fadila, Kalli dakinki, Kalli kitchen dinki komai upside down. Kina ganin wannan shi zai Hana Yayi abinda yayi niyya? A’a! Se kaimi da courage hade da strength da zai samu. Karki manta the society we’re in, Namiji is always favored more than mace a kasar Hausa, shiyasa zakiga namiji yana neman mata bayan yana da aure amma da kince zaki kashe auren the society will curse you, zasuce it’s too small ki kashe aurenki, idan Kece kazama the society will tell him take another wife, they will never give him a solution to his problem sede kara aure. Anty Fadila kiyi hakuri, idan da ace Inada karfin Iko da babu Macen da zata wahala, kuma Inshaaa Allah ki dauka zancen aurennan ya mutu babu shi. “

Inayin Shiru tace 

“Mama tayi gaskiya da ta saka miki HIKMA lallai kina dashi. ” 

Murmushi nayi jin yadda tayi flattering dina, se na daidaita nace 

“Tohm ni kuma Kin cemin, macuciya, munafuka me nayi? ” 

Gani nayi ta dauke kanta alamar she’s shy, Har na fitarda rai zatayi magana se naji tace 

“Hikma na daukeki tamkar immediate sister Dita, ban taba miki kallon kanwar mijina ba. ” 

Se tayi Shiru hakan yasa nace 

“Uhmmmm ” 

Alamun Ina jinta, tace 

“Ashe ba haka kika daukeni ba, Ashe har zaki iya jin zaki auri Mussadiq, mui kishi dake? ” 

Kawai kallon tababbiya na Fara mata, lallai Anty Fadila is insane, if not ta manta tsakanina da Hamma Mussadiq ne? Cikin wani irin takaici da wani abu da ya tsaya min a makogaro na Mike na ware veil din Dana daura nayi hanyar fita, da hanzari tabi bayana wannan Karon itake Hana ni fita, zuciyata Kamar zata fashe Haka nake ji, kawai se na Fara kuka ina fadin 

“Anty Fadila! Kallon da kike min kenan? Munafuka ko mazinata? A Ina kika taba ganin Yaya da kanwa Uwa daya uba daya Sunyi aure? A Ina? Muna musulmai?…… ” 

Hannuna ta riko a ranta tana fadin Hikma you’re too innocent, an rufeki da yawa! 

“Allah koda ace ni din yar riko ce Bazan iya kallon Hamma Mussadiq a saurayi ba balle har na aureshi, Baki kyauta min ba, ba kiyi tunani yadda ya dace ba. ” 

Rungumeni tayi tana jin relief a ranta Dan tasan I’m my own boss, Inada kafiya da naci, kuma hardly nayi magana biyu. Sakinta nayi na juya nayi ficewata daga gidan. Ina zuwa kofar gida naga Hamma Mussadiq yana kulle Mota, jin sheshekar kuka yasa ya juyo, yana ganina ya taho yana fadin 

“Hikmah keda wa? ” 

Wata harara na wurga mishi sannan na wuce, gaba daya haushin shi nakeji dan Bashida hankali. Yana ganin Haka ya wuce gida ya samu Anty Fadila inda na barta 

“Uban me kika yiwa Hikma ta fita tana kuka? ” 

Ko uffan batace masa ba, tayi shigewarta parlour, hakan ya tunzura shi, Ya bita yana fadin 

“ko me kika ce mata, se na aure ta sede ki mutu! Ko ki bar gidan” 

Dagowa tayi tace 

“Inason in fada maka, kada kayi dragging Hikma cikin abinmu, she has nothing to do with this, she’s completely innocent sede idan ka shirya fada mata Baffa da Mama tsintar ta sukai” 

Wani mugun kallo Yayi mata tareda fadin

Ko ta kanshi bata bi ba, dukda ranta yay mugun bacin abinda ya fada, ita ce ladan noma kenan? Kanta ta girgiza ta wuce toilet dan yin alwala don Tun fita ta aka Fara kiran Sallar Maghrib. 

Koda na isa gida, seda na tsaya nayi alwala a tap din tsakar gida sannan na shiga ciki, ina shiga mukai karo da Aneeysa taci jeans trouser da wata top kanta babu dankwali, kallonta Nayi na watsar a raina inajin haushin abinda ake a familynmu, shiyasa koda wasa auren zumuncinsu baya birgeni Ko sau daya, Kai wani lokacin ji nake am not part of them, Kamar idan aka hadu Duka, se Inaji na Kamar bare na rasa wannan feeling din. Ko kuma yadda kowa ke son culture dinshi amma ni Fulani da culture dinsu bai taba birgeni ba se wani soyayya da nakewa barebari, Ko ganin kanuri nayi se Inji Kamar dan Uwa nane. Nasha fada gurin Mama akan rashin yin fulatanci, se da kyar ta samu nakeyi. Na tsani yadda idan zaka auri Dansu to se kaje gidansu ka zauna Kamar yadda akaiwa Anty Fadila, ga Aneeysa nan ma an kawo ta, tunda bikinsu nan da 4 months, shi Hamma Mustapha bare zai aura ya rufawa Kansa asiri. Ni kuwa bama a zance na, Baffa ya kirani akan Ko Inada wani aikin hada da bikinsu nace babu, yayi min tayin Wasu cousins dinmu daya Sunanshi Aiman a England suke da iyayenshi, mamanshi ce kanwar Baffa, tunda Tazo ta ganni a bikin Hamma Mussadiq ta like min, bata sati bata kirani ba, amma danta is too spoiled Bazan iya da Yaran mummy ba. Se Suhail shikam Dan yayar Mama ne, bamu shiri da mamanshi duk haduwan da Zamui da ita se tana min kallon banza, bana bukatar wannan surukar, na karshen Abba ne Dan gayu Kamar Mace, ga iyayi koda yaushe shi ya iya, Mr perfect ake ce mishi da Baffa yasan yadda nake jin haushin shi bana tunanin zai yimin tayin aureshi. 

Ko Kunyar Baffa Banji ba saboda kullum ina gayawa kaina, matsalar aure is a life time problem, think wisely kafin ka zaba, gwara gwara ma Aiman saboda mamanshi amma Sauran a kaisu bola. Na cewa Baffa bana son daya daga cikinsu, a take kuwa aka cike min jamb form online, na cika ABU Zaria, physiology matsayin course din da nake so. 
Washegari Misalin Karfe takwas na safe, Inata sauri na tafi school saboda Munada early food and nutrition essay exams, kuma ita ce last paper da zamuyi. Da kyar nasha tea saboda nasan daf nake da makara. Ina fitowa parlour, I was super shocked ganin Anty Fadila a zaune, baki a hangame na nufeta Har na manta abinda ya faru the other day. Rungumeta nayi Ina fadin 

“Wannan buga sammako Haka?” 

Murmushi tayi ta dungure min kai tace 

“jiya baki fada min jibi saukar ku ba, Nazo taya Mama aiki” 

Gosh! Na dafe Kaina ni Kaina ina tunanin na manta da saukar gaba daya, gaba daya Daren jiya a wasiwasi Ya kare min, Haka kurum nake jin puzzles din dake gabana akwai Wanda is not placed right. Ni nasan mu musulmai ne, Fulani dake zama a kasar Hausa masu riko da aladarsu. I thought for many times it can’t be coincidence Hamma Mussadiq yace zai aureni sede idan daya daga cikin mu biyun ba Baffa da Mama suka haifemu ba

“Hikma zaki makara fa, wannan deep tunanin is not good” 

Wannan ya dawo Dani hayyacina, kaina na gyada ko Mama ban nema ba na fice Kamar zan tashi sama. Ina zuwa Bus zata tafi, hamdala nayi nabi bus din, ko a ciki banga daya daga cikin yan class Dinmu ba, hakan yasa na samu guri na zauna nayi Shiru Inata tunanin rayuwata, idan har zuciyata ta raya min daya daga cikin ni Ko Hamma Mussadiq ba su Baffa suka haifemu ba, to ni ce ba yarsu ba. Saboda duk wani abu na jini Hamma Mussadiq ya dakko amma ni banida wani abu da zai nuna cewar su iyayena. Gabaki daya se naji hankalina yayi matukar tashi, idanuna na runtse wani Bari na zuciyata yana gasgata baa gidanmu nake ba yayinda wani barin ke kalubalantar hakan. 

Ranar exams nayi ta ne kawai, bawai Dan nasan me na rubuta ba, idanuna kadai sun isa su nuna ample of Tashin hankalin da nake ciki. Muna fitowa na nufi gate saboda bana son mu hadu da kowa, Allah Allah nake na fita amma my wish wasn’t granted, nayi bumping Najaatu. Dagowa nayi da niyyar bada hakuri Se Naga Najaatu ce, dariya tayi tace 

“Nemanki nake tayi” 

Tsayuwata na gyara, Ina daidaita nutsuwata nace 

“Ya exams? ” 

“Kin manta Tun jiya nayi tawa, ke zan tambaya wannan ai” 

Murmushi nayi nace 

“Not bad at all” 

Nodding kanta tayi tace tana Jan hannuna 

“Aure Zanyi Hikma” 

Da mamaki na kalleta dukda ba abin mamaki bane tunda Tun muna jss3 take zancen aure, zama mukai kan Wasu gossip chairs nace 

“Zakiyi ko zaayi miki? ” 

Hannunta ta watsar a iska Tana dariya tace 

“All the same Kawata. Bayan Neco da sati biu” 

Idanuna na bude sosae har seda ta kauda kanta, saboda tana yawan cemin bata kaunar nayi mata full light da idanuna, Tsoro suke bata. Dariya nayi nace 

“Sorry Aminiya, Kinsan week daya da nasu Hamma Mus’ab da Hamma mustapha? ” 

“Ba zakizo ba kenan? ” 

Bakina na rufe ina Dan dariya nace 

“ko event daya ne zan leko” 

Rungumeni tayi tace 

“Kinga mijin, bafullatani kyakyawa? ” 

Dariya nayi nace 

“Haka kika iya, gwada maza. Bari kiga na tafi gida, se next month” 

Daga Haka mukai sallama, naji dadi Dan at least damuwar da nake ciki ta ragu sosae. 

A hankali rayuwa ta cigaba da tafiya, wata Rana zuma, wata Rana madaci. Anyi bikin saukar quranin mu. Anyi shagali sosae. Yan Uwa sun mini kara Kamar Wanda ake biki. Sati biyu daga wannan lokacin muka fara NECO, tareda Aneeysa akai mana registration muke zuwa tare. Bahaushe yace albarkacin kaza, kadangare kan sha ruwan kasko. Kullum Hamma Mus’ab kaimu yake ya dakko mu. Babu fashi kowanne aiki ko yakeyi se ya barshi yazo Ya dauke mu. Babu ruwana da sabgar su, abinda ya dameni shi ne a gabana. Kullum se nayi tunanin su waye suka haifeni, su waye iyayena. Dukda babu alamar nuna akwai yiwuwar su din basu suka haifeni ba amma Haka kurum nake jin akwai breakage along the way. Ban taba budar baki na tambayi wani ko na fadawa wani ba Har Anty Fadila saboda kunya nakeji nauyin hakan nakeji, Ina ganin banyi musu adalci ba. 

Ranar alhamis, muna zaune ni da Aneeysa wadda muka fara shiri da ita kwana biyu saboda yadda kullum muke tare, kuma taga bana shiga sabgarta se ta yadda makaman yakinta ta rungumeni. Muna zaune muna solving wani quadratic equation, Mama na serving Baffa Se su Hamma suna danne dannea wayoyinsu. Muna gamawa Aneeysa ta janyo wani bowl Wanda muka zuba popcorn da caramel topping, Munyi akan inhar muka samu answer da steps din daidai zamu ci, idan ba Haka ba kuwa to sede muyi kyautar shi. Hannu ta bani muka tafa sannan muka fara munching dinshi, kowa yana lumshe ido Dan dadi. Idanuna na mayar kan network news din da Baffa yake zaune yana kalla. 

Wani mutumi ne a tsaye akan podium, flash yanata haska fuskarshi ga dandazon Yan Jarida sun kawaye shi. Gaba daya na tattara hankalina na mayar kan wani rantsatsan speech dake fita daga bakin mutuminnan, Ya manyanta a kalla zai tasarwa 50 years, idan bai kai ba to kadan ya rage babu, shima saboda yadda na kura masa idanu yasa na fahimci hakan, amma lokaci daya bazaka fadi hakan ba. Dogo ne yanada tsayi, fari tas dashi, kana kallonshi kaga dan gayu Wanda by all means yakeson batar da shekarunsa. Yana sanye da Wani lafiyyayan grey suit, idanunshi cikin farin garegaren medical glasses. Daga yadda yake magana zaka dinga jiyo yadda yake fitarda sautin kowanne word, American accent Yayi aiki Dan Ya fito radau, kana jin maganarshi Kasan America ta Gina Dan Nigeria.

Juyowa nayi na Kalli Baffa dake kurbar tea nace 

“Baffa waye wannan? ” 

I was super curious nasan waye wannan, waye shi. Sau daya na kalleshi amma naji wani abu me girma a tare dashi, ban taba jin wannan yanayin ba, not even on Mama or Baffa. Love at first sight, ba so na soyayya ba irin Wanda nayiwa Abdallah ba, No is just a different feeling da nake dashi da ban taba jin irinshi ba akan kowa, so Wanda yake natural, within a minute Ya gama circulating dukkan sassan jikina. 

Baffa ya dubeni yaga yadda na tsura ma mutumin ido yace min 

“Last week aka mishi appointment na CBN governor. Mutumin yanada kirki anata yabon shi, da alama Zaiyi aiki. ” 

kaina na gyada mace 

“Baffa Ina son na ganshi” 

Duka aka kwashe min da dariya, suna ganin wauta ce kawai, amma bazasu gane me nakeji akan Mutumin ba. 

“Ai Uwata, meeting such people is very hard, da kina tweeter Se kiyi following account dinshi.” 

Da sauri Kamar ina jira naje na dakko wayata aka bude min tweeter account mukai searching  *ABMaina* Ranar Har sha daya ina bincike a profile dinshi. Yawancin trips din da yayi ne ,guraren da yayi Karatu, se official aikin da suke akan gyara CBN da other banks. 

Washegari muka fara hada Lefe, kullum se Munje kasuwa, ranar muka dawo a mugun gajiye ana a week to bikin na cewa Mama Bazan kara raka ta ba, ni gajiya nake, kullum na dawo da kyar nake iya tashi Washegari, saboda azaba. 

A gaba dayan rayuwarmu mukan dauka the only heart break da muke samu shi ne akan soyayya. A cikin rayuwa ta na fahimci, ba haka bane. Akwai abinda yafi wannan bacin rai. 

Cikin nasara muka kammalla NECO na zama graduate Kamar yadda nake mafarki kullum. Sede wani hanzari ba gudu ba. Ashe ko JAMB ban ci ba, balle naje ABU dana kwallafa rai a kai, Babu Wanda ya sanar dani, don tuni sun sake result din amma Baa fada min ba. Se ranar da muka gama school sannan Baffa ya fada min. Nasha kuka Kamar raina zai fita. Ina ganin tamkar an nesanta ni ne da wani abu da zai faru dani a rayuwata. 

A Haka a wannan halin aka Fara bikin su Hamma. Dukda bawai ina wani jin dadi bane sosae a lokacin amma na ji dadin bikin, ko bikinsu Anty Fadila albarka. Tamkar wannan ne karo na farko da Mama zata aurar da Ya’ya, mutane sosae. Ranar asabar aka daura musu aure su hudu. Tunda aka daura auren dake da yamma ne kowa ya Fara shirin dinner, amma abinka da mata bamu muka gama shiri ba se bayan Sallar ishai. Lokacin Aneeysa ta shigo Dan kira na, Tayi kyau na karshe. Wani material Baki da adon golden akai mata gown dashi. Tayi kyau na karshe abinka da farar mace, gani nayi tayi turus tana wurga min harara, dauke kaina nayi Ina kokarin daura igiyar Takalmi na, Wanda yake flat sandals ne silver. Dan dukkan takalmana flat ne saboda yanayin halittar kafar, ganin nayi mata banza yasa ta matso ta zauna gefena tace 

“Haba Hikmah, saboda abinda Hamma Mus’ab yayi miki jiya, shi ne baza kije dinner ba? ” 

Kaina na dago lokacinda na gama fixing Takalmin kafata, kafadar ta na dafa, fuskata dauke da Murmushi nace 

“Kinyi kyau, Hamma Mus’ab yayi saa! ” 

Turen hannuna tayi tace 

“Wai me yasa kike Haka ne Hikmah? Yanzun wa kikeso yaje miki” 

“Ni nace Bazan Je ba? I didnt” 

“To gashi Kinsa, wani kayan daban” 

Lumshe idona nayi nace 

“Aneey, Kinsan Najaatu yau dinner dinta, banyi attending kowanne event ba. Babu dadi kinga” 

Batace min komai ba ta fice, ranta a mugun bace. Kaina na rausayar kawai na Mike na fito. Nazo parlor Naga an zagaye ta ana tambayarta abinda yasa take kuka. Ni dariya ma ta bani da mamaki, can dakin Mama na taddo ta nace 

“Mama zan tafi” 

Kafin ta bani amsa Sega Maman Aiman ta shigo, Tana ganina tace 

“Me yasa bazakije dinner Aneeysa ba, gata can se kuka take. Na zata jiya kin hakura akan abinda Mus’ab yayi miki, kuma dama sako da sako ai ya gaji Haka. ” 

Dan Murmushi nayi nace mata 

“Allah Mummy wannan ya wuce, best friend Dita akewa biki Zanje, lekawa zanyi na koma na Aneeysa din” 

Kanta ta gyada tace 

“OK, bata fahimta bane, yi maza kije na Kira Aiman Ya kaiki, se ya jira ki gama sannan ku koma can din. ” 

Kaina na gyada, na fahimci takun Mummy dole de takeson salkafa min danta. Tunda suka zo daga London, dukkan wani motsina a idonta, Dan Ko fadan da mukai da hamma Mus’ab, bayan ta fattatake shi seda tayi min fada, me yasa na kula abokinshi, bayan ga manyan Yara masu sona, me zanyi da wannan kazaman abokan Mus’ab. Ni dai Bance komai ba Dan na fahimci danta take yiwa campaign ba kowa ba. 

Tare muka fita da Aiman, shi Bashida surutu, if I guess right babanshi ya biyo, Dan Mummy tana iya magana ita daya saboda azabar surutu. Unlike Aiman tunda muka gaisa bai Kara cemin komai ba, seda mukai tafiya sosae sannan yace min 

“Naji Ance you didn’t make your JAMB” 

Kaina na gyada mishi Bance komai ba, shima Se yayi Shiru kafin tamkar an tsikare shi yace 

Story continues below


“Inason Mummy, Mummy na sonki. I’m sure Kinsan tana son hada mu aure ni dake, dukda tace Kamar akwai abinda ke damunki. Kuma nima na fahimci hakan, Kamar Kinada bad past experience akan soyayya. ” 

Shiru yayi ya dan kalleni sannan ya maida kanshi kan titin ,yana anticipating yaji nace wani abun. Nikam mamakinshi nake, Kodan babu abin mamaki babu he’s a psychologist, abinda yayi degree da masters akai kenan. No wonder yake karanatar every mood na mutum. 

“I see all of you men as betrayers” 

Na fada a hankali, amma ga mamakina se ji nayi yace

“Why?” 

Kallonshi nayi Dan I never thought zaiji, dauke kaina nayi daidai shigowar mu gurin, amma maimakon mu fita se ya saka lock a kofar, da sauri na kalleshi muka hada ido saboda shima kallona yake, dauke kaina nayi nace 

“please! ” 

Murmushi yayi me sauti yace 

“Naga Yanzun couples din zasu shiga, mu jira ayi clearing gurin” 

Kaina na gyada kawai, can gurin Ya sarara hakan yasa muka fito dan shiga gurin. Muna shiga na samu guri can karshe muka zauna, but somethings caught my eyes, abubuwa biyu, na farko ankon dinner Najaatu ne a jikina amma Se naga nan ma ga Yanmata sanye dashi. Na biyu gefen Hamma Mustapha Kawata nake hangowa Najaatu, kallon Aiman nayi nace 

“Hamma Aiman, Ya sunan matar Hamma Musbahu? ” 

Kanshi Ya Dan dafe yana son tunawa, dake age mate suke yace 

“Najaatu….. Hashim” 

Idanuna na dan zaro sannan nace 

“Ita ce wadda nake fada maka ai.” 

Kanshi Ya gyada da Murmushi yace 

“An hutar dani” 

Tare mukaje can inda suke muka gaggaisa, dukkanmu Munyi mamakin Ashe Najaatu ce amaryar Hamma. Aneeysa ta janyo ni mukai hoto, na sakko zan tafi Hamma Mus’ab ya saka min kafarshi, God! Banda ace Aiman na gurin Ina tunanin karyewa zanyi, da sauri ya taroni yana jeramin Sannu. Cikeda mamaki na dubi Hamma Mus’ab ko a jikinshi, Murmushi ne fal fuskarshi saboda gwada Aneeysa da MC din yakeyi. Hannuna na zare daga na Aiman na wuce seat dinmu na karba bag dita nayi waje, Ina zuwa daidai motar Aiman Ya iso shima. Lokacin tuni na Fara kuka saboda I was embarrassed, Dan MC har cewa Yayi nayi a hankali, me nayiwa Mus’ab Haka da zafi? Bantaba jin dakinshi koda na single second ba. Tsakanina dashi se kyara da cin zali, I don’t know why. 

Motar Aiman Ya buden ,cikin murya cikeda lallashi yace 

“It’s okay, shiga mu tafi” 

Babu musu na shige, shima ya juya ya zagaya Ya tada motar. A hankali muke tafiya, Har ya samu gefen hanya Ya gangara yayi parking, dagowa nayi da idanuna da fuskata da suke sharkaf da hawaye, kuka nake sosae saboda da nace babu wani abu da Mus’ab zaimin na kara kuka, amma Yanzun abin yafi karfin haka. Na rasa me nayi mishi da zafi, me na tare mishi. Bashida burin da ya wuce ya kuntata min. Aiman kam baice Dani komai ba Illa tissue box da ya dakko daga Kan dash board ya ciro ya mikon. Babu musu na amsa, sede a jikin tissue din tamkar ana Kara tunzura ni ne, na dinga kuka Kamar danshi nake, Ko kadan bai gaji da miko min ba. Sede ganin Naki na daina kuka yasa yace 

“Hikma ki daina kuka Haka. Mutane irin Mus’ab doesn’t deserve your tears Ko kadan. Shi ya bata miki rai, shi yana can gefen matarshi yana enjoying every minute of it. Nayi tunanin Tun jiya mukai Maganar babu abinda Mus’ab zai miki Ki dubeshi, see the way you’re crying like a baby  

Cikin kuka nace 

Kai ya dafe, yasa dayan hannun ya dafa steering wheel, yana kallona. Na jima ina kuka ba na wasa ba saboda wani kunci nakeji a raina. Sosae Ya dinga bani baki har na daina kuka, Inada wani abu wuyarta a lallasheni shikenan. 

Kaina na gyada cikeda jin dadin maganganunshi nace, Ba tareda na fahimci zahirin abinda yake nufi ba, duk tunanina Ya koma kan Karatu ne

“Inshaaa Allah” 
Daga haka ya fara driving saida ya rakani har daki sannan ya juya ya tafi washe gari anata haramar tafiya  ya kirani akan nazo yana kofar gida yana jirana

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *