HOD’IJAM CHAPTER 7 KARSHE BY NOORIEEYAH
Www.bankinhausanovels.com.ng
Na cigaba da wanzar da rayuwata cikin birnin america ba tare da sanin me duniyata ke ciki ba,sai dai akwai wasu sabbin qarin canji da na riqa fuskanta daga Yaa Mukhtar,watoh daga sa’ilin da muka baro asibiti on that faithful day,ban sake numfashin sa’a guda ba tare da sanin Yaa Mukhtar din ba,ya fara bibiyar duk wani motsina tamkar wanda akai wa cune na,asubar farko kiranshi ke tadani,wayewar gari kuwa kafin ya wuce makaranta a gidanmu zaiyi branching,haka idan yataso,sannan in ba ai sa’a ba kafin lokacin baccin shi yayi ma zan sake ganin shi,and a kullum tambayar d’aya ce.
“Hayatiey Yaya kike jin jikin ki?kina ganin akwai wani sauyi a tattare da ke?bakya jin wani sauyi a tattare dake?ko kinajin zazzabi da wani abu makamancin hakan?”
Tun ina amsawa da tarin mamaki shimfide a fuskata har yazamana na saba da hakan,na saba da sabon sauyin kulawa da nake samu daga gareshi,na kuma dauki al’amarin na aje shi guri mai dan girma cikin zuciyata,tare kuma da goge duk wani shakku da nake ji game da Yaa Mukhtar din,ko banza inajin wannan kulawar tashi abin nagode kuma na yaba mashi ne.
Ban sare da al’amarin shi ba sai kusan bayan wata d’aya da kamar sati biyu da zuwanmu asibitin ba,yakirani a daren ranar talata misalin qarfe takwas da rabi na dare.+
“Ina wuni Yaaa Mukhy.”
Na hanzarta jifanshi da gaisuwata,duk a qoqarin daqile tambayoyin da sukai matuqar gajiyar dani wajen amsa su,sai dai still ba wai na tsira ba ne,
“How is Ni’imatuu feeling today?kinajin wani sauyi a tattare dake?”
A sannan na sake tuno ciwon kan da ke hanani sukuni tun kwanaki shidda da suka shude,sai dai naqi sanar dashi ne gudun abinda ka iya zuwa yaje yadawo,mussaman ta bangarenshi da har yanzu nagaza comprehending dalilin da yasa yake bani wannan er banzar kulawar.
“No i am perfectly fine,kana ganin hakan ke nuni da samun sauqi na gaba d’aya?”
“No i don’t think,dama i wanted to tell you gobe ki shirya zamu koma muga Doctor Ben,to make sure babu sauran wani abu dake damunki.”
Ya bani amsa muryar shi dauke da er damuwar da nakasa tantance me ke kawota mussman in na fada mashi qalau nake.
Ban musa mashi ba,coz nima dai din inason ganin Likitan deep inside me,saboda ciwon kan dake yawaan damuna,duk da cewa mild one ne,amma rashin barina yasa nake tunanin ko akwai abinda ya janyo mani shi,sannan kuma dama inaso in tabbatar da cewa babu sauran infection din a tare dani,duk da cewar banfasa jin mild contraction ba lokaci zuwa lokaci,sai dai bai zama worst din da har zan kai ga fada ma wani yanda nake ji din ba.
Bayan gama wayar na miqe domin isa kitchen din gidan,nikaina ina mamakin yanda yanzu ba abunda ke burgenj kuma yai man dadi irin in sha ruwa mai shegen sanyi hade da lemun tsami a ciki,zama nake sosai in kwankwade shi kamar Allah ya aiko ni,yanzun ma direct cikin fridge na nufa for the reserved one da na aje awanni biyu da suka shude,har wata nutsuwa nnakeji tana saukar man in ina sham ruwan,hakan yasa guri nake samu insha iya shana,kana inyi topping da duk wani yoghurt din da yazo gabana,dama can ni din ma’abociyar son yoghurt ce.
Ina shirin barin Kitchen dinne Mommy ta shigo,tana dan dariya tace,
“Wannan shan ruwa da kike Niiimah na hankali ne?bakya tsoron ya riqa qulle maki ciki?anya Niimah ba zaki sarara wa shan ruuwan sanyin nan ba haka?”
Kamar kullum amsa guda ce nake baiwa duk wanda ya lura da maitar son da nake wa ruwa aa gidan yanzu.
“Allah Mommy nikaina bansan yaushe nafara qaunar ruwa haka ba,ruwa mai tsamj to be precise,kamar naci ance its a strong anti biotic.”
STORY CONTINUES BELOW
Dariya tayi Mummyn kana ta hada da ce man,kwarai kam anti biotic ne tunda da lemun tsami a ciki.
Dariya mukayi gaba daya na wuceta na nufi dakin Aunty Madina d ayanzu cikinta ke tasar ma wata uku da sattittika,zuwa yanzu kam abun boye yafito fili,domin da laulayi yataso ta gaba dole ta boye boye ta qare aka fahimci dawan garin,sai dai fadan da mukai expecting daga Mummyn sam bamu ganshi ba,hasalima kamar tafi kowa murna da samuwar cikin,shikenan fa aka shiga ririta kamar kwai.
***
Qarfe bakwai da kwata a gaban gidan Dr Grema taiwa Yaa Mukhtar,ni dinma sanin uzzura man da zeyi yasanyani shiryawa da wuri,duk da wani irin fatigue da nakejin na bibiyata yau tunda na bude ido,amma na dauki hakan a matsayin rashin baccin wurin da banyi ba muna can mun raba dare ni da Aunty Madina muna chapter.
“How are you feeling today?”
Ohhhh ikon Allah,bawan Allahn nan ya sarara mani haka mana,ai yabari ko gaisawa ne muyi kafin ya miqo mani wadannan tambayoyin da sun kai qololuwar fara bani haushi da takaici.
“Ba sosai ba,mild ciwon kai ke yawan damuna cikin en kwanakin nan,ga kuma kasala da nikaina ban san ina da ita ba.”
Kawai naga yakamata in fada mashi,qila inyaji hakan zai sarara man,naga alamun so yake yaji nace wani abu na damuna yaji dadi,toh inba haka ba ne menene wannan kafirin naci?sai dai mene?a take yanke na fara nadamar sanar dashi,domin jikin shi na rawa ya miqo dogon hannun shi saman goshina.
“Are you serious?yaya kike jin ciwon kan?kina amai ne ko kuwa?”
If im not mistaken,kuma inba kunnuwa na bane ke fada mani qarya,kamar na tsinto amusement cikin sautin shi,hakan yasani dan yin jim mussamman saukar hannun shi bisa goshina,ba zan iya tuna ranar da abu makamancin haka yafaru tsakaninmu ba nan kusa.
“Amai kuma?”
Nima na tambayeshi,toh me ya kawo na inyi amai daga ciwon kai?banajin na tuna inda nace mashi zazzabin malaria ko typhoid na damuna,a lokacin naga ya dan sassauta dokin da nake hangowa shimfide a kan fuskar shi.
“Ermmm,well i thought ko harda amai ne,forgive my misunderstandings.”
Nikam ban kuma cewa komi ba na kame bakina nai shiru,mussaman dai da naha ya zame hannun shi dake bisa goshinawannan ikon Allah dai da yawa yake,muna gab da isa asibitin ne na hango wani mint chewing gum,banma san na dauka na bare ba sai bayan da na jefa bakina na hau taunawa sannan na lura da kallon da yake man.
“Sorry for my attitude, naji kawai inason ci ne.”
Yana mani wani irin kallo yace,
“In mun fito zamu biya insiya maki carton carton, remind me please.”
Nidai naa bishi da toh,tunda hhar qasan raina naji inason kullum in riqa taunar cingam din.
Daalama Doctor Ben din yasan da zuwanmu,tambayoyine masu qarancin yawa ya riqa yi mani,daga nan kuma ya aikani lab aka dauki blood sample dina,waiting room mukadawo domin jiran likitan,after some few minutes da basu gaza ashirin ba ya kira nemi ganin Yaa Mukhtar din shi kadai,tun daga time din da Yaa Mukhtar din ya baro office din na Dr Ben na fahimci wasu al’amura masu tarin girma a cikin idanuwan shi,al’amarin da har yau nakasa yarje wa kaina ribar shi akan yin hakan.
Munbar asibitin bayan likita ya tabbatar mani da dacewar da akayi a aikin da akai mani a satittikan baya da suka wuce,yaqara da fada mani ciwon kan danake dan yi da kuma kasala da nake yawan ji a jikina suna faruwa ne saboda sabbin changes da jikina ke undergoing, yaqara da fadin komi zai koma normal nan ba da jimawa ba,dadin dadawa harda hadoni da wasu magunguna da ban damu da sanin wadanne iri bane,na daiga folic acid da paracetamol, sune kadai na iya ganewa a ciki.
STORY CONTINUES BELOW
“Now you are perfectly fine,do you think you need something?”
Kalmar da yafara jifana da ita kenan bayan mun dauki hanyar barin asibitin,hakam yasa na girgiza mashi kaina alamun ban buqatar komi,a lokacin kuma na tuna da in sanar dashi qila nan da sati biyu zan iya barin qasar,domin gaf nnake da kammala abinda yakawoni sai abubbuwan da baa rasa ba,wanda qila cikin kwanaki qalilan zan gama da su hopefully.
“Kasan nakusa komawa gida like ive told you kwanakin baya,inaso dai naje nayo wa su mammy tsaraba in babu damuwa.”
Fuskar shi ce ta canza kamar yanda tayi kwanakin baya din dana sanar dashi same maganar,bankawo komi a raina ba,nafi tunanin kila wani abune ke damun shi.
“Wane actuall time ne kika da tabbacin zaki tafi?i want to know!”
“Anything zuwa nan da sati biyu,i just need to go and do the bookings ne and rest,and Ibrahim brothern Mummyn Dr Grema yace zai kaini.”
Wata iriyar dariya yayi da bansan dalilin yin ta ba,coz a tunanina babu wani abun dariya da ya faru bare har takaishi ga yin ta.
“Babu inda zaki je har sai na baki wannan umarnin.”
“Ahhh”
Bansan lokacin da Ahhh din yafito daga bakina ba,it’s been ages since Yaa Mukhtar din yai mani magana in such a bossy way,in ban manta ba tun rasuwar iyayena,but why the sudden change now,amma duk da haka banyi qasa a guiwa ba na nemi jin dalili duk kuwa nasan bashi ma da dalilin,besides wannan abun ma dai naga abinda ya shageni ne ba shi ba,then why the attitudes?
Bai kalleni ba iillah tuqinshi da ya cigaba da yi a hankali,daalama bani da amsa,nima ganin haka sai na ja bakina na tsuke,tafiya ce dai ba fashi in Allah ya yarda nan da sati biyu zanbar qasar nan.
Kafin ya ajeni gida sai da yabiya dani wani mall ya jibgo mani kayan zaqi da su chewing g din da mukai magana dazu,dama dai abun na raina,ganin a yanayin da muke ciki yasa ban nemi da in tuna mashi ba,ashema yana sane,tabe bakina nayi lokacin da muka iso gidan Dr Grema.
Gama parking din shi yayi daidai da kai hannuna zan balle handle din motar in fice,sai dai kalamen da ya jefeni dasu sun sanya ni dakatawa,haka kuma na jiyo fuskata shimfide da bayyanannen mamaki.
“Get ready nan da sati daya zaki dawo gidana da zama.”
Kallon kanka qalau na riqa binshi dashi,tare da kallon me kake nufi da hakan a lokaci guda.
“Bangane ba.”
Na furta a hankali.
“I do hope kigane kafin lokacin dana dibar maki,inma baki gane din ba dai still its my duty to clear your head,but kafin nan adhere to what i said earlier.”
“Toh a kan wani dalili Yaa Mukhtar?misali ma let’s assume i will not be leaving this soon,what on earth ne kuma zai maidani zama gidanka?i mean does that even makes sense?”
Bandamu da yanda yanayin shi yakoma ba,domin kallo guda nai masa ya juye mani baqin mugun Mukhtar din dana sani shekarun baya ba,he looks dangerous, but i don’t care,wannan ma ai hauka ne.
“Fice man daga mota kafin in maki abinda zai bata mana rai mu duka.”
Ba musu na sanya hannuna na balle motar nai ficewata,har a lokacin kuma nakasa tantance dalilin duk wadannan surutan.
“Ubanwaye zai biyoki da kayan da kika bari?”
Najiyo muryar shi a bayana,hakan yasa na waigo da sauri domin tabbatar da shi dinne har ya biyoni,harara na balla mashi kana na juya a fusace bayan na jefeshi da kaalmar “ba’aso,ka cinye tsiyarka.”
Nidai da gudu na idasa shigewa gidan kafin ya kassara ni,don alamu sun nuna gab yake da ya sanya mani hannu,ganin yanda yake ta huci kamar naci ban biya ba.
STORY CONTINUES BELOW
Shigata gidan da bai gaza minti biyu ba naji kiran wayar shi,da kamar ba zan d’aga ba amma na canza shhawara,a tunanina qila shima yaga rashin dacewar abinda ya fada dinne ya sanya shi kirana,sai dai sake dab’awa akai,abinda yace din ya sake kada mani en hanji.
“Wallahi wallahi karki bari in sake kama ki kina irin wannan gudun,kina da hankali kuwa?ko so kike ki jazaman bala’i?”
Bai nemi jin amsata ba yaciga da zuba man kwandunan masifa,masifar da sai daga baya na fahimci dalilin yin ta,kuma kamar yanda yafada dinne,ba tare dana sake damuwa da abinda yace ba na cigaba da sabgata,sabgar da ta hada da siyayyar tsarabar da zanyiwa su Nabeela da sauran en gidan namu,ban tashi tsinkewa da lamarin na Yaa Mukhtar ba sai ana gobe satin da ya dibar mani zai cika,a ranar ne kuma ranar da na fara fahimtar halin da nnake ciki duk kuwa da cewa har a lokacin ban kawo wa raina komi ba.
Tun wayewar garin ranar natashi da wani irin azababben tashin zuciya,ga dai zuciyar tawa na tashi amma babu amai,nayi nayi ma inyi aman ko zan samu sa’ida amma hakan baisamu ba,al’amarin dayasa nai kkwance akan gadona ina maida nunfashi sama sama,nasani jikina kwata kwata baya man dadi kamar da,sai dai ina danganta hakan da aikin infection da akai mani kamar dai yanda Dr Ben yafada,amma abun yafara so yafi qarfina,wane irin abune hakka daga neman lafiya na bige da wani ciwon da ada can sam bana jin shi.
Kiran wayarshi ne ya shigo kamar kullum,wannan karon nagaji da boyon ciwon danakejin yafara takurani,hakan yasa ina daukar wayar na fara rera mashi kuka a hankali.
“Yaa Mukhy bani da lafiya,wlh something is wrong with me.”
Na iidasa maganar ina shashsheqa,atoh ni nagaji,naga alamar dai inban furta ba gaf nake da shiga wani hali,and a ganina abokin kuka shi ake gayawa mutuwa,duk da cewa naga yanzu bai cika damuna da akwai inda ke mani ciwo ba,mostly sai dai ya isheni da masifar inbi a sannu indena wannan rawar kan da garajen nawa,wanda ni bana ma bi ta kai domin zantukan nashi ta kunnena suke bi su fita ta dayan kunnen.
“Calm down please,mubi komi a hankali Ni’imah kinji ko?now tell me,me dame kikeji?”
Ya tambayeni in a very calm manner.
“Zuciyata ke tashi kaman mene,and nama kasa yin aman ballantana in samu relief,in fact my whole body is not normal,im just stres…….”
Banqarasa ba naji wani amaiii yataso mani da qarfi,ba shiri nasaki wayar na falfala toilet,wannan karon dagaske aman yake domin kuwa gadan gadan yataho nakuma rinqa kelayashi ba sassautawa,sai da nagama amayar da duk wani sauran unprocessed abincin da yai saura tumbina,harma yazmaana kakari ne yai saura,daqyar nasamu aman yatsaya na wanke fuskata nafito a jigace,ban bata lokaci ba na yayibo chewing gum na jefa bakina ina lumshe ido,komawa nnayi domin sake kwanciya,sai alokacin kuma na tuna sa wayata dana cillar gefe guda,da sauri na janyota,ilai kuwa har a lokacin bai katse kiranba,hakan yasa nai saurin maida wayar a kunnena ina ambatar hello.
“Hellooo,Ni’imah are you there?”
Wannan karon kamar tafiya yake,domin kunnuwama najiyo mani qarar iska alamun tafiya yake.
“Aman ne ya sarqe ni,don Allah kazo ka kaini asibiti.”
“Karki fita ko ina gani nan zuwa na baro school,im on my way yanzun nan.”
Toh kawai nace mashi,sai dai ina shirin kashe wayar ya hanani,wai inkwanta inbar wayar a kunnena ya riqa jin numfashi na,nidai toh kawai nabishi da shi nayi yanda yace din,kana na cigaba da tauna cingam din danakejin yataimaka manj sosai wajen samun sassauci akan abinda nake ji.
Sallamar Aunty Madina cikin dakin nawa ya fargar dani daga tunanin dana dan fada,kana ba tare da na kashe wayar ba nacireta aa kunnena na aje gefe,lokaci guda ina tambayar Aunty Madinan inda zata ganin tayi shirin fita.
“Zanje wani cafe ne can kusa da school akan project dina,and da zuwa nai kimani rakiya,sai naga ma kamar baki riga da kinyi wanka ba koh?”
Dan yamutsa fuskata nayi
“Wallahi kwata kwata banjin dadin jikina Aunty Madina,ga Yaa Mukhy naan ma wai zaizo ya kaini clinic.”
“Ayyah sannu pretty,Allah yaqara sauqi ko duk kewar tawa ce haka har kinfara?ni sai yanzu ma nagane ba wani ciwo,duk ciwon missing dina ne.”
Nima dariya nabiye mata muka rinqa yi ina cew
“Kuma fa haka ne Aunty Madindin,missinggities ne ke damuna,kikawo agaji ki hanani tafiya nigeria please.”
“Er tusa,gara ki koma ko ma huta da wannan zaryar da Yayankin nan kema,duk da dai kin maidani er iska kince babu wata alaqar lobayya tsakaninku.”
Dariya na sake sanyawa,ni narasa dalilin da yasa suke dauka kamar soyayya ce tsakanina da Yaa Mukhy,ba su sani bane soyayya is the last thing da zata iya shiga tsakanin mu,amma sunkasa ganewa,mussaman aunty madinan da malam ibrahim.
“Kai Aunty Madina,sau nawa zance maki Yaa Mukhtar ba saurayina bane,infaact ni da yake wa kallon kucaka kwaila,ai kuwa kinsan babu abinda zaici dani.”
Tana shirin fice take bani amsa.
“Keh ni rabani da wannan iskancin,ai ko makaho yashafa yasan Mukhtar qaunarki yake yarinya,kisani inma baki sani ba.”
Nikam dai banaake cewa komi ba baya ga komawa baya danayi na kwanta ina sake nanata maganganun nata a zuciyata,can babu dadewa da tafiyar Aunty Madinan call dinshi yashigo wayata.
“Fito muje,ina waje.”
Doguwar riga na zura na figi wayata nayo hanyar waje,sanin bakowa a gidan yasa ban damu da in fadi innda zanje ba,wannan karon maimakon inganshi cikin mota ina fita na hangoshi tsaye a bakin motar shi,har yau nakan rasa wanda suits ke wa kyau fiye da shi,no matter how kuwa na duba na hanga,har ma nakan riqa zancen a zuciyata shin mutumin nan yasan kuwa yanda suits ke bala’in matching dinshi?ko shakka babu profession din da ya zaba yatafi da tsari kuma da zubin halittar shi.
“Barrister Mukhtar Gaya Esq.”
Na ambaci sunan a raina,duk da sanin cewar yanzune ma zai shiga final year a karatun nashi.
“Hattara karki lasheni da kallo,im i that cute shine baki taba fada mani ba?”
Muryar shi da tai nasarar sanya wata muguwar kamani ta dawo dani hayyacina,aifa kuma nabani,ni banma san dalilin da ya kai idanuna kanshi ba.
“Excuse my behavior hankalina ne baya jikin.”
“I see.”
Itace abinda yace yaje gefe gami da bude mani qofar motar tashi,nidai ba baka sai kunne,nasanya duwawuna na zauna ina jiran wani sabon iyayin,toh iyayi mana,inba haka ba meyene na wani bude mani qofa bayan ba abu bane da na saba da gani ba.
Maimakon mu nufi asibiti kamar yanda na zata sai naga ya dauke hancin motar zuwa gidansu da a yanzu yazama gidan shi,domin dai yanzu shikadai ke rayuwa cikin gidan tunda ba zuwa american akeyi ba.
“But Yaa Mukhy inace asibiti zaka kaini?kamar haka mukayi dakai?”
Ba tare da ya kalleni ba ya jefeni da maganar da ta sanya tusa subuce man ba shiri,take yanke kuma naji kamar zawo na son kamani.
“No need to,because nasan meke damunki Ni’imah,you are pregnant,kece baki sani ba,amma yanzu kinsani.”
Dariya ce ta subuce mani,take kuma na riqa kokuwar son tuno wani month muke,sai naga ma ashe may muke,kenan ba April fool yake man ba,kuma ma that aside,yaushe muka fara er wasa irin wannan tsakanina da shi,ma meyakawo irin wannan wasan saboda Allah?
Tsaki nayi wanda bansan ma nayi shi ba sai bayan yafito.
“Kina da hankali?karki sake yi mani tsaki,kibar ganin kina dauke da cikin d’ana ba shi zai hanani lallasaki ba.”
“Eyeeeeh na’am?cikin wani d’an?kambala’in can.”
Na furta hankalina a dan tashe.
Ina kuma shirin bude baki nai magana ne ya dakatar dani ta hanyar daga man hannu,
“Adana maganar ki sai mun shiga ciki,magana d’aya ce,kuma zancen gaskia,kona taba wasa dake ne?”
Kamar doluwa na riqa girgiza kai.
“Well,You are two months old pregnant with my baby,and i Mukhtar Gaya is the father!copy that?”4
Wane copy lokacin ai na dade da daskarewa a zaune.Ciki?Ni ke dauke da ciki?duk da qananan shekaru na,ina da ilimin sannin hanyar da ake daukar ciki har ma ta kai ga samun d’iyoyi,sai dai a iya tunanin da na riqa dagewa wajen tunawa,qwaqwalwata ta gaza tunamin lokaci ko ranar da na taba had’a shimfida da wani d’a namiji,nasani,nasani kwarai ban taba zina ba,ban taba saida mutuncina ga wani ba,ballantana har ta kaini ga daukar ciki,innalillahi wa’inna ilahirraju’oun.+
Fuskata dauke da wani irin bayyanannen tashin hankali na dago ina duban Yaa Mukhtar sin,yau daya sai naga yamun wani irin baqiqqirin a fuskata,lokaci guda kuma na zana layin sunan shi cikin mutanen da zan iya bugar qirji in kirasu da maqiyana,toh inba makiyinka ba,haka kurum me yakawo a jefeka da irin wannan mugun alkaba’in?
“Nikuwa Yaa Mukhtar me na taba maka a duniya da kake nema ka riqa bin rayuwata da mugun alkaba’i irin wannan?ina hadaka da girman Allah da ka yafemani koma menene,because…..”
Muryata ta shaqe sabida kukan da ya fara cin qarfina,ga kuma wani kallo da yakoma baya yana jifana dashi,wanda nakasa gane ma’anar shi
“Because this is too much for my heart to bear Yaa Mukhtat,na roqeka karka sake yi mani irin wasan nan don ya rasulillahi.”
Wannan karon na ida barkewa da kukan,yau ni nake ganin qiyayya qiri qiri,toh inba qiyayya ba menene wannan?
Nayi tunanin zai dubeni yace inyi hakuri wasa yake,nakuma yi tunanin qila zai yi nadamar jifana da kalamen da suka firgita ni,sai dai hasashen nawa bai je ko inaba ya jefeni da abinda ya idasa tarwatsa guntuwar nutsuwar da tai mani saura.
Na riqa bin takaddanun da ya jefo mani bisa cinyoyina da idanuna dake faman shatatar da hawaye,na riqa qoqarin fahimtar rubutun dake zane da farar takardar,duk da hawayen dake yi mani katanga da rubutun,ban kasa karanto sunana baro baro bisa takardar ba.
Duk da cewar rubutun dake zane da takardar ba rubutu ne da zan iya karantawa ko fahimta ba kai tsaye ba,hakan baisa nakasa fahimtar cewa takardar dauke take da sunan asibitin Dr Ben ba,dadin dadawa heading din dake kai ya nuna takarda ce dake nuni da pregnancy test result,a kuma qarancin natsuwar da tai manj saura na iya karanto +ve a a jerin da rubuce rubucen suke.
“Innalillahi’wa’inna’ilaihirraju’ooon.”
Itace kalmar da na riqa maimaiatawa yayin da kaina da idanuwana ke duqe ina sake bin takardar da kallo,wannan karon cikin ficewar hayyaci,hawayena kuwa dama tuni sunfara jiqa takardar,yau wace iriyar masifa ce nake gani?inaso ne na tuna,inaso ne kwarai natuna rana guda daya jal da na taba kebewa da wani namiji,namijin ma Mukhtar Gaya.
Gyaran muryar shi bata sanya na fasa kukan da nake sharba ba,har yanzu bani da qarfin bude baki na sake magana,bakina yaman nauyin da bai taba ba,zuciyata na wani irin bugun da bata taba ba,ga kuma qwaqwalwata na tseren gudun fahimto man shin dama ana samun ciki haka nan daga sama?ko kuwa ana shan shi a ruwa ne kamar yanda naji ana fad’a?
“Hey,Ni’imah listen to me please.”
D’ago da kaina nayi ina dubanshi,duba mai cika da tarin m’anonin da basu da iyaka,haka kuma jira nake yai mani bayani,eh bayani nake son ji,so nake ya fayyace mani al’amarin da ya fara nasarar tafiyar da sauran farin cikina,eh farin ciki na mana,ai inajin daga yau munyi adabo da wata kalma mai kama da farin ciki da walwala,idan har wannan zancen yazamana gaskia,duk da har yanzu a qasan zuciyata fata nake ace hakan duk mafarkine,mummunan mafarkin daa bzanso in sake maimaita makamancin shi ba.
“Ki taimakeni ki dena wannan kukan nikam,ko baki da labarin illar hakan a gareki?or do i have to remind you that yoy are not the same person few months back,yanzu ke mai dauke da juna biyu ce,babyna na a cikin ki,ki rufa mana asiri ki dena kukan nan,i don’t like it.”
STORY CONTINUES BELOW
Kallo na riqa binshi da shi mai cike da tsananin tsanar shi da dimbin mamakin ahu,domin lokaci guda nagama yarje wa kaina cewar he took advantage of me ba tare da sani na ba,raina a dagule na hanzarta juyawa na bude murfin motar na fice da sauri,domin kwarai a yanzu bani da qarfi ko kuzarin yin wani abu,zuciyata gaf take da bugawa.
Tafiya nake da dukkan qarfin da yai mani saura,ba kuma tare da nasan inda nake jefa qafata ba,abu guda ke manj yawo a jiki da zuciyyata shine,wai yau ni Niimah ni ke da cikin haihuwa ba na cin abinci ba,ciki na haihuwa,cikin da bani da masaniyar ta yaya,kuma a ina nayi shi,cikin da bansan ta ina zan fara fuskantar duniya da shi ba,yau ta kasance mummunar rana a gareni,har na riqa jin me ma yakawoni american?har gashi nazo na bige da yin ciki,cikin ma wai danuwana yayi man shi,take Mammy ta fado mani a rai,shikenan nasan qarshena yazo,don nasan bani da wani tsimi ko dabara,Mukhtar yagama ja man alkaba’i.
Bani da masaniya akan abinda ya faru,nadaiji anyi sama dani,ko kafin in ankare an sab’ani a kafada tamkar wata yarinyah er shekara hudu,tuni dama na dade da wage baki na riqa kwantsama ihu da iya qarfina,sai dai ihunka banza nake,domin ko tarin wani mahaluqi banji ba ballntana un sanya ran cetoh.
Duk da bige bige da hantsile hantsilen da na riqa yi bai sanya ya sauke ni ba,inaji ya sanya key ya bude entrance din shiga cikin gidan,nakuma aza zai cillar dani a parlor ne sai naji akasin hakan,domin ji nai yana hawa stairs dani,na riga nasan ko ina na gidan saboda zaman da mukai cikin gidan a da,hakan yasa na fahimci dakunnan baccin gidan ya nufa dani,ban fahimci ina nake ba sai bayan naji ni kan lallausan italian bed din dake girke a dakin,kallo guda naiwa dakin nagane dakin baccin Daddyne a da.
Banyi qasa a guiwa ba na zabura zan falla da gud,wannan karon da ya damqoni cire vail din dake reto a wuya na yai ya daure mani hannayena da qafafuna guri guda,inbanda nishin wuya shima babu abinda yake hakan yasa yana gama qulleni yai warwas bisa sofa din dake gefen gadon yana maida numfashi,ba shakka yarinyar nan ta shammace shi kai!
“Ni ka kwance ni,wallahi Allah ya isa tsakani na da kai,mugu azzalumi dan iskah,ba zan taba yafe maka ba,macuci mai fuska biyu.”
Ni kaina da nake zagin ban taba sanin na iya su ba,na dai tsinci bakina da yin su,sai dai wanda nake aikawa zagin ko gezau beyi ba,hasalima wani murmushin gefen baki naga na kwace mashi,daga karshe ma sai ya haqura ya hau dariya a hankali,dariyar da nagama sakankancewar ta rainin hankali ce.
Bansan ma yataso ba,sai dai naganshi a gabana yai mani qerere a ka,ba tare kuma da na iya karanto me yake shirin yi mani ba naga ya hau kwance dauriin da yai mani,yana gama kwance ni ya nuna man qofa gami da cewa,
“Oyaaa tashi muje in maida ki gidah.”
I wasn’t expecting that,amma banyi qasa a guiwa ba na miqe da hanzarina,sai dai miqewata yayi daidai da jin wani irin amai yataho mani da qarfi,kafin inyi yunkurin nufar bandaki har nafara kelayashi,wannan karon amaan ba na wasa bane,duk da babu komi a cikina banfasa kwararo ruwa ba,har takai ta kawo yunkuri kawai nakee ina nishi.
“Sannu,sannu Hayatiey,im so sorry,tashi muje ki wanke fuskar ki.”
Sai yanzu da na dawo hayyyacina na fahimci me ma yakeyi,ashema rabi da kwatan aman a jikin shi na kelaya shi,sannan kuma inbanda rawa babu abinda jikin shi keyi,gaba daya nagama jigata bana ko iya d’aga hannuna bare in sauka daga kan jikin shi da nake kwance kashirban ina numfashi sama sama.
Ji nayi wani irin kuka yasake kwace man,ba shakka nagama yarje wa kaina cikin ne da ni,domin duk wasu alamu da shaidu da zasu nuna ina dashi din sun nuna,mussaman da sai yanzu ne ma na tuna banyi period ba last month tun lokacin da nake tsammanin ganin shi,sai dai rashin yin be dameni ba,tunda an ce mani akwai wadanda ba ko wani wata sukeyi ba,hakan yasa na danganta yiwuwar hakaan da wannan,ga kuma wata na biyu ma yana gaf da qarewa still banyi ba,kenan na tabbata mai ciki?ni kuma haihuwa zanyi ba tare da nayi aure ba?ni Niimah zan haifo dan shege,zan zama mace ta farko a ahalinmu da zata karya record din yin abun kunya.
STORY CONTINUES BELOW
Na sake tsagewa sa kuka ina cewa,
“Why?whyy Yaa Mukhtar?meyasa zakaci amanata har haka?don Allah me nai maka?”
Wannan karon kwantar da kaina yayi bisa kafadarshi yana faman jijjiga ni,bana fahimtar komi a bakin shi da ya wuce kalmar “i am sorry Hayatiey,i am so sorryyyy i have no any other option ne.”
“Bangane you have no any other option ba Yaa Mukhtar?cikin nan garin yaya na sameshi?when,where and how na sameshi?qwaqwalwata ta gaza tunomin daidai da rana daya da wani abu mai auna intimacy da ya shiga tsakaninmu,i know,i know i have never share a bed with anyone a duniyar nan,garin yaya nasamu ciki?”
“Its a long story Ni’imah,its a lo…….”
“Cut it short!”
Na katse shi cikin qufula da qosawa.
“Yes,cut it short, inason jin ta inda ni Niimah nasamu ciki.”
“Okay,but first muje ki fara kintsa jikin ki,nima dubi gaba daya kin b’ata man jiki.”
Kallon banza na jefeshi da shi,tare da na ubanwaye yajaman inba kai ba?ilai kuwa ya fahimci kallon,hakan yasa ya miqe tsaye da sauri gami da dagoni yana cewa,
“I will make it up to you,ni ne ko?”
“Mtswwww”
Naja wani mugun tsaki inajin tsanar shi na samun guri cikin zuciyata,ba shakka ba zan taba yafewa wannan baqin mugun ba,kana kuma da sauri na fizge hannuna duk da rashin qarfin da jikina ke dashi,hakan yasa nai baya suuu zansha qasa,kkafin in ida kaiwa naji yai mani masauki a qirjin shi,amma saboda masifar haushi da takaici sai da na dago na bangaje shi na shige bayin na barshi nan tsaye cikin amaan.
Qyanqyamin kaina nake,gaba dayana nai jage jage da amai,hakan yasa na tube kayana na shige shower,ina wanka ina kukan takaici,gaba daya tunani na ya tsaya,so nake nasan ta ina zanfara,ta ina zan bullo?kuma me zan gaya wa dunia inta bude ido ta ganni da cikin shege?
“Abortion!”
Kalmar ta daki qwaqwalwata,take kuma naji wani sanyin na shigata,wannan din ita kadaice hanyar da zanbi in rabu da alaqaqai,hakan yasa cikin qarfin guiwa na hanzarta dauraye jikina na dauro towel zanyo waje,sai a lokacin kuma tunani na ya sake dawo dani cewa baa gidanmu nake ba,hasalima qaton gardi na nan waje yana jirana,al’amarin da ya sanyani runtse idanu hawaye na sake gangaro man,nashiga uku na,abinda na riqa nanatawa kenan,ga wata kafirar yunwa da nakejin tana qwaqwalata,jikin har yafara rawa inajin jiri.
Da naga ba sarki sai Allah sai na daga muryata da qarfi ina kuka mai hade da ihu,na dan yi da yawa kafin naji alamun shigowa dakin,kenan ma fita yayi baya dakin,da saurin shi yaqaraso yana tambayata menene,cikin kuka nace mashi,
“Toh ba yunwa nake ji ba kamar zan mutu,don Allah ka samo man ko shayi ne in sha.”
Bansan na roqeshi ba,burina a lokacin ahine inji tunbina ya dauka,ji nake kamar an man yasa a cikin cikin nawa,gaba daya na manta da batun wani ciki,idanuna sun rufe abinci kawai nake son ci.
“Toh fito muje in hada maki,ko cikin toilet din zaki ci?”
Shaf na manta da wani boye boyen da nake,da sauri na fito nai gaba hanyar ficewa daga dakin,don ko kallon inda yake tsaye banyi ba sai da na jiyo shi yana man magana tukunna.
“Zo ga kaya ki sanya tukunna.”
Sai a lokacin kunya ta dan kamani na dawo baya ina harharde qafafu,kana na dan saci kallonshi inga ko kallona yake naga sam hankalin shi ma yanaga miko man wata sabuwar doguwar riga mai kalar maroon,a lokacinne kuma na lura d ashe harma yagyara gurin da nai amai shima ya canza kaya,hakan yasa na fizgi rigar daga hannun shi na fada bayi domin in saka.
STORY CONTINUES BELOW
Tsaki nayi bayan na lura da jiqewar da inner wears dina sukai,haka nan na zura rigar ba tare da nasaka komi ba,sauqina ma rigar mai hawa biyu ce,kuma yadin me dan kaur ne duk da silk ne,mayafin rigar naa daura kana nayi waje,ina fitowa muka hada ido,baa tare da na saki fuskata ba nai gaba abina,tun a wajen sauka daga kan stairs raina ya sake mugun baci,sakamakon jiyoshi da nai daga bayana yana zabga man masifa.
“I told you to be careful Earlier,meyasa wai ke kunnen qashi gareki?ko so kike kije ki zame ki jazamani musiba?”
“Ni dama zan zame din infadi,qila idan nai sa’ah Allah ya rabani da wannan shegen cikin.”
Na bashi amsa kaina tsaye yayin da nake dora duwawun kan daya daga cikin kujerun da suka zagaye dinning table din.
“Let me warn you!”
Na tsinkayo muryarshi daga kan stairs din,sai a lokacin na lura da ashema bai qarasa sakkowa ba.
“Let me warn you,wallahi billahi,wani abu yasamu babyna ba zan qyaleki ba,indai akan wannan cikinne a shirye nake da cuzguna ma koma waye ne,ko da kuwa uwar da zata kawoshi dunia ne,ki kula!”
Kukan ne yasake dawoman,na miqe tsaye nima ina bashi amsa cikin tsiwa da masifa,ha’an abun ne naga akwai tsabar rainin hankali da iskanci ciki,a dake ka akuma hanaka kuka
“Wallahi ko tsautsayi bai sanyashi ya zube ba,ni nan da kaina zan zubda shi,kayi abinda zakayi daga nan”.
Baice man komi ba ya fara sakkowa daga kan stairs din,ba tare kuma da yace komi ba ya nufi kitchen,cikin en mintuna ya fito hannunshi dauke da qaton mug da wani plate can daban mai dauke da fresh burger,tunda na dora idanu akan burger din na manta da masifar da nake,ko kafin ya qaraso naa miqe na isa inda yake na amshe plate din,zama kawai nayi na hau cin burgern kamar tsohuwar mayunwaciya,ko bi ta kan shayin da ya hada man banayi,dama guda biyu ce amma cikin mintuna da basufi biyar zuwa shidda ba na tada ta,kana daga nan na dauki mug din tea din na kafa kai na qwanqwale shi tasss,ina saukewa nai ido hudu da bread a shafe da nutella bisa wani plate din,ban tambaya ba na janyo shi na hau ci,sai da naci almost slice biyar kana na kora da wani juice din da ban damu nasan sunanshi ba nakoma baya ina mmaida numfashi.
Sai a lokacin na dago kai naganshi tsaye ta can gefe ya harde hannayenshi yana bina da idanuwa,ganin nagama ya sanyashi matsowa gami da jan kujerar dake fuskantar tawa.
“Bravo!thats a job well done, and you know what?you ate amazingly, kinga ko banza zaki haifo mani qaton baby boy or girl,duk da dai hopefully inafatan yazama namiji coz i want to end my life watching a mini me kusa dani.”
Banza nai dashi gami da jan wani asirtaccen tsaki,mutumin nan mugun dan rainin wayau ne,ji wani dai zancen banza,zancen bur inji tusa,ai in sha Allahu yau ba sai gobe ba saina zubda cikin nan,sai dai yakasheni inyagadama.
“Kazo kamaidani gida,ina da abinyi.”
“I thought na fada maki kindawo nan da zama,ko kuwa zaki iya nuna wa dunia kinyi ciki babu aure?”
“Nikuma i thought yanzun nan ba da jimawa ba nagama tabbatar maka da cewar cikin nan sunan shu zubabbe?because ko ba don kunyar dunia ba,ba zan taba yadda in hada jini da baqin mugu azzalumi irinka ba.”
Nikaina da nai maganar nayi expecting one blow seven die,sai dai ba hakan bane ya biyo baya ba,hasalima dage kanshi yayi sama yana dariya,sai da yayi ma’ishi kana ya maido da kallon shi kaina with so much amusement yace,
“Calm down darling,hadn’t been ban shirya wa al’amarin nan ba,bama zan fara qirqirarshi ba tun farko,you see….”
Ya gyara zamanshi yana sake fuskanta
“Kinga wannan cikin da ke jikin ki?like ive said earlier i am the father,ta yaya nazama ubanshi while i have never lay you down koh?well,you want to know how?ki hasasho hakan daga ranar da na kaiki asibitin Dr Ben instead of your Doctor…..”
Ya shiga bani labarin yanda abubuwan suka wakana,which left me mouth agaped and disurbed, nakuma sake sakankance wa kaina mugunta irin ta Mukhtar gaya,sai dai har a lokacin tambaya guda ce nake mashi wacce yaqi sam yabani amsarta.
“Meyasa?meyasa sai ni?me yasa yazabi da yai wasa da rayuwata har haka?menai mashi?”
Har yau da nake baki labarin nan Ammy bai fada mani dalilin shi ba,sai dai ni da kaina na samar wa kaina amsoshin tambayata.
“Sabida ya tsaneni,saboda zalunci,saboda son zuciya irin nashi,kuma saboda ya tozartani a idanun duniya,yakuma sanyani cikin halin qaqanikayi!”
A lokacin ya tabbatar mani da zubar da cikin nan na nufin rasa tawa rayuwar,domin rantsuwa yai mani a lokacin cewa tsaf zai aika dani barzahu kaman yanda na aika da gudan jinin shi,yayi nasarar amfani da rashin wayona sosai ya tsorata ni da kalmar mutuwa,daga nan kuma yai amfani da Mammy wajen sake assasa wutar tsorona,domin nuna man yayi zai kirata kai tsaye yafada mata garin dadi soyayya ta debemu har yai man ciki,tarko na farko kenan da ya fara dana man wanda ya tsoratani,nasani nasani kwarai,bayyanuwar wannan zancen a kunnuwan Mammy tamkar watan bankadar rufin asiri na ne,domin nafi dan dakon tasha sanin kafirin son kanta da kuma fifita nata akan koma waye.
Yakuma dage wajen nuna mani cewar idan harma na bujire mashi still nice zan kwana ciki,because ni diya macece,so duk wani consequences din al’amarin kaina zai fada,domin yagadama yace baisan zance ba,maana ciki ba nashi bane,kuma tsaf zai rantse da alkurani cewa baitab’a kusanta ta ba,a qaramin tunanina a lokacin duk sai naga kuma hakanne,toh kuwa in haka ne inajin yin abinda yace din shine rufin asiri na,na riqa tuna kalmomin shi na qarshe.
“Ni alfarma guda zakiyi mani,kamar yanda kema zanyi maki wannan alfarmar,ki hakura ki haife mani cikina,nikuma nayi alqawarin daga ranar da kika haifeshi ko duk duniya zata taru a akaina bazan fadi wacece mahhaifiyar shi ba,zan rufa maki asiri,zan tsare mutuncinki da kike gudun zubewarshi,wannan alqawari ne da na daukar maki,Allah ne shaidata.”
Na lumshe idanuna inajin bani da wani option da ya wuce yin abinda yace din,ko don rufin asirina da kuma karewar mutunci da qimata,because bana hangoma yanda zan fuskanci dunia da jama’r cikin ta da wannan cikin da har yanzu bansan wane suna ne yadace dashi ba,ko kuwa zan iya kiranshi shege kai tsaye?1
***Yai amafani da kalamai da kuma matakai masu matuqar tsaurin da suka sanyani yarje mashi gaba d’aya,mussamman ta bangaren Mammy da nakejin nan ne zanfi quntata matuqar ta san da zance,a ranar ban kwana gidan ba kamar yanda ya buqata,sakamakon plan din daya tsara man wajen sanar da en gidan Doctor Grema.2
Bayan nakoma gidan da kwana biyu,zuwa lokacin nagama kintse kintse da gyare gyaren kayana na tafiya nigeria kamar dai yanda ya tsara in sanar da su,da kanshi yazo ya daukeni mussaman don gudun rakani airport da suke da niyyar yi,na rabu da su cikin kewa da nauyin zuciya,mussamman sanin cewa ba tafiya zanyi ba,a hasashen shi a qallah in qara watanni bakwai ko fiye da haka a cikin birnin na america.
Mammy kuwa dama bai samu matsala da itaba wajen shirya mata qarya,a cewarshi akwai wasu zunzurutun kudade da gwamnatin america take shiryawa duk passinjojin da suka rasu a cikin wannan hadarin jirgin,ba’a maganar kuma ma’aikatan cikin jirgin,qwarai suke da kaso mafi girma cikin kudaden,hakan yasa ba zan samu damar dawowa ba soo,domin gaskia kawai sai an ganni,dama ba wai damuwa tayi da dawowar tawa ko rashin ta ba,hakan yasa tace Allah taimaka yakuma bada sa’a,ita dai matsalarta shine yakula yadena man wannan shishshigin,domin dai bata so,shikuma a lokacin yakanyi wani irin murmushine yabita kawai da toh.
***
Yau kimanin sati na daya da dawowa gidan Yaa Mukhy,and cikin satin nan da dawowata gidan yanda kuka san laulayin na jira ne in dawo,yanzu bani da katabus,idan har before ma akwai sauran tantama da nake dashi akan cikin toh yanzu duk ya kau,domin zuwa yanzu munzama aminan juna nida amai,qa’idane koma ince dole ne duk wayewar gari sai nayi,amma kuma ba zan sake ba sai kuma wata safiyar.
Ba zan iya tuna ranar da na sakar wa Yaa Mukhtar din fuska ba tun bayyanuwata a gidan,duk kuwa da irin shishshigin da kuma nuna kulawar da yake tunanin yana man,bai taba burgeni ba ballantana inji na yaba mashi,hasalima tsabar haushi da sabuwar tsanar shi ce ta ke sake samun gurin zama cikin zuciyata,banajin zan taba yafe wa mutum irin shi,mussamman da har yanzu nakasa tantance dalilin da zaisa ya gurbata mani rayuwata har haka.
Cikin bacci naji cikina ya dan murda,hakan yasa na bude idanuwana ina dan runtse ido,tun wayewar garin jiya nake danjin ciwon,amma nakasa fada mashi,saboda ma bani da dalilin fadin,fata na riqa yi inama hakan zaizama sanadiyyar zubewar cikin,sakkowa nayi daga gadon da nufin in shiga toilet in wanke bakina,yunwa nake ji bani da yunwa ba,kai kace banci abinci ba kafin na kwanta ba,ni kaina mamakin wannnan shegen cin da nafara cikin en kwanakin nan nake,tsoro nake kar nazama tuleliya kamar yanda na lura Aunty Madina ta fara zama kafin nataho.
“Oh Allah sarki,Aunty Madin,ko yaya take yanzu?nasan zuwa yanzu cikin nata yafara qwari.”
Na ambaci hakan a zuciyata,ba shakka nayi kewar su,raina ya sake baci da na tuna qaryar da Yaa Mukhtar din daga baya yakirasu ya danqara masu,wai yanzu bani da wayane,na yadda wayan,thats why bansamu kiransu ba tunda na dawo nigeria,mutumin ku dai ya tsattsara su bayan ya cire layina dake kan wayata yabarni da kwankwon waya kawai.
I don’t know how he normally does it,amma kullum idan na fito zan iske abinci kusan kala biyar a shirye,ga kuma junky foods da suka sake zame mani ababen so yanzu,nagama sa wa raina kila ordering abincin yake before yatafi school,domin ban iya tuna randa nataba ganin shi a kitchen yana girki,gaskia ban iya tunawa.
Zama nayi na dibi girkina yanda yakamata,naga dai inbanci ba ma kashe kajna zanyi a banza a wofi,its better ma inci din insan naci,don ba zan akshe kaina ba a banza a wofi ba,can saman sofas din da suka qawata parlorn naje na kwanta rubda ciki ina kallon tashar Mbc 2,gefena kuwa tiqa tiqan shawarma ne guda biyu a zaune cikin plate,ga bottle of lemon juice a gefe ina korawa.
STORY CONTINUES BELOW
Hankalina yayi nisa wajan kallon wani movie wai shi “Dead Pool” da ake nunawa a tashar Mbc 2 din,hakan yasa banji shigowar shi ballantana sallamar shi,nidai naji wata iriyar tsawa d ata sani miqewa da sauri ina zare ido,shifa mutumin nan na lura be cika saiti ba,na menene zaizo ya tayar man da hankali ina tsaka da hutawa ta.
“Hala baki da hankali ne?”
Zumbura baki nai gaba ina qunquni,ah ah toh nima fa mutum ce,ta yaya kullum sai dai yadaga ido yaita fama kirana da mara hankali,bayan nasan ba abubuwan marrasa hankali nakeyi ba,toh na menene ni zaabi a isheni.
“Sau nawa zan ce maki ki dena wannan rubda cikin?ko har yanzu motives dinki na nan nason kashe man baby?”
Shiru nai bance mashi komi ba,ni har ga Allah mantawa nake da wani babatun shi akan rubda cikin da nake,atimes ma mantawa nake da wani ciki a jikina,tunda dai beyi kwarinma da zanji babu dadi ba in nai rubda cikin.
“Get up kafin raina ya ida baci.”
Ba musu naa miqe ina yatsina fuska,aikin banza kamar wani ubana yariqa man wata isa isa.
Zuwa yanzu yaqarasa shigowa tsakiyar parlorn,zama yai gefena lokaci guda yana kai hannun shi saman goshina.
“How are you and my baby today?”
Zame kaina nayi cikin jin haushi,idan da akwai wata dabi’arshi guda dana fi tsana toh wannan ce,and bansan sau nawa zan nuna mashi rashin jin dadin abunda yakeman ba.
“Don nikam kadena tabani banaso.”
Na sake bashi warning kamar yanda nasaaba a duk lokacin da zai kai hannun shi jikina.
“You are stupid Ni’imah,i hope you know that?”
Dama kullum amsar shi kenan,daga nan kuma sai yajayo ni da qarfin tsiya yabi ya lalube goshina da wuyana,wai nan duk jin yaya temperature dina yake na ranar.
Daga nan kuma yashiga bina da tambayoyin yaya nakejin jikina?naci abinci ko kuwa ina buqatar wani abu daban?a kullum amsata no ce,ko da kuwa ina buqatar,ba don komi ba sai don in bashi haushi.
A haka yau da gobe,da dadi babu dadi muka cigaba da rainon cikin da yazame mani alaqaqai,ba zan manta ranar da na fara jin motsin shi ba,i was in awe,the feeling is exceptional, duk da inajin ba zan taba son dan ba at that moment sai da naji wani abu mai girma na shigata,har yazamana each and every moment har so nake inga ya motsa.
Tun ina boye mashi motsin nashi,har takai takawo da kanshi ya gane,tun daga nan kuwa ban qara samun lafiya ba daga gareshi,a kullum safiya kafin yaatafi makaranta sai yazo yagama qare mana kallo kafin yake tafiya,wani zubin idan yayi sa’a ina bbacci yakanyi kasadar shafa cikin ba tare da sani na ba,domin dai sai da na dauki matakin gaske wajen ganin yadena tabani,duk kuwa da cewar hakan ba qaramin zagi yajawo man ba wajen shi,a cewarshi qwaila irina har wani abu gareni a jikina da zai bashi shaawa?that in shiga hankalina in gane dalilin da yasa yake man haka,ba don komi bane sai don ajiyarshi dake cikina.
Lokacin da cikin yamiqa ya tunkari wata na bakwai zuwa na takwas kuwa tuni na dan fara hayewa,duk da dama bana cikin mata masu rama,kai tsaye zaa iya sanyani cikin categoryn din mata masu dan jiki maana chubby,hakan yataimaka wajen boye girman cikin sosai,sai dai qirjina da sukai matuqar fitowa a wannan lokacin.
Anti natal yazamana duk bayan sati yake kaini asibitin Dr Ben,ranar kuwa da scanning yanuna gender din babyn kasa rufe baki yayi,abu kadan na kamashi yana murmushi shi kadai,bakina bazai iya misalta irin son da Mukhtar kewa cikin nan ba,ta bakin tashi ce da yake cewa ajiyace yabani,kuma yakusa ya amshi abinshi.
Kwanaki sun shude a inda watannin cikin suka tasarwa watanni takwas zuwa tara,zuwa wannan lokacin dama yariga da yagama cika gidan da duk wasu kayan babies da babyn zai buqata,nakan rasa ina yake samun ma wasu information din game da newborn,sai dai na danganta hakan da yawan browsing da nake yawan kamashi yana yi,mussamman akan delivery.
STORY CONTINUES BELOW
Zuwa yuanzu zama daqyar ne tashi daqyar,sannan kuma na fahimci wani sabon canji sosai daga gareshi,mussaman yyawan fadan da yake mani yanzu duk yakau,hasalima jure duk wasu mood swings dina yake,baya nuna bacin rai ko yamun masifa kamar yanda yakeyi a baya,laallabace da rarrashi yanzu a tsakanin mu,abu kadan yace man sannu,ko wani guri na miki ciwo ne?idan kuwa ya riskeni ina sharbar kuka gigicewa yake yaita faman bani hakuri,a haka dai muke lallabawa har zuwa lokacin da Dr ben din ya umarce shi yakawoni asibitin domin a fidda babyn,a cewar shi bazan iya haihuwa da kaina ba mussaman ganin cewa im still a virgin,aside that cs dinne kawai yakamaceni ko don gudun wasu complications(matsaloli) da ka iya zuwa.
***
Ranar alhamis itace ranar da tayi daidai da cika 40 weeks da nayi,ni kaina zuwa wannan lokacin na riga da na sare,nakuma gaji da cikin,ji nake kaamar duk nauyin duniyyar nan ne aka sanya man shi cikin ciki na,hakan yasa kullum safiya ni kenan cin pineapple,saboda naji ance tana taimakawa wajen triggering labor,amma duk da haka shiru kake ji kamar an aiki bawa garin su,gashi kuma Dr Ben din yace sai munga any sign of labor kafin yakawoni asibitin.
Yauma kamar kullum munje nayo exercise kamar yanda doctor ya umarceni da yi kullum,tun a hanya nake jin kamar marata na qullewa,amma kuma cikin en mintuna sai ta saki,amma ban fada mashi ba,a haka dai muka lallaba daqyar muka dawo gida,dawowar mu cikin gidan yayi daidai da jin wani azababben ciwo da nayi,ai bansan lokacin da na duqefa na hau rafka salati ina sanar da ubangiji,ganin hakan yasanya shi sungumata gaba daya ya nufi mota dani,dama zan iya cewa tun sati biyu da suka gabata yagama hada jakan haihuwar tamu ya sama mata matsugunni a bayan motarshi,hakan yasa babu abinda muka tsaya dauka sai asibiti.
Isarmu asibitin da misalin qarfe tara na safe suka amsheni,mussaman dai dama ga irina dake da appointment da likitan,bayan yayi en dube dube ne ya tabbatar da haihuwar ce,cikin awa da baifi guda ba angama shirya ni zaa shiga dani tiyata room,daqyar Yaa Mukhtar din ya sakar man hannu,gaba dayanshi a susuce yyake kamar shi ke naqudar,nidai addu’o’ine duk wacce ke bakina ita nake kamowa,fatana in haihu lafiya ko na rabu da wannan qajagar,mussamman sanin da nai lokaci qanqani ya rage mani in fita daga wannan qangin rayuwar,nakusa yarda qwallon mangwaro in huta da quda,a tunanina kenan.
Sai dai tunanin da nake tunda din ya yanke ne a lokacin da allura ta sake ni na bude idanuwa na a resting room,da dan mild ciwon kai na farka,sai daga baya a hankali naji dama dama na fara rarraba idanu cikin dakin,lokaci guda nakai hannuna saman cikina naji shi sumul kamar ba nawa ba,wani irin relief ne naji ya biyo baya,bandamu da sanin ina babyn ba don baya gabana,babban abunda ke gabana yanzu shine in bude ido inganni a nigeria,inaso qwarai nai nesa da duk wani abu da ya danganci Mukhtar da danshi ne,nidai burina inbar qasar,suje su qarata dashi da danshi.
“Mrs Mukhtar how are you feeling now?”
Muryar Dr Ben ta doki kunnuwa na,ai ban ma ji shigowar su ba,harda ma Yaa Mukhtar din,hankalina na ga yanda zan fella inbar qasar nan ba tare da nabar duk wani foot print da zai nuna naa haihu ba.
“I’m good thank you.”
Na yi qarfin halin bashi amsa,qwarai banajin ciwon komi,sai dai ta inda aka yankani,shima kuma ba wani abu nakeji da zai hanani ida nufi na ba.
Wasu en aune aune likitan ya sake yi man,bayan ya tabbatar man da cewa komi na tafiya yanda yakamata,yanzu kuma zaa kawo mani baby na in bashi nono,mussamman ya nuna mani amfanin hakan wanda ni ta dayan kunnena maganganun nashi suke bi suna wucewa,ni zan shayar da wani abu waishi d’a? D’an ma na Mukhtar Gaya?Allah ya sawwaqe na riqa ayyana hakan a raina.
Sai dai mene?tunda nurse tai knocking bayan fitar Doctor rungume da wani kyakkyawan jariri a shirye cikin kayan sanyi masu shegen kyau naji wani abu mai tarin girma ya gifta mani,ban sake sanin menene ba sai bayan ta dora man shi a hannuna,duniyata ce tai mani qiqam,na riqa jin wani sabon al’amari na keto bargo da jinina,wani irin so da bansan ina da ikon yin irin shi ba naji yana shigata farat d’aya,na riqa jin wata iriyar qauna maras iyaka na bin ilahirin jikina,so ne kuma mai dadi da banajin na taba yi wa wani irin shi bayan iyayena,although this was exceptional.
STORY CONTINUES BELOW
“Hayatiey yaya kika ga Babyna?very handsome koh?”
Bansan meyasaba,amma sai naji kalamen shi sun ban haushi kai tsaye,bangane babyn shi ba?hakan yasa nai banza dashi ina sake bin fuskar jaririn da kallo,kwarai he is very cute,tun a lokacin kai tsaye zaka iya karanto kamannin shi da Yaa Mukhtar din without any doubt,amma bansan meyasa ba hakan ma haushi yabani,a ganina ai dani yakamata yai kama,tunda dai nice uwarshi,ni kuma na haife shi.
“Thank you Ni’imah for completing me,nagode nagode kwarai dagaske.”
Na sake tsinkayo muryarshi,wannan karon ma bance komi ba baya ga hararar da na danqara mashi,dama yabar wani gode man don ba yafe mashi zan ba,har abada kuwa.
Shiru mukayi muna ta kallon babyn dake ta rarraaba idanu yana wawurar hannun shi,sosai nakeson bashi nonon,amma kuma presence din Yaa Mukhtar din ya hanani,nakuma rasa yanda zanyi ince yafita,hakan yasa sai dai naita buga tsaki ina mutsu mutsu.
“Duk da nasan conditions din dake tsakanin mu,amma still zan roqi alfarma guda a gurin ki.”
Na sake tsinkayo shi,bai saurari abinda zance ya cigaba….
“Ina hadaki da girman Allah da ki shayar man dashi yau kadai,kafin gobe mu koma Nigeria in samu me shayar mani dashi.”
Bansan ya akai ba,nadaiji gabana yai wata iriyar ffaduwa,amma still ban motsa ba,hakan yasa na sake tsinkayo muryar shi.
“Please,ba don halina ba.”
“Toh ka fita mana!”
Na bashi amsa bayan na cuno baki gaba,qiris nake jira in fashe da kuka,domin ji nake kamar dunia naa shirin juyaman baya,bai qara cewa komi ba ya juya yafita yana waigenmu,kamar hira nake kuwa na sake riqo babyn dakyau ina sake kallon shi,so da qaunarshi suka taru sukai man rubdugu,hakan yasa na qanqameshi a qirjina ina zuba mashi kissess a goshin shi.
Bansan haka uwa keji ba,ashe haka akeji?ya salam!saosaita shi nayi da kyau na ciro nonon da dama nurse ta riga da ta wanke man shi na miqa mashi,ikon Allah kamar yana jira kuwa ya kama a hankali yana sha,hakan yasa nai zugudi ina jin duniata na samun mazauni cikin tashi sabuwar duniyar,take yanke kuma na riqa jin anya zan iya hakura nabar shi?
Banyi aune ba naga mutum a kaina,bansan ma ya shigo ba,may be saboda nayi niisa ne wajen kallon babyn da mamakin son da naji inaa mashi yaqi ya sakeni.
“Kema kinajin me nake ji ne game da Babyna?”
Bansan lokacin da na buga tsaki ba,wai inbanda iskanci sai yariqa cewa babyn shi babyn shi,sai kace shi haifa man d’an.
“Ya za ai inji abinda kakeji tunda daga sama ya fado.”
Nabashi amsa kaina tsaye ina huhhura hanci,lokaci guda ina qoqarin maida mamana ciki riga,ah toh don banga dalilin da zan tsaya gardin kawai na kalle mani qirji haka nnan siddan ba.
Girar shi guda ya d’age,kafin nan yace….
“Excuse me,what does that mean?”
Cikin qunquni nima nabashi amsa.
“Shafa kaji.”
Dariya yayi lokaci guda yana mai girgiza kai.
“Karki damu nasan meye matsalarki,yanzu miqo man yarona inji dumin shi.”
Ai bansan lokacin da na hayayyaqo mashi ba ina zuba masifa.
“Dallah malam ka saurara man,zaka bi ka isheni akan wannan abun,toh ai abinci yake ji kana iya sarara man haka nan.”
“Ohhh really?”
Wannan karon kama haba yayi gami da riqe qugu yana kallona with some kind of expression.
Komawa nayi baya ina hura hanci,yoooh iskancin banza har ni za a gaya wa d’a,dan da ni nai gwagwarmaya da dawainiyar abuna,amma yake neman yi mani kafidiri da gwalammaso akan shi.
“It seems something is wrong with your head,inajin i should clear your doubt.”
Juya idanuwa na nayi ina gyara zaman babyn akan hannuna.
“Whatever”
Anan ne naga ya sakaya fuskar tashi da serious face,ni dama im more dan serious,don tsakanina har ga Allah haushi yake bani,hakan yasa nima na sake tsuke fuskata ina harare harare.
“Ki shirya na riga na siya mana tickets,gobe zamu bi jirgin qarfe hudu na yamma zuwa Nigeria,daga nan sai kiyi wa Mammy bayanin yanda kika samu yaro.”
Ji nai cikina ya hau juyawa,a hankali kuma saiga gumi yafara karyo mani,me kenan?yana nufin ya manta da alqawarin da yai mani?meyasa zai ci amanata haka?innalillahiwainna ilaihirraju’oon,cikin tashin hankali nace
“Amma ba haka mukayi da kai ba,meyasa zaka karya alqawarin da kaimani?”
Wata harara ya wurgo man.
“Toh me kike so in maki Ni’imah?i thought yanzun nan kika gama nuna mani d’a naki ne ba nawani ba?”
“Kayi hakuri ba nufi na ba kenan.”
Nabashi amsa muryaata a sanyaye,lokaci guda inajin qirjina na nauyi,shin ta ina zanfara rayuwa ba tare da babyna ba?inajin mutuwa zanyi,take hawaye suka fara gangaro mani na fara rera kuka.
“Kinga its okay,na menen duk wannan kukan?wannan wani decision ne da ke zaki yanke wa kanki shi,ni abinda kikace shi zanyi and you know that.”
Nasan me hakan ke nufi,hakan yasa na sake bude maqoshi ina gabza kuka,wannan karon majina ma ta dade da yi mani sallama,ga babyn na kama na naniqe ina faman kuka,inason babyna,ta yaya zanfara denying din shi?
“Well the choice is yours kamar dai yanda na fada maki tun farko,me kikace?”
Fuskar Mammy ce tai man shigar burtu xikin zuciya,na hango irin masifa da jalalar da zan shiga,a yarinta ta a sai na riqa ganin ai gara dai in hakura da babyn,tunda gida daya zamu zauna sai in riqa boyewa ina bashi nono ba tare da sanin kowa ba,daga haka zan rayu da shi cikin lumana ba tare da qima ko mutuncina sun zube ba,hakan yasa cikin qwarin guiwa nace mashi
“Don Allah nidai ka riqe man alqawari karka bari Mammy tasan ni na haife shi,please Yaa Mukhy.”
“Case closed!so it shall be Hayatiey.”
Ajiyar zuciya nayi ina share hawayen idanuna,sai naji kamar ina dan samun relief hakan yasa na muskuta a hankali domin gyara zamana,
“Kawoshi in riqe maki shi.”
Da kamar ba zan bayar ba,amma sai na hakura na miqa mashi mussamman dana tuna deal din dake tsakaninmu.
Bayan ya amshe shi ne ya sanyashi a qirjin shi yana lumshe idanu,ina hango yanda labbanshi ke motsi a hankali,bansan me yake cewa ba,bankuma damu da insani ba,nidai yanzu babban burina a dunia shine kar Mammy da sauran jama’ar gari su gane nice mahaifiyar jaririn nan,duk kuwa da azababben son shi dake bin lungu da saqo na jikina.
“Go back to sleep Hayatiey,tomorrow we have a long journey ahead.”
Na tsinto muryarshi a gefen kaina,yayin da hannunshi guda ke rungume da Babynmu,dayan kuma yama shafa sumata,lumshe idanuwa na nayi yayin da wani bacci mai nauyi yai gaba da ni.**
Daga nan na dora mata da yanda muka baro america zuwa nigeria,yanda na riqa copping, yanda na riqa fama da al’amura masu tarin tsauri,daga nan kuma na sanar da ita yanda nasan asalin ko ni din wacece,ashe ba Sulaimanu Dambatta bane mahaifina ba,ashe Ammyna zalunta na tayi ta hanyar samar dani,ashe hanyar da aka samar da nawa d’an nima ta nan aka samar dani.+
Zuwa yanzu kuka yaci qarfin ta yayin ta zo qarshe wajen baiwa Ammyn labarin ta,zuciyarta tai mata nauyi a karo na barkatai cikin rayuwarta,a yayin da al’amuran ke sake sabunta kansu cikin idanuwan ta,ba shakka ita din tana cikin jarabawa da kuma gararin rayuwa.
Tunda ta fara bata labarin Ammyn ke riqe da hannayen ta,kuma zuwa yanzu da ta gama bata labarin tana mai cigaba da wani irin kuka mai ciwo batai qoqarin hanata ba,bata hanata ba domin babu amfanin hanatan,ko banza tanajin qila fitar hawayen su rage mata wani kaso kadan na daga nauyin da zuciyarta ke dako,ba shakka wannan yarinya taga iftila’in rayuwa,taga jalala a mafi qarancin shekaru irin nata.
Kwarai tayi namijin kokari waje ganin ta danne nata kukan,sai dai hawaye da suka kasa dena fitowa daga kwarmin idanuwanta,can qasan zuciyyarta kuma ta riqa jinjina girman labarin Ni’iman,ta riqa auna shi bisa mizani na hankali,sosai takeso ta yarje wa kanta yanda qaddara mai muni irin wannan zata afkawa qanqanuwar yarinya irin wannan.
“Astagfrullah!Astagfru’llah!”
Ta hanzarta neman gafarar ubangijinta,domin kwarai tasani babu ta yanda Allah baya jaraba bawan sa,koda bawan kuwa yau aka haifeshi,ga qaramin misali nan kuma bayyananne,shi yanzu Fawad ba samar dashi akai bata hanyar aure ba?a yanzu bashi da masaniya ko ikon kokawa samuwar tashi a banqasa,duk kuwa da cewar hakan ba zai canza cewar tashi qaddarar kenan ba,qwarai qaddararshi kenan wacce ke tafe da sanadi,mahaifin shj kuwa shine sanadin kafuwar tashi qaddarar.
Sai da tayi kukanta ma’ishi yazamana yanzu babu abinda yai saura sai qananan jawaye da ajiyar zuciya kana Ammyn tai qarfin halin bude bakin ta da yai mata nauyi tace,
“Ni’imah labarinki,labarine mai tarin girma ,tausayi,da kuma abin mamaki,and ba zan boye maki ba ya tabani fiye da dukkan wani abu da ya taba gifta duniyata,na tausaya maki kuma ina kan tausaya maki kwatankwacin tausayawar da uwa zatai wa d’anta.”
Ta numfasa kana ta cigaba,
“Abu na farko da zanfara fada maki shine,Ni’imah kiyi hakuri,kiyi hakuri da yanda rayuwarki ta juya cikin dan qanqanin lokaci,ki kuma dauki hakan a matsayin wata qaddara daga cikin qaddarorin da Allah ya wanzar ga duniyarki,nasani,nasani kwarai mutane mafi kusa dake suntaka rawa wajen bata duniyar ki,sai dai inaso ki sancewa rayuwarki bata baci ba,rayuwarki bata gurbata ba matuqar zaki dena duba wadancan abubuwan ki fuskanci abinda gaba zata haifar maki.”
Ta sake numfasawa ba tare da ta jirayi jin wani abu ba ta cigaba…
“Ni’imatu ina so kisani cewa zan zame maki uwar da kika rasa,zankuma zame maki uban da baki da masaniyar wayeshi a ban qasa,zan zame maki yayun da baki taba samu ba,inkuma zame maki qannen da bakk da su,nayi alkawari in sha Allahu zan zame maki dangin da babu kamarsu,sai dai nima inaso kiyi mani alkawarin shafe babin waccen rayuwar da kikayi a baya,nasani ba abu bane mai sauqi,sai dai still inaso ki jajirce akan hakan kinji ko?ki manta da past dinki and focus on your future,ke yarinya ce qarama wacce take da tarin damanmaki a gaba in sha Allah,inaso ki manta da wani abu wai shi Mukhtar Gaya,ki fiddashi daga duniyarki gaba daya da duk abinda ya shafeshi,yin hakan kadai shi zai taimaka maki wajen fuskantar sabuwar rayuwar dake tafe tana jiranki.”
Ba tai kokarin hanata wani kukan da ta dade da sake farawa ba,hasalima kwanto da kanta tayi bisa kafadunta tana jijjigata a hankali.
“Yi kukanki Ni’imah,yi kukanki to your own satisfaction, saboda daga yau,daga rana irin ta yau inafatan bazaki sake kukan baqin ciki a rayuwarki ba,you deserve to be happy,and in sha Allahu da taimakon Allah zamu ida wannan nufin,but as of now yi kukanki Ni’imah,kinji ko?”
STORY CONTINUES BELOW
Girgiza kai kurum take,yayin da takejin wani abu mai girma ya toshe makogwaranta,ba shakka ko a yau Allah ya dauki ranta ba zata taba dena godewa karamcin baiwar Allahn nan ba,kalamenta sun debe kaso mafi tsoka na daga quncin da zuciyarta ke dako,ba shakka wannan babin qaddarar da yai sanadin hadata da Ammy ba zatai qasa a guiwa ba wajen godewa Allah ba,Allah yagama mata komi da ya sanyata a hannu nagari,lallai Allah abin godia ne.
“Ammy bani da kalamen da zan godewa karamcin ki,karamci da kirkin ki mai tarin yawa ne,kuma still bani da abinda zan biyaki da shi da ya wuce addu’ah,ina fatan Allah yai maki sakayya da aljannar firdausi,nagode da dukkan qaunarki gareni Ammy,nagode da karamcinki,nagode da kuma yarda dani da kikai,nagode Ammy,nagode….”
Hannun Ammyn da ya dafa mata baki alamun tai shiru ya sanyata yin shirun tana mai sunkuyar da kanta a kari na biyu.
“Ni’imah godiyar ta isa haka,sai dai kisani d’a na kowa ne,haka zalika babu wanda ya girmi jarabawar ubangiji,ki kwantar da hankalin ki kicigaba da kula da yaronki kinji ko?inaso ki cire duk wata damuwa a ranki,ki manta da past dinki and just focus on your future,you have a lot on your bucket list kinji ko?da yardar Allah zaki zama abin kwatance cikin al’umma.”
A yanzu ne take sake jinjina mutunci da karamci irin na mutanen katsina,ba shakka har bayan ranta ba zata taba dena godewa karamcin da ta samu daga mutanen ciki ba.
Daga haka Ammyn ta umarceta da ta tashi ta shiga toilet ta wanke fuskar ta,kafin nan kuma ta sanyata tai mata alkwarin cewa zata manta da komi ta fuskanci sabuwar rayuwar da zata fara,take kuwa tai mata wannan alkawarin,ai tanajin zuwa yanzu babu abinda matar zata nema a gurin ta ta gaza yi mata shi,matuqar tana da iko kuwa.
Fitowar ta yayi daidai da tashin Fawad,hakan yasa Ammyn ta umarceta da ta zauna ta bashi nono,zaman ta babu dadewa ta sake tsinkayo muryar Ammyn a lokacin tana shirin fita daga dakin.
“Yawwa Niimah banaso inji ko da wasa kinbawa wani labarin nan naki kinjiko?and regarding Fawad ko da wasa banaso inji kin fada ma wani cewa ba dan sunna bane,a barshi a matsayin ke din bazawara ce,kamar dai yanda kowa ya zatan cewa rabuwa kukai ke da mijinki inaso ya zauna a haka,kar inji kar ingani kinyi kasadar fada ma wani cewar baki taba aure ba kin jj ko?”
Da sauri na daga kaina gami da tabbatar mata da zanyi duk abi da ta ce din.
“Yanzu ba zaki gane dalilin da yasa nai haka ba sai nan gaba,inafatan kin fahimceni?”
Ta sake tambayata.
“Na fahimta Ammy,in sha Allah zaki sameni cikin masu jin maganarki.”
“Yawwah Ni’imah,nima nagode kwarai da samunkj cikin zuri’ahta,yanzu dai kigama shayar da shi ki fito parlour ku gaisa da Daada,tun dazu naji shigowarta,yanzu ni bari nayi gaba in kin gama ki sameni a can.”
“Toh shikenan Ammy ,ganinan zuwa in sha Allah.”
Sai da ta jefeni da murmushin da sam baka raba fuskarta dashi kana ta fita,a hankali nabi bayanta da kallo yayin da na riqa tuno fuskar tawa mahaifiyar,a lokacin kuma na riqa jin kamar ta cancanci inyafe mata,ko babu komai mahaifiyata ce,duk kuwa d acewar har yanzu bani da masaniyar dalilin da yasa tai hakan.
***
Kaduna Nigeria.
Dukkan su suka bi bayanshi da kallo bayan yabar falon,maganar gaskia kowa na matuqar tausaya mashi,idan ka debe Mammy da idanunta suka riga da suka rufe sai da taga yiwuwar auren,auren da take ji a jikinta shine silar samuwar farin cikin d’anta,sai dai ba ta sani ba,wannan auren shine mafari,ko kuma ince silar rugujewar al’amura masu yawa.
“Mammy anya anyi wa Mukhy adalci kuwa?for goodness sake he is too young for all this tantrums.”
Adda Bilkisu ta furta cike da jimami bayyananne,sai dai Mammyn ko kallon ta batayi ba,hasalima tsaki taja gami da miqewa tsaye tana shirin barin falon,me kuma ta tuna sai ta ja ta tsaya tana duban Addan sheqeqe.
STORY CONTINUES BELOW
“Dakyau Bilkisu,dakyau!har ni zaki duba ki fada wa abinda ya kamata da be kamata ba?adalcin banza da wofi kike magana akai,wai ni tsaya ma tukunna,akwai wani adalcine da ya wuce wannan?aure nayi mashi fa Bilkisu,aure nayi mashi ba lasisin zaman dadiro na qulla ba kamar yanda waccan shegiyyar yarinyar tasa sukayi a baya,ai ni kam dai Allah ya isa tsakanina da Ni’imah,ba zan taba yafe mata ba.”
Baki sake Addan ke duban Mammyn,zuwa yanzu tanajin bai kamata al’amuran Mammyn su cigaba da bata mamaki ba,duk da dai tasani wannan sabon baqin halin da ta ara ta yafawa kanta ba hanya mai billewaa bace,sai dai duk da haka mamakin Mammyn ba zai daina kamata ba,ta kan rasa yaushe al’amuran nata suka giga haka.
“Mammy ba nufi na ba kenan,ku fahimceni please,what im trying to say is that,saboda Allah farin cikin Mukhtar should be your first priority, Mammy ku dubi Mukhtar,just look at him Mammy,cikin kwanakin da basu gaza goma ba dubi yanda ya koma,dubi yanda ya canza,haba Mammy where is your motherly love?inaji maku tsoron yin abinda zai ja maku cizon yatsa,Mukhtar is not into this girl Mammy,duk da yace ya amince wallahi Mammy ku kunsan hakan bai kai zuci ba,haba Mammy ku riqa reasoning mana.”
Wannan karon Mammyn bata ce komi ba,kawai kallon Bilkisun take tanajin tamkar ta maketa,wai ita kam wadanne irin yara Allah yabata masu kafirin iyayin tsiya?na menene yarinyar da ta haifa da cikinta ta tasa ta gaba tana tsara mata abinda ya kyautatu da wanda be kyautatu ba,ashe har anzo wannan qarnin?1
“Tashi ki fice kibar man gida Bilkisu.”
“Amma Mum…..”
“Ki rufe man baki banson ji,just get out of my house right now Bilkisu.”
Zata sake magana Adda Bena da ke gefenta tun dazu bata tsomaa masu baki ba ta dakatar da ita ta hanyar rufe mata baki.
“Do as she said please,karki sake cewa komi.”
Cewar Adda Benan tana girgiza kai,lokaci guda Bilkisun ta miqe gami da saba jakarta ta figi key din motarta dake saman center table ta fice ba tare da ta sake cewa komi ba,al’amarin da yasa Mammyn tabi qeyarta da harara.
“Shegiyar yarinya har ni zakiy ma waazin qarya.”
Ta furta yayin da take sake yun kwafa,kana lokaci guda ta juya ta nufi hanyar dakinta,yau kam yakamata ta huta,duba da irin gajiyar dake tattare da ita tun jia da aka daura auren Mukhtar din da Fadwa bata jin ta samu sukunin hutawa,so take zuwa gobe in ticket din da ta siya masu yafito su tattara su bar qasar,tana da tabbacin barin su qasar zuwa wani muhallin zai taka rawar gani wajen sake qulla shaquwa da soyayyar da yake ikirarin baya yi ma Fadwan.
“Mai shegiyar qaryar tsiyah.”
Ta furta a qasan ranta yayin da take dora haqarqarinta saman gadon ta,ita har gobe bba zata taba yarda Mukhy baya son Fadwa ba,tafi ta’allaka iskancin shi da ganin Ni’imah da shegen dansu da yakeyi,toh yanzu babu su,dolen shi ya haqura ya rungumi er matarshi mai son shi.
Bata damu da sanin inda Fadwan ta shuga ba,tafi ta’allaka hakan da qila tana can tana idasa shirin tafiya,ko kuma itama har yanzu baccin gajia take,duk kuwa da cewar ba wai biki akayi ba,daurin aurene kawai da hada tsirarun mutane,sai er qaramar walimar cin abinci da akai anan harabar gidan nasu,A haka bacci mai nauyi yai awon gaba da ita.
***
A hankali ta tura qofar dakin nashi,dama ba tai tsammanin samun shi yana bacci ba,duk.kuwa da cewar bayan la’asar ne,kwance yake saman sofa din dake cikin dakin shi yayi rubda ciki yana kallon wani abu mai kama da hoto,ilai kuwa da ta matso kusa hoton Ni’imahn ne da Fawad wanda ya daukesu a gadon asibiti bayan da ta haihu,yau dinnan da safe yaje aka wanko mashi hoton daga wayarshi akai mashi qaramin enlargement da ya qawatu cikin wani golden frame mai kyawun gaske.
Shigowarta bata sanya shi fasa abinda yake ba,hasalima tunda ya dago yai mata kallo daya bai sake ba,cigaba yayi da kallon mutanen da bugun zuciyar shi na tafiyane da so da qaunar su a kowacce daqiqah,ga kuma tarin kewar su da suka taru sukai mashi rubdugu,kwarai da gaske ko da wannan kadai Allah yabarshi yaji a jikin shi.
STORY CONTINUES BELOW
“Amma dai kasan hakan baida kyau ko?how could you be staring at this idiot while im here standing in front of you Mukhtar?gaskia da sake!”
Dariya ta bashi qwarai,amma yai kokarin daqile dariyar,lallai yarinyar nan ba qaramar er iska bace,bata san gaba dayanta tarata yake ba,amma sannu a hankali zai sauke mata haukan dake kanta,hakan yasa ya dauki frame din gaba daya ya rungume a qirjin shi,domin dai mutanen nan biyu dake jikin hoton su kadai sukai mashi saura a duniyar shi,duk kiwa da cewar bashi da masaniyar inda suke a halin yanzu.
A fusace ta zura hannu ta fizge frame din,ba tare kuma da ta saurari komi ba ta daga shi dubi saitin bango ta maka shi da bangon,abinka da glass ji kake tusssss,ya tarwatse gaba daya,tana ganin haka ta koma gefe tana huci,domin dai ashirye take da duk wani abu da zai kawo wa zamanta da Mukhtar din cikas,da da yanzu ba daya bane,yanzu matarshi ce ita,matar sunna,saboda haka bata ga dan kan abun uban da ya isa yakawo mata iskanci ba a zamanta da shi ba,ko da kuwa shine.1
“Get out of my room Fadwah.”
Ta tsinkayo muryarshi a hankali,lokaci guda kuma idanuwanshi a rufe suke yayin da maqogwaron shi ke sama da qasa,kallo guda zakaiwa fuskarshi ka hango zallar bacin ran da ke kwance male male a kan fuskar tashi,sai dai hakan bai tsorata hajia Fadwa ba,hasalima masifa tafarayi akan cewar babu inda zata tunda dai ai itama yanzu tana da iko da dakin,ko ya manta cewar yanzu ita din matar shi ce ta sunna.
“Don’t let me repeat myself,wallahi billahi idan kika bari nataso zakiyi danasanin sanina a rayuwarki,just get out of my sight.”
“Mukhtar babu inda zani,hasalima nan zan kwana,surutunka babu abinda yake mani,you better let me be.”2
Ba tare da ta sake saurarar shi ba ta fada bandakin shi,bata damu da ta sanya key ba ta hau tube kayanta ta shige cikin shower, yau ko da ubanwa yake yawo sai yazo sun darji soyayyah,abunda ta dade tana muradi,and tafi kowa sanin wani irin mutum ne shi,duk da yasha subucewa trap dinta ba sau daya ba ba sau goma ba,takan rasa shin menene aibunta da ko hannunta bai taba shaawar riqewa ba,duk kuwa da cewar tasha kamashi rungume da yanmatan shi ko friends din shi a school,amma ita ko oho,hasalima nunawa yake kamar ita din bata kai matsayin da zaa kulata ba.
“Zaka gane shayi ruwa ne inkazo hannu.”
Ta furta hakan a bayyane,sai dai bakinta ne ya rufe ruf lokacin da tai ido biyu dashi tsaye a bakin toilet din yana qare mata kallo,duk kurinta sai da gabanta yafadi,domin zata iya rantsewa yanayin shi yayi matuqar tsorata ta,sai dai kuma da gudu ta dake gami da basarwa tacigaba da abinda take gabanta na dan faduwa.
Ba tayi tsammanin qarasowa yayi ba,ta dauka fita yayi,sai dai jin wata iriyar damqa d ayai mata ya sanyata wata azababbiyar faduwar gaba,hakan yyasa da sauri ta juyo tana kallonshi kamar me shirin shigewa jikin ta,bai damu da tsiraicin ta ba,domin shi dinma he is half naked,dagashi sai qaramin short nicker,kafin ta san menene ya sunkuce yayo waje da ita,bai direta ko ina ba sai kan gadon shi,zuwa yanzu ta fara tsorata matuqa ainun,mussamman da ta dubi fuskar shi taga babu sauran rahama a cikin ta,menene maanar hakan?ta hau ja da baya tana jan duvet din gadon domin rufe jikin ta.
“Zan bakk abinda kika dade kina nema ne,may be you will be off me and stop getting on my nerves.”
Kambu,lallaima Mukhtar ya raina mata hankali,yana nufin a haka kamar mai shirin yin dambe ne zai bata abinda take so?ko da takeson hakan ai ba kamar yaqi take so al’amarin yatafi ba,babu wata soyayyah ko affection yake nufin zai amshi budurcin ta?infact ita she is not even ready,dama dai duk kuri ne irin nata.
“Lie down flat.”
Ta tsinkayoshi yayin da yake kokarin raba jikin shi da nickers din shi,baya tayi zuwa qarshen edge din gadon tana zare ido,wani yawu ne ta hhadiye mai bala’in tauri,ji kake quuuutttt.
“Whaaa….whaaaat are you doing ne haka Mukhtar?are you okay?”
Marin da ya dauketa dashi ya sanyata yin shiru tana mirgina kai,jitai ji da ganinta sun tafi hutun taqaitaccen lokaci.
“Bitch i said lie down flat,else i scatter the hell outtaf you.”
Wannan karon jitai muryar tashi takoma mata kamar ta horror,jikinta babu ta inda baya rawa,hakan yasa da sauri tayi abinda yace din tana kuka,hankalinta bai gama tashi ba sai da taga yana bare condom yana sanyawa,take ta sake tsurewa ta shiga rere kukan tashin hankali,toh da kuma taga ya dauko face mask ya saka sai yyaqara confusing dinta,takuma kasa tuna dalilin da zai sanyashi sanya face mack a yanayi irjn wannan.
Tunanin ta ne yya datse yayin da taji ya damqeta da qarfi,yakuma hada da gashinta ya riqe katamau,wannan karon gaba daya bakin ta wage ta riqa kurma ihu,bata gama sanin menene ainihin azaba ba sai da taji wani abu ya shigeta kamar anyaka ta da takobi,anan ne ta sake sakin wata qarar azaba da dukkan qarfinta,a banza domin wanda take ihun kukan don yaji baima san tanayi ba,domin airpods din dake manne da kunnenshi zai tabbatar maka da gaba daya sauti yakeji,ba tare da ya damu da komi ba yacigaba da tafiyar da ita cikin tsananin sauri da mugunta,bai damu da ihu ko yakushin da take mashi ba,sai da ya tabbatar da yakai inda zaije kana ya dagata yai wulli da ita ta daki fuskar gadon,kana ya miqe ya cire face mask din da air pods din ya nufi hanyar bayi a lokacin da yake kokarin sabule lalataccen condom din domin disposing.3
Tana nan a kwance kamar gawa har lokacin da ya fito looking fresh,sai da yagoge sumarshi dake digar da ruwa yakuma shirya cikin qananan kaya kana ya dubi inda take sheme tana cigaba da kukan azaba,jini jinin daya gani saman bedshit din yatuna mashi da yanda ya risketa,tabe baki yayi don bawai burgeshi tayi ba don yasameta a virgin,da sannu zata san ko shi wanenen,da sannu zata san baa shiga rayuwar shi ai wasan tamola da ita da sannu zatai begging for mercy and freedom,a lokacin da ta gama tabbatar wa kanta da cewar shi din mallakin Ni’imah ne ita kadai.
“Get your filthy ass off my bed wifey.”
Wannan karon batai mashi musu ba,domin bata shirya shan wata azabarba,domin ranta yagama bata dalilin da yasa yai mata haka,ashe shi din mugune har haka?ashe bashi da hankali bashi da tausayi?kanta ya kulle ta rasa wane irin tunani zatai,hijabin Mammy da ta shigo da shi ta yayi ba ta zura,tana daga qafa da qyar ta nemi hanyar barin dakin,saai dai muryarshi ta dakatar da ita,kafin kuma tai wani motsi har ya iso inda take tsaye tana sharar kwalla.
“How was it?”
Ta tsinkayo shi gefen kunnenta,yayinda yakama hannunta guda ya matse lokaci guda yana mai tsura mata idanu ,babu annuri akan fuskarshi,ita gaba dayama yanzu tsoron shi takeji,hakan yasa bakinta na rawa tace,
“It was,it was okayyy.”
“What?”
Yadaka mata tsawar da ta sata qanqame jikinta tana mai cigaba da kuka.
“How dare you called this shiitt okay?kina nufin bakiyi enjoying din shi ba?ohhh may be we have to go for a second round i guess.”
Da sauri tace,
“Mukhtar it was superb, it was amazing,don Allah kayi hakuri,na tuba.”1
“Shhhhhhhhhhh”
Ya matse mata baki yana harararta,
“In kin gadama kiba Mammy labarin abinda yafaru,you will be in for it,now get out.”
Da sauri taja qafafunta da take jin kamar an bubbuge mata su ta fice tana share kwalla,meyasa takejin tamkar nadama na shigarta?
Ni kuwa nace haba yarinya me akayi?ai ba ai komi ba,ba dai kince inba Mukhtar ba sai rijiyah?toh gaki ga shi nan,happy marriage life hajja Fadwa Hisham.
***
Well,Assalamu alaikum lovies,ya hakuri dani?nasani kwarai kuna hakuri dani,nakuma gode da qaunarku akan littafin nan.
Zanyi amfani da wannan damar infada maku cewar anan nakawo qarshen Hodijam part one,and part 2 din zaizo maku cikin watannin da ba su gaza biyu ba,koma ba zasu kai ba,i can’t actually say right now,amma dai abu guda nake so ku sani shine part 2 din zanyi releasing din shine when it is completed,ma’ana ba zan riqa update dai dai da daidai ba har sai nagama shi gaba daya.