HUDA YAR KARYA CHAPTER A
☁️☁️☁☁☁☁☁☁☁️☀
🐔 _*(HUDAH Y’AR KARYA….💁🏼)*_
🐤🐤🐤🐤🐤🐤🐤
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🐛
_Written By *ASY KHALEEL…✍🏻*_
Wattpad@asykhaleel
Facebook Group
Asy khaleel nvls grp
IG @asykhaleel
1️⃣-1️⃣0️⃣
Wata hadaddiyar motace ta paka a haraban wani shahararran hotel da ya amsa suna, (Hamdala hotel.)
Take kallo ya koma a kan masu fita cikin wannan motor, cikin nutsuwa Hudah ta bude murfin gaban motar tafito, yayinda classic Feedoh ta biyo bayanta sa’annan ta maida kofar ta datse hannunta rike da key car dinta,
Sannu a hankali suke takawa kai daka gansu kaga mata masu aji, ahaka suka doshi cikin hall din, har lokacin idanun jama’ar dake wajan akansu yake, ba kamar Hudah da tafi dauke masu hankali because yanda taci uban ado kai kayi zaton diyar merusau ce lolz (gwamnar Kaduna kenan.)
***
*TUNA BAYA*
HUDALLAH ‘yace ga malam Yunus, dattijon kirki wanda yasan darajan dan Adam, suna zaune a (unguwan dosa Kaduna) matarsa daya sakeenah suna kiran ta da Mamy, su biyar ne wajan iyayen su Hudallah itace babba kuma ita kadaice ‘ya mace sai kannenta maza su hudu, hakan yasa take samun kulawa akowani bangare awajan mahaifan ta, dukda mahaifinta ba wani mai karfi bane amma babu laifi suna cikin rufin asirin Allah domin,
Gidan kansu suke zaune, sedai ba wani babban gida bane daki ukku ne sai kicin da bayi da dan filin tsakar gida, sun sami tarbiya dai-dai gwargwado kasancewar M. Yunus mutum ne mai kishin addini, dangane da karatun ya’yansa yana iya kokari a bangare biyun nan ba’a barsu a baya ba wato Arabi da boko.
Lokacin da Hudah ta kare primary, gaba daya al’amuran suka wuyata wa Ma. Yunus, ahaka ya sama mata gurbin karatu a secondary skul don yana burin su sami ilmin zamani kodan halin rayuwa,
Asannan ne Mamy taso daurama Hudah tallah, Sam Baba yaki amincewa acewarsa wannan ai cibaya ne, da dai yaga ta matsa masa akan yaa kamata surinka sana’a, ga kuma kasuwancin nasa abin sai hamdala don harya kaiga dakyar ake samun na abinci hakan yasanya yabata damar ta yiwa su Huzaifa kannan Hudah kenan, tinda su din mazane da dan sauki amma Hudah kam yayi doka ko bayan ransa idan ta daura mata tallah beyafe ba, sedai ya amince data sakata wajan koyan sana’ar hannu, shi dinma awajan mace yar uwan ta ba shagon maza ba,
Haka kuwa akayi Mamy tafara kasuwanci kala kala wasu ana shigowa asaya acikin gida, wasu kuma ya’yanta maza ke fita dashi, Hudah kam tuni an kaita koyon dinki. Kasancewar akusa dasu akwai wani Babban plaza na wata shahararriyar seamstress, lokaci lokaci take daukan yara masu koyo, sai kuma ga Mamy takai Hudah bayan ta rufe amsar yara acewarta sai tayima wasu freedom don haka.
Kudi masu yawa, Mamy ta biya kafin ta amshi Hudah aikuwa su Hudah an maida hankali sosai, hakan yasa karatunta ya durkushe makaranta ya zamana yau aje gobe aki zuwa,
Ana cikin haka kwatsam M. Yunus ya tashi da amai da zawo yini guda yayi a hospital yace ga garinku nan.
*innanillahi’wainna’ ilaihirrajiun*
Ku biyo *KING ASY KHALEEL* danjin ya rayuwar Hudah zai kasance.😘
☁️☁️☁☁☁☁☁☁☁️☀
🐔 _*(HUDAH Y’AR KARYA….💁🏼)*_
🐤🐤🐤🐤🐤🐤🐤
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🐛
_Written By *ASY KHALEEL…✍🏻*_
Wattpad@asykhaleel
Facebook Group
Asy khaleel Novel’s grp
IG @asykhaleel
1️⃣1️⃣-2️⃣0️⃣
Tin bayan rasuwan M Yunus gaba daya al’amura suka sake cudewa su Mamy da yaranta, ada gani take duk ya barta da dawainiya wannan dalilin yasa bashi da damar yasata ko ya hana ta, magana kadan zeyi ta haushi da fada tamkar itace mijin badan komai ba,
Sai dan ganin d’an sana’ar da take suna haduwa su rufawa juna asiri, sai bayan ta rasa shi a sannan ne ta fahimci lallai ba karamin kokari Baba yake ba, ta gane cewa lallai rike gida sai namiji, amma dan rashin gdy irin namu na mata wani lokacin har namiji yafita yasan yanda yayi yakawo mana, a memakon musa hannu biyu mu kar6a muyi godiya ga Allah, sai mu raina watama sababi zata kama ita don bata sami yanda take so ba,+
Anan nake jan hankalin yan uwana mata da murinqa godiya da abinda Allah ya horewa mazajan mu, Allah ma yana cewa,
لإن شكرتم لآ زيدنكم
Ma’ana idan kuka gode sai Allah ya dad’a muku, Allah ka wadata mana zukatan mu ameen.
Haka dai rayuwan Mamy da ‘ya’yanta yacigaba da wakana basu da wani matemaki sai Allah, dangin M.Yunus da sukazo ta’aziya daga kauyen Zamfara, sunso su dauke mata nauyin wasu ya’yan, Mamy ta nuna Sam bazata bada yaranta akai mata kauye a zube su a gona ba maganar karatun su kuma ko oho, sunyi iya kokari akan tabasu koda mutum biyune, Mamy takafe akan Sam bazai yuwu ba, dan haka suka barta da yaranta, tin lokacin ba wanda yasake waiwayar su daga 6angaran dangin miji,
Awahalce Mamy tayi kwanaki arba’in dinnan na takaba, kasancewar batada daman yin sana’a sai wanda yaga Allah ya temaka masu, aifa tana fitowa ta fara kasuwanci ba kama hannun yaro, kama daga kansu omo, sabulu, kayan miya, kayan lashe lashe na yara kala kala duk saidawa take, yaro da babba a unguwan kowa yasan gidanta, har suna aka radama gidan waishi gidan (qwalama) tayi hakan ne domin su tsira da mutumcin su don Mamy mace ne wanda Sam bata jurewa quncin rayuwa, da wannan kasuwancin sukeci suyi sauran buqatu hatta karatun ya’yanta babu abinda ya canja, abangaran Hudallahi fa??3
Yanzu takai kimanin shekaru ukku a wajan koyon dinki, sosai take da fahimta har mamakin ta mentor dinsu take wanda suke kira aunty Munirah, Hudah tafi yawancin wa’inda suka rigata zuwa wajan fasaha don,
Babu kalar dinkin zamani wanda yake gagarar ta dinkawa, sedai dan gyara kadan da ake mata awajan yanka, hakan yasa tashiga ran munirah sosai don tana temaka mata ba kadan ba, shiyasa itama take dan yi mata ihisani in sunyi aiki tana sammata dan na kashewa, dakyar da gumin goshi Mamy tasamu Hudah ta zana junior waec, tin daga nan Hudah ta yakicar da makaranta mamy tayi juyin duniya akan ta daure takare secondary ta amshi certificate dinta, sam Hudah ta sharawa idonta toka tai watsi da maganar Mamy don ita ranta yafison dinkin nan burinta tadan kara gane wasu abubuwan aiyi mata freedom itama ta faracin gashin kanta, Mamy tana gani dole tasa ido don Hudah kafiyane da ita, sanin cewa koda ta matsa mata akan setayi tofa kudinta zata 6ata abanza, tasan halin Hudah tinda tace batayi tofa baza tayi abinda akeso ba dole kasa mata na mujiya👀
*_Wannan kenan._*
*WACECE HUDALLAH*??
Saiku kasance tareda *KING ASY KHALEEL* danjin cikakken tarihin..
*HUDAH YAR KARYAH* 💁🏼☁️☁️☁☁☁☁☁☁☁️☀
🐔 _*(HUDAH Y’AR KARYA….💁🏼)*_
🐤🐤🐤🐤🐤🐤🐤
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🐛
_Written By *ASY KHALEEL…✍🏻*_
Wattpad@asykhaleel
Facebook Group
Asy khaleel Novel’s grp
IG @asykhaleel
2️⃣1️⃣-3️⃣0️⃣
*HUDALLAH*
Yarinya ce wanda bazata wuce shekaru goma sha bakwai, tsayawa bayanin suffofin Hudah wannan zai zama cin lokaci, kai tsaye zamu iya cewa Hudah masha Allah, ajawan halitta duk wani abu da akeso ga ‘ya mace Hudah ta hadasu, abu dayane ya hanamu karyata malam bahaushe dayace,
(mutum tara yake bai cika goma ba)
Wannan abu shiya tauye Hudah harya hana asalin sahihin kyawun halittar ta ya bayyana wato quncin rayuwa, ma’ana rashin wadata,+
Hudallah yarinya ce ma’abociya kwarjini da farin jini duk wanda ya zauna da ita koda na yini gudane nan da nan yake jin tashiga ransa, tin tana karama ta kasance yarinya maison ado da kyalkyali, yar qarama da ita tasan tashafa wannan ta liqa wancan, abin nata har yakai ga Mamy bata da damar aje kayan kwalliya afili, in kuwa tayi koskuran ajewa yanzu Hudah zata mamayeta tai kaca kaca dasu, haushi yayi kamar ya kashe Mamy, tayi bugun harta gaji, Baba kam lallashin ta yake da cewa tayi hakuri yarinya ne kuma daman su mata ai da ado aka sansu, don haka ya fara sayawa Hudah kayan kwalliyarta ita kadai tayi yanda takeso, atakaice dai Hudah tin tana karamar yarinyar da bata wuce wasan kasa ba, karyane kaganta ka raina mata, mace ko namiji kowa sonta ake don kuwa ko kaine
( hasidin iza hasada)
dole kaganta ka yaba koda kuwa a cikin zuciyar ka,
Wannan hali ko ince dabi’a nata yana matukar burge iyayenta sosai, dan Hudah sam bata shiga cikin kazaman yara sa’an ninta, sai ma kyamarsu da takeyi, abunda iyayenta basu gane ba shine, acan kasan zuciyar ta tana da wani ra’ayi ko kuma sha’awa, ita dai a rayuwa babu abinda yafi burgeta kamar rayuwan ‘ya’yan masu kudi, dik inda zataga majiya dadi ita dai suna burgeta tanajin inama iyayenta masu kudine, hatta a makaranta in kinga Hudah tana haba haba da mutum tana yashe hakora to taga alamun sassauci ga yaro, misali tana ganinka a koda yaushe cikin tsafta kuma kana zuwa da kayan lashe lashe irin na yan gayu, lallai yanzu zaku kulla abota da Hudah,
Abun nata yayi kamari a cikin zuciyar tane lokacin da Mamy ta kaita wajan Munirah, nan fa Hudah tafara karo da ‘ya’yan masu kudi wa’inda iyayensu ke kawosu don agwada su, ta fata ganin fitattun yan mata masu ji da kansu, kasancewar Munirah gwanace acikin teloli kuma duk yawancin customers dinta masu kudine irinsu takema dinki, wannan dalili yasa Hudah ta zabi zaman plazan Munirah akan karatu, akwana atashi Hudah tana kara wayo tana qara sa buri aranta, har yakaiga ta fara tsarawa kanta irin rayuwan daza tayi da irin wa’inda suka canci tayi rayuwan dasu *wannan kenan.*
Nidai nace..
Anya kuwa HUDALLAH?
Anya haqanki zai cumma ruwa?
Shin mutum ya isa yakai kansa inda Allah be nufeshi da zuwa ba??
To anan dai marubuciyar take tunatar daku iyayen yara!!
Musan cewa kananan yara wa’innan da kuke gani amanarsu Allah yabamu, kuma tabbas saiya tambayemu akan tarbiyan da mukai masu, don haka.
Ya zama dole musa ido sosai akansu dolene mu lura da yanda suke tafiyar da rayuwansu domin wani yaron, yana tasowa ne da halin sa mekyau ko akasin sa,
Yake yar uwa kisa ido bisa tarbiyan ‘ya’yanki, idan kika lura danki ko yarki nada wani hali wanda kin tabbata idan wannan hali yabishi har girma, lallai bazai kaishi gacin nasara ba, to anan abinda ya kamaceki shine,
Tin wuri ki dage da roqa masa Allah kada ki aje abun amatsayin yarinta, ki daure kina tashi tsakiyar dare kina kai kukan ki ga Allah kuma ki yawaita yin sadaqa da nufin Allah ya dubeki ya biya miki bukatarki ya canjawa danki wannan mugun hali, ya kuma shirya miki su bisa dai-dai din hanya, wallahi matukar kika rike wannan kika zamo uwa tagari mai yiwa ‘ya’yanta wannan adduar insha Allah koda an hukunta danki sai yayi takadaranci tofa abin zaizo dasauki sosai, kai da yardan Allah bama zai gagareki ba yar uwa je ki gwada!.
Sosai iyayen yara suna babban koskure bisa kola da tarbiyan ‘ya’yansu, walh wata uwar batama kaunar ace ga laifin danta, gasunan acikin gari, kiga karamin yaro ya taso da muguwar bakar zuciya tamkar ya kashe kansa, tsakanin sa da yara yan uwansa kuwa sai zalumci, yau ya cuci wannan gobe ya cuci wancan, amemakon ke uwa kinga haka, ki dage dayi masa nasiha da addua ba dare ba rana, kuma lokaci lokaci kina bada sadaqa ga manyan malamai don su tayaki addua, a a sai kiji ana cewa yarinta ne kowa da irin nasa, wanima abunda yayi ai ba’a tona ba, gashi yanzu angirma an bari, dan haka shima bari zeyi, kai wata uwarma wlh kai tsaye zatace ai da’ace shi ake cuta gara shi yayi, iyaka dai in anzo in bada hakuri, amma miye amfanin raganci kullum yaro yazo maka da kuka, to bari kiji uwar san zuciya,
Irin sune da zarar yaro ya fara zama matashi saiya zama dan sara suka, gasunan muna gani acikin gari qananan yara yan 15 to16yrs sune suka addabi mutane da soke soke, sai alokacin ne hankalin iyaye ke tashi aita wani fade fade, basu gidan boka basu gidan malam, tana fadin a temaketa wane ya fara bin yan sara, Hmmm Hajiyata sai yanzu?
Sai yanzu bayan kin baro shiri tin rani?
Eh yanzu fa dole hankalinki ya tashi tinda kinsan danki bashi da garantin zega gobe, rayuwansa tana cikin hadari, kullum cikin dayan biyu yake, ya kashe ne ko kuma shi a kashe shi, to mudai.
Ya Allah ka shirya mana zuria ameen.
Ku dai bini sannu ahankali danjin cigaban lbr, luv u all my followers, voters n readers😍☁️☁️☁☁☁☁☁☁☁️☀
🐔 _*(HUDAH Y’AR KARYA….💁🏼)*_
🐤🐤🐤🐤🐤🐤🐤
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🐛
_Written By *ASY KHALEEL…✍🏻*_
Wattpad@asykhaleel
Facebook Group
Asy khaleel Novel’s grp
IG @asykhaleel
3️⃣1️⃣-4️⃣0️⃣
Duk wani dan abunda Hudah tasamu a wajan aikinta iyakacin ta sanar da Mamy ta fatar baki, amma ko ganinsu bata bari tayi, gabaki daya a kayan kwalliya suke tafiya bama isarta suke ba, dayake ba ko wani lokaci Munirah take basu kudi ba, ahaka har tacike 4yrs tana koyon aiki, wanda a iya ka’idan plazan lokacin ne take yaye rayan aikinta indai sun cike shekaru hudu (4years,) a lokacin ne Hudah ta matsa wa Aunty Munirah da maganar yaa kamata itama ta sallameta, ga abokan aikinta wa’inda tama rigasu zuwa duk tayi masu freedom, sedai Munirah tace Hudallah ki kara hakuri ina sane dake,
Sosai take tunanin rabuwa da Hudah don tana amfanuwa da ita ba kadan ba, awannan lkcn yawancin customers dinsu duk kawayan Hudah ne, gashi a dokan plazan yaran aikinta basu da daman cin gashin kansu agaban ta, dole komin iyawanka ka jira har tayi maka freedom,
Duk aikin da aka kawo nata ne koda kuwa ta hanyar Ka aikin ya samu, sedai ta kanta idan tai ra’ayi takan dan sammasu na kashewa, +
Hudallah tayi sabo da ‘ya’yan masu kudi sosai a plazan Munirah, duk yarinyar dataga alamun tana wankuwa dakyau Hudah batajin kunyar cewa ta bata number dinta tana santa da kawa, a nanne suka hadu da classic Feedoh inda suka kullah abota mai ban sha’awa wanda har yayi sanadin kulluwan zumunta a tsakanin iyayen su,
Classic Feedoh
‘Ya ce ga Alhj Lawal, babban ma’aikaci ne a gwamnati, suna zaune a Malali Lowcost Kaduna, Alhj Lawal mutum ne mai tausayin nakasa dashi ko kadan abun hannun shi be rufe masa idoba, hakama matarsa Hajiya Hafsat, mace ce maison jama’a suna kyautatawa makusantan su, ganin shakuwar dake tsakanin ‘yar su da Hudah yasa Momi ta aje lokaci ita da yaranta suka kaiwa Mamy ziyara.
Tin da Dad din Feedoh ya gane Hudah marainiya ce yake temaka masu har yakai ga sunzama tamkar yan uwa, lokaci lokaci Mamy takanje gaishesu daganan tayi gdy bisa kokarin da Dad keyi dasu,
Tsakanin Hudah da Feedoh Shakuwa ce maiban sha’awa, duk weekend suna tare da juna, in suka hadu basa kaunar abun dazai kawo rabuwansu, tahaka dai kawancen nasu ya sami asali, sedai kuma kash.
An samu banbancin hali a tsakanin wa’innan amienai, kasancewar ita Firdausi tana maraba da duk wani wanda ya furta mata Kalmar so, sam babu ruwanta da kallon na wuce da ajin wance, mai kudi ko talaka duk abu daya ta daukesu, shiyasa ma Hudah batasha wuya ba wajan kulla abota da Classis Feedoh. Feedoh ta fara karantar halaiyar Hudah ne ganin yanda take nuna halin ko in kula ga samari, ko alama Hudah bata sauraron masoyanta, inba dai ta gyalla ido ta hango abun data hango ba atare dakai, wato kudi,
(masu gidan rana)
Wani lkc takanji haushin Feedoh in taga tana amsa sallamar samarin dake tsayar dasu suna akan hanya, acewar Hudah wannan ai zubar masu da aji takeyi, haba tarasa wa’inda zata tsaya dasu sai wa’innan kananan qwarin, girgiza kai Feedoh tayi hade da murmusawa tace my Hudancy kenan matar manya,
Allah dai yanuna mani auranki lfy, harna hangoki hakimce a gidan mulki, dariya sukayi tare da bama junansu hannu.
Sosai Feedoh tazage dan ganin ta fashintar da kawarta hakan bedace da ita ba, ai baka yawaita burin duniya aranka bakasan ya rayuwa zata zo maka ba, Hudah sedai ta amsa da toh naji Hajiyata, haka suke gudanar da lamuran su babu maijin tsakaninsu, sedai dazaran Hudah ta kauce Feedoh tana kokarin dawo da ita hanya, ammafa ko kadan Hudah bata canja ra’ayinta ba, kusan duk wasu friends din Feedoh masuji dakansu sunyi sabo da Hudah, dazaran wani hidima ya samu kaman biki ko birthday party sai sun gayyaci Hudah don tana matukar burgesu, acewar su yarinyar tayine tako wani fanni, gata dakyau ga iya dressing uwa uba tsabar iya takunta da jan class don indai ba wanda yasan asalinta ba, ba wanda zaiyi zaton, wai Hudah ba yar wani mai fada aji bane a cikin garin kaduna,
*Sai kinyi Hudah yar karya👍🏻😛*
****
(Munirah tailoring shop)
Seda Hudallah
tayi 5years cikakku sannan Munirah tayi mata Freedom, inda ta hadata da shatara na arziki, don ita kanta Hudah tayi mamakin Aunty Munirah, sam batayi zaton zata mata adalci haka ba, a iya sanin Hudah Munirah tayi kokarin gaskene ta hadaka da karamin sewing machine, scission, da dai dan kayayyakin aiki masu saukin kudi,
Saiga Hudah da babban keke na wuta sabo fitikil, generator sabo dal da duk wani abunda tasan tailor yana bukata sai data hadama Hudah, aifa Hudah duniya sabuwa.
Hargida customers suke biyo Hudah da dinkuna, haka idan biki ya taso kawayanta suna mata hanyar samun aiki sosai, irin gown din amare da sauransu, shiyasa kullum tana cikin dinkin anko, masha Allah kudi Hudah take samu bana wasaba dan bata dinkin kasa da 5k, sedaifa data samu zata shiga market ta fatattako siyayyah, dik bikin da aka gayyaceta sai tayi anko, kuma komai set take hadawa, irinsu takalmi jaka mayafi su abun wuya komai to Match take hadawa ta yanda babu taron da zata shiga a raina mata,
Haka dai rayuwan Hudah yacigaba da tafiya masoya kam gasunan sunmata chaah, sedai anyi rashin sa’a ba irinsu Hudah ta tsara a rayuwanta ba, tadai yarda yau taci kudin wannan garan gobe ta wankin sha-aha-sha,
Kullum ita kenan tana wajan biki ko party, kai da abu yai abu Hudah sai ta aje ashobi amatsayin kauyanci, ayanzu tsarin datake kai shine,
Duk wani bikin daya taso tayi cancel din anko a tsarinta,
Haka kuwa tana kallo abokan karyan nata zasuyi ta buga-buga kowacce hankalinta baya kwanciya sai tayi anko,
Hudah sedai ta lafe da aiki yaimata yawa batada time din shiga kasuwa,
Sharewa dasu take sai ta kammala duka dinkunan mutanen data amsa, inta dai-daici ta cika jakarta taf da kudi, sai irin ana saura 2days afara events sa’annan zata shiga kasuwa,
Idan an fitar da atamfar 5k ne Hudah inta tashi na 10k take saya, haka in material sukayi ita saita sayi babban wanda aka fitar, sannan ta tsara masa dinki, maganar high hill, bag, costume, abun wuuuuuh,
Haka take fasawa cikin tsararrakinta tamkar gimbiya da kuyangunta, a wani taron ma Hudah takanfi amaryan hadewa hakan yasa yan mata suka fara tsanarta, shine silar lakabin da suke mata da.
*HUDAH ‘YAR KARYA*
Tin suna fada abayan idonta harya kai, ga da ga kawayenta ke kiranta da hakan, tayi masifa akan su bari bataso harta gaji ta hakura.
Ganin abun na Hudah bana hankali bane yasa Mamy tazo mata da shawarar ya kamata tariqa adana wani abun, indata daura da yar nasihanta na cewa,
“Haba Hudallah ya kike mance matsayinki ne, kefa marainiya ce yanzu idan hidiman auranki ya taso wa muke dashi wanda zai tsaya mana?
Nayi nayi dake koda dan adashin nan kishiga kin ki, ace dazarar kin samu kudi sedai ki tafi kasuwa ki kwaso kayayyaki, ke kadai akwatunki uku ciccike da kaya, wasu kayanma kin mance kalarsu kuma kullum kokarin kwaso wasu kikeyi, wannan ai shirme ne gara kodan kayan kitchen ki rika siya kina adanawa watarana zasuyi mana rana”
Budar bakin Hudah sai cewa tayi, “toh Mamy yanzu so kikeyi in ringa fita tsumma tsumma?
Ko kin manta ance gatan miji yafi gatan gara?
Nidai ki tayani da addua in sami irin mijin da nake so, bama iya kayan kitchen ba har dana bedroom duka da kudinsa za a hada, kinga kuwa gara in gyara kaina ina fita dagwasgwas kona samo miki maidan maiqo maiqo, koya kikace Mamyta?”
Murmushi Mamy tayi hade da girgiza kai tace, Allah ya nufa, dukda haka adai riqa sara ana duban bakin gatari,
Ayau su Hudah sun tashi da farin cikin kammala secondary school da kawarsu Feedoh tayi, kayataccen celebration sukayi anci ansha anyi farin ciki, da yammaci Dady ya damkawa Feedoh dan makullin motor, woww fadar murna bata baki, wajan Feedoh da kawarta Hudah, qanqame junansu sukayi Hudah tanajin tamkar ita aka baiwa motar tasan dai tasuce su biyu, yanzu kam dole a sake sabon taku💃🏼
Kusan atare suka koyi motor da Hudah dik sanda driver zai fita da Feedoh saita gayyaci kawarta Hudah kafin wani lkc sun iya, yanzu HK babu inda basu fita ba tare da anyi driving nasu ba,
Bikin kawarsu Humaida ne ya taso Hudah tayi dinkuna har taba uku lada, yayinda ita kuma ta fifita tata shigar, cikin tsadadden material suka halarci taron dinner da aka shirya anan Hamdala hotel Kaduna.
*_toh masu bibiyata kundaiji cikakken tarihin Hudah, yanzu kuma zamu garzaya Hamdala hotel dan ganin wace wainar ake toyawa._*
*Now shower me with love by voting n commenting* 😍☁️☁️☁☁☁☁☁☁☁️☀
🐔 _*(HUDAH Y’AR KARYA….💁🏼)*_
🐤🐤🐤🐤🐤🐤🐤
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🐛
_Written By *ASY KHALEEL…✍🏻*_
Wattpad@asykhaleel
Facebook Group
Asy khaleel Novel’s grp
IG @asykhaleel
4️⃣1️⃣
Guri yayi kyau sosai an kayata side na amarya da ango da flowers masu ban sha’awa isowar su kadai ake jira,
Isar su Hudah sun tadda Hall din a cike da yan mata da samari,
Waigen inda zasu samu wajan zama suke,
Can daga nesa Hudah tahangi space akusa da wasu yan mata, su biyu ne zaune agaban dinning table mai dauke da kujeru hudu,
“Woww Fee dearie kallo gefanki na dama ga space a wajansu mu karasa”
Hudah tayi maganar kamar mai rada tanama Feedoh nuni dasu ,
“A’a fa Hoo dearie karki kaimu inda za a mana kallon raini ko kuma amana korar kare, ki kalla yaran dakyau mana sonfi karfin mu daga gani manyan kai ne, ji mutanen dake tsaye suna neman gun zama amma ba wanda ya nufesu saimu, kalla snacks and juices dake shakare da table din gabansu ko ba a fada ba kinsan ba banza ba, maybe ma suna tare da guys nasu”
” Toh matsoraciya in zaki zauna kizo muje koma su waye ni wlh sunyi bala’in burgeni tin dana shigo dasu nayi tozali,
Shiru Hudah tayi nadan lkc tana kare musu kallo.+
“kutt gaskiyar ki Fee dearie zai yi wuya su mana kallon arziki, duba kiga su kansu kaman ba tare suke ba, wannan ta juya face wancan ta kauda kai, tsabar yanda ko wacce take ji da kanta yasa, ko irin hira tsakanin su babu, kai gsky fine chicks nan sunyi ba karya”
Su Hoo dearie manyan gari, suwaye sukayi da har suka fiki acikin hall dinnan?,
Sarkin kalle kalle, ke wlh kibi a sannu, ina miki tsoro kada wata rana ki kalloma kanki aljanu”
Muryan Ablah suka tsinkayo tadan jima a bayansu batare da sunsan da isowanta ba, dan taji duk abinda suke fada, rungumeta sukai suna daria, cikin murna Feedoh tace, “shiyasa nake sonki Ablah akwai fadin gsky , ina kuka shige ne sai raba ido muke bamu ganku ba, har wannan uwar hange hangen tanaso ta kaimu wajan da za’aci ubanmu”
Dariya sukayi tare da tafawa, “ai Hoo dearie ba sauki Allah dai ya shirya mana ita”
Cewan Ablah sa’annan ta jasu suka yi wajan friends insu,
Zamansu keda wuya, amarya da ango suka shigo. an gudanar da komai akan tsari. Anci ansha amarya da ango sun rausaya inda friends da yan uwa, suka tara masu kyaututtuka. sai fatan Allah basu zaman lfy, agurguje jama’a keta harramar tafiya don dare yayi, fitowa su Hudah sukayi sai raba ido take ko Allah zai sa ta sake ganin yan matan nan, gaba daya hankalin ta yana wajansu,
Har zasu shiga moto ta hango fitowansu daga hall din, daaam taji gabanta ya fadi ganin kyawawan samarin da suka sakosu a tsakiya, daga yan matan har guys din ko kai waye dole ka lalace wajan kallon su, duk wanda ka kalla kasan Allah yayi hallita a wajan, ga kamu sassaucin rayuwa wanda yanayin dressing da fatar jikin su kadai ya isa shaida, sosai Hudah ta susuce wajan kallon fitattun masoya, yanda suke takawa kamar masu tausayin kasa shi yafi komai tafiya da hankalin ta har suka wuce ta gabanta batare da ta daina kallonsu ba, take ta raina kanta wani sabon rashin godiya yasake dira mata azuciyarta,tana raya ashe duk shirme mukeyi villagers ake kallon mu,
Feedoh tuni ta dade da shigewa moto, ganin wucewan su yasa tayi kasa da glass din motar tadan leko da kanta,
“Toh Hajiya tunda sun wuce ai sai kizo mutafi ko in kama kaina”
tana fadan haka ta bushe da dariya harda dukan seat din kusa da ita tana fadin,
“ohh Hudancy Allah rabaki da wannan fitinan nan sha’awan. Gsky kanki akwai matsala”
Hudah kam kobi takanta batai ba, ganin sunyi sallama da samarin sun nufi inda suka paka motarsu, tayi hanzarin nufan inda suke da saurinta,
“Assalamu alaikum”
Atare Asy and Salheart suka waiwayo jin muryan dake musu sallama, kallon up and down cute salheart tai mata tawani yamutsa face kamar taga kashi, batare da ta amsa mata ba taci gaba da tafiya,
Murmushi Asy tayi sannan ta amsa da,
“Ameen wa alaikissalam, young lady hw r u?”
“Wlh am fine ina fata kema haka?”
“Lafia kawata meke tafe dake”
Asy ta jeho mata tambaya,
“Alheri ne my friend wlh tun da na ganku hakanan naji kun burgeni, zanso jin sunayanku idan babu takura”
Asy tadanyi murmushi, “sunana Asy Khaleel kawata kuma cute salheart”
Woww NYC names, ni kuma Hudallah, Asy zatai magana sukaji an saki wani wawan horn ba shiri suka dode kunnuwa,
“Haba cute miye haka zaki kashe mana kunnuwa”
Asy tafada tareda juyawa, da sauri Hudah tace number ki plss, agurguje Asy ta karanto mata batare data jiraba tace,
” byee”
“Owk bye bye friend, thanks 4 given me ur precious tym, we talk on phone” bye
Sai da ta adana lambar tajuya ranta fari sol tamkar tahadu da ‘yan matan aljanna,
Sosai ran Feedoh yakai kololuwa wajan baci, sedai ko alama bazata iya tafiya tabar Hudah ba, da tuni tasan inda dare yamata, yanda sukama Hudah shiyafi kona mata rai dan ta tsani wulakanci a rayuwa, shiyasa bata taba koskuran wulakanta mutum, wani bangaran koma tafi jin haushin Hudah ai ita take kai kanta don haka kome aka mata ita taso,
Seat din mai zaman banza, Hudah ta zauna, ganin yanda Feedoh ta murtuke face yasa ta rungumota
“Haba Fee dearie am sorry tawa, na tuba kuma daga yau nagama kalan kawaye tinda na hadu da Asy Khaleel, ta isheni ga kuma Fee dearie ta”
Figan motar Feedoh tayi bata ko saurari Hudah ba, suka fice daga hall din.
*KING ASY KHALEEL..* ❣️☁️☁️☁☁☁☁☁☁☁️☀
🐔 _*(HUDAH Y’AR KARYA….💁🏼)*_
🐤🐤🐤🐤🐤🐤🐤
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🐛
_Written By *ASY KHALEEL…✍🏻*_
Wattpad@asykhaleel
Facebook Group
Asy khaleel Novel’s grp
IG @asykhaleel
4️⃣2️⃣
Seda Feedoh ta fara sauke Hudah gida, sannan ta kama hanyan gidansu, zuciyar ta cike da fargaban abunda zata tarar saukin ta daya dady baya gari,
Direct Hudah tayi dakin ta ganin Mamy tayi bacci, da shigarta kayan jikinta ta sauya, izuwa na bacci tana yi hade da yan wake waken ta,
Bayan ta kammala taje ta tada Mamy dan ta sheda mata ta dawo,
Fada Mamy ta fara yi mata akan daren da tayi, Hudah najin haka ta fice tabar mata dakin tana kumbura baki,
“Duka ko goma batai ba shine wani dare yayi za a isheni da sababi ai sai kiyi tayi ke kadai”+
Abunda take fada kenan tana qunqunai harta isa dakinta,
Tana shiga ta datse kofar, ta juya ta haye gado abinta,
Da sauri ta janyo phone dinta dake saman drawer, nan take murmushi ya bayyana a fuskarta, tunawan da tayi yaufa tayi kasaitattun new friends, don harta rada masu suna Queen and star,
Da azama tayi dialling num din Asy sai kuma tayi tunanin ko basuje gida ba,
“karfa in cika zakewa taji haushi na”
Tafada a ranta, yanke call din tayi, ta fara aikawa Feedoh text naban hakuri tasan yau fada wajan Momy sai abunda hali yayi, Mamy ma maidan sauki tayi fada inaga Momy, wacce ko alama bata so ‘yarta tayi dare a waje.
Tana aika wa Feedoh text din, zuciyar ta ya gaza hakuri, nan take ta dannama Asy kira,
Daure take da towel iya cinyarta, isowarta gida kenan tayi shirin shiga wanka. Jin kara a wayarta alamun shigowan kira yasa ta maida kallon ta ga screen din wayar,
Tsaki ta doka ganin batasan num dinba ta juya tashige toilet,
Haka hardai kiran ya katse ba a daga ba, jiki a sanyaye Hudah ta dangwarar da wayar a gefe, sai a sannan ta tuna batai ko sallar magrib ba, nan ta tashi ta dauro alwalla, a gurguje ta gabatar da kara’in sallan ta, tana idarwa, again wayarta ta dauka ta sake try lamban Asy,
Dai-dai tana zaune gaban mirror tana ta yan shafe shafen ta, taji ringing a wayar ta, again dai number dazuce ta gani,
Saida ta doka wata uwar tsaki ta dauka a fusace don taji ko waye ke shirin takura mata yanda ta gaji hutu kadai take bukata,
Cikin ruwan sanyi taji an ambaci, “Hello”
Take Asy ta gane muryan don haka tadan kwantar da murya ta amsa da “Hello”
Hudah tai saurin cewa,
“Nice Hudallah da muka hadu daku dazu”
“Owk Hudah ya kikaje gida?”
“Lafia lau wlh ina fata kema haka!”
“Alhamdllh yanzu ma shirin kwanciya nake naga call inki,”
“Syyah Sorry my Asy star Allah yasa ban takura ki ba!”
Saida Asy ta dan murmusa jin sunan da ta kirata dashi , nan take taji yarinyan ta burgeta kunsan Asy wajan son girma ko gyambo yana kunyarta,
Cikin nishadi ta mayar mata da cewa,
“Haba Hudancy wani irin takura, ai yawan gaisuwa yafi yawan fada, nima saida nazo gida naji haushin rashin amsar no din ki da banyi ba,
Gashi kuma lkc daya naji kin kwanta min arai kamar mundade da sanin juna gskiya kinyi min, komai naki yana burgeni, gaki haddadiyar yarinya ga iya dressing, I luv u my Hudancy”
Wani irin zillo na dadi Hudah tayi tsananin murna yasata kankame pillow da take rungume dashi,
“Tnx my Asy star, Dik ni kadai wannan yabo, I really appreciate it, gskia kina da kirki ba kaman kawar nan taki ba, koda yake girmanta ne yakai shiyasa banma ji haushin ta ba, har nayi mata suna da Queen”
Asy tai daria tace, “bazaki gane halin cute lkc daya ba, tanada kirki sosai, matsakar daya ce ita dai bataso haka kawai ka shiga lamarinta, but ahankali in kika saba da ita da kanki zaki bani story, kuma fa kin san me?”
Sekin fada dear!”
“Dazufa Bayan mun tafi a moto take cewa dressing dinki ya burgeta kin iya make up kamar ba yar village ba lolx” 🤣
*Biko, Shower both me and the story some love😍, So you can get an update regularly* 😁☁️☁️☁☁☁☁☁☁☁️☀
🐔 _*(HUDAH Y’AR KARYA….💁🏼)*_
🐤🐤🐤🐤🐤🐤🐤
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🐛
_Written By *ASY KHALEEL…✍🏻*_
Wattpad@asykhaleel
Facebook Group
Asy khaleel Novel’s grp
IG @asykhaleel
4️⃣3️⃣
Sakwakwaf Hudah taji ilahirin jikin ta babu sauran nakka, har lkcn wayar na makale a kunnin ta sedai ta kasa furta komai tunanin ta, wai yau ita ake kira da yar village,
Lallai gaskiyar masu Karin magana, gaba da gaban ta don ko Baba ma da Baban shi,
Daurewa tayi tadan kirkiro murmushin karfin hali, jin datayi Asy ta fara bata hakuri don ita kanta Asy taji ba dadi data gaya mata hakan, kunsan ance magana zarar bunu, in tariga ta fito sai hakuri,
Dakyar Hudah ta iya furta,
“Babu komai wlh karki damu kawata, a yanda nalura da yarinyar tana jin kanta sosai, kuma da gani yar *BABBAN GIDA* ce kinga kuwa abunda yafi hakama zata iya kirana dashi girman ta ne yakai,
Amma plss mai kuka gani alamun kauyanci a tare dani?
Dan Allah my Asy star karki 6oye min komai, bawai da wani manufa nayi miki tambayar ba no, ina so ne nima in karu da ilmin ku kasancewar kun burgeni tsarinku yayi min, shiyasa nashiga lamarin ku batare da neman izinin ku ba, don haka na yarda dake na baki wuka da mana, na aminta dake Asy star ina so ki wayar min dakai tayanda bani ba hatta friends dina susan lallai na hadu da mata masu aji” +
Asy ta kada kai tana daria, azuciyarta tace lallai yarinyar nan za aje dake, afili ta ce,
“Insha Allah my Hudancy zan kuwa fede miki biri har wutsiya,
Saikin zama star acikin kasaitattun mata bama cikin villages people ba”
Wani irin dadine ya mamaye Hudah cikin tsananin murna ta furta,
“Wayyo Allah dadi kai amma fa yau nayi farin fita haduwata daku, My Asy *KE ALHERI CE,* please dan kyankyasa min miye sirrin abin?”
“Me kikeci na baka na zuba, kisa ranki a inuwa kina tare da Asy, wannan sai mun hadu, kuma a ina kike da zama?” cewan Asy khaleel.
“Ina nan U/dosa akan layin sarkin margi, ke kina inane?” Hudah ta tambaya.
Abuja street U/rimi no 15″
“Yes nasan gurin kice min kuna G.R.A ne, ai da gani biri yai kama da mutum, insha Allah kuwa zaki ganni but kidan tofa min kadan mana pls my Asy star”
“Yaasalam”
Asy ta furta jin kosawa irin na Hudah, kwantar da murya tayi tace,
Haba kawata idan baki jin kudin da muke konewa, ki kalli tym yanzu 11pm ake nema dare yayi ki bari zan shigo next week insha Allah,”
“Kutt next week kike magana ai kamar 1year take awajena, ni yanzu haka jina nake tangaras kamar yanzu gari ya waye min. kudin waya kuma karki damu akwai ni da wani sauna wanda shi dama aikinsa kenan lolz”
“Shikenan kice in gyara zama yau ba maganar bacci”
Asy ta fada tana daria,
“Yauwa tawa ashe kin gane pls muje kai tsaye ina sauraronki, dan Allah banda boye komai.
To malama Hudah nasan abinda kike son karin bayani akai, bazai wuce cewan danayi kin iya dressing kamar ba yar village ba!.
So agskiya zamanin nan da ake ciki kanmage ya riga ya waye, indai ke din wayayyan ce kallo daya idan kikama mutum, ba saikin kara na biyu ba zaki karanci abubuwa da dama a tare dashi, anan zaki gane koshi waye, shin yakai inda akeso ko kuwa shishigi ne be karasa ba,
In zaki iya tuna kollon da cute tai miki zaki fashinci abunda nake nufi.
Bari dai in miki gwari gwari, kamar yanda kike wankuwa dakyau a wajan kwaliyar jiki ba Wanda zai raina miki don kin fita daban a cikin kawayan ki, so kamata yayi muga fatar jikin ki itama tasha bambam da tasu, sai kuma ba haka ba, wasu friends din nakima sune abun kallo a fatar jiki ba keba,
Hakan shiya tabbata mana cewa baki kai ba akwai sauran kauyanci a tattare dake, kuma ahakan ke kina ganin babban yarinya ce, amma in kika lura zakiga kananan yara suke bibiyar ki, a yanda kike yanzu ba zaki dinga manyan kamu ba, cox dik wani mai hannu da shuni ko dan *BABBAN GIDA* maiji da kansa bazai kawo miki hari ba, don mazan yanzu ba suturar jiki suke kallo ba no,
Sunfi so suga yarinya taci ta koshi gaba a cike baya a cike fatar jikin nan kamar ka ta6a jini ya tsirto,
Yauwa yanzu za kiga manyan qwari suna miki layi, to sun hangi romo kwance a tattare dake,
Amma ahaka dan wai kinyi ado, ana kallonki haka a tsaye ba gaba ba baya, ilahirin jijiyoyin jikin ki a warwaje ana iya kirga yawansu, dan Allah wani maiji da kansa ne zekai kansa gareki, sedai kiga kwananan qwarika sun dabai bayeki kina kakka6e su suna kara like miki to duk an hada villages Asy ta kece da dariya mai sauti.
Vote n cmmnt pls
*KING ASY KHALEEL….*❣️☁️☁️☁☁☁☁☁☁☁️☀
🐔 _*(HUDAH Y’AR KARYA….💁🏼)*_
🐤🐤🐤🐤🐤🐤🐤
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🐛
_Written By *ASY KHALEEL…✍🏻*_
Wattpad@asykhaleel
Facebook Group
Asy khaleel Novel’s grp
IG @asykhaleel
4️⃣4️⃣
Tinda Asy ta fara magana Hudah ta zama kamar status, dai-dai da ga6ar jikinta bata iya motsaya duk dan kada afadi wata kalmar da bata jita ba,
Yanda ta tattaro dukkannin nutsuwar ta bana tunanin ko sallah take tana taro hankalin ta haka, ohh ya Allah ka shiryi masu irin wannan hali amin.2
Itama dariyar ta biye Asy suka dan taba, daga bisani Hudah ce ta dan tsagaita sannan ta daura da cewa,
“Wlh kawata duk abunda kika fada hakane kuma na yarda dake, ina matukar farin cikin haduwata daku, sedai ni ina ganin ba yanda za ayi in zama kamarku, sbd ni iyayena talakawa ne hasalima mahaifina ya dade da rasuwa, suturar ma ni keyi ma kaina abinci kuwa sai Mamy tayi sana’a take siya mana, kinga ina zanga abunda zan dinga ci har jikina yayi irin naku?
Sannan ni a tsarina ina kyamar yin bleaching sam banason kurajen nan irin na masuyin bleaching , kinga ba wai kauyanci ne ya hanani zama irin ku ba, kawai rashin wadatane dan haka cute tayi koskuran kirana villager”
Dariya Asy ta sake yi sannan ta ce,
“Ba kinga halin kauyancin naki ba, ana kaiki kina qin zuwa, ance miki ke bakauya ce kinqi yarda, to bari kiji har yanzu kanki a duhu yake, mudin da kike ganin mu wasune kinga matsayin mu ne?
Kinsan sirrin mu ne?
Maybe ma kin fimu wani abun, duk yanda kike tunani ba haka abin yake ba, kawai idan ka iya takunka dolene adama dakai, waima kina shiga social media kuwa?”
Asy tadan dakata tana sauraron Hudah dake cewa,
“Eh na taba bude whatsapp sedai ban Dade ba naga 6ata lkc na zanyi abanza, na rufe shi”
“Ai naga alamun haka da kina harka da mutane a online tabbas da kinfi haka sanin wasu abubuwan, amma karkiji komai ki koma online zamu hadu soon, zan hadaki da classic ladies fitattun matan da suka amsa suna mata,
Sannan ya dace kisan bawai yawan tara sutura kadai shike futo da yarinya ba no, wani lkcn tara kayan beda wani amfani idan kika lura babu wacce takeso aganta da kaya yau in wani hidimar ya taso a sake ganin ta dashi, kokari ko wacce take yazamana kullum kalar shigarta daban, ko ba haka ba kawata?
Ajiyar zuciya Hudah ta sauke ta ce,
“Hakane wlh don ni kaina wasu kayan nawa har mantawa dasu nake, atsarina indai nayiwa kaya sawa biyu zuwa ukku wlh sun suremin sedai inta ajiya”
“Toh kin gani ashedai kin gane abunda nake nufi, shin waima da kike fadin baki da abunda zaki gyara jikin ki, ina kike samun na dinki ko kina nufin wani keyi miki ne,
Naga dai akalla dressing dinki na yau abeja kudi ba ya lashe sama da 25k kai zema iya fin haka yanda kika hada komai to match ina kika samo kudin?
“Wlh ni nakeyi kin san inada sana’ar hannu, babu kalar dinkin mata wanda banayi, yawancin ankon bikin nan duk ni na dinka su, toh matsalar dayace dazaran kudin sun shigomin kaf a kaya nake narkar dasu, don ni gskia Allah ya sani banason aganni cikin qasqantacciyar shiga”
Sosai Asy ta jinjina mata sannan ta ce,
“Ke ashema kina da sana’a mai kawo kudi, to bari kiji abunda baki sani ba, wannan dressing din ba irin ta zakiyi ba a yanzu,
Zaki daina saka atamfar kasa da 20k
Zaki daura lace harna sama da 50k
Zaki saka material komai tsadarsa
Zaki saka voyel, shadda irin ta yayan manya,
Zakiyi shigar larabawa, turawa, indiyawa inyamurai yarbawa, ke in takaice miki har mota Zaki shiga kisha sha’anin ki da ita irin na Wa’inda suka isa, kuma duka a kudin da basu taka kara sun karya ba,
Amma abin sirrine sai mun hadu zan sanar dake yanda tsarin yake,
Yanzu abunda nakeso dake duk wasu kudin da zasu shigo miki, ki dage da gyara jikin ki ya zama boobs naki sunyi duma duma hips naki ya fito sosai abubuwan zaman nan suyi tandama tandama ga fadi ga tsini, ya zamto ko wani juyi in kika yi suna fadin ya kagani?
Fatar jikin ki tazamo lugui lugui kamar ta yaran goye, and ya zama dole ki shafa mai yanda zaki dan haska duk da kedin farar ce amma ance in kana da kyau to ka kara da wanka, maganar quraje, wannan kananan mai kike magana, ya za ayi in cire 5k in sayi mai ko sabulun wanka qwaya daya jal a 5k koma sama da haka, sannan ya sani kuraje ai kuwa da anyi bura uba dani don wlh saina mayar an biyani kudina,
So yanzu dai kinji abunda nace akwai kayayyakin tado da breast na Muslim in kina kyamar na bature, in kin shirya sai ki nemeni zan hadu miki Wanda zasu dace dake,
Zan sanar dake abubuwan da zakina chi Wanda zasu temaka wajan gyarar fatar jikinki acikin sauki,
Ina ganin anan zan dakata don bacci nakeji dear, ga kuma wayata naji ta fara bara zanar kamawa da wuta, don tadauki zafi sosai, akwai sauran bayanai dole sai gani gaki abun zetafi yanda akeso, sedai na jiki my Hudancy!.
“Tirqashi”
Hudah ta furta, sanan ta numfasa ta cigaba da cewa,
“Laillai fa masu iya magana sukace wani wan wani wani ko baban wani ne, ai dole ma in nemoki my Asy star Asy my mentor my lovely Asy. Dole in gano inda kike a gobe gobe kodan inji wa’innan surruka, insha Allah kuwa zaki ganni tin safe,
Sannan zan taho da10k, ko zasu isa afara kafin in karasa wasu dinkuna,?
Heheheee Asy ta buga shewa jin an anbaci kudi, tasan ko banza zata yagi rabonta, ta amsa da
“Eh to sedai adan fara gyaran breast kinsan mayuka suna tsada, zamu fara da boobs nd hips, sai kuma fruit din da zakina ci b 4 kudin su shigo, dear saina jiki byee,
Kit Asy ta katse kiran don kadama Hudah ta sake tsareta da wani maganar, rabonda tayi doguwar hira haka ko ita ta manta,
Dogon miqa tayi hade dayin salati ga manzon tsira, jijjiga hannunta tayi alamun gajiya ta ce,
“Wannnan yarinya duk ta wahalar dani, amma ba komai ta kawo 10k din ko banza zanci 3k don ba a banza zanyi wannan dogon bayanan ba dan uwarta.
*Oya shower me with love by voting n commenting endless if this chapter really made u feel something*☁️☁️☁☁☁☁☁☁☁️☀
🐔 _*(HUDAH Y’AR KARYA….💁🏼)*_
🐤🐤🐤🐤🐤🐤🐤
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🐛
_Written By *ASY KHALEEL…✍🏻*_
Wattpad@asykhaleel
Facebook Group
Asy khaleel Novel’s grp
IG @asykhaleel
4️⃣5️⃣
Juye juye kawai take a saman gado sam bacci ya gagara daukan ta,
Kalaman Asy su suketa kaikawo a qwalwarta, ba abunda yafi d’aure mata kai sai cewan da Asy tayi,
Zaki daina daura atamfar kasa da 20k
Zaki daura lace harna sama da 50k
Zaki hau moto irin ta wa’inda suka isa!.
Anya kuwa?
Karfa San gayu yasa inkai kaina makasa, Anya yarinyar nan ba yar mafiya bace?
karfa ta hadani da yan shanjini in shiga uku!.
Nooo gskia Asy batayi kama da yar mafia ba, don naji tana cewa a kudin da basu taka kara sun karya ba, to kodai suna da masu siyar masu da kayan ne da sauqi?
Kai inaaa ba haka bane indai ba kayan sata suke siya ba, ina zasuga kudin siyan kayanda take lissafo min bare kuma ni, zan dai bari zuwa goben in naje naji yanda abun yake,
Da wannan tunanin bacci barawo yai nasarar sace Hudah sedai.
+
Kiran sallan farko a kullum Hudah, don ta aje abin a ranta har mafarki seda tayi, dirowa tayi daga saman bed, take tafara harhada dad’add’un d’inkunan mutanen data aje batai ba, wasu an biyata wasu kuma ta raina kudin ne irin wanda take kunyan su, to saita amsa taita ajiya,
Aikuwa dik ta fito dasu kafin akira sallan asubahi harta yanka wasu.
Yau kam ita ta tada Mamy yin sallah sa6anin da sai Mamy tasha fama da ita sannan ta tashi, wani sa’in ma sai gari yayi haske take tashi, Mamy batai mamaki ba tasan hakan nada nasaba da taso kudi, don haka takeyi da duku duku take tashi tahau keke kafin wayewan gari kuwa ta hada wasu.
Misalin shadaya na rana Hudah ta gama shirin tafiya U/rimi, tsaye take gaban Mamy tana mata magiyar ta ranta mata dubu biyar kafin anjima za a zo kar6an dinki, dayake a wayewan garin nan harta hada kala biyu ta kuma kira duk wasu datasan kayan su yana hannunta tace su kawo kudi zata hada musu.
Mamy dai cewa tayi “Allah ya tsareni d’an jarin da nake juyawa muna cin abinci shi zan tatara in baki ki watsa su, duka sai mu taru mu tsuguna, ke kuma naki dama ba amfani yake mana ba, dakin samu sedai kwashi banza kwashi hofi, to kima bar had’ani da Allah sisin kwabona bazan baki ba”
Dole Hudah ta hakura ta fita dana hannunta daman 12k ne taso Mamy ta bata aran 5k sai taba Asy 15k yanda za’adan fara da tsoka, haka ta kama hanyar U/rimi batasha wuyan gane guri ba, har kofar gida mai nappep ya ajeta.
Wayarta ta fiddo a cikin jakar dake rataye a kafadarta, irin mai dogowar igiya ce wanda ake kira suwaga, d’and’asheshiyar bag ce milk colour wanda take kala daya da tsikareran takalmin dake makale a qafarta, shima me igiya ne wanda shi kansa abun kallone gashi yayi masifar dacewa da qafar , duka sunyi match da d’an siririn mayafin dake sagale a wuyata,
Jikinta kuwa tawa hadaddiyar gown ce purple colour, English wear ne ta kama jikinta dam, duk wani tudu da qwari babu abin data 6oye,
A idonta kuwa sanye take da dansiririn farin glass wanda ya qara fito da asalin kyawun face dinta, dogon hancin kawai kake gani.
Yayinda Zara zaran yatsun hannun ta ke sanye da wasu zobuna na azurfa, Wanda musamman taje museum aka qera mata masu harafin name enta,
Dayan hannun wani tsadadden agogo ne wanda saurayin ta ya siya mata, sai zube daya a yatsar ta na tsakiya Wanda shi akoda yaushe yananan a hannunta, tin ranar da suka hadu da Feedoh, daga tace zoben nan yamin kyau take Feedoh ta zare shi ta zurama Hudah shiyasa takemai laqabi da,
*TSANTSAR HALACCI* kai in takaice muku, mutum ko shine hasidin iza hasada, wajan iya kushe da hassada, lallai in har yaga Hudah a cikin wannan shiga to dolene yace ta hadu iyakar haduwa.
Cikin takonta na isa da qwarewa wajan sarrafa kowace ga6ar jiki, ta isa jikin bishiyar flower wanda akaima bangon gidan su Asy ado dashi,
Jingina tadanyi jikin itaciyar sannan tayi dialling no din Asy, bugu daya ana biyu aka dauka,
“Cikin muryan bacci Asy ta ambaci welcome my Hudah kin iso kenan?
Dayake Hudah ta sanar da ita gatanan a nappep.
“Murmushi Hudah tayi ta amsa da,
“Eh wlh gani a waje sarkin bacci har yanzu baccn ne be barki ba?
Asy tadan dara gami da cewa,
“Ai *kece sila* jiya kin wahal dani dayawa, dani nan fitowa koma ki qaraso kawai!.
“A’a nidai futo kimin jagura idan nashigo in doshi ina?”
“Owk gani nan”
Nan dai Hudah ta tsaya tana jiran futowan ta, sai kuma ta fara kalle kalle, sosai tsarin uguwan ya burgeta, azuciyarta tace,
Gaskia G.R.A yayi yaushe zaka hada da getto erea, wanda hayaniyan yara kadai ya isa ya buwayeka, nan kuwa silent baka ganin d’an kowa awaje kai arziki da dadi, ya Allah ka azurtamu duniya wa lahira,
Ni da nake kusa da ita na amsa da ameen namesake don wlh ba wanda beson jin dadin rayuwa,
Sedai haushin rashi makaho yace ido da wari inji bahaushe.
Hankalin ta tamaida ga gidajen alfarma dake unguwan kaf babu na kushewa, sedai wani ya daranma wani dama kuma Allah beraba dai-dai ba kome kake ganin kana da to wlh wani yafika, mai hakuri dai shiyake da riba awannan rayuwa. Ajerin 6angaran su Asy zamu iya cewa gidansu shine baya agurin, shidin ma babban gidane sedai daganin tsarin ginin bana zamani bane irin dai da anyi tashe yanzu kuma abun ya lafa,
To dama haka Allah ya fada mana, sauqi yana tare da qunci haka qunci yana tare da sauqi, shidai Allah yanaso dik yanda ka samu kanka to kayi godiya.
Tana tsaka da kallo nan kallo can Asy ta fito,
Tayi kusan 2mns idonta kyam akan Hudah, azuciyarta kuwa cewa tayi.
Woww gskia yarinyar nan tayi ba karya, yo wannan ai kwanan nan zatace mudin me?
Murmushi kawai Hudah take aika mata, ganin haka.
da gudu Asy ta nufota ta rungume tamkar ta dade da saninta, babu wani fargaba ko shakkun datake akan Hudah, don Asy tana da son jama a, bare kuma Hudah da take sakaran kofar samuce ta bude.
Ganin irin tarban da Asy ta mata hakan yasa tasaki jikinta rai daya tabi Asy suka karasa cikin gidan..
*KING ASY KHALEEL…* ❣️☁️☁️☁☁☁☁☁☁☁️☀
🐔 _*(HUDAH Y’AR KARYA….💁🏼)*_
🐤🐤🐤🐤🐤🐤🐤
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🐛
_Written By *ASY KHALEEL…✍🏻*_
Wattpad@asykhaleel
Facebook Group
Asy khaleel Novel’s grp
IG @asykhaleel
4️⃣6️⃣
Cike da nutsuwa Hudah ta gaisa da mahaifiyar Asy, sa’annan ta kawo tsaraban turaruka masu kyau ta bata..
Kyakkyawar dattijowar da suke kira Mama, cikin sakin fuska ta amsa tana sanya mata albarka,
Daga bisani ta maida duban ta ga yar tata ta ce.
“Asy banfa gane yarinyar nan ba, anya na santa kuwa?
“Mama ba zaki santa ba, kawata ce tin muna makarantan Malam yunus, karatu ta tafi can qasar Egypt kwanan nan tazo”
Asy na kaiwa nan tabi hanyar kitchen tana daria.+
Allah sarki Mama ta fada,
“Ashe ‘yar tawa bakuwa ce, ya sunanki ne?
Murmushi kadai Hudah keta zubawa, jin shareriyan da Asy ta shara lkc guda, a kunyace ta amsa da,
“Sunana Hudallah”
“Masha Allah sunanki mai dadi da ma’ana, ya karatu Hudallah?
“Alhmdulillah Mama muna ta6awa”
“Madallah to Allah ya temaka, cewan Mama, suna cikin haka Asy ta dawo hannun ta rike da dan madai daicin tray tayi ripping dinshi da wata leda mekyau.
Kallon Hudah tayi tace mukarasa daga ciki ko Hudancy!
Owk tafada tare da mikewa ta bi bayan ta suka yi dakin ta,
Gefan gado Asy tai mata nuni data zauna, wani qaramin table Asy ta janyo ta aza tray din akai, sannan ta dai-dai ta zamanshi a gaban Hudah ta ce.
“Bismillah my Hudancy ‘yar sudaniya… Atare suka bushe da dariya,
“Aifa my Asy kin iya gillota babu ko kunya.
Ni din da ko hanyar Lagos bansani ba, rana daya harkin kaini Egypt.
Cikin dariya Asy ta ke cewa.
Yo ai dressing din jikin ki na kallah take naga kinfi kama da yar qasan Egypt din, bakiga Mama harta shiga ba, wlh kin hadu Hudancy na kuma yarda bakya shigan qasqanci wanan irin kashe kala aini sakin baki da hanci nayi ina qare miki kallo.
Hmmm Hudah tadan murmusa gami da cewa,
“Ah haba dai miye abun kallo a yar villg…. Bata qarasa ba Asy ta toshe mata baki tana daria.
“Kai Hudah baki da dama ashe baki manta ba.
To kisha kurmin ki kin tashi a yar village kin zama wise girl ..
Hudah zatai magana Asy ta tari numfashin ta da cewa.
“Yanzu dai kafin mu tsunduma kogin hira. Kidan ta6a wannan takai hunni tana 6are ledan data rufe tray din.
Fruit ne aciki ta kawo mata masu energy irin su.
Kwakwa, gwaiba, Apple, danino, inibi, kankana lemon abarba, tarkace kala kala ta hado mata duk ta yankasu kanana ta shirya su kashi kashi abun saiya bada ma’ana.
Sosai Hudah ta jinjina karamci irin na Asy, don ta burgeta matuka, dubanta tayi ta ce.
“Kai my Asy star duk ni kadai wannan kayan dadi haka ina zan kaisu kaman dai mu goma zamu sha?
“Duka ki take cikin ki dasu, kinga ni babban abincina kenan, bana sauraron waise an kawo na duka gida,
Ke nifa ko irin saurayi zaizo gurina yadan kirani kafin. Yana cewa mai zan taho miki dashi cewa nake fruit ko in fadi wani drink din mai energy.
Kema yanzu na baki samples don duk suna cikin plan dinmu,
Irin wannan ciman shi akafi so mu yawaita cinsu musumman mu mata,
Bawai koda yaushe ki take ciki da abinci me nauyi ba no.
Anfi so muna yawaita cin fruit wani lkc in kina da dama kiyi juice na kayan itatuwa zallah .
Ina fada miki in har kika jure cin ya’yan itatuwa wlh cikin qanqanin lokaci zakiga yanda fatar jikin ki zata sha bamban data wanda bata samun cin irin su, ga kuma qarin lafia ajiki.
Betsaya iya nan ba, indai wannan ciman ya kama jikin ki to wlh ko mijin da kika aura seyasan ya auri mace mai ni’ima, in kuwa kina da kishiya ayi dace ita din ballagaza ce, to wlh sunanta sorry dan zata kwashi kashinta ahannu.
Ke Hudah amfanin fruit yana da yawa, yar uwa ki gwada zaki bani lbr.
Bari mu koma 6angaran na Fulani da kuma mazaunai.
Akwai had’e had’en da akeyi na kunun alkama da farar shinkafa,
Kayan hadin suna da yawa domin dadi ake hada mai sosai, sai ayi garin su, kullum da safe ki malkada gyadarki ki dafa sai ki rinqa damawa da ruwan gyadan,
Bayan kin dama sai ki kawo garin madara ki zuba in kina son sugar kisa wlh akwai dadi sosai ga kuma gyara fatar jiki, yazama shine abin breakfast din ki,
Za kiga yanda nonowa zasu yi tantsama tantsama, nan da nan zaki ga kin canja,
Sannan akwai tablet da cream Wanda zaki hada dasu, na yarda da aikinsu kuma ba suda illah na gwada na kuma yaba,
Sai kuma sabulun wanka dasu mayuka, irin su turarukan jiki, akwai na Muslim akwai na bature wanda ya amshe ki shi zakiyi, ko kuma muyi mix kinsan bature shegene nashi emergency ne.
Hannu Hudah ta bata suka tafa,
Murmushi kawai Hudah takeyi.
Lokaci lokaci takan dauki abunda ya mata takai baki. Sedai hankalin ta na wajan abunda Asy take fada.
Asy tacigaba da cewa,
Matakin farko daya kamata ki fara dauka kenan kin tsaya sai tara tsummoki kinan adole ga yar gayu.
Yanzu kije na baki nanda 6months zakiga yanda zaki canja,
A lokacin ne zakiga masu qumban susa suna yi muku kara kaina da manyan motoci a kofar gida.
“Hahah kina bani dariya Asy, inafa zanga irin wa’inda kike nuji nida nake a ghetto erea!.
“Ke dalla wayace miki na miji yana kallon wani ghetto?
Ai wlh sedai in baki cika yanda suke so ba,
Tabb wai ghetto hmmm hudah dakwai sauranki wlh,
Yo namiji indai ya hanga ya ganki fara sol, yanda kike da dogon hancin nan kaman ke ki kaiwa kanki, ga kuma gashi dai-dai gwargado, ya ganki gaba acike baya masha Allah.
Nonowan nan nayi atsaitsaye kyam suna yi kaman zasu tsokale mai ido,
Maganar hips kuwa,
Duk inda kika motsa suna fadin.
(Bana yara bane in ka isa taso ka taya!)
Fatar jikin ki taushi li6is, by mistake hannun ki in yadan hadu da nashi ilahirin jikinsa saiya amsa, to yashi lallausar hannu wanda ko audugan rimi albarka,
Tuni dama kin gwane wajan iya dadadan kalamai da kuma sarrafa idanuwa, dama gaki dasu dara dara tubar kallah.
Dik sanda yazo hira, cikin kissa zakina watsa masa wani sahihin kallo mai dauke da sakonni kala kala,
kutt ai wlh ko Ubanshi ne gwamnar garin nan tuni zakiga ya haukace miki, sai abunda kika ce, hidiman da baya yima uwar data haifesa shi zakiga yazo gidanku yana yi,
Gaisuwar da ko Uwarsa da Ubansa basa samun kwatan kwacin ta,
Gwuiwa bibiyu zaki ga yana kwasa a gaban iyayenki.
To ya hangi gidan dadi,
Ke wlh wani ma take zaisa a rushe gidanku amaida shi ginin zamani koda beyiwa iyayensa ba,
Hmmm kedai kibar namiji dan banzane akan mace, wlh ba abunda baza su iya ba, har kike kawo batun wani ghetto erea, wlh ko dajin rugu kike qarewanta kenan, to namiji zai iya binki indai kin hada abunda yake so.
Kedai tsaya kallon ruwa kwado yai miki qafa.
Itama ta bushe da daria harda kwanciya,
Tuni daman Hudah daria take harda su hawaye,
Asy kam ta haqiqice abunta sai zuba dogon sharhi take. saiji suka yi an baki kofar dakin da qarfin tsiya..
*Oya shower me with tsantsan So😍 by voting n commenting harma sharing da masoyanku if dis chappy really made u feel something*☁️☁️☁☁☁☁☁☁☁️☀
🐔 _*(HUDAH Y’AR KARYA….💁🏼)*_
🐤🐤🐤🐤🐤🐤🐤
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🐛
_Written By *ASY KHALEEL…✍🏻*_
Wattpad@asykhaleel
Facebook Group
Asy khaleel Novel’s grp
IG @asykhaleel
4️⃣7️⃣
Cikin takon ta na isa da taqama ta kutsa kai cikin dakin.
Wani mugun kallo tabi Asy dashi batare data furta komai ba,
A6angaran Asy da Hudah ba karamin firgita sukayi ba,
Gaba dayansu numfashi suke saukewa, Asy ce ta iya furta.
“Amma cute kin cucemu, wlh duk nayi zaton Mama ce taji hirar da mukeyi ko kuma yaya Musa, dan walakanci Ashe..
Cikin fushi cute ta dakatar da ita da cewa,
“Common yimin shuru, wlh ban tabbatar ke wata sauna bace sai yau, nayi kusan 5 minutes ina knocking dan banzanci bakiji ba kina can kina zuba kamar bishiyar kanya, aganin ki kinyi gwanin ta ne, to wlh ki canja tsari wannan zubar mana da aji kike”
Tana kaiwa nan taja dogon tsaki, afusace tayi gaban wardrobe ta hankade kofar kaman shine yai mata laifin.+
Asy kam binta da ido tai, ganin tana kokarin 6alle mata murfin wardrobe yasa ta cewa,
Cute wai kanki daya kuwa, sai wani abu kike kamar kinyi tatil, inji dai ba shishan kika shawo min ba?
Mugun kallo ta Watso mata sannan ta sake maida hankali ga tufafin dake shirye a ma’adanin su.
Wani yellow mayafi ta janyo wanda yakasance tamkar mahadi ne da super java dake jikin ta,
Linke mayafin wuyarta tayi, sa’annan ta yafa yellow din,
Batare data kalli daya daga cikin su ba, ta juya zatabar dakin.
Asy tayi murmushi tana girgiza kai, ganin fita zatai dagske, tadan kwantar da murya ta kira sunanta,
“salheart”
Chak ta tsaya kamar wacce aka tsayar da remote. sedai bata yi kokarin waiwayowa ba, bare kuma Asy tasa ran amsawar ta,
“Ina zakije ne haka?
Shine tambayar da Asy ta jefeta dashi.
Tayi kusan 2mnts kafin ta bude baki ta ce,
“Bamuyi dake zanshiga central market ba?”
“Ohh hakane fa nadan manta, so kin fito da mota ne, plz dan jirani mana in dan watsa ruwa, inaso ki saukeni tudunwada Mama ta aikeni gidan aunty Hafsa”
Sai a sannan cute ta juyo ta sakarma Asy wata uwar harara, sai kuma taja dogon tsaki tana cewa.
Ajirgin sama nake ba mota ba, dayake bani da aikin yi bari in tsaya jiranki harki gama sokancin ki, tana kaiwa nan ta fice tabar dakin.
Dik wannan abunda ake, koda ta wutsiyar ido cute bata kalli inda Hudah take ba, bare tasan anyi tsiranta awajan,
Asy ta danyi dariyar yake, sedai sam bataji dadin abinda cute tama Hudah ba,
Kallon ta tamaida ga Hudanllah, wacce ta qame guri guda tana gallon ikon Allah.
Amemakon taga 6acin rai atare da Hudah, wani abun mamaki murmushi ne kwance bisa sarbadediyar fuskar ta, don ita yarinyar tagama burgeta irin su tafiso arayuwa, aganin ta sune mata masu aji.
“Kawata kiyi hakuri da halin cute miskilancin ta over wlh, ammafa idan yan mutuncin suna kusa sekiga kamar ba ita ba” cewar Asy,
“Laah ni wlh hakan da takeyi naji yarinyar ta kara burgeni sosai she is socialize wlh pls ki bani no inta da address zan gwada sa’ata mugani don tsarin ta yamun, inason miskilin mutum, har gida zanje na same ta nasan ba zataqi sauraro na ba” .
Asy ta kadakai tace
“Saikinyi Hudancy, zakuwa kinyi mamakin tarban da zatai miki, salheart tana da mutumci sosai, inhar kikaje gidansu tasan darajan baqi. Amma yanzu tana gidan yayanta bata cika kai kawaye gidan sedai in ta koma gidan Mama,
“Owk itama nan area take?
“no tana kawo ne wani lkc kuma tana gdn yayanta kinsan yarinyar yargatace takarshe, dayake Dad dinsu ya rasu kuma itace Auta, matsalar daya, ko kadan yayunta basa mata da wasa kuma basa cika sakar mata kudi, woww aida munga abu wajan salheart,”
Daria sukayi Hudah tace gata da iya sakawa mutum suna, jiya an kirani yar village, ke kuma yau kin zama sauna lolz”
Cikin dariya Asy tace.
“Saima kinga sunayan samari awayar ta zakisha dariya, kowanne da sunan da tayi saving no dinshi, irinsu transper, ashobi, hamago, qanqamo, wayau yasan naqi, ke abun se ita lolx.
Ni kuwa nasan dalilin kirana haka,
Shirar data tsinkayo munayi CE bataso, tasan tabbas yau zakiji sirrin mu, zai zamto kamar tsirara kike kallon mu, ni kuwa tinda kika nuna kinason ki qaru da ilmin mu komin fushinta saikin shigo cikin classic ladies, barima muci gaba lkc yana ja kafin Mama ta ji shirun yai yawa,
Mungama da fannin gyaran jiki kinji amfanin fruits kuma karki riqeshi da wasa sai mu koma…
_Wani fanni kuma zasu koma? Sekun biyoni, Vote, cmmnt, follow da kuma sharing shine farin cikin ku a gareni_
*KING ASY KHALEEL* ✨☁️☁️☁☁☁☁☁☁☁️☀
🐔 _*(HUDAH Y’AR KARYA….💁🏼)*_
🐤🐤🐤🐤🐤🐤🐤
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🐛
_Written By *ASY KHALEEL…✍🏻*_
Wattpad@asykhaleel
Facebook Group
Asy khaleel Novel’s grp
IG @asykhaleel
4️⃣8️⃣
Dangane da clothes ba wani burgewa bane ki zauna babu cin mekyau bakya yin duk wani abunda zai miki amfani don kawai ki tara kaya, dik kudin da kika samu yana wajan dinkuna, sannan ko wani dressing kina so sai kinyi to match, aiko wlh kina da qaton aiki a gabanki.
Kuma hankalin ki kullum ba zai ta6a kwanciya ba, don kuwa duk yanda kika kai ga haduwa wlh in har zaki shiga cikin taro sai kinga dressing din wata wane naki,
Kinga kuwa kullum kina cikin buri ba zaki yi wani abun amfani ba,
Yanzu abunda nake so dake, kiyi kokari sosai wajan gyara jikin ki, in dai kika goge kika dawo kalar manya, to maganar kayan sawa karkiji komai, bama irin wanda kike sawa ba, yanzu nakece raini zakina sakawa, ni zan kai ki inda ake rent sai wanda yai miki, ko wani irin kaya kike so akwai awajan,
Kinga yafi kita takura kanki, nasan dai anaso a fita daban cikin friends irin an gayyaceki wajan biki ko wani party shine dai zakaso ace kayi zarra acikin sa’a, to kuwa duk irin dressing da kike so zakiyi komin tsadar kaya zaki samu awajan, wanda yazama dole ki siya kamar English wears don sune na zaman gida yau da kullum, baya dasu dik kalar kayan da kike so suna bada hayar su English wears kadai basu cika ajewa ba”+
Asy tadan dakata tana duban Hudah data watsa mata na mujiya.
“Yane Hudancy naga kin tsareni da ido ko baki gamsu ba?
Ajiyar zuciya Hudah tasaki tare da cewa.
To mezan ce my Asy abunne naji ba yanda nayi zato ba, yanzu kamar ni inje ina saka kayan renting agani na hakan ai cibaya ne”
“He he he heeee”
Asy ta buga shewa tare da cewa,
Sai kinyi Hajjajo Hudancy, wato kenan ahaka har wani kama gareki lallai da sauranki wlh,
Hmmm zanso kije wajan nan kiga mata masu kama ba irin ki ba, matan manya masu ji da kansu kiga yanda suke fakawa da motoci na alfarma suna d’aukan hayar kaya, sai dai yawanci masu kudi sunfi kar6an gold, irinsu jaka da takalmi, costume, ke wasu ma harda kayan suna amsa, irin Wanda zaka shiga cikin taro asan ka saka, ko irin an gayyace su meeting ko wani taron farin ciki, sai kawai suje suyi rent abunda suke so, tsadadden material shadda ko lace tare da mahadin shi kamar su mayafi jaka da takalmi irin na 30k ko sama da hk, sai kiga sun faso cikin taron jama’a suna taku daya bayan daya kamar basa kashi.
Kiga yar uwanki mace tana satar kallon ki, to dama abun duk karya ce dakin dawo gida ki tube kayansu ki maida masu, ko banza kin dai yi fafa inma pics ne kinyisu kala kala, ba kuma shegiyar da ta isa tasan sirrinki sai wanda kika so takanki kika sanar da ita.. ke inma akwai wanda taso kureki, ko irin ta ganki da hadadden passion ko bag tace yai mata kyau a ina kika siya, ce mata in tana so zaki kawo mata, kina zuwa wajan, in dai sunci moriyarsa zasu saida miki shi a farashin sauki, ke kuma sai ki saka ribar ki, kinga ko tanan kin qaru,
Hudah tadan murmusa gamida cewa,,
“To sukam basa ko tsoron a gudu musu da kaya irin wannan zunzurutun kudi da kike min lissafi, aiko in hakane saina kwashi kaya harna sama da dubu dari biyu, sannan insa kai abina, ko mai kama dani sunbar qara gani awajan lolz”
Dariya Asy tayi sosai, kana ta daura da cewa,
“Wlh Hudah akwai ki da ban dry, yo an gaya miki haka kawai zasu dauki kayansu subaki basusan ko ke wacece ba?
Ai kamar kije rancen kudine a bank, sai anyi bincike sosai akanki an san koke wacece.
Da atunanin ki haka kawai matsayinki na sabuwar customers sai kije a dauki kaya abaki sannu. To bari kiji bayan bincike sai ma kin saka hannu agaban lauya akan duk abinda kika 6atar ko kika lalata sai kin biyasu kudinsu don kamfanin bata daukan asara, shiyasa yawanci ‘ya’yan manya suke harka awajan bama kowa yasan wajan ba, ni kaina wata kawata takaini wajan, saikin ganta babanta mai kudine sosai yanzu haka tana America karatu, sabon danayi dasu yasa har nake kai customers su basu kaya don sunyarda dani sosai ina kawo musu customers shiyasa ba kowani abu suke karban kudina ba,
Sosai Asy ta dage tanama Hudah famfo, yanda ita Kuma Hudallah tayi naam da zancen Asy, dama akace inda zuciya ta karkata.
Haka sukayi sallama akan Asy zata kawo mata kayan gyaran jiki zuwa yanma, don Hudah ta cake mata10k wanda zasu fara dasu…
_Vote, Cmmnts n ff me pls_
*KING ASY KHALEEL..* ✨☁️☁️☁☁☁☁☁☁☁️☀
🐔 _*(HUDAH Y’AR KARYA….💁🏼)*_
🐤🐤🐤🐤🐤🐤🐤
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🐛
_Written By *ASY KHALEEL…✍🏻*_
Wattpad@asykhaleel
Facebook Group
Asy khaleel Novel’s grp
IG @asykhaleel
4️⃣9️⃣
Hudah bata zarce ko ina ba, sai gidan su Feedoh, cikin zumudi ta shiga karanto mata abin dake tafe da ita, bata 6oye mata komai ba nagame da hanyar da Asy ta sakata, a irin gajeran tunanin ta abun aiyi mata murna ne tana ganin taci gaba.
Sosai ran Feedoh yai matukar 6aci dajin tsaka mai yuwar da kawarta ke neman afka kanta ciki, 6acin rai ta nuna bilhaqqi, babu alamun wasa ta dubeta ta ce,
“Haba Hudah wai mi yasa kullum girma kike kina qara cin qasa, yanzu da hankalin ki kike neman jefa kanki cikin wannan fitinar?
Nasha nuna miki kibi rayuwa a hankali ki dubi matsayin ki fa, wlh mutum bai isa yakai kansa inda Allah bai hukunta masa ba, duk mai hankali kuma masoyinki wlh bazai sakaki a wannan hanyar ba matsayinki na marainiya,
Har kike wani kwaso jiki kinzo ki fadamin a ganinki zanyi farin ciki kenan?
Har wani fadi kike farar albishir yanxu a wannan zancen ina abin farin ciki?
To ni dai ko kinqi ko kinso bazan gaji da gaya miki gaskia ba don haka kibi rayuwa a hankali, sannan ban amince da ki jefa kanki a wannan tsarin na hayar kaya ba, gara dai gyaran jiki shi abune maikyau, shima kibi a hankali, dama zakiji shawara ta, ki manta da wannan yarinyar, akwai littafi na gyaran jiki zalla, yanzu haka ina dashi gara ki amshe shi ki dinga hadawa da kanki yafi kije inda za a kara dasa miki burin duniya, wlh ba komai kega wannan rayuwar duniyar ba sedai rudi, in ka biye mata ta kaika ta baro.+
Shiru Hudah tayi bata furta komai ba, ganin babu alamar wasa a tare da Feedoh tasan in har ta tsaya gardama, zata iya fadawa Momin su shiyasa ta yi kaman ta gamsu, tai saurin kawar da zancen bayan ta nunawa Feedoh ta yi naam.
Misalin shida na yanmaci Asy ta isa gidansu Hudah, da fara’a suka gaisa da Mamy wacce take zaune gaban murhu tana kwashin tuwo,
Bayan sun isa dakin Hudah, nan Asy ta firfito da kayan data hadoma Hudah,
Hade haden kunun alkama da farar shinkafa sai kuma sauran kayan da ake buqata ta kashe masa kudi kamar #5000 don tayi mata hadi mai kyau ta saka komai yanda ya kamata, saida ta tabbatar ta nuna mata yanda zata hadasu, gefe guda fruits ne suma dai ba zasu huce na #2000 ba, a taqaice dai Asy taci riba da ita harna #3000 dama ta saba da wannan business din shiyasa take faran faran da kowace kawa tasan komai wayonta saifa ta amfana da ita,
Godiya Hudah tayi sosai, ta kuma karrama Asy dai dai iyawan ta, suna tsaka da hira, idon Asy ya sauka akan wasu sarqoqin dake zube gaban dressing mirror,
“Wowww” tafada tare da mikewa ta isa aban mirror tana fadin,.
” ohh Hudah ina kika samu sarqan nan, na dade ina nemanta ban sama ba, ina santa sosai, a ina zan sami irinta plz?
Murmushi Hudah tayi tare da cewa,
“Nima nadan jima da siyanta, ni kuma damuna take da nauyi ki dauka kawai in kina so, daman anata kawo mata hari dayake kowa yaga sarqan sai yayi mgn”
Habawa Asy abun nema ya samu wai matar bakanike ta haifi spanner, ai tuni ta tattarata dasu zube da abin hannu duk ta danna a jaka.
*2 MONTHS LETTER*
_Hudah tayi sabo da kawayenta datai masu laqabi da Queen and star. Izuwa yanzu mutumci suke da salheart sosai, tuni dama Asy ta sakata a groups na fitattun yan mata masu ji da kansu, cikin qanqanin lkc ta saba da mutane dayake Allah yaima Hudah baiwar farin jini don ko naman suna albarka, maganar gyaran jiki tuni fatar Hudah ta sauya kala, cikin watanni biyun nan harda qiba tayi abubuwan da ake nema sunfara bayyana, kasancewar dama akwaisu rashin kula dasu shi ya hanasu fitowa kunsan babu abinda bayason gyara, duk lkcn datayi sabon hadi tana dibanma kawarta Feedoh Mamy dai ta zubama sarautar Allah ido, don yanzu Hudah ta daina cin abincin gida, suna gani take tasa kayan dadinta a gaba, sedai dan wanda take samma Mamy, kannenta kuwa sai wanda yai mata aiki shi take kallo, in kuwa tasaka bakai ba kaima kasan sauran. Dalilin hutawa da jikinta ke samu sai abubuwan gyaran datake ci suka samu damar cika aikinsu, kowa ya ganta yasan yanzufa ba Hudan da bace, hutawa take sosai inka ganta saman keke to lallai kudi take so aikin gida daman ba’a sata a lissafi. Hmmm su Hudallah duniya sabuwa lol._
*********** *********** ***********
cike da damuwa take fadin,
“Dan Allah Momy ki roqan min Dadina ko zai amince mu tafi tare da Hudah wlh nayi sabo da ita sosai, ba zanji dadi ba in mukayi nisa da juna, sannan ina tausayin Hudah akwaita da wauta ga yawan kawaye Momy ina tsoro kar kawayen banza su jefata hanya mara kyau, Momy ahalin yanzu ni kadaice nake iya controlling enta don ko mamy bajin maganan ta take ba, ina tsoro kar ta jefa kanta wani hali, cikin muryan kuka Feedoh take maganar, a yayinda Momy take bayyana mata cewa, aiki ya maida dadinta Lagos kuma ya tabbata mata cewa sati mai zuwa zasu tattara gaba daya su koma a can, dayake shi mutum ne mai bukatar iyalinsa a kusa dashi ko tafiya yayi baya wuce sati daya, yanzu haka cewa yayi su cigaba da shiri harma ya samu wanda zai aje ya kula masu da gidan.
Tausayin yar tata ne ya kamata tasan dama dole hakan ne zata kasance don akwai shakuwa sosai atsakanin su, cikin taushin murya ta fara lallashin ta,
“Haba Nana a ina kikaga ana haka, sai kawai muje mu tinkari mahaifiyar yarinyar da wannan mgn, ko kin manta mufa ba dagin Uwanta bane bare na Uba, haka kawai sai muce su bamu ita mutafi gari mai nisa har Lagos, wannan ba abune mai yuwa ba hakuri zakiyi Nana tah,
Batun kinyi sabo da ita daman dole wannan ranar tananan tafe ko babu mgnr tashinmu kinsan dolene ko waccenku tayi aure, aure kuwa yana iya barin qasan dakai gaba daya, don haka banason ki tada hankalin ki, kuma insha Allah babu abinda zai sami Hudah sai alheri, addua zakici gaba da yin mata, dake da rashinki babu daya dazai shirya Hudah addu’ar dai ita zakici gaba, sannan hakan ba yana nufin Kun rabu kenan ba insha Allah wataran zaku hadu kuma zakuyi zumunci koda baku kasance a jaha daya ba,
Sosai Momy ta kwantar mata da hankali saida taga tadan saki ranta, tace ta tashi su fara kimtsa wasu kayayyakin, haka Feedoh ta tashi jiki babu qwari tana tunanin yanda zasuyi missing jina ita da aminiyarta Hudah..
Washegari tin safe ta shirya cikin skirt da riga, na English wears sai dan siririn mayafin data yane kanta dashi,
Key car inta dake saman drawer ta dauka, ta dauki jakarta ta rataya, a palo ta tada Momy suna tattaunawa da wata dillaliya dake dady yace dik su rabar da kayan gidan in kuma da wanda zasu siyar badai zasuyi jigilar tafiya da kaya ba,
Amutumce Feedoh ta gaida bakuwarsu, sannan ta maida dubanta ga mahaifiyar tata ta ce ,
“Momy ni natafi saina dawo, murmushi yake Momy tayi ganin yanayin damuwar da yarta tashiga ta amsa mata da,
“Adawo lfy Allah ya kiyayeki, ki gaida Mamin taku”
Feedoh ta amsa da
“Ameen Momy zataji insha Allah”
Sannu ahankali take gudanar da tuqinta ahaka ta isa kofar gidan su Hudah kallo daya zaka mata kasan tana tattare da damuwa…
*KING ASY KHALEEL…* ✨☁️☁️☁☁☁☁☁☁☁️☀
🐔 _*(HUDAH Y’AR KARYA….💁🏼)*_
🐤🐤🐤🐤🐤🐤🐤
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🐛
_Written By *ASY KHALEEL…✍🏻*_
Wattpad@asykhaleel
Facebook Group
Asy khaleel Novel’s grp
IG @asykhaleel
5️⃣0️⃣
Tin shigowan Feedoh Hudah ta fahimci akwai damuwa atare da ita, sau biyu tana tambayar ta ko lfy sedai Feedoh ta amsa mata da cewa dai2 nake dear,
Mamy tana jinsu sedai tayi murmushi dayake tin a jiya Momin Feedoh ta sanar da ita abinda ake ciki, tasan ba makawa dolene sai sun shiga yanayin damuwa shiyasa batai hanzarin sanar da Hudah ba,
Hini jingur Feedoh tayi suna tare da Hudah bayan sunyi sallar la’asar ne Feedoh ta dan kwanta gefan gado ta kife kanta a pillow tana tunanin taya zata sanar da qawarta abunda ake ciki,
Hudah ce tashigo tana rike da plate da gurasa a ciki, ganin Feedoh akwance hakan ya kara tabbata mata akwai ayar tambaya a tare da ita sanin cewa duk inda taje dazarar anyi la’asar zaka samu tana hanzarin tafia gida,
Aje plate din gurasar tayi ta karasa bakin gadon ta sake jefo mata tambayar.
+
“Wai dan Allah Mi yake faruwa dake ne daerie ?
Banyi zaton akwai wata damuwar ki dahar zaki iya boyemin ba amma babu komai ngd da hakan sedai ina fata Allah ya shigo cikin lamuranki,
Jin kalaman dake fita a bakin Hudah yasata yunkurin tashi zaune, cikin sanyin murya ta furta.
“My Hudallah kenan damuwata ba wata bace face kewarki da zanyi munriga munshaku da junan mu amma ba yanda muka iya haka Allah ya hunkunta”
Cikin rashin fahimta Hudah ta dubeta ta ce.
“Banfa gane in da zancenki ya dosa ba kimin gwari gwari mai hakan ke nufi?”
Anan Feedoh ta labarta mata abin dake wakana,
Kanta Hudah ta dafe takasa furta komai, haka suka kasance ba wani walwala, bama iya su kansu ba, duk wanda yasan shakuwar dake tsakanin su saiya jinjina rabuwan nan tasu.
Ana gobe tashinsu, tin safe Hudah ta isa gidan danufin tadan temaka masu da shirye2.
Tuni daman kayan dakin Feedoh kaf Hudah aka baiwa harda wasu kayan sawanta, Momy ma ba’a barta a baya ba, duk wasu kayayyakin aikin gidan Mamy ta barma, wasu kuma ta rabawa maqwaftan su, kwana Hudah tayi agidan, kasancewar jingin safe Dady yasa akai masu booking daman shi tuni yayi gaba kwanansa ukku kenan da tafiya, haka suka kwana suna hira na bankwana tare da baiwa junansu shawarwari ba kamar Feedoh data dage tanama Hudah naseeha.
Acan airport dakyar aka 6an6are Feedoh da Hudah rungume junansu sukai suna kuka duk wanda yake gurin ya tausaya musu, hawaye kwance bisa fuskar Feedoh ta shige tana dagawa Hudah da sauran friends inta hannu, da gudu Hudah ta juya ta rungume Mamynta tana kuka maiban tausayi….
*KING ASY KHALEEL…* ✨☁️☁️☁☁☁☁☁☁☁️☀
🐔 _*(HUDAH Y’AR KARYA….💁🏼)*_
🐤🐤🐤🐤🐤🐤🐤
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🐛
_Written By *ASY KHALEEL…✍🏻*_
Wattpad@asykhaleel
Facebook Group
Asy khaleel Novel’s grp
IG @asykhaleel
5️⃣1️⃣
Tin tafiyar su Feedoh, Hudah ta zama silent sauqinta daya su Ablah suna yawan ziyartan ta dan sudan rage mata kewa, ga kuma Queen and star, sedai ta rage shige masu sosai a dalilin nunar da ita da Feedoh keyi, koda kasancewa yanzu basa kusa bata fasa aikinta ba akan Hudah kusan kullum sai sunyi waya.
*AFTER 6 MONTHS*
Akwana a tashi masu iya magana sukace mai hali baya fasa halinsa, tuni Hudah ta watsar da fadar Feedoh a halin yanzu sukanyi sati ko a waya basu gaisaba, daman Feedoh tafi kokarin kira, tinda ta koma skull itama tarage nemanta sedai lokaci lokaci.
+
Iyanzu kam baya da Queen and star, Hudah tana tare da ya’yan manya da kuma ‘yan karya wan’inda sukace su Asy tai bani guri.
Awannan lokacin Hudah ta gama cika yanda ya kamata, ta hada duk wani abu da akeso ‘ya mace ta kasance dasu, tayanda duk wani da namiji mai lafia in har zai daura idonsa akanta tofa sai yayi saurin neman tsari ga shedan, dan kuwa ko kai waye saika raya wani abu game da ita,
Haka dai rayuwa tacigaba da tafiya maganar dinki tuni Hudah ta yakicar yanzu samari suke daukar hidimanta duk abinda takeso da rawar jiki zata samu mai kawo mata, awannan lokacin ne Mamy take yawan matsa mata da maganar ta fitar da miji tayi aure, dan ta gaji da wannan layi da ake masu akofar gida, ace duk cikin masoyanta ba wanda ya mata ya takeso ayi da ita, daga karshe Mamy cewa tayi ta bata 2months ta fitar da miji in kuwa taki zata tattarata takaima can dangin ubanta dan bazata ja mata abun magana agari ba, a hakanma bata tsira ba sosai akeyi dasu a maqwafta wai ta saki yarinya ta lalace, kunsan duk abinda kake ciki idon mutane nanan akanka.
*** *** ****
A6oye Cute salheart ta shirya taron birthday party batare da sanin daya daga cikin yayunta ba, dayake sunyi mata gargani akan hakan, kasancewar gidansu mutanan qwaraine masu kokari wajan kiyaye dokokin Allah sunsha nunar da ita cewa,
Babu wani alfanu ga taron da zaka hada shi wanda babu makawa sai an sa6awa Allah, idan muka lura da yanda yan’mata da samari sukeyin yanda sukaso a wajan party musamman birthday party, sannan ga kuma yanda yan mata suke fitar da tsaraici suna karayyara qugu kowa yasan muslumci bai halatta hakan ba, duk lokacin dataje masu da bukatarta na birthday party sukance basu yarda tayi a hall ba, mafi sauki tayi farin cikinta a gida kuma banda tara gayyar banza. Hakan yasa ta shirya abinta a 6oye, datemakon saurayinta daya kama mata kasaitaccen hall na wa’inda suka isa, an kashe kudi masu tarin yawa su Asy da Hudah an gama tanadin fitinannun rigunan da za’a farfasa da ita awannan taro, ita uwar gaiyar kuwa wuhuhuuu abun ba’a magana musamman aka fita waje dan nemo rigar da zasa saka a wannan rana, ranar birthday tinsafe Asy da sauran friends keta kaikawo wajan ganin komai yatafi yanda suka tsara, misalin hudu na yammaci suka aje lokaci, dake sunata gargadin babu african time duk girman gurin nan ni danaje 4:15 bansamu shiga ba hall ya cika makil da haddadun yan’mata da samari isoyar cute da jaruminta kadai ake jira abunda basu sani ba shine….
_Shine mai😳? Ina sauraran ra’ayoyinku kafin mu shiga next page_
*KING ASY KHALEEL…*✨☁️☁️☁☁☁☁☁☁☁️☀
🐔 _*(HUDAH Y’AR KARYA….💁🏼)*_
🐤🐤🐤🐤🐤🐤🐤
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🐛
_Written By *ASY KHALEEL…✍🏻*_
Wattpad@asykhaleel
Facebook Group
Asy khaleel Novel’s grp
IG @asykhaleel
5️⃣2️⃣
A can gidan uncle Haiydar an samu wanda yaje har gida ya sanar da shi danyen aikin da cute ta shuka,
Dafarko yaso ya karyata, duk da yasan zata iya aikatawa.
Ganin qwaurafi bai kar6u ba, nan take wanda yakai masa rahoton ya fidda invitation card wanda sukayi na gayyatan friends,
Jiki asayaye ya Haiydar yasa hannu ya kar6a yana girgiza kai lokaci daya ya birkice nan da nan idanunsa suka koma kamar garwashin wuta yayinda zuciyarsa ke tafarfasa dalilin ganin sunan dake jikin card din tare da cikakken address na hotel din da zasu gudanar da taron,
Iska ya busar ya sake kai dubansa ga card din, kallo yake yana kada kai azuciya yake kara karanto abinda idanunsa ke gane masa.
Ina gayyatar friends maza da mata don tayani farin cikin zagayowar ranar haihuwata. Address, seventeen hotel, no 6 tafawa balewa way, u/rimi GRA Kaduna. Time 4:00pm, gargadi bamu yarda da African tym ba, Allah yabaku ikon zuwa mungode..
+
Dasauri ya kalli agogan dake daure a tsintsiyar hannunsa yaga 2:30 zabura yayi ya mike kamar wanda wutar NEPA taja, a razane bakonsa ya fice daga palon saboda tsananin tsorata da yayi,
Uncle Haiydar baiyi wata wata ba ya afka mota ikon Allah shi kadai ya isar dashi gidan Momin su lfy, dan kuwa tukin kawai yake amma hankalinsa baya a jikinsa fatansa daya ya iske cute a gida,
Fitowanta daga wanka kenan sauri sauri tadan shafa mayukanta ta zira doguwar riga na atamfa, ta matsu tabar gida tin safe takejin gabanta na fadi, tana ji ajikinta kamar asirinta zai tonu.
“waiiii da kuwa na banu dasu yaya, inaga kasheni ne kadai ya Haiydar ba zeyi ba wannan tunanin shiya daddabi zuciyarta, sai tayi tunanin koma dai ta fasa ne?
Sai wata zuciyar tasage tinzirata da cewa,
Haba dai ai wlh da kinyi bala’in kwafsawa, toma ya zakiyi da mutanen da kika gayyato?
Karfa ki manta kin fada a whatsapp, fb, dasu instagram, babu inda ba’a sani ba mutane da dama sunyi shirin halartan taron kodan susha kallo.
“kaii ina bazan iya wannan abun kunyar ba garama ayi inyaso ko sunji daga baya nasan maganar dukane zafin zai wuce ya fiye min naji kunya.
Da wannan shawarar tayi naam, dan haka agurguje tagama shirin tafiya wajan da za ayi mata makeup, tuni daman ita suke jira harsun matsa mata da kira gudun kadda a makara kasancewar kwalliyar da za a tsara mata zai dauki lkc sosai, tinda safe ta tsarawa Momi karyan zata raka anty Haifah bikin kawarta Hancy Momi bata kawo komai aranta kasancewar tasan da maganar bikin, ta amince dataje amma sai data kira Haifah taji lallai itace ta bukaci taimata rakiyar..
Fitowa ta kenan tana shirin taje tayi sallama da Momi anan tayi kaci6ur da ya Haiydar, ganin irin kallon da yake mata jikinta yahau 6ari lokaci daya taji fitsari na shirin kufce mata, cikin matsanancin tsawa ya jeho mata tambayar…
“Zaki tafi wajan birthday party da kika shirya ko?
Bude baki tayi da nufin bashi amsa, taku daya yayi ya cafkota tare da sakar mata wani wawan duka a baki, wayyo abinka da jikin hutu nan da nan jini ya fara ambaliya,
Ihun da Momi taji yasata fitowa a rude, ganin haka yasa ya Haiydar yai saurin janta ya shige dakinta ya datse kofar,
Kururuwa su anty Humairah da Momi suke amma yaya yaki budewa saida yaga nunfashinta na neman daukewa saboda tsananin azaba sa’annan ya fito yana huci kamar wani zaki.
Kan Humairah yayo wacce musamman ya biya gidanta ya taho da ita acewarsa dasaninta ake komai itace shugaba, aifa tana ganinsa ta antaya aguje tashige dakin Momi dasauri ta datse kofa.
Tinda yafara dukan cute, asace Hameeda takira aunty Haifah ta sanar da ita ga halin da ake ciki,
wayyo zo kuga saurin sa6a goyo wajan Haifah tasan ba makawa sai yasa an taho da ita tinda har ya dauko anty Humairah, bata tsaya sawa ba, a dari ta fice tabar gidanta.😅
_Kindly Vote n Cmmnt pls_
*KING ASY KHALEEL…*✨