HUTU CHAPTER 8

HUTU




CHAPTER 8




A kwana a tashi ba wuya yau kwana uku kenan da fara karatun Binta kuma sosai take ganewa ba laifi wanda yayi daidai da yau kwana daya cur kenan Kausar bataji muryan Hydar ba, shi be kira ba kuma in ta kirama baya shiga sedai ace mata not reachable, in hankalinta yayi dubu ya tashi dan gabadaya ta kasa samun natsuwa, kallo daya za’a mata asan ba lafiya ba, zaune take a parlor tana kallo amma gabadaya hankalinta na wani wurin, ganin ba sarki se Allah yasa ta dauki wayanta tareda dannawa Ummi kira dan taji ko sunyi waya da Hydar amma Ummi tace be kirata ba, Khalil ta kira nan ma lbrn duk dayane shima be kirashi ba, ajiye wayan tayi tana addu’an Allah yasa dai lfy. 

Yau kusan kwana hudu kenan layin Hydar baya shiga, ba Kausar kadai ba har su Ummi a halin yanzu hankalinsu a tashe yake, hatta Binta tasan antyn ta ba lau ba dan yanzu Kausar ko magana ma batawa mutane, aikima bata zuwa dan batada kuzarin zuwa,  zaune take a daki ta zubawa wuri daya ido tana tunani wayanta ya fara ringing, seda aka sake kira sannan taji ringing din, dubawa tayi taga ba numbern naija bane da mamakin wake kiranta  ta dauka ba tareda da tayi magana ba, “Hello Kausar”, taji muryan Hydar, da sauri ta sauke wayan daga kunnenta tareda duba numbern ta tabbatar bana naija bane sannan ta mayar tareda cewa “Mine kaine?”, “nine wifey ykk?”, ba tareda ta amsa mishi ba tace “haba mine ina ka shigane haka kai baka kira ba kuma idan an kiraka baya shiga, we were all worried sick about you”, ajiyar zuciya ya sauke sannan yace “I’m sorry dear, wlh tafiyan ba zatane ya kamamu, kuma inda muke kauye ne ba network”, hankali a tashe tace “kana ina?”, “ina Niger”, ya bata amsa, “innalillahi, meya kaika Niger”, jin yadda take magana yasan hankalinta a tashe yake a hankali yace “Kausar mun rigafa munyi maganan nan dake, pls karki damu don’t worry I will be back safe and sound, ki tayani da addu’a kinji”, Kausar da hankalinta ya riga ya kai kololuwa wurin tashi tace “Mine in kanayiwa girman Allah ka dawo”, shi dariya ma ta bashi yace “look don’t worry, I was trained for this fa, karkisa damuwa a ranki komai ze tafi daidai Insha Allah, ki tayamu da addu’a”, ganin ba sarki se Allah yasa tace “shikenan, Allah ya baku sa’a”, “ameen”, yace, ganin muryanta na rawa yasan kuka zata mai saboda haka yace “I have to go now, zan kiraki anjima”, “ok dear take care of ur self kaji”, ” I will”, yace da ita sannan sukayi sallama ta kashe wayan ranta na kuna. 

Kausar da Binta kuwa seda suka fara zuwa office Kausar taga clients dinta tayi sauran abubuwan da zatayi, Binta se zagaye dan karamin office din takeyi dan ya mata kyau dukda ba wani girma ne dashi ba, seda Kausar ta dau lokaci sannan ta gama suka fito suka wuce hospital din, Khaleel ne ya dubata bayan ya mata test ya shaidawa Kausar she’s stable muddin Binta zataci gaba da shan medication dinta yadda ya makata, godiya Kausar tamai yayi murmushi yana cewa “kema bari mu gwada ki”, da mamaki ta kalleshi tareda cewa “gwajin me”, “se nayi zan fada miki”, mikewa tayi tana cewa “nidai dai lfy lau nake bana bukatan wani gwaji”, dariya yayi yace “shikenan naji kije, amma ki sani zaki dawo ko ba dade ko ba jimawa, ni kuma ina nan ina jiranki”, “hmm kai ka sani da wani zance, ‘yar albarka tashi muje kinji”, mikewa Binta tayi suka fita suka bar Khaleel yana mata  dariya dan shida yace ze mata gwaji yaga abinda ya gani daya sashi fadin haka. A mota Binta ta kalli Kausar tace “antyn meyasa mukazo asibiti”, “Binta mun zo ne dan a duba lfynki, yanzu bazaki gane ba se nan gaba”, da haka Binta tayi shiru Kausar tace “in mun koma zan fara koya miki yadda zakiyi amfani da laptop dinki, monday zaki fara zuwa school, ina nufin makarantar boko, amma hade yake dana arabi”, da sauri Binta tace “anty da gaske”, “da gasken gasken”, Kausar ta fada tana kallon expression din Binta which is priceless dan ba karamin murna Binta keyi ba harda motsa jiki. 

Mall ta kai Binta ta siya mata school bag biyu, black shoe biyu da white trekkers na sportwear da white socks sunfi dozen, Binta harda hawayen murna dan dadi, batasan dame zata biya Kausar ba sedai ta rakata da addu’an samun rabo duniya da lahira. Gida suka koma da kaya riki riki a hannu, Hajara da saurinta tazo ta karba kayan a hannunsu ta shiga musu dashi ciki tana musu sanda zuwa, kallon agogo Kausar tayi taga shida harda en mintuna tace “kina nan kenan”, “eh hajiya girkin ne ya danyi yamma amma yanzu zan wuce”, “shikenan ki gaida gida”, Kausar ta fada tana juyawa wurin Binta tace “zanje na watsa ruwa kema kije kiyi ki shiga da kayan daki”, “toh”, Binta tace sukayi sallama da Hajara ta fice Binta ta shige dakinta Kausar kuma ta haura sama tana tunanin Hydar, ” ko ya yake?, yana samun abinci me kyau kuwa, makwancinshi nada kyau?”, ta tambayi kanta amma ba amsa, daki ta shiga tareda rage kayan jikinta ta fada bathroom. 
Yau ya kama Monday kuma yaune Binta zata fara attending school, saboda zumudi tinda tayi sallan asuba ta kasa kowa bacci dan Kausar ta fada mata da wuri zasu bar gidan, 6:30am Kausar ta leko dakin taga Binta na duba karatun lesson dinta tayi murmushi sannan ta karasa da sallama, “amin wa alaiki salam”, Binta ta amsa tana rufe littafin ta, zama Kausar tayi Binta ta kalleta tace “good morning”, tana gama fada ta rufe idonta wai kunya, Kausar tayi dariya tareda cewa “eyehh, waya koya miki wannan”, a hankali tace “lesson teacher”, Kausar tayi murmushi tareda riko hannun Binta tace “haka nakeso ki dage da karatu kinji, ki iya turanci sosai yadda ko ina kika shiga a fadin duniyar nan zaki iya communicate da mutane”, “Insha Allah zan bada himma”, Kausar tace “dats my girl, kinyi wanka”, kai Binta ta girgiza alaman a’a Kausar tace “tashi ki shiga wanka, bari na ciro miki kaya”. 

Blue pencil jeans ta dauko mata da white top a gaban an rubuta wake up & make up da blue ink sannan ta dauko mata karamin baby hijab white da flat baby shoe, tana fitowa Kausar ta barta ta shirya itama tayi nata dakin jallabiya kawai ta zira da mayafinshi ta dauko kudi, car key da purse dinta ta sauko, koda ta koma dakin Binta ta shirya tayi kyau abunta, Kausar ta dauko sch bag dinta ta sa mata socks da shoe dinta jiki dan tanada tabbacin zasu bata uniform, koda ta duba lokaci it’s almost 7:30am kuma gashi Binta bataci abinci, kitchen ta shiga ta hada mata cornflakes ta mika mata tace “sha mu wuce”, seda ta tabbatar Binta ta koshi sannan suka bar gidan, school din da dan nisa, a compound tayi  parking taga suna assembly Binta kuwa se murza  hannunta takeyi dan duk ya jike da zufa cus she’s nervous, kallonta Kausar tayi taga yadda tayi narai narai da ido ta kamo hannunta tace “Binta ki kwantar da hankali ki, wannan sch din sa kika gani sch ne na manyan masu kudi hatta yaran shugaban kasan makarantar nan suke zuwa, nima nan nayi shiyasa na kawo ki, basa duka haka zalika kowa abinda ya kawoshi yakeyi, gabadaya en makarantar nan en ji da kaine, saboda haka inaso ki cire wannan tsoron kar su rainaki, kin ji”, kai Binta ta kada tana mamakin of all schools meyasa na yaran manya za’a kawota ita da ubanta ba kowan kowa ba”. 

Nan ta basu form suka cike Binta batada passport dole aka kira school photographer yazo ya mata sannan akayi directing dinsu zuwa cashiers office, a nan suka biya kudin komai harda list of books da aka basu duk ta siya mata, nan take aka bata Uniform abin mamaki harda belt, a nan ta canza white top ne da navy blue jacket se skirt daidai gwiwa amma ba straight skirt bane, se hijabi ko beret ta zaba hijabi aka bata, uniform har three pairs Kausar ta siya mata da sport wear biyu wanda wando ne tracksuit da top dinshi wanda yake indicating house dinta, pink house aka bata, aka bata textbooks da exercise books ta fito student tsaf abinta se murmushi takeyi, Kausar seda ta mata pics ba adadi sannan suka fita suka fara neman Js3A da taimakon school map dinda aka basu, class din yana fourth floor suda en SS3 saboda kar a takura musu tinda sune en waec, suna ganin class din Kausar taja hannun Binta suka karasa wata yarinya suka gani zaune tana copy din timetable dinda aka basu Kausar ta kirata ta fito wajen class tareda gaisheta Kausar tace “en mata ya sunanki”, tace “Afeefah”, murmushi Kausar tayi tace “nice name,  toh ga  kawa na kawo miki, sunanta Fatima amma Binta ake kiranta, pls do take good care of her”, murmushi Afeefah tayi tace “no problem”, 500 Kausar ta ciro taba Binta tareda cewa “kiyi lunch idan akayi break”, “toh anty na gode”, murmushi Kausar tayi ta juya tana dagawa Binta hannu itama haka har seda ta  sauka tana wondering yadda Binta zatayi cope a wannan school din, koda Binta ta juya bataga Afeefah ba, seda ta shiga class ta zaune tace “har kin shigo, ga kujera”, seat din kusa da ita ta zauna tareda ajiye bag dinta daya mata shegen nauyi. 


Story continues below


“Ungo copy the timetable, teachers suna meeting kafin su fara shigowa”, kallon Afeefah Binta tayi sannan ta kalli timetable din Afeefah, Afeefah ganin yadda take kallo tace “bakiji abinda na fada ba”, sincerely tace “ban gane ba, banajin turanci”, mamaki ne ya cika Afeefah amma se batace komai ba ta fara rubutawa Binta, tana gamawa ta mika mata tareda cewa “wannan shine subjects dinda zamu dingayi a kullum, idan kinji gida ki nunawa antynki ita zata gane”, “nagode”, Binta tace tana karba daga hannunta. Haka akayi dinga karatu ko wani teacher ya shigo se yace Binta tayi introducing kanta, kaman tayi kuka haka takeji saboda yadda en ajin ke mata dariya idan tace batajin turanci, sosai taba Afeefah tausayi, koda aka tashi break kin fita Binta tayi, Afeefah ce ta fita ta siyo mata chips da coke ta kawo mata, Binta kuwa ta dau aniyar setayi karatu kota halin yayane, se ta tabbata babu wanda ze kalleta ya mata dariya, hadiye kukanta takeyi har aka tashi school, tana fitowa taci karo da Kausar, kallo daya Kausar ta mata tace “ya dai”, hawayen da take kokarin hadiyewa ne sukayi nasarar zubowa dama Kausar tasan za’ayi haka saboda haka bata nemi karin bayani ba ta rungume Binta tana bubbuga bayanta tareda bata baki har tayi shiru, Islamiyyan dake cikin school din sukaje aka mata gwaji malamin yace aji biyu ze sata, ga mamakinta Afeefah ma Islamiyyan take zuwa, dogon riga har kasa suke sawa fari, se hijab off sunna navy blue, sosai kayan ya amshi Binta Kausar ta rakata har aji sannan ta wuce, “kema ajinan kike?”, taji muryan Afeefah da murmushi tace “eh”, zama sukayi aka fara karatu sosai take gane karatun dukda da turanci sukeyi amma suna hadawa da hausa, karfe shida aka tashe su driver din Afeefah yazo ya dauketa cikin mota kirar 4matic, motan ma bude mata akeyi, Binta kuwa se mamaki take ganin kusan gabadaya yaran makarantar da driver dinsu, tana nan zaune Kausar tazo ta dauketa se hiran sch din sukeyi har suka kai gida. 




✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴

Wani ya gani zaune yana painting ba tareda tunanin komai ba ya karasa wurinshi cikin maye, abinku da fararen fata kowa harkan gabanshi yakeyi ba ruwan wani da wani, kujeran da yake kusa da mutumin yaja ya zaune su Jamil dai se kallon ikon Allah suke, kallon mutumin yayi yace “pls paint for me”, ba indiyen ba tareda ya damu cewar cikin maye yake ba yace “ok will u give me the description”, “hmm”, Anwar yace, nan take mutumin yasa sabon card akan sketch board ya dauko brush ya fara zana abinda Anwar ke fada mishi, mutane masu wucewa tsayawa sukeyi suna kallon ikon Allah ganin shirmen da mutumin ke zanawa wasu harda dariya ciki kuwa harda MK da Jamil, shi kanshi me zanen murmusawa yakeyi ganin ya biyewa mashayin giya wanda ya bugu suna zana shirme, seda yayi nisa yaga drawing din ya fara making sense tuni mutanen dake wurin suka nutsu harya gama, babu abinda akeji a wurin se “wow, she’s beautiful”, Anwar ajiyar zuciya ya sauke ganin hoton Binta zane a gabanshi, su Jamil baki sake suke kallon fine girl dinda aka zana cikin gown zaune tana murmushi, sedai idonta yayi ciki ciki kuma dats all he can remember saboda cikin maye yake kuma last ganinshi da ita sanda tabar hospital ne amma dukda haka zanen ba karamin kyau yayi ba, mikewa yayi ya ciro kudi a wallet dinshi ya mikawa mutumin sannan ya karba sketch dinshi yayi gaba su Jamil na binshi a baya har seda suka tabbata ya isa gida lfy sannan suka wuce suna hiran shirmen da Anwar ya dinga yi ashe nan abinda ke ranshi yake fada aka zana mishi. Anwar kuwa koda ya shiga gida kallon hoton yakeyi yana cewa “why did u leave me, why did u run away when u don’t have to,  why?”, haka ya dinga sumbatu har bacci yayi awon gaba dashi besan inda kanshi yake ba. 

Anwar besan inda kanshi yake ba seda garin Allah ya waye sannan ya tashi da matsanancin ciwon kai, rike kanshi yayi hannu bibbiyu yana shirin mikewa idonshi suka mai harba da sketch din Binta dake ajiye gefe, dauka yayi yana kallo besan sanda dariya ya kubce mishi ba a ranshi yace “tunanin me nakeyi har na bari aka zanata, yarinyar da bansan duniyar da take ba”, dogon tsaki yaja tareda cukurkude sketch din ya wurgar gefe ya mike ze shiga bathroom se kuma ya dawo ya dauka tareda warwarewa ya ajiye kan gado ya shiga bathroom din, wanka yayi yayi alwallah ya fito yayi sallah sannan ya shiga kitchen dan wani yunwa ke kwakularshi, kwai ya soya ya hada tea ya dawo parlor tareda kunna tv yana cikin cin abinci wayanshi ya fara ringing, koda ya duba Mom ya gani rubuce a jikin screen din, silent yasa wayan saboda beson damuwa dan tinda yazo karatu sau daya ya kirata, itace me kiranshi kullum amsawa kuwa seyaga dama, Mom duk tabi ta damu da lamarin danta, intawa Dad magana kuwa se yace ai Anwar din ba yaro bane. 

Gajiya tayi da kiranshi ta ajiye wayan, yana gama cin abinci ya dau wallet dinshi ya fita, frame yaje ya siyo ya dawo gida yasa hoton Binta cikin  din sannan yayi hanging dinshi a daki yadda daya tashi daga bacci face dinta ze fara gani kullum, murmushi yayi me ciwo sannan yace “I want to forget you but I don’t know how, the more I’m trying to forget u the more I fall for u”, shafa hoton yakeyi yana sumbatu yanaji kaman zata fito daga cikin hoto ta tanka mishi amma yasan it’s not possible, agogon hannunshi ya kalla yaga it’s almost ten kuma yanada lecture 10:30, jakanshi ya dauka da duk wani abu daze bukata ya fita tareda kulle apartment dinshi. 

✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴

Hydar ne zaune  kan wani dutse duk ya pante fuskanshi da baki Kausar yakeson kira amma ina ba service, wani dogon tsaki yaja yana takaicin wannan  rashin service din, soldiers dinda aka kawo Niger gabadaya hankalinsu ba’a kwance yake ba musamman ma masu iyali dan kuwa yadda suke zaton abin ya wuce nan, fada akeyi sosai tsakanin sojajin da en kunar bakin wake, dayawa an mutu wasu kuma an hospital anji musu rauni, Hydar Kausar ce shi matsalarshi dan ko kadan bayason hankalinta ya tashi, abokin aikinshi El Ameen ne ya karaso wurin tareda mika mishi ruwa yana cewa “daka daina wahalar da kanka dan gabadaya service ya dauke, babu yadda zamu yi dole se hakuri, gashi yanzu hankalin kowa a tashe yake  dan bamusan next plan din mutanen nan ba, da alama dai an gama da spies dinda muka tura”, kurban ruwan Hydra yayi yace “hakane, Allah ya shige mana gaba, sedai El Ameen let’s do each other a favor”, da mamaki El ke kallonshi yace “Favor kuma”, Hydra ya kada kai yace “tomorrow at the battle field let’s stick together, u watch my back I watch yours, ba wai fata ba amma koda abu yazo da tsautsayi dole daya cikin ya rayu, hankalina ba’a kwance yake ba saboda haka if don’t make it u have to make it, in kun koma gida go to my family ka fada musu I love them alot”, kallonshi kawai El Ameen keyi dan kuwa besan me zaice ba, se daga baya yace “kana magana kaman ba soja ba, remember we don’t give up, forget kawai ka kwantar da hankalinka Insha Allah komai ze tafi daidai”. 



Kwance suke a hideout dinsu suna bacci amma kuma a zahiri ba bacci sukeyi ba, their bodies are resting but their minds are open, cikin sojoji hamsin da aka turo su goma sha bakwai suka rage lafiyarsu lau a cikin wata daya, Hydar daya kasa bacci saboda jikinshi na bashi ba lfy ba yaji alamun mutane na tunkarosu, a hankali ya shiga tada en uwanshi kowannensu ya mike tareda gyarawa jira kawai suke a matso  suyi fire, a hankali Hydar ya matsa kusa da El yace “remember what I told u”, tsaki El yayi tareda maida hankalinshi kan kallon ta inda target dinsu zasu fito, cikin abinda be wuce 30secs ba aka fara fire suma suna mayarwa, cikin ikon Allah kuwa yau suka samu nasarar kashe en kunar bakin waken tareda kama leader dinsu sedai unfortunately an harbi sojoji biyar uku sun mutu biyu sunji rauni cikin wa’anda aka harba kuwa harda Hydar. 


✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴

Kwance take tinda ta shigo daki ta kasa bacci, gabadaya ta kasa sukuni, ganin ba sauki yasa ta tashi ta dauro alwallah ta tada sallah tayi nafila raka’a hudu sannan ta dauko qur’ani ta soma karantawa, Kausar rabon data bude qur’ani ita kanta ta manta amma yau fargaba da tsoro sunsa ta bude, karatu take tana hawayen da batasan dalilin zubarsu ba, gabadaya ta rasa sukuni, tsoro ya gama mamayeta, zuciyarta banda Hydar babu abinda take kira, tun tana hawaye harta fara kuka a hankali daga baya kuwa kukan nata ya fito sosai, Binta dake karatu taji alamun ana kuka, kallon agogo tayi taga karfe uku da rabi na safe, “wake kuka”, ta tambayi kanta, abunku da dare ko ina tsit, jin kukan na karuwa yasa ta tsorata itama, tashi tayi ta fito ta kunna flashlight din wayan da Kausar ta bata a hankali take hawa sama harta kai dakin Kausar ta shiga kwankwasa tana kiran “anty, anty”, amma shiru, jin kaman kukan daga dakin Hydar yake fitowa yasata komawa bakin kofar dakin ta shiga kwankwasa amma Kausar ta kasa tashi ta bude mata dan gabadaya ji tayi ko yatsa bazata iya dagawa ba, a hankali Binta ta bude kofan ta shiga ganin Kausar zaune kan sallaya tana kuka yasata karasawa wurinta da sauri tareda cewa “anty meyasame ki”, shiru Kausar tayi ta kasa magana ganin haka yasa Binta yin shiru tareda rungumo Kausar jikinta ai kuwa Kausar kaman an kara rura mata wutan kukan ne. 

✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴

Ummi cikin bacci taji gabanta yayi mummunar faduwa ta tashi tana maimaita “Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, la haula wala kuwata illa billahil azeem”, seda ta maimaita sau uku sannan ta kalli agogo karfe uku harda en mintuna, glass cup dinda ke ajiye kan bedside drawer ta dauka zata sha ruwa amma hannunta ya kasa rike cup din saboda rawan da yakeyi, daga karshe ma cup din sabulewa yayi ya fadi kasa tareda tarwaste wa, Abba dake kwance gefenta ya tashi zaune tareda cewa “meya faru, naji kaman fashewar abu”, kallonshi tayi tace “alhaji latsomin yaron nan a waya muji lfyrshi, yau kusan sati kenan rabon da ya kira”, cike da mamaki yace “acikin daren nan, ko kinsan karfe nawa kuwa”, tace “nidai in kana yiwa Allah kiraminshi”, girgiza kai yayi dan yasan mother’s instinct ke dawainiya da ita, wayanshi ya dauka ya kira Hydra amma kwatakwata baya shiga ya kalleta yace “wayanshi baya shiga, kiyi hakuri ki kwanta da safe zamusan yadda zamuyi”, badan ranta yaso ba ta kwanta amma gabadaya hankalinta ya koma kan Hydar. 

Zaune suke suna breakfast Mom ta kalli Dad tace “nikam dan Allah ka kokarta ka tura Khaleel India in kai bazakaje ba, ya dubomin yaron nan”, seda Dad ya kurba ruwan tea sannan ya kalleta da kyau yace “indai Anwar ne karki damu, zamuje mu kai mishi ziyara amma ba yanzu ba”, shiru tayi bata sake magana ba Dad ya kalli Khaleel yace “Babana kacemin kanada magana, yi hakuri bansamu zama bane kwana biyu nan”, murmushi Khaleel yayi yace “ba komai Dad”, Dad ya kada kai yace “toh ina jinka me kakeso mu tautauna, ko muyi excuse din kanmu ne saboda kar mom dinka taji”, yayi maganan yana kallon Mom data aika mishi da hararan wasa, yayi dariya Khaleel ya soma sosa keya dan besan daga ina ze fara ba, kallonshi Mom tayi ta mike tana cewa “bari na baku wuri”, sannan ta shige kitchen abinta. 


Dad yace “ina sauraronka”, kanshi kasa yace “Dad dama so nake in ka samu lokaci ka gana da Alhaji Mahmoud”, “mahaifin Hydar kenan?”, Khaleel ya kada kai tareda cewa “eh”, Dad yace “toh ince dai lfy”, “lfy Dad, dama wai ‘yarshi na gani kuma naga tamin shine nace bari in ka nemomin izini wurin mahaifin ta sena fara nemanta”, murmushin Dad ne ya fada yace “alhmdllh, yau Allah ya nunamin ranar da nake muradin gani, karka damu Insha Allah zamuyi waya dashi, in yana gida zanje na sameshi a gida idan kuma yana office zan bishi chan”, “ngd dad”, ba gdy ni bari na wuce, mikewa Dad yayi yama Mom sallama ta rakashi kar compound, dawowan da zatayi taga Khaleel na tsalle yana “YES!”, tayi dariya tareda kai mishi duka a baya tace “ja’irin yaro”. 

✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴

El Ameen iya rikicewa ya rikice ganin Hydar kwance a gabanshi ba alamun numfashi ga jini se fitowa yakeyi kaman ruwa, rungumo Hydar yayi jikinshi yana kuka sosai su kansu sauran seda suka zubda kwallah dan kuwa anyi rashin jarumi, managarci, mara tsoro me kare kasarshi, ambulance dinda aka kirane sukazo wurin aka samu akasa dukkansu a mota aka wuce dasu hospital. El Ameen ya  kasa zaune ya kasa tsaye se yanzu yake tuna maganganun da Hydar ya mishi, kuka yakeyi kaman mace, yasan basu wani dade da haduwa da Hydar ba amma kuma Hydar akwai shiga rai, koda kuwa kwana daya kuka dashi balle kuma ace suna neighbors.



Doctors seda suka kwashi lokaci me tsayi sannan suka samu numfashi Hydar ya dawo, sukayi treating dinshi suka cire bullet din sannan suka bashi daki dan he’s in a state of coma, El Ameen dakin da aka kwantar da Hydar ya shiga sannan ya zauna kan kujera yana kallonshi, dat bullet was meant for him amma Hydar ya karbar mishi, ashe he means it sanda yace “u watch my back I watch urs”, yau idan Hydar ya mutu baze taba yafewa kanshi ba, kallon kirjin Hydar yakeyi daidai gefen zuciyarshi inda aka harba, bandage ne a wurin ga ruwa da jini duk ana kara mishi at the same time. Fitowa El yayi jin ance motansu yazo, masaukinsu aka kaisu dan su samu suyi wanka suci abinci su huta sedai dukkansu jikinsu asanyaye yake, ace cikin su hamsin su bakwai ne zasu koma gida lfy lau, wa’anda aka rasa kuma dayawansu  sunada iyali, haka sukayi duk abinda zasuyi kowa ka ganshi babu lakka a jikinshi kaman ba soja ba. 


✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴

Kausar canza channels takeyi har ta tsayar dashi CNN duk da bata kallon news yau setaji tana ra’ayin kallo, Headline din yafi komai daga mata hankali OUT OF FIFTY SOLDIERS ONLY SEVEN SURVIVED_Niger Nigeria. Tashin hankali, kallon hoton survivals din take ko zataga Hydar dinta amma babushi babu me kama dashi, a hargitse ta tashi tayi dakinta hijabi kawai ta zira ta dau key ta fito, a 360 taja mota tana kuka taba kowa tsoro ganin yadda take tuki, gudu takeyi kan titin kaman babanta ne ya ginashi, cikin minti goma ta karaso gidansu Hydar da kukanta ta shiga ai kuwa ta iske Ummi da Abba gaban TV a parlor, Ummi ma kukan takeyi Abba kuwa shiru yayi jikinshi yayi sanyi, yana daurewa ne kawai amma shi kanshi hankalinshi ba’a jikinshi yake ba. Kausar jikin Ummi ta fada suka rungume juna Abba yace “dan Allah ku kwantar sa hankulanku, na kira kuma ancemin akwai wa’anda ke hospital, kuyi addu’a Allah yasa Hydar namu na cikinsu”, amma ina kaman badasu yake ba (mata akwai mu da raunananiyar zuciya). 



Wayan Abba ne yayi ringing koda ya duba daughter ya gani rubuce yasan Anty Maryam ce, da kaman baze dauka ba se kuma ya dauka ya saita kanshi yace “salamu alaikum, mamana kice da kira da sassafe”, cikin rawar murya tace “Abba ka kalla news @8am kuwa, banga me kama da Hydar ba”, “kwantar da hankalinki Maryama na kira kuma am shaidamun wasu na hospital, karkisama ranki damuwa”, lallashinta yayi sosai sannan sukayi sallama suka kashe wayan. News fa ya zagaye gari, Naija ba lfy ankashi soldiers dinsu, masu kuka nayi, masu jimami nayi, masu makoki nayi, masu musu nayi, kowa da abinda ya dameshi. Lokaci daya Kausar jikinta ya dau zafi, zazzabi ya shigeta farat daya, ganin haka yasa Ummi tsagaita nata kukan tareda kwantar da hankalinta ta kama Kausar suka shiga daki, kwantar da ita tayi tana lallashin ta tace “Kausar kukan ya isa haka, insha Allah babu abinda zamuji ko mu gani se alheri, ki daina kuka a wannan yanayin da kike cike, karkisawa kanki wani ciwon”, duk maganar nan da Ummi keyi kallon me ciki takewa Kausar, a hankali Kausar ta fara hadiye kukanta tareda lumshe ido har baccin da batasamu yinshi ba ya kwashe ta cikin kankanin lokaci Ummi ta zauna tana kallonta cike da tausayawa. 

Wasa wasa Kausar daga ciwon kai ciwo ya zama babba, da wani mugun zazzabi ta tashi ga yunwa dan tin safe ko ruwa batasa a baki ba, da kyar ta iya dafa bango ta shige bathroom tayi alwallah ya fito, sallaya ta shimfida sannan ta zauna tayi sallan azahar a zaune dan bata ganin zata iya iyayi a tsaye. Tana idarwa Ummi ta shigo fuskarta dauke da murmushi ta zauna bakin gado tareda cewa “Allah ya karba”, Kausar ta amsa da “Ameen”, Ummi ta gyara da kyau tace “albishirin ki?”, Kausar kanta a daure tace “goro”, Ummi ya sakeyin murmushi tace “su Hydar na hanyar dawowa, ya dai samu rauni amma ance an samu an cire bullet din, kuma koda sun karaso hospital za’a wuce dashi direct, da yamma zamu iya zuwa ganinshi”, sosai hankalin Kausar ya dan kwanta jin mijinta na raye amma tanajin ance an harbeshi ta fara hawaye, a zuciyarta tace “tsinannu suna nema su nakasa min miji”, a fili kuwa cewa tayi “alhmdllh Allah abin godiya”, kallonta Ummi tayi sosai sannan ta mike tace “bari nasa akawo miki abinci, in kince seki sauko, Maryam ma na kasa”, “bari kawai muje naci a chan”, mikewa tayi amma jiri ya debeta ba shiri ta koma ta zauna, Ummi dake lura da yanayinta tace “lfy, kodai jikinne?”, a hankali Kausar  tace “jiri nakeji”, “zauna nan bari a kawo miki abincin”, ta fada tana taba jikin Kausar da sauri tace “ya jikinki yayi  zafi haka? Bari na kira Khaleel”, bata jira cewar Kausar  ta fita. 



Ba jimawa ta dawo hannunta dauke da abinci tace “sauko kici”, saukowa Kausar tayi taga lafiyayyen sakwara da miyan taushe ai tuni miyanta ya tsinke, wanke hannu tayi ta dawo ta cika cikinta dam tayi gyatsa ta ture plate, se a lokacin taji zuciyarta na tashi kaman zata harar, da sauri ta tashi tayi bathroom ganin da gaske aman zatayi, duk wani abinda taci seda ya dawo gabadayanshi, ji tayi an bubbuga mata baya ta dan dago taga Anty Maryam ce tana mata sannu, gyara wurin tayi ta kuskure bakinta tareda wanke fuskanta sannan suka fito tareda Anty Maryam, “sannu dama baki da lfy ne?”, Anty Maryam ta tambaya tana zaunar da ita kan gado, “lfyta lau, zazzabin  yau ya tasar min”, “ayyah sannu, kodai zazzabin kewan Hydar ne, karki damu yana hanya”, Anty Maryam ta fada ciki da zolaya, murmushi kawai Kausar tayi tana  neman kwanciya, ganin haka yasa anty Maryam gyarawa ta kwanta da kyau sannan ta fita ta bata wuri dan taga alaman bacci takeso tayi. 



Parlor ta koma ta zaune kusa da Ummi dake wasa da babyn Anty Maryam Aflah tace “Ummi amma fa Kausar batada lfy, naje na tarar tana hararwa”, kallonta Ummi tayi tace “na kira Khaleel, ni inaga kaman juna biyu ne da ita”, “Allah koh, da alaman kam”, anty maryam ta fada tama daukan Aflah dake miko mata hannu, suna zaune suna hira wanda kusan duka hiran Hydar ne Khalil ya shigo da sallama suka amsa mai, bayan gaishe gaishe yace “ya kuma mukaji da fargaban abinda ya faru”, Ummi ta sauke ajiyar zuciya tace “da godiya, ga matarshi chan ma zazzabi ya rufeta”, “bari na dubata”, mikewa yayi anty Maryam na biye dashi har dakin da Kausar take, koda suka shiga har tayi bacci, Anty Maryam ta tasheta saboda Khalil yayi aikinshi, yana cikin dubata yace “ni nasan za’ayi haka, ai kwanaki da kika kawo Binta asibiti nace ki tsaya in dubaki kika ki”, shiru tayi batace komai ba ya diba jininta tareda cewa “bari naje na gwada a lab, zan dawo anjima”, godiya anty Maryam ta mishi ya fita, tabi bayanshi tareda jawa Kausar kofa. 


Cikin awa biyu Khalil ya dawo tareda musu  albishirin Kausar na dauke da juna biyu har na tsawon wata biyu, murna a wurinsu ba’a  magana while ita kuma Kausar ji take dama kasa ya bude ta shige dan kunya, Ummi tarairayarta takeyi kaman zata maida ita ciki na murnar ta kusa ganin tsastsun tilon danta, Kausar ganin karfe biyar kuma har yanzu ba lbrn Hydar gashi Abba be dawo ba ta kalli Ummi tace “Ummi zanje gida na dawo”, Ummi tace “bazaki zauna ba ‘yar nan”, “bazan dade ba, akwai abunda zanyi ne”, “toh sekin dawo, ki kula da hanya ko insa driver ya kaiki”, “a’a Ummi I can manage”, fita tayi bayan ta musu sallama bata tsaya ko ina ba se sch dinsu Binta dukda basu tashi daga Islamiyya ba amma ta musu magana ta dauko ta, kallon Kausar Binta tayi tace “anty bakida lfy ne?”, “is it dat obvious?”, ta tambayi Binta wacce ta bita da ido, tayi murmushi sannan ta kamo hannunta, Binta najin dumin hannunta tasan bata lfy, “Binta Antynki batada lfy saboda an harbe Uncle dinki”, da sauri Binta tace “Anty waya harbeshi”, “nima bansani ba Binta, amma kinsan me?”, Binta ta girgiza kai Kausar tace “Antynki nada ciki, zata haifo miki kani ko kanwa”, ta fada tana hawayen farin ciki, itama Binta sosai taji dadi har ta kasa boye murnarta tace “anty Allah ya inganta”, “Ameen Binta”, Kausar ta amsa a daidai lokacin da suka shiga layinsu. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *