IN AN KI JI (BA A KI GANI BA) BOOK 2 CHAPTER 7 BY ZAINAB LAWAN BIRGET
Mun tsaya
Safina ta kuma harararta “Naja’atu ki fita daga idona na rufe, ba dake nake Maganar nan ba amma na lura gigin auren nan yana so yasa ki manta cewar a gaba dake nake”. Ta juya ga abokiyar maganar tata wato Rumanatu “Kin gane ko Ruma, he is not my type, inazan kai wannan mutumin da wannan rusheshen cikin sa? Ai sam bai dace da ni ba”. Tuni Rumana ta kosa da zancen sabida ta lura maganar tafi karfinta, dan ko a karshen hirar sai tace “Allah ya kyauta”. Amman a ranta mamaki ne ya cika ta “Ita kuwa Safina me ta dauki rayuwa ne? bata san rawar ‘yan mata ce na gaba ya koma baya
Anyi biki an gama lafiya an kai amare dakunan su sai dai kwata-kwata Safina bata saki jiki irin yadda ta saki a bikin Rahama ba domin sam bikin bai gamsar da ita ba, shi yasa ma bata gayyaci kowa ba saboda yanda Naja’atu ta ki bata hadin kai suyi biki na karya na burgewa, taki ta matsawa Muhmod ya bata kudade da za su yi shagalinsu, walima kawai suka shirya babu wani lunchen balle kuma su shirya hadaddiyar dinner. Tunda aka fara hidimomin bikin Safina take dararewa, taki ta shiga cikin jama’a saboda surutu da tankata da ake yi, ‘yan kauyen su sun cika gidan taf, dangin Innarsu duk sun taru, abokan wasa sai gori suka yi mata, su na mata tsiyar kannenta sun yi aure ita kuma ta daurewa boko gindi, duk wannan surutun da ake yi babu abinda ya dameta sabida tasan idan ta tashi zaben miji duk sai ta rufe bakin masu tsegumi, dan miji na kece raini na shiga taro zata zabo.
Hatta a wurin Inna ma Safina ta samu sauyin fuska, duk wasu kaya da Inna tadade tana Tarawa domin Safinar yanzu ta fito da su ta jera a dakin Naja’atu. Tunda Naja’atu ta share mata hawayenta ta wanke mata zuciyarta daga .kuncin da Safina ta kunsa mata tunda ta kori Sulaiman, badan haka ba da tuni sun jima da
Www.bankinhausanovels.com.ng
auren su, wata kila ma har da albarka ‘ya ‘ya, sabida tuni ta gano karya Safina saboda har yanzu Sulaiman din bai yi aure ba sabanin yadda Safinar take cewar an zaba masa mata ne a dangin su shi yasa ya rabu da ita.
Ko kusa Inna bata damu da rabuwar Safina da Kamal kamar yanda ta damu da rabuwar ta da Sulaiman ba, haka kawai take kaunar Sulaiman gani take ma Safinar ba zata kuma samun kamar shi ba har abada.
Kwanci tashi babu wahala a wajen Allah karatu ya zo karshe tunda har gashi Safina na rubuta project dinta na kammala karatun digiri, kwanaki kalilan kuma suka fara rubuta jarrabawar fita, a nan ne Safina ta tattara duk tunaninta da nutsuwarta waje guda ta dage sosai dan ganin ta samu sakamako mai kyau, so take yi ta samu sakamakon da duk masoyanta za su yi farin ciki da shi, sakamakon da zai faranta ran Innarta tasan bata bata lokacinta a banza ba, burinta shi ne samun sakamakon da Babanta zai yi alfahari da shi dan ta san halinsa duk abinda mutum zai yi ya faranta masa rai to yabi bayan maida hankali akan karatu, gashi ya bata goyon baya sosai, bai takura mata da zancen
Www.bankinhausanovels.com.ng
aure ba. Ba tare da wata matsala ba ta kammala jarrabawarta cikin nasara ta dawo zaman gida dan jiran sakamako.
Cikin kasa da mako daya taji duk zaman. gidan ya gundureta, a ganinta zaman gidan zaman takura ne da zaman rashin ‘yanci ko fada da sa idon Inna kadai sun isheta sosa ta tsani zaman gidan, sai jimamin rabuwa da abokan karatun ta wadanda suka yi shekara hudu tare, shekara hudu ba kwana hudu bace, su fadi tare su tashi tare, suyi karatu tare su yi discussion tare, lallai sabo gubane, ji take kamar ta rabu da wani bangare na farincikin rayuwarta dan a yanzu babu wanda take jin dadin zama da sun irin kawayenta friends ne iri-iri maza da mata, taji zafin rabuwa dasu musamman ma wadanda ba garinan suke ba, haduwa zata yi musu wahala sai dai gaisawa a waya da sauran hanyoyin sadarwa, lokacin da sakamakon. ya fito baka ga murna a wajen Safina ba, ta samu. sakamako na biyu mafi daraja wato second class upper, Babanta har kyautar sarka gwal ya bata, hatta Inna dake fushi da ita ba karamin murna tayi ba. Balle kuma yayenta maza yaya Ismail yaya Abbas, Umar da ma Usman, haka ma kannenta sukai ta tayata murna musamman ma Rahama da tafi kowa kusanci da ita.
Www.bankinhausanovels.com.ng
Zaman Safina a gida kafin fitowar takardunta na hidimar kasa ji take yi kamar akan kaya take, kwata-kwata bata jin dadin zaman gidan, sabida gidan ya yaye babu mutane sabida tuni yaya Umar da yaya Usman suka soma aiki a Abuja gashi an aurar da Naja’atu da Fatima dadin akan Rahama da aka aurar a shekara baya, sun zama ‘yan tsiraru a gidan daga ita sai kanenta Rabi’atu da Nusaiba sai kuma dan autansu Aliyu, gidan shiru babu abokan hira tunda daisu Rabi’a yara ne ko da yake ina ma taga lokacin hirar, ko ayukan gida kadai sun ishe ta domin ba a yi musu tarbiyyar barin iyayensu da aiki ba duka su suke aiyukan gidan.
Koda ta gaji da zaman kadaici sai ta
yanke shawarar koyar tuki dama ta dade tana da
burin ta koyi tukin mota kuma yanzu ta samu
dama, direba guda Alhaji Nura ya ware mata
yake koya mata mota domin yana da burin
.mallaka mata motar da zarar sunyi aure, ba a
dauki wani lokaci mai tsawo ba hannunta ya fada.
Tun bayan data gama makaran take dari darin kar ayi mata maganar aure saboda yanda ta lura idanun kowa yana kanta, sai kuma aka yi sa a babu wanda ya yi mata maganar in ka dauke Inna wacce a kullum ba ta da aikin da ya
Www.bankinhausanovels.com.ng
wuce wannan, amma ita mitar Inna sam bata daga mata hankali domin in da sabo ta riga ta saba, da ma Babanta take ji sai kuma aka yi sa a bai yi mata maganar ba. Tuni Safina ta daukewa kanta zuwa kauyensu dan ta samawa kanta lafiya daga irin surutan da suke yi mata domin sune suka fi kowa damuwa da zancen aurenta, duk kokarinta na ganin ta nisanta kanta da duk wani abu da zai ja mata ɓacin rai amma ran nan kwatsam sai ga yayan Babanta da kuma kanninsa sun zo takanas tun daga kauye kan batun aurenta,ba karamin daga mata hankali suka yi ba domin yayan Babanta har wa’adi ya dibar mata na wata uku idan bata fito da miji ba zai zabar mata mijin da kansa, bada wasa yake yi ba domin kuwa tasan halinsa na fada da cikawa, mutum ne mai zafi da bai lamuntar wargi, haka suka yi mata tatas daga ita har mahaifiyarta suka tafi suka barta cikin matsanancin kunci, bacin raida kuma tashin hankali kwanaki biyu a tsakani ta sama warakar damuwarta, domin kuwa takardunta na tafiya bautar kasa sun fito, rasa inda zata saka kai tayi domin murna sabida ta samu damar kaucewa shingen da aka saka mata, haka zata yi ta yaudarar su Inna tana dauke hankalin su Baba har sai ta samu irin mijin da take so, ba wai
Www.bankinhausanovels.com.ng
samari ne bata da su ba, har yanzu bata yi katarin gamo da namijin daya hada duk abinda take da bukata ba, duk wanda ya zo gani take yi tafi karfinsa, haka kuma bai hana i
dan sun yi mata kyauta ta bajinta ta karba ba, idan taga mai alamar mamora ne zata saurare shi idan kuma ta raina kurar mutum kallo daya zata yi mai ta taka mai birki ya kama gabansa, ganin haka yasa mutane da yawa masu sonta suka janye jikinsu dan su tsira da mutuncinsu. Duk irin abubuwan da take yi babu wani lokacin data taba tsayawa ta yi karatun ta nutsu balle har tayiwa kanta fada, koda yake ai mai hankali ne kadai ke gane furfura a jikin tunkiya.
Tare da Nafisa suka je karbo takarda na su na jihar Bayelsa aka tura Safina ita kuma Nafisa jihar Ogun.
Safina ta dafe kirji tace “Na shiga uku, yanzu ni ina na san hanyar zuwa wata Bayelsa, abin tsoro ma kaje kudun nan rikici ya barke a kasheka a banza a wofi abar ‘yan uwan ka da kuka.
Nafisa ta yi murmushi tace “Wato ke rigima ma kike tsoro? To ai akwai abinda yafi rigima ma tsoro”.Mene ne shi?” Safina ta tambaya..
Www.bankinhausanovels.com.ng
“Bayelsan nan fa a take wato yankın Naija-Delta, kin san yayana a River state ya yi bautar kasar sa ce min ya yi lokacin da suka je yawo aka dinga yi dasu ana kada musu kararrawa kamar wasu kayan gwanjo ana shelar wai kar wanda ya tabasu kayan gwamnati ne, banda an yi hakan da tuni sun zama tarihi”.
Safina ta kara tsurewa “Wai har naman mutane suna ci? Wallahi babu inda za ni ni dai tsoro nake ji”.
Nafisa tace “To yanzu ina mafita?”. Safina tayi ajiyar zuciya kawai ba tare data ce komai ba.
Nafisa tace “Da mu matan aure ne shi ne za su iya yi mana alfarma su canja mana bayan mun yi orientation”. Safina ta rasa abinda yake yi mata dadi, tunaninta ya tsaya cak saboda fargabar yanda mutanen gidansu za su karɓi al’amarin musamman ma Inna da kuma uwa-uba ‘yan uwan mahaifinta na kauye, kila duk wahalar karatun da tasha ta tashi a banza kenan, kila bata da rabon zuwa bautar kasa.
Nafisa ta katse mata tunani “To mai zai hana ki tuntubi Alhaji Maitama tunda kin san yanda harkar kasarnan take, kawai idan kasan wani shike nan, ina ganin tunda ya san manya mutane ya yi cuku-cuku idan zai yiwu a dawo da
Www.bankinhausanovels.com.ng
mu Arewa muyi abin mu”. Safina ta sauke ajiyar zuciya “Lallai kin kawo shawara zan tuntube shi”. Haka kuwa aka yi suka tafi orientation amma ga mamakinta sai taji dadin zaman Bayelsan fiye da zatonta, ji tayi ina ma tayi zamanta anan har ta gama bautar kasa. Ashe duka tsorata mutane ake yi akan zuwa kudu amma babu komai a cikinta, tayi abokai maza da mata wadanda suka zo daga wasu jihohin daban-daban, tana matukar jin dadin zama da abokanta, kasancewar sun fito daga kabilu daban-daban lokacin da suka gama orientation sai taji bata son baro garin, duk da cewar rayuwar camp akwai kalubale amma duk sai taji bata son baro camp din, sam bata son kowama gida musamman ma idan ta tuna da irin halin matsin lambar da take ciki akan batun auren, tasan Baba zuba mata ido kawai ya yi dan yaga iyakar gudun ruwanta, duk ranar data kaishi karshe ba zata ji da dadi ba,musamman ma Inna da kamar ta dauketa ta kaita gidan miji saboda irin matsuwar da tayi taga ta yi aure.
Kafin ma su dawo daga orientation tuni Alhaji Nura ya gama yi mata komai game da inda zata yi bautar kasa, ya yi sa a an dawo da ita gida Kanon Dabo, abinka da harkokin kasar nan in dai kai wani ne ko kuma ka san wani shi
Www.bankinhausanovels.com.ng
kenan, nan da nan aka samar mata gurbi a ministry of works and housing (ma’aikatar aiyuka da gidaje) Ta ji dadin irin tarbar da aka yi mata a ma’aikatar, karramata suke yi sosai ganin wanda ya kawota babban mutum ne, su uku ne a ofis din da aka ajiye ta, namiji daya da wata kabila suna nuna mata komai a matsayinta na sabuwar ma’aikaci, duk abinda ya yi mata tsauri kuma saisu karba su yi mata, da yake tanada kwazo da maida hankali kuma tana kula da duk abinda ake koya maya, gashi kuma tana da wayo da kissa da ladabi da girmama na gaba nan da nan sai ta siyesu, shi yasa basa nuna mata kyashi.
Bautar kasar yana tafiya daidai rannan bayan ta baro ofis ta biya bankinda take ajiye kudi zata fitar da wasu kudade da Alhaji Nura Maitama ya turo mata, account ne daba wanda yasan tana da shi.ba
Bata samu nasarar fitar da kudin ba ta A.T.M, hakan ne ya tilasta mata shiga cikin banki dan tayi korafi ko kuma tayi amfani da check, koda ta yi korafi sai aka ce mata wai accout din nata ya samu matsala yanzu haka ma kudaden da ke cikinshi an yi suspending dinsu, ba za a iya cire ko sisi daga account din ba, hakan ya biyo bayan wani yunkuri na un-authorise used da aka yi akan account din nata da ake zargin barayine
Www.bankinhausanovels.com.ng
suka yi, hakan ne ya tilastawa bankin suka rufe account din kuma aka ce mata wai sai ta ga mataimakin manajan banki.
Ba ta da wani zabi dan haka ta tafi ofis din mataimakin manaja da aka yi mata nuni da shi, da zuwanta ta kwakwasa kofar daga ciki ta ji an ce “Yes come in”. Ta murda kofar ta shiga, ta yi zaton zata ga wani babban mutum a matsayin ma’aikacin manaja amma ga mamakinta sai taga wani dan siririn saurayi mai ruwan Larabawa, idan har ba balarabe bane to kwara ne, domin kuwa farin shi ya so ya yi yawa, kyakkyawan gaskene mai doguwar fuska da dogon karan hanci, bakinsa dan karami, labbansa kuma ja zur kamar an zizara musu janbaki sai sheki suke yi, sumarsa akwance take har keyarsa, kwantacciyar girarshi mai yalwar gashi ta kusa
gadewa da juna. Ya bude baki tare da nuna mata kujera “Have a seat”.
Sai taga hakoranshi farare tas kamar bai taɓa tauna wani abu da su ba, hakan ya dada fito da kyansa sosai, tayi maza ta dauke idonta daga kanshi domin gudun karta kasa daukewa idan tadade tana kallonshi, irin bayin nan ne da ubangiji yake halitta wadanda kyansu yafi karfin misali.
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG