IN AN KI JI (BA A KI GANI BA) BOOK1 CHAPTER 16 KARSHE BY ZAINAB LAWAN BIRGET

IN AN KI JI (BA A KI GANI BA) BOOK1 CHAPTER 16 KARSHE BY ZAINAB LAWAN BIRGET

Www.bankinhausanovels.com.ng 


Mun tsaya 

Zai iya yuwuwa a yanzu jinin naka ya hau sakamakon wata razana da ka yi ko kuma wata matsananciyar damuwa daka tsinci kanka a ciki, amma kar ka damu insha Allahu zamu shawo kan matsalar, idan har kabi shawarwarin da za mu baka ka kiyaye ka’idojin tunda abin baiyi nisa ba, kayi kokari ka rage yawan tunani, sannan ka

kawar da duk wata damuwa da kake tare da ita, kuma ka kiyaye shan magunguna akan ka’ida, idan kabi wadan nan ka’idojin zaka iya zama lafiya ba tare da ciwon ya ci gaba da bunkasa ba, Allah ya bada lafiya”. Likita ya juya ga Iliyas yace.
“A dinga kula da mara lafiya sosai domin kasan hypertensive patients suna bukatar kulawa sannan kada a rika barin shi a cikin hayaniya ko cikin jama’ar da zasu dame shi, a rika bashi kwarin guiwa ana kuma kwantar masa da hankali da kalamai masu dadi kar a dinga sanar dashi wasu abubuwa na ɓacin rai ko tashin hankali”. Iliyas “Insha’ Allahu za a kiyaye mun gode likita”. Iliyas ya karbi takarda magunguna ya wuce pharmacy ya siya a maimakon su tsaya a shagon Sulaiman kai tsaye falon mahaifinshi suka wuce, abinka da dan dangi cikin kankanin lokaci gidan ya cika da jama’a da ‘yan uwa kowa ya zo duba shi, bayan ‘yan

dubiya sun lafa Hajiyar Sulaiman ta tsare Iliyas tana tambayar shi abinda ya same shi. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Wai shin wannan wane irin ciwo ne líkita ya gano a jikin Sulaiman? Domin mu duka a zaton mu ulcer gare shi saboda shi mutum ne mai sakaci da cin abinci, lokaci da dama yanda aka kai masa abinci haka ake fitowa dashi bai ci ba,
lokuta da dama sai yace min ai yaci a kasuwa”. Iliyas ya yi shiru kamar ba zai fada mata ciwon da yake damunsa ba, ta katse masa tunani da cewar “Amman kuma naga ciwon ya yi kama da ciwon asuma, dubi yadda numfashinsa yake kaiwa da komowa”. Jin wajen data karkata akalar tunaninta yace mata.
“Kar ki damu Hajiya zazzabin malaria ne mai zafi ya kama shi, a sakamakon gwaje gwaje likita ya gano jininsa ya dan hau”. Nan da nan Hajiya ta dafe kirji tare da rufe baki “Subhanalla yanzu shi kenan Sulaiman ya hadu da hawan jinni? To a garin yaya ya hadu dashi alhalin ko ni bani da hawan jini?”. Iliyas ya dan tausasa murya.
“Hajiya kada ki damu ba wani abu da yardar Allah zai warke cikin lokaci kankani tunda dan kadan ne yahau ba da yawa ba, kuma irin wadan nan ciwukan zamanin ba dole sai anyi gadon su ba, ba kuma yawan shekaru bane yake kawo su ba, jarrabawa ce kawai irin ta rayuwa”. A sanyaye zuciyarta cike da karaya tace “To Allah ya bashi lafiya”. Iliyas ya amsa da Amin “Amman Hajiya zan so mu tafi da shi can gidana domin anan mutane za su yi ta damun shi da hanayaniya kuma gashi likita yace akwai bukatarya samu hutu sosai, Hajiya tace idan katafi dashi zaka takura kanka tunda kaima ba iyali gareka ba kuma sännan kana zuwa aiki, yace ba damuwa zan kula da shi yanda ya kamata, idan zan tafi aiki Ahmad sai ya dinga zuwa yana kula da shi tunda haka ne sai ku tafi Allah ya yi muku albarka ya kuma kara hada kanku, Iliyas ya mike yana amsa wa da Amin Hajiya, har bayan fitarsa addu’ar dai take ci gaba da kwarara musu domin Iliyas amini ne babu abinda za su ce da shi sai addu’a ya tallafi rayuwar Sulaiman ta hanyoyi da dama, fatanta Allah yabar amincin nasu har karshen rayuwarsu! Www.bankinhausanovels.com.ng
Tun daga lokacin Sulaiman ya koma karkashin kulawar Iliyas ya ci gaba da jinyarshi yana kara kwantar maida hankali, yana bashi baki da kalamai masu dadi yana debe mai kewa sosai, ga abinci na musamman reduced sait meal  da ake shirya mai daga gidansu Iliyas din kasancewar shima ba aure gareshi ba, idan ya tafi aiki kuma Ahmad ne yake zuwa yana kula da shi, da haka har Sulaiman ya soma warwarewa ya samu sauki.
A nan ma bai huta da zuwa ‘yan dubiya ba domin ‘yan uwa da abokai suna ta zuwa duba shi. Bayan sati biyu Iliyas ya dauke shi suka sake komawa asibiti kamar yadda likita ya bada umarni, bayan an sake auna blood pressure din Sulaiman ansamu nasara jinin ya dan sauka da kaso goma, likita ya sake rubuta magunguna sannan ya kara bashi shawarwari muddin kana son lafiyarka ta dore to dole ne sai kabi dokokin da aka gindaya maka, yanzu kaga jininka ya fara sauka don haka sai ka ci gaba da shan maganin da sauran kaidojin da aka doraka akai, insha Allahu cikin kankanin lokaci jininka zai dawo normal za a nemi hawan jinin a rasa,suka yi godiya suka mike.
Har yanzu Iliyas bai samu yadda yake so ba, akan Sulaiman domin dai har yanzu bai sanyawa zuciyarshi dangana game da lamarin Safina ba, nutsuwa ta yi karanci tare dashi, bashi da aikin yi daga yawan tunani sai zancen zuci a lokuta da dama ma har akan ga bakin shi yana motsi yana surutu shi kadai, wannan ba karamin dagawa Iliyas hankali yake ba, abin ya dame shi sosai ya rasa yanda zai yi da Sulaiman domin yau ma daya dawo daga aiki ya tadda Sulaiman shi kadai a cikin daki ya yi tagumi ya yi jugum yana tunani, takaici ya kama Iliyas domin ya baro Ahmad a falo yana kallo shi kadai ya tsani
wannan kadaicin da Sulaiman yake yi sam ya kauracewa shiga cikin mutane ya nesanta kanshi da duk wata walwala da nishadi, ya aro tsananin damuwa da bakin ciki ya dorawa kansa, Iliyas ya yi sallama wajen sau biyar batare da Sulaiman ya amsa ba hasalima bai san da shigowar iliyas din ba hankalinshi yana can ya lula duniyar tunani saida Iliyas din ya yi gyaran murya sannan Sulaiman ya yi firgigit ya Ankara da shigowar shi cikin bagararwa yace.
“Barka da shigowa yaushe ka iso ne?” Iliyas yaki amsawa sai wani kallo daya bishi dashi mai cike da ma’anoni da yawa, ina da zaka ji na shigowata tunda kana can duniyar tunani? Ka riga ka yi nisan da baza ka ji kira ba, Sulaiman yace.
“Kada ka damu dan uwa ni babu duniyar dana shiga ina tare da ku”, Cikin damuwa yace. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Mai yasa baka tausayin kanka? Ko bakabar tunani don komai baya kamata ka bari domin tsira da lafiyarka, ka tuna fa halin da kake ciki, kasan dai dokokin da likita ya kafa ma”, “kayi hakuri tunani bayin kaina bane, hakan nan nakan. ji damuwa a cikin zuciyata sai tunanin wasu
al’amura su dame ni nan da can”. Iliyas ya rufe shi da fada dan haushi.
“Wai shin kai haka zaka dauwama, cikin kunci da bacin rai? Haka rayuwarka zata ci gaba da tafiya babu sauyi? Haka kake so muma ‘yan uwanka mu kasance cikin rashin walwala da nishadi mu dinga rayuwa babu dadi saboda halin daka jefa kanka a ciki? Duk kabi ka tsangwami rayuwarka saboda ka rasa mace daya? To shin idan Safina ta mutu kaima ka daina rayuwa kenan?”.
“Idan Safina mutuwa ta yi zan dangana na yi tawakali na ci gaba da yi mata addu’a amma ka tunafa a yanzu kiri-kiri tana raye da ranta da lafiyarta ta zabi wani na, ta zabi wani ba niba sabida tsabar butulci irin na ‘ya ‘ya mata, ta ya bazan koka ba”. Nan take hawaye ya wanke masa fuska ganin hawayen sa yasa Iliyas ya dan sassauta “Haba Sulaiman kasan ganinka cikin
wannan halin yakan jefani cikin damuwa,Sulaiman
bana son naga bacin ranka bana son ganinka cikin kunci da taskun rayuwa yanayin da Safina ta jefaka nima ya sanya ni cikin kunci kullum da bakin cikin nake kwana da shi nake tashi, haba dan uwana shin ba zaka tausaya min ka dawo da farin ciki a cikin rayuwarka ba”.Nan da nan shima sai kwalla ta fara zubo masa, Sulaiman ya taso ya iso gare shi ya dafa shi.
“Kayi hakuri abokina nima bana son damuwarka, bana son zubar da hawayen ka, ka fadi yanayin da kake son ganina a ciki na yima alkawarin zan maida kaina irin yanda kake son ganina”. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Yauwa abinda nake so dakai da farko kasa a ranka don ka rabu da Safina bashi ne karshen rayuwarka ba, ba lallai sai da ita zaka yi farin ciki a rayuwa ba, kana da ‘yanci da sauran damar da zaka nemo farin ciki da nishadi a rayuwarka, ina son daga yau ka cire wata halittar Safina daga zuciyarka, ka shafe babinta daga rayuwarka, ka maida soyayyarta wani abu da bashi da amfani a wajenka ka tattara ka zubar a bola, ita da soyayyarta ka mayar da su tamkar matattu ka binnesu da zarar tunanin Safina ya bijiroma ka daina tunata a matsayin masoyiyya sai dai mayaudariya maci amanar kaúna, sannan idan ka dage da addu’a sonta ba zai yi wuyar gogewa daga cikin zuciyar ka ba, daga nan kuma sai ka zama gwarzon namiji ka zama jarumin kanka ka dinga jan ragamar zuciyarka kana tursasata kana nuna mata ba lallai ne tasamu duk abinda take so ba, shi kenan sai zuciyarka ta saba, sai ka dinga sarrafa ta irin yanda kake so, a sannan ne zaka bude sabon shafin rayuwa wadda babu Safina a ciki, sabuwar rayuwa zaka tsinci kanka mai cike da armashi babu son kowa a zuciyarka sai son Allah da Ma’aikinsa da kuma soyayyar wadanda suke sonka, a lokacin kai kanka zaka yi mamakin irin rayuwar da zaka tsinci kanka a ciki mai cike da walwala da nishadi babu damuwar komai a ranka”, wadannan dogayen bayanai na Iliyas su suka sa Sulaiman ya kyalkyale da dariya wadda rabon dayayi irinta tun kafin ya tsinci kansa a cikin wannan yanayin yace.
“Karka damu abokina in dai cirę Safina daga zuciya kake bukata to daga yau na goge Safina, sonta, kaunarta da duk wani abu daya shafeta daga zuciyata har abada na cireta daga rayuwata kenan, na barta bari na har abada wanda ba zan sake tunata ba”. Iliyas ya ware hannunsa cikin farin ciki suka rungume juna, bayan ya sake shi ya dauko takardun daya shigo da su ya mika masa, cikin doki ya bude takardun admission ne Iliyas ya samo mai, D.E ne wato Direct Entry inda zai je ya dora karatun Www.bankinhausanovels.com.ng digirinsa, ya rungume takardun yana murna Iliyas yace. “Fatanmu dai Allal ya baka lafiya ka wartsake sosai, sai kaje kayi registration da kanka”. Sulaiman cikin tsantsar farin ciki da doki yace “Nifa ko yanzu na warke garau nake jina, a shirye nake ko da a gobe za a fara lakca, ni Sulaiman ina maraba da wannan sabuwar rayuwa da zan fara”. Cikin murna shi Iliyas yace “To Allah ya sa kafara a sa a, amma kayi hakuri ka bari sai ka warware tukunna sai ka yi registration din da kanka domin akwai ragowar lokaci kafin a rufe”. Sulaiman ya gyada kai.
“To amma yaya maganar kasuwancin da muka yi kwanakin baya domin da Hajiya ta zo kwanakin baya na bata umarni a saka gidan a kasuwa domin za mu yi kasuwanci da kudin, itama taji dadin haka tace na hada da gonarta domin mu samu isasshen jari ka san gonar tana da girma sosai, shi kenan idan kudin suka samu sai mu fadada harkokin sosai da nace atamfa da shaddodi kawai zamu dinga shigowa da su, to yanzu tunda munsamu isasshen jari sai mu dinga hadawa da electronics da shigo da kayan kitchen”.
“Good wannan shawara ce mai kyau Allah ya rika mana yasa afara a sa’a”.Da sannu cikin ikon Allah Sulaiman ya warware tare da taimakon dan uwa amininshi Iliyas domin koda yaushe cikin jan hankalinsa yake tare da bashi shawarwari, a koda yaushe maganarshi daya ga Sulaiman idan har ya bari ciwon Www.bankinhausanovels.com.ng damuwa ya kayar da shi tofa babu ruwan Safina, ‘yan uwan shi da masoyan shi kawai za a bari da rashinsa, dan haka ya daure ya taimnake su kada ya kassara kanshi, Sulaiman ya san gaskiya aka fada masa dan haka karfi da yaji ya cire Safina daga layin masoyan shi, ya dawo da  farin ciki rayuwarsa, domin ya fuskanci rayuwa ta gaba wato rayuwar karatunsa da kasuwanci su.  Kasuwancin nasu ya kankama, kuma da
alama akwai haske da nasibi a ciki domin da jarinsu mai kauri suka fara harkar.

Alhamdulillah mu hadu a littafi na biyu domin jin makomar Sulaiman da kuma Safina dama irin tataburzar dake tafe cikin ‘yan matancin Safina.

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *