IN AN KI JI. (BA A KI GANI BA) BOOK1 CHAPTER 2 BY ZAINAB LAWAN BIRGET

IN AN KI JI. (BA A KI GANI BA) BOOK1 CHAPTER 2 BY ZAINAB LAWAN BIRGET

Www.bankinhausanovels.com.ng 


Mun tsaya 

Gani na yi ta yi kama da amarya”. Inji
Sulaiman. Www.bankinhausanovels.com.ng
Rahama ta danyi dariya “Au, su amaren
har wata kama garesu? To baka canka daidai ba
domin ita wannan da kake gani ko shekarar
aurenta ma bata kama ba, karatu take son yi mai
zurfi…” Sulaiman ya katse Rahamna ganin ya ji
abinda yake bukatar ji Wato dai allurer ruwa ce
mai rabo ka dauka?”

“Haka ne” Rahama ta amsa masa a
takaice.
Kice nima na shiga sahun masu nema
ko ni ne mai rabon?” Inji sulaiman.
Rahama tace “Mai zai hana, Allah ya
bada sa’a”.
Sulaiman yace “Ni fa da gaske nake
shin za ki bani kawar nan taki kuwa?”
“Ai bansan inda rana zata fadi ba, ka
gwada sa’arka ko Allah zai sa ka dace, amma ba
kawata bace ‘yar uwata ce”.
Wasa-wasa sai gashi har Rahama ta
yiwa Sulaiman cikakken kwatancen gidansu. Duk
hirar da suke yi Safina tana jinsu amma tayi shiru
tare da hade rai tana kallon wani sashen daban
lokaci-lokaci kuma takan harari Rahama ganin
yanda ta saki jiki tana kwatanta masa gidansu
harda fada masa sunayen su. Ita kanta Safina
gayen ya Cijeta matuka, fari ne dogo, sumarshi a
kwance luf-luf abin sha’awa, kyakkyawane sahun
farko gashi kuma dan kwalisa mai kashewa kansa
kudi, da ganin suturar dake jikinsa da kuma jin
irin tsadadden turaren daya sanya ka san babban
yarone, alamun hutu da jin dadi duk sun bayyana
a gareshi, ya fi kama da manyan ‘yan kasuwa ko
manyan ma’aikatan da suka kama kasa.
cikin dan takaitacen lokaci Safina ta

Www.bankinhausanovels.com.ng
nazarci haka daga gare shi, saidai ko kUsa bata yi
wani na’am dashi ba domin baya CIkin tsarin
sahun mazan da take burin aure, akwai wasu
sharudda da take burin mijin aurenta ya kasance
ya cika su data lura shi Sulaiman din bai cika suba
a, hakan ne ma ya sanya ta .taki sakar masa
fuska.A karshe Sulaiman ya yi musu
gagarumin rangwame a kudin atamfofin da suka
siya duk daya rubuta ainihin kudin kayan ne a
cikin kundin da yake rubuta kayan da aka siya, da
alama shi ne zai cikasa kudin a aljihunsa sun rabu
tare da alkawarin zai kawo muzu ziyara har gida
domin su samu damar tattaunawa a cikin tsanaki,
shi ya yi musu rakiya har bakin titi ya nemar
musu adaidaita sahu drof wanda zai kaisu har
kofar gida.
Sai da suka fara tafiya sannan Rahama
ta dubi Safina cikin tsokana tace “Wai yau kurmar
karfi da ya ji kika zama ne? Kina jina da mutum
amma kin ki kice komai?”
Safina ta tabe baki To me kike so nace
alhalin kin tsaya kinà zuba harda kwatanta masa
gidanmu?”
Babu wani zancen zuba, ni dai kawai
ina goyon bayanshi ne, Allah ya tabbatar da
alheri, na lura yana da saukin kai kuma ga
kamala dan haka nake kyautata masa zato”.
Safina ta dan murmusa tace “Gaskiya
yana da kirki da son jama’a gashi kuma
kyakkyawa ne na gaske, sai dai duk da haka…”
Bata barta ta karasa maganar tata ba ta katseta
Ya isa haka Safina, kin fadi abinda ya kamata ki
fada amma na san abinda kike shirin fada a gaba
ba alkhari bane, kar kiyi kokarin furta kalaman
batanci akan shi kamar yadda kika saba yi akan
sauran samarin, kin dai. ga irin karamcin daya yi
mana, bai kamata ki saka masa da haka ba. Koda
ya zo gida dan Allah ki daure ki saurare shi tunda
babu wanda yasan abinda zai faru gobe”.
Safina ta yi kwafa tace “Amma dai kin
san bana raayin irin wadannan samarin ko?
Burina shi ne na auri wani gawurtaccen dan book
kuma kusa sosai ko kuma hamshakin dan
kasuwar da ya amsa sunan sa, kuma kin fi kowa
sanin haka, amman mai ya saka kike so na baiwa
wannan gayen dama alhalin bashi da kudin da zai
iya samar min da daular da nake burin samu a
gidan aure, kina gani fa a karkashin wani yake
abinda yake samu baifi ya kashe gararin gabansa
dashi ba balantana har ya iya daukar Www.bankinhausanovels.com.ng
hidimomina”.
Wani irin kallo Rahama ta jefi Safinà da
shi “Wato har yanzu kina tare da wannan dogon
burin naki? Matsayina na yar uwarki bazan daina
baki shawarar dana saba baki a kullum ba, yana
da kyau ki bar wannan hange-hangen domin
kuwa babu inda zai kai ki, duk mai mutuncin daya zo wurin ki baki tsayawa ma ki saurare shi balle
har ki basu damar ku fahimci juna”.
Safina ta yi wata wulakantacciyar dariya , a yatsine tace “Taya kike tunanin zan bata
fassara raina abinda lokacina
wajen saurarensu
alhalin babu wand azan iya yin soyayya dashi a
Cikinsu? Idan har na sake na auri daya daga
Cikinsu ai na ruguza wa kaina rayuwa na kuma kwari
Rayuwata tunda mafarkan da nake yi ba za su zama
gaskiya ba, burina ba zai cika ba”.
Cikin mamaki Rahama tace “Wadanne
irin burikane da har kike tunanin ba za su cika
ba?”.Safina ta murmusa “Kar ki damu da
sannu za ki sansu”.
“Me yasa kike tunanin su ba za su iya
cika miki burinkan ba Rahama ta sake tambaya.
“Juma’ar da zatai kyau tundaga
labaraba ake ganeta, su wadannan suma da kike
gani a kanki kansu basu da tsarin mai kyau, ba
kuma za su iya tsara min rayuwa mai kyau ba,
zan raba burina na samun rayuwar daula a nan
gaba”.
Mai adaidaita sahun yana jinsu suna ta
tafka mahawara a tsakaninsu a karo na farko ya
sanya musu baki da cewar “Yar uwa ke dai kawai
ki roki Allah ya zaba miki miji nagari, amman
wani zabe ba naki bane, ki yi fatan samun rufin
asiri da kwanciyar hankali a gidanki,  akan
zaci wuta a makera amma a isketa a masaka,
abinda kike hange sam bashi bane”.
Safina ta kalleshi kallon sakarci “To
mallam na ji na gode”. Amma a ranta kallon dan
sheda ta yi masa “Ko _ina ruwan shi da maganar
mu? Wani kidahumi dashi me ya sani game da
halin da duniya take ciki da har zai yi min
wa azi?” Ta fada a cikin ranta.
Da yake Hausawa sun ce raayi riga,
kowa da irin ta shi, Kallon da Rahama take yi wa
maganganun mai adaidaita sahun ya sha bamban
da kallon da Safina take masa, domin ita ta gamsu
dari bisa dari da abinda ya fada, gashi dai ba
wani Babba bane amma ya fahimci rayuwa daidai
gwargwardo, Bature ma cewa ya yi Maturity is
not just the accumulation of years, it is the
collection of experiences and their intensities”
Shi kuma mai adaidaita sahu a na shi
Bangaren sai ya raina wayon Safina tuni ya gano
bata da zurfin tunani gata dai tamkar wayayya
amma ashe bahaka abin yake ba, da ma masu
azanci zance suna cewa “Do not judge book by its Www.bankinhausanovels.com.ng
cover” Ita a zatonta auren mai kudi da rayuwar
babbar gida shi ne jin dadi, bata san s
amun miji
nagari da zaman lafiya sun fi komai dadi. Ko
kuma dan taga tana da tsantsar kyau shi yasa
take yiwa maza yanga? Wannan ce tambayar da
ya yiwa zuciyarsa da bai samu amsarta ba.
**
Shi kuma Sulaiman tafiya suka yi suka
barshi da tunani, har aka tashi daga kasuwa babu
hirar da yake yi da ‘yan shagon na su sai zancen
Safina, ta riga ta tafar masa da zuciya fatansa bai
Wuce na samun nasarar shawo kanta ba idan ya
je gidansu a matsayin bakonta.
Bayan ya koma gida ma bai fasa
zancenta ba, musamman ma da suka hadu da
amininsa Iliyas. Koda Iliyas yaji zancen Safina
yaki karewa wajen abokinsa sai ya kada baki yace
Wai me ka gani tare da yarinyar nan ne da naga
ka rikice akanta haka?”
Kamalarta, kamun kanta da kuma
tsantsar kyawunta su suka ja hankalina gareta
har na kasa boye abinda yake raina saida na Isar
da sakon zuciyata duk da cewar Alhaji yana
shagona a lokacin, tana da matukar kyawu fiye
da zatonka gashi ta iya kwaliya, hakika idan na
samu yarinyar nan a matsayin matata ba karamin
dace na yi ba”.
yas ya yatsino fuska kana yace
“Abokina bana son ka rika kallon kyale-kyale
wajen zaben budurwa, kyau babu kyan hali
tamkar shayi ne babu sikari, yana da kyau kayi
duba zuwa halayenta dan gudun yin kitso da
kwarkwata”
Sulaiman ya ce “Nima ban yi la’akari da
kyanta kadai ba, na fahimci tana da nutsuwa da
kamun kai, da alama yarinyar yar babban gidace,
ina da tabbacin cewa sun samu kyakkyawar
tarbiyya domin itama yar uwarta haka take”.
To Allah ya tabbatar da alkhari” Inji
Tliyas.
Sulaiman yace “Yauwa abokina addu’ar
da nake bukata kenan domin ban sani ba ko zan
samu karbuwa a wajenta ko kuma akasin haka na
lura tana da jan aji idan don idan ba sa,a nayi ba
watakila ta danwanani kafin ta karbi soyayyata”
Babu laifi lokacin da Sulaiman yaje
wajen Safina ya samu shimfidar fuska, ta yi mai
kyakkyawar tarba. Ta saki fuska fiye da ranar da
ya fara ganinta, dama ba wai son shi ne bata yi
ba domin bashi da wata makusa da za a kishi
akanta, kawai dai bata yi naam. dashi bane
saboda tana ganin kamar tafiyarsu ba zata
doreba tunda bashi da irin makudan kudaden da
take hari.
Wanka wata shadda ya yi ash colour,
dinkinsa mai kyau filtex da ya dace da zubinsa,
matashi ne dake kan ganiyarshi ta samartaka,
gaye ne da zata iya shiga dashi ko ina kuma ya
fitar da ita kunya domin kuwa ya hadu,
matsalarsa kawai bashi da abokan rayuwa(masu
gidan rana). Www.bankinhausanovels.com.ng
A cikin hirar tasu ne ya gabatar mata
da tarihin rayuwarsa a takaice kamar haka
“Sulaiman shi ne sunana kamar yanda kika sani ni
haifafen kwaryar birnine a unguwar gabari, na yi
karatun firamare da sakandire dama makarantar
gaba da sakandire duka a birnin kano. Banyi wani
zurfin karatu ba, diploma na yi na dakata inda
na tsunduma kasuwanci saboda yanayin rayUwa,
Sai dai ina sa ran ci gaba da karatu anan gada
idan damar hakan ta samu”.
“Kimamin shekaru biyar da suka wuce
Allah ya yiwa Mahaifina rasuwa gidanmu gidane
na iyali domin ina da yayye da kuma kanne, mu
goma sha uku ne ya yan mahaifinmu. Ina da
amini kuma dan uwa mai suna Iliyas tare muka
tashi da shi tun muna yara, kowa yasan mu yana
da matukar muhimanci a rayuwata, ina fatan
kema za ki dauken da muhimmanci kamar yadda
yake a wajena ina fatan kin gamsu da dan
takaitaccen tarihin dana sanar dake game da
kaina, idan kuma akwai wani abu da kike son ji
game da ni wanda ban fada ba sai ki tambaye
ni
Safina ta girgiza kai cike da gamsuwa
da bayanansa, itama ya tattambayeta wasu
abubuwa ta bashi amsa daidai gwargwado, duk
da cewar basu dade suna hirar ba amma sun
tattauna batutuwa masu amfani da suka shafesu,
sun fahimci abubuwa sosai game da kawunansu.
Kyauta ta farko da Sulaiman ya bata ya saka ta
soma sauya tunani akan shi, kyauta ce ta bajinta
da kuma nuna tsantsar kauna ga wacce yake so,
babu shakka idan ya ci gaba a haka to tafiyarsu
zata dore, ta yarda da azancin nan da Hausawa
suke cewa, mai zuciya ake fadawa biki ba mai
dukiya ba, ta lura Sulaiman din yana da zuyciyar
da zai iya yi mata duk abinda take so duk da
cewar bashi da tarin dukiya.
WACE CE SAFINA?
Sunan Mahaifinta Alhaji Yusuf Bala
tsohon Mallamin Makaranta ne a kwalejin ilimi ta
tarayya dake nan Kano wato F.C.E Kano, yana da
mata guda biyu Sa adatu wato Inna da Asiya
wato Umma, Inna ita ce Mahaifiyar Safina kuma
tana da ya ya shida, ya yin da ita kuma Umma
mahaifiyar su Rahama take da ya ‘ya biyar
JImulla goma sha daya Www.bankinhausanovels.com.ng
Gidajen na lyali da aka ginashi bisa
doron hadin kai da kaunar juna, yaya Isma’il ne
Babba likitan zuciya ne (cardiolost) a babban
asibitin kasa dake Abuja yana da matarsa Kubra
da yarsa Amira a can Abujar suke amma yakan
zo ganin gida duk bayan sati biyu, yaya Abbas shi
ne na biyu, shima a bangaren kiwon lafiya yake,
likitan kashi ne (othorpedicst) a Asibitin kashi na
Dala, akwai yaya Umar dakuma yaya Usman
wadanda suke karatu a jami’ar Ahmadu Bello a
halin yanzu, Safina ce kebin yaya Usman sai
kuma Rahama wacce tsakaninsu bai wuce wata

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *