INAAYA CHAPTER 3
Sound in alarm in wayan inaaya ya tashe su daga bacci su duka ukun kashe alarm in tayi tana duba wayan taga 5:42am ita ta fara saukowa daga kan gadon ta nufa toilet ta dauro alwala ta fito ta shimfida sallaya ta bude trolley nata ta fiddo wani long hijab na sallah ta saka ta kabbara sallah, saida tayi nafila sannan tayi sallah asuba tana zaune kan prayer mat in har ta gama karanta azkar inta sannan ta tashi tayi hanyan koma wa gado bata ma tsaya bi takansu mimi da inteesar ba saboda baccin dayake idonta haka suka gama suma sukayi joining in ta suka koma baccinsu.
9:00am na safe ringing in wayar shi ya tada shi har ta katse bai dauka ba sai dan siririn tsaki dayayi saboda baccin bai isheshi ba haka ya fada toilet kawai yayi wanka ya fito ya shirya cikin black sweat pants inshi da black riga yayi kyau kaman wani balarabe gashin kanshi ya kwanta sai kamshin turare yake mai dadi haka ya fito daga part in nashi ya nufa cikin gida, Ammah ce zaune a parlour sanye take da wani atamfa blue color dinkin boubou daga gefenta kuma ahmad ne da jallabiya a jikinsa kofa sukaji an turo su duka suka maida duban su ga kofan Aliyu ne ya shigo yana tafe a hankali har ya iso kusa da ammah ya zauna kan carpet Ahmad ya gaisheshi ya amsa masa lafiya lau sannan ya gaida ammah cikin cool murya “Ammah ina kwana An tashi lafiya? Ya gajiya?” Yafada a tare smiling ammah tayi tana “lafiya qalau my son gajiya ya bi lafiya Alhamdulillah hope
you’ve fully rested” amsa mata yayi da eh sannan tace ya tashi yayi breakfast dining ya nufa kai tsaye ya bude kulolin yaga dankali ne sai egg and pepper soup sai kuma wani kula dauke da yamballs, plate ya ja ya zuba yamballs guda uku da soup kadan ya zauna yafara ci a hankali, Bayan ya kammala cin abincin shi yadawo parlour ya zauna yana kallon Al jazeera da Ammah ta kunna kaman wanda ya tuna wani abu wayanshi ya jawo ya duba wanda ya tashe shi daga bacci gani yayi abokin shi ne fareed ya danyi tsaki sai kuma yayi murmushi hade da tashi yace ma ammah “ammah zan koma part ina but please ammah da rana inason nasha zobon nan irin na jiya it was so nice” kallonshi Ammah ta tsaya yi sai tayi yar dariya tace “to banda abunka aliyu ai daga gidan mamii mukazo dashi” har zai tafi yaji abunda ammah ta fada sai yace ” toh ammah ba sai a gaya wa mamii ba tasa ayi mani ko ma naje gidan nata yanzu har sai anyi mani na dawo dashi” smiling yake wanda ya kayatar da kyakyawan fuskan nashi ammah dariya tayi tana fadin “to yi maza ka tashi kaje kai dan mamii” haka ya fita daga parlourn da smile a fuskanshi.
Rai a bace inaaya ta tashi daga bacci saboda karan wayan mimi daya tasheta duka kawai ta kai wa mimi tana fadin “tashi your phone is ringing har ya ta da mutane bacci” tashi mimi tayi tana turo baki tana murza idanu ta mika hannu ta jawo wayan da har ya bar ringing caller Id in taduba taga cewa sultaana ce nan tayi saurin calling back ringing uku tayi akayi picking mimi tace “clap for yourself sulty you just woke us up”
Sultana~ohh come on babe just wanted to tell you guys get ready I’m coming over yanzu ba da dadewa ba ya habeeb zayayi dropping ina
Mimz~ ehh ehh me kikace? Ya habeeb is dropping you off wow can’t wait to see you sai kinzo
Sultaana~can’t wait to see me or the person dropping me? Sultaana ta fada ina a teasing tone ai kam kaman ana jira sukaji an fashe da dariya mimi ta juyo taga wayake dariya taga intee ce take dariya amma tana kwance idanunta rufe kaman mai bacci
Mimz~ ugh! You guys kuna da issues gotta go now sai kinzo bye! Mimi ta fada tana kashe wayanta ta ajiye shi ta juyo taga inteesar ta tashi zaune smiling tayi mata tace “good morning babe” amsa mata tayi da morning ta tashi ta nufa hanyan closet tana shiga intee ta kalla inaaya sukayi dariya inaaya tace ” poor girl she’s deep in love” shiru sukayi kafin intee tace “yess inee i can see but I just pray and hope she’s not breaking her heart cux you know how this guys are”
“Yess that’s right zainabuu and InshaaAllah she’s not cux i saw how he was looking at her I can’t say he likes her but he might and i pray he will” Amin sukace a tare kowa yayi shiru, inaaya ta jawo wayan ta taga miye time taga 11:50 and 4missed calls from sultaana ignoring kawai tayi don tasan ce mata zatayi zatazo so wayanta na silent shiyasa bata ji ba. After like 20 minutes mimi ta fito daga closet in tayi wanka ta saka wani black pencil jeans da top blue sai Abaya wani black yasha stones multi colored sai kamshi takeyi dagowa sukayi suna kallonta inteesar tace “iyyeh sissy is so fine MashaaAllah” smiling tayi tace thanks babyy, inaaya kuwa tashi tayi tace “let me take a bath too” tanufa hanyan closet in tare da jan trolley nata.After what seems like forever sai ga inaaya ta fito sanye da peach maxi skirt da black top sai ta daura black veil a kanta yayi kyau sosai duk juyowa sukayi suna kallonta data fito intee tace “kai wlh Alhamdulillah i have beautiful sisters yau kam picture day ne let me take my bath too we’ll snap tire” tana fadin haka tana saukowa daga gado ta fara tafiya tayi hanyan closet ta shiga ciki nan su inaaya suka zauna shiru kakejin su kowa busy with phone inaaya na duba whatsapp messages mimi kuwa was busy scrolling and checking on instagram(did i mention ya abby got her a new phone). Ko da inteesar ta fito they were all busy with their phones basuyi noticing inta ba nan ta ce “girls get your lazy ass up muje mu gaida Ammah muyi breakfast before sultaana tazo amd then we’ll plan for the day” sai a sannan suka juyo suka kalleta MashaaAllah tayi kyau cikin purple morrocan gown inta “MashaaAllah sis you’re also cute” suka fada, smiling tayi tace “ohh well FYI i know so let’s go” fita sukayi daga dakin su duka suka nufa parlourn kasa inda Ammah ke zaune har lokacin da Ahmad beside her yana shan tea yana scrolling wayanshi, karasowa sukayi duk suka zauna sannan suka gaida Ammah ita kam murmushi tayi masu tace “MashaaAllah my daughters are beautiful Allah yayi maku albarka” da amin suka amsa ahmad kam dagowa yayi ya kallesu one by one sannan yace “Ammah kar kija kansu yayi girma fa they’re the ugliest in the family” harara suka sakan mashi mimi tace “amadu you need good deliverance wlh may god deliver you” sukai ta mashi dariya har saida ammah tace ya isa su je dining suyi breakfast. Sai after zuhr prayer suna zaune a parlour suna kallon oceans eight a macbook din inteesar sai wayan mimi yayi ringing sultaana tagani tayi saurin dauka “hello sulty” daya bangaren sultaana tace “heyy you guys should come out now I’m at the gate i mean now fa!” Da sauri mimi tace ok ta kashe wayan tana gaya masu sultaana tazo tayi upstairs da guda ta nufa daki ta dauko Abayan ta tasaka ta yafa veil in a kanta tasauko kasa tagansu yanda ta barsu nan tace “let’s go tanafa jiran mu” pausing kallon sukayi suna nufa hanyan gate inaaya ta kwance dankwalinta ta yafa shi itama inteesar wani purple veil ne ta yafa suna fita sukaga motan ya habeeb suka karasa wurin motan, suna zuwa inaaya bata jira ba ta bude front seat tana “malama ai sai a fito ko” da smiling face in sultaana tace karo tace “oww my girls” ta
fito daga motan tana hugging inteesar nan inaaya ta gaida ya habeeb dake drivers seat yana sanye da jeans and shirt sun matukar masa kyau ya amsa da faraa nan intee ba ta bude back seat ta dan zauna itama tana gaidashi ya amsa yana cewa “wannan kaman zainabu ko” frowning inteesar tayi tace “haba ya habeeb wace zainabu thought ka bar sunan nan fa it’s been a year yakamata ka manta” dariya kawai yayi yana dan satan kallon wanda ke tsaye a waje ita kuma mimi tana nan tayi freezing a tsaye tunda ta ganshi ko moving da kasa yi nan suka fito motan suna mishi ban kwana bayan sun ciro trolley in sultaana daga boot in motan da wani backpack ash color, inaaya ce taje mata trolley in inteesar kuwa ta dauka backpack in sukayi hanyan gate mimi kam na biye da su ta kasa ce wa komai nan sultaana tace “oops! Na manta da sakon Ammah a mota da umma tace na kawo mata pls and please mimi ki dauko mani please be fast yana a front seat” kamar bazata je ba sai taga yanda sultaana ta marairaice fuska sai ta juya ta tafi. Dariya suka sa ka su duka inteesar tace “sultaana wlh baki da sauki can’t you see the tension between them da zaki ce taje” tana dariyanta tace “yess i know it’s intentional”. Tana zuwa kusa da motan har yayi reverse yana tafiya a hankali ta dan sa hannu alamun ya tsaya sai ya tsayar da motan a hankali take takawa har ta isa wurin motan ta bude sit in gaba taci karo da manyan idanunsa ya kafeta dasu nan da nan ta rikice ta fara stammering “errh errm uhm ina wuni ya habeeb” amsa ta yayi cikin cool but husky voice nashi yace “lafiya kalau meema ko” gyade kai tayi alaman aa a hankali ta furta “mimi” killer smile inshi yayi mata yace “ohh ok” shiru ta danyi dan ta manta me tazo yi ma kaman wacce aka gayama wani abu sai tayi saurin cewa “sorry erm! Dama dama sultaana tace ta bar sakon Ammah I should get it for her” ohh ya fada his mouth forming an o shape yace shigo ki dauka yana baya a hankali tazauna akan seat in gaba tana mika hannunta baya ta dauko wani leda ne da sauri ta tashi ta fito tana “toh toh sai anjima” smiling kawai yayi mata ya ja motanshi nan ta tsaya tana kallon motan tana jin haushin kanta why will she have to be acting weird a gabanshi haka ta fara tafiya a hankali koda ta shiga gate bata tarar dasu ba so tasan definitely suna daki, tana shiga dakin a bakin kofa ta aje ledan su kam kaman jira sukeyi suka ci gaba da dariya inteesar nacewa “ohh mimi you’ve no shame me kika dade kinayi fada mana muji me ya ce maki” tana magana tana rike dariyanta sukam su sultaana da inaaya dariya kawai sukeyi inaaya ce tace “ohh my gosh don’t tell us har yayi proposing this one that you’re busy blushing” frowning tayi ta yi shiru dasu ta zauna kan couch ta kwantar da kanta ta lumshe ido nan sultaana itama ta fara nata “ohhh god look she has closed her eyes maybe she was reminiscing what happened! Please is my bro romantic? Please did he say the three magical words” in a teasing tone sultaana ta fada nan mimi ta tashi ta ce “i hate you guys I’m going home” nan suka tashi sukayi engulfing inta into a group hug su duka suna fadin “habaa babe you can’t go you know we love you” smiling tayi alamun ta hakura suka ci gaba da kallonsu suna dariya da raha. Ammah ce ta shigo dakin nasu ta tadda su suna kallo tace ah ahh wa nake gani kaman sultaana nan sultaana ta tashi ta rungumeta tana cewa “Ammah inaa wuni ni ce ya hanya” lafiya qalau daughter ya mamanki ta fada “tana lafiya tace na gaidaki harda sakon ki na turaren wuta ta bani” ledan ta dauko ta ba ammah bayan sun gama gaisawa nan ammah tace “yauwa inaaya so nake kuzo driver ya kaiku gidan ku kuce ma mamii dan Allah dan nata ke son zobon nan irin na jiya tasa ayi mishi” dan smiling inaaya tayi tasa kai a kasa tace “Ammah ai ni nayi” murmushi Ammah tayi tace “ahh to MashaaAllah ashe ma mai zobon na gidan nan sai kuje kitchen kuyi mashi kuma ku zakuyi lunch tunda ga ku har ku 4 kowa ta kama kuyi lunch inaaya kuma tayi zobo” amsa wa sukayi da toh suka taso zasu tafi kitchen sai inaaya tace “wai ni dai nasan ya naseer hates zobo ya akayi yakesha yanzu” intee ta amsa mata da “dummy! Bashi ba ya Aliyu ne” tana mentioning aliyu heart in inaaya yayi wani double flips sai tayi shiru can tace “ina yake ne ban ganshi ba” mimi ce tayi dariya tace cux you were sleeping jiya da baffah yayi introducing nashi and besides ba da shi muka dawo daga airport ba a motan ya abby” bata sake cewa komai ba har suka karasa kitchen ita dai inaaya she was just feeling some kind of way. Ana kiran sallah laasar suka kammala girkinsu inteesar tayi fried rice dataji kayan hadi tana kamshi da coleslaw sai mimi tayi pounded da egusi soup, sultaana tayi taking charge of desserts inaaya kuma ta hada zobo tayi spicy chicken wings suka jera duka komai a dining suka koma daki don gabatar da sallah.
Karfe biyar Ammah ta sa ahmad ya kirasu suzo aci lunch gaba daya nan suka hadu da sultana suka gaisa suna ta maganan school haka har suka isa wurin dining kowa ya ja kujera ya zauna ana jiran naseer da aliyu, naseer ne ya fara shigowa suka gaishe shi ya amsa sannan ya zauna kujeran dake kusada ahmad bayan kaman 10minutes sai ga aliyu ya shigo parlourn yana tafiyan sa a hankali har ya karaso dining in ya gaida abbah its kam inaaya freezing tayi a wurin tana jin muryan shi har ya zo ya ja kujeran dake gefenta wanda shi kadai ya rage ya zauna kamshin turarenshi ne ya daki hancin ta her heart was beating slowly like very slow rufe idanunta tayi tana dafe chest, inteesar ce ta fara gaidashi sai mimi sai sultaana, inaaya kam da kyar tayi gathering confidence inta ta ce mashi ina wuni a hankali amsa mata yayi shima ciki ciki a hankali “lafiya” ko kallon gefenta baiyi ba ita kuwa abincin ma taji ya fitan mata a rai, karar curtleries kawai kakeji kowa ya zuba abunda zaya ci inaaya kawai tura abincin takeyi don duk tarasa me yake mata dadi muryan Ammah taji tace “inaaya to ki dauko zobon mana” to tace ta tashi ta nufa kitchen ta bude fridge in data sakashi ta dauko ta fara tafiya a hankali tana zuwa zata aje kusa da ammah sai Ammah tace “ai kai kusa da yayanku kawai” a hankali ta tako ta dawo seat inta ta aje kusa da shi zata zauna taji magananshi ciki ciki yace “pour some” cup in dake gabanta ta jawo ta juyashi ta zuba mashi ta kusa cika cup ya daga mata hannu alaman ya isa tadauka zata mika mashi yasa hannu zaya karba fingers nashi suka sauka kan hannunta mistakenly wani kaman shocking taji a hanunta jin fingers nashi kan hannunta ba shiri tasaki cup in yafadi kasa ya zube fortunately cup in bai fashe ba cux unbreakable cup ne, juyowa kowa yayi yana kallonta sorry tace sannan ta ruga kitchen ta dauko mop tazo tayi clearing mess in tayi excusing kanta ta hau sama ta shiga daki kawai ta fada kan gado tears falling from her eyes.
k i hope so” inaaya tace mata “yes it’s so” plate in abincin data ajiye a side drawer ta dauko ta mika mata tace “gashi Ammah tace we should make sure kin cinye” kar ba tayi with smile on her face tace “ok i sure will” ta fara cin abincin a hankali har ta cinye tass har ta gama suna nan zaune a kan gado nan sultaana ta jawo handbag nata ta ciro phone nata tace oya selfie time nan ta shiga snapchat inta nan ta dinga sa masu filters suna crazy styles, basu san time ya wuce ba saidai sukaji kiran sallahn magrib suka tashi duka don gabatar da sallah. Bayan sun gama sallah ne Ammah ta shigo dakin ta tambaya inaaya lafiya nan take gaya mata dama kanta ne ke ciwo kuma ya daina sannu ammah tayi mata sannan ta fita daga dakin.zama sukayi kowa rike da wayanshi shiru kakejin dakin sai sultaana ta dago tace “seriously I’m bored why don’t we go out and have some fun you know muje cold stone grab some ice cream and pizza and then a long drive” duk dagowa sukayi suna kallonta with happiness laced on there faces “wow what an idea sultaana” inteesar ta fada sai itama mimi tace “yeah what a cool idea but I don’t think ammah zata bar mu” “ehen it’s simple we’ll just go and meet amadu beg him and then sai muce ma Ammah da ahmad zamuje period!” “Wow great idea inee” inteesar ta fada sai sultaana tace “it’ll be time for isha in an hour so mu bari sai munyi sallah sai muje” “yes but for now muje muyi convincing amadu” mimi ta fada tana yar dariya “yes right” suka fada a tare sannan suka tashi suka fita daga dakin. Kasa suka sauka suka fita daga cikin gida gaba daya sukayi wani part dake facing na aliyu suka shiga dakuna uku ne kowane da toilet a ciki da parlour daya a part in parlour in is very simple wasu grey L cushion ne a ciki sai tv da curtains wani daki suka nufa wanda shine na farko daka bi wani corridor knocking suka shiga yi a hankali “who’s knocking” sukaji an fada “yaya Ahmad it’s me inaaya” tasowa yayi ya bude dakin ya gansu a tsaye su hudu with smiles on their faces gyara tsayuwa yayi ya jingina da kofan yayi folding hannuwan shi a chest nashi yace “please this facade don’t suite you is better ku fada mani me kukeso” inaaya ce ta fara magana “haba yaya Ahmad in mu” “ohh please inaayatu you’re not a good actress last time I checked I’m just two months older so when did i become yaya” “habaa ahmad the hot guy for the ladies” sultaana ta fada tana murmushi ai kam nan ta tabo shi ya fara smiling yana what do you want? “So please we want to go out to cold stone to get some pizza and ice cream and then go for a long ride” murmushi yayi yace “and you know Ammah won’t let you go out in the night without a guy so that’s why you want me to help you by going out together” a tare suka fada “yess” ce masu yayi “ohhk then, I’m in but till after prayer” dan tsalle sukayi suna yayy suka juya suka fita da ga part in suka koma cikin gida. Suna shiga cikin gida inteesar tace bara taje ta sanar ma ammah su kuma sukayi dakin inteesar bayan yan few minutes sai ga inteesar ta shigo tana smiling tace “yesss night outing it is girls ammah ta bar mu” murna sukayi ta yi suka shiga toilet one by one kowa ya dauro alwalan shi ana kiran sallah suka kabbara sukayi sallah su sai bayan sun gama sultaana ta zauna tana dan touching up fuskan ta duk suka shirya sannan suka fita suka ce ma ammah sun tafi tace Allah ya kiyaye suna shiga part in su ahmad su ka tar da shi a parlour zaune da wani black trouser da white tee yayi kyau MashaaAllah yana ganinsu yace to su je fita sukayi duka suka nufa motan da zasu tafi dashi benz ce E class E350 white color da tinted glass super dark shiga sukayi inaaya ce front seat sai su intee a baya dama kullum idan an zo shiga mota inaaya ke sauri tashiga front cux she loves sitting a front seat. Tada motan sukayi ya fara driving a hankali inaaya ce tayi connecting wayanta a motan tasa wakan mad by sarz suna ta bin wakan a hankali sai kawai sukaga yayi parking kofan gidansu inaaya kallonshi suka tsaya yi irin kallon nan na lafiya? Kafin suyi magana sukaga ya fita su ma fitowa sukayi suka bi shi cikin gidan suka shiga suka tarar da mamii zaune a parlour da ita da twins gaishe ta sukayi suka zauna sai ganin aneesah sukayi tana saukowa daga stairs sanye da wani black gown tayi dan light make up saukowa tayi ta gaisa da su inteesar da mimi suka ce mata “wow kinyi kyau baby sis” blushing tai ta yi sai cewa tayi ya ahmad ina wuni yace “lafiya nee are you ready” amsawa tayi da eh sukayi ma mamii sallama suka fita suna zuwa wurin mota inaaya na saurin shiga gaba ahmad ya zo ya bude kofan motan yana ce ma aneesah “get in nee” smiling aneesah tayi ta kalleshi sannan ta shiga tana ma inaaya stucking out tongue haushi taji kawai tashiga baya ta rufe kofan da karfi dariya su mimi suka mata sai tayi wani tsaki “ahmad you know this is not right ko” smiling yayi yace “sorry inee but nee is the fav” bata sake ce mishi komai ba har suka isa cold stone na cikin gwarimpa pizza suka fara order a dominos sannan suka shiga coldstone kowa ya fada flavors in dayake so nan suka zauna suna ci suna pictures su ahmad da aneesah kam suna gefe yana ta bata labari nan inteesar tace masu “hey guys ku juyo ayi snapping naku fav and fav juyowa sukayi nan sukaita daukan su picture wasu pictures in sai blushing takeyi haka suka gama suka tafi for their long drive.
ce jikin screen in tayi saurin dauka hade da cewa “ya habeebi good afternoon to what do i owe this call” dariya yayi yace “heyy lil sis lafiya qlw i need your help ne” tace “ok I’m all ears” yace “yauwa please numbern meema zaki bani please wani friend ina ya tura mun picture nata yace I should help him get her number idan na santa” smiling sultaana takeyi tace “who is meema ya habeeb” mimi kam tana jin tace meema tayi saurin dago kai tana kallonta “meema your friend mana” sai sultaana tasa dariya sosai tace “oww ya habeeb mimi not meema” su kam su inaaya sunajin tace mimi hankalinsu yadawo kanta suna jira ta gama wayan su ji me ya faru “ohhk riight away ya habeeb” “thanks lil sis” yafada with a smile sannan sukayi sallama ya kashe wayan sultaana kam na kashe wayan ta tashi tana yar rawa su inaaya kam sun damu su ji me ya faru mimi kam na zaune batace komai ba, saida tayi mai isarta sannan tace “hmm! Guys love one tin tin so ya habeeb thinks I’m still a child he said I should give him Erm! Meema’s number” bata karasa ba ta fashe da dariya “you guys need to hear how he’s pronuncing meema with so much love” dariya su inaaya sukayita yi sai sultaana tace thats not all fa “wai he’s telling me that wani friend inshi ya tura mashi picture inta yace please ya samo mishi numbern ta idan ya santa, imagine fa what kind of a story is this kawai bayasan ya fada mani pop and clear shi yakeso” dariya sukayi suka fara teasing mimi kawai sai wayanta ya fara ringing wani flipping heart inta yayi tana ganin new number dauka zatayi sai kuma tasan halin yan uwan nata closet ta shiga ta rufe kofan da key su kam suna ganin ta shiga suka bi ta suka tsaya jikin kofan suji me take cewa, tana shiga zatayi picking sai ya mutu har zata juya ta fito sai wayan ya fara ringing tana dauka tace “assalamu alaikum” muryan da ko a mafarki taji shi bata mantawa taji ance “wa alaiki salaam beauty” jin abunda yace yasa ko motsi ta kasa sai numfashin data keyi kawai, a dayan bangaren shima shiru yayi sai after like 2minutes sai yace “hope kin gane mai magana” da sauri tace “Aa” dariya yayi sannan yace “its habeeb” kaman ta aje wayan ta ruga haka taji sai ta daure tace “ohh ina wuni ya habeeb”
ya yan wurin ya abby motan ya abby suka shiga su hudu a baya dayake cikin motan nada space so basu matse ba ya abby ne yazo ya shiga drivers seat sun zata naseer zaya shiga gaba kawai sai su ka ga aliyu ya bude gaban ya shigo hankalin inaaya ya tashi her heart was beating su mimi suka gaisheshi da kyar itama ta gaisheshi duk tayi loosing control of herself har ya tada mota ya dan fara tafiya kadan kawai inaaya dake gefe tayi saurin bude kofa zata fita tsayawa ya abby yayi da sauri gannin tana shirin fita yace mata “sis lafiya ina zakije” da kyar ta samu tace “Erm ya abby sorry dama naga mu 4 ne a nan kuma akwai space a motansu ya leesha da can zanije” haushin maganan nata aliyu yaji bai san sanda ya daka mata tsawa ba “my friend get in before i slap you da kinsa da akwai space kikazo nan din” jiki na kyarma ta shiga ta rufe kofan suka tafi su kuwa su intee sai kallan lafiya suke mata cux sun san they agreed on shiga same car har kaduna but all of the sudden ta canza babu wanda yace komai dai shiru kakeji a motan they were all busy with their phones. Sai past 12 suka shiga garin kaduna nan sukayi hanyan gidan baba dake rabah road unguwar rimi kaduna, gida ne babba mai part hudu ba duplex ne ba kana shiga main gidan dan wuri ne kaman open courtyard sai kofan da zaya kai ka babban parlour in gidan, suna isa duk yan gidan suka fito tarban su waje baba da mama sai haneefa da ishak sun ji dadin ganin juna suka gaisa kafin suka shiga ciki drivers in duk suka shigo masu da kayan su, saida suka dan huta sukayi sallahn azahar sannan suka ci abinci, bayan nan iyayensu maza suna a parlour sunata tattaunawansu na yan uwa haka iyayen nasu mata ma suna can parlour in mama suna ta fira tamkar yan uwan juna.
bakin gate yana jira su fita, a hankali suka fara bude kofa zasu fita mimi ma tazo zata bude kofa cikin sassanyar muryan shi yace mata “to where ma’am?” Kaman jira aminnan nata keyi suka sa dariya ya juya ya bi su da harara da gudu suka sauka suka shiga cikin gidan suna dariya. Suna shiga ya juya motan suka kama hanya shiru kakejin motan har sai da ya habeeb ya yi breaking silence in yana cewa “beauty yau babu magana ko nayi wani abun ne” kaman bazata ce komai ba sai kuma tace “aa nothing ya habeeb” smiling yayi kawai ya cigaba da driving har suka isa cilantro parking yayi ya fito sannan ya zagaya ya bude ma ta kofan ta fito a hankali kaman tana tausayin kasan haka suka shiga ciki side by side table of two ne suka zauna wanda dama yasa an masu reserving. Order sukayi placing aka kawo masu they ate in silence yana ci yana dagowa yana kallon mimi da ta ke ci a natse har suka gama sai yace mata “lets talk?” Dagowa tayi ta kalleshi da alamun what about? Smiling yayi yace tell me more about you likes and dislikes you know shiru tayi kafin tace “uhhm ohhk so can’t say much about likes but some dislikes depends on my mood” gyade kai yayi alamun ya gane sai yace mata “when is your birthday?” “26th September” smiling yayi yace “oww same month mine is 8th September” smiling tayi itama tace cool shiru suka dan yi kafin yace uhmm “can i ask you something its too personal tho” gyade mashi kai tayi sai yace “do you have a boyfriend?” Batayi zaton question in ba sai zaro ido tayi ta duke kai sai tace “no” a hankali yar dariya yayi yace “nice” a haka suka yi shiru sai kuma yace ” mimi please lend me your ears i have something to tell you please” sai tace mishi “I’m all ears” sai yayi shiru na few seconds sannan ya ci gaba “I don’t know how you’ll perceive it but by Allah i mean each and every word I’m about to tell you and it’s from the depth of my heart, mimi I really like you I mean no guy can resist not liking you, you’re beautiful,cool, calm,religious you’re just perfect for me in every way mimi!!!!
esar black abaya tasaka tasha stones da maroon bag inta mimi kuma wani doguwan riga na material blue tasaka da black hand bag sun gana shiryawa sannan suka sauka kasa parlour suka tarar da ummi da khadija a gefenta suna zaune suna firar uwa da diya wuri suka samu suka zauna suna sanar ma ummi da murmushinta itama tace “ahh ahh yo shi dan nawa haka akeyi baya sanar ma ummin shi zayazo” duk dariya suka yi sai tace masu “to maza ku tashi kuje malam haruna ya kaiku kuma ku gaishe mani shi” amsa mata sukayi da to sannan suka tashi suna nufa hanyan fita sukaji khady tace “nima ku gaishe mun da ya sai’doo kuce ya ajemun tsaraba na safe” murmushi inaaya tayi tace “to! An gama” fita sukayi suka gayama malam haruna driver sannna suka shiga mota mimi na gaba sai inteesar da inaaya a baya, it was a silent drive har inaaya ta kagara a isa taga yayan nata suna isa daidai gate ko ida parking malam haruna baiyi ba ta bude ta fito da gudu tashiga cikin gidan nasu tana kiran “ya sa’idoooo!” Tana shiga parlour duk suna kan table suna cin abincin da mamiii,daddy,abba,ammah,aneesah,twins,ahmad,naseer,abby, sa’id da aliyu duk bata kula da sauran mutanen ba ta shigo da gudunta kan ya sa’id kawai idanunta suka fada da sauri ta karasa tana hugging inshi nan su mimi suka shigo dama suna biye a bayanta, kaman wata karaman yarinya ta fara hawaye “I missed you so much wlh ya sa’id can’t tell you how happy i am” bata sake daga hugging inshi datayi ba take maganan nan sai yace “awwn! I also missed my sister like so so much that was why I decided to surprise her” suna cikin magana sai daddy yace “su inaaya to sannu! Me dan uwa duk bakiga mutanen dake zaune ba ke me yaya shi kadai kika sani” ya karashe maganan shi yana dariya ai kuwa duk kowa yasa mata dariya sai a lokacin ta sake shi ta juyo taga dukkansu harda su abba ashe nan kunya ya kamata ta rufe fuskanta da tafin hannu abba na dariya yace “ahh yo mamana kunyan me zakiji ai duk mu ne” nan ma suka kara mata dariya sai a lokacin ta gaishe da su daddy,abba,ammah da mamii faran faran suka amsa mata sai mamii tace “mu kadai kika gani ne nan” sai ta juya ta kara ganin sauran ita har ga Allah duk bata kula dasu ba ta gaishe da ya abby da ya naseer suka amsa mata lafiya lau tana ganin aliyu sai ta zare ido dan ta dade bata ganshi ba fuskan nan nashi straight ba wani wasa a tattare dashi heart inta ya fara duka nan kaman bazata gaishe shi ba sai ta hada ido ta mamii taga hararan datake mata nan ta daure tace “ya aliyu ina wuni” yana juyo wa ya kalleta sai tasha jinin jikinta yace “lafiya qlw” sai tayi shiru sai aneesah tace “uhmm mamii ai ni inaace ma mun yi sadaka da ita mutumin da baya son zama gidansu yanzu kinga da tasu ta hadasu ai tazo” kowa na kan table in dariya yayi ita kuwa inaaya ta harare ta tace “kiyi ma mutane shiru nan” sai daddy yace dasu “to ya isa kowa yayi shiru a gama cin abinci” yace ma inaaya dasu mimi duk su zauna suma nan kowa cikinsu yaja kujera ya zauna itadai inaaya kujeran gefen ya sa’id ta ja ta zauna saida ta zauna taga kujeran ke facing aliyu nan tayi dana sanin zama saboda duk takasa natsuwa hannunta sai shaking yakeyi. Bayan sun gama cin abinci duk suna parlour zaune inaaya dai tana maqale da ya sa’id ita kuwa mimi tana daki ya habeeb ya kirata inteesar kam na nan duk tayi shiru gashi data dago sai sun hada ido da ya sa’id shi kuwa sai ya sakin mata murmushinsa mai kyau nan daddy yake sanar masu gobe akwai family meeting gidan baffah around 4pm za ayi meeting sosai a tattauna and kowa will be attending it yau baba zayazo da iyalanshi ammi da mommy ma duk suna kan hanya a yau zasu iso garin abuja saboda akwai family dinner tonight, sunyi murna sosai saboda suna jin dadin duk family meeting in nasu every year gashi this time around kowa da kowa na nan.