INDA RAI CHAPTER 1 BY FADILA SANI BAKORI

INDA RAI CHAPTER 1 BY FADILA SANI BAKORI 



                Www.bankinhausanovels.com.ng 

Bismillahir rahmanir rahim. 

ASALIN LABARIN. 

University of lagos. Wasu ‘yan mata ne guda uku, na hango suna tafiya, daga gani daga lecture suka fito, ko wannansu hannin shi rik’e da  handout. D’aya daga cikin ‘yan matan,da katawa da tafiya tayi, tana kallan ta kusa ita ta ce, ” Khadiya lafiya naga sai sauri kike, kamar zaki tashi sama? “. Wadda aka kira da khadija, cikin  fara’arta, ta ce, “Hafsat Wallahi sauri nake, mun yi waya da Yaya Umar yana hanya, ya kusa shigowa lagos za yi visiting d’ina”. Murmushi Hafsat ta yi, ta ce, “ki ce yau munada manyan bak’i, tom Allah ya kawo shi lafiya”. Daga haka su Hafsat suka wuce, kasan cewar su a hostel d’in makarantar suke, inda ita kuma Khadija a waje Mahaifin ta ya kamamata haya”. 

Kasan cewar ba wani nisa bane tsakanin university d’in da Khadija ke karatu da inda ta ke haya,  hakan yasa ba wata tafiya mai nisa tayi ba, ta k’arasa. Tana zuwa ta sa key ta bud’e  d’an ma dai-dai cin d’akin da ta ke haya. Masha Allah d’akin babba ne ba laifi,dan duk abin da ta ke buk’ata akwai aciki. Tana shiga ta zub’e kan babbar mattras d’inta irin wadda ake kira gado huta, tana zama kira na shigowa wayarta. D’agawa tayi tana limshe ido, ta ce, “Hello Yaya Umar”. daga can ban k’aran ya ce, ” Gani abikin k’ofar d’akin ki na k’araso”.yana fad’in haka ya kashe wayar. 

 Khadija da ke kwance ta ta shi  ta je ta  ta bud’e k’ofar”. Umar dake tsaye cikin nuna jin dad’i da missing d’in Khadija da ya yi  ya rungume Khadiya,ahaka suka k’arasa ciki, suna zuwa, khadija ta zame da wa yau, tana murmushi ta  kallai ta ce, “Yaya Umar shine sai da ka shigo lagos ka sanar dani zuwanka”. Khadija ta fad’i maganar tana turo baki”. 

Murmushi Umar ya yi, ya ce, “Khaddy ki yi hak’uri nima zuwanne yazo min kai tsaye, amma ko gida ba’asan da zuwana ba, Katsina nace musu zani”. Khadija b’ata fuska ta yi, ta ce, “Tom me kazo yi? “. Murmushi Umar ya yi, ya ce, “Ke nazo gani mana, haka nan naji ina buk’atar ganinki”.Khadija kallan Umar ta yi, tana murmushin jin dad’in abin da ya ce, ta ce, “shine ka k’i fad’ama Ummana zaka zo! “. “in na koma zan fad’a mata”. Cewar Umar”.

Khadija tashi tashi ta yi, ta ce, tom tashi muje kaci abinci”. 

Restaurant d’in kusa  su, Khadija ta kai  Umar yaci abinci. Bayan sun dawo gida ne, ya yi Sallalolin da aka biyo shi. 

Haddare Umar na nan kuma bai ma Khadija maganar ta fi ya ba, hakan yasa Khadija ta kallai ta ce”Yaya Umar amma dai anan zaka kwana ko?”. Khadija ta fad’i maganar da wasa. 

Umar kallan Khadija ya yi, ya ce, “Khadija ko rata kike ko?, tom anan zan kwana”. 

Abu kamar wasa har 10:30Pm Umar bai ma Khadija maganar zai tafi ba. Khadija ko ganin hakan yasa ta ce, “Yaya Umar dare fa ya yi”. “Yau ina sha’awar kwana da Babyna ne”. Cewar Umar. khadija batare da fargabar komai ba, ta tashi ta je ta rufe k’ofar, Sannan ta d’akko sabon bedsheet ta shimfid’a a mattras d’in. Bayan khadija ta gama ne, ta je ta kwanta kan ‘yar k’aramar lover chair d’in da bazata d’auki tsawanta ba, ta ce, “Yaya Umar good night am feeling sleep”.

 “Uhm tun yan zu Baby ban yarda ba, kuma nan bazai isheki kwanciya ba, bai d’auke tsawanki ba, dawo nan ki kwanta”. Umar ya nuna mata kan katifar. 

Khadija tashi ta yi, tana kallan Umar ta ce, “Yaya Umar kusa da kai?, Allah bazan iya ba”. Umar b’ata fuska ya yi, ya ce, “Taya zaki kwanta nan ki yi baccin ta kura, ki dawo nan ki kwanta, tom me ye aciki?, ni ba yayanki bane, kuma wanda zai aure ki in Allah ya yarda”. Umar tashi ya yi ya je ya koma hannun Khadija ya ce, “Haba k’anwata nifa yayanki ne, kuma miji gareki daga kin kagama karatun nan zamu tabbatarma su Daddy da soyayyar mu, mu yi aure, ko yan zu fa dan kece kika hana da yan zu sun san da Soyayyar mu. Haka Umar da dad’in baki ya ja wo hannun Khadija ya dawo da ita kan matrass d’in ya kwantar, shima ya kwanta kusa da ita yana mai rik’e da ita.. 

Khadija cikin fad’uwar gaban da ta tariski kanta ta d’ago tana kallan Umar ta ce, “Please Yaya Umar ka matsa tom”. “Haba dear nifa d’an’uwanki ne, me ye dan na kwanta kusa da ke, ki tuna fa damuwa da kene da Soyayyar da na ke mi ki tasa na taso nazo wajanki, Kawai dan inga kyakkyawar fuskarki, da d’an sajan nan naki”. Ya fad’i maganar yana shafa gefan fuskarta inda sajanta ya kwanta”. 

Khadija dai shiru ta yi, ta kasa cema Umar ko mai, amma acikin zuciyarta bata ji dad’in yadda suka kwanta ba.

Umar ko ci gaba da shafa fuskar Khadija ya yi yana mai yaban kyan da Allah ya yi mata, zame hular kanta ya yi wai yaga kitsonta. “Wow dear wa yayi mi ki wannan kitson haka?, amma ya yi kyau”. Umar yana maganar ya shashshafa kan Khadija”. 

Khadija cikin siririyar muryarta, ta ce, “Yaya Umar please ka yi bacci kaga kace gobe da wuri zaka wuce”. ” Khadija ke dai ki yi baccin ki nikam bana jin bacci”. Cewar Umar”. 

Wani irin bacci ne ya kwashe khadija lokaci guda, ita dama bata da wuyar bacci sai dai in bata kwanta ba. Cikin bacci Khadija ke jin Umar na mata wasu irin abubuwa masu wuyar fassarawa, tun tana jin abin kamar a mafarki, harta fara jin abin azahiri. 

Khadija afurgice ta bud’e idonta, sai dai ahalinda taga Umar ne yasa ta ta yi sauri ta rufe idonta, tana mai ture Umar tana matsawa,  cikin furgiji da tsoro, Khadija ta ce, “Yaya Umar me kake shirin aikatawa gareni ne haka!! ?, dan Allah yaya Umar ka rufa min asiri dan Allah! “. Khadija ta idasa maganar cikin rawar murya tana kuka. duk yadda Khadija ke ture Umar tana ya kushinshi tana bugunshi kota ina, Umar bai kyale Khadija ba, sai da ya yi mata Fyad’e”. 

Allah sarki lokacinda Khadija ta farka ta ganta ahalinda ta ke ciki, ta tabbatar Umar ya yi mata Fyad’e sosai Khadija ta rud’e, kuka sosai Khadija ta ke, kamar ranta zai fita, tana cewa, “Yaya Umar dama wannan ita ce soyayyar da ka dad’e kana cewa kana min, dama burinka kenan akaina?, ka b’atamin darajata ta ‘ya mace? , me kake so in cema wanda na aura!? “.Khadija ta fad’i maganar cikin tsananin kuka”. 

Umar tashi ya yi  cikin damuwa da yanayin da yaga Khadija ciki, ya matsa inda ta ke, ya ce, “Khadija kika ce me nake so kicema Mijin da kika aura?, Kina nufin duk soyayyar da nake fad’in ina miki ta baki ce, koko kina so kice ba sonki nake ba, sha’awarki nake?, tom ko d’aya, Khadija karki sake tunanin abin da zaki fad’ama Mijin da zaki aura, dan baki da miji sai ni,kuma ni na san Wacece Khadija,  Wallahi Khadija ban tab’a sonki da sunan yaudara ba, haba k’anwata ko ina yaudara zan yaudari k’anwata ne, dan Allah Khadi ki yi shiru kar kanki ya yi ciwo, Wallahi ina sonki so kuma na aure, ba bu abin da zai hanani auranki, daga kin gama karatunki zan bayyana soyayyar mu ga Iyayyan…. “. 

Khadija hana Umar ya yi maganar da ya ke fad’a ta yi, ta hanyar cewa, “Yaya
Umar bana sonka, natsa nake, Ka tashi kafuta bana son ganinka!, ka fita nace!!! Umar tashi ya yi, zuciyar shi yana mai jin zafin maganganun da Khadija ke fad’a garesa, Umar kallan Khadija ya yi, ya ce, “Khadija zan tafi kamar yadda kika naima, Sai dai ki sa ni Ina sonki, kuma Insha Allah zan aure ki, abin da nai miki kuma ki yi hak’uri so. … “. 

“Kafita nace!, bana son jin komai dan Allah , kafita!!! “. Khadija ta fad’i maganar cikin kuka”. 

Umar fita ya yi, batare da yak’ara cewa komai ba”. 

Khadija ko haka ta zau na tana ta kuka, data ga kukan ba zai mata maganin komai ba, ta tashi ta yi ta shiga toilet ta tsarkake kanta. Khadija koda da fito bata tsaya nai man abin da zata ci ba, ta koma ta kwanta”. 

Umar ko yana fita direct airport ya nufa dan komawa Kano”. 

Khadija ta nan kwance ba ita ta tashi ba sai da taji yunwa na nai man mata illah sannan ta samu ta yunk’ura ta tashi, ta had’a ma kanta tea ta sha”. 

Yau kwanan Khadija Uku kenan bata fita ko ina ba, dan ko lecture ta bar zuwa, kuma kullum Mahaifiyarta zata kirata awaya koda wasa Khadija bata fad’a mata zuwan Yayan ta Umar ba, bare kuma ta fad’a mata abin da Umar ya yi mata, ta ki fad’ama kowa dan acewarta wannan sirrin zuciyarta ne, Umar ko dama tun da ya tafi ta yi adding number sa a blacklist, ya kira ta da wata number ya fi ak’irga amma sanin shine yasa ba ta d’aga ba, sak’on text massage ko ya turo mata yafi ak’irga amma ko karantawa bata yi ta ke delate d’in shi. Wannan kenan”. 

B’angaran Umar ko sosai hankalin shi ya tashi yadda yaga Khadija ta yi fushi da shi, sai dai ya yi ma kanshi alk’awarin baya k’ara kiran ta awaya”. 

Yau Khadija ta tashi ta yi shirin zuwa lecture, ta tafi. Tana zuwa Hafsat ta tareta da fara’arta ta ce, “Khadija lafiya yau kwana Uku kenan baki shigowa school?,

 Khadija kallan Hafsat ta yi kamar bazata amsa mata ba, sai kuma ta ce, “Ban da lafiya ne”. “Allah ya baki lafiya”. Cewar Hafsat”. 

Haka khadija ta saki ranta taci gaba da rayuwarta kamar da,sai dai duk lokacin da Khadija ta tuna ta rasa kimarta ta ‘ya mace, sosai abin ke tab’a zuciyarta, gashi fushin dole ta ke yi da Umar dan sosai ita kanta ta ke son Umar, duk da tana ya k’i da zuciyarta dan ganin ta sa ma kanta tsanar Umar aranta.

Wannan kenan”. 

Bayan wata d’aya da zuwan Umar lagos. Khadija gaba d’aya ‘yan kwanan nan ta rasa gane abin da ke damunta, duk abin da taci sai ta yi amai, gashi kusan kullum da zazzab’i ta ke kwana, yan zu haka fitowarsu kenan daga lecture, suna ta fiya ita da Hafsat,da sauri ta samu gefe guda ta rakub’e tana amai, da sauri Hafsat ta je ta da fata tana mata sannu, Faro da ke hannun Hafsat ta mik’ama ta ta wanke bakin ta, kad’an ta d’an huta sannan ta tashi suka tafi”. 

Hafsat kallan Khadija ta yi, ta ce, “Khadija ki je likita ya duba ki mana, 3 days fa kenan kullum kika zo sai kin yi amannan”. Khadija kallan Hafsat ta yi, sai kuma ta fashe da kuka. 

Hafsat hankalinta tashe ta ke tambayar Khadija lafiya, ta ce, 

“Haba Khadija me ye kuma abin kuka, ko ciwan ne? “.

 Kai Khadija ta girgiza ma Hafsat sannan ta samu gu ta zau na, tana kallan Hafsat, in da ta ke ta nuna mata alamun ta zau na. 

Hafsat zama ta yi, tana mai kallan Khadija alamun ina jinki”. 

Khadija kallan Hafsat ta yi, tana goge hawayan da ke idonta, ta ce, “Hafsat ina cikin rud’ani na tashin hankali, ina tsoran zuwa likita ya duba ni Hafsat dan ina tsoran abin da zai fad’amin”. Hafsat kallan Khadija ta yi da mamaki ta ce” kamar ya Khadija? “. “Hafsat Yayana Umar ya cuceni, ya zuban min da mitincina,  Hafsat zuwan da Yaya Umar ya yi kusan Five week’s  kenan, alokacin ya yi min Fyad’e”. Khadija ta fad’i maganar tana share hawayan da  ke zubar mata. Hafsat cikin tsoro ta kalli Khadija ta ce, “Khadija Yaya Umar fa kika ce ya yi miki Fyad’e!? “. Kai Khadija ta d’aga tana mai share hawayanda ke zubar mata”. 

Shiru Hafsat ta yi, dan tama rasa abin da zata ce, sannan zuwa can ta kalli Khadija ta ce, “Khadija ya akai ki ka bari haka ta faru? “.cikin kuka Khadija ta ce, “Hafsat na ce miki Fyad’e ya yi min, Wallahi yan zu haka bana d’aga Kiran shi, nayi block d’in duka numbersa, sannan na yi block d’in sa a WhatsApp d’ina da Facebook”.  Shiru  Hafsat ta yi sannan ta ce, “Duk da haka Khadija ki yi hak’uri ki tashi muje private Hospital d’in kusa damu d’in nan adubaki”.

 khdaja cikin kuka ta ce, “Hafsat ba zani ba, ina tsoran abin da za a fad’amin”. 

“Insha Allah abin da kike tunani bashi bane, ki tashi mu tafi”. Cewar Hafsat. Khadija ta shi ta yi suka tafi zuciyarta na cike da fargabar abin da za afad’a mata.  tafiya suke amma addu’a ta ke Allah ya rufa mata asiri kar ace ciki ne”. 

Suna shiga cikin asibitin, wata nurse Hafsat ta sama tai ma bayanin abin da ke tafe da su, tana so ai ma k’awarta  awan ciki ne. 

Likitar wani d’an abu taba Khadija ta ce ta kawo mata fitsarinta”. 

Khadija hannunta na rawa ta amshi abin ta shiga toilet d’in gun,  ta yi fitsarin ta fito ta mik’ama nurse d’in”. 

Allah sarki Khadija gu ta samu ta zau na zuciyarta ta cike da fargaba da tsoran tsakamon da zata gani”. 

Khadija na nan zau ne ba bu wanda ke mawani magana tsakaninta da Hafsat, dan ita kanta Hafsat cikin fargaba ta ke. Suna nan zau ne nurse d’in ta fito, ta yo gunsu, dukkan su tashi su kai tsaye, suna mai sauraran abin da Nurse d’in zata….. 

Khadija na nan zau ne ba bu wan da ke ma wani magana tsakaninta da Hafsat, dan ita kanta Hafsat cikin fargaba ta ke. Sunanan zau ne nurse d’in ta fito ta yo gunsu, dukkan su tashi su kai tsaye suna mai sauraran abin da nurse d’in za ta ce. 

Nurse d’in ko lura da ta yi hankalin Khadija atashe ya ke yasa, ta kama hannun Khadija ta zau nar  da ita, sannan ta mik’a ma ta wata ‘yar k’aramar takadda da ke hannunta. 

Khadija k’in amsar ta kardar ta yi tana kallan nurse d’in, ta ce, cikin rawar murya, “Dan Allah ki fad’i min abin da ke damuna, bani da natsuwar karantawa”. 

Nurse d’in kallan Khadija ta yi, tana tab’e baki ta ce, “kina d’au ke da cikin wata d’aya d….. “. 

Fad’uwar da Khadija ta yi ne, yasa nurse d’in ta yi shiru bata k’arasa fad’in abin da ta ke fad’a ba. 

Da sauri Hafsat ta yo kan Khadija tana bubbugata, cikin rud’ewa”. 

Nurse d’in kama Khadija suka yi suka shigar da ita inda aka tana da dan kwantar da muta ne”. 

Duk wani tai mako da ya kamata nurse d’in taba Khadija shi. 

Khadija sai gaf da magriba ta farka da kuka, tana suru tai kamar haka, “Hafsat dan Allah kice ta zubar min, Wallahi Abbana kashe ni zai  y.. “. Hafsat da sauri ta yo kan Khadija, dama tana kusa da ita, ta rufe bakinta ta ce, “Sannu Khadija, dan Allah ki yi hak’uri ki kwantar da hankalinki mana, inda aikin gama ya riga ya gama, wannan kukan da kike yi ba wani magani da zai mi ki sai da ya k’ara mi ki wa ni ciwan, yan zu mafita ya kamata mu nai ma”. 

Khadija tashi ta yi ta zau na kamar wadda aka tsakura, tana kallan Hafsat ta ce, kamar za tai kuka, “Tom Hafsat na yi shiru, dan Allah ki kira nurse d’in ta zubar min, Wallahi Hafsat Abbana idan ya ji labarin ina da ciki kashe ni zai yi ko ya kure ni”. 

Shiru Hafsat ta yi, sannan ta ce, “Tom bari in kira nurse d’in “. 

Hafsat fita ta yi sai gata da nurse d’in sun dawo tare”. 

Nurse d’in kallan Khadija ta yi, ta ce, “Sannu ko?, ya ki ke jin jikin naki? “. “Naji sauk’i “. Cewar Khadija”. 

khadija kamo hannun nurse d’in ta yi, ta ce, “Dan Allah ki tai makeni kira ba ni da cikin nan”. Khadija ta idasa maganar cikin zubar hawaye. 

Nurse d’in kama hannun Khadija ta yi, ta ce, “Khadija sunan ki ko? “. Kai Khadija ta d’aga mata”. 

Nurse d’in ta ce, “Khadija me yasa gaki kamar mai hankali amma kika biyema rud’in samari ki kai ciki? “. Khadija goge hawayan ta ta yi, sannan ta ce, “Sister Wallahi Fyad’e ya yi min, dan Allah ki tai maka ki zubar min dan Allah “. “Ki yi hak’uri Khadija Allah ya hana zubda ciki, ban tab’a ba kuma bazan tab’a ba, ke ma idan zaki ji shawarata kada ki zubar, ki yi hak’uri ki rungimi k’addarar ki,dan kwanaki akwai wata yarinyar da mahaifiyarta ta kawota azubar mata da ciki, tom ni dama gaskiya ba aikina bane,Sister Jimmai ta bata maganin zubar da cikin tasha, amma Wallahi haka yarinyar nan tasha wahala kuma cikin bai zube ba. Khadija in dai zaki ji maganata ki yi hak’uri ki ta addu’a inda Allah yaso sai cikin ya zube da kan shi”. 

Khadija hanun Hafsat ta kama ta ce, “Hafsat dan Allah ki mata bayani ta zubar min Wallahi Abbana kurata zai yi”. “Khadija bikiji abin nurse d’in ta ce ba ne, ta ce bata zubar da ciki, yan zu tashi muje gida sai asan yadda za ai”. 

Hafsat biyan nurse d’in ta yi, takama Khadija suka tafi”. 

Suna shiga d’akin Khadija Khadija ta fad’a kan mattras d’inta tana wani irin kuka. 

Hafsat kallan Khadija ta yi ta ce, “Khadija zafa ki d’ora ma kanki wani ciwan, dan Allah ki yi hak’uri aikin gama ya riga ya gama yan zu mafita zaki nai ma. Yan zu ki tashi mu yi magana”. 

Khadija ta shi ta yi zau ne tana kallan Hafsat alamun ina jinki”. 

Hafsat kallan Khadija ta yi sannan ta ce,”Khadija har yan zu kina kan bakanki na zubar da cikin? “. 

Kai Khadija ta d’aga ma Hafsat. Hafsat ta ce, “Khadija baki tsoran ki mutu wajan zubar da cikin, me zaki cema mahalicinki?, Wallahi Khadija ki yi hak’uri ki ringumi k’addarar da Allah ya d’ora maki,dan ni gaskiya ni bazan b’oye miki ba, idan har kika ce sai kin zubar da cikin nan nima zan cire hannuna  akai, dan idan na biye miki aka zubar nima ina da kama so, dan da wanda ya zubar da wanda ya bada Shawara azubar duk Allah sai ya kamasu da laifi, dan manzan Allah (S. A. W)  ya ce Manyuridillahu bihi khairan, Yusuf minhum. wanda Allah ya nufa da alkairi sai ya jarabce shi, dan haka wani alkairin Allah ke nufarki da shi, karki kuskura ki fad’i jarabawar nan, ki yi hak’uri kita addu’a Allah zai kawo miki mafita cikin sauk’i. Dan mahaifiyata tana yawan fad’amin duk wanda bai tab’a aikata zuna ba Allah na amsar addu’ar sa daga ya yi, kinga ke kuma biki tab’a ai kata zuna ba, wannan ma fin k’arfi akai miki, kuma Allah zai saka miki,dan haka ki yi hak’uri insha Allah Allah zai kawo miki mafita cikin sauk’i”. 

Khadija dai bata ce komai ba, share hawayan da  ke zubar mata Kawai ta ke yi, sai zuwa can ta d’ago tana kallan Hafsat, ta ce,  cikin murya irin ta wadda ya gaji da kuka, “Hafsat zan yi hak’uri kamar yadda kika ce, zan ringumi k’addara, amma ki sani sai dai in bar zaman gidan Abbana har abada, dan Wallahi Abbana yana yawan fad’a shi in dai Yarinyar shi ta yi ciki, kasheta zai yi, sannan ita kanta Ummana tunda na zab’i karatu a lagos ta ke yawan jan kunnena kar in zo in biyema samarin bariki in d’akko  musu abin kunya,  dan in dai nayi haka ba dai gidansu ba, tom ki fad’amin yan zu taya zan tun kari Mahaifana da maganar inada ciki, haba ba zan ma iya ba, ki ban Shawara tom ya zan yi? “. Khadija ta idasa maganar tana kuka”. 

Shiru Hafsat ta yi dan bata san abin da zata cema Khadija ba, sai zuwa can ta ce, “Khadija nima ayan zu ban da wata mafita, sai dai kamar yadda nace miki, ki yi ta addu’a, nima zan ta ya ki, sannan ki yi hak’uri, ki yi shirya da Yaya Umar idan zaki ji shawarata, ki fad’a mai halin da kike ciki, dan yana da kyau ya san da maganar cikin”. Shiru Khadija ta yi, sannan ta ce, “Hafsat idan nace mai ina da ciki maganin me?”. “Tom Khadija bamu san abin da Allah ya yi ba, ko Allah ya k’addari zuwan abin da ke cikin ki duniya, kinga ko ai dole za’atambayi Ubansa”. 

Kuka Khadija ta fashe da shi ta ce, “Insha Allah Hafsat bazan goya d’an shegeba, insha Allah ba zan haifi abin da ke cikina ba”. Khadija ta idasa maganar da kuka sosai”. 

Hafsat dai ta dad’e tana ba Khadija baki da lallashi da nuna mata mahimmancin yadda da k’adddara. Hafsat ba ita tabar gidan ba har sai da ta ga Khadija ta sha tea d’in da ta bata kuma ta dai na kukan da ta ke yi sannan tai mata sallama ta tafi”.

Bayan Hafsat ta tafi  Khadija zama ta yi tai shiru, tama rasa tunanin da za tai,sannan ta samu ta lallab’a ta tashi ta shiga toilet ta watsa ruwa, ko zata ji  sanyi, bayan ta fito ne ta yi sallolin da aka biyota”. 

Tun da ga wannan rana khadija ta maida hankalinta a addu’ar Allah ya ra bata da cikin batare da tasha magani ba, dan abinci ma bata ci sosai duk da tana jin yunwar sai taji kamar zata mutu sannan ta ke daure wa taci, ita atunaninta idan taji Yunwa sosai cikin zai zube, hakan yasa bata cin abinci sosai. 

Wannan kenan”. 

Wacece Khadija da Umar? “. 

Khajiya ita ce  ta uku awajan mahaifinta, su Uku Iyyansu suka haifa, Aminu shine babba, sai Aisha, sai ita Khadija.  

Mahaifin khadija d’an kasuwa ne babba, dan indai kace gidan alhaji Bala mai kanti za’akai ka har gidan su Khadija. 

Mahaifin Khadija da Mahaifin Umar wa da k’ani ne, Mahiafin Umar ya kasan ce shi ne babba, inda shima Umar ya kasance shine babba awajan Iyayan shi. 

Tun Khadija bata gama cika budurwa ba Umar ya fara nuna yana son ta, sai dai koda ya je ma Mahaifiyar Khadija da maganar  nuna mai ta yi kar ya furta ma Khadija sai ta gama karatu. Shi kuma Umar tsoran kar wani yarigasa ya sa ya samu Khadija ya furta mata kalmar so.. 

Tun khadija na d’aukar abun kamar wasa har itama tazo ta fara son Umar da gaske, duk da mahaifiyarta na yawan sanar da ita duk lokacin da ta sake ta kamata tana Soyayya tom daga wannan rana ta gama karatu aure za tai ma ta.

Ita kuma Khadija Allah ya yota mai son karatu, hakan yasa ta samu Umar ta fad’a mai abin da Mahaifiyarta ta fad’a mata, ta kuma ce mai duk lokacin da ya bari mommy’n ta ta gano suna Soyyya tom daga wannan rana zata rabu da shi. 

Wannan shine dalilin da yasa Umar ya ke b’oye soyayyar da yake ma Khadija babu wanda ya sa ni a iyayansu, daga shi sai Khadija sai kuma Allah da ya halicce su. 

Umar kusan komai nashi agidan su Khadija ya ke yinsa, Umar bai tab’a nuna ma Khadija wani  buba wanda ya ke alamu da yana  Sha’awarta, hakan yasa koda Umar ya je wajan Khadija a lagos, da ya ce zai kwana bata ji komai ba bare ta hana shi Kwanan,  sanin halin Yayan nata da tayi mai hankaki da tunani, , sai dai abin yazo mata a bazata inda Umar ya bata mamaki wajan yi mata Fyad’e”. 

CI GABAN LABARI. 

Khadija haka ta yi hak’uri da cikin jikinta, duk da kallo d’aya in kai ma Khadija za ka ga tsantsar ramar da ta yi. Yan zu haka shirye-shirye zana  Exam suke yi, kuma daga sun gama sa su je hutu. Hakan  yasa hankalin Khadija ya k’ara tashi sosai, dan gani ta ke daga taje Mahaifiyarta zata gane tana da ciki”. 

Ranar da su Khadija suka yi Exam d’in k’arshe kuka tai ta yi, bayan sun fito ne, daga holle d’in, Hafsat ta samu Khadija da ke kuka kamar wadda akaima mutuwa, dan ko gurin zana Exam d’in tana yi tana kuka, ahaka ta gama”. 

Hafsat cikin tausaya ma  halinda Khadija ta ke ciki ta ce, “Khadija nasan kina cikin damuwa, kuma dole ki damu, amma ni dai hak’urin nan dai shi zan ce mi
ki ki k’ara yi, da kuma addu’a sai kiga duk abin da zai zo mi ki ya zo mi ki da sauk’i”. 

Khadija kallan Hafsat ta yi tana goge hawayanta, ta ce, “Hafsat dan Allah ina kama da mai ciki? “. “A’a Khadija baki kama da mai ciki, ai kin ga cikin naki bai fi wata biyu ba, insha Allah su Mommy har kije ki dawo baza su gane ba”. Cewar Hafsat”. 

Ajiyar zuciya Khadija ta yi, sannan ta ce, “Tom Allah yasa “. 

Har d’akin Khadija Hafsat ta raka Khadija, sannan suka yi sallama da juna Hafsat ta tafi, inda Khadija kuma ta koma ta kwanta dan sai gobe zata hau jirgi ta tafi”.

Washe gari da wuri Khadija ta yi sammakon ta fiya Kano.

Ko acikin jirji Khadija kallo d’aya za kai mata ka gano tana cikin damuwa . Khadija na awanan halinne ta fara jin announced d’in saukar jirki. 

Firgigi Khadija ta yi, dan sai taga sun yi saurin da basu tab’a yi ba. Khadija jan trolley bag d’in ta ta yi, cikin wani yana yi, ahaka ta samu mota wadda zata kaita gidan su”. 

Kasan cewar gidan su Khadija duk ansan da dawowarta yau,  hakan yasa, aka shirya mata abinci na alfarma. 

Mahaifiyar Khadija tana zau ne afalo Khadija ta yi sallama, cikin k’ok’arin dawowa da walwalarta kamar da, dan kar Mahaifiyarta ta fahimce ta”. 

Mahaifiyar Khadija cikin murnar ganin autarta ta tashi ta nufi Khadija ta na washe baki, ta ce, “Oyoyo My beautiful daughter “. Khadija fad’awa ta yi kan Mahaifiyarta tana mak’alk’ale ta. Mahaifiyar Khadija jan ye Khadija ta yi, tana kallan Khadijar, ta ce, “Khadija lafiya baki da lafiya ne, kika rame haka? “. Mahaifiyar Khadija ta idasa maganar cikin damuwar yadda taga Khadijar ta rame sosa. 

Khadija cikin nuna ma Mahaifiyarta ba komai ta ce, “Mama Wallahi haka kowa ke cewa, amma babu abin da ke damuna, sai dai fargabar Exam da na d’an yi”. 

Mahaifiyar Khadija cikin damuwa ta kamo hanun Khadija ta ce, “je ki watsa ruwa kizo ki ci abinci, amma gaskiya bana tunanin zan barki ki koma makarantar nan, haba wannan rama haka, sai kace wadda ke da wata muguwar lallurar”. 

Khadija dai haka ta samu ta shige bedroom d’in ta, Khadija na zuwa ta fad’a kan makeken bed d’in ta tana kuka. Khadija ta dad’e tana kuka sannan ta tashi ta shiga toilet ta watsa ruwa ta fito”. 

Lokacin da Khadija ta fito falon zau ne ta iske Mahaifiyarta. 

Tun daga nesa Mahaifiyar Khadija ta kureta da ido tana kallanta. Khadija side d’in derning space ta nufa Mahaifiyar Khadija ta ya fito ta da hannu alamun ta zo”.

Khadija cikin fargaba ta k’arasa wajan Mahaifiyarta. Mahaifiyar Khadija kallan Khadija ta yi, ta ce, “Khadija me ke damunki? “. 

Gaban Khadija fad’uwa ya yi jin tambayar da Mahaifiyarta tai mata, amma sai ta dake ta cije, ta ce, “Mama ban da wata damuwa, nafi tunanin Exam ne ya ramar dani, amma ki bari kafin in tafi zaki ga na yi k’iba”. 

Kai Mahaifiyar Khadija ta jinjina dan ta yarda da abin da Khadija ta ce”

Khadija ko ganin Mahaifiyarta ta gamsu da zan can ta, ya sa ta nufi hanyar derning space d’in”

Khadija sosai ta ci abinci, dan Yunwa ta ke ji, Khadija na cikin cin abinci taji sallamar Umar,  da sauri Khadija ta d’ago tana kallan Umar da ke shigowa Falon. 

Umar ko bai san da zuwan Khadija ba ya zo ne kawai, ya gaida Mahaifiyar Khadija”. 

Umar na nan zau ne suna hira da Mahaifiyar Khadija.

Bayan sun gama gaisawa ne Umar ya tashi zai tafi,dan bai san da zuwan Khadija ba. Umar har ya tashi zai tafi Mahaifiyar Khadija ta ce, “Khadija zo ku gaisa da Yayanki”. 

Khaidija da har ta fara jin dad’in Umar zai tafi, batare da yasan da zuwan ta ba, dan bata son sake had’a ido da Umar”. 

Umar ko cikin mamaki da Boye farinci kin shi naganin Khadija,ya ce, “laa Mama Yau she Khadija ta zo? “. “Yau-yau d’in nan tazo”. Cewar Mama”. 

Khadija ko cikin danne tsanar Umar da ta yi, ta k’araso falon……. ✍️

IN DA RAI LABARINE MAI SARK’AK’IYA SISTER, YADDA KIKE TUNANIN LABARIN BA HAKA YA KE BA, AMMA IDAN KIKA BINI A HANKALI ZA KI GANE AINIHIN INDA NA DOSA. ³ ⁴

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *