INDA RAI CHAPTER 2 BY FADILA SANI BAKORI
Khadija ko cikin danne tsanar da tai ma Umar ta k’arasa falon. Tana zuwa ta samu gefan Mahaifiyarta ta zau na, sannan cikin kau da kai ta ce, “Ina wuni”. “Lafiya klau Khadija, ya karatun”. Cewar Umar. “Lafiya”. Khadija ta ba Umar amsa”.
Sallamar Aisha ce Yayar Khadija ya sa Umar ya yi shiru da abin da ya ke son fad’a.
Khadija cikin murnar ganin Aisha ta tashi, tana “Oyoyoo Aunty Aisha”.
Rungume juna su kai, inda Aisha ta d’aga Khadija daga jikinta tana kallanta ta ce, “Khadija ba ki da lafiya ne, kika rame haka! ? “.
Aman da ya taso ma Khadija ne, ya sa ta saki Aisha ta ruga bedroom d’in ta tana kwarara amai.
Daga Aisha har Mahaifiyar Khadija da kallo suka bi Khadija. Aisha kallan Umar ta yi, ta ce, “Yaya Umar wai bakaga yadda Khadija ta dawo bane?, Yarinya ta rame haka sosai, sai wani haske da ta yi”. Aisha ta idasa maganar cikin alamun damuwa. “Aisha nagani ban yi magana bane”. Cewar Umar”.
Suna nan zau ne suna jajanta ramar Khadija, sai ga Khadija ta tafo ahankali kanta ak’asa.
Dukkan su da kallo suka bita har ta k’araso Falon”.
Aisha kallan Khadija ka wai ta ke ko kyaftawa ba ta yi. Aisha kallan Khadija ta yi, ta ce, “Khadija me ke damun ki? “. Gaban Khadija fad’uwa ya yi dan ta san Aunty’nta ta shegen bin diddik’i. Khadija cikin jarumta ta ce, “Aunty Aisha ba abin da ke damuna k’ila dai fargabar exam ce da nayi”.
Aisha kallan Mahaifiyar su ta yi, da ita ma Khadija ta ke kallo , ta ce, “Mama anya ko Khadija ba ciki gareta ba? “. “Ciki kuma Aunty Aisha!?”. Khadija ta fad’i maganar arud’e.
“Eh ban yar da da ke ba Wallahi!!! “. Cewar Aisha ”
Umar cikin fad’uwar gaba da bugama Aisha tsawa ya ce, “Aisha wannan wata irin ban zar magana ce ki ke yi? “.
Mahaifiyar Khadija ko da sai yan zu ta samu bakin magana ta ce, “Haba Aisha wannan wata irin magana ce?, shikenan dan ta rame sai ki ce ciki gareta, kin san yadda zuciyata ta amsa kuwa? “. Mahaifiyar Khadija ta idasa maganar cikin rauni.
Aisha kallan Mahaifiyarta ta yi, ta ce, “Mama Wallahi ki dubi Khadija da kyau ki gani cik…. “.
Tsawar da Umar ya yi ma Aisha ce tasa bata k’arasa fad’in abin da ta ke fad’a ba.
Aisha kallan Umar ta yi, ta ce, “Yaya Umar nifa ba zan tab’a yarda da Khadija ba in ba asibiti aka kai ta ba, aka tambatar ba, haba Mama ku dubi Khadija fa ku gani, Yan zu me ye abin kuka?, me ye yasa ba zata yi magana ba ta kare kanta ta tsaya tana kuka? “.
Shiru Mahaifiyar Khadija ta yi tana kallan Khadija ta kasa cewa ko mai. Umar ne ganin haka ya ce, “Shikenan Mama inda haka ta ce, “Da akwai wani friend d’ina gobe Aisha ta zo sai mu je ya dubata”. “Yauwa Yaya Umar Allah ya kaimu goban”. Cewar Aisha”.
Khadija dai ta kasa cewa komai, sai aikin kuka ta ke.
Umar kallan Khadija ya yi ya yi ma Mama Sallama ya yi tafiyar shi, gaban shi na tsananin tsananta fad’uwa. Umar tunani ya fara yadda za ai ya yi magana da Khadija ya ji shin da gaske ne tana da ciki, amma bai samo mafitar yadda zai yi magana da ita ba. Umar Kiran Khadija ya yi awaya amma harta katse Khadija bata d’aga ba, dama kuma Umar ya yi tunanin haka, hakan yasa bai sake kiranta ba dan yasan ba d’agawa zai tai ba”.
Can gidan su Khadija ko bayan tafiyar Umar, Aisha ganin hankalin Mahaifiyar su ya tashi da maganar kamar Khadija na da ciki da ta yi, ya sa, ta zau na tana kwantar ma Mahaifiyarta da hankali ta hanyar cewa, “Mama dan Allah ki kwantar da hankali ki, maganar nan fa ba tabbatarwa na yi ba, zargi ne, kuma ba lallene ya zama gaskiya ba, ke da kanki kin san Khadija ko saurayi bata da shi, sai dai ko acan makarantar ta yi saurayi ba mu Sa ni ba.. “.
Khadija ta sauri ta amshe zan can ta hanyar cewa, “Aunty Wallahi bani da saurayi amakaranta”. “Ok sai anan ki ke da shi? “. “Cewar Aisha”
“Aunty Aisha bani da saurayi ako ina “. Aisha dai shiru ta yi bata tan kaba.
Mama ce ta ce, “Aisha dan Allah ki bar maganar nan idan Yayanku Umar ya ce gobe zai kai ku asibitin abokinsa ya duba ta”.
Aisha kallan Mama ta yi, ta ce, “Tom Mama Allah ya kaimu goban”.
Aisha ba ita ta bar gidan ba sai dare mijinta ya zo ya d’auke ta”.
Umar haka ya kwana yana mai son magana da Khadija, amma babu hanya, dan ya kirata ya fi ak’irga ta k’i d’aga Kiran, hakan yasa dole Umar ya rubu da ita”.
B’angaran Khadija ma haka ta yi kwanan tashin hankali, dan tana matuk’ar firgicin gobe, tom idan aka kai ni aka ce ina da ciki wa zan ce ya yi min?, Yaya Umar, kai tom yau shema zasu tsaya su saurare ni, ya Allah ka d’auki rayuwata kafin gobe, wayyo Allah me zan ce ma Mama”.
Haka Khadija tai ta magan-ganu ita kad’ai, ahaka wani wahalallan bacci ya d’au ke ta mai tattare da mafarkin akaita asibita ance ta nada ciki Mama ta ce karta ko ma masu gida, daga nan ta san inda dare ya yi mata.
Firgigi Khadija ta farka ta na nishi, dan ta zaci da gaske abin ya faru. Khadija tashi ta yi tai alwallah ta yi sallah raka’a biyu ta kaima Allha kukanta”.
Washe gari Mama ta ji Khadija Shiru-shiru bata fito yin break fast ba, hakan yasa Mama ta shiga bedroom d’in Khadija dan ganin lafiya.
Zau ne Mama ta iske Khadija ta fito wanka ga mai nan ta tasa tana kuka, dan tasan saura mintina kad’an ta bar gidan. Khadija da sauri ta d’ago kanta tana kallan Mama”.
Mama da mamaki ta ke kallan Khadija, sannan ta ce, “Khadija lafiya kike kuka?, ko da gaske ne kina da cikin?, dan tun jiya da Aisha ta yi maganar nan naga yana yinki gaba d’aya ya can za”. Mama shiru ta yi tana kallan Khadija da ta kasa cewa ko mai sai kuka da ta ke ta yi. Mama cikin zaro ma Khadija Ido ta ce, “Khadija ki fad’amin gaskiya, kina da ciki kamar yadda Aisha ta ce k…. “.
Sallamar Umar ce ta katse maganar Mama. Mama fita ta yi jin sallamar Umar”.
Umar cikin girmamawa kamar yadda ya saba ya gaida Mama, bayan sun gama gaisawa ne, Umar ya ce, “Mama da ma na biyo ne, In d’au ki Khadija mu biya gidan Aisha mu d’auketa , daga can sai mu wuce asibitin aduba Khadijar “.
Mama kallan Umar ta yi, sannan ta ce, “Umar anya ko Khadija bata da ciki kamar yadda Aisha ta ce, dan tun jiya tun da Aisha ta yi maganar nan, Khadija ke kuka, yan zu haka ko break fast ba ta yi ba, tana d’aki tana kuka”.
Umar share zufar da ke zubo mai ya yi ya ce, “Mama badamu inda yan zu zamu asibiti adubata, ko me ye ma ai zamu gani”. “Haka ne”. Cewar Mama. Sannan ta ce, “Bari in kirata ta zo in ta ga dama ta yi break fast d’in ku wuce”.
Mama bedroom d’in Khadija ta koma lokacin da ta koma Khadija har ta
sa kaya ajikinta.
Mama kallan Khadija ta yi, ta ce, “ki shirya ki fito ga Yayanki Umar na jiranki zaku tafi”.Mama na kaiwa haka ta juya ta fita ta bar Khadija”.
Khadija cikin fad’uwar gaba da mutuwar jiki ta idasa shiryawa ta fito.
Khadija direct derning space ta nufa, ta na zuwa ta had’a tea dan shi ka d’ai za ta iya sha”.
Mama jin Khadija shiru, ta daga mata tsawa ta ce, “Da Allah can Malam ki yi sauri ke ake jira! “. Khadija da sauri ta idasa shanye tea d’in, ta tako zuwa falon, cikin sanyin muryarta ta ce, “Ina kwana Yaya Umar”. Umar ido ya bi Khadija da shi ganin yadda ta rame sosai. Sannan ya ce, “Muje ko? “.
Khadija bayan Umar tafi suka fita”.
Umar da kan shi ya bud’e ma Khadija Mota ta shiga ta zau na, sai dai kamar Khadija jira ta ke ta shiga motar tana shiga ta fashe da kuka.Umar bai kula Khadija ba sai da suka bar unguwar sannan ya tsaya, yana kallan Khadija, cikin sanyi ya ce, “Khadija”. Khadija shiru ta yi bata tan kama Umar ba”.
Umar jin Khadija ta yi shiru, ya kuma cewa, “Khadija dan Allah ki yi shiru ki saurare ni muyi magana,da gaske ne kina da ciki Khadija? “.
Khadija d’agowa ta yi tana kallan Umar, kamar ba zata yi magana ba sai kuma ta ce, “Mamaki kake?”. Umar cikin alamun furgici ya rik’o hanun Khadija ya ce, “Khadija dan Allah ki aje komai magana mu yi magana,Dan Allah kina da ciki? “.
Shiru Khadija ta yi, sannan zuwa can ta ce, cikin kuka, “Da gaske nake ina da ciki”.
Umar rik’e kan shi ya yi da k’arfi yana ambatan Innalilahi wa inna ilaihirraju’un”. Umar ya dad’e dafe da kan shi, dan yasan tabbas cikin jikin Khadija cikin shi ne. Umar tambayar kan shi ya fara” Wai ya ma akai na aika ta haka ne?, Wayyo ya Allah”. Umar ya dad’e ahaka sannan ya d’ago kan shi yana kallan Khadija ya ce, “Khadija ke me shawaranki yan zu? “.
Khadija shiru ta yi kamar ba zata ce ma Umar ko mai ba, dan sosai ta ke jin haushin shi, dan duk shi ne ya sata cikin tashin hankalin nan da ta ke ciki. Khadija cikin muryata mai kama da ta damuwa ta ce, “Ban da Wa ta shawara”.
Umar shi kan shi shiru ya yi, dan bai san Wa ta mafita ba. Kallan Khadija ya yi ya ce, “Ki ci gaba da nuna masu Mama baki da ciki, ko yan zu idan muka je gidan Aisha tai miki magana, ki ce mata ke fa baki da wani ciki”.Khadija dai bata amsa ma Umar ba. Umar koma yaja motar shi suka tafi”
Dai-dai k’ofar gidan Aisha, Umar ya yi parking. Kallan Khadija ya yi ya ce, “Shiga ki ce mata ta yi sauri ta fito”.
Khadija batare da ta kalli Umar ba ta ce, “Idan muka jefa aka tabbatar ma da Aunty Aisha ina da ciki, baka tunanin halinda zan shiga?”. Umar kallan Khadija ya yi, ya ce, “Ki je kikirata na ce”.
Khadija fita ta yi daga Motar ta shiga Gidan Aisha”.
Aisha na zau ne afalo tana jiran k’arasowar su Khadija, dan Mama ta kirata ta ce mata ta shirya ga Umar nan sun ta ho da Khadija. Hakan yasa Aisha shiryawa, Aisha zau ne ta ke su Khadija kawai ta ke jira su tafi. Khadija ta yi sallam ta shiga”.
Khadija cikin k’ok’ari n dawowa da walwalarta ta gaida Aisha, bayan sun gama gai sawa ne, ta ce, “Aunty Aisha Yaya Umar na waje ya ce kizo mu je”. Aisha ma yafinta ta d’auka ta ce, “muje”. Umar na zau ne Aisha da Khadija suka k’araso.
Aisha cikin girmamawa ta gaida Umar ta ce, “Yaya Umar har kazo kenan? “. “Eh Aisha, ina su Auwal fa? “.
“Suna School”. cewar Aisha”.
Aisha shiga ta yi Umar kuma yaja motar suka tafi. Suna shiga cikin Asibitin, Umar ya kira Usman awaya. Bayan sun gaisane Umar ya ce, “Usman gani a Asibitin ku, kazo yan zu dan Allah “.
Su Umar na nan tsaye Usman abokin Umar ya zo.
Khadija ko ga banta babu abin da ya ke yi ban da dukan Uku-uku”.
Usman na zuwa sosai suka gaisa da Umar, sannan ya kalli Umar ya ce, “Umar lafiya dai ko? “. Umar mai da kallan shi ga Aisha ya yi, ya ce, “Aisha ki mai baya nin abin da ki ke so”.
Aisha gaida Usman ta yi. Bayan sun gama gaisawa ne, ta ce, “Dama wannan yarinyar ce, mu ke so aima awan ciki”. Aisha ta nuna Khadija da ke kusa da ita”.
Usman Office d’in shi ya kaisu su, sannan ya ba Khadija Wata rubber ya ce yana buk’atar fitsarinta.
Khadija amsa ta yi ga banta na masifar fad’uwa. Toilet d’in gun Khadija ta shiga ta yi fitsarin, ta da wo ta mik’ama Usman”.
Usman amsar fitsarin ya yi. Bai fi minti goma ba Usman ya dawo. Kallan Aisha ya yi, ya ce, “Malam Aisha na yi ma ta awan fitsari kamar yadda kuka buk’ata, ba ta da ciki”.
Aisha shiru ta yi, ba wai dan bata yarda da abin da Usman ya ce ba, ta ce, “Amma likita me yasa ta yi haske haka?, kuma inajin tana yin amai ma “. “Eh to aman da ta ke yi, Ulcer ce, sannan hasken nan da ta yi shawara ce”. Cewar Usman”
Aisha cikin gamsuwa da kalaman Usman ta yi, mai godiya sosai, sannan suka tafi, inda kuma Aisha gaba d’aya sai ta ji kunyar k’anwarta ta ta ke”.
Khadija tunani ta ke taya haka ta faru, wai bata da ciki, tom ko da gaske ne bata da cikin?, kai k’arya ne, yana yinda ta ke jin kanta kad’ai ya tabbatar mata tana da ciki, sai dai in da Yaya Umar suka had’a baki. Wata zuciyar ta ce ma ta, tom kinga sun ware ne ai duk maganar da su kai agabanku suka yi. Wani irin farin ciki Khadija ta ji yazo mata ta ce, Ya Allah kasa maganar kikitan nan ta zama gaskiya.. “.
Maganar da Aisha tai ma Khadija ce ta katse ma ta tunaninta. Aisha cikin damuwa ta rik’o hannun Khadija ta ce, “Khadija dan Allah ki yi hak’uri da zarginki da na yi, Wallahi gaba d’aya ne naga kin riki d’emin kin koma min kalar mai ciki, ashe shawara ce, dan Allah ki yi hak’uri kinji k’anwata? “.
Khadija cikin sauke ajiyar zuciya ta ce, “Babu ko mai Aunty Aisha”.
Can gida ko Mama ta k’osa su Khadija su dawo ta ji saka makon awan da akaima Khadija. Mama na nan zau ne Su Aisha su kai sallam suka shigo. Inda shi Umar yana sau ke su bai shiga ba ya tafi”.
Mama cikin k’osawa bayan ta amsa sallamar su Aisha ta ce, “Aisha ckin ne ko? “. Aisha dariya ta yi, ta ce, “Mama dan Allah ki bar maganar nan, nima ban san meke damuna ba, Wallahi bata da ciki ashe shawara ce da Ulcer,”.
Allah sarki Mama cikin jin dad’i ta rungume Khadija tana cewa, “Allah sarki ni na san Khadijata baza ta d’akko min abin kunya ba “.
Yau ma dai haka Aisha ta wuni kamar jiya, sai dare mijinta ya zo ya d’au ke ta suka tafi gida. Khadija ko da daddare bayan ta yi shirin kwanciya, ta yi tunanin ta kira Umar ta tambaye ta ji da gaske ne ba ta da ciki. Khadija wayarta ta d’akko ta danna ma Number umar kira……. ✍️
Khadija ko da daddare bayan ta yi shirin kwanciya, ta yi tunanin ta kira Umar ta tambaye shi ta ji da gaske ne ba ta da ciki. Khadija Wayarta ta d’akko ta kira Number Umar .
Umar ko lokacin yana kwance dan tun da Usman ya tabbatar mai da cikin Khadija Wata biyu har da kwana kai, akai ya rasa sukuni, dan har Mahaifiyar shi sai da ta gane ya nada damuwa, gashi ya rasa wanda zai fad’a ma wa ya bashi shawara, gashi ita ma Khadija ba saurarar shi ta ke ba bare ya kirata ya ji ya zasu yi.
Umar na awannan tunanin ne ya ji kira ya shigo wayar shi, kamar ba zai d’auka ba, sai kuma ya kai hannu ya jawo wayar. Da mamaki ya ke bin scream d’in wayar da kallo ganin Number Khadija. Tana gaf da tsinkewa Umar ya yi sauri ya d’aga. Umar kanga wayar ya yi yana mai sauraran abin da Khadija za ta ce, sai dai kuma shiru ne ya biyo ba ya. Dan Khadija ta kasa magana. Um
ar jin shirun ya yi yawa, ya ce, “Hello Khadija ya kike, ya jikin naki? “.
Khadija kamar ba zata amsa ba sai kuma ta ce, “Uhm dama na kiraka ne inji da gaske ne ban da ciki? “.
Umar shiru ya yi na d’an wani lokaci, sannan ya sauke ajiyar zuciya mai k’arfi, ya ce, “Khadija ki na da ciki da gaske, ni na ce ma Usman ya fad’i baki da ciki. lokacin da kika shiga Kiran Aisha na kira shi awaya na ce mai za mu zo da wata yan zu zai mata awan ciki, amma ko ya auna ya ga tana da cikin tom kar ya fad’a, kin ji yadda mu kai da shi”.
Khadija ajiyar zuciya ta sau ke mai k’arfi, mai cike da damuwa da fargaba”.
Umar ko jin Khadija ta yi shiru, ya ce, “Khadija gobe da safe ki zo gida kisaman za mu yi magana kinji? “.
“Tom”. Khadija ta ce, dan mafita ta ke nai ma ido rufe. Khadija na fad’in haka ta kashe wayarta”.
Washe gari da wuri Khadija ta tashi ta yi wanka, sannan ta je ta yi break fast. Bayan ta gama break fast ne, ta kalli Mommy’nta ta ce, “Mama za ni gidansu Maryam”. Wato gidan su Umar kenan, kamar yadda jiya Umar ya ne mi ta je.
Maman Khadija kallan khadija ta yi, ta ce, “Tom Khadija sai kin dawo, amma idan kin kai dare ki rok’i Yayanki Umar ya kawo ki”.
“Tom Mama “. Cewar Khadija sannan Khadija ta zira zimbilelan hijab d’in ta wan da ya fi tsawanta, ta tafi”.
Khadija na fita daga gidan su ta samu Napep za ta hau kenan, kira ya shigo wayarta picking call d’in ta yi, ganin Number Umar”.
“Hello Khadija kina ina ne? “. Cewar Umar.
Khadija shiru ta yi na d’an wani lokaci sannan ta ce, “Ina layin gidan mu, zan hau Napep ne zani gidan”.
“Karki hau ki jirani anan gani nan zuwa”. Cewar Umar”.
Khadija hak’uri ta ba mai Napep d’in ta fasa hawa. ta ja gefe ta tsaya tana jiran Umar.
Khadija ba ta wani dad’e sosai agun ba, motar Umar ta tsaya”.
Umar fitowa ya yi ya zo in da Khadija ke tsaye ya tsaya, kallanta ya yi, sannan ya ce, “Khadija mu shiga Mota sai mu yi magana ko? “.
Khadija bin Umar ta yi ta shiga Motar ba tare da ta yi magana ba”.
Umar ba tare da ya ce ma Khadija ko mai ba ya ja motar suka tafi.
Khadija kallan Umar ta yi, ta ce, “Ina kuma zaka kai ni? “. “Ki tsaya ki gani mana”.Umar ya ba Khadija amsa ya na mai ci gaba da tuk’insa”.
Khadija da mamaki ta kalli Umar ganin ya yi hanyar Asibitin da suka je jiya. Ka sa daurewa ta yi ganin ya yi parking a parking space d’in Asibitin, ta ce, “Me kuma za mu yi anan? “.
Umar fita ya yi, ya bud’e ma Khadija ya kamo hannunta ba tare da ya amsa ma ta ba.
Khadija dai da mamaki ta ke bikin Umar”.
Umar ko bai tsaya ko ina ba sai bakin Office d’in Usman, sannan ya ki ra shi awaya, ya ce, “Hello kana Office d’in ka ne? “. Daga can b’angaran aka ba Umar amsa da “Eh, ka shigo ina nan”.
Umar shiga Office d’in ya yi, inda Khadija ta bishi ita ma tana mamakin abin da za su yi “.
Bayan Umar sun gama gaisawa da Usman ne, ya kalli Usman ya ce, “Usman so ni ke ka zubar da cikin jikin Khadija “.
Usman ba tare da ya ce ko mai ba ya tashi ya fita daga Office d’in, jin kad’an ya dawo da wasu k’ana-nan magani a hannun shi da ruwa Faro, ya mik’ama Khadija da ke tsaye ta kasa furta ko mai jin abin da Umar ya ce.
Khadija da kallo ta bi Usman ta k’i amzar maganin da ya mik’a ma ta”.
Umar kallan Khadija ya yi ganin bata amshi maganin da Usman ke mik’a ma ta ba, ya ce, “Khadija ki amsa mana, zai tai maka mi ki ya rabaki da cikin”.
Khadija wani mugun kallo tai ma Umar sannan ta ce, “Da na san wannan shirman ne da ban biyoka ba Wallahi”. Khadija na fad’in haka ta juya zata tafi.
Da sauri Umar ya jawo hannunta ya ce, “Kina da wata mafitar ne bacin wanan ?, idan kuma kina da ita tom ki fad’i “.
Khadija ba tare da ta kalli Umar ba kanta ak’asa ta na mai k’okarin danne kukan da ke son zuwa mata ta ce, “Kasar min hannuna dan Allah in wuce”.
Umar cikin lallashi ya ce, “Dan Allah Khadija ki yi hak’uri mana azubar da cikin, idan ba haka ba nan da watanni kad’an fa su Mama su iya ganewa, dan Allah ki yi hak’uri kisha wannan maganin”. Umar ya fad’i maganar ya na mai mik’a mata maganin da ya amsa hannun Usman”.
“Wallahi Yaya Umar ba zan shaba, saboda na yi yin k’urin hakan tun a lagos, likitar ta ankarar da ni illar hakan, dan haka ba zan shaba”. Khadija ta fad’i maganar tana mai jan hannunta da Umar ya rik’e.
Umar kallan Khadija ya yi, ya ce,
“Khadija ki fahimtan illar barin cikin ta fi ta zibar da shi yawa, dan Allah ki amsa ki sha”.
Khadija fusge hannunta ta yi da tsiya daga rik’on da Umar ya yi mata, cikin kuka ta fara magana ta ce,
“Ba zan shaba Yaya Umar, ba zan sha ba!! “.
Umar shima cikin jin haushin yadda ya ke ta lallab’a Khadija ta sha ta k’i sha , ya ce, “Kada Allah ya sa ki sha Khadija kar ki sha d’in, amma ki sa ni idan har ki ka fita nan biki sha maganin nan ba, zan cire hannuna akan lamarinki! “.
Khadija bata tsaya sauraran Umar ba ta ja k’ofar Office d’in ta fita..
Usman kallan Umar ya yi, ya ce, “Umar idan na fahimta cikin jikin Khadija naka ne, haka ne? “. Umar sosa kai ya yi, ya ce, “Usman Wallahi duk da ba lalle ne ka karya da abin da zan ce ba, amma ni na san abin da ya faru tsakanina da Khadija rubutaccan al’amari ne, dan har yan zu ina mamakin kaina, ni kaina ban san yadda akai na ai kata haka ba”.
Usman kallan Umar ya yi, ya ce, “Amma gaskiya kar ka fita da ga lamarin yarinyar nan, kamar yadda ka ce, ni sai inga inda ‘yar’uwarka ce ka yi maganar auranta mana inda gaske ka ke sonta, kaga ko wata hud’u ta yi ta haihu asirinku rufe, ba kamar ace ta haihu atiti ba, kuma kai kan ka idan magana ta fita da wana ido za ka kalli Iyayanku?, gaskiya idan za kaji maganata ka yi gaggawar nai man auranta Wallahi “.
Umar sosai ya gamsu da shawarar abokinsa Usman, hakan ya sa ya yi mai sallama ya tafi. Sai dai Umar koda ya fito bai ga Khadija ba, babu in da bai du ba ba amma ba bu Khadija babu alamar ta, hakan ya tabbatar mai da ta tafi. Shiga Motar shi ya yi shima ya tafi “.
Khadija ko ta na fita ta samu Napep ba ta tsaya ko ina ba sai gidansu.
Sosai mama tai mamakin ganin Khadija ta dawo da wuri haka.
Mama tambayar Khadija ta yi, ta ce, “Khadija lafiya daga zuwa kika dawo? “. Mama munyi waya da Maryam bata nan shi yasa na fasa zuwa,na dawo”.
Mama dai kai ta girgiza dan ta san in dai Maryam bata nan Khadija bata zuwa gidan su Umar ta dad’e. Maryam k’anwar Umar ce”.
Umar ko gida ya koma, ya je ya samu Mahaifiyar shi zau ne a falo .
Hajiya Mariya kallan Umar ta yi, ta ce, “Umar lafiya ko na ganka yan zu da rana, yau baka je aiki ba ma ko? “. kai Umar ya sosai, sannan ya ce, “Hajiya ina cikin wata ‘yar damuwa ne”.
“Damuwa kuma Umar, me ke damunka? “.
Umar cikin k’asa da kan shi ya ce, “Hajiya idan ba za ki manta ba, na tab’a mi ki maganar ina son Khadija shekaru kusan Uku da suka wuce, tom ita ma Mama na yi mata magana alokacin, amma ta sanar da ni sai Khadija ta gama ka ratu, tom ni kam Hajita ina tsoran kar lokacin da Khadija zata gama karatu ta samu wani, lokacin da zan furta mata kallamar so ta k’i amince min, shine na ke rok’onki Hajiya, dan Allah kima Abba magana ni ina son Khadija so na aure, na san yan zu daga naje gidan su Khadija da maganar Mama zata ce karatu, sai ta gama, tom ni na yarda da karatun, dan Allah Hajiya a aura min Khadija kafin ta koma hutun nan, ni kuma zan barta ta koma ka
ratunta, ka wai dai ina son haka ne saboda ina fargabar kar wani ya rigani shiga zuciyarta”.
Shiru Mahaifiyar Umar ta yi, sannan ta ce, “Tom Umar ban k’ima ba, amma bana son Mahaifinka yaji maganar nan, gara in fara zuwa in samu Hajiya Zainab mu yi magana sannan, saboda bana son ashiga hak’inta, daga Mahaifinka ya ji maganar nan shikenan”.
“Tom Allah ya sa ada ce”. Cewar Umar”.
Mahaifiyar Umar Umar ta sa ya kaita gidansu Khadija, inda yana ajeta ya yi gaba.
Mahaifiyar Khadija da fara’arta ta tar bi Mahaifiyar Umar”.
Bayan sun gaggaisa ne, Mahaifiyar Umar ta kalli Mahaifiyar Khadija ta ce, “Hajiya Zainab d’anki ne ya aiko ni”. “Tofa, Umar kenan, tom ina ji, ya ce me? “. Mahaifiyar Khadija ta idasa maganar tana murmushi.
Dariya Mahaifiyar Umar ta yi, sannan ta ce,
“ki manin shekara Uku kenan, Umar ya saman ya ce min yana son Khadija, na nuna mai karatu ta ke ya bari ta k’arasa, tom daga nan bai k’ara min maganar ba sai yau, wai dan Allah yana son kafin Khadija ta koma hutu ad’aura auran shi da ita, ala bashi sai ta tafi ta ci gaba da karatunta, idan ta gama sai su tare, saboda wai shi yana tsoran kar wani ya riga shi, shine na ce bari in zo in sa me ki inji ta bakinki tukun? “.
Shiru Mahaifiyar Khadija ta yi, Sannan ta kalli Mahaifiyar Umar ta yi Murmushi, ta ce, “Umar kenan, nima ko ya tab’a yi min maganar yana son Khadija, dan ni ce ma na hana shi sanar ma Khadija, na ce mai ya bari sai ta gama karatu sannan”.
Shiru Mahaifiyar Khadija ta yi, sannan ta ci gaba da cewa, “Wallahi Hajiya Mariya tun daga ranar na k’udiri Khadija bata da miji sai Umar, ni yan zu hak’urin da na ba Umar shi zan k’ara bashi, ya kwantar da hankalin shi Khadija bata da Miji sai shi, amma ya yi hak’uri, saura k’iris ta idasa, ala bashi daga ta gama sai ai auran, dan Wallahi yan zu haka Khadija bata kula ko wana saurayi na hana, kuma Wallahi duk dan Umar na yi haka, dan haka ya kwantar da hankali shi”.
Mahaifiyar Umar cikin gamsuwa da abin da Mahaifiyar Khadija ta ce, ta ce, “Haka ne kam, inda ta kusa gamawa, ai gara ta k’arasa”. Nan ma suka bar zan can, suka kamo wani.
Mahaifiyar Umar sun dad’e suna fira da Mahaifiyar Khadija, sannan tai musu sallama ta kira Umar awaya ya mai da ta gida”.
Umar ko da yazo kunyar shiga gidan su Khadija ya yi, hakan yasa ya kira Mahaifiyarsa ya ce”Hello Hajiya ki fito na k’araso”. “Ka shigo ku gaisa mana”. Cewar Mahaifiyar Umar “.
Umar shiga ya yi badan ya soba.
Bayan sun gaisa da Mahaifiyar Khadija ne, ta kalli Umar d’in ta ce,
“Umar naji sak’onka, ka yi hak’uri ka ji ?, Khadija bata da miji sai kai, kuma kaga saura shekara d’aya ya ragema Khadija ta gama karatunta, dan haka daga ta gama ni kuma nai ma ka alk’awari cikin lokaci za ai auranka da ita”.
Umar cikin jin kunya ya yi ma Mama godiya ba dan yaji dad’in abin da ta ce ba, sannan suka tafi shi da Mahaifiyar shi, dan yaso ace Mahaifiyar Khadija ta amin ce mai”.
Haka Umar ya hak’ura bai k’ara ta da maganar auran Khadija ba, in da bai da wata mafita. Ga Khadija kuma ya yi ya yi tak’i shan maganin zubar da cikin, k’arshema ta kuma adding Number sa a blacklist . tun daga ranar Umar ya yi alk’awarin ba zai k’ara nai man Khadija awaya ba, sai dai in ita ce ta nai mai, amma kuma niyyar auranta har abada tana nan aran shi, dan ba kad’an ya ke son Khadija ba”.
Khadija ko haka ta yi hak’uri ta b’oye damuwar da ke ranta har hutun su ya k’are. Hutun su Khadija na gaf da k’arewa ne Mahaifinta ya dawo dan baya k’asar.
Shi kan shi sai da ya yi Complain d’in ramar Khadija”.
Maganar cikin Khadija ko babu wan da ya kuma tada maganar, tun da doctor Usman ya tabbatar musu da Khadija bata da ciki, sai ya kauda ma kowa tunani akanta. Dan Aisha ma sosai ta yarda da maganar shi, dan har yan zu in ta tuno tana jin nau yin k’anwarta Khadija “.
Ana gobe Khadija zata koma hutu, Aisha da Maryam k’anwar Umar suka zo gidan, inda basu suka ta fiba sai dare”.
Umar ko kusan kullum sai yazo gidan su Khadija, sai dai gaisuwa kawai ke had’asu, ita ma in bata ganin idon Mama bata gaida shi. Umar da ya ji tafiyar Khadija gobe kud’i masu yawa ya ba Mama ya ce ta bata. Dan Mama har sai da tai fad’an kud’in ta ce sun yi yawa”.
Adaran ranar da Khadija zata tafi, tana zau ne ita kad’ai a bedroom d’inta ta yi ta gwumi ta yi nisa acikin tunani mama ta shigo.
Mama hannun Khadija ta kamo ta ce, “Khadija lafiya?, ko duk tunanin barin gidan ne? “. Murmushi Khadija ta yi, ta ce, “Tom Mama ai ko kad’anne mutum zai yi tunani in zai bar gida”.
Murmushi Mama ta yi, ta ce, “Tom ai kece kika zab’i nesa, gashi Yayanki Umar ya baki”.Mama ta mik’a mata kud’in da Umar ya bata. Khadija amsa ta yi ta ce, “nagode, ai mai godiya”.
Mama ta dad’e suna fira da Khadija sannan ta tashi ta tafi ta kwanta”.
Washe gari musalin 10:00AM jirgin su Khadija ya tashi suwa lagos”.
Khadija na sauka ta je ta siyo abinci ta ci, sannan ta gyara d’akin ta, ta kwanta tana hutawa.
Washe gari, Khadija ta shiga School. sosai su kai Murna ganin juna ita da Hafsat, dama Hafsat ta riga taji labarin komai ga me da Khadija inda suna gaisawa ta WhatsApp”.
Haka Khadija ta mai da hankalinta ta ci gaba da karatu, sai dai kullum cikin addu’ar Allah ya sa cikin jikin ta zube ta ke”.
Akwana atashi babu waya har lokacin hutu ya kuma zuwa ma su Khadija, inda yan zu duk wan da ya kalli Khadija ya ga mai ciki.
Yan zu cikin watan shi na biyar kenan, dan ma cikin fari ba wani ganewa ake ba, kuma yan zu Khadija gaba d’aya tabar ma’amala da gyal’e sai hijabai gudin agane mata. Duk inda ake maganar tashin hankali da razana tom hankalin Khadija atashe ya ke, dan sun kusa samun hutu, dan ma hutun ba mai tsawo bane, amma duk da haka ta san wannan karan kallo d’aya Aunty Aisha za tai mata ta fahimci halinda ta ke ciki,hakan yasa Khadija hankalinta ya yi k’ololuwar tashi”.
B’angaran Umar ko har yan zu bai kuma Kiran Khadija ba, dan ya yi alk’awarin bazai k’ara kiranta awaya ba”.
Yau Khadija sukai final Exam. Bayan sun fito ne, Khadija ta kalli Hafsat da jajayan idonta, dan yan zu kukan ya fara gagarta, hawayan sun k’are acewarta. Ta ce, “Hafsat k’arya dai tazo k’arshe, inda yan zu kallo d’aya za ai min asan ina da ciki, kinga ko k’arya ta zo k’arshe”.
Shiru Hafsat ta yi, Sannan ta ce,
“Tom ni kaina Khadija gaba d’aya tuanin ki Kawai nake, amma dan Allah karki kaji da abin da na ke fad’a miki, addu’ar nan dai ita za ki ta yi, insha Allah ko mai zai zo da sauk’i “.
Ahaka dai suka rabu, Hafsat na ta kwantar ma Khadija da hankali da kala mai masu dad’i”. Khadija na kwance tana tunanin tafiyarta gobe. Kira ya shigo wayarta. Khadija cikin fad’uwar gaba ta amsa Kiran ganin Mahaifiyarta ce mai Kiran, tasan tafiyar ta gobe za tai ma ta……. ✍️
Duk yadda kike tunani labarin ba haka ya ke ba Sister,
Ke dai ki bini ahankali , za ki fahimci inda zan dosa.