JAMALUDEEN COMPLETE
Mallan Adamu haifafen garin Zaria neh, yana zaune a Unguwar Iya dake cikin zaria city, Yana zaune da matarsa Amina da y'arsu guda d'aya mai suna Jaleelah anma ana ce mata Ummy saboda sunan Mahaifiyar mallan Adamu ne...
Jaleelah yarinya ce y'ar shekara goma sha takwas, tanada Ilimin addini daidai misali, Na boko ne bata samu ba dan a primary five ta tsaya kasancewar Mahaifinta baida hali, ga kuma chuta ta Makanta data sameshi lokaci guda..
Hakan ne yasa Ummy da Mama suka kasance cikin wani hali har takai Ummyn ta koma Suyan wara kofar gida dan su samu abin rufawa juna asiri. Ummy yarinya ce Mai tarbiya gata kyakyawa ga diri hakan ne yasa samari ke b'ulb'ulowa tako ina suna santa saida yawancin su da maganan banza suke zuwa hakan ne yasa bata kulasu.
Saurayinta d'aya mak'ocin su Sunanshi Bilal, yana matuk'ar tausayama halinda su Ummy suke ciki duk da shima ba wani k'arfi gareshi ba, lebura neh so dayawa yakan sayo d'an kayan abinci daidai gwargwado ya kawo gidansu Ummy, hakan ba b'aramin d'adi yakema Mahaifanta bah.
Yau tana shara a tsakar gida ta jiyo tarin Baba gashi Mama ta fita taje mak'ota barka, tsintsiya ta aje dasauri ta k'arkad'e hannunta a jikin k'od'adiyar zanin atamfan dake jikinta, kwance ta sameshi yana tari sosai, idanunshi sun jujuya, tsugunnawa tayu gabanshi ta fashe da kuka
"Sannu Baba, Sannu Allah ya baka lapia"
Tarin yake ba k'ak'autawa,
Kuka take duk ta rud'e dama ita abu kad'an kesata kuka, fitowa daga d'akin tayi dasauri ta ja hijabinta dake igiya tayi waje, a xauren gidan ta had'u da Mama tana ganinta ta k'ara fashewa da sabon kuka
"Mama jikin Baba ya tashi"
Ai ba shiri Mama ta shiga gidan hankali tashe, d'akin ta shiga ta tarar dashi kwance sai aman jini yakeyi, nan da nan Mama ta fashe da kuka tana tsugunne gabanshi, Ummy ta shigo d'akin dasauri idanunta cikeda kwalla
"Mama mu kaishi Asibiti"
D'agowa Maman tayi hawaye na bin idanunta
"Da wani kud'i zamu kaishi Asibiti Ummy?, kinsan bamuda kud'i"
Fita tayi da gudu kamar tab'abba ta fita kofar gida tana waige waige, kuka takeyi sosai lokaci guda tana Addu'a, daky'ar ta samu me napep ta tareshi tace
"Mahaifina ne baida lapia dan Allag badan niba ka taimaka min mu fito dashi"
Bah musu ya fito daga napeep din suka shiga gidan, har lokacin Mama na zaune gaban Baba tana kuka, ganin Ummy ta shigo da wani yasa ta d'ago dasauri
"Mama mu kamashi akaishi Asibiti"
Bah musu suka kamashi suka fito dashi, komawa Ummyn tayi ta shiga d'akinta ta d'auko wani k'ullin bak'in leda
a hankali ta kwance ledan, kud'i ne yan dari biyar ta rungume kud'in tareda fashewa da kuka, kuka take sosai tana cewa
"Kayi hak'uri ya Bilal zanyi anfani da kud'inka"
Ta maida kud'in ta kulle ta fito daga gidan dasauri, Asibitin Gambo sawaba suka nufa, suna lsa ta biya mai keke napeep nurses sukayi Emergency dashi, Suna nan tsatsaye wata nurse ta fito tana rik'e da wani paper a hannu
"Ku kuka kawo wannan patient din koh"
Mama ta matso
"Eh mune"
Papern ta mik'a mata tana cewa
DOWNLOAD HERE👈