JARIRI CHAPTER 5 BY AMEERA ADAM
Jariri na ganin haka ya tuntsire da dariya harda riƙe ciki, zage Daddy ya ci gaba da yi yana ci gaba da waƙar Ɗan maliyo maliyo. Sai da ya gaji dan kansa sannan ya yi tsalle ya dira akan ruwan cikin Daddy yana cewa. “Kaji tumbuloƙoƙo tumbul-tumbul” baka jin ƙarar komai sai sukuwar Jariri akan ruwan cikin Daddy, yana sauka ya je ya ɗauko kan ragon ya ɗora a cikin Daddy ya janyo hannuwan Daddy ya ɗora akai sannan ya buɗe ƙofa ya yi tafiyarsa.+
Da asuba Inno ce ta fara tashi har tayi alwala ta ce. “Kai anya Salisu ya tashi kuwa na ji shiru kamar masu baccin mutuwa banda rashin ɗa’a sallar asuba abar wasa ce, idan mutum bai so yake a ɗebe masa albarka ba a shiga jam’i yana kwance.” Dada ɗaya daga cikin ƙawayen su Inno ne da suka zo suna dan ɗakin Inno cike yake da ƙawayensu tsofaffi wasu ma sun daɗe basu haɗu ba. Dada tayi caraf ta karɓe zancen.
“A’a Rakiya kika sani ko bai dawo daga masallaci bane?” Goggo da tashin ta kenan ta riski maganar ta ce. “Gaskiya Salisu bai tashi ba ai baya taɓa tafiya masallaci sai ya yi salawaitun bugo ƙofa.” Inno fuuuu ta nufi bakin ƙofa kamar wacce aka dakatar da ita ta dawo ta ce. “Bari dai nayi tawa sallar kar na rasa jam’i na ɓalɓace dan wannan ba halin ɗa’a bane” Sallah suka gabatar ko carbi basu ja ba suka ji daga falo Mummy na rafka salati cikin kukan.
Inno cikinta har karkarwa yake ta ce. “Shikenan ni dama nasan ruwa baya tsami banza. Wallahi Salisu bai taɓa yi mini rashin ɗa’ar nan ba” da sauri suka fice har suna gware da junansu, suna zuwa Falo kowa ya yi turus dafe ƙirji suka yi suna ja da baya ganin abin da yake faruwa. Inno da Goggo cikin haɗin baki suka, “Wallahi shi ne” Mummy da ke ta kuka tana jijjiga Daddy ta ce. “Inno shi wa?” Inno ta ce. “Jariri wallahi ba kowa zai yi wannan rashin ɗa’ar ba sai shi” kafin Mummy tayi magana Goggo ta sheƙawa Daddy ruwan da ta ciko a cikin kantamemen kofi. A zabure ya sauke ajiyar zuciya sannan ya miƙe ya sunkuya ya dafe ƙugu yana cewa. “Salawaitun salo, salawaitun salo…” gabaɗaya sakin baki suka yi suna kallon ikon Allah Goggo ta ce. “Yau ni nake ganin salawaitun rayuwa Salisu wani sabon salon salawaitun ka samo haka?” Sai a lokacin Daddy ya ɗago ya kallesu sannan ya koma daɓar ya zauna ya fashe da kuka yace. “Inno ku taimaka wallahi zai iya kasheni” Inno ta dafe ƙirji ta ce. “Wa?” Daga wajen bakin ƙofa suka ji ance. “Ni ne nan…” tun basu gama jin abin da Jariri yake faɗa ba gabaɗaya zabura a guje kowa ya yi ta kansa.
Daddy da Mummy da Wasu ƙawaye su Inno mutum biyu suka shige ɗakin su Inno, Inno da Goggo tare da sauran ƙawayensu suka faɗa ɗakin Mummy, kowannen su cikin tashin hankali suka banko ƙofar tare da dannan mata sakata. Inno jikinta banda karkawa babu abin da yake yi Goggo kuwa ta saki fitsari babu adadi a gurin, wata ƙawarsu me suna Uwani daga tsaye ta dinga sakin zawo, basu yi aune ba suka ji Jariri ya fara buga ƙofa yana cewa. “Ku buɗe ƙofarnan kona ɓalle ta na shigo, idan kuka bari na shiga ƙafafuwanku na cinye” Uwani ta gwalo ido waje ta ce. “Dan Allah ku buɗe kar ya shigo ya illata mu” Goggo ta ce. “Baki san salawaitun hatsabibancin sa amma da baki yi fatan buɗe ƙofar ba” Da ƙarfi ya ci gaba da bugawa Uwani na jin haka ta yunƙura ta nufi ƙofar zata buɗe.
Gabaɗaya suka yi kukan kura suka cakumo ta Inno ta ce. “Mu danna ta banɗaki idah ba haka ba tsaf zata nuna mana halin rashin ɗa’a, da ta sabautamu gwara mu ɗebe mata albarka.” tana rufe baki suka shiga kiciniyar tura Uwani banɗaki ƙiƙi-ƙiƙi tana cijewa.
Daddy na shiga ɗakin bai tsaya wata-wata ba ya janyo jibgegen bargonsa ya ƙudundune a ciki yana sauke ajiyar zuciya, Mummy da tayi firƙai-firƙai ta zagaya cen bayan gado laɓe sai ƴan idanuwanta kake hangowa. Ƙawayen su Inno Inna Lami da Ta rasulu sai sakin fitsari suke daga tsaye.
Bayan wasu Awanni Nusaiba da Hafsa ne suka fito tsakar gida jin shirun ya yi yawa, dai-dai nan Halifa da Salim suma suka fito Salim yace. “Wai yau lafiya naji babu motsin su Daddy ga su Inno masu sammako ma basu fito ba” tare suka tura kofar falon suka shiga Hafsa ta fara cewa. “Innoniyos ina kuka shiga ne” sai da suka je tsakiyar falo sannan suka ji motsi akan fanka, ɗaga kan da zasu suka hango Jariri ya diru yace. “Oyoyo Daddyna” zaro ido suka dinga yi suna ja da baya Nusaiba na ganin haka ta juya a guje ta fice Hafsa da Salim ma suka rufa masa baya, Halifa ma juyawa zai fita da gudu sai kuwa Jariri ya yi caraf ya riƙe masa wando ta baya.Halifa da ƙarfin gaske ya riƙe kofa yana zunduma ihu da neman agaji, Jariri dariya yake ƙyaƙyatawa rarrafowa ya yi ta gadon bayansa ya ɗafe dai-dai wuyan Halifa yace. “Daddy kamun makawuya” Halifa nan take cikinsa ya kaɗa wata dabara ta kawo masa akan yasa hannu ya fisge Jaririn ya wurgar, da sauri ya kai hannu da niyyar wurgar da Jariri aikuwa ƙam yaji ya maƙaleshi cikin wata irin murya Jaririn yace. “Wallahi ka cireni da kanka zan tafi Daddy” Halifa na jin haka ya fashe da kuka yana cewa. “Jama’ar gidan nan ku kawo mini ɗauki Jariri zai kasheni” Inno dake cikin ɗaki ta fara ƙyaƙayata dariya harda tuntsirawa Goggo ta leƙa ta window ta hango yadda Halifa ya yi zuru-zuru yana ihu, ta fara dariya ta ce. “Cen dai kai da shi kun fi kusa lokacin da muka gaya maka salawaitun rashin ɗa’ar da ya yi mana ba ƙaryata mu kuka yi ba.” Inno cikin dariya ta ce. “Hansai wallahi da Jaririn nan zai birgeni ya nuna Halifa halim rashin ɗa’a” tana faɗa ta kuma tuntsirewa da dariya ta ci gaba da cewa. “Da zai samu mazaunansa ya dinga gartsa masa cizo da ya gane karyatamun da ya yi.” dukda suna cikin fargaba lokaci ɗaya suna kwashe da dariya.+
Goggo ta ce. “Ita kuma ƴar banzan cen me salawaitun fi’ili wai ita tayi Ɗa, na so ace lokacin da take shayar da shi ya fille duk abubuwan biyu muga ƙaryar iya shegen salawaitun tsiya.” wannan karanma suka ƙara kwacewa da dariya.
Suna cikin haka suka ji Halifa ya ƙwalla ƙara yana cewa. “Bani da shi wallahi bani da bashi ba nine uwarka ba ni Daddynka ne” kasaƙe suka yi har gware suke wajen ganin sun leƙa ta window dan ganin abin da yake faruwa.
Halifa akan dole ba dan yaso ba ya saki ƙofar suka fara kokawa da Jariri, Jariri tun ƙarfinsa yake kiciniyar buɗe rigar Halifa yana tura kansa ciki yana cewa. “Yunwa nake ji ni zan sha” Halifa da ya gama haɗa gumi yace. “Dan Allah ku taimaka mini zai zuƙeni” Inno ta kwashe da dariya ta ce. “Gwara ka tatse banza da ba ni ka so nunawa rashin ɗa’a ba, zuƙe shi ku kuka haifo jaraba ai” suna cikin wannan kokawar ji kakr Ƙiiiiii anyaga rigar Halifa da sauri Jariri ya ɗafe Halifa yana wawure-wawure.
Daga cen ɗaki Daddy na cikin bargo ya zuro kai yace. “Mummy yara muna ji muna gani haka zamu bar Halifa a hannun hatsabibin cen?”
Ta rasulu tayi farat ta ce. “Barshi su ƙarata cen gayyar tsiya. Kai Jama’a Halifa ya haifi ƙaddarar duniya, wallahi yau idan Ra
kiya ce zata ƙara haihuwa idan na dawo gidan ubana Me sabulu zai dawo duniya.” Mummy ta miƙe ta ce. “Gaskiya bazan iya barin Halifa a cikin wannan halin ba bari na buɗe ƙofa naje na ceto Ɗana sai dai duk abin da za’ayi ayi.” Daddy na jin haka ya zaburo yace. “Sadiya karki buɗe ƙofar nan, karki buɗe wancen gundulallan ya shigo wallahi ƙarasa ni zai yi.” Mummy na zuwa bakin ƙofa Daddy ya taso da gudu ya janyota, nan take suka shiga kiciniya a tsakaninsu ana cikin haka su Ta rasulu sai ji sukai tusa na rashi a ciki suka rasa wanda yake yi tsakanin Mummy da Daddy, Inna Lami tuntsire da dariya ta ce. “Jarabar duniya yau me nake ji yana tashi kamar salansar mashin.
Daga cen wajensu Halifa kokawa sosai suke yi, Halifa ba ƙaramin mamakin ƙarfin wannan Jaririn ya yi ba ganin Jaririn har ƙasa yake damfarar da shi. Wannan karan Jariri ya samu nasarar jefar da Halifa cen ƙasa da sauri ya yi sufa ya faɗa kanshi yana wawure-wawure yana cewa. “Daddy zan sha.” Inno na ganin haka ta kuma fashewa da dariya da ƙarfi ta cewa Jariri. “Maza tsotse shi tass idan kaso komawa ciki ma ka danne shi ka koma Goggo ta ce. “Haba Rakiya wannan ai sabon salon rashin imani ne yanzu idan ya nemi komawa ciki a gurin Halifa ai mun ga ta kanmu, ba Halifa kaɗai ba hatta mu sai mun shiga siraɗallazi.” Sai kuma Goggo ta tuntsire sa dariya harda hawaye sannan ta ce. “Kai jama’a ni da Adahama waya ga Halifa da sake sabuwar haihuwa.” Aikuwa lokaci ɗaya suka ƙara kwashewa da dariya Inno ta ce. “Da kuwa ranar munga ɗiban albarka ido biyu” Uwani da ke cikin banɗaki ta ce. “Rakiya ki dubi Allah da ma’aiki ku buɗe ni daga bayin nan wallahi banda zarni da wari babu abin da nake shaƙewa a ciki” Inno ta ce. “Uwani wallahi idan kinga kin fito sai ƙurar wancen Ƙunduss ɗin ta lafa dab baza ki jama bana rawar banjo ba haka kawai.”+
Halifa ganin Jariri na niyyar cimmasa yasa ya ci gaba da ihu yana neman taimako amma shiru kake ji, Halifa na ganin haka ya rushe da kuka yana cewa.
“Jama’a dan Allah ku agaza mini wallahi zai kashe ni” ganin ihun ba zai kaishi ba yasa Halifa ya taƙarƙare ya ɗurmawa Jariri dundu a abaya da sauri Jariri yayi tsalle ya ɗaga shi yana muzurai da zare idanu. Da gudu Halifa ya miƙe yana shirin fita wannan karanma Jariri yayi caraf ya ƙafar wandonsa. Halifa cikin kuka yace. “Dan Allah kayi haƙuri ɗana wallahi bazan ƙara dukanka ba.” Jariri sakinsa ya yi yace. “Tashi Daddy ” ba musu Halifa ya miƙe fuska duk ta jiƙe da hawaye.
Jariri ya kalli ƙofar ɗakinsu Inno yace. “Kaje ka buɗe ƙofar ɗakin cen, ni kuma zan buɗe ta cen” ya ƙarasa faɗa yana kallan ƙofar ɗakinsu Daddy.
Halifa daɗi yaji dan yasan wannan da ma ce ya samu da zai iya guduwa ta ruwan sanyi ba tare da ya wahala ba, kamar Jariri yasan tunanin da Halifa yake yi kenan yace. “Kuma wallahi Daddy idan ka fita daga ɗakin sannan sai sawa gidan nan wuta kowa ya mutu.” yana gama faɗa ya tofar da yawu a ƙasa sai ga wuta ta kama a guri, jikin Halifa ne ya ɗauki rawa da sauri yace. “To Ranka shi daɗe sai abin da ka ce.” Jariri tafiya ya fara yi yana tafe yana rangaji yana tura ciki gaba.
Su Inno na jin haka suka rafka ihu lokaci ɗaya suna fashewa da kuka, Goggo harda sakin fitsarin tashin hankali.
Halifa bai damu da kukan da suke ba dan shi daɗin hakan ma ya ji da ace shi kaɗai zai sha izayar Jariri gwara ace kowa ma yaji ba daɗi daa mutuwar yawa kaka ce.
Jariri bugu ɗaya ya yiwa ƙofar ta ɓalle yana tsaye yaga Mummy da Daddy suka riƙe da juna sai gumi suke, ƙugu ya riƙe yana kallansu sannan ya nuna su da hannu yace.
“Ku fito nan”
Ta rasulu na jin haka ta hau rawar jiki gumi na keto mata ta ko’ina, daga Daddy har Mummy rasa wanda zai fara yin gaba akayi, Daddy ne ya kalli Mummy yace. “Kije ana magana mana”
Mummy maƙalewa tayi tana tirjewa ta ce. “Kai ka wuce mana” Jariri yace. “Wallahi duk wanda ya bari nazo gurin da yake sai ya goya kansa…” Tun bai rufe baki ba da sauri suka matso suka fito cikin falon.
Jariri bai bi ta kansu ba ya juya gurin Halifa da yake ta faman buga ƙofa su Inno na kuka, yana zuwa bugu ɗaya ya yi mata itama ta ɓalle sannan ya leƙa ya nuna su Inno yace. “Maza kuma ku fito” bai waiwaye su ba kai ƙatsaye ya fice daga falon ya nufi ɗakin da su Nusaiba suke itama bugu ɗaya suka yi mata ta buɗe sasannan ya taso su suka nufo babban falo gurin da ya bar Halifa da su Daddy.
Jariri kallan Daddy ya yi yace. “A duk faɗin gurin nan wa kafi so” Inno da ke wajen su Goggo har bangaje su take ta matso ta ce. “Ɗannan gani nan nice uwarsa” Jariri ya cewa Daddy. “Wai haka ne?” Daddy ya gyaɗa kai sannan yace. “Hakane ranka shi daɗe.”
Jariri ya wuce ya fisgo cajar Laptop ya miƙawa Daddy yace. “Ungo kayi mata ciki ashirin” Daddy shiru ya yi yaƙi karɓa Inno nan take ta hau zare idanu. Jariri yasa hannu ya janye Daddy da Inno gefe yace.
“Ku kun fita daga cikin lissafi. Ku fa kowa ya nuna mini wacce yafi so ko wanda ya fi so” duka shiru sukayi ganin gaka yasa Jariri ya guga musu tsawa yace.
“Ba za ku yi magana ba?” cikin haɗin baki suka ce. “Babu wanda muka fi so” Jariri ya gyaɗa kai yace. “To shikenan”
Yana juyawa ya tawagar Mudul nan take sai ga wasu ƙananan Jarirai sun fara shigowa daga waje kowanne hannunsa ɗauke da bulali, dakatar da su Jariri ya yi sannan ya ƙarasa gurin Daddy ya ɗaga bulalar hannunsa ya yi tsalle ya zuba masa a ƙeya, nan take Daddy ya hau susa yana roƙon Jariri. Jariri bai saureshi ba ya juya gurin Inno tun kan ya ɗaga bulalar ta fara kuka tana roƙonsa.
Iya ƙarfinsa ya ɗaga hannu ya ɗaurewa Inno ƙeya da bulalar nan take ta kwanta a gurin banda birgima babu abin da take yi, Kallan ƴan uwansa Jarirai ya yi yace. “Na baku dama kuyi ta zane su da bulalun hannunku.”
Tun bai rufe baki ba suka fara zuba musu mulalin hannunsu, Ta rasuwa duka biyu akayi mata ta sume a gurin Inno, Goggo da Inna Lami tun suna cikin hayyacinsu har suka fara fita. Ganin wannan ba zata kai su ba yasa Daddy yayi kukan kusa ya girgije ya miƙe haka ya dinga wartar Jariran ɗaya bayan ɗaya yana bugawa da ƙasa.