JAWAHEER
CHAPTER 1
Page 1
Kasar Spain kasa ce da take da mutane fararan fata wato turawa sannan ita wannan kasar yare daya takeyi wato Spanish sai wasu tsirara suke English a airport mutane ne makil anata ihu tare da gudu Wanda yaja hankalin Wanda basu san dalilin ihun ba, suma suka fara dubawa koh lafiya wani matashi ne kallo daya zaka masa kasan cewa shima bature ne jami’an tsaro ne a zagaye dashi yayin da mutane suke ta faman miki mishi paper da biro wasu kuma nata faman daukanshi hoto tafiya yakeyi yayin da yake daga musu hannu shima wata yarinya karama yaga tana miko mishi takarda da biro tsayawa yayi ya amsa tare dayi mata signing sannan ya shafa kanta ya mika mata takardan har waje mutane suka bishi inda motoci ke jiran su, daya daka cikin motar aka bude mai Ya shiga yana daga ma mutane hannu jan motar akayi Suka bar wajan, wani dangareren Gida suka nufa bayan Sun faka aka bude motar fitowa yayi ya nufi kofar shiga cikin gidan bell ya danna wata baturiya daka gani Mai aiki ce dan Tana sanye da kayan masu aiki itace ta bude kofar ganin wanda yake bakin kofar yasata saurin rungumeshi tare da fadin sannu da zuwa duk cikin yaren Spanish suke magana da Fara’a ya amsa da nagode ina Dad? Tace yana ciki yan….. Kafin ta karasa sai ga wani mutum ya fito dan dattijo da sauri ya nufi saurayin yayi hugging dinshi yana fadin My son barka da zuwa dan sakinshi yayi tare da buga kafadan shi yana fadin ina alfahari dakai murmushi saurayin yayi tare da fadin ngd Dad zama yayi akan kujeran dake falon wanda yasha kayan more rayuwa tare da fadin mai aka ajiye min? Dad yace your favorite mai aikin gidan ce ta Kawo mai coffee amsa yayi tare da fadin thank gina yana dan hadawa da turanci cikin maganan shi, Sha ya farayi sannan ya tashi ya nufi dinning inda ya bude wata hummer ya zuba abinci ya fara ci bai wani ci da yawa ba ya tashi ya haura dakinshi dake gidan wai waye wannan saurayin ne….. Muhammad samir sunansa dan asalin kasar Spain ne domin a nan mahaifinshi yake dan kwallon kafa ne a laliga wanda yake bugama FC Barcelona yana daya daka cikin manyan yan kwallon da ake alfahari dashi a duniya baki daya Wanda akafi sani da m samir tun yana yaro Dad dinshi yace Mum dinshi ta rasu bai taba ganin koda hotan mum dinshi ba, abun yana damunshi sai yasa bai cika zama kasar shi ba dan yana fushi sosai idan ya tuna bai san waye mum dinshi ba, a hannun gina ya taso duk da ita ba musulma bace amma mahaifinshi na kula Dashi tun yana karami yake son buga kwallon kafa kasancewan son kwallonshi yayi yawa yasa bai wani yi karatu mai zurfi ba daka secondary Skul ya gama ya fara buga kwallon kafa duk da sai mai hanya yake samu shima Dad dinshi yana daya daka masu kudin kasar Spain sai yasa bai wani sha wuya ba wajan hayewa, da yana premier league inda yake buga ma Manchester United daka baya ya koma laliga yake buga ma Barcelona wanda aka bashi number 7 domin irin cin kwallon da yake yi number dinne ya dace Dashi sunan mahaifinshi Muhammad Ali, sai yake amfani da sunan Dad din nashi Kafin nashi, m samir matashin saurayi kwata2 shekaranshi 28 a duniya yana da kudin Dashi kanshi bai san nawa ke gareshi ba domin bayan kwallo yana business amma bashi yake kula dashi ba yana da budurwa mai suna sonia yar kasar England duk da ba musulma bace amma yana sonta kuma ita yake son aura tunda addininshi bai haramta mishi hakan ba wannan shine kadan daka labarin shi……
Koda ya shiga daki wanka yayi yasa boxer da singlet kwanciya yayi tare da daukan wayanshi yana dannawa message ne kala2 gasu nan duk bai bude ba ga wasu na kara shigowa Dan tsaki yayi domin bai san ta yanda zai fara karantawa ba inda yana tare da Sonia ne data karanta mai dialing din number dinta yayi ya kara a kunne bugu biyu ta daga tare da fadin swt hrt I miss you wen r u coming bck dariya yayi mai sauti tare da fadin Sonia yau fah nazo Spain and jiya muna tare tace kasan bana son kayi nisa Dani in baka dawo ba nan da 1 week zan zo Spain yace OK zan dawo b4 d tym kafin nan munyi match din da za’ayi inma ban dawo ba sai kizo dan nima nayi missing dinki sosai nan sukaci gaba da hira na soyayya duk cikin harshen turanci kafin suka kashe wayan.
*NIGERIA*
Garin abuja wata matashiya ce cikin riga da wando tasa karamin gyale ta yane kanta kallo daya zaka mata kasan yar wani babban mutum ce domin cikin falon da take zaune ya isa ya nuna maka suna da dukiya yarinyar fara ce tana da tsawo amma ba sosai ba sannan kuma ba wada bace tsawonta dai normal tana da manyan ido sosai ga gashin ido kaman tasa lashes gata fara kaman kalan larabawa kyanta ya wuce duk yanda mai karatu yake tunani wani saurayi ne ya shigo falon da sauri ta tashi tana fadin Ozil dan Allah karfe nawa barce suke da wasa nasha koh 2 ne gashi nasa duk channels din da ake kwallo amma ba’a fara ba, yace toh m samir ai ba zasu nuna ba a nan nima yanzu gidan ball zani inga irin cin da za’a ma Barcelona tace haba dai muna fa da m samir taya za’a cimu dariya yayi yace haba mu madrid ai muke da yan wasa ba kuba gidan madara tace dan Allah ni mubar wannan musun muje Gidan kallon tare in yaso in mun dawo asa mana irin dish din Gidan kallon, wata mata ce ta amshe da fadin amma kam jawaeer kina da aiki dan rashin mafadi da kamun kai sai kice zaki Gidan kallon ball bayan kin san duk Maza ne a ciki babu mata? Kai kuma kabir harda biye mata koh? Baki ta turo tare da fadin mum dasu M samir za’a buga fa kuma kin san in ban ganshi ba zan shiga cikin damuwa, Mum salati tayi tare da fadin jawaeer anya ba gamo kikayi ba ki dauki son duniya ki daura ma wanda bai san dake ba bai masan da zaman ki ba may be ma bai san kasarki Nigeria ba, tace mum taya zaki ce bai san Nigeria ba bayan anayin World Cup nidai Mum mun tafi kallo sai mun dawo ta kalli kabir tace Ozil muje dan Allah tym na tafiya fita sukai suka bar Mum na jimami tare da tausayin yarta ita kuma kalan jarabawan ta kenan son dan kwallo har take fadin shi zata Aura in bashi ba babu wanda zata Aura gashi ita ba yarinya ba balle ace yarinta ne tunda yanzu tana shekara 20 dai2 a duniya zama Mum tayi tana tuna baya lokcin da jawaheer taga m samir ta rude take fadin shi zata Aura har take gaya ma dad dinta kullum tayi sallah sai tace Allah yasa ya aureta wai wacece jawaheer?…….. Ku biyoni dan ji yawan comment shi zai nuna min kuna son ci gaba…..
Alhaji Jibrin mai dala dan kasuwa ne na daya wanda a Nigeria ake alfahari dashi bama Nigeria ba harta kasashen waje baya siyasa duk wani Abu da akeci shi yake kawo wa babu wanda bai san sunanshi ba a Nigeria harta karamin yaro yasan Alhaji Jibrin mai dala yana daya daka cikin masu jerin masu kudin duniya za’a iya cewa yana cikin na hudu ko na uku matarshi daya hjy bilkisu yaransu uku umar shine babba yana aiki a nnpc yana da Mata sai khalil shi bashi da aure ya kammala karatun shi Oxford sai jawaheer da take karatu a nan abuja tana 2lv tana karantan English duk da dukiyar su sunyi karatun addini dan dukansu babu wanda bai sauke al’qur’ani ba da sauran littafai, mahaifinsu yana matukar ji da jawaheer baya iya musa mata ga duk abunda take bukata kodan ita daya ce Mace yarshi oho, jawaheer kyakyawa ce ajin farko gata fara Sol kaman balarabiya ga manyan ido ga lips dinta Pink gwanin Sha’awa tana da hanci dogo siriri komai dai Alhmdlh, kabir Abokin khalil ne yana zuwa Gidan suna kallon ball jawaheer bata son kwallo koh kadan gashi idan anayi su Khalil a falon Gidan suke zama su kalla wata rana jawaheer ta dawo daka lecture taga suna kallon ball zama tayi tana dan yatsina fuska a dai2 lokacin akaci kwallo khalil ya kwala ihu kallon TV din tayi taga wanda yaci kwallon gabanta ne taji yana dukan uku2 M samir taji ana ta fadi shi yaci kwallon wani irin dadi takeji da taji musulmi ne nan ta Fara tambayan Khalil waye wannan yace M samir kenan tace wani team yake yace Manchester United lokacin yana Man u bai koma barce ba, wayanta ta dauka tayi searching sunanshi a Google nan taga biography nashi da pictures dinshi ta Fara saving tun daka ranan ta fara kallon Ball kabir kuma ya zama abokinta kullum suna cikin waya yaushe za’ayi premier league sometimes ma har Gidan ball take zuwa taga koh an rubuta in Man u za suyi wasa tun bata fadin manufarta ba harta fara gaya wai ita shi zata aura Mum dinta inta fara maganan tsaki takeyi tace bata da hankali Dad dinta kam biye mata yakeyi in Mum dinta taji hakan sai tabar musu wajan dan ba zata iya jin wannan shirmen na jawaheer ba in banda abunta ina ita ina farin fata bature mai kyamar bakin fata yau koh kasar su kaje haka za suyi ta nuna maka kyama musamman ma idan suka ganka bakin fata ita gwara jawaheer dinma fara ce sol, duk wani receiver jawaheer tasa ansa a Gidan dan kawai saboda kallon ball dakinta ta manne shi da hotunan m samir duka Khalil dan Manchester United ne kabir kuma dan Madrid suna ce mai Ozil sai itama jawaheer yar Manchester United ce da M samir laliga suka siyeshi ya koma Barcelona itama tabar man u ta dawo Barcelona dan ita M samir take bi, jawaheer bata kula ko wani saurayi saboda a ce warta m samir zata Aura wannan shine labarin jawaheer bari mu dawo kan labari.
Koda suka isa gidan kallon ball cike yake da mutane makil duk maza jawaheer tsayawa tayi tana tunanin yanda zata shiga kallon kabir tayi tace Ozil taya zan shiga?bude kofar motar yayi tare da fadin ina zuwa fita yayi jim kadan sai gashi yace mata ta fito, fita tayi ta bishi sukai ciki Ashe Gidan kallon ball din waje2 ne akwai na yaku bayi akwai na masu hali kuma yana da girma daki daya suka zauna ita da kabir babu kowa a ciki gashi har anyi nisa, Madrid suna cin daya Barcelona kuma 0 ana 1-0 jawaheer kallo takeyi amma kaman za tayi kuka dan takaici domin su ake ci shiko kabir sune suka ci, M samir ne ya buga wata kwallo ta shige Raga ihu ta saki tare da fadin a gooooooo wow my Luv ina sonka shiko kabir shuru yayi tare dajin haushin cin da Barcelona sukayi yanzu sun dawo 1-1 har akaje half time babu wanda ya kara ci suna nan zaune ita da kabir suna fira har aka dawo, ci gaba akayi da kallo Real Madrid ne suka kara ci jawaheer kam haushi kaman ya kashe ta ana cikin haka aka buge m samir ya fadi kasa tare da rike kafar shi jawaheer bata san lokacin data fara kuka ba buguwan sosai yayi dan haka dole aka cire shi aka sa wani jawaheer ganin haka yasa ta fara kuka Dan tasan m samir ba karamin buguwa yayi ba wanda yasa har ya kasa tashi fita tayi daka Gidan kallon da gudu tana kuka tare dajin radadi cikin zuciyarta mota ta shiga kabir yazo ya sameta yana fadin haba jawaheer maiya sameki kuma kinga kun kara ci ma, tace kabir baka ga anji ma my samir ciwo ba har an cire shi mai yasa bazan yi kuka ba? Kabir yace haba jawaheer aiba wani serious ciwo bane, tace what ba serious ciwo bane kana ganin har an cire shi kuka ta kuma Saki tare da fadin dan Allah shigo mu koma Gida kabir kafin zuciya na ta buga kabir cikin tausayin kanwar tashi kuma kawarshi tunda yanzu sunfi shiri ma akan Khalil shiga motar yayi ya kunna suka tafi babu abunda kake ji sai kukan jawaheer hmmmm.
A haka suka Isa gida yana fakawa ta fita da gudu tayi hanyar falo a hanya suka hadu da khalil tareta yayi yana fadin jawaheer kukan miye haka kufa kuka ci wasan kun cire madrid cikin kuka tace bros baka ga anji ma M samir ciwo ba, kallonta yayi na second biyar sannan yace kiyi hakuri kibar wannan kukan zai tashi a next wasa zaki ganshi dago kai tayi tace dagaske? Kai ya daga mata alaman eh yace dawa zaku buga next tace *CELTA DE VIGO* yace ok karki damu ki daina wannan kukan kabir na gefe yana kallonsu dakyar tayi shuru ta shiga ciki ido ya bita dashi yana tausayin kanwar tashi da yake ganin abun nata ya wuce tunaninshi dan shi dauka yake duk abunda take fada wasa ne amma yanzu abun ya fara bashi tsoro, kabir ne ya dafa shi tare da fadin kaga sis gaba daya hankalinta ya tashi, khalil yace ozil abun jawaheer ya fara bani tsoro fah kalla yanda take kuka dan kawai anjima M samir ciwo, kabir yace hakane amma jawaheer tana sonshi ne kaga duk abunda ya faru dashi dole taji wani iri ,khalil yace haba kabir irin wannan son yayi yawa kalla fah yanda tazo hankali tashe tana kuka, kabir yace kasan masoyi baya san ganin masoyinshi cikin wani hali, khalil tsaki yayi tare da fadin wlh abun yana ban mamaki in banda jawaheer ita da take Nigeria yar Africa ina ita ina wani bature wanda ko mutuwa za tayi bazai iya cewa yana sonta ba balle yace zai aureta haba aishi nasan bazai iya bama ace celebrity ya auri yar africa yar nigeria kuma gashi bature impossible abun kunya ne a gareshi, kawai dai sis na son daura ma kanta abunda yafi karfinta ne kawai, kabir yace haba khalil miye abun kunya a cikin SO wlh so ya wuce duk yanda kake tunani shifa so babu ruwanshi da addini launin fata, ka duba ka gani musulmi yake auran christen sannan turawa nawa ne suke auran yan africa….. Khalil ne ya dakatar dashi tare da fadin inma bature ya auri yar africa toni ban taba gani ba mutanan da suke kyamar bakar fata duk da jawaheer fara ce ita yar africa ce kuma idan suka tashi jam’u zasuyi suce bakar fata yan africa so kaga duk daya ne sannan shifa M samir duk duniya an sanshi sai kawai ace gashi yana auran yar Nigeria haba impossible mu ma bar wannan maganan kawai ,kabir yace bari kaji khalil abunda nake so ka fahimta shifa so babu ruwanshi sai kaga namiji handsome amma idan kaga matarshi sai kaji wani iri dan muni, haka sai kaga mace mai kyau amma mijinta mummuna kaman a yanka shi a boye wukan dan muni, toh kaga shi so babu ruwanshi da launin fata kyau muni kawai idan zuciya taji ta kamu toh babu ruwan mutum da duk abunda wani zaice, khalil murmushi yayi kawai tare da fadin kasan waye M samir kuwa world celebrity ne wanda ganinshi kawai tashin hankali ne sannan idan ya fito mutane zagayeshi sukeyi tako ina duk da yawan security din da suke zagaye dashi ko kasan yawan billions din da yake samu duk month banda na business dinshi da ake mai? Kabir ka daina yaudaran kanka wlh M samir yafi karfin jawaheer duk da jawaheer babu namijin da zai ganta baiyi burin auranta ba ,amma farin fata bature bazai auri jawaheer ba dan turawa suna kyaman mu sosai, kabir yace hmm khalil M samir musulmi ne bana tunanin zai kyamaci musulmai koda kuwa yan africa ne…. Khalil yace kai ni maganan nan ta isheni muje ka raka ni,kabir yace yunwa nake ji wlh ka bari inje ciki inci food din mum sai mu fita khalil tsaki ya danyi tare da fadin kazo muje mana ba dadewa zanyi ba haka kabir ya bishi suka fita tare.
Koda jawaheer ta shiga cikin falon gidan taga mum dinta da dad da gudu ta fada jikin dad din nata tana kuka cikin damuwa iyayen nata suke tambayanta ko lfya mai aka mata? Cikin kuka tace dad anjima M samir ciwo mum tsaki tayi tare da kawar dakai daka kallonsu da takeyi dan tasha ko wani abu aka mata da farko ashe shirmenta ne data saba dan haka mum take daukan duk wani abu nata indai akan M samir ne, dad ya kalli mum yace haba bilkisu mai yasa kike irin haka kina ganin yarinya ta shigo cikin wannan halin sai ki dinga sakar mata tsaki ,tace toh mai zance? Indai akan wannan shirmen ne na jawaheer bani da abun cewa sai dai tsakin yarinya kullum bata da aiki sai fadin M samir M samir haba dan Allah ,jawaheer jin haka yasa ta kara fashewa da kuka dad yace yakuri J ki kyale mum dinki sannan M samir zai tashi insha Allah cikin shagwaba tace dad dagaske? Kai ya daga ya kuma cewa insha Allah, hawayen fuskanta ta goge tare da fadin dad dan Allah yaushe zaka hadani dashi? Murmushi yayi tare da fadin Ambassador dinmu na kasar Spain bashi da lafiya yana asibiti munyi magana idan ya warke zai fadamin sai ya hadaku dariya ta saki tare da fadin kai dad ina sonka sosai dad idan ya ganni zaiji yana sona kuwa? Mum tsaki tayi ta tashi tabar wajan dan takaici shiko dad ci gaba yayi da sauraran yar tashi yace sosai kuwa ai nasan idan ya ganki saiya rude sosai dan babu wanda zaiga my daughter yace bata mai kyau ba ,jawaheer cikin jin dadi tace dad kaga idan muka hadu ina gama skul sai ayi bikin mu koh?dariya dad yayi yace duk yanda kika tsara hakan za’ayi tashi dad yayi tare da fadin bari in fita ina da meeting karfe 6 kice ma mum dinki na fita tace ok dad take care yace i will my dear fita yayi ita kuma ta nufi dakin mum din nata ,a zaune taga mum tayi tagumi jawaheer tace mum lfya kuwa? Mum ta sauke ajiyan zuciya tare da fadin yauwa zo nan ki zauna bayan jawaheer ta zauna kusa da mum take cewa dad yace in fada miki ya fita,kai mum ta daga alaman toh, sannan ta kalli yar tata tace jawaheer wai yaushe zaki gane kin girma ne? Yaushe zaki farka daka wannan mahaukacin mafarkin da kikeyi ne? Shifa wannan mutumin da kike hauka a kanshi bai sanki ba yau ki duba shekarunki ishirin a duniya amma baki da saurayi tsayayye duk masu sonki in sunzo sai ki koresu yaushe zaki fahimci cewa shi wanda kike hauka a kansa bazai iya auranki ba….. Kukan jawaheer din ne yasa mum yin shiru tana kallonta cikin kuka tace mum ba mafarki nakeyi ba Mum kema kin san M samir gaskiya ne yana cikin duniyar mu kinga mum shiba mafarki bane mum bana jin zan iya auran ko wani namiji inba M samir ba wlh mum shi nake so inama zan iya nunama duniya zuciya ta taga irin son da nake mishi mum ko kin san idan ban sami M samir ba zaku iya rasani mum wlh ina cikin hayyacina tsantsar sonshi ne yasa nake duk wannan abun mum ki fahimce ni….. Salati mum ta saki tare da fadin nashiga uku wlh jawaheer kin samu tabin kwakwalwa….. Tace mum lafiya na qalau babu abunda ya sami kwakwalwa na ,mum cikin tausayi tace inko babu abunda ya sami kwakwalwanki toh wlh kinyi gamo ne cikin biyun nan dole akwai daya ban taba ganin irin wannan masifan ba dan Allah jawaheer ki cire wannan abun indai kina so in tabbatar da kina cikin hankalinki, kuka jawaheer ta kuma saki tare da fadin mum nayi kokarin inyi hakan amma na kasa mum idan ban auri M samir ba mum bana tunanin iya ci gaba da rayuwa na mari mum ta sakar mata ji kake tas…….
Rike wajan tayi tana hawaye mum tace jawaheer ki farka daka wannan mafarkin da bazai taba zama gskya ba, keba yarinya bace ki daina yaudaran kanki kuka mum ta saki itama ta fara magana cikin sanyin murya tare da sigar rarrashi tace jawaheer ke daya ce y’ata mace ina sonki fiye da yanda kike tunani bana son duk wani abu da zai saki cikin damuwa koya taba lafiyanki nafi kowa son inga yau kin sami abunda kike so amma wannan abunda kike so bamai yihuwa bane dan Allah jawaheer ki cire wannan kwallon a ranki da shi dan kwallon da kike so ki nutsu ki fitar da miji cikin manemanki kiyi aure idan kikayi aure hankalinki zai kwanta zaki manta da wani M samir, kai jawaheer ta fara girgizawa tare da fadin kiyi hakuri mum inama zan iya hakan da nayi farin ciki Allah ya sakamin son M samir bana iya ganin zan iya rayuwa da wani namiji inba shiba mum ki fahimce ni ban taba kin duk wani abu da kika fadamin ba wannan yafi karfina ne son M samir a jini na yake wlh mum Allah shine daya koh toh idan ban sami M samir ba zan iya mutuwa tana fadin haka ta tashi tabar dakin mum din nata da gudu tana kuka itama mum din kuka ta saki tare da fadin wlh jawaheer tayi gamo dole insa ayi mata addu’a na shiga uku wannan wani irin bala’i ne ita kuma irin tata jarabawan kenan son bature wanda suke kyamar yan africa suke kiran yan africa animals mum daukan wayanta tayi ta kira maman kabir hjy hauwa, bayan ta dauka suka gaisa hjy hauwa tace bilkisu lfya kuwa naji muryanki kaman kina cikin damuwa? Tace hmmm hauwa kedai bari kawai wlh jawaheer tana son sani cikin damuwa maganan nan bata waya bace kina gida yanzu in shigo? Hjy hauwa tace ina nan ki bari bari ni inzo mum tace toh sai kin shigo ina dakina in kinzo hjy hauwa ta amsa da toh sannan suka kashe wayan.
Basu dade dayin sallama ba hjy hauwa ta shigo gidan, da sallama ta shigo dakin mum, mum ta nuna mata waje tare da fadin bismillah ga waje nan, bayan hjy hauwa ta zauna mum tace hmmm hauwa ina cikin damuwa sosai, hauwa tace mai yake faruwa bilkisu kimin bayani nan mum ta fara bama hjy hauwa labari irin abubuwan da jawaheer takeyi itama hjy hauwa salati tayi tare da fadin ikon Allah wannan wani irin sabon al’amari ne haka? Mum tace wlh kema kya fada yarinya kaman wacce tayi gamo da aljanu, hjy hauwa tace gskya nima ina tunanin haka domin inba aljanu ba babu abunda zaisa ta dinga tunanin haka Allah sarki jawaheer ,mum tace toni yanzu miye mafita? Hjy hauwa tace mafita daya shine mu kaita wajan malami ya mata ruqiya kin san akwai *BAQIN ALJANI* *sunan novel dina* da basa bayyana sai suyi tasa mutum yaita abu kaman hauka ko su hana mutum aure duk yanda akayi jawaheer tana tare dasu inko ba haka ba ai ba zata kamu da son wanda bata taba gani ba bata da tabbacin ma zai aureta ,mum tace oh ni bilkisu na shiga uku ,wlh da walaki dan jawaheer da ba haka take ba tama tsani kwallon kafa amma lokaci daya yarinya ta birkice, yanzu yaushe zamu wajan malamin? Hjy hauwa tace bari in kirashi inji yaushe yake nan, doka mai kira tayi ringing uku ya dauka bayan sun gaisa tace mlm dan Allah yaushe kake nan akwai yarinyar kawata da take da matsalan jinnu inaso mu kawota koh Allah zai sa a dace, ban san mai yace mata ba naji tace toh Allah ya kaimu sannan sukai sallama, kallon mum tayi tace yace gobe da karfe hudu mu sameshi a islamiya sannan tare da jawaheer din zamu ,mum tace Allah ya kaimu, hjy hauwa tace ameen wannan abu sai an hada da addu’a, mum tace kedai bari wlh idan kika shiga dakinta gaba daya hotan dan kwallon kafa dinne duk ta manne shi dashi sai kace abun hauka harta cup din da take amfani dashi na kwallon kafa ne duk an manna hotan yaron a jiki rannan tiles din dakinta naji tana fadin zata sa a saka mata mai hotanshi wai a cire mata na dakinta dakyar na hanata sai carpet tasa ta rufe tiles din carpet dinma mai hotan yaron, hjy hauwa tace ikon Allah jawaheer ita tata jarabawan kenan Allah sarki yarinya mai nutsuwa amma lokaci daya ta canza kiyi hKuri insha Allah gobe idan mukaje wajan mlm komai zai zo da sauki insha Allah, tashi hjy hauwa tayi tare da fadin bari in koma gida dare yayi mum tace toh ngd sai goben fita hjy hauwa tayi
Bata dade da fita ba khalil ya shigo dakin yana fadin mum ina jawaheer naje dakinta inata nocking naji shuru gashi tasa key a dakin kota fita ne? Mum tace hmmm tana ciki babu inda taje ya wuce tana can tana tunanin shirmen banzan ta data saba,khalil yace kai sis rigima dazu muka gamayi da ita wai anji mishi ciwo shine tazo tana kuka wlh mum abun sis ya fara bani tsoro fah ,nasha wasa takeyi amma naga ita dagaske takeyi ashe, anya mum ba zamu kai autarki asibitin kwakwalwa ba, hararanshi mum tayi tare da fadin ai duk kune kuka sata fara kallon wannan shirmen dariya yayi tare da fadin babu ruwana mum tunda bani nace ta kalla ba ita ta kawo kanta harta fara kallo gashi yanzu ta fini zagewa, mum ajiyan zuciya tayi tare da fadin Allah ya kyauta ya amsa da fadin ameen sannan ya tashi yana fadin mum inaso inje dubai cikin week din nan gskya, mum tace mai zaka jeyi? Dariya yayi ya fara tafiya yace indan huta mana na gaji da zama waje daya, mum tace matsalanka ce wannan tunda ga office an baka kaki zuwa kullum kafi son kaita zama gida yau baka can gobe baka can, dariya kawai yayi sannan ya fita.
Jawaheer tunda ta shiga daki ta rufe take ta faman aikin kuka a kasa ta kwanta akan hotan M samir tana shafa wajan fuskanshi tana fadin nasan zaka soni kaman yanda nake sonka inaji a jiki na, zanzo gareka very soon inaso ka nuna ma mum lafiya na qalau kawai sonka ne yamin yawa kazo ka aureni ka nuna ma mum baka fi karfina ba ni nasan kaine zaka aureni kazo kaba mum mamaki kaji my luv kuka ta kara saki tare da furta ina sonka sosai nasan yanzu kana cikin wani hali na ciwo amma Allah zai baka lfya inajin zafin jin ciwonka har cikin raina…….. Hmmm ku biyoni muga yanda zata kaya da jawaheer a wajan mlm shin zama ta yarda taje kuwa? Dagaske aljanu gareta kaman yanda mum tace duk ku biyoni …
KASAR SPAIN
M samir tunda aka fitar dashi daka filin kwallo aka nufi hospital dashi domin ba karamin faduwa yayi ba, koda aka nufi asabiti dashi hannunshi na rike da kafarshi yana cije baki, gocewan kashi yayi an kaishi asibiti kafin ace me har an gyara kafan nan labari ya bazu na ciwon da yaji inda masoyanshi keta jimami koda dad dinshi yazo hspt din cikin tashin hankali amma ganin yaron nashi a zaune yana waya yasa hankalinshi yadan kwanta saida ya gama wayan sannan ya kalli dad din nashi yana dan murmushi tare da fadin dad yakake dad din ya amsa da fadin my son ya kafan naka da fatan dai baka jin zafi sosai kai ya daga alaman eh duk cikin yaren spanish suke maganan, kallonshi dad din yayi sannan yace my son dawa kake waya haka? Ko wacece nasan soyayya kukeyi, dan murmushi yayi sannan yace sunanta sonia yar england ce ba kowa yasan muna soyayya ba sai yasa ba’a baza labarin ba, fuska mahaifinshi ya tamke sannan yace my son ka rabu da ita kasan bana son ka auri wacce ba musulma ba, M samir ya kalli mahaifin nashi sannan yace dad miye dalilinka bayan kasan addini na bai haramta min auran wacce ba musulma ba, baka tunanin jahadi zanyi idan na aureta tayu ta musulunta, kai dad din nashi ya girgiza alaman bazaka gane ba, sannan yace my son kasan kai fitaccene a duniya u r d world biggest celebrity zanso ace ka auri musulma domin duniya tasan kana kishin addininka ka duba ka gani yawanci celebrity musulmai basa auran musulma yawancinsu na rasa miye dalili sannan idan suka auri wacce ba musulma ba tarbiyan yaransu yakan banbanta kai yanzu da kake son auren yar england koh kasan yau idan kuka rabu yaran da kuka haifa sun zama nata? Sannan kasan daka ranan da suka koma gareta addininta za suyi kaga baka da ikon hana su, amma in musulma ce koda yar kasar england dince idan kuka rabu yaranka a wajanka zasu zauna duk da ka’idan kasarsu ce haka mace keda iko da yara amma su musulmai a wajansu ba haka bane tunda ba haka addininmu yace ba ,namiji shine shugaba ba mace ba, m samir murmushi yayi tare da girgiza kai yace dad duk da haka bana tunanin zan iya fasa auren sonia muna son junanmu and tunda tana sona duk wani abu da nace shi za tayi, dad murmushi yayi tare da fadin ba zaka fahimta ba har yanzu kai yaro ne, m samir dariya yayi tare da fadin dad next month zan cika 28 fah shima dad din dariya yayi tare da fadin koda 40 ka kai a matsayin yaro nake kallonka….. Shigowan dr ne yasa firan nasu ya tsaya dr yace ya kafan? Amsawa yayi da fadin ban san mai zance ba inajin zafi sosai ,dr yace kayi hakuri zai rage, kai ya daga alaman yaji, dr yace ga press nan da yawa suna son sanin halinda kake ciki ko zan iya fada musu halin da kake ciki? Yace miko min phone dinka bashi dr din yayi ya shiga wajan recording ya fara magana cikin harshen turanci tunda sako ne yake son bayarwa ga duniya baki daya musamman ma masoyanshi….. Ina lafiya ina kira ga masoya na da suyi hakuri nan bada dadewa ba zasu ganni, amma yanzu ina bukatan addu’a daka garegu ngd yana fadin haka yasa stop tare dayin saving ya mika ma dr din wayanshi tare da fadin kaba yan jarida din, dr din cikin jin dadi ya fita domin wannan maganan da yayi a wayanshi ba karamin kudi zai samu ba dan saida ma yan jarida zaiyi.
NIGERIA ABUJA
washe gari bayan jawaheer ta tashi bata fito daka daki ba ganin har 11 yayi bata fito ba yasa dad dinta ya nufi dakinta amma a rufe saida ya kira sunanta sannan ta tashi tazo ta bude mai kofar, rungumeshi tayi tana kuka tare da fadin dad dazu naji a news M samir ya sami gocewan kashi dad dan Allah ka kaini spain in ganshi ko zanji dan sauki, dad cikin tausayin y’ar tashi ya dagota daka jikinshi yana share mata hawayen fuskanta yace kiyi hakuri jawaheer ki daina wannan kukan nayi miki alkawarin hadaki dashi indai Ambassador kasar spain na nigeria ya warke, cikin kuka tace dad koba ta hanyar ambassador ba zaka iya hadamu plz dad do something ni daya nasan mai nake ji a cikin raina dad yace shikenan my dear zansa a mana visa na kasar spain zamu tafi cikin week din nan cikin jin dadi tace i luv u dad, dariya yayi tare da fadin muje kici abinci toh ,binshi tayi suka nufi dinning zama sukayi dad da kanshi ya zuba mata abinci ta fara ci mum ta fito tagansu ta tabe baki tare da fadin Allah ya baki lfya jawaheer dad yace bata jin dadi ne? Mum tace a’a ina nufin lafiyan wannan sabon haukan da yake son kamata, tamke fuska dad yayi tare da fadin kinga bilkisu ki dinga sanin abunda zaki dinga fada akan jawaheer bana son irin abubuwan da kike mata kina nunawa kaman baki damu da ita ba,mum tace Allah ya baku hakuri nayi shuru dad yace hakan shine alkhairi jawaheer na zaune tana jinsu lokaci daya kuma ta fada duniyar tunani gata a kasar spain sun hadu da M samir ya ganta ya rude harya furta mata kalman so ido ta lumshe cikin jin dadi a hankali ta furta i luv you too wanda bata san maganan ta fito ba jin mum dinta tayi tana fadin kaga abunda nake fadama koh wlh jawaheer tayi gamo da aljanu, ya kamata ka yarda da abunda nake fadama, dad baice komai ba illa kallon jawaheer din da yake tayi cikin tausayi duk cikin yaranshi yafi son jawaheer sai yasa komai ta kawo yake dauka harya biye mata amma a gskya wannan karan shima ya fara tunanin abubuwa da dama duk da dai baya son ya nuna mata ta gane, ganin irin kallon da dad dinta yake mata irin kallo na tuhuma yasa tabar wajan da sauri, mum hannu ta tafa tana fadin oh ni bilki naga takai na, yarinya sai tayi abu kaman mai aljanu anjima kuma tayi kaman mai tabin hankali, dad yace wlh bilkisu abunda kike ma jawaheer inda badan ke kika haifeta ba da sai ince kin tsaneta ne, akan me zaki dinga danganta ta da me aljanu ko tabin hankali duk wannan maganganun da kikeyi sam bai kamaceki ba ki daina ma y’ata irin wannan munanan alkaba’in bana so, shuru mum tayi bata kara cewa komai ba dad tashi yayi tare da fadin ni na tafi villa ina da meeting da shugaban kasa, mum tace Allah ya taimaka amma dan Allah kayi hakuri bana so ka fita kana fushi dani kaji my handsome, dariya dad yayi tare da fadin kin iya zolaya bilkisu ki ganni tsoho dani kice min wani handsome cikin dariya itama tace ai a haka kullum nake ganinka, fita yayi yana fadin bari in tafi 12 dai2 zamu fara tattaunawa, har yayi nisa mum tace anjima zamu fita nida jawaheer cikin jin dadi yace ko kefa ai yana dakyau ki dinga janta a jiki sosai sai kun dawo sannan akwai kudi a wardrobe din daki na in bakya bukatan taba naki ,yana fadin haka ya wuce.
Karfe hudu dai2 mum ta nufi dakin jawaheer cikin shirinta ganin jawaheer tayi tana zaune tana kallon waya nufanta tayi tana fadin jawaheer kinyi sallah kuwa? Tace mum ina fashin sallah ai, mum tace ok toh maza ki tashi ki shirya zaki raka ni, tace mum kije kawai bana jin fita yau kaina na ciwo, mum tace haba jawaheer fitan nan danke zanyi fah, tace mum ina zamu? Mum tace kedai ki tashi ki shirya ban san dogon zance, bata fuska tayi tare da fadin wlh mum kaina ciwo yake dakin bari gobe mu fita ,mun tace kin san bana son shirme koh maza ki tashi kisa hijab muje, kallon mum tayi tace hijab kuma ina zamu haka? Kodai wani ne ya rasu? Mum tace babu wanda ya rasu kawai wajan da zamu ne bana bukatan ki bini saida hijab, badan taso ba ta shirya tare da saka hijab din, mota suka shiga mum tace jawaheer ta zauna a gaba, hjy hauwa zata zauna a baya ita da mum ,bayan sun shiga driver yaja gidan hjy hauwa suka biya suka dauketa sannan suka nufi islamiyyan, hjy hauwa tace driver yayi parking bayan ya tsaida motan suka fito amma banda jawaheer mum tace jawaheer ki fito mana bude motar tayi ta fito shiga islamiyyan sukayi inda aketa karatu wani office suka shiga suka zauna babu kowa a ciki jim kadan sai ga wani mutum yazo ba wani babba bane amma kana ganinshi kasan mlm ne dan irin shigan da yayi, gaisawa sukayi sannan hjy hauwa tace mlm ga kawata nan sannan ga yarinyar nan sai a sannan jawaheer ta dago ta kalli mlm din, mum tace mlm dan Allah a mata ruqiya domin aljanu ne nake tunanin suka shigeta, jawaheer da sauri ta kalli mum din nata ta fara hawaye tare da tashi tsaye……