JAWAHEER CHAPTER 2

JAWAHEER 



CHAPTER 2


Ta kalli mum tace mum mai hakan ke nufi? Mum kallon aljanu kike min kuka ta saki mai karfi tare da fadin mum nifa lafiya na qalau bani da komai kaman yanda kike tunani kallon mlm din tayi tace mlm ka kalleni dakyau nayi kama damai aljanu ko tabin hankali? Matsowa tayi kusa da mlm ya danyi baya kadan tare da fadin auzubillah karki matso kusa dani haram, mum ta tashi ta rikota tare da fadin zoki zauna jawaheer kwace jikinta tayi daka na mum tace mum bazan iya zama ba, amma inaso mlm ya cire miki zargin da kike min yanzu, kallon mlm tayi da yayi shuru yana kallon ikon Allah, tace mlm mai zaka min ka nuna ma mum dina ni lafiya na qalau, mlm yayi gyaran murya tare da fadin da farko dai ki zauna zanyi miki yan tambayoyi kadan, zama tayi akan kujera tare da kallon mlm tace inaji, mlm yace ya sunanki? Tace jawaheer, kai ya daga alaman yaji yace kina mafarkin ruwa ko wani yana saduwa dake kai ta girgiza alaman a’a, yaci gaba da tambaya kina mafarkin gaki a daji ko kuma ana binki tace a’a, nan dai yaita mata tambayoyi tana bashi amsa harya gama ya dauko wani magani ya bata yace tasha, bata musa ba ta amsa tasha bayan ta shanye tace mlm shikenan? Yace eh an gama, tace mlm bari kaji wani abu kasan miye matsalata? Shuru yayi ba tare da yace mata komai ba tace mlm Allah ya jarabceni dason wani mutum wanda badan nan kasar bane dan kwallon kafa ne nasan zaka iya saninshi sunanshi M samir, mlm a kullum inna kwanta ina ganinshi yana kuka tare da fadamin yana da wata matsala amma idan abun ya fito kar in gujeshi duk wuya in zauna dashi sannan yamin zai aureni duk wuya yace in daure ni tashi ce, ban taba fadama kowa wannan ba kullum sonshi na karuwa a raina duk da a kullum ina kokarin in cireshi a raina amma na kasa, abun kaman kara karuwa yakeyi kullum tun bana iya fadama iyayena harna fara fada musu abunda ke cikin raina dady dina ya fahimceni amma ita mum dina ta kasa itace mahaifiyata ita ya kamata tafi kowa fahimta na tasan wani hali nake ciki ya nake ji, amma mum ta kasa fahimta na saita fara min kallon aljanu da tabin hankali wanda hakan yana batamin rai mum dina tana nesa dani wanda hakan yasa nafi sabawa da dad dina akan mum dina shuru tayi domin kukan da yazo mata lokaci daya, wajan yayi shuru na wajan second biyar sannan taci gaba da fadin kiyi hakuri mum ina fadin hakane dan kisan abunda yake damuna, ban taba soyayya ba sai akan M samir duk da bai san inayi ba, sometimes nakan so incire abun a rai na har inyi kokarin sauraran wasu amma na kasa, tashi tayi tace mlm nasan kai zaka iya fahimta na wlh bana tare da wani cuta illa ciwon so wanda nasan idan ban sami abunda nake soba zai iya zama ajalina, nasha kallo a fina finai irin abubuwan da so yake haifar wa dariya nakeyi ko ince karya ko hauka, domin ina tunanin hakan bazai taba faruwa da gaske ba, ashe ba haka bane, yau gashi abunda nake ma dariya nake ganin karya ne gashi ya faru a kaina har nima ana min kallon mara hankali, ni nasan wannan yana cikin jarabawan rayuwa na, mlm pls make my mum to understand dat i dnt have any jin tana fadin haka ta fita, duka da ido suka bita mum kasa magana tayi mlm yace hjy yarinyarki bata da aljanu kaman yanda kike zargi sannan bana tunanin tana da tabin hankali lafiyanta qalau, kawai tsabar son mutumin nan ne yasa mata take haka which kuma abunda na fahimta kaman bata da kawaye wanda take fada musu matsalanta ku take fadama wa amma dad dinta yana fahimta har yake biye mata amma ke kina nuna mata kaman ta sami tabuwa, kuma ita a nata ganin kune ya kamata kusan wani hali take ciki tunda kune iyayenta, hjy ya kamata ki dinga janta a jiki kina bata shawar wari wanda zata fahimta koda tana firan dan ball din da takeso ki daina nuna mata kyara hakan yakan sa yaro ya tsani kanshi yaga kaman iyayenshi sun tsaneshi yana da kyau ka maida danka abokinka ta yanda zaku dinga bama juna shawara jan yaro a jiki yana sa komai zaiyi saiya fadama iyayenshi sannan nunama yaro kyara yana sa ya dinga boye abubuwa da yawa wanda in ba’ayi wasa ba nan gaba za’ayi dana sani wanda ba’a fata, jikin mum yayi sanyi tace ngd mlm tabbas hakane jawaheer bata da kawa ko daya na tabbata inda tana da kawa da tare zasu dinga shawara rashin kawar ne yasa take fada mana ni kuma sai inki fahimta in dinka mata kallon hauka, mlm kasan ba komai iyaye suke dauka ba amma yanzu da naji maganan ka na fahimci komai yaronka ya fada maka koda shirme ne ka nuna masa kulawa akai, nan suka ma mlm godiya tare da bashi kudi yaki amsa yace dan Allah yayi baya bukatan kudi saida mum tace babu kyau maida hannun kyauta sannan ya amsa suka wuce, a mota suka sami jawaheer tana ta kuka, mum cikin tausayin yar tata suka karasa motar bayan sun shiga mum tace jawaheer kiyi hakuri kibar wannan kukan batai shuru ba har suka sauke hjy hauwa suka wuce bayan sun shiga gida da sauri jawaheer ta shiga gida tana kuka a falo taga dad dinta nufanshi tayi tana sauke ajiyan zuciya, cikin damuwa yake tambayanta mai aka mata? Bata bashi amsa ba sai kukan da take tayi mum ce ta shigo falon ganin dad yace bilkisu mai aka mata haka? Kodai wannan magan ganun naki kike ta fada mata? Hjy bilkisu cikin damuwa tace kayi hakuri da abunda zan fada maka yanzu inaso kamin adalci sannan ka fahimce ni, wlh nayi hakan ne dan ina zargi amma daka baya saina fahimci kuskurena, munje wajan wani mlm ne a islamiya domin ina zargin aljanu jawaheer take dasu, dad yace what? mum tace kayi hakuri ka gama saurara na shuru yayi amma fuskanshi a tamke nan mum ta bashi labarin abunda ya faru, dad baice komai ba sai kama hannun jawaheer da yayi yace tashi kije kiyi wanka kizo kici abinci sannan ki fara shiri jibi zamu tashi zuwa spain bata san lokacin data tashi ba dan murna lokaci daya kuma tace dad r u serious? murmushi yayi tare da fadin yes jawaheer bana daukan abunki da wasa komai naki inaso inyi miki yanda kike so hugging dad dinta tayi tare da furta u r d best dad in d world tana fadin haka ta nufi dakinta.


Kallon mum dad yayi yace bilkisu na rasa mai yasa gaba daya kika canza bakya jin duk maganan dana fada miki, yanxu kinji dai abunda mlm din yace Allah yasa ki dauka kiyi amfani dashi, tace kayi hakuri insha Allah komai ya wuce sannan wannan abunda ya sami jawaheer na jarabawa zan kara dagewa wajan roqan Allah akan ya zaba mata mafi alkhairi a rayuwa, yace yauwa ko kefa, dan murmushi tayi tare da fadin kasan ita daya ce yarinya ta mace duk wannan abunda kaga inayi duk sonta yaja hakan tunda babu mai so yaga nashi ya shiga wani hali, dad yace hakane sai muyi ta addu’a sannan tare na mana visa harda ke zamu tafi jibi da khalil mum tace tafiyan family ne kenan gaba daya dariya dad yayi yace mun dade bamuyi irin tafiyan nan ba gaba dayan mu, tunda muka dawo daka saudiya bamu kara fita mu duka ba naso muje harda umar babban dansu kenan, amma yace shima zaiyi tafiya, mum tace Allah ya taimaka, ya amsa da ameen…… Toh jawaheer za’a spain koya zata kaya???


Jawaheer shiri take sosai domin tafiya spain ko abinci bata iya samu taci dan murna sai dad yayi dagaske take ci, kaman yanda dad yace jibi zasu tafi hakan ta faru domin dai rana bata karya inji masu iya magana, yau jirginsu ya daga zuwa kasar spain…..


Su jawaheer an sauka a kasar spain tunda suka sauka ta lumshe ido tana jin wani irin nishadi tare da farin ciki sai take ganin kaman gata ga M samir nan, wata katuwar mota ce taxo ta daukesu da kayansu wani gida suka nufa gidan sama, bayan sun karasa gidan suka shiga komai na gidan an rufe da farin kyalle saboda kura cirewa sukayi suka zauna a kujeran falon, hjy bilkisu ta kalli mijin nata tace wannan gidan fah nadai san baka da gida a kasar nan, murmushi yayi tare da fadin saboda jawaheer na siya, munyi waya da ambassador akan ina son gida a kasar nan shine ya hadani da wani kin san shi yana asibiti, toh wannan gidan ma mutumin yace nayi sa’a harta yan kasar sun kasa siyan gidan dan yayi kudi da yawa, mum tace ah lallai kam ai dole dan gidan ya hadu gskya duk da banga ko ina ba, jawaheer ta tashi tare da fadin bari inga gidan khalil shima binta yayi nan sukai ta zagaya gidan wanda yasha kayan more rayuwa ga gidan kato a kalla dakuna sun kai bakwai a gidan, mum tace ma dad naga su turawa basa irin gida haka babba, yin katon gida sai balarawa, dad yace suma yanzu turawan sun fara, jawaheer ce ta fito daka wani daki tana fadin dad ni wannan ne dakina na riga na zaba, dad yace ok dear duk inda ya miki nan zaki dauka, khalil yace dad ya kamata a bata daki a kasa ne, kafin dad yayi magana ta amshe da fadin sai kace namiji zan zauna a kasa dad shi zai zauna a kasa ya dinga gadi yaga masu shiga da fita, khalil yace ni din zan zama mai gadin nufota yayi da nufin ya kamota ta fara gudu shima yana binta dad da mum dai dariya sukayi mum tace kuna jin karfin jikinku ne sai yasa kuke ta wannan gudun, saida suka gaji dan kansu suka zauna suna maida numfashi, dad waya yayi aka kawo musu abinci tare da masu aiki biyu turawa duk ta hanyar mutumin da ambassador ya hadasu dashi, saida suka huta sannan alhaji jibrin mai dala ya shirya dan zuwa duba ambassador a asibiti, harda su mum da jawaheer jawaheer tayi shigan riga da wando sai tasa boyfriend jacket akai mai tsawo tare da yafa karamin gyale a kanta ta nada shi kaman hijab, duk da batai makeup ba tayi kyau sosai, cikin wata sabuwar jeep suka shiga nan driver yaja su suka nufi hspt din, kafin su shiga dakin da ambassador yake saida aka basu wani kaya suka daura akan nasu domin haka ka’idan asibitin yake, bayan sun shiga suka sami ambassador yana jin jiki duk da yana dauriya amma kana kallonshi kasan ciwo nacin shi, alhaji jibrin mai dala yace sannu ambassador ya jikin ya amsa da fadin da sauki alhmdlh, nan suma su jawaheer suka gaidashi ya amsa da fadin jikin alhamdlh, alh jibrin yace dama haka kake jin jiki? Ambassador yace ai jiki yayi sauki ma sosai akan da, cikin tausayi alh jibrin yake kara fadin Allah ya kara ma lfya, ambassador yace ameen, amma lfya kuwa PA dina yace kana ta kira cikin damuwa? Alh jibrin yace ah a ka barshi kawai inka warke mayi magana, ambassador yace haba haba ka fadi mana kai ka sani koh zan tashi, alh jibrin yace zaka tashi mana insha Allah, dama akan maganan dan kwallon kafa din nanne M samir wlh kaga yarinya ta ga tanan ya nuna jawaheer wacce tayi tsuru tana sauraransu, ita take son ganinshi, ta hanamu sukuni, ambassador yayi shuru yana ji har alhji jibrin ya gama sannan ya sauke ajiyan zuciya tare da fadin babban magana, alh jibrin yace kaman ya? Ambassador yace gsky ganin M samir yana da matukar wuya kaman a nigeria ne talaka yace yana son ganin shugaban kasa kaga hakan bamai yuhuwa bane a garesa, inaga kaman ma wannan zaifi sauki, domin M samir yana daya daka cikin matasa masu kudin duniya ganinshi zaiyi matukar wuya dama wani ne daka cikin yan kwallon dana hadasu, sai dai ta ganshi in za suyi wasa a cikin fili, jawaheer fita tayi da sauri tana kuka tare da fadin shikenan bazata sami ganin M samir ba shikenan burinta da mafarkinta zai zama karya kenan mota ta shiga ta zauna tana ta rusgan kuka driver din da aka hadasu yana ta kallonta ta mirror cikin tausayi, gashi babu daman ya tambayeta ko lfya,


Haka su dad suka shigo motar suka sameta tana ta rusgan kuka, nan dad ya fara aikin rarrashi amma kaman kara zugata yake dan haka ya barta in sunje gida ya rarrasheta dakyau, koda suka isa gida fita tayi tana kukan dukansu suna tausaya mata musamman dad, zata wuce daki khalil ya rikota yana fadin haba lil sis mai yasa zaki sa kanki cikin damuwa haka? Cikin kuka tace bakaji abunda ambassador yace ba tunda ambassador bazai iya hadani dashi ba bana tunanin zan iya ganinshi tako wani hanya, shikenan komai nawa ya tsaya, bazan sami cikan burina ba bros ina son M samir a kullum da burin ganinshi nake kwana nake tashi indai ganinshi zaiyi wuya har haka kenan mafarki na ya zama karya….. Kasa tayi tana kuka cikin tausayi dad ya matso kusa da ita yace jawaheer kiyi hakuri insha Allah na miki alkawarin ganinshi tako wace hanya, kai ta girgiza tare da fadin dad baka ji abunda ambassador yace ba  gwara in koma nigeria in nemi ganin shugaban qasa zaifi min sauki akan ince ina son ganin M samir, dad bana tunanin zanyi tsawon rai domin duka tunani na da jini na yana tafiya da M samir a kullum, zuciyata tana bugawa da tunaninshi dad in har ganinshi zai zama wahala a gareni miye amfanin rayuwa na? Ganin kowa yayi shuru yana kallonta yasa ta danyi murmushi wanda ake cewa yafi kuka ciwo tace dad nasan kuna min kallon rashin hankali ko wani abu makamancin haka, nasan koda kai bakamin mum tana min, amma abunda nake son ku fahimta shifa so ba karya bane wlh da ana cire abu a rai da tun tuni na cire shi na huta amma Allah ne yasa min sonshi wanda nasan shine kaddarata Allah yamin komai na rayuwa ban rasa komai ba komai nake so ina samu amma abu daya ya gagareni samu shine farin ciki na wato M samir, na yarda Allah baya bama bawa komai dole saiya jarabceka, wasu Allah kan basu dukiya da komai sai ya hanasu haiyuwa wasu kuma sai suzo a talaka abinci ma dakyar suke samu amma sai Allah ya azurtasu da haiyuwa lallai babu yanda Allah bayayi lumshe ido tayi wanda ya kada yayi ja, tace dad bana son zama a kasar nan inaso mubar nan da gaggawa nasan bazan iya cire M samir ba amma zan koma kasata inje inyi ta jinyar zuciyata har lokacin mutuwa na yayi…… Hmmm muje zuwa


Shuru tayi tana kuka.. Mum ta matso kusa da ita tare da rungumota tace kiyi hakuri jawaheer tun farko abunda nake so ki fahimta kenan amma yanzu alhmdlh tunda kin fahimta, ba komai bawa yake soba yake samu a rayuwa duk kudinka duk gatanka akwai abunda yafi karfinka, sannan Allah yakan jarabci bayinsa ta hanya da dama idan kayi hakuri sai ya zama hala silan shiga aljannanka, nasan abunda kikeji jawaheer amma inaso kiyi tawakkali kiyi kokarin cire M samir da tunaninshi a ranki duk da nasan ba abu mai sauki bane gareki, amma ki gwada kiba wani chance ya shigo rayuwanki zaki rage duk tunanin M samir,…… Murmushi tayi wanda ake cema yafi kuka ciwo tace mum bana tunanin zan iya hakan domin son M samir a jini na yake bana tunanin zan daina sonshi har sai ranan dana daina numfashi…. Mum tace jawaheer ki gwada bama wani dama zaki manta dashi …… Tace shikenan mum zan gwada tana fadin haka tayi dakinta ta kwanta tana kuka.


Dad ya kalli mum tare da fadin miye mafita? Mum tace mafita daya shine mu koma nigeria ka zaba mata wani ta aura zata cire duk son wannan mutumin da nasan bazai taba auranta ba, dad shuru yayi can ya nisa yace Allah kasa mu dace, duka suka amsa da ameen khalil shima dakinshi ya shige haka su mum.


Jawaheer tunda ta shiga daki take kuka har bacci ya dauketa,cikin baccin ne tayi mafarki…… Gata da M samir cikin wani garden wanda an saka kujeru da shape din heart kallonta yake tayi yana mata murmushi lokaci daya kuma ya tamke yace mai yasa kinzo kusa dani kike son ki kara yin nesa dani? Ko kin daina so nane? Tana kokarin yi mishi magana ya tashi cikin fushi yayi gaba tashi tayi tana binshi da sauri tana kokarin ta bashi hakuri amma yayi mata nisa, farkawa tayi duk tayi zufa sai faman sauke ajiyan zuciya take lokaci daya kuma tasa kuka tare da fadin bazan tafi ba bazan bar kasar nan ba har sai na ganka kaman yanda kake bukata cikin kuka take fadin Allah ka nuna min M samir da gaggawa Allah ka tausayamin badan halina ba, Allah kasan ina son wannan bawan naka tsakani da Allah, Allah ka tausayamin koda bazai aureni ba Allah ka nunamin shi a zahiri kuka ta kara saki mai karfi.


Kwanan su jawaheer biyar a spain bata fita ko ina, kullum tana gida tana kuka tare da roqan Allah ya nuna mata M samir in alkhairi ne a rayuwanta dad yace su shirya jibi zasu tafi dama sati daya za suyi, jawaheer tace dad babu inda zani, dad yace kaman ya? Tace dad sai naga M samir zan bar kasar nan, mum ji tayi kaman an daba mata wuka dan takaici cikin damuwa tace haba jawaheer kece fa kika ce mubar kasar nan sai yasa mukace sati daya kawai za muyi dan Allah kiyi hakuri kizo mu koma zamanki a nan baida wani fa’ida domin babu abunda zai kara miki inba takaici da bakin ciki ba, jawaheer ki taimaki rayuwanki tare da namu kibar wannan mutumin munfi kowa kaunarki ke bakya tunanin halinda muke shiga idan muka ganki cikin damuwa haba jawaheer ko so kike ki kashe mu da naki damuwan? Kuka jawaheer ta fara tare da fadin kiyi hakuri mum nima bada son raina nake haka ba, wlh mum zuciya tane take sani aikata duk wannan abun nasan kuna sona fiye da tunani na sai yasa kuke hakuri da duk wani abun dana kawo kuke dauka mum kodan farin cikin ku zanyi kokari in manta da komai amma dan Allah ku tafi ku barni a nan na wata daya nayi alkawarin in banga M samir ba wlh zan dawo sannan inaso inna dawo ku bani auren duk namijin da kuka zaba min, zan rungumi kaddarata nayi alkawari mum, wani guntun hawaye ne ya silalo a fuskan mum na tausayin yar tata inama tana da hanyar ganin M samir dayau saita sada yarta dashi kodan tayi farin ciki lokaci daya kuma ta rungumeta tana shafa mata baya tare da fadin kiyi hakuri jawaheer ni mahaifiyarki ce bana son ganin damuwanki duk kankantansa sai yasa wani lokacin nake miki abu wani iri amma badan bana kaunarki bane a’ah duk saboda kar kisa kanki cikin damuwa bana so ki zauna a kasar nan ke daya, jawaheer ke mace ce kuma kina da rauni bawai ban yarda dake bane a’a tarbiya ya zama abunda ya zama sai yasa naki yarda ki fita karatu waje nace ki zauna a abuja kiyi inkin gama ki dawo gida, dan Allah jawaheer kiji tausayina ki bimu jibi mu koma tare badan niba, cikin kuka tace mum baki taba tambayana abu na kasayi miki shiba a rayuwa ko inyi miki musu, amma wannan karan kiyi hakuri mun bazan biku ba M samir ya fadamin kar inyi nesa dashi in zauna….. Mum salati tayi cikin kuka tace a ina kika hadu dashi harya fada miki hakan? Tace cikin mafarki na mum yayi fushi dani saboda nace zan bar kasar nan, mum tace jawaheer anya lafiyanki qalau kuwa? Yanzu ke mafarkin ne kike yarda dashi? Murmushi jawaheer tayi tare da fadin mum nasan mafarki ba gaskiya bane amma akwai wanda yake zama gaskiya wannan mafarkin da nayi inaji a jikina gaskiya ne shima yana jin wani abu a tare dani, cikin takaici mum tace dan Allah tashi ki bani waje sannan wlh jibi dake zamu tafi kinji na rantse dakinta ta nufa tana kuka.


Wata baturiya ce ta fito daka cikin jirgi kallo daya zaka mata ka gane tana da kyau sosai bata da tsawo sosai tasa riga da wando fuskanta tasa glass kanta tasa brown attachment jan dan karamin akwatinta take har wajan da taga wani ya rike abu mai sunanta SONIA alaman ita yazo dauka cikin harshen turanci tace mishi hi am sonia yace mata ok nan suka nufi inda aka faka mota ya bude mata ta shiga direct asibiti suka nufa, wani daki ya nuna mata ta shiga tana budewa taga M samir a ciki yana zaune shi daya yana duba wayanshi da sauri ta nufeshi tayi hugging dinshi tare da fadin nayi missing dinka ya jikinka, lolaci daya kuma tasa kuka dagota yayi yaja mata hanci tare da fadin bana son kukanki naji sauki dana ganki saina kara samun lfya so stop crying kin san bana san ganinki cikin damuwa dan murmushi tayi tare dasa bakinta cikin nashi tayi kissing dinshi na wajan minti daya sannan ta sakeshi tace i really miss u murmushi yayi tare da fadin i miss u too inga tunda kin zo zan koma gida saiki dinga kula dani kai ta girgiza tare da fadin babu inda zaka sai abunda dr yace cikin dariya yace i luv you so much baby u r my happiness, manneshi tayi a jikinshi dad dinshi ne ya shigo dakin kallo daya ya musu yaji tsanar yarinyar …….


Sonia tana ganin dad din M samir ta ganeshi dan ta sanshi a hoto, mika mai hannu tayi shima bata yayi sannan tace hi am sonia from england  am samir girl i know dat he told u about me but iz good to introduce by my self, dad din tsayawa yayi yana kallonta duk da bawai ya dauki hakan da wani abu bane dan turawa ne su sun saba ganin fiye da haka amma shi mahaifin m samir musulmi ne kuma yana kishin addininsa sai yasa baya sha’awan ya auri wacce ba musulma ba, abun takaici ma ita wannan gata ba musulma ba kuma yar kasar england dad din fita yayi tare da fadin ni na tafi sai zuwa anjima, dad bai dade da fita ba dr ya shigo ya duba shi m samir yace yana son tafiya gida dr yace ya bari gobe sai ya tafi gidan dan yau za’a cire mai abunda aka samai a kafa, kai ya daga alaman ok, bayan fitan dr sonia ta kalli m samir tace mai yake damun dad dinka ko bashi da lafiya ne? Yace maita gani? Dan murmushi tayi tare da fadin naga ina mishi magana ya daure fuska kaman baya so na? M samir dariya yayi yace ba haka bane dad yana da sauki a hankali zaki fahimci haka, kallonshi tayi tace badai a gidanku zamu zauna ba koh? Yace mata a nan zamu zauna kina da matsala da haka ne? Tace eh bazan iya zama gida daya da dad dinka ba, dan shuru yayi yana nazarin magananta tare da tunanin abunyi…. Katseshi tayi da fadin in kuma baka da wajan sani zan tafi hotel, murmushi yayi tare da fadin no ba zaki hotel ba kece fa matar da zan aura komai kike so dole inyi miki akwai gidana sai muje can ki dinga kula dani har in gama warkewa, kai ta daga mishi alaman gamsuwa sannan suka canza firan da maganan yanda zasu tsara auransu in sun tashi yi.


Jawaheer gaba daya duniya ta mata zafi, maganan mum take ta tunawa da tace dole tare zasu koma, gashi dad dinta yana ji baice komai ba, dan tsaki tayi lokaci daya kuma ta tashi tayi toilet wanka tayi ta shirya cikin wata doguwar riga english wear tare da yafa karamin gyalen kayan, duk da batai makeup ba tayi kyau sosai idonta yayi zuru2 alaman tana cikin damuwa, falo ta fito taga mum a zaune ita da khalil, tace mum zan fita in dawo, mum cikin jin dadi tace ko kefa jawaheer ai gwara ki saki ranki dan murmushi tayi khalil yace muje tare nima inga gari ita da khalil suka fita a kafa har sukaje wani katon super market gaba daya rigunan da m samir yake sawa ta dinga jida da duk wani abu da akwai pic dinshi a jiki, tare da daukan ball har guda biyar khalil tausayi yaji tana bashi domin yana gani wannan abun na jawaheer ya wuce yanda yake tunani in tayi wani abu kaman ba ita ba, har ta gama khalil bai dauki komai ba yana kallonta cikin damuwa, kallonshi tayi tace yadai babu abunda zaka siya kai? Ajiyan zuciya yayi tare da fadin babu abunda zan siya muje mu biya kudin mu wuce, bayan sun biya kudin wasu daka cikin ma’aikatan suka tayasu fitar da kayan khalil ya tsayar da taxi akasa kayan suka wuce gida, koda suka isa gida mum da dad suna falo, jawaheer ajiye kayan hannunta tayi sannan ta nufi inda dad yake ta zauna tana fadin dad plz kazo muyi magana dan Allah dad ka tashi muje, dad dariya yayi tare da fadin ok muje, tashi yayi suka fita mum ta girgiza kai tare da fadin Allah ya baki lfya.


Jawaheer kallon dad tayi tace dad dan Allah ka tausayamin karka bari mum tace zata tafi dani, kasan ban samu abunda nazo garin nan danshi ba,plz dad ka tausayamin ka bari inga m samir ,dad yace jawaheer kiyi hakuri ganinshi ba abu bane mai sauki amma kizo mu koma insha Allah nayi miki alkawarin sadaki dashi amma sai kinyi hakuri kin bani lokaci kadan, kai ta girgiza tana hawaye tace dad ka tausayamin badan niba dad idan na koma gida wlh tunani zai kasheni tunani zaisa in mutu zuciya ta zata buga dad wata daya kawai nake bukata wlh dad in ban ganshi ba nayi alkawarin zan dawo sannan bazan kara yi muku maganan shiba duk da nasan ba abu bane mai sauki amma zanyi shuru har sonshi ya kashe ni, dad jikinshi yayi sanyi yasa hannu yana share mata hawaye yace kiyi hakuri jawaheer kinji mum dinki ta rantse amma zan mata magana kinji? Kai ta daga alaman eh.


Washe gari jawaheer ta shirya cikin riga da wando tasa wani karamin gyale ta rufe kanta sannan tasa boyfried jacket akan kayan yau babu laifi ta shafa powder tayi kyau sosai saita fito kaman balarabiya wata karamar jaka ta dauka ta rataya, falo ta fito babu kowa hakan ya mata dadi sosai dan bata son tambaya, taxi tahau ta fadamai inda zata hospital din da ambassador yake aka kaita sauka tayi ta biya kudin taxi din ta shiga asibitin a dai2 lokacin taga an bude wata kofa an turo wani akan keke ido ta ware tare da fadin M sa……. m samir…………..


*ina godiya ga masoya novel din jawaheer sannan masu kira na ko yimin message idan suka jini shuru ina godiya sosai da sosai a kullum maryam obam tana alfahari daku masoya na kudai kawai kuci gaba da suburbodo comment da shrhi*


Dago kai yayi suka hada ido shida ita ganin irin kallon da take mai wanda ya saba ganin irinshi amma sai dai nata ya banbanta da sauran domin duk wanda ya ganshi sauri yake ya bashi paper dan ya mishi signing amma ita wannan tsayawa tayi ta bude ido tana kallonshi abun ya dan bashi mamaki dan haka ya sakar mata murmushi ko zata dawo cikin hayyacinta inma tana tunanin bashi ta gani ba amma ko gezau batayi ba daka kallon nashi da takeyi kai ya girgiza dai2 lokacin da aka turashi suka wuce gabanta jawaheer yanda kuka san gunki haka ta tsaya ido bude bigeta din da akayi ne yasa ta dawo hayyacinta ta fara dube2 amma bata ganshi ba jin ihun da ake tayi yasa ta fita da gudu wanda yayi dai2 da lokacin da aka taimaka mishi ya shiga mota  wani irin kuka ta saki da taga anja motar daya shiga sun bar wajan, da yake turai ne babu ruwan kowa da kowa haka tayi kukanta dan kanta ta gaji ta tashi ta fita daka asibitin ta fasa zuwa wajan ambassador da tayi niya.


Gida ta koma da kuka a nan taga dad shida khalil ganin ta shigo tana kuka dad ya tashi ya rikota yana tambayan lfya jawaheer daka ina haka mai aka miki maiya faru dake duk lokaci daya ya jero mata tambayoyin data kasa amsa mishi sai kuka,mum ta fito da sauri tana fadin maiya faru kuma? Cikin kuka tace dad wlh yau naga M samir da idona, mum tsaki tayi tare da fadin abun naki har yakai haka koh? Cikin kuka tace mum daka Allah babu kowa koh?….. Toh wlh naga m samir da idona, dad yace a ina? Tace dad naje asibiti domin inga ambassador saboda in kara roqanshi ko akwai wata hanya ban kai da zuwa dakin ambassador ba saigashi an turo m samir akan keke daka wani daki an fitar dashi, khalil yace baki mishi magana ba? Tace wlh na kasa gaba daya lokacin dana ganshi komai nawa ya tsaya har murmushi yayi min, wani hawaye mai zafi ya kara fito mata tace koda yau nabar kasar nan zanyi farin ciki domin naga abunda nake burin gani nake mafarkin gani kuma sai dai kash burina bai cika ba tunda ban mai magana ba, kamo hannun mum dinta tayi tana kuka lokaci daya kuma ta tsugunna a kasa kaman mai neman gafara tace mum baki yarda dani ba koh? Mum tayi murmushin karfin hali tace na yarda dake jawaheer murmushi jawaheer tayi sannan tace mum ki tausayawa rayuwar yarki nasan kunfi kowa sona mum wlh da kinji abunda nakeji da kin amince da duk wani abu dana roqa daka gareki wlh mum duk wannan abun da nakeyi saboda so nakeyi wanda bani nasa ma kaina ba Allah ne yasa min mum yau koda M samir bai aureni ba inaso inyi magana dashi koda sau daya ne a rayuwa na mum dan Allah ki barni inyi wata daya a kasar nan kafin in dawo na miki alkawarin indai nayi wata daya ba tare dana ganshi ba wlh zan dawo sannan na baku zabi ku aura min duk wanda yayi muku, mum dan Allah ki tausayamin, mum ajiyan zuciya tayi tare da dago jawaheer daka tsugunon da tayi, tace shikenan na yarda zanyi kaffara na rantsuwan da nayi zan barki kiyi wata daya amma kema ki sani ki riqe alkawarin da kika dauka in bakiga M samir ba duk wanda muka baki zaki yarda ki aureshi? Kai ta daga tare da fadin nayi alkawari mum ko waye zan aura mum tace shikenan sannan inaso ko mai za kiyi kiji tsoran Allah ki riqe mutuncinki a matsayinki na diya mace wacce rayuwanta kalillan ne, tace insha Allah mum bazan baku kunya ba, ranan jawaheer ta saki jiki na farko yau taga M samir gashi kuma mum ta yarda zata barta haka sukai ta fira dan gobe su mum za su wuce nigeria.


M samir yana kallon lokacin da jawaheer tayi kasa tana kuka abun ya bashi mamaki na farko irin kallon da take mishi da kuma sanda ta fito da sauri taga sun wuce tayi kasa tana kuka abun ya daure mai kai har yaji yana son sanin dalilin kukan nata duk yanda akayi yasan ba yar kasar su bace dan bata mishi kama da yar kasar suba dan tafi mishi kama da balarabiya gaba daya da tunanin jawaheer suka karasa gidanshi da zai zauna shida sonia, bayan sun shiga ciki sonia tace bari taje ta mishi wanka yace nope zaiyi da kanshi dan yasan dad dinshi zai iya zuwa at anytime in kuma yaga hakan ranshi zai baci shi kuma baya son batama mahaifinshi rai, babu yanda sonia batayi ba amma yaki yarda tashi yayi yana jan kafa ya shiga toilet yana iya tafiya amma yana dan dingishi an sashi a keken tura marasa kafane saboda shi celebrity ne inya fito da kafanshi duk yawan security dinshi mutane za suyi ta ihu gashi kuma asibiti ne sai yasa aka sashi a kai kuma duk da hakan mutane sun ganshi din koda ya shiga toilet tunanin jawaheer ne ya dawo mishi mai yasa take kuka koma dai miye daka gani tana cikin damuwa sannan daka ganin alamunta tana son magana dashi, a hankali ya furta i have to find her.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *