Jikinta a sanyaye ta shiga cikin unguwar tana tafe tana hardewa xuciyarta Na bugawa a hnkl har ta karaso gidan wayam taga kofar gidan ta kwankwasa garba me gadi ya bude mata ta shige tana kallon bangaren su yaya khaleel ajiyar xuciyata tayi yau Na tsalleke cin mutuncin yaya haisam kai tsaye dakinta ta nufa ta baje a gadonta tana maida numfashi tunani masu yawa sukai mata cunkus da sauri ta mike ta kunna glof din dakin haske ya kauraye ko ina ta je jikin mudubi ta kurawa kanta ido meyasa bata kama da danginta ? Ta saki ribbon din da ta daure gashinta ya sauka gadan bayanta ta karewa kanta kallo fara ce tasss doguwa bata da jiki tana heart face da dara dara idanu hade da dankaramin baki ta sunkuyar da kanta tabbas kalarta kalan Fulani koma larabawa ne tana da matukar Kyau Sam batayi kama da sauran yan uwanta su David ko mamanta da papanta ba tayi kama dasu koda kuwa ta kafafuwa ko hannaye da yatsu ikon Allah ! Ta girgixa kanta tabbas ikon shine ta danyi tsaki bata son irin wannan tunanin dan yana jefa xuciyar ta cikin rudu da tashin hnkl jikinta asanyaye ta mike ta fice daga dakin tai bangaren hajja kakarsu yaya khaleel kai tsaye ta shige falon ta sameta xaune tana karanta jaridar leadership tayi sallama duk da ba dai dai tayi ta ba hajja ta amsa mata cikin sakin fuska Jennifer naam hajja kin dawo daga wajan Maman taki ko ?? Kanta a sunkuye ta amsa da eh Na dawo hajja tana nan lfy ? Lafiyan ta lau mashaa Allah suka kurawa t.v kallo sbd lbrin da ya ja hankalinsu Na shaye shayen kayan maye da matasa sukeyi hajja taja tsaki Allah ka shirya mana xuri’a amin Jennifer ta fada hade da mikewa kina da wata matsala ne Jennifer ?? A a hajja Na xo Na dubaki ne in da akwai aiki a a babu aiki to zan wuce OK Jennifer gwara kije ki huta ai kina kokari ma sannu ta wuce hajja tabi bayanta da kallo cikin tausayawa yarinyar tana matukar bata tausayi girgixa kai tayi Allah ya shiryeki in dai xaki shiryu
Tana fitowa daga dakin kai tsaye bangaren Rubayya ta shiga ta tana kwance akan gado tana kallon Indian series ( qubul hai ) Rubayya ta dago kai cikin fara’a Jennifer ya akayi ?? Na dawo daga skul ban sameki ba Momy tace min kinje gaishe da Maman David eh cen naje ban dade da dawowa ba ayya ! Kayane gasu nan nayi kwalema nasan xasuyi miki tunda kusan size dinmu daya da murna ta kalli akwatunan data nuna mata wow ! Nagode Anty ruby taxaro ido Anty kuma Jennifer ?? Haba dai dan Allah karki kuma Sa’anni muke fa ngd sosai ruby bako mai kin cancanci fiye da hakan ma ta tashi ta kinkimi akwatin xuciyarta cike da jin dadin kayan ta fice tana mata gdy kai tsaye dakinta ta nufa Taiwa kayan daidaya atamfofine tsala tsala da shaddoji da lesa lesai manya dukkansu kusan sabbine dan babu alamar hudu ko uku ta dafe kai tana murmushi mutanen gidan nan suna da karamci da girmama dan adam duk da bata dade ba dan bata wuce wata 1 da satittika tana musu aiki ba mutun dayane yake masifar gallaxa mata haisam tayi ajiyar xuciya ya tsaneta sbd banbancin addini ta kwanta bacci me karfi ya sureta cike da mafarkai marasa kan gado