JENNIFA CHAPTER 7

JENNIFA CHAPTER 7

 
 
 

Ta gama wankin da sauri ta shanya ta koma daki xuciyarta tunkushe tana kuma mmkin bakin hali irin na haisam tana nan xaune aka kira sallar magrub da sauri ta tashi daga kwanciyar da tayi tana sauraron kiran sallar xuciyarta na kwadai ta mata abubuwa da dama karar wayarta taji jikinta asanyaye ta duba Maman David xuciyarta tayi sanyi kadan ta daga oyoyo mamana oyoyo Jennifer mama ta amsa kina lfy dai ko ? Lfy nake mama ya papana da su David suna nan kalau suntafi skul nayi missing dinku mama ta fada ashagwabe sorry Jennifer muma duk mun damu darashin ki kusa damu ranar Sunday kixo nan gida mutafi Church tare da brothers dinki damm ! Gaban Jennifer ya fadi rabon ta da xuwa Church har ta manta to mama zanxo yawwa kina dai aikin ki akan kari ko ? Eh tafada jikinta duk yai sanyi baki da wata damuwa ko ? Babu mama haka ake so sai xuwa anjima zan xubawa customers abinci ltr yata tayi mata addua takashe wayan wulli Jennifer tayi da wayan ta dafe kanta Sam ! Xuciyarta bata son xuwa Church kishingida tayi tana tuna abubuwa masu yawa da suke damunta takasa fadawa kowa kuma tana tsoron yankewa kanta hukunci asalima tarasa da inda xata fara warware matsalarta amincewarta aiki a gidan nan yana daya daga cikin warwarewar tunkushashshiyar matsalar ta takuma rasa ta ina xata fara mikewa tayi jikinta asanyaye ta fito daga dakinta tayi hanyar kitchen dan yau baxata ci abinci da mutanen gidan nan ba kicibus sukayi da zahra ta zabgawa Jennifer wani kallo na raini cikin isa da izza ta bude baki da kyar kamar bata son maganar kije ki gyaramin daki ta wuce tana rufe hanci Jennifer ta bita da kallo ta dawo baya tai hanyar dakin zahra ta bude kamshi me dadin shaka ya bigi hancinta wannan shine karon farko da ta taba shigowa dakin nata ko ina tsab haka dai ta karkade ta share da wanke toilet ta fesa air freshener ta sauko down stairs a falo ta gansu ita da ya haisam gabanta ya fadi taxo xata wuce atsorace hade da faduwar gaba kee! Taji muryar ya haisam jikinta na rawa ta xo maza da Allah ya fada cikin tsawa ubanwa ya baki ixinin cin abinci damu tayi shiru kanta akasa mgn nake miki ! Da sauri tace ya haisam zahra da take kallo tace na fuskanci ya mahboob yana da feelings akan yarinyar nan tsaki haisam yaja cikin jin haushi shi ya Sani amma baxa a kara cin abinci da itaba inyaso yabita dakinta suci tare hmm zahra tayi mmkin dayake bani da baya iyajin warinta ta fada tana done hanci wari ?? Jennifer ta maimaita aranta zahran ta waiwayo ta kalli jennifer tun xuwanta gun sai yanxu ta kalleta hnklinta na kan tv da take kallo shishshigin naki yanaso yayi yawa kitsaya iya matsayinki tashi ki bawa mutane guri kazama kawai ya haisam yafada yana jefa mata mugun kallo na kiyayya da tsana da sauri ta mike tayi bangarenta ranta bace abincin daba taciba kenan ta kwana da yunwa da bacin rai 

6:00am ta tashi ta gama komai da wuri dan batasan su dinka haduwa da mahboob taga ma tayi wanka ta bar daki ta yi can bayan gida inda babu Wanda xaiyi tunanin xuwanta wajan ta jinkina hade da sakanta jikin ginin wajan tasan tabbas mahboob ya ganta damunta xaiyi da tmbyoyi koma yace taxo suyi break fast itakam yanxu kome xai mata baxata kara xuwa wajan cin abincinsu koda kuwa xata yini da yunwa tana nan zauna har gyangyadi ya kamata abinka ga Wanda baisamu ishashshan bacci ba hk tayi baccin axauna 

9:32am ta farka a gigice sbd rana ta daki fuskarta da sauri ta mike tayi dakinta tasa mukulli ta rufe tayi kwanciyarta tasan basu gama break fast dinba tayi baccinta me isarta dan safiya ne kadai time din hutunta duk inda 12:00pm ba ita ba sauran Hutu 

Bugun kofar dataji ne yasa ta mike zumbur akuma tsorace ta bude kofar karaf suka hada ido yana murmushi sannu sarkin baccin safe ta daure fuska dan tana son yakiceshi ya shigo dakin daxu ina kika shiga naita nemanki da safe ? Tayi shiru kanta akasa sbd ya tsareta da idanuwa nayi wani aikine OK ya fada zanje unguwa sai yamma xan dawo me kikeso na taho miki dashi ?? Tayi shiru taji dadi sosai ta girgixa kai bana son komai ya bata rai baxaiyiyu ba zanyi fushi muddin kika ki fadamin shirun ta kumayi sbd batason me xatace tana so ba ya juya ya fice ranshi abace tabi bayanshi da kallo tana jin haushin kanta tayi rashin hnkl bai kamata tayiwa Wanda ya damu da ita haka ta shi taje dining ta kwashe kayan da sukaci abinci ta gyara wajan ta Dora na rana telephone tayi ring Momy ta gani ta amsa jennifer in kin gama kixo toh Momy ta amsa aladabce 

Sauri tayi ta gama tana adduar Allah yasa ba laifi tayi ba a falo ta taddasu ita dasu Rubayya da zahra suna hira suna kuma kallo kin gama jennifer ? Momy ta tmbyeta tana kallonta eh Momy na gama OK yayi Kyau sannu da aiki Allah yasaka amin Jennifer tafada tana jin dadin adduar Momy xakuje kasuwa ne keda Rubayya yau dadyn su xai dawo xuwa yamma tayi murmushi Allah ya dawo dashi lfy amin Jennifer kije ki shirya to tamike da sauri tayi dakinta a gaggauce ta shirya doguwar riga tasa baka arabiyan gown wacce rubayya ta bata tayi rolling din kanta da gyalen rigar ta fito tsaye ta tadda rubayyan kusa da motarta tana waya gefe taja ta tsaya tana kallon bayanta Jennifer ta lumshe ido Rubayya tana matukar birgeta sbd tana bata darajta dan adam duk kaskancin Sa ta waiwayo tana kallon jennifer fuskarta dauke da murmushi muje ko jennifer ta bude mota tashiga suka fice 

3:27pm dai dai suka dawo daga kasuwa gaba dayansu suka fada kitchen sbd 7 dady xai dawo girki sosai akayi kala kala basu gama ba sai wajan 5:00pm da wani abun alokacin hjy uwani me kawowa Momy yan aiki ta kawo yanmata su biyu wayanda xasu yi aiki tare da jennifer dukkansu hausawa ne daki jennifer ta shige tana adduar Allah yasa kada su dinka nuna mata wariyar launin fata wanka ta shiga toilet tayi ta fito tana shafa mai bayan tagama ta xo kitchen ta Debi abincinta ta koma daki ta ci ta xo mayar da plate din kitchen Momy ta kirata falo cikin fara a Jennifer ga mataimaka kin samu jennifer ta kallesu sannunku da xuwa suka bude hkr suna dariya yawwa sannun ina yini ? Suka gaishe ta ta amsa da lfy lau xuwa gobe Jennifer sai ki nuna musu kan aikin yau gidan namune duk muna busy inyaso na raba muku aikin da kowacce xatayi toh Momy ki kaisu dakin kusa dake nan xasu xauna ta mikawa jennifer mukullin dakin ta amsa sannan tace su taso su biyota da jakar kayansu ta kaisu dakin nasu ta nuna musu yadda xasuyi amfani da komai na dakin sannan ta koma kitchen ta gyarashi tsab takwaso girke girken ta Jere a dining ta gyara gidan tasss ko ina ya dau sheki ta kunna turaren wuta ta koma dakinta 

7:35pm taji motoci na shigowa gabanta ya fadi dady ya dawo itakam bata sanshi ba sai photon shi kawai take gani taji hayaniya na tashi daga babban falo tasan farin ciki sukeyi da murnar dawowar dadyn nasu oh inama itama rayuwarta irin tasu ce? Da sauri ta kauda tunanin da yake tunxurota 

Wajan goma taji tsit jikinta asanyaye ta shigo falon ba kowa yayi kaca kaca ta kwashe kayan wajan ta kai kitchen ta share ko ina nan da nan wajan yai Kyau ta koma kitchen ta gyarashi ring taji na telephone da mmk ta daga muryar ya khaleel taji kixo ki gyaramin daki taxaro ido cikin Daren nan ina tuni ya kashe waya takalli agogan kitchen din 11 saura 11/12

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *