JIDDATULKHAIR CHAPTER 57 BY KHALISAT HAIDAR

Parking Abuturrab yyi a kofar gidan Ramlah, Ramlah ta bude motar xata sauka, Jiddah ma ta bude xata sauka, Hijab dinta taji ya rike gam daga kasa, ta kallesa da mamaki amma ta ma rasa abinda xata ce, Ramlah ta kulle motar bayan ta sauka tana jiran ganin ko saukowa Jiddah xata yi, Jiddah ta marairaice tana rike da handle din kofar motar murya can kasa tace “Meye haka wai, ka sakeni in sauka mana” Abuturrab ya hada ido da kanwarsa dake tsaye still waiting for Jiddah to come down, a hankali ya sake Hijab din Jiddah ta bude motar ta sauka da sauri, Ramlah ta masa murmushi tace “Sai da safe yaya” Nodding kawai yayi, tuni Jiddah har ta shige cikin gidan, Ramlah ta bi bayanta… Karfe sha daya da wani abu Ramlah na kwance kusa da Ahmad dake operating laptop dinsa, tace “Doctor” ya kalleta yace “Yess dear” Tace “Ina son in maka tambaya ne dama” Ya bar danna laptop din da yake yace “Ina jin ki” Tace “Nasan yaya baya boye maka komai da ya shafi rayuwarsa da dai sauransu…” Murmushi Ahmad yayi yana kallonta, tace “Ka gaya min gaskiya ko da akwai wani alaka tsakanin sa da Jiddah” Yace “Me yasa kika min wannan tambayar?” Ta d’an yi shiru sai kuma tace “Naga wasu abubuwa ne da suka yi confusing dina” Yace “Kamar me?” Ta gyara kwanciya tace “Daxu a can gida muna xaune tare da Jiddah ya shigo yace in je in debo masa abinci, bayan na dawo da abincin sai ban gansu a parlor ba, i dropped the food sai ga Jiddah ta fito daga bedroom din Ummi, she didn’t say a word ta fita, i was so surprise bayan few minutes na karasa dakin na gansa shi ma a ciki, sai kuma still daxu ya ajiye mu a gida, xata sauka mota naga ya rike hijab dinta but duk basu san na gani ba” Kallonta kawai Ahmad yake babu ko kiftawa yana sake assimilating din abinda tace, can yace “Sai aka yi yaya?” Tace “I don’t know what she told him kuma daga baya naga ya saketa ta sauka motar” Ahmad dae yyi shiru, Ramlah tace “Tun daxu abun ya tsaya min, cause I am confused” Ahmad ya jawo laptop dinsa ya ci gaba da abinda yake, Ramlah tace “Ko akwai wani abu da ake boye mana ne Doctor?” Ahmad yace “I am confused just as u now Ramlah” Ramlah bata kuma cewa komai ba, Bayan few minutes ta mike ta fita dakin, dakin da Jiddah take ta nufa ta bude a hankali tana kallon cikin dakin, kwance ta ganta idonta a lumshe ta lullube da hijab dinta maimakon blanket da ke ajiye gefe, ta fi minti biyu a tsaye har xata juya Jiddah ta bude ido, mikewa xaune Jiddah tayi tace “Kina son wani abu ne?” Ramlah ta sakar mata murmushi tace “Nothing naga baki kashe wuta bane” daga haka ta kashe fitilar dakin ta juya ta fita ta kulle kofar, Jiddah ta lullube har kanta da Hijab din jikinta ta lumshe ido… Karfe daya da rabi na dare Abuturrab na kwance Aneesah na gefensa kamar xata shige jikinsa tana bacci, lumshe ido yyi ya bude, ya mike xaune a hankali being very careful not to wake Aneesah ya sauka kan gadon ya nufi kofa ya fita parlor ya xauna saman kujera ya rike kansa, ya fi minti talatin a nan sai kuma ya mike ya tafi bandaki ya dauro alwala ya fito… Washegari da ciwon kai sosai Abuturrab ya tashi, hakan bai hanasa ya shirya ya fita gida karfe goma ba ya tafi can gidansu, sai da ya jira na kusan minti talatin sannan suka dau hanyar Hayin rigasa da Abbansa, Alhaji Umar, da wani aminin Abban nasa, shi yake driving so absentminded, har suka iso hayi yayi parking dai dai layin Mai anguwa, kasa ce masu komai yayi, shi dai Abba kallonsa kawai yake ganin yayi parking babu wata magana, ya saci kallon Abban nasa, suna hada ido ya bude motar yace “Abba xa mu karasa ciki da kafa babu nisa” Daga haka ya sauka sauran ma duk suka sauka, Xaunawa Abuturrab yyi saman tabarman dake kofar gidan Mai anguwa suka gaisa da mutane biyu dake nan, Abuturrab ya d’an shafa kansa yace “Gun Mai anguwa muka xo” wani matashi yace “Ayya ai bashi da lafiya yau kwanansa uku a shika” Kallonsa Abuturrab ya dinga yi babu ko kiftawa, sai kuma yace “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un… Allah ubangiji ya tashi kafadunsa” Suka amsa da Ameen, mikewa yayi yana kallonsu Abba dake tsaye suna jin duk abinda Abuturrab yyi da matasan, Abba da Alhaji Umar da abokinsa suka ma Mai anguwan fatan samun lafiya sannan suka koma gun mota, Abba yace “Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi, idan ya samu laifi sai a dawo ayi magana” Shi dai Abuturrab bai ce komai ba ya tada mota tunani iri iri a ransa, gida ya maida su Abba sannan ya karasa bangaren Ummi ya gaisheta, Ko minti uku bai yi a parlon Ummi ba aka bude kofar, Aunty ta shigo tana kallonsa tace “Wato da ni kake gaba a gidan nan ko Aliyu, sai dai ka shigo ka yo bangaren uwarka idan ka gama abinda ya kawoka ka fice kayi tafiyarka, to kayi ta banxa in dai nice wllh, dama uban me kake tsinana ni da shi banda ma ni da nayi tsaye kan lamarinka tun baka kai haka ba, in dan ta ita uwar taka ce ka xata xaka kai matsayin da kake yau?? To wllh kayi da ni Aliyu, kuma ni nasan tsinanniyar da ta shiga tsakanina da kai, nasan musabbabin duk wannan abinda kake min, xa kuma tasan ni er halaq ce….” Tana gama fadin haka ta fita tana huci, Shi dai danna wayarsa kawai yake, Ummi dake dakinta duk tana jiyo Aunty ta ta6e baki ta gama abinda take ta fito, gaisheta yayi bayan ta xauna, ta amsa tace “Akwai wani abun da tayi maka ne wanda ban sani ba take maka gori yanxu?” Yana danna wayarsa yace “Ko daya Ummi, ni babu wani abu da ta ta6a min” Ummi tace “Ohk, to me ya hadaka da ita yanxu baka shiga ka gaisheta?” Yace “Ra’ayi” Tace “Kamar yanda for years kayi ra’ayin dena shigowa gaisheni sai ka ga dama” D’an murmushi yayi yace “Aa Ummi” Tace “Toh Allah ya kyauta” Shi dai bai ce komai ba, tace “Har yanxu kuna samun matsala da Aneesar ne?” Ya kalli Ummi yace “Me kika gani Ummi?” Ummi tace “Sai naga abu xan tambayeka?” Ya girgixa kai yace “Aa Ummi, tana gyarawa yanxu” Ummi tace “Toh gaya min meye damuwarka Aliyu” Ya daga kai yana kallon Umminsa, Ummi tace “Tell me” Yyi kasa da idonsa, sai kuma ya mike ya koma gefenta ya xauna yyi kasa da murya yace “Ummi addu’a kawai nake son ki taya ni da shi” Tace “Baxan yi ba sai ka gaya min me ke faruwa” Yyi shiru ya rasa abinda xai ce, bayan few seconds cikin sanyin murya yace “Ummi , I don’t know how everyone is going to take this, but…” sai kuma yayi shiru yana jin xuciyarsa na bugawa, Ummi tace “Bother not… Go ahead tell me what’s happening, i might take it softly” ya marairaice mata yace “Might kuma Ummi, you just have to take it softly” tana kallonsa tace “Ina sauraronka” Ya d’an kalli kofa, Ummi na ganin haka ta mike tace “Mu je daki to” Mikewa yayi ya bi bayanta xuwa dakin. Driving Abuturrab yake a hankali har ya isa gida, bayan yayi parking ya sauka motar, baka ta6a fadin wani kalan expression ne a fuskarsa a lkcn, yana shiga parlor Aneesah ta leko daga kitchen tace “Welcome back my Captain” Yace “Thank you” tace “Na gama hada maka kayan, kaje ka duba ko sun yi” yace “Sai nayi sallah” Bandaki dake parlon ya shiga ya dauro alwala ya tafi masallaci don lokaci yayi, Aneesah ta karasa ta dau wayarta dake ringing bayan ya fita, ganin Aunty ke kiranta ta daga ta kai kunne, daga daya bangaren Aunty tace “Kar ki kuskura yayi tafiyar nan baki amshi abin nan ba Aneesah” Aneesah na ci gaba da taunar cingam din bakinta tace “Sai kace ina hauka Aunty, na fa gaya maki yanxu lafiya muke xaune babu komai wllh, duk abinda nace yana yi, girki kuwa kan ya dawo weekend chef salmah ta xo ta min varieties in xuba a deep freezer, sai dai in ciro inyi warming, kuma wllh yana ci yanxu, gida kuma kafin ya dawo nake sa almajirai su shigo har sama da dakinsa su share tsaff, in basu batattun kwanuka ta can bayan gidan su wanke, iyaka in kunna burner in cika turaren wuta… ” Aunty tace “Toh kun kara hada shimfida kuwa?” Aneesah tayi wani dariya tace “Na fa ce maki Aunty Safara’u ma ta yo min sako me yawa last week bayan wanda kika kawo min, lafiya lau komai ke tafiya yanxu” Aunty tace “Toh madallah haka nake son ji, ni kuwa kinsan har yau ko xuwa gaisheni a bangarena baya yi, to amma ni nasan tun bayan da ya rabu da tsinanniyar yarinyar nan da naji ana ce ma Jiddah hakan ya faru, duk gaba daya ya canxa min ke kyace ni makiyarsa ce” Aneesah tace “Ikon Allah, to ita Jiddar haka xaki xuba mata ido Aunty??” Aunty tace “Ahaf ashe wasa da ni kike… Anjima dai ina nan shigowa in amshi kudin nan na ranan…” Aneesah tace “Aa Aunty ki bari ko jibi don nasan kafin ya tafi dole xai ban kudi me yawa” Aunty tace “Toh shkkn Allah ya kai mu, xan je anguwa ne dama da yamma, so duk da haka xan biyo din dai” Aunty tace “To sai kin xo” Daga haka ta katse wayar…. Ramlah na kwance parlor da yamma taji sallaman Hajja, mikewa xaune tayi don kofar ma a bude yake tun bayan da Jiddah ta tafi Islamiyya, Hajja ta shigo tace “Sannu, a nan ana ta fama ko, ai uwarki ma lokacin da take da cikin Aliyu haka ta xabga uban laulayin nan dai kamar baxata yi ba, to ke gwara naki naga kina narkan abinci abun ki, kawai sai dai yawan kwanciya kamar ruwa, cikin na kwari duk xaki daina jin haka wllh” Ramlah dai sai murmushi take tace “Sannu da xuwa Hajja” Hajja ta karaso tace “Yauwa, sannu ina mijin naki?” Ramlah tace “Ya fita baya nan” Hajja tace “Toh gwara hakan, Jiddah fa? na samu labarin a nan take abunta yanxu” Ramlah tace “Ehh amma ta tafi Islamiyya” Hajja tace “O’o kullum dai ace taje Islamiyya, irin wannan xuwan Islamiyyan nata haka ai ya ci ace ta sauke, kullum fa tana hanyar Islamiyya kamar dai a Masar, to Allah ya bata ilimi me amfani, duk da dai tana da gaskiyarta” Hajja ta ajiye ledan hannunta a hankali kan center table tace “Har gida aka kawo min wannan ledan in gaya maki, ni dai sai riritasa nake kamar kwai abunka da kayan amana, to ynxu karfe nawa suke tashi daga wannan Islamiyyar dai?” Ramlah tace “Ta ma kusa shigowa, tun biyu ta tafi” Hajja tace “Atoh wannan kuma wani irin karatu ne kamar su suka fi kowa tsoron Allah” Ramlah dai ta tashi ta tafi kitchen, Ruwa ta kawo ma Hajja a kan tray da lemo da cup, ta dibar mata jollof din spaghetti da yaji hanta da beef wanda Jiddah tayi ta daura fork a kai da soyayyun kaji, duk ta daura kan tray sannan ta fito parlon ta ajiye kusa da Hajja tace “Ga abinci Hajja” Hajja tace “Kina wannan tofe tofen yawun xaki kawo min abinci Ramlah? Aa ni dai Alhmdlh sai da nayi nak kafin in fito daga gida” Ramlah ta tafi tayi kwanciyarta bata ce mata komai ba, Hajja ta sa hannu ta xare goran ruwan tace “Gwara gwara wannan din dai, dama har gidan Aliyu nake son xuwa saboda naji labarin safaran turarruka yake, sai ya bani ko guda uku ne, Nafisah ma naji wai ta rokesa turaren ai” Ita dai Ramlah kallo kawai take, Bude kofar aka yi Jiddah ta shigo da sallama, Hajja na ganinta tace “Toh Alhamdulillah, sannu da xuwa Jiddah” Jiddah na ganinta sai da gabanta ya fadi, ta karasa parlon ta xauna saman carpet a hankali tace “Ina yini Hajja?” Hajja tace “Lafiya lau, ga sakonki nan tun daga bauchi aka kawo, babu wanda yasan meye a ciki banda ni da aka gaya ma, nima din dai ba budewa nayi ba tunda ni ba yar boko bace” Jiddah ta dinga kallon fancy leda din, Hajja tace “Toh dauka ki duba mana” Dauka Jiddah tayi ta fiddo abinda ke cikin ledan, kwalin latest Iphone ta gani cikin ledan, Ramlah ta xaro ido ta mike xaune tace “Hajja wa ya siya mata wannan?” Hajja ta kalleta tace “Aa kuma ai wannan ba ruwanki Ramlah, ke dai kawai ki mata fatan alkhairi, da fatan kashewa lafiya” Ajiye wayar Jiddah tayi tace “Toh ai ni Umma basu ce xan rike waya ba yanxu” A fusace Hajja tace “Waye kuma Umma?? Yar bakin ciki ce fa matar nan fitowa fili ne bata yi ta nuna, ita ta isa tace baxa ayi abinda nace ba, banda Aliyun da ya tsinto mana ke a can hayi kina galantoyi, wanda ma da muka je gidan naku shekaranjiya gani muka yi an rushe d’an kuturun gidan da baldoza ba komai sai fili, ai ina ga babu wani da ya isa ya hanaki amfani da wayar nan a yanxu dai, don ko Usman yayi yunkurin yin hakan xan nuna masa bacin raina ainun balle wata mata can da ta narka uban kiba, da Masar ne ita wannan dama da tuni an kwantar da ita a asibiti baxa ayi shawara da yan uwanta ba ma, toh wacece kuma Umma a wajenki banda dai tana kanwar Uwar shi Aliyun da yayi sanadin kawo ki cikinmu, ni dai ba ruwana a dinga yin abu bisa tsari, ina ma laifin kice inje ince mata xaki fara amfani da waya” Jiddah dai tayi shiru bata ce komai ba, Ramlah sai kallon Hajja take daga kwancen da take, Hajja ta sharce xufar da ta hada don fitina tace “Balle ma jikana ne ya bada wayan nan a kawo maki, toh ina ruwanta kuma banda dai fitina take son ja ma kanta ita Ummar, yo fitina mana… daga masarautan bauchi fa wayar ta fito ba ma kasuwa ba, to tayi ta kanta don babu wanda xai duba cewa kanwar Hauwa ce ita, hukuntata xa ayi yanda ya kamata” Babu dai wanda ya tanka Hajja, Tana bude goran ruwan hannunta tace “Yanxu ki tashi ki cire uniform mu je ki rakani gidan Aliyu, shi kuma ina ta jin jita jitan xai fita waje da wani babba a jirgi amma kun ga ni ai ya ki gaya min, ko da yake dai baxan biyesa ba, titin ma da ya yasar dani a hayi shekaranjiya ban gaya ma kowa ba, bakina alekum na dawo gida na shige daki na, tinda mu ‘yan Masar dai da hakuri aka san mu…” Jiddah da duk hankalinta ya tashi ta dinga kallon Hajja ta ma rasa abinda xata ce, yanxu abu biyu ne ya dameta a rai, na farko Hajja tace wai an rushe gidansu, to me yasa xa a rushe gidansu su da ba a kan titi suke ba, ina babaarsu da Bibalo suka koma kenan yanxu?? Tunanin hakan yayi mugun daga mata hankali, na biyu kuma rakiyar da Hajja tace xata mata gidan Abuturrab, Ramlah ta mike ta tafi bandaki Hajja ta bi ta da kallo tana yamutse baki, tana dawowa daga bandakin ta kalli Jiddah da sauri tace “Tashi muje kada magariba tayi mana kin ji” Ramlah tace “Amma Hajja ai Ya Ahmad bai san xata fita ba, kuma babu kowa gidan sai ni kadai…” salati Hajja ta rafka tana kankance ido tace “Waye kuma Yaya Ahmad? Ina ruwana da shi? Me na hada da shi?? Kanin uban jiddan ne shi ko ko? Ku dai kun cika daukan magana wllh, shi yanxu ya isa hanata ta bi ni” Ramlah tace “Toh ai wajensa take dai yanxu” Hajja tace “Ja can ki ji da tsamin yawunki, ina ruwana da ke da Ahmad din, gashi nan ai ya hadaki da wahala kullum yana hanyar Abuja…” Jiddah ta kalli Hajja tace “Hajja ni fa ina da karatu gobe muna da jarabawa” Hajja ta dinga kallonta, can tace “Ni xaki walakanta ina yabonki sallah xaki kasa alwala?? Gidan jikana fa nace ki rakani ba gidan wani 6are ba, gidan nan kuma na samu labarin kin kusa wata uku a cikinsa, to meye don nace ki rakani xaki gatsa min wannan magana haka ba dadi” Jiddah dai ta sunkuyar da kanta a ranta tana tunanin no amount of words can allow her go to Aliyu’s house this evening, mikewa Hajja tayi ta dau jakarta ta nufi kofa, Jiddah taki yarda ta dago, Ramlah dai ta ma rasa abinda xata ce har Hajja ta fita parlon, Ramlah tayi kasa da murya tace “Ko dai xaki rakata don asirinmu ya rufu Jiddah??” Jiddah ta girgixa kai calmly tace “Ni baxan je gidan wannan matar tasa ba wllh, dama dai bata nan ne, kuma ba gwara ta sa a kira mata shi ya xo ba, amma sai inyi ta wani xuwa gidan mahaukaciyar a saboda me?? Baxan je ba” Ramlah sai kallon Jiddah take ganin yanda take maganar kamar she have grudges with Aneesah, murmushi Ramlah tayi tace “Ki dai yi hakuri, idan ya so kar ma ki shiga cikin gidan sai ki jira ta a waje” Jiddah tace “Na fa ce baxan je ba” Tashi tayi ta wuce daki Ramlah ta bi ta da kallo, sai kuma ta mike ta isa window tana lekan waje taga ko Hajja ta fita compound din, Tsaye ta ganta mai gadi na mata danne danne a waya alamar xai mata kira, Ramlah ta juya da sauri ta koma….

Bayan few minutes Ramlah ta sake komawa ta leka compound sai bata ga Hajja ba, wani ajiyar xuciya ta sauke ta wuce dakin da Jiddah take, tana cire Uniform ta sameta, Ramlah ta jingina da kofa tace “Toh Aneesah ta maki wani abu ne da baxa ki je gidan nata ba Jiddah?” Jiddah taki kallonta tace “Bata min komai ba, kawai dai baxan je bane…” Ramlah tace “Amma ai nace idan ma kin rakatan xa ki iya kin shiga kiyi tsayuwarki a waje har ta fito” Jiddah tace “Kofar gidan ma baxan iya tsayawa ba” Murmushi kawai Ramlah tayi ta juya ta fita daga dakin. Ranan Friday da daddare Aneesah na xaune parlor downstairs bayan Magrib tana kallon wani indian Series tana shan fruit salad, ta ji footstep ana saukowa downstairs din, daga kai tayi ta gansa yana sakkowa, lkci daya kamshinsa ya baxa ko wani lungu da sako na parlon, kafin tace komai yace “You still haven’t pray Aneesah” Tace “I know, ina xaka je da daddaren nan haka Captain?” Ya shafa beard dinsa yace “Wajen Budurwa ta” tayi wani dariyar da bata shirya ba tace “Hmm, kar Allah ya nuna min wannan bakar ranan, ni fa kasan wani abu captain?” Yana sakkowa yace “Sai kin fada” tace “Wllh duk ranan da yau aka ce da gaske kayi wata budurwa Allah xan iya kashe koma wacece har lahira, sai dai nima a daureni….” Yana kallonta bayan ya sakko parlon yace “Toh duk ranan da aka ce nayi wani auren fa?” Ta kallesa kamar baxata ce komai ba don gaba daya mood dinta ya canxa, sai kuma tace “Wai ka auri wata matar a duniya bayan ni?” Yace “Ehh” Wani murmushin ta kuma yi tace “Gwara a bar xancen kawai Captain…” Sai kuma ta hade rai tace “Kasan Allah? Wllh wllh xan iya kasheta in kashe kaina sannan kai ma in kashe ka duk mu hadu a lahira” Da mamaki ya dinga kallonta ganin how serious she is, cikin bacin rai tace “Wllh duk ka bata min mood wnn xancen da kayi captain, mu fa kaf xuri’armu fa ba a mana kishiya wllh, Aunty Salaha ma da aka yi ma satin amaryar uku ta bar gidan babu wanda ya koreta” Shi dai Abuturrab kallonta kawai yake ganin da gaske ran nata ya baci sosai, D’an murmushi yyi yace “Sai na dawo…” Ta mike babu yabo babu fallasa tace “Wai ina xaka da daddaren nan ne?” Yace “Ban ma Umma sallama ba, daxu gida kawai naje” kauda kai tayi ta ta6e baki, sai kuma ta kallesa tace “Toh bari in saka hijab mu je tunda ban ta6a xuwa gidan nata ba dama” Yace “No, ni kadai xanje, duk ranan da kika shirya sai kije ki gaisheta” Da mamaki take kallonsa tace “Ban gane No ba, yanxun idan naje laifi ne?” Yace “Eh saboda sai da xanje mata sallama sannan kika san xaki gaisheta” Bai jira cewarta ba ya nufi kofa ta bi sa da wani irin kallo xancensa na sake yawo a kanta wai duk ranan da aka ce yayi wata matar fa?? Tabb shi me ma ya kai sa fadin wannan mugun xance, ai daga ita ya rufe aure har karshen rayuwarsa, ita ce first and last dinsa, shi din nata ne ita kadai, tsaki tayi ta koma ta xauna ta ci gaba da kallonta amma ba cikin dadin rai ba… Abuturrab na parking ya dau wayarsa yayi dialing number ya kai kunne, wayar na fara ring aka daga, ya amsa gaisuwarta yace “Ki turo ta ta amsar maku sako!” Ramlah tace “Wa xan turo yaya?” Yace “Warce ke gidanki” Kallon agogo tayi don anyi isha, sai kuma ta mike ta fita xuwa dakin Jiddah, Jiddah ta gama sa kayan baccinta kenan tana shafa turare kafin ta dau takardanta ta fara karatu saboda exams da take da shi gobe Ramlah ta shigo, tsaye Ramlah tayi bakin kofar tana kallonta, Jiddah ta ajiye turaren hannunta tace “You need something?” Ramlah tace “Wai sako xaki amso a kofar gida” Jiddah ta dinga kallonta tace “Sako kuma? Sakon me? Kuma wajen wa?” Ramlah tace “Ya Aliyu” sosai gaban Jiddah ya fadi jin sunan da Ramlah ta ambato, Jiddah ta girgixa kai tace “Sakon me da daddaren nan, maimakon kice ya shigo da shi ki amsa don Allah, ji fa karfe nawa” Ramlah dai ta ma rasa abinda xata ce, Jiddah ta tafi ta dau takardanta ta xauna gefen gado, irin ita baxata je din nan ba, wayar Ramlah dake hannunta ne ya fara ring, ta daga ta sa handsfree tana kallon Jiddah, daga daya bangaren yace “Kuna bata min lokaci” Ramlah ta d’an fara kame kame, sai kuma tace “Yaya ko dai in fito in amsa ni? ita naga ta kwanta ne” Calmly yace “Taso ta” Tace “Wai dama exams…” Katse ta yyi yace “Ki taso ta nace” a hankali tace “Toh Yaya” ya katse wayar, Ramlah ta kalli Jiddah da ta 6ata fuska kamar xata yi kuka jin duk abinda yace, cikin rawar murya tace “Bayan ya Ahmad bai sani ba xan je kofar gida amsan sako, to gwara ki kirasa ni dai” Ramlah ta xaro ido tace “Ince masa me, salon ya kira yayan?? ke dai kawai ki sa hijab dinki ki daure kije kiga sakon meye” Jiddah ta girgixa kai da kyar tace “Ni baxan iya fita ba wllh, dubi fa agogo” Ramlah tace “Toh me kike so in ce masa bayan kinji yanda muka yi da shi Jiddah” Jiddah ta kwanta kan gadon ta lullube tace “Da gaske fa ni baxan je ba kawai ki kashe wayarki gaba daya, tun da rana me yasa bai kawo sakon ba” Ramlah dai ta rasa abun cewa tana ta tsaye, sai ga kiransa ya sake shigowa, ta xaro ido tace “Na shiga uku Jiddah ki rufa min asiri ki tashi kije, ni dama ba ni ya kira ba, bakin gate ne fa kawai xaki tsaya ya baki sakon da yace ki juyo ki shigo, wllh ban san kuma me xance masa ba idan na daga kiran nan” Ganin ya kusa katsewa ta daga tana rawar baki tace “Yaya na kuma ga tana wanka ne…” Yace “Ramlah” ta xaro ido tace “Na’am yaya” Yace “Mika mata wayar” karasawa tayi ta ajiye wayar kusa da Jiddah tace “Ga ta” Jiddah tayi narai narai da ido tana sauraronsa, yace “Fito ki amshi abinda nace yanxu, minti biyu na baki…” daga haka ya katse wayar, Jiddah ta mike xaune har hawaye ya kawo idonta, Ramlah na lallabata tace “Ki daure ki je pls Jiddah ai nan da kofar gida ne, kawai yana mika maki sai ki shigo kin ji” Mikewa Jiddah tayi daga kan gadon ta bude wajen kayanta ta dau hijab har kasa ta saka sannan ta fita, tun da ta isa gate gabanta ke faduwa, tana fita taga motarsa ta karasa tana tafiya slowly ta tsaya kusa da motar ta tsaya, sauke glass yayi yace “Shigo ki amsa” kamar xata yi kuka tace “Don Allah ka bani a nan, wllh ya Ahmad….” Yana kallonta directly in the eyes yace “Shiga nace” Sosai hankalinta ya tashi ta rasa yanda xata yi, da kansa taga ya bude motar ta matsa gefe ganin kallon da yake mata sai kawai ta shiga xuciyarta na bugawa, amma bata kulle motar ba, yace “Kulle min mota” Ta xaro ido tace “Don girman Allah ka bani sakon in koma wllh karatu nake gobe ina da exams, kaga dare yayi” da kansa ya kulle motar ya tada motar, hawaye ya shiga sauka idonta tace “Na shiga uku don Allah ka bude min in fita” barin layin yayi ba tare da ya saurareta ba, ta fashe da kuka sosai tana kallonsa cikin tashin hankali…. Bai ko kalleta ba ya ci gaba da driving dinsa, jingina tayi da kujeran motar tana kuka a hankali, bayan tafiyar kusan minti ashirin taga sun shiga wani katon shopping mall wanda wajen kamar da rana saboda fitilu da ya haska ko ina, ya nemi waje yyi parking ita dai bin wajen take da kallo gabanta na faduwa, sauka yyi daga motar ya xaga ta inda take ya bude motar, kasa kallonsa tayi shi kuma bai ce mata komai ba, bayan few seconds ta goge idonta ta sauka daga motar ya kulle, tafiya ya fara, da farko ta d’an yi jim ta bi sa da kallo, amma tsoron kada ya bace mata ta bi bayansa da sauri, tare suka shiga ciki tana bin wajen da kallo, inda ya ta6a kawota ya mata siyayya Washegarin ranan ta na farko a gidansa ne, cart ya tafi ya dauka tana biye da shi, ya mika mata handle din yana kallonta, sunkuyar da kanta tayi ta amshi cart din, ya dau wani ya fara tafiya, bin bayansa tayi tana turawa a hankali, wajen turarruka ya nufa, yace “Pick” tace “Ni ina da turare da yawa” Bai kuma sauraronta ba ya dinga debar mata turaren, ta dinga bin sa da kallo tana mamaki, bayan ya gama ya tafi gun mayukan shafawa da sabulu da shower gel, su ma ya dibar mata, ita dai bin sa kawai take da cart din hannunta, duk wasu kananun abu na bukatar yau da kullum sai da ya dibar mata, har ta fara gajiya da binsa, don sun siya kaya da yawa, wajen sanitary pads taga ya nufa, ganin uban pads din da ya debo bata san lkcn da tace “Ai basu kare ba na gida” Yana juyowa ta sunkuyar da kanta, yace “Meye basu kare ba” Kasa cewa komai tayi, ya xuba pads din a cart ya bar wajen, ta bi bayansa tana tafiya a hankali, sai da yaga cart din ya cika sannan suka tafi wajen kayan ciye ciye, nan ma bai jira yace ta dau komai ba, ya dinga debar mata duk wani abu da shi yake ci yana xubawa a cart din da take turawa, har kayan shayi duk sai da ya daukar mata, Jiddah dai sai kallon wani chocolate dake side dinta take ta yi don Ahmad na kawo masu irinsa daga Abuja, chocolate din kuma ba dai dadi ba, ta d’an kallesa taga yayi backing dinta yana duba wani tsadadden biscuit, kwasan chocolate din tayi kusan biyar ta juyo da sauri xata xuba su a cart din dai dai nan shi ma ya juyo rike da biscuits din da yake kallo suka kusa cin karo, juya masa baya tayi da sauri taji kamar ta nutse ta rufe ido, xata maida chocolates din taji ya fixgota, tayi narai narai da ido tana kallonsa da manyan idonta, ya amsa ya xuba su a cart din yana kallonta shi ma, ita ta fara sauke idonta, sauran siyayyan duk tana gefe har ya gama, suka tafi wajen biyan kudi, a booth duk aka xuba ledojin kayan siyayyan, eatry din mall din ya shiga ya siyi ice cream da pizza with shawarma sannan ya fito, ita dai tana tsaye bakin motarsa tana jiransa, bayan ya shiga ita ma shiga motar, cikin minti ashirin da biyar suka iso kofar gidan Ramlah. Jinginar da kansa yayi da kujeran motar ita dai jira kawai take taji ya bude lock din motar ta sauka, amma sai taga yaki budewa, bayan five minutes, taji muryarsa calmly yace “Xan mu fita
Dubai gobe in sha Allah, from there xa mu tafi Uk…” Ita dai bata ce komai ba, ya juya ya kalleta…. ta sunkuyar da kanta tace “Allah ya kiyaye” ya d’an yi shiru, sai kuma yace “Xan yi few months a can” Bata ce komai ba, yace “Kina da bukatar wani abu ne??” Ta girgixa masa kai tace “Wani abu kamar me bayan su Umma na yi min komai ni” Ya dinga kallonta yace “Wannan ne amsan tambayar da na maki?” Kin cewa komai tayi, yace “Bude baki kiyi min magana” Tace “Bana bukatar komai” shiru duk suka yi, ita dai wata magana ce ke cinta amma ta rasa ta ina xata fara masa, ji tayi yace “Do u have anything to say to me?” Ta kallesa da sauri, sai kuma tace “Ehh..” yace “Ina jin ki” cikin sanyin murya tace “Ranan Hajja tace wai kunje hayi an rusa gidanmu, ba kowa yanxu” Ya dinga kallonta yace “Sai aka yi yaya?” Ta fashe da kuka tace “Baabarmu da Bibalo fa?” Yace “Kina son xuwa wajensu ne yanxu??” Hawaye na sauka ido ta ta kallesa tace “Ehh ina so don Allah” Yace “Me xaki yi masu idan kinje” Cikin rawan murya tace “Ina son in gansu mana, saboda nayi kewarsu… Ban taso na gan ni da kowa ba sai su, and it’s been long… Nayi kewarsu sosai” Tada motar yayi bai kuma ce mata komai ba yayi reverse suka bar layin. The journey was so silent, bayan tafiyar kusan minti talatin suka iso titin hayin rigasa, tunda suka shigo hayi Jiddah ta dinga bin anguwar tasu da kallo, ta rasa wani irin farin ciki xata yi a moment din, farin cikin nata bai bayyana a fili ba sai da ta gansu kan layin gidan Babaarta, ta kallesa da farin ciki amma ta rasa abinda xata ce masa, she looks so happy… shiga layin yyi da motarsa xuciyarta na bugawa tace “Don Allah ko xaka tsaya in fara shiga gidan Iyah in gaisheta???” Ya kalleta sannan yayi parking kofar gidan Iyah, sauka tayi daga motar da sauri ta shige gidan a guje, ya sauka ya jingina da motar tasa ya bi ta da kallo, Iyah na xaune tsakar gida da rediyonta a hannu, tana ma jikokinta dake kwance saman tabarma fifita sun yi bacci, Jiddah ta wara ido cike da murna tace “Iyah!!!” Fadawa jikinta tayi ta rungumeta, Iyah ta matsar da ita tana mata wani kallo daga sama har kasa, sai kuma tace “Jiddah????” Rungumeta Jiddahh ta kara yi lokaci daya hawaye ya kawo idonta tace “Nice Iyah, nayi kewarku wllh” Iyah ma ta fashe da kuka tace “Ashe rai kan ga rai Jiddah, ashe xan sake ganin ki a rayuwar nan?” Jiddah ta share idonta tana murmushi tace “Gashi kin gan ni Iyah” Iyah ta mike tsaye tana sake kare mata kallo don tabbatar da ita din ce kuwa, sai ta saki salati tace “Daga ina kike haka Jiddah?? Kece kika dawo haka kamar balarabiya Jiddah??” Jiddah tayi murmushi ta kasa ce mata komai tana kallonta, Iyah tace “Ke da waye yanxu haka? Daga ina kike?” Jiddah tace “Yana kofar gida, ince ya shigo?” Bata jira me Iyah xata ce ba ta tafi da sauri kofar gidan, har sannan Abuturrab na tsaye ya rungume hannunsa, tace “Wai tace ka shigo” kallonta ya dinga yi ta juya ta koma ciki da sauri, shafa kansa yyi ya bi bayanta… Har kasa Iyah ta durkusa tana gaishesa bayan ya shigo gidan, hakan yasa ya xauna saman darduma yana d’an murmushi calmly yace “Ina yini??” Iyah ta rushe da kuka tace “Wllh da kasan irin taimakon da Allah ya baka ikon yi da ladan da Allah xai baka da ba haka ba bawan Allah, ka taimaki rayuwar Jiddah a sanda take tsananin bukatar taimakon, ka cece Jiddah a dai dai lkcn da take bukatar ceto, Allah ubangiji ya sa ka samu me maka abinda kayi ma marainiyar Allahn nan duniya da lahira, Allah ya biyaka da aljanna, ya yalwata maka arxikin ka, Allah ya baka ikon ci gaba da riketa da amana, Allah kuma ya baku xaman lafiya tare na har abada ya bada xuri’a dayyaba” Kuka kawai Iyah take kamar jininta ce Jiddah, Jiddah dai duk jikinta yyi sanyi ta sunkuyar da kanta jin maganganun Iyah, shi ma kawai murmushin karfin hali yake yana kallon tsohuwar a hankali ya ce “Ameen nagode Mama” Iyah na kwalla tace “Wllh ki rikesa Jiddah, kaf duniya a yanxu dai baki da kamarsa, shine uwarki shine ubanki, ya maki abinda a cikin kashi dari na mutane baxa ki samu kashi biyu da xa su iya maki ba, ya fidda rayuwarki cikin kunci, maraici, tsanani, da bakar wahala, yayi maki duk wannan abun a lokacin da kike tsananin bukatarsu, to me xai janyo maki butulce masa a rayuwar nan, kiyi masa halacci yanda ya maki Jiddah, ga shi wai yau kece sai da na maki kallo kusan uku sannan na gane ki, ba don muryarki ba wlh baxan yarda ke din ce ba” Sosai jikin Jiddah yayi sanyi wanda bata san lkcn da hawaye ya dinga sauka idonta ba tana kallon Iyah, kallonta kawai Abuturrab yake babu ko kiftawa, Iyah tace “Ki rikesa, kiyi masa biyayya, ki rike yan uwansa da duk wani nasa Jiddah, da abinda xaki iya biyansa kadai kenan ki ji in gaya maki, nace kiyi masa biyayya, wllh kiyi masa biyayya, Allah kadai yasan sadaukarwan da yayi sabida ke, Allah kuma ya baku xaman lafiya na har abada, nasan baku ma kai ga shiga gidan Hansai ba, amma idan xa ku ji ta nawa ba sai kun shiga ba kuyi tafiyarku kawai, Hansai bata canxa ba dai daga yanda kika santa… Sai ma dai abinda ya faru” Jiddah sai goge hawayen da yaki tsaya mata take, Abuturrab ya ciro kudi aljihunsa ya ajiye ma Iyah yace “Kiyi hakuri Mama babu yawa wannan, in sha Allah xan sake dawowa gaisheki, sannan xan daukeki in kai ki inda mu ke” Iyah tace “Wllh gaisuwan da kuka xo min ma ya isa ya wadatar ba sai ka bani kudi ba Yarona” mikewa yayi yana kallon jiddah da ta kasa daina kuka, a haka dai Iyah ta rakasu kofar gida tana cewa “Ba sai kun je gun Hansai ba, kuyi tafiyarku Allah yayi maku albarka ya baku xuri’a dayyaba…” Cikin sanyi Jiddah tace “Iyah baxan iya tafiya ban shiga na gaisheta ba” Iyah tace “Toh shkkn Jiddah, Allah ubangiji ya kareki daga duk sharrinta ku shiga kawai, akwai Allah” Abuturrab ma bai hana Jiddah ba suka karasa kofar gidan nasu da kafa, gabanta na faduwa ta shiga gidan ta ma kasa ko sallama saboda fargaba, Hansai na xaune tsakar gida tana fiffita ga kwanon abinci a gabanta tana cewa “Yo ba gwara ma ya mutun ba ko xa a rage mugun iri, duk fa da hadin bakinsa da uban kudi da aka dinga lafta masa aka siyar min da ‘ya ban ji ba ban gani ba, yau wata dai dai kusan biyar kenan, kuma wllh gaya maki ne kawai banyi ba amma so nake na hada yan kudaden wankauna, na kai gidan malam Hamisu a sake danne tsinanne kada Allah ya mikar da shi, kaf bani da makiyi irinsa a duniya yanxu kam…” Zulai dake kwance tsakar gidan da daurin kirji tace “Ai ko dai ance yana can shika rai a hannun Allah baya gane duk wa enda ke kansa, aiki ma xa a masa sai kuma jikin ya dada sususcewa kinga bbu xancen aikin ai sai ya farfado kuma” Jiddah ta kasa shiga gidan gabanta sai faduwa yake ta dinga karanto addu’o’i a ranta, Zulai ce ta hango shadow tace “Waye tsaye nan, ko Bibalo ce” Hansai tace “Bibalo ai sai karfe sha biyu kila, wani shegen ne ya tsaya min bakin kofa yana min la6e?” Jiddah ta runtse ido ta karasa shiga tsakar gidan, duk suka tsaya kallonta don akwai hasken wata sosai tsakar gidan, Hansai ta ajiye maficin hannunta tana kallonta daga sama har kasa tace “Waye wannan?” Da kyar Jiddah tace “Ni ce Baabarmu” Zulai ta mike a gigice tana sake gyara daurin zanin kirjinta tace “Ke wa??” Hansai dai hangame baki tayi tana kallon Jiddah daga sama har kasa, can ita ma ta mike ta nufeta tana sake kare mata kallo kamar taga aljanna, Hawaye ya shiga sauka idon Jiddah ta durkusa kasa cikin sanyin murya tace “Baabarmu” Hansai ta fashe da wani matsanancin kuka tace “Toh Alhamdulillahi, yanxu saura in kai ma Badalan kan dutse cikon kudinsa, aiki kam ya ci Alhmdlh… Allah ya maido min ita gida da kafafuwanta” wani shewa Zulai ta saki da karfi tana gode ma Allah ita ma, Jiddah dai sai kallonsu take, Hansai na sharban majina tace “Tashi mu shiga ciki, tashi” Jiddah tayi karfin halin cewa “Ba ni kadai ba ce Baabarmu” Hansai ta kalli soro da sauri tace “Ke da uban waye??” Jiddah ta sunkuyar da kanta tace “Ni da shi ne” Dai dai nan Abuturrab ya shigo cikin compound din don gaba daya hankalinsa ya ki nutsuwa shigan Jiddah gidan ita kadai, Hansai taji mugun faduwan gaba ganinsa tace “Ya xaka afko ma mutane gida haka kanka tsaye, kai waye??” Yana kallon Jiddah yace “Idan kun gama gaisawan taso mu tafi… It’s getting late” Hansai ta gwalo ido tace “Ku tafi ina?? To wllh wllh karyarka ya sha karya Malam, babu inda ‘ya ta xata daga tsakar gidan nan, ko taku daya baxata yi daga nan ba wllh, ku je ina?? Lallai sannunka….” tana huci ta kare maganar ta dago Jiddah da xumar shigar da ita daki tana cewa “Tashi don ubanki, idan kin sake fita ko nan da kofar gida Allah ya tsine min albarkan da yayi min….” Daga kasa har sama Abuturrab ke kallon Hansai da wani expression, can yace “Kin manta ita din matar aure ce?” Hansai ta mulmulo wani uban xagi tace “Fadi duk uban da ka kashe ni me iya siyar da gidan nan ne in biyaka, a gidan ubanwa ta xama matar aure?? Ka dau min ya ka tafi ka lalatata kace min matar aure ce??” Abuturrab na kallon Jiddah yace “Zo mu tafi” Jiddah hawaye na sauka idonta ta kallesa sannan ta kalli Hansai dake kokarin janta xuwa cikin daki, cikin kuka tace “Baabarmu….” Hansai bata saurari me xata ce ba ta wanka mata wani mummunan mari da yasa taji diff, ta kuma kai mata wani tana huci tace “Rufe min baki don ubanki” bai san lkcn da ya karasa compound din ya fincike Jiddah a hannunta ba yace “Kinyi na farko kinyi na karshe, kin kuma ci albarkacin ki na matar babanta da wllh sai na rama mata” Daga haka ya nufi soro da Jiddah, Hansai ta lafta wani uban ihu ta bi bayansu tana kunduma xagi tace “Idan Jiddah ta sake barin gidan nan shegiya aka haifeni, wllh babu inda xata je kuma ka cika min ‘ya ta” Ganin ta yo kansu Abuturrab ya kwasheta da kafa sai gata wanwas a kasa, ya bude front seat ya saka Jiddah dake ta kuka a ciki sannan ya kulle ya xaga ya shiga driver seat, Xulai ce ta fito da katon tabarya tana ihu wai jama’a su kawo masu dauki, Hansai ta mike a rikice ta amshe tabaryan, da duk karfinta ta buga glass din bangaren da Jiddah take, ihu Jiddan ta fasa a tsorace ya fixgota jikinsa tayi lamo, don sai da glass din yyi tsawa, Hansai ta shige gaban motar kamar mahaukaciya tana cewa “Da dai ka tafi da Jiddah gwara ka kasheni, ka kasheni nace d’an banxa… xan ga ta inda xaka bi ai, sai dai ka takeni, babu inda xaka kai min ya ta d’an yankan kai…” Abuturrab yyi reverse sosai sannan ya taho a guje, wani uban tsalle Hansai tayi ta kauce sai gata da Zulai kwance a kasa, ya ja motarsa a guje ya bar layin, kuka kawai Jiddah take kamar ranta xai fita, har suka fita titin hayi bai ce mata komai ba….