Parking yayi ya sauka yana kallon mai gadi dake xaune a waje, wanda har ya mike xai bude gate a tunaninsa Ahmad ne sai ya ga akasin haka, suka gaisa Abuturrab ya shafa kansa yace “Suna ciki?” Yace “Aa gaskiya basu jima da fita ba” Yace “Ba kowa a ciki yanxu?” Mai gadin yace “Babu kowa, ko awa daya basu yi da fita ba Yallabai” Abuturrab ya tsaya kallonsa, Mai gadin na washe baki yace “Da na ga motar ma na xata su ne ai” Abuturrab yace “Ohk, shkkn ba ma sai kace masu na xo ba… Sai anjima” Daga haka ya koma motarsa ya shiga, a hankali yake driving din… Parking yayi ya jinginar da kansa da kujera, bayan few seconds ya dau jotter a cikin motarsa da biro, ya cire pieces daya a ciki, kan steering ya ajiye takardan ya fara rubutu a jiki, bayan some minutes ya gama rubuta abinda xai rubuta ya maida biron sannan ya linke takardan gently, ya kashe motar ya sauka ya shiga cikin gidan, knocking yyi jin kofar a kulle, cikin minti kadan Maimoon ta bude kofar, matsawa tayi tana kallonsa daga sama har kasa, lkci daya ya daure fuska, ta xaro ido tace “Au, sannu da xuwa yaya” Da sauri ta juya ta koma parlon, Umma dake xaune Jiddah ma na xaune kasa daga kusa da ita ta daga kai tana kallonsa, tunda Jiddah ta kallesa sau daya ta sunkuyar da kanta, Ya karasa parlon ya xauna yana kallon Umma yace “Ina yini Umma” Tace “Lafiya lau, aka ce yau xaka yi tafiyar?” Yace “Ehh in sha Allah…” Sai kuma ya shafa kansa yace “Naga ban xo mun yi sallama bane” Umma tace “Bayan wanda mu ka yi a gidan Yaya?” Ya sunkuyar da kansa, Maimoon dai na tsaye sai kallonsa take, idan ta kallesa sai ta kalli Jiddah da taki dago kanta sai wasa da fingers dinta take, Umma tace “Toh ki kawo masa ruwa Maimoon” Maimoon tace “To Umma…” Har ta kai bakin kofar kitchen din ta tsaya tana kallon Jiddah tace “Jiddoh xan xuba moringa din yanxu, ki xo ki gani” Jiddah ta d’an kalleta, Umma tace “Ba kince kina son koya ba, ki tashi ki je” Mikewa Jiddah tayi ta wuce kitchen din, da gefen ido ya bi ta da kallo a sace yanda Umma ma baxata sani ba, Umma tace “Amma daxu mun yi waya da Ahmad yace xai je kai ka airport…” yace “Ehh Umma, xan koma yanxu.. nan da awa daya da rabi ne flight din” Umma tace “Toh Allah ubangiji ya tsare, ya kai ku lafiya ya dawo da ku lfya” Yace “Ameen” Jiddah na shigowa kitchen Maimoon ta kulle tana kallonta tace “Kawai sai naga yaya Aliyu, alhalin for almost 2 weeks bai xo gidan nan ba” Jiddah ta hade rai tace “Toh me yasa kike gaya min?” Dariya Maimoon tayi har da tafe hannu tace “Aa ni fa kawai hira nake maki wllh…” Jiddah ta juya xata fita Maimoon ta rikota tana dariya tace “Ke wllh ni kawai jajantawa nake son mu yi da ke” Jiddah tace “Ki sakeni fita xan yi” Maimoon tace “Dallah ki tsaya in hada miyan tukunna, to meye don nace kawai sai ga yaya Aliyu, au ni na ma xata Safiyya ce nake maki wannan maganan, abinda mun saba gulman mu haka, amma ke kina so ki min wata fassara” Jiddah dai bata ce komai ba sai kallon miyan dake saman gas take, Maimoon ta tafi ta dau ruwa da coke ta daura kan tray ta dawo tana kallon Jiddah ta mika mata tace “Don Allah ki kai masa kar miyan ya kone” Da sauri Jiddah ta matsa ta tafi gun miyan tace “Bar min miyan xan dinga dubawa kije ki dawo” Maimoon ta hade rai tace “Kika san me xan ma miyan to?? Ni wllh wani lokacin kina bani mamaki, meye a ciki kawai dai kije ki dungurar masa da tray din a gabansa ki taho, wllh ba don miyan ba ni da kaina xan kai, ai ni aka sa ba ke ba” Maimoon ta d’an yi tsaki ta ajiye tray din tace “Haba, sai kace warce nace ki kai ma wani dodo ruwan sha” Gun miyan ta tafi tana juyawa, sai kuma ta nufi kofa a tunanin Jiddah daukan ruwan xata yi ta kai masa, sai taga bata dauka ba, Maimoon na fita parlor ta kullo kofar kitchen din tana kallon Umma tace “Umma wai Aunty Malika na ta kiranki, kamar wayarki na daki koh?” Umma tace “Ta kira ki ne?” Maimoon na d’an rawan baki tace “Haka dai tace min” Mikewa Umma tayi ta nufi hanyar dakinta tana cewa “To ai wayar na daki” Maimoon ta koma kitchen da sauri tana ci gaba da juye juyen miya bayan gas din ma a kashe yake tace “Kawai minti nawa kin kai ruwa kin dawo, idan ba dai da akwai wani abu a ranki da kike boye ma mutane ba” Jiddah dai bata ce komai ba sai kallon tray din take, Maimoon banda satan kallonta babu abinda take, daukan tray din Jiddah tayi daga karshe ta nufi kofa tana tafiya kamar bata son yi, ta bude ta fita, sai da ta shigo parlor taga Umma bata nan, ta fara kalle kalle, yana ganin haka ya mike, ta dungurar da ruwan kamar yanda Maimoon tace, xata juya yyi saurin kamo hannunta, ta juya ta marairaice masa murya kasa kasa tace “Wllh xan maka ihu ka sakeni, ka daina min abun nn da kake yi bana so” jan hancinta yayi har sai da ta ji xafi sannan ya saka mata takardan hannunsa a tafin hannunta yana kallon kwayar idonta, fixge hannunta tayi daga rikon da yayi mata kusan a guje tayi hanyar dakin amma takardan da ya bata na hannunta har sannan, ya bi ta da kallo kafin ya juya, ido hudu suka yi da Maimoon da ta d’an bude kofar kitchen din tana lekosu, ai da sauri ta yi jamming kofar bayan sun hada ido, yayi hanyar kitchen din, saura kadan ta tunkude miyan kan gas din bayan ya shigo kitchen din, sai xare katon idonta take tace “Xa a xubo maka abincin ne Yaya?” Janyo hannunta yayi yace “Ba dai kin iya munafurci ba??” a gigice tace “Don girman Allah kayi hakuri yaya, naje kulle kofa ne sai ka gan ni…” Bai saurareta ba ya bude kofar kitchen din ya fita yana rike da hannunta…. Umma ce ta fito parlor tace “Au, tafiya yayi shashashan?” Babu kowa parlon balle a bata amsa, Ta wuce dakinsu Jiddah taga Jiddah kadai a dakin tace “Aliyun ya tafi ne?” Jiddah tace “Ina daki ban sani ba” Umma tace “Toh ga shi ki amso min kati na dubu daya a waje” Jiddah ta d’an xaro ido amma bata ce komai ba ta amshi kudin gabanta na faduwa, Umma na fita dakin ta saka hijab dinta ta fita ita ma, duk jikinta a sanyaye ta fita compound, tana isa gate ta leka waje ta ga motar Ahmad instead, amma Abuturrab ne a ciki Maimoon na tsaye daga window din kusa da shi ta daddage tana cewa “Ni dai wllh ka tura yanxu kafin ka tafi yaya, haka kawai idan ka je ka manta bayan na sanka da mantuwa, kawai bari in kira maka account number din ai yana kai na” Ko kallonsu Jiddah bata sake yi ba ta nufi kantin da xata amso kati, Abuturrab na danna wayarsa yace “Call the account number” tana washe baki ta shiga kira masa account number dinta har ta gama, snn ta fara kallon wayarta dake hannunta tana murmushi, cikin few seconds sai ga alert, ta duba da sauri taga dubu hamsin, wani tsalle ta doka tana tafe hannu sannan tayi masa blow din kisses tace “Nagode sosai yayana, Allah ya saka da alkhairi, Allah ya kara maka budi, Allah ya kai mana kai lafiya ya dawo da kai lafiya” Komawa baya tayi ganin ya tada motarsa tana daga masa hannu har ya bar layin, baki har kunne ta shige cikin gida, Jiddah ma ta shiga gidan don duk tana kallon abinda Maimoon take a titi…. Dakin Umma jiddah ta tafi ta kai mata katin sannan ta fito ta shiga nasu dakin, gaban madubi ta tafi ta dau takardan da ta ajiye bayan ta shigo dakin daxu, daukan takardan tayi ta shiga warwarewa, haka kawai ta ji gabanta na faduwa, ganin ta kusa gama budesa ta rufe idonta, sai da ta warware gaba daya sannan ta bude idonta a hankali tana kallon content din takardan gabanta na faduwa, “Ni ba matarsa ba, ni ba muharramarsa ba… amma yake min wasu abubuwa da bai dace ba a addininmu, bayan duk wani da yasan karatun addinin nan namu yasan haramcin yin abinda yake yi, ya kuma san hukuncin wanda ya aikata hakan, kullum tunanina wanda xan kai ma kararsa… ya takura ni, ya takura ma rayuwata bayan kuma ya sakeni kowa kuma ya shaida ya sakeni…..” Boldly daga kasan rubutun aka rubuta “Ur mentality Jidderh!!! And I know u might be questioning my fate, amma ki saka a ranki ba dai dai kike da sauran yan matan da ke gaban iyayensu ba yanxu, you ain’t of the same level with them… abu kadan xa ki yi Allah yayi fushi da ke! … no doubt na fi ki sanin addininmu, limit ur interaction with MALE, limit ur going out, and by so doing, u are respecting ur religion” Jiddah ta karanta content din takardan nan yayi sau biyar amma ba abinda ta gane, da ta dauko hanyar ganewa sai abun ya ruguje kan ta kai karshe, a hankali ta linke takardan ta yaga, sai da tayi masa pieces sannan ta tafi ta bude window ta watsar, Maimoon ta shigo dakin ta ajiye wayarta gaban mirror tace “Ke bikin kawar nan tawa fa sati me xuwa ne, ina ta son in kira Aunty Ramlah ince ta baki waya in gaya maki muna da biki, kuma ba karamin casu xa ayi ba, hope kun gama exams before then?” Jiddah ta tafi ta xauna gefen gado tana duba farcenta tace “Ban gama ba” Ta gefen ido Maimoon ta kalleta ta d’an ta6e baki ta nufi kofa tana cewa “Ko da yake ke ai sai da izini, mu din dai” Daga haka ta fice, Jiddah ta bi ta da kallo. Bayan sati daya Jiddah suka gama exams suka yi hutu ta dawo gidan Umma yin hutu… Ranan friday ita da Maimoon da Safiyya suka shirya xa su gaida Ummi, Da yake driver baya nan, Umma ta basu kudin adaidaita tana sake jaddada masu kar su kwana saboda Islamiyya gobe, Maimoon tace “Haba Umma karfe biyar na yi xa mu juyo, har sun nufi kofa Maimoon ta kalli Jiddah tace “Anya baxa ki sa Hijab ba Jiddah?” Safiyya tace “Saboda me?” Maimoon tace “A’a ba saboda komai ba, gani nayi ya fi mutunci” Daga sama har kasa Safiyya ta kalleta tace “Shi yasa naga kin sa Hijab din ke ai” Jiddah tayi ficewarta bata sake sauraron Maimoon ba, Safiyya tace “Duk wani harka na iyayi kin fi kowa iyawa” Maimoon tace “Aa daga magana sai cibi ya xama Kari, ni dai ba kawai suggestion na kawo ba” Safiyya tace “Why didn’t u suggest that for ur self??” Maimoon tayi ficewarta tayi banxa da ita. Suna isa gidan direct bangaren Ummi suka wuce, Aneesah na xaune parlon da kanwar mamarta Safara’u da ta tare a gidanta tun bayan da Aliyu ya bar kasar, Ummi ma na parlon alamar dai su ma xuwansu kenan, Maimoon na ganin Aneesah ta hade rai tana kallon Ummi tace “Ummi ina yini?” Ummi tace “Lafiya lau Maimuna, daga gida ku ke haka?” Maimoon tace “Ehh wllh Ummi, Hajja na nan?” Ummi tace “Hajja ai tana Bauchi” Maimoon tace “Ohk” daga haka ta wuce dakin Ummi, Aneesah ta bi ta da kallo, Jiddah ma ta durkusa ta gaida Ummi, Ummi ta amsa da fara’a, wani kallo Aneesah ta dinga yi ma Jiddah kamar ta ga kashi, Jiddah ta kasa kin gaida Safara’u ganin babba ce, Aneesah na jin ta gaida Safara’u tayi ma Safara’un alamar kar ta amsa ta hanyar ta6a ta da sauri, ai ko Safara’u taki amsawa, Safiyya ta gaida Ummi sannan ta gaida Aneesah da Safara’u ta mike ta wuce dakin Ummi, Ummi na kallon jiddah tace “Tashi ki bi su ko” Mikewa jiddah tayi ta bi bayansu, Aneesah dai sai kallonta ta gefen ido take, ta rasa dalilin da yasa da taga Jiddah sai hankalinta ya d’an tashi, Safiya ce tsaye tana kallon Maimoon tace “Me yasa baki gaida Aunty Aneesah ba?” Maimoon da ke kwance kan gadon Ummi ta mike tace “Wacece kuma Anty Aneesah? Me na hada da ita da xan gaisheta?” Safiyya tace “Matar Yaya Aliyun??” Maimoon tayi wani dariya tace “Ta jira dai taga matar tasa ta ainahi… Wannan matar me yi ma mutane kallon rainin hankali da walakanci ne xan gaishe da, ji fa ranan da muka je gidanta abinda ta mana har xaki ce in gaisheta, a da nayi vow har in mutu baxan sake komawa gidan yaya Aliyu ba, amma dai nayi istigifari kwanan nan don can ne ma dabar mu idan Allah ya so nan ba da dadewa ba, sai ta raina kanta wllh, don ni tattara kayana ma xanyi in koma gidan sai dai in Umma ce ta hanani ko shi ya korani” Daga Safiyya har Jiddah dai kallonta kawai suke, ta murguda baki ta mike ta fice daga dakin yanda xata sake bin gaban Aneesah ba tare da ta gaisheta ba, ai ko Aneesah ta bi ta da kallo kasa kasa xuciyarta na tafarfasa har ta fita parlon. Kamar yanda suka sanar ma Umma karfe biyar suka fara shirin komawa gida, Ummi ta basu kudin mota sannan tace “Amma fa ku shiga ku sallami Aunty duk da bata dade da dawowa ba” Sallama suka mata suka fita, Jiddah tayi pretend kamar xata je ta sha ruwa, Maimoon da Safiyya suka shiga part din Aunty, Tana xaune parlonta da Aneesah da Safara’u, suna gaisheta ta mike rai bace tace “Wato ke Maimoon don baki da kunya baki gaji kunya ba ita Aneesar xa ki gani ki ki gaisarwa ki wuce don Ubanki??” Maimoon ta tsaya tana mata kallon tara saura amma taki cewa komai, Aunty na tafe hannu tace “Maxa fitar min daga parlor kada in rotsa maki kai, shegiya fitsararriya kawai” Aneesah tace “Ae kawai da kin kyaleni da ita Aunty, ita karamar alhaki ma?? Wllh so nayi watarana Allah ya kawota gidana in mata koran kare, uwar me gaisuwarta xai kare ni da shi dama?” Maimoon tayi wani dariya tace “A gidan yayan nawa xa ki yi min koran kare??” Aneesah ta mike tana huci tace “Kya dai je ki nemi yayanki amma ba Aliyu ba, idan kuma da akwai abinda ya fi koran kare wllh sai na aiwatar gareki in har rashin hankalinki ya ja ki xuwa gidana, don wannan gidan a yanxu ko shi Aliyun ba shi da wani say a kansa, yau da Ramlah ko Nafisah ko Aisha ce suka ki gaisheni shine xan ji takaici amma banda ke karere gayyar tsiya” Maimoon tayi wani shewa tace “To mu xuba dake shege ka fasa, kuma wannan gidan da kike takama da shi sai ya gagareki xama kwanan nan ba da wani dadewa ba wllh, abota xa ki kulla da sleepless night very soon…” Da gudu Maimoon ta fice daga parlon tana murguda baki ganin Aunty ta yo kanta tana kunduma mata wasu axababben xagi kamar bamagujiya, ita dai Safiyya na tsaye kamar shashasha, Safara’u kuwa sai dannan xuciyarta take tunda Aunty da Aneesah nayi ita bai kamata ta sa baki ba, Aunty tayi mata tsawa tace “Fita kema, gantalallu gayyar tsiya kawai….” Safiyya bata ce komai ba ta fita daga parlon, tuni Maimoon ta ja Jiddah suka fice daga gidan ranta fess ta fesa masu rashin kunya iya rashin kunya, sai da suka nufi titi Safiyya ke cewa “Wllh baki ji Maimoon, baki jin magana, Umma ta hanaki wannan halin kin ki, idan ma sun xageki meye na biyesu bayan kin san ba sa’anninki bane su??” Maimoon tana tafe hannu tace “Ba ruwana da tsufansu, ai ance respect begets respect, Respect should only be given to he who deserves ita, wato dai he who respect his or her self, basu yi respecting din kansu ba balle inyi respecting dinsu, haka kawai a xagi ubana dake kabari a kan wata banxa jaka can kaxama da ita kike expecting inyi shiru kamar ban san ciwon kai na ba?? To wllh ban rama yanda nake so ba ma, sai ranan da muka fara bata sleepless night a gidanta sannan xata gane ni ba kanwar lasa bace…” Wani shewa Maimoon tayi cike da farin ciki, Safiyya tace “Ke da wa xaki bata sleepless night din” Maimoon ta bude hannu tace “Ohoo a xuba ido a gani, shi sa Jiddah asirinta a rufe taki shiga nima da na sani wllh kawai ce ma Ummi xanyi to amma inyi wucewata, uwata ce ita da dole sai na gaisheta??” Safiyya tace “Ni dai ba ruwana ki daina wnn halin da kike….” Maimoon tayi gaba ta ki sauraran Safiyya kuma, Jiddah dai tafiyarta kawai take bata ce masu komai ba, a ranta kuwa taji dadin dubaran da tayi na shigewa kitchen da yau har da ita xa a hada a xage ubanta dake kabari. Bayan kwana biyu Jiddah na xaune kan darduma ta idar da isha Maimoon ta shigo rike da wayarta dake kare kunnenta, ta nufeta ta mika mata wayar tace “Kema ku gaisa, Safiyya ma sun gaisa, har da Umma ma sun gaisa” Jiddah na kallonta ta amshi wayar, screen din ta fara kalla ta ga “Yaya A” ta kai wayar kunne tayi shiru, Maimoon tace “Toh kiyi magana mana ai bai katse ba fa” daga daya bangaren taji yace “Shiru kika yi?” Lokaci daya ta dau muryarsa wanda hakan ya ja mata faduwar gaba, ta d’an hade rai a hnkli tace “Ina yini” Yace “How are you?” Tace “Lafiya” juyawa Maimoon tayi ta lallaba ta fita dakin….