JININ JIKINA COMPLETE
“`A fiction and Love tale story “`
.
MUNIELURV
.
_Dukan yabo ya tabbata ga Allah (S.W.T) dayabani ikon fara rubuta wannan Novel’dina mai tattaken *jinin jikina* kuma ina rokonsa da yabani ikon idar wa_ (Ameen). _wannan Littafin na saudaukar gareki cwt Mommah Aunty sis_ *Bismilahir Rahmanir Rahim* _Dedicated to Aunty sis_
.
*kiiiiiiiit kake ji ta taka burki amma ina sai da ta buge yarinyar tiiiim tafadi kasa jini na zuba ta ko ina a fuskanta gata kwance luuu a kasa kamar mutaciya,ankace kobo mutane sun hallato da sauri ta bude motan ta fito da gudu tana ganin yanayin yarinyar a kwance tace wa mutanen”pls help me put her into d car” hk suka cin cin cimeta suka sata motan da karfi ta tada motan at 360 ta wuce National hospital dake garin Abuja. ” Nurse! Nurse!! Ta kwalla musu kira” “Ganin yanayin su yasa nurses zuwa da gadon tura marasa lpy,suka turata sai cikin hsptl” “Direct wani daki aka shiga da ita, taso shiga amma doctor ya hana Ba yadda ta iya hk ta hakura taxauna a waje ita dai addu’ar ta bai wuci Allah sa yarinyar is alive” “Tana zaune a wajen kusan 30mins kenan da shigan Dr dakin, bude kofan da akayi neh ya dawo da ita sense’dinta ta tashe tace” “Doctor hope ol x wel? ina fatan she ix not dead? duk tajero mai tmbayn a lokaci daya” “Sai da ya gama goge jikinsa da cire hand gluf na hannunsa yace follow me to my office” ” tana biye da shi suka karasa cikin office din yace have a seat tukun ta zauna yayi gyran voice sanan yafara dace wa” “Hjy ki kontar da hnklin ki d gal x fine kawai tadan ji raiunin neh a forehead sai kuma jikin ta dayaxama dole ya mata ciwo sabide fadi Wanda tayi yaja numfashi yace she has olredy regain conscious yanxu allura na mata zata iya kai wa nan da next 12hr tana bacci,gawanan takarda ya mika mata yace is ol her medication Ku saya and pls patients din taringa cin abinci sosai” “Gdy sosai tayimar sanan ta wuce pharmacy tasai maganin ta dawo dakin da yarinyar take kwance” “Ta iso bakin bed din a hnkl ta sami waje ta zauna ta kura yarinyar ido tana kallonta she is cute ta furta a hankli ta kai hannun ta tashafi fuskanta” “Wayanta neh yayi kara takai duba kan screen taga “son” a rubuce ta dauka tare dacewa” “Hello son” “From d other hand yace yes Mom ina yini” “Lpy ta amsa sa” how are I doing there? “Alhamdulillah ” insha allah cikin week dinan i will b home,am eager to b home wlh I miss u mum” ” Miss u too son”
.
“Nan suka Dan taba hira ta ke sanar dashi abinda ya faru ya jajinta tare dayimata sai da safe” “Sai yanxu ta tuna da gida ta kira wayan Dad ta gayamasa abinda yafaru yace gasunan zuwa yanxu ” “Tanan zaune suka iso humaira da fareeda ce suka shigo sai Dad dake biye dasu nan fah suka jajinta abinda ya faru” “Fareeda tace hey little sis ki ga yarinyar so cute ga gashi and kinsan meh da gani bata wuce 14-15yrs Ba kai ni dai na samin little sister duk suka kwashe da dariya” “Mum tace gaskiya nima from d look I take to her naji ina sonta” “Hk dai sukayi ta surutu har can kusan 9:00 na dare Dad yace sutafi kememe suka ki wai su a dole sun sami sister zasu kwana Ba yadda su Mum suka iya dole suka yarda farida da humy su kwana nan suka musu sai da safe suka wuce gida”.
.
_the following day_ Fary da humy ne zaune suna hira tun bayan idar da salla’n asuba and almost 7:00am morning kmr ance su juya ai ko suna juyawa idon su ya sawka kn ta hannun ta na motsawa alaman tafara farfadowa. “A hnkli take bude idanunta tana karewa dakin kallo nan eyes dinta suka sauko kan su fary firgitt tayi yunkurin tashi “arrggghh” ta dafe kanta dake sarawa da sauri suka karasa gunta dagota sukayi tare da jiginar da ita “sorry”saying both ov them wit pity voice” “Farida tace little sis go cal d Dr hurry up, da sauri ta fice xuwa Koran Dr” “Batafi 2mins Ba suka shigo tare ya duddubata yace Ba wani matsala only if kanta Dan difitently yasan xai yi ciwo amma su bata hot tea da food sai tasha magani ya fita” “Ina nake ask ita wacce har yanxu ban San sunanta Ba” “Dafata farida tayi tace nan asibiti ne sannu kin sami accident neh jiya mahaifiyar mu ce ta bugeki” “Runtse ido tayi a hnkl abinda ya faru da ita yasoma dawo mata absulotely jiya tasan tana tfy not knowing inda xataje and tana ganin Abu dishe dishe taxo taji kanta a kasa tiiiimmm” “Salamarsu Mum da Dad neh ya farfado da ita from her from her dream, suka karasa har bakin gadon Mum ta karasa hannun ta tarike ta furta sorry ya jikin ol asking” “Binsu kawai take da ido with out speaking any words” “Fareeda help her clean up and u auta zo ki hada mata break” “OK Mum both answering” “Fareeda ce ta taimaka mata tayi brushing tare da wanka bayan nan ta dauro alwala suka fito” “Salolin da ake binta jiya ta taramasu before taking her break” “Bayan ci abincin Mum da kanta tayi feeding dinta tare da bata drugs nata while shi kuma Dad yaje settling bills nasu before ayi discharging nasu” “Sai da suka kammala break tare da kimsawa before suka fita Dan tafiya gida”. °°°°°°°°°°°°° At home sun iso suka yi parking na motansu a parking lot, babban gidane nagani a fada up stairs yane wanda yasha pent lemon green ga flowers da sauran shuke shuke masu kyau kana ganin gidanan kasan Ba gidan karamin mutum bane wajen parking lot ma cike yake damm da motoci kamrsu Prado Mercedes Benz, Accord 2016 da sauran manyan motoci a kalla zasu kai 7 a wajen.. “Itakam ido take ta gwalowa wannan gidan hk” “Karasawa ciki sukayi Mum ta umurcesu da su wuce stairs da ita zuwa anjima itakuma suka wuce da Dad” “A can dakinsu fareeda sukaje nan suka yi wanka suka canza before suka sauko downstairs” “A babban falon gidan suka hallatta Dad yayi gyran murya before ya fara da cewa” “Baiwar Allah kin dai ga mai ya faru dake Dan hk muna mai baki hkr bisa abinda ya faru, sannan Abu na gaba zamu so jin daga ina kike Dan mu maidaki Dan munsan tabbas duk inda iyayen ki suke tho hnkl’n su a tashe ya ke suna Neman ki” “Sai ki fadamana gidanku da unguwarku Dan maidaki yana ida’wa nan yayi shiru tare da cewa muna sauraron ki” “Nan da nan ta fashe da kuka tace ni bani da kowa a garin nan ban San kowaba yau shine rana ta na farko a garin nan tana matsar yar kwalan da su tarumata a ido” “Shiiii cewar Mum tana bubbuga mata baya bar kuka ki bamu lbrn ki insha Allah xamu taimaka miki kinji” “Nan taja dogon numfashi tare da cewa:”
****
Ni sunana *Muskan* asalin mahaifina haifaffen dan garin bauchi neh fulanine na usul mahaifiyata kuma Hafsat Ba yar nan bace ita yar Egypt ce.. “Mahaifina Alh Isma’il ya kasance babban Dan kasuwa yana sana’ar export da import yana fitar da kaya waje da shigarwa tunda yake shekara 20yrs a duniya iyayensa suka sami accident suka mutu dake shi kadai mallaka kuma ya girma hkn yasa aka dau dukiyarsa aka damka masa toh fah nan wani baffan shi Dan uwan abban sa yaji kyshi da bakin ciki dake Abbana yayi mkrnt ya hada har degree ta fannin business ya soma tafiyar da kasuwancinsa cikin ikon Allah kasuwanci ya bunkasa har ya kai ga Baffa Ba jin tsoron nuna masa kyashi da bakin ciki amma shi Sam basa gabansa” “Watarana yaje Egypt business nan suka hadu da ummana basu dau wani lokaciba suka kulla soyayya shakuwa mai karfi tashiga tsakanin su har ya kai ga maganan aure iyayen ummana basu yi wata wataba suka Ba Abbana auren ummana kasamcewar sun bincika halinsa wajen abokan kasuwancinsa nan wani abokin Abba ya wakilcesa aka daura aure bisa sadaki dubu 20k daga nan kuma akabasa amaryarsa suka dau hangar 9ja”wannan kenan..
.
“Tunda Abba ya dawo da Umma ya fadawa Baffa yayi aure can ya sababi da surfa matsifa wai ai shi isma’il bai dauke matsayin uba coz in ya isa da shi toh bazai je yayi aure without letting him knowing Ba” “Abba dai shiru yayi masa amma shi duk maganan nan daya fada bai daukesu abakin komai mtsssww Kansu ake ji nan ya dau umma ya nufi gidan sa da ita kasamcewar yacewa iyayen umma karsu sai mata ko tsinsiya ” “Sun isa gidan komai akoi intact kamar dama akoi mace ” “Nan dai Abbana da umma su zauna cikin “So” da “Kauna” kullawa sosai Abba ke bata Ba abinda ya damesu ko daga musu hnkli zaman su mai matukar burgewa” ” watanni sun shude hk shekaru kusan uku amma shiru ko bari umma bata taba yiba hkn Ba karamin tayar mata da hnkl yake Ba Dan tasan Baffa da Matar kande Sam basa kaunarta ga kuma rashin haihuwa nan fah ta ringa daga hnklinta amma Abba kullum cikin kwantar mata hnkli yake kan ai haihuwa na Allah neh kuma ko da yaushe ai xai bata idan ya mata irin wadan’nan kalamain takan samu nutsuwa” “Ana hk wataran umma ta sami ciki zo kaga murna wajen Abba da Umma wayyo dadi kulawa sosai suke Ba cikin gashi sun dau duk wani son duniya sun daurawa ciki hkn ya haifar da bakin ciki sosai zuciyar Baffa da inna kande Dan gani suke ai Idan umma ta haihu shikenan baza su sami damar cin arziki bah nan suka fara tunanin hallakata amma Sam duk wani mugun aikin su baya ci har suka hakura zuwa haihuwana” “Wata alhamis umma ta tashi da tsananin na kuda nan hankalin Abba ya tashi sosai su Ka nufi asibiti nan fa Allah ya albarkace su da samin `ya” “Murna kam ba adadi bazai faduba wajen Abba banda su Baffa da zuciyar su fal da bakinciki amma a fili suka nuna farin ciki “hmmm ni dai Munie nace Allah ya shiryesu (Ameen). “Ranar suna aka radamin suna *MUSKAN* ma’ana {Smiling} Murmushi”domin tunda na shaki iska’n duniya Abba ya daga ni nake ta murmushi nan ya zabamin sunanan ” “Na taso cikin gata da jin dadi gani kyakyyawa duk da ina karama na kasance mai kyau a hk har nakai Shiga mkrnt aka sani gashi kuma ina da bala’in kokari kwakwalwana na saurin daukan Abu ina girma kyawuna na dad’a karuwa, kuma tun ina karama na fuskanci Baffa basa son iyayena kai harni kaina basa sona hkn yasa na ke ganin tsangoma da wula kanci iri2 ” “Ina da shekara 15yrs a duniya likacin ina ajin ss1 na zama cikakiyar budurwa kyawuna ya Dada bayyyana nan fa Maza da yawa sun kawo min farmaki amma ina ni Sam basa gabana kuma kullum cikin min kashedi tare min hani da kula samari Dan yace yamin miji” “Mijin da ni van San saba Abba ma haduwa sukayi airport da shi yana aiki acan sakamakon taimakon da yawa Abba na wasu makudan kudin dake briefcase wasu barayisuka so warcewa nan wannan bawan Allah yataimaka ya kamasu Abba ya mishi godia yamasa kyauta amma atapir ya ki Dan HK ya gayyacesa zuwa gidanan mu cin abinci nan suka je tunda suka iso ya ganni yacewa Abba yana sona irin taimakon da yayiwa abba kuma ya gane shi yaron mai hankaline nan ya basa ni amma kan sharadin sai na gama mkrnt hk ya amince ni de kam murna nake Dan irin kulawanda yake bani nace na sami yaya tun yana boyemin soyayyarsa har yazo ya bayyana min soyayyarsa” “Dama shi Dan jihar Abujane aiki yaje bauchi amma yawacin yafiya fita aiki wajen kasarnan yana tun wani zuwansa bauchi da yayi yake fadawa Abba xai fita waje karo karatu zai Dan jima bai dawo amma da ya dawo zai tura iyayensa ayi maganan aure Abba ya amsa da tho da zai tafi na sha kuka sosai sabida a Dan kankanin lokacinana har munsaba sosai hk ina gani ya tafi”
.
“Tunda ya tafi yakan kira abba su gaisa wani lokaci abani wani sa’in kuma yace a gaida ni har zuwa wani lokaci Dana wayi gari na gamu da labarinda ya girgizani sakamakon rasa iyayena Dana yi a wata plane crash da suka samu a hanyarsu ta zuwa Egypt wajen dangin umma tashin hakanli Ba irin Wanda ban shigaba na rasa parent dina both 2 wayyo nayi kuka har na gaji na gode wa Allah ” “Nan ta fashe da wani irin kuka mai tsuma rai”
******* *
Mum CE ta ringa lallashenta har ta samu ta tsaigaita kuka’n ” _Nima nan Munira mai dauko muku rahota na gayra zama hade ta goge hawayen fuskana Dan dauko rohoto_ lolz! “Ta ci gaba dacewa an yi xaman makoki lpy bayan sadakan 7 iyayen umma sun so tfy dani amma atapir Baffa ya hana HK ina ji ina gani suka tfy kasar Cairo” “Bayan tfy’n su kowa ya watse su Baffa suka dawo gidan mu da zama nan fa na soma fuskantar mawuyacin rayuwa Dan ko kadan Baffa,matarsa dakuma yarsu Nana basa ragamun” “Ga maganan mkrnt shiru nayi j.s.c.e amma Baffa yayi min registration na senior class na ci gaba yaki kai karshema ranann da na tunkaresa da maganan cigaban skul ya balbaleni da bala’i Ba iyaka kai karshe kam harda duka” “Amma ita Nana tana zuwa nata skul’din a LYS dake garin bauchi while ni da dukiyan ubana kememe an hanani xuwa mkrnt ” “A hk nayi missing skul kusan term daya basu da niyan sani nan nasake tunka rar su amma wanann karon Ba tsoro Baffa ya CE aure xai min tashin hankali” “Ba irin tashin hankalin da ban shigaba gashi Ba ya Salman *mai sona* (littafin rafi’at) tabbas nan nasan nayi babban rashi ga na iyaye ga rashin uwa uba Ba Salman shi da nake ganin shi zai iya tsamoni daga wanann kangin wuyan bani da ko lamban sa dama can a wayan Abba muke waya tunda ya tafi” “Wasa gaske magana ya kankama kan lalle aure za su min gashi duk wani kasuwancin Abba ya dawo hannun Baffa abinda yafi takaici ma ganiin kusan sa’an Abba zasu auramin at 15yrs old na aure miji mai kusan 50yrs ” “Nan da nan fa hnkl na ya tashi Bana iya cin koda abincin kirki ga wani uban rama Dana yi duk na lallace ga yawan tunani iri2 kullum addua’ata bai wuci Allah yadawo da ya salman Ba amma shiru shiru bai dawo Ba” “An sa ranar biki wata daya har ya kawo ana saura kwana hudu daurin aure nan fah na soma tunanin gudo wa daga gidan hkn yasa watarana ana jibi daurin aure mijin da zasu auranmun ya zo dazai tafi yaban makudan kudi nan nayanke shawaran guduwa a Daren'” “A Daren na sulale na bar gidan asuba ta gari yasameni a Tasha’n bauchi da gari yayi haske na sami motan da xai zo abuja na shiga nan muka daga sai birnin tarayya'” “Tun ina cikin motan nake tunanin inda za ni gashi ban san ko inaba can na tuna Ashe ina tafiya da foton ya salman na kudiri niyyan pic’n zan ta nunawa ko Allah xai samesa ” ” tafiya mukayi mai Dan tsawo muka isa nan muka sauka tundaga tashan na fara nuna photon amma Ba Wanda ya sansa wasuma kallon mahauciya suke mun hk na yi ta tafiya duk Wanda na gamu da shi a hanya sai na nuna masa photon amma amsa daya yane shine *bamusan saba* ina cikin tafiyan na gaji ga yunwa na addabana na soma jin jiri ga idanuwana na ganin dishe dishe na xo tsallaka kwalta ban Ankara Ba naji an bugeni daga nan kuma mai ya faru daniba sai farkawana da ganina a gadon asibiti har kawo yanxu kenan” “Nan tayi ajiyan zuciya tace wanann shine takaitaccen labarina” “Kowa na parlorn yayi shiru suna masu jinjina wa lamarin duk sunji tausayin *Muskan* Dad ne ya yanke shirun da cewa” ” MUSKAN munji labarin ki kuma mun gamsu Dari visa Dari ni nan ya nuna kansa zan zame miki uba ya nuna Mum ita kuma ki dauke ta matsayin uwa wadannan kuma yana referring da su humy da fareeda kuma sisters naki dan yanxu we are family mun zama zuri’a daya hk kuma *JINI DAYA* {liitafin Aneelurv} daga yau ki daukeni just as ur father kinji” “Dan murna kasa magana tayi sai kukan farinciki take Ashe akoi sauran irin bayin Allah’n a duniya lalle waennan *sun min hallaci* {book na eshart tsefe} Dad neh ya tasamota da duniyan tunanin da cewa:'” “Karki damu ai yiwa Kaine sannan Abu na gaba insha Allah sai na cikawa abban ki burinsa na ganin kin auri Salman duk inda yake zan nemo sa da yardanAllah yana kai wa nan ya umarcesu da wuce daki MUSKAN ta huta” “Suna barin wajen ya juya da kallon ga Mum yace:” “Ina fatan hkn ya miki daidai?” “Mum tace tabbas ya min ai duk abinda Ka yanke ya min kuma ni gsky ina jin son yarinyar nan a raina” “Dad yace nima dai haka fatan mudai Allah ya bamu ikon kula da tarbiyanta da sauke nawin kanmu ” “Mum tace Ameen”
.
A daki na hango su humaira tare da Muskan , fareeda CE tace: “Muskan ki Saki jiki damu mun yan uwan ki neh ki dauke mu matsayin sisters dinki kuma Allah ma ya ji ya gani mu muna sonki yan zu sonki yafara bin *JININ JIKINMU* kuma bazamu daina sonki Ba daidai da rana daya” “Kasa furta komai Muskan tayi ita dai tana son mutanan har cikin *Jinin jikinta* kuma ta dau alkawarin zama da kyauta ta musu kamar yadda zatawa mahaifanta da yan uwanta .dafata humaira tayi a kafada Sis don’t think this nothing kinji ai yiwa Kaine from today and till infinity u r part ov us! “Muskan ta ce a gaskiya kun min hallaci bansan da wani kalma zan fara gode muku Ba I had no words to thank u guys ol what I can say may Allah reward both Mum, Dad and u sisters with abundant of jannatul fiddaus” “Amen both answer d siblings” “Muskan gaskiya kina da kyau ga sunan ki irin na Indians kuma wlh kina kama da KUMUD na cikin film dinan mai suna SAHR ASMAR fadar fareeda.ko Ba tana tmbyn humaira?” “A wlh ni gaskiya harnayi wa big bro kamu inji humaira” “Gaskiya nima ina bayanki yar uwa mun wa babban yayan mu kamu irin wanga kyau ai baza mu so wani ya aure ki Ba illah big bro Dan zaku fi dacewa nasan shima he will lyk u inji fareeda” “Uhmm Muskan tace kufa wlh kun cika surutu ko kun manta nifa ina da miji Ya Salman ta lumshe idonta wlh bazakusan yadda nake jin shi a raina ba son sa yazama *Jinin jikina* his love has just been part of me a kansa na San soyayya and his my first and last love insha Allah Bana hada sonsa da wani da na miji da yardan Allah” ” tabe baki sukayi a hade suka furta su loverya manya dama hk kikayi nisa a son Salman lalle kam kin kamu dayawa.. amma kin San meh fareeda ta tmby?” “Muskan tace a’a sai kinfada” “Wlh big bro din ma Sunansa SALMAN amma mu muna kiransa da FARIS Allah u will lyk him if u meet” “Hala ma yafi naki salman din kyau humaira said winking her eyes at Muskan” “Mikewa Muskan tayi tace ni wlh kun cikamin kunne da surutu haa’a tayi exclaiming kun ga bacci zanyi ta juya musu baya tayi kwanciyanta” “Dariya suka yi duka hade da mikewa suka fice zuwa wajen Mum” “Sun sami Mum a parlour suka yi tamata zuba kan muskan they love ,lyk her and so on.. _Evening_ _3:30pm_ ••••• Fareeda nagani kusa da muskan dake bacci a hankali kamar mai rada take radamata ta tashi lokacin sallah yayi” “Bude ido tayi marai raice fuska kamar mai shirin kuka ita a dole an tasheta bacci hk ta lallaba ta shiga toilet tayi alwala ta fito hade da gabatar da sallah” “Tana idarwa tayi addu’a duk fareeda na kallonta tace kizo muje Mum na kiranki” “Tho tace hade da mikewa” “Fareeda na gaba itakuma tana biye da ita suka iske Mum a parlour bayan sun zauna ” “Mum tace sai yanzu kika tashi _daughter_ ask Mum??” *taji dadi yadda Mum takirata da _daughter_ tace ehh Mum ita ma takira da Mum kamar yadda taji su fary na kiranta da shi” “She feel happy too yadda ta kira ta _Mum_ nan tace fareeda ta hada abinci ta kawo mata” “Minti kadan ta hada ta kawo Mum taja muskan kusa da ita tayi feeding dinta tun tana jin kunya har ta cire..dama hk Mum take da son yara gashi Allah yabata muskan, su fareeda ma halinta Dana Dad sukayi wajen son mutane shiyasa lokaci daya suka muskan ” _wannan kenan_ “A haka su Ka raba yinin rana suna nuna kulawarsu ga muskan har dare” “Koda dad zai dawo sai da yasayamata kayan kodayi kamar su chocolate da ice cream ya kawo mata” “Sun sha hira sun har dare amma ita muskan dake Ba mai surutu va eh /a’a kawai take binsu da shi” “Nan suka yi ta fama har barawon bacci ya kwashe su”
******
“` One week later“` A yanxu MUSKAN ta warware tazama yar gida kuma jiki alhamdulillah ta ji sauki a sati daya data zauna dasu Mum har sun saba dasu coz a yanxu sunanan kamar iyayenta barin ma su farida data maidasu kamar sisters dinta” “Mum, Dad da duka yan gidan na kyauta tamata suna korarmata da tunani suna kuma kokarin faranta mata” _wannan kenan_ A hankali take sauka kan stairs’din tana takawa wane kamar mai jin tausayinsa Ba wata make up vane tayi applying a face dintaba amma she’s looking cute and sweet” “Farace amma va Sol ba! Tana da manyan idanu wanda zamu iya Kira _sexy eyes_ ga dogon hanci kamar Biro da Dan mitsitsin bakinta Wanda colour dinsa _pink_ shape dinta ya bayyana kasancewar _gown_ ce a jikinta takasance meh shape din _coca cola_ ce kirjinta a cike suke dukiyar fulanin nan suntsaya kamar wani dasasu akayi duka da dai wannan matshiyar ba babba bace amma hakan bai hana gano halittarta ba kai masu karatu karshe ce ita inatsaya bayyana muku suffofinta sai kuce karyana cox ta kure tunanin mai karatu _she damn beauty and fresh_ ” _amma ni munie haryan zu kaina a daure yake Dan ban gane wannan matashiyarba buh she look familiar hmm muje zuwa ma ji wacece_ “Takarasa falon kenan ta fada jikin Mum tace; “Wassshh” Mum wlh am hungry tana rike da cikinta alamar she’s Hungry “MUSKAN” Mum tace” “`totally speechless na saki baki, hanci kai har kunne ina kallon wacce akakira da MUSKAN Dan da farko ban an ganetaba sai yanxu da akakira sunanta“` “`toh fa masu karatu kunga yadda muskan ta canza nasan zakuso ganinta lolz“` “Na’aam Mum ta amsata” “Baki son cin abinci na lura dake zaman da mukayi na one week dinan sai kici kadan kice kinkoshi saikuma kayan kolama.. ko ask mum?” “A’a wlh Mum kawai ni fa ban yawaita cin abinciba tun asalina a cewar MUSKAN” “Mum tace toh naji nidai tashi kije kici abinci dubeki kamar wata Wanda za’a hureta maza tashi mum ta fada” “Tashi tayi tana daria Mum bata da dama takarasa dinning table” “Kujera ta ja tazauna nan ta bude kololin taga dai _fried rice_ ne ciki ga _peppe cikcen da coslo_ a wormers din kdan ta diba a plate ta ringa tsakura hk har ta kammala tanufi falon wajen Mum” “Harkin ci abinci” “A naci” Takarasa wajen Mum ta kwanata a ciyanta” “Mum kaina kaikayi tana fada tana tsotsawa” “Sannu Kawa na kaika ya miki nan Mum ta soma kaikayamata suna cikin hk fareeda da humaira suka shigo” “Assalamu alaikum”fadar su fareeda “Wa’alikum salam”su Mum suka amsa “Suna karasawa duk suka xube a kan _sofa_ dake falon suna maida numfashi alamar sun gaji nan idansu ya gane musu MUSKAN dake lafe ciyan Mum fareeda tace; “Kefa katuwar banza ce fa jibi yadda kika wani yin shabe shabe da kee kamar wata yar 2yrs” “Turo Dan karamin bakinta tayi tace Mum kin gansu ko” “Barsu karki kulasu daughter ai haushi suke ji karki kulasu Ku kuma kutashi kutafi tunda abin naku tsokanane oya tace da su” “Toh su Mum an yaye mu yanxu sai daughter inji humaira” Komeneh kutafi kuba mutane waje Mum said” “Tabe baki sukayi suka haura sama abinsu” °°°°°°°° _30 mins later_ “Fareeda CE ta sauko cikin shirin atampa super lemon green mai ratsin flower orange tace Mum zan fita” “Inazaki ask Mum” “Zanje gidansu Marian ne zamu rabon iv’nta ” “Ok a dawo lpy” “MUSKAN ce ta sauko daga cinyan Mum tace big Sis zan biki” “Toh yi sauri kidauko mayafinki” “Da gudu ta haura sama batafi 1mins Ba ta dawo” “Nan suka fita bayan sunma Mum sallama” “Mintuna kadan ya kaisu gidansu mariam bayan sun kwashi gaisuwa suka fita rabon IV” ‘Sai yamma lis suka dawo gida bayan sun idar da sallah’n both magrib da isha suka Dan taba hira kadan suka kwanta bacci kasan cewar sun gaji”…..
*
“`
_washegari_ Yau ya kasance _weekend_ sabida hk basu tashi da wuriba sai wajajen 10:00 suka tashi nan sukayi wanka suka shirya cikin English wears dukansu shirt da pencil jeans neh amma shirt din ya sauko har gwiwa nan suka sauko parlour don break fast” “A dinning suka baje kasancewar Halyma mai aikinsu ta shiryamusu break nan suka yi serving Kansu suka soma ci.. Suna kan ci Mum da Dad suka sauko cikin nasu shirin suma dinning suka nufa wajen daughters dinsu suka ja kujera suka zauna.. “Morning Mum and Dad both of them said” ” Morning my precious daughters both Mum and Dad reply”asking hope all is wel” “Yeah Dad ol is fyn..koba fareeda tafada ta na mai kallon yan uwanta” “Eh komai is well fadan Muskan da humaira..nan suka cigaba da cin abincinsu ciikin nutsuwwa da kwanciyar hankali” Suna kammala wa suka shirya fita yawon shakatawa zuwa Amesium park da sauran wajajen shakatawa.. Haka suka kammala weekend dinsu cikin nishadi Dad ya kaisu wajaje dama yakaisu har sahad da sauran plaza’s ya musu sayayya.. Ciki har makaranta da Dad zai sa MUSKAN sun je yimata interview.. A halin yanzu an ma MUSKAN registration a mkrntar su humaira zata fara zuwa ranar _Monday_ anmata interview ta cinyesu duka kasancewar ita din mai kokari ce shiyasa bata wani shan wuya wajen amsa tambayoyin da aka tambayeta ba aka bata class SS1A duk da suna second term Dad yaji dadi korai da gaske dama shi fatanshi tasamu ta daura daga inda ta tsaya vai yi mamakiba Dan a labarinta yasan iyayenta masu haline tho yasan tayi makaranta mai kyau.. ————– _Monday morning_ _6:30am_ Duk sun shirya cikin uniform dinsu mai karamin skirt _mini skirt_ mai design na Burberry sai _suit blue_ shine a mazaunin kayan su da _baret_ shima _blue_ sun sa _legis_ a kasan skirt nasu sunyi kyau abinsu humaira kenan da MUSKAN” “Itakuma fareeda sai 10:00takeda lectures” “Saukowa sukayi suka hau yin breakfast basu dau lokaciba suka kammala suna shirin fita falon Dad ya sauko ya musu addua’ar Allah ya tsare hade da Jan kunne kan su maida hankali kan karatu banda wasa da kuma frndship da maza duk wacce tayi haka har yaji toh zatagamu da fushinsa yabasu 1-1k na break ya musu Allah kare suka fita zuwa mota driver ya ja sai skul.. _7:30am at school_ Sun iso driver ya saukesu suka Shiga cikin mkrnt” “Mkrnt ne na yayan masu shi sabida hk kowa harkan gabansa ya ke Dan duk sunaji da arzikin iyayensu bamai shiga sabgar wani” “Anyi duk wasu Abu daya kamata kamar su Assembly da sauransu nan aka watse zuwa class humaira da kanta ta raka MUSKAN nasu class din ta tafi nata” _back to class_ Wata yarinya da zatayi saukin Kai ta zo wajen MUSKAN tace “Hey my name is Ameena Abba Mahmud” “Am MUSKAN isma’il Aliyu” “Nice to meet u” “Nice to meet u too ” “Have a seat ta nunamata gefen nata seat’din suna zama techern physics ya shiga nan ya soma ggudanar da class cikin nutsuwa sosai yan ajin sun maida hankali sai da yagama class Tass sannan ya ce: “Hope every body understand” “Yes suka answer shi” “Gud”yayi exclaiming! so who can drive the three equation of motion?ask.. “Tsitt suka yi shiru” “Muskance ta daga hannu alamar zata amsa” “Yes young Lady stand up said d teacher” Tashi tayi a nutse ta amsa tambaya cikin muryanta mai dadin sauraro ga Kuma turancinta mai kyau” Clap for her inji teacher’n “Tap tap tap class din ya dau tafi ta burge kowa a class din” “Ahaka dai suka yini ranar wannan malamin ya shiga wancan ya fita har aka tashi” “Muskan taji dadin skul din ga kuma new Frnd dinta meena koda suka je gida tayi ta Ba Mum hiran skul murmusshi kawai Mum keyi tana binta da eh/a’a MUSKAN kenan yarinya kyakyyawa da nutsu ga kokari da hazaka..
*Two weeks later*
After two weeks*
A yanxu MUSKAN tada gogewa Dan a kalla tanada *one month* da zama wajen su Mum, makaranta kam ba’a magan Dan tsab ta maidaa hankali sosai kan abinda ya kaita bata kula kawaye illah meena da wata kubrah sune kawayenta friendship da maxa kam batamayi Sam bata ganin maza da gashi a Kansu,teachers dinsu kam kowa naji da ita Dan kokari yanxu hk ma itace _class rape_ dinsu..
Dad da Mum na matukar jin dadin halayyarta da kuma kokarinta a mkrnt suna kuma kokarin kyautatamata suna mutuwan sonta kamar `yar cikinsu.
MUSKAN bata da wata damuwa a yanxu illah kewar masoyina abin sonta muradinta bugun zuciyarta YA SALMAN dinta burinta da addu’ar ta a kullum bai wuci Allah ya nunamata Shiva Dan hk nema she make a Vow not to love any guy apart from him tace;
.
“Zuciyata, gangan jikana, ruhina,soyayyata duk naka ne YA SALMAN sonka na *jinin jikina* Allah ya nunamin kai masoyina Amen.. Fadanta kenan kullum da addu’arta.
_____
★★★
_2:00pm_
A vakin gate na school na hango MUSKAN ,meena da kubrah tsaye ga dukkan alamu an tashi ne Dan ga `yan skul’din a waje kowa na jiran azo daukarsa suna hira ransu meena tace
“MUSKAN wai yaushe zakije gidan mune”
“Uhm karki damu kawalli insha Allah a weekend zan xo inji MUSKAN”
“Kedai hka kike Allah yasa da gaskene ku6rah tace”
“Ameen insha Allah da gaskene in Allah yayarda MUSKAN ta vata amsa daidai nan motocin su suka iso zuwa daukansu suka wa juna bye-bye kowa ya Shiga nasu suka kama hanyan gida”
“Tafi sukayi mai Dan nisa tukun suka isa gida”
“Driver yayi parking a _parking lot_ sa’annan suka fita zuwa cikin gidan”
“Da sallama suka shiga parlourn”
.
” Mum ce dawata Mata wacce baza ta haura shekara 40yrs tana da kyau Ba laifi gefenta kuma wata budurwace wacce itama da gani she would’nt past 25yrs amma kana ganin wanga 6udurwan zaka San yar boko ce kuma tasan duniya Dan wata arniyar armless ce a jikinta da wata karamar boyfriend jacket sai dankaramin gele da tayi rolling da shi ta toshe face da sunglasses kafa daya kan daya kamar Ba iyayenta ne va a zaune wajen MUSKAN ce takare mata kallo hade da tabe baki tace wannan dagani za’a yi `yar rainin sense hmmm., amsa sallamar da su Mum sukayi neh ya dawo daita hankalinta Mum tace;
“Harkun dawo daughters”
“Ehh Mum suka amsata a taikaice fuskan MUSKAN fal da wannan murmushinta mai. Sanyi hade da gaidata da bakinta, matar kadai ta amsa banda wancan 6udurwan”
“Faty wai 6akiji ana gaida ke bane? matar tacewa 6udurwanda ke zaune”
“Um.um naji sannunku ta amsa a yatsine”
“Basu bi ta kanta Ba suka tashi suka haura sama abinsu”
.
“Matar tajuya da kallonta wajen Mum tace hajiya ina kika samo wannan kyakyyawar yarinya ga fara’a da murmushi matar ta tamvaya”
“Mum tace `yata ce ta amsata a takaice”
“Tace kai Masha Allah”
“Faty da tunda aka fara zance take ta tabe baki, ita wannan yarinyar bata mataba sau wani murmushi kamra wacce aka wa kyuatan aljannah kuma hk kawai tunda ta kalli yarinyar ta tsaneta”
“MUSKAN itama suna shiga daki ta yi wulli da bags nata tace humaira kinsan meh kuwa ta fada”
“A’a sai kin fada”
“MUSKAN tace wlh ni wannan yarinyar damuka baro a parlor yar rainin sense ce kifa ga abinda tayi muna gaidata amma tawani dauke kai tana babbatsewa mtssww ni nama tsaneta ma wlh..
.
“Humaira tace indai wancan neh hk take yar abokin Dad ne muma nan bama sonta sai wani ji da kai ta dauko wani girman kai ta daurawa kanta ko kadan batayi halin mum nata da Dad dintaba, kuma kinsan wani abin haushi wai fa ahakan tana son big bro”
“Amma shifa ko kulata bayayi infact shima ya tsaneta ko hanya baya so ya hadasu balle suyi exchanging words”
“Hmm lallekam Allah ya shirya shi wlh bata haduba tunda ita take kai kanta wa namiji da sunan “SO” mtswww I hate her ta fada hade da mikewa fada toilet abinta..
.
_toh masu karatu kunji fa faty tace ta tsani MUSKAN, hk itama tace ta tasani faty.. Nidai Munie nace wannan akoi wata babban al’amari kenan amma 6oyayyiya ce Wanda ni kaina mai dauko rahoto bansani Ba but keep in touch zakuji sannu a hamkali_
.
Wanka sukayi suka daura alwala bayan sun idar da sallan suka shafa mansu hade da applying _light makeup_ kaya iri daya suka sa sunyi kyau sai kace _yan tagwaye_ coz humaira Nada kyau itama baza a barta abayaba .
“Kai Sis kinganki kuwa humaira tafadawa MUSKAN”
“LA ke baki ga kankiba sai ni Allah kinfi kyau nasani fadar MUSKAN cikin zolaya”
“Tab wane ni ai ko makahone ya lalima yasan ke ta karshene humaira tafada itama cikin cigan wasa”
“Bugu MUSKAN ta kaimata irin na wasa tace ke dalla munyi kyau dukka we are looking gorgeous both taja hannunta suka fita parlour Dan cin abinci”
“A hankali suke taka stairs din had suka doso parlour’n sai killer smile dinnan na MUSKAN take tayi har suka isa gun Mum”
“Harkun shirya daughters”
“Eh Mum”
“Kunyi kyau kuje kuci abinci kuzo na aikeku”
“Tho suka ce hade da wucewa dinning”
Faty da tunda suka sauko take karewa MUSKAN kallo yadd takeda kyau ga komai da ake son ganin mace dashi ta Tara tace a zuciya hmmm lalle yarinyar nan tanada kyau she has anything da akaso tanata tunanin nan a zuciya wata bangaren zuciyanta kuma yace toh ina ruwanki da kyaunta ai kema kinada kyau, why meyesa wai na damu da yarinyar nan ne kuma meyesa na tasaneta for the first tym seeing her, haka tayita tunani ganin batada amsan tambayan yasa taja tsaki mtsssww Wanda bata San yafito fili Ba’
.
Mamarta ne tace faty lpynki kike tsaki??
“Bata fuska tayi tace Ba komai Mummy”
‘Allah yasa fadar mummyn ta”
Ameen ta amsa a yatsine”
Su MUSKAN sunci abinci suka zo karban aikan da Mum zata musu , tabasu aikan dama kudi zasu kai gidan wata kawar Mum nan suka karba suka fice abinsu hade dayiwa mummy’n faty sallama basu bi takan faty va suka fice'”
Suna fita 6asu dad’e 6a su faty sukama Mum sallama suma suka tafi”
Fareeda ta dawo ta tarar da Mum kadai 6asu MUSKAN take tambayansu Mum tace ta aikesu, tace faty da mummyn ta sun zo suna gaida ke”.
Tace Ina amsawa gomma da Allah yasa bana gida dan ban son abinda zai hadani da yar rainin sense dinnan “
Allah ya shiyeku yanxu kude bakusan faty ko kadan Cesar Mum”
Hmm Mum bazakisan wannan yarinyarbane wlh bata kamun kai Sam ga wani uban girman kai da take dauke da shi”
Yar banza naji tashi ki 6arnnan ta kai hannun zata 6ugeta,da sauri ta tashi da gudu ta haura sama tana dariya”
Mum ma dariyan take tace yara duk kunbi kun rainani kun daukeni kamar abin wasan Ku zamu hadu ai”
_Mum kenan haka take da daughter’s dinta abin sha’awa in Ka gansu_
________
_8:30pm_
Da daddare duk suna zaune a parlor suna hira sun gama cin abinci kenan”
Wayan Dad ne ya soma kuka yana Neman agaji ,Dad ya leka ya”SON” rubuce kan screen din, yakai hannu ya dauka hade da cewa”
“Hello son”
“Na’am Dad ina yini”
“Lpy qalau yasu mum da sisters”
“Lpy yansu gasunan duka muna ma tare,ya mikawa Mum”
Amsa tayi suka Shiga gaisawa take tam6anyan sa yaushe zai dawo”.
Yace Mum nima ina son dawowa sabida ina missing gida amma aiki yamin yawa yanxu a hakama Bana London sun turani wani aiki can Cyprus kusan na 6-7 month shiyasama ban sami zuwaba wancan karon danace zan zo”
Ayyah Allah ya karemun kai son amma ni dai kayi kokari gana gama wancan months da suka debarma kadawo kayi aure Dan am eager naga jikokina suna zagaye dani ina jin kiri niyansu”
Insha Allah Mum ina dawo wa zanyi aure kuma yar Nigeria zan Aura Kuma nasan zaki sota”
Yawwa allah ya maka albarka”
Ameen Mum I love you”
“I love u too son take care”
Nan aka Bawa su fareeda suka gaisa kowa yata xuba mai shirme banda MUSKAN da tunda ta karbi wayan suna gaisawa take jin kamar tasan muryan kuma tana feeling something inside her game da voice dinsa ga husky voice dinsa mai dadin sauraro”
.
Haka shima bangarensa kullum idan sunyi waya aka baiwa MUSKAN yakanji kamar yasan muryan kuma shima yana feeling something about her gashi shi ko sunanta bai saniba and 6ai ta6a ganin koda pics dinta Ba koma dai menene shikam he lyks her sweet voice”
HK ranar kowanne su ya kwana da tunanin Dan uwansa har barawon barci ya daukesu””
.
____________
______
*It has been Long time now almost one year and half*
_Bayan shekara daya da rabi_
Ayanxu kam komai yana tafiya daidai su MUSKAN har angama SS1 suna SS2 second term a yanxu HK Dad ya yanke shawaran zai hada MUSKAN da humaira su zana Waec /neco tunda itama MUSKAN tanda da kokari hartafi wasu dasuke SS3 kai harda wasu na higher institution”yasamo musu malamin lesson gana Arabic duk ana musu sosai MUSKAN ta maida hankali Dan burinta a rayuwa bai wuci tazama Doctor Ba shiyasa bata wasa da karatu ko kadan”
“Gashi sai Dada girma take kamaninta ya Dada bayyana haka suffofinta tazama budurwa Mum naji da ita Dan tana wa danta kodayin hada jini da ita, gata shiru shiru abinta Ba ruwanta bata cika surutu Ba Abu kadan Ka mata sai murmushi batada saurin fushi shiyasa yan gidan ke jin dadin zama da ita”
Yanxu kam ta karatu suke basa wasa, ahalin yanxu kam har ta saba da bro FARIS (big bro) yayan su fareeda SALMAN wanda suke kira da FARIS shima haka ya saba da ita sai ya na wasa da ita kamar sauran sisters diinsa sai dai har yanxu basu taba ganin photon juna Ba amma ya San sunta MUSKAN sai dai shi zuciyarsa bata yardar masa kan MUSKAN’dinsa bane a gidansu amma what he no yana sake sonta Dan sunan MUSKAN’dinsa data ke dauke dashi, yanxu burinsa ya dawo yaje yaga _baby boo_ dinsa Wanda a kalla yanxu yakai _2yrs_ rabonsa da jin sweet voice dinta kullum yana cikin watching na pics dinta”
.
Itama bangarenta the same think takeyi kullum cikin kallon pics dinsa take ,akoi ranar da fareeda ta kamata tana kallo tayi tayi da ita kan ta ga pic din ammma MUSKAN ta hana haka ta hakura ta kyaleta amma ta dau alwashin sai ta ga pic dinnan ko da yaushe”
_one week later_
Su MUSKAN anfara Waec kullum yanzu a cikin karatu suke basu da lokacin Kansu they are busy always”
Yau sunyi paper na hudu Wanda ya kasance mathematics sun gaji sai kusan 3:00pm suka dawo gida”
“A gajiye suka shiga falon suka Tatar da Mum na waya da alama kuma tana murna Dan yadda take wayan zakaga farin ciki fal kwance a fuskanta, kallonta suka tsaya yi har ta gama wayan”
Kamar hada baki sukayi wajen fadan”what a happy face Mum”
Smiling tayi tace your brother will be arriving in two days”
Yeah suka hay murna da rawa bro will be home we r very happy”
Da murna suka haura sama”
Yau dai haka yan gidan suka yini murna suka kwna murna”.. .
.
_nima dai munie na tayasu murna, ina fatan fans sun tayasusuma lolz!_….
_____
_bayan kwana biyu_
A cikin wannan kwanakin yan gidanan murnan da suke baxai faduba barin shi uban gaiyan wato FARIS Ba wadda ya kaisa murna Dan shi murnansa na yadawo yaga _Baby Boo_ dinsa..
Yau ta kasance laraba _Wednesday_ kuma yau suke sa ran FARIS zai dawo, kuma jirgin su zaiyi _landing 2:00 sharp_ sabida hk tunda suka tashi sallan asuba basu komaba sai faman gayra gayre ake da soyesoye Ba abinda kake ji a gidan sai kamshin _aromas_ dake tashi MUSKAN ce tayi hanyan kitchen a ciki ta tarar da Mum dasu fareeda suna ta faman girki da sallama tashiga suka amsata Mum tace”
“Kin gama gyran dakin son din”
Ehh na gama Mum”
.
“Da kyau toh zo ki hada kunun ayan nan”
“Nan taje tasoma hadawa ksancewar ta Kware sosai fannin girki da hada local juice tana cikin yi take jin faduwar gaba da bugun zuciya kuma ita ta rasa dalili”
Mum CE ta lura da yadda tayi sako sako da ita kamar wacce bata jin dadi tace MUSKAN lpy’r ki kuwa?ta tambaya”
“Ehh Mum lpy kawai dai yau tunda na tashi nake jin faduwar gaba ga zuciyata na bugawa da sauri sauri inajin kamar akoi abinda zai faru dani ne”
Allah ya sawwake ki yawaita karanta “HASSBUNALLHI WANI’IMAL WAKIL” zai rage faduwar gaban kinji”
“Toh Mum na gode” nan taci gava da aikinta tana maimaita addu’ar har ta Dan sami sasaucin faduwar gaban”
Sunyita aiki har saida suka hada komai sukayi breakfast suka ci gaba da girki sai kusan 12:20 suka kammala komai suka hada a dinning table”
” sun dafa fried rice, sunyi cusslo,da peppe chicken, tuwon shinkafa da miyan danyar kubewa, ga peppesoup na kayan ciki daya sha kayan kamshi, kunun aya juice,da coconut juice, sai sauran abinda baza a rasaba”
Sunadaga daki 1:20 duk sunyi wanka sun idar da sallah Saura make up, kowa sai faman Dan wannan a fuska shafa wancan lakuci wannan tsakanin fareeda da humaira banda MUSKAN dake zaune tana ta kallonsu sai murmusawa take har suka gama, fareeda tace wlh yau ko danneki sainayi namiki make-up ke kullum sai kishafa powder da lipstick sai Dan kolli kice kingama make-up c’mmon kizo namiki make-up hala yayana yaganki ya kyasa tana jinta har ta gama tace sai kiyi ai ta nufi hanyan wardrobe Dan dauko kayanta, fareeda tajata baya hade da zaunar da ita gaban mirror nan suka soma kokawa ita MUSKAN sam bazatayi applying makeup Ba while fareeda tayi insisting sai tayi humaira nadaga gefe sai kallon ikon allah take hk sukayitayi daga karshe MUSKAN ta yarda ta zauna nan fareeda ta soma aiki sai da ta fitar da ita Tass da makeup kuma tayi wani uban kyau gashi dama tuncan tana da kyau gata jinin larabawa habawa nan suka isheta da surutu kan tayi kyau ita kanta da taga mirror tasan tayi Ba karya kuma tun can hausawa sunce *inkana da kyau*(Littafin AneeLurv) *toh kakara da wanka* wata arniyan _swiss less_ ce _black colour mai ratsin red_ suka sa dukansu dinki dogon _Riga na Dubai they All look beautiful , nan suka sauko suka tarar da su Mum itama irin shigarsu ce a jikinta bambamcin colour ne ita nata _Orange colour ratsin flowers green_ Dad kuma wata dakakeyar shadda ce fara wow! Family’n sunyi kyau sOsai Nan suka fita zuwa parking lot mota _Benz da parado bakake suka dauka_ fareeda na Jan su while driver na Jan su Dad a Prado..
_2:00pm at airport_
.
Daidai time dinnan suka isa airport kuma lokacin jirgi yake sauka, in Ka dubi fuskokin family’s din zakaga tsantsan farincki a tattare dasu MUSKAN ma na daya daga cikinsu sai dai ita faduwar gaba da bugun xuciyarta ya tsannanta GIB! GIB!!GIB!!! Zuciyarta ke harbawa da sauri2….
_____
Zuciyarta vai tsananta 6ugawa6a sai lokacinda jirgin ya sauka,har fareeda ta lura da yadda tayi suko2 da ita ta tam6ayeta amma tace 6a komai just her hrt beat fast and fast, duk idon su na akan jirgin ganin mutane sun fara fita kowa so yake shi/ita ,ya/ta fara ganin SALMAN FARIS 6anda MUSKAN data kasa samun natsuwa she feel something strange gonna happen, kamar hadda baki dukka sukayi in a sound voice suka ce YA FARIS suna nuni da yatsa inda yake saukowa daga matakalan jirgin da takunsa kamar Wanda yake jin tausayin takawa, hakan yasani kallon direction din da suka nuna Dan ganin waye FARIS sabida in daukowa masu karatu rohoto”
_FARIS matashine Wanda 6azai wuci shekaru 30yrs 6a a haihuwa, ma’abocin kyau da murmushi,farine amma Ba sosaiba(chocolate colour) kana ganin sa zakasan fulanine na usul, skin dinsa mai shinning, suman kansa kuma acike take irin na larabawa yana son Tara gashi 6aya haski sam saidai ya taje yashafa mai da perfumes masu kamshi sai su kwanta suyi luff dasu koya musu style, fuskansa duk saje ne suka mamaye sun sha gyra da gyemun kadan irin Wanda larabawa ke 6ari, yana dogon hancii,hade da middle eyes waenda ba kanana ba kuma ba manya ga wasu uban eyelashes kamar mace koda yaushe a lumshe idon suke hakan yasa ake masa lakabi da (mai idon bacci) yana kuma da baki Dan madaidai ci (middle mouth) waenda lips din suka kasance jajaye (red) ta fannin body kuma yanada faffadan kirji hade da parks (sparks) kamar na Justin bieber kasancewar yana daga jiff muscles dinsa a murde suke masu daukan hankali,sai zararan yatsun sa both kafa da hannu hmmm reders SALMAN FARIS na karshe ne ya hadu ya kai namiji iya namiji nasan wasu suna so su gansa lolz! Baza Ku gansa Ba toh kallan kufara fada ko wacce tace tana sonsa..ni na Riga Ku toh_
Wannan kenan!
.
Sanye yake cikin uniform na pilot farare kal da su sai sheki suke sun matukar amsan skin dinsa sai gwala ido yake Dan hango family’s dinsa fuskan sa dauke da murmushi take ya hango su suma suna gwala ido suke yana murmushi yana nufansu suma maida mishi murmushin suke kowa so yake shi yazama first na hugging dinsa banda MUSKAN datayi mutuwar tsaye tana kallon mai dosowa wajen kamar tasan fuskan take gani bata gaskata magartaba sai da yazo dab da su, Dad ya ware hannayensa xaiyi hugging dinsa kamar ance ya juya ya kalli gefe ita ma hk kamar ance ta daga kanta, ai ko tana dagawa yana juyawa karapp idanunsu ya hade they couldn’t believe such a dream they just start to exclaimed totally speechless “
“Bab- ba- baby boo saying FARIS murmuring”
“Ya salman ita ma tafada muryanta na rawa”
“No-no-no am just dreaming this couldn’t happen this not my baby boo she could b here I couldn’t believe such an idiot dream Marin kansa yasomayi inma yana mafarkine ya farka ganin bashi da amsa yasa shi”
” matsowa dap da ita yayinda suna iya jiyo numfashin juna hannunsa ya kai ya shafi fuskan ta yana kallon idonta itama idonsa take gani buh she couldn’t stand watching him into eyes hakan yasa ta saurin sauke idonta hakan da tayi ya tabbatar masa MUSKAN dinsa ce hugging dinta yayi tsam a jukinsa shaf ya manta da su Dad a wajen yasoma surutu”
.
“Baby boo so u r d one how possible will U b here at airport u miss me huh! I guess so I miss u too all does years I did missing and loving my baby gurl I love u so much, ita dai MUSKAN kokarin kwatan kanta take dan tasan su Mum na nan amma shi shafff ya manta dasu”
Suma dai sai kallon ikon Allah suke yadda son ya manta sunanan he’s blindly in love ya manta da su”
_wannan shi ake kira da kallo ya koma sama_
“Kamar mai rada ta rada da masa a kunne ya salman stop this mum, Dad and ur siblings are here and can’t u see we are at airport all eyes on us”
Hakn data fada yasasa saurin sakinta shi kam manta shafff da su Mum awajen kunyace ta kamasa ganin he did something crazyly ya soma tsotsa keya Kansa a kasa yana jin kunya, itama hk kanta na a kasa shi yayi karfin hali ya Dad, Mum em-em”
“Shiitt Dad ya daura yatsansa a lips nasa we don’t owe u an explanation u have already explain nothing more let b riding home yana magana fuskansa dauke da farincki, mum ma hk nata face din, _farinciki biyu ne a fuskan gana dawowan son, gana samun surkuwa da sukayi_
“Mota suka Shiga dukkansu 4 a Benz FARIS na jansu MUSKAN na gefensa while su fareeda na baya, bakinsu ya mutu sun kasa magana ganin big bro a lo6e yana driving ma yana kallon Baby Boo dinsa, tabe baki sukayi suka hada baki wajen fadin “su lo6ayya manya”
“Ku kuka sani fadar FARIS”
“MUSKAN kam shiru tayi duk ita kunya takeji kuma tasan yau km nata ya kare wajen su fareeda”lolz!
_finally inataya MUSKAN da FARIS haduwa da juna_
__________
______
Tafiya sukayi kusan na 30-40mins suka isa gida, a parking lot yatsaya bayan yayi parking duk suka fita suka dunguma zuwa cikin gida a parlour suka tare shi FARIS baiwani zama Ba yace bazayaje ya watsa ruwa humaira da fareeda suka bisa da trolleys dinsa daki, suna dawowa Mum da Dad sun haura Sama suma ai ko nan suka Tarawa MUSKAN duka fareeda ta kaimata a baya irin na wasan nan tace munafuka Ashe dama wanga PIC dakike boyewa na yayana ne? “
“Ehh MUSKAN tafada cike da kunyan tana sunde kai”
“Nifa kidaina wani sunde kannan Dan vaizai taimakaba mun Riga mun kamo bakin zaren fadar humaira”
“Gomma kam kifada mata ai yanxu munsan ya salman dinki shine bro FARIS, Aunty mu fareeda tace hade da kanne mata ido daya(wink) “
“Ni wlhy Bana so kubarni ko nagayawa Mum Allah”
“Ai saiki kije kifada idan bakida kunya humaira tafada hade da murkud`amata Baki()”
“Wait wait kubar surutun nan fadar fareeda tace amma ni wlhy wannan abin ya ban mamaki duk zaman da mukayi da ke muka kasa gano ki, kodashike kina boye foton saurayin naki shiyasa and kuma Ba wani pics na FARIS dakitaba gani a gidan and vamutaba mishi sending pics namu tareba kuma numbrn da nake Whatsapp dashi baiyida shiyasa bai taba ganin dp naba, amma ai kuna waya bakitaba ganeshiba be?”
“MUSKAN tace gsky so dayawa idan muna waya nakan ji kamar na San mai muryan abubuwa dayawa yakan yi sai naji kamar ya salaman dina ne amma bantava kawowa kan ya FARIS shine ya salman dina”
“Hhhhhhh yarinya yanxu dai kam munsan anhadu da masoyi naji yana wani kiranki _baby boo_ saura kisa lo6e a gaba ki manta damu hk examz aje rubutawa ana tunanin ya FARIS wlhy saina gaya Dad”
.
“Ki fadama Dad din mara kunyan yarinyar kun wani sa _baby boo_ dina a gaba kun cikata da surutu,FARIS kenan yana magana ya doso so fitan sa kenan daga part dinsa, sanye yake da wata _red shirt_ da _blue jeans trouser_ yasha ado kamar mace _he look handsome_ fuskan dauke da killer smile nasa ya nufo so”
“Sweet yafada kamar mai rowan voice dinsa waennan marasa kunyan sun cikaki da surutu ko? Ai nasan za’a Rina daga ganin yadda suke binki da kallo a airport don’t mind them kinji babyboo dina, Ku kuma wlh duk wacce tasake na sake kamata tasamin wifey a gaba tana jero mata surutu wlh munsa kafan wando daya da ita, in kunne yaji… Ya ciza red lips nasa yace kunsan mai zai biyo baya, daidai nan su Mum suka karaso”
“Dad yace son mai kakeyiwa daughters dina”
Keya yasoma tsotsawa alamar Mara gaskiya umm Ba komai kawai muna wani discotion ne”
“Kada kai kawai Dad yayi Dan yaji irin maganansu duka, yace ok toh Ku taso muje mu ci abinci, duk suka mike zuwa dinning nan fareeda ce tayi serving dinsu kowa ya zauna yana ci”
“Yummy! Dilicious Mum nasan ke kidafa ummmm yana fada yana ci, sukam kallo kawai suke binsa dashi yadda ya zage yake ta aika loma sai da yayi nakk tukun ya dau kunun aya ya bi abincin dashi sai dai kamar kunun ayan yafi abinci dadi yace, Mum what a sweet juice hk”
“Murmushi mum tayi tace yayi dadi ko, guess wacece tayi, kallon su yafara yi 1aftr d other sai da yagama kare musu kallo tsapp yayi killer smile dinsa yace I guess _Baby Boo_ ce tayi hhhhh am good at guessing? Hope nayi guessing daidai dan nasan waennan baxa su iyaba ya nuna su fareeda”
,
Mum da Dad kam sunfi kowa farinciki yadda son ke cikin farinciki kuma tunda can dama shi mai raha ne da wasa, da wasa da dariya suka gama cin abinci nan suka koma parlour”
Suna zaune Dad ya Sanar da son abinda ya faru a rayuwar MUSKAN tun rabuwarsu, har kadeta da Mum tayi da zaman ta a gidan kama izowa rana ita yau”
“Sosai ya tausayawa _baby boo_ dinsa nan yace Dad yanxu komai ya wuce tunda na dawo insha Allah zan kula da ita kamar yadda Abba ya ban amanarta tun yana Raye”
“Thats y I so much loves u son nasan u will do it Ka kula da MUSKAN just as u did to your own sisters kaji”
“Insha Allah Dad”
“Daughter zo Dad yace da MUSKAN”
“Zuwa tayi ta zauna akasa wajen kafan Dad nan ya shafi kanta yace my daughter ga FARIS ko zai kula dake kinji just obey him ,what ever he said stop u should stop dat and what ever he said u should do it just obey him and do that hope am clear, dama can nasan kina da hankali da biyayya so ki ci gaba da zama good girl kinji, Allah ya muku albarka dukka”
“Suka ce Amen”
Duk suka mike zuwa daki banda FARIS da ya fita amma badan yana so Ba kawai dan yana ganin su Dad ne amma shi in so samune ya kasance da _baby boo_ dinsa coz he miss her wit out word saying and he can’t deny it buh ai zai dawo anjima hk ya hakura ya tafi zuwa gari'”
“A takaice dai hk itama MUSKAN ta yini missing her soulmate”…
__________
_____
_*night time*_
A babban falon gidan dake kasa suka yada zango duk sun idar da sallah sun kammala cin abinci ana fira gwanin ban sha’awa tsakanin mahaipa da ya`yan su amma shi FARIS duk hankalinsa na akan _*Baby boo*_ dinsa ita ma kusan hkn ne da sun hada ido ya sake mata murmushi itama tana mayar masa duk abinda suke Mum na kula dasu basu sani Ba ita dai tafi kowa murnar wannan Abu dama tun can addu’ar ta kullum Allah yasa MUSKAN ta kasance matar FARIS ta kudiri aniyan hada su dama Ashe tana nata Allah na nasa 6atama San tunda su masoya bane murmusawa kawai take irin nasu manya, humaira ce tayi magana tace wai ni bro vazaka bamu tsarava bane tayi tambayan kamar wata mutuniyar kirki ta wani sunde kai”
“Yar rawan kai bazan vayar Ba toh ko zaki dakan nasan kin girma fadar FARIS”
“Ayyah ya FARIS pls mana fareeda tace kamar wata baby”
Karku sani ciwon kai oya je ki dauko babban trolley’n da kuka aje”
“Yeah ta fada ta tashi tana rawa tanufi dakin nasa ta ja trolley’n ,tazo ta jibgesa a gabansa ta zauna kusa dashi”
.
“Ke tashi wlhy ko na hanaki tsaraban jin haka yasa humaira mikewa da sauri ta koma gefe, nan ya bude ya Fiddo da kayanki ya soma baiwa kowa nasa, da su mum ya fara”
Wata haddadiyar _swiss les_ guda biyu ya da mayaukan shafawa dasu turare ya baiwa mum, yabaiwa Dad wata arniyar agogon _Rolex_ shima da perfumes masu tsada, albarka sukayi ta samasa da Addua’a sukayi ta masa”
Meye Kun wani tsareni da eyes FARIS ya fada cikin zolaya”
“Babu suka basa amsa”
“Hhhhhh yara dama kuce akoimana, ya cire wasu English wears Riga da wandona guda hudu2 ya mika musu dukkansu uku sai da takalma masu kyau guda biyu2 ya basu sai perfumes suma ya basu sai washe hakora suke suna zabga uban godia,wasu kwalin waya ya cire guda 3 ya baiwa kowa daya2 kallo suka tsaya yi totally speechless this is a great suprise ever iPhone7 ya saiwa kowannensu tsalle sukayi tare hugging dinsa fareeda da humaira suka hau basa Peck a cheeks thank you so much brother wayyo zamu mutu Dan dadi rawa sukafara suna kwasan kayansu Bari naje daki nasa a charge wayyo yau zan hau whatsapp da iPhone7 dadi kasheni suka haura stairs da gudu kamar yara suna ihun dadi MUSKAN kam tana nan wajen sai yanxu ta samu damar yimishi godia Addu’a sosai tamasa kuma he appreciate d prayers, hk su Dad sunji dadi cox sunsan MUSKAN da nutsuwa nan su Dad suka musu sai da safe suka haura sama zuwa nasu dakin aka bar FARIS da MUSKAN”
.
“Mikewa yayi yace _*Baby Boo*_ tayani daukan trolley ki kaimin shi daki, Ba musu ta rufe hade da daukawa duk yana kallon ta ido kawai ya xubamata har ta soma ja suka je dakin, suna shiga ya fada gado yace ahhhh kaina yaran nan kunsamin ciwon kai, sorry tace dashi bara nakwo magani fita tayi cikin 2mins ta dawo da paracetamol ta ballama tace ya FARIS ga maganin tashi yayi ya kai hannu zai karbi maganin ya hada da hannunta hade da jawota ta fada gefensa yace zauna anan ya nuna mata gefensa Ba musu ta zauna ya gama shan maganin kanta na akasa tana wasa da Zara zaran yatsunta kallonta yayi ya lumshe ido yasake budesu ya gyra murya cikin husky voice dinsa mai kashe jiki yace _*baby boo*_ tace na’am yace look at me”
“Uhmm ni bazan kalleka tafada cikin tsigar shagwaba”
“Oh no Baby boo pls look at me ,I miss does sexy eyes for all does years I spend missing them “
“Dagowa tayi tana ganinsa shima ita yake kallo yace MUSKAN a hankali kamar wani zai jiyo su”
“Yace MUSKAN ina sonki ban taba so Ba a kanki na San dadin so kuma
akanki nasan zafinta cikin shekarun da nayi Ba ke kusa Dani Bana kuma jin murayanki kona kira wayoyin Abba basa shiga hk na umma I suffer wlhy nazama kamar wani zararre every were anytime maganan baby boo kadainake u knw what abokan wajen aikina ko wani lokaci sukance kona tabu ne idan na fara kiran Baby boo Anwar kam Frnd dina dake najeriya cewa yake na haukace idan nafara maganan Baby boo I so much loves you I can’t do without u, u have already being part of me u r d Queen of my heart, my heartbeat,I don’t knw how to tell u buh wat I knw is I love u more than word can say”
“Ya FARIS nima ina sonka I love u more than I love my self bansan nima yadda xanfadamaka Ba amma kasani MUSKAN na Sonka u mean alot to her”
.
“Lumshe ido yayi tabbas Ba karya ya San yayi dacen mace Allah ya barsa da MUSKAN dinsa”
Nan suka taba Dan firansu na masoya abin burgewa sai 10:00 ya rakata daki taje bacci badan sun so rabuwaba hmmmm _*love bird kenan*_ “
Kowannensu da farinciki ya kwanata bacci”
Masu karatu nasan zakuso kusan waye SALMAN FARIS??
_*Takaittacen Labari*_
_*FARIS dai Dana wajen Alh Ahmad Salman da hjy Zainab, Alh Ahmad ya kasnce Dan garin Gombe State shida matarsa duka fulanine su na usul auren dangi akai musu dukkansu kuma yan boko ne alh Ahmad ya karanci Public adminstration ita kuma business ta karanta,auren so da kauna sukayi shekara daya da aurensu Allah ya azurtasu da cikin dansu wato FARIS ,ciki na da wata Tara ta haifi santalelen danTa ranar suna yaci sunan kakansa SALMAN ake Kiransa da FARIS,tun lokacinda suka haifi FARIS Allah yabuda musu arxiki samu ya karu har wajen saida motoci babba Dad ya bude a garin abuja sai da FARIS yayi 12yrs a duniya aka haifi fareeda lokacin faris na jss 1 a secondary school ,fareeda na da 3yrs aka haifi humaira, yara dai suna shan gata kuma Allah na Dada buda ma Dad har ya kai ga anfara dama siyasa da shi ,yara sun girma FARIS har ya gama secondary school nan yace shi pilot yake son zama ba’a bata time Ba aka turasa school of aviation dake London, lokacin fareeda na ss1 itakuma humaira na jss2 , a kwana a tashi Ba wuya wajen Allah har FARIS ya kammala degree diinsa, itakuma fareeda ta gama secondary school nan itama tasami admission a Nile university dake Abuja ,shi FARIS sai dai ya xo Hutu ya koma Dan ya cigaba da masters acan ,a halin yanxu da yadawo ya gama karatun har sun basa aiki a can, Dad kam yanzu arziki ya ci uban na da yanxu yana matsayin minister of education wannan kenan*_”
__________
______
_*Cigaban labari*_
Washegari
Da safe misalin 8:00am na safe MUSKAN ce gaban mirror tana shiryawa cikin uniform kasancewar yau suna da papern biology, humaira ma ta fito wanka tana tsane ruwan jikinta ,fareeda CE ta shigo dakin tana murmushi tace yawwa MUSKAN nake jira ki tashi , lpy yadai MUSKAN tafada tana kokarin sa baret nata kan Dan karamin hijab na kanta, ehh lpy kawai dai ina so ki tayani anjima kanwata zaki min duk abinda nafada ai ta karasa maganan cikin fuskan tausayi, ina jinki malamata MUSKAN tafada tana hararanta cikin tsigar wasa, uhmm dama nace Ba in kuka dawo pls kidafamana Dan waken ki mai dadin nan, nasan dama aiki zakisani shiyasa kike wani yin fuskan tausayi toh ni bazan dafaba inji MUSKAN tafada tana kokarin daukan instruments na makarantan ta, fareeda tace pls mana matan big bro haba baby boo na ya FARIS wlh ke kadaice nasa Ba wata saike nan taringa kodata har tasamu tayarda kan zata dafa musu in suntaso daga paper,humaira kam banda dariya Ba abinda take yadda taga an koda MUSKAN da sunan ya FARIS ta yarda zatadafa Dan waken, nan suka fita bayan sun gama shiryawa suka bar fareeda ita kadai a daki, suna fita fareeda ta kyalkyale da dariya harda rike ciki lalle MUSKAN wlhy yanxu na ringa cin Dan wake kenan ina kodaki da sunan ya FARIS”
Suna fita falon yana shigowa sanye yake cikin jenci mai dagon hannu da dogon wando kana ganinsa kasan ya tasone daga training kayan sun amshesa yayi kyau dukda Ba wata ado yayi va zubamasa manyan idanunta tayi fuskanta dauke da murmushi shima ita yake kallo tayi bala’in yimasa kyau duk da itama uniform ne a jikinta shima fuskansa dauke da murmushi har ya karasa wajensu, su suka soma gaidasa ya amsa hade da cewa yan matan Mommy sai ina yanxu ya tambayesu, sai school muna da papern 9-12 yau zamu rubuta biology suka basa amsa'”
Yace toh kuje kuyi breakfast kamin na shirya sai na kaiku, toh suka bisa da shi suka wuce dining table Dan yin break, shima daki ya nufa Dan shiryawa,”
.
Cikin 30mins duk suka kammala shima har ya shirya cikin wasu kananan kaya shirt blue da jeans baki, hannunsa dauke yake da wata haddadiyar agogon na kamfanin Gucci, yatsunsa kuma suna dauke da zobunan azurfa guda uku daya a hannun hagu ,guda biyu kuma a hannunsa na dama har ya karso wajensu MUSKAN couldn’t stop staring and admiring his beauty cikin zuciyarta kuwa cewa tayi gaskiya idan ta mallaki ya FARIS tagama morewa Dan yakai namiji iya namiji da duk burin mace ta mallaki irinsa tana cikin tunanin nan taji ya ja karan hancinta, shagwa6e fuska tayi tace wlhy ya FARIS da xafi fa, yace toh meye kina ta wani kallona tundazu baki ma San nazo wajenkuba kin kafeni da idanunki, bu66uga kafa ta soma kamar wata karaman yarinya cike da shagwa6a tace nifa Ba kai nake kalloba kawai kawai sai kuma tayi shiru ganin yadda ya zubamata ta idanunsa masu rikitar da ita, kwaikwayanta yayi ya marairaice fuska yace kuma meye ai baki karasaba, humaira CE tace ya FARIS Dan Allah ni Ka kaimu school tundaxu kunxo kuna ta zuba soyayya kalan Ku samu late invigilator ya hanamu paper ke kuma MUSKAN gaki lover girl kinata biyemasa ko, LA LA yarinyarnan ni kike fadawa hk tho baza a kaiba invigilator’n ya hana papern Oya wuce ki ban waje kona bugemiki baki stupid girl kawai yafada yana nuna mata kofan fita”
Fita take tana gunguni ai gaskiya na fada kuna wani shan love bako jin kunya kuma ai laifin MUSKAN ce dake biyemasa wlhy zan hadu da ita yau, meye kike fada?yayi tambayan yana nnufota, ai Ba shiri takwasa da gudu tayi waje, shi ko ya koma yace Baby boo mu tafiko karna saki late invigilator ya hanaki paper, murmushi tayi suka jera har wajen motan cikin bakin accord 2016 ya jasu zuwa school din yana ajesu ya cire 1-1k yabasu duk suka masa godia har sunfara tafiya yace baby boo! nan ta komo yace I LOVE YOU murmushi tayi tace I LOVE YOU TOO hade da cewa Take good care of ur self yace I will insha Allah bye-bye yayimata tana dagamasa hannu har ya bace, saukan dundu taji abayanta tana juyawa taga humaira ce murmushi tayi takama hannunta tace zo muje Sis fisgewa humaira tayi tace zakice muje ai bayan kingama shan love wlhy ki kiyayeni inba haka Ba nagayawa Dad ya kori ya FARIS ya koma wajen aikinsa in yaso naga yadda zakuyi love din yar air kawai, yi hakuri Sis inji MUSKAN takama dukka kunnuwanta biyu alamara tayi hakuri, rungumeta humaira tayi tana dariya tace ai dolena na hakura matar yaya guda suna dariya har suka shiga Hall aka fara exams”
.
Basu suka gama exam Ba sai wajajen 12:30 nan driver ne yazo ya daukesu ya kaisu gida, basu tarar da kowa agidanba illah mai aikin su daki suka nufa bayan sun watsa ruwa suka nemi lpyn gado nan da nan bacci ya kwashesu”
FARIS na hango zaune da abokansa biyu wato Anwar da Aliyu suna hira sai dariya suke faman kwasa ina ganin hk ni diba a 360 na isa wajensu Dan dauko wa makaranta rohoto lolz!
FARIS yace Anwar kazata bazan ga baby boo dinaba ko naga kadaukeni kamar mahaukaci kullum in namaka maganta sai dai kayitamin dariya toh wlhy yanxu danake gayamaka tana gidanmu ni nan yanuna kansa ni na kaisu school da humaira, Nan ya kwashe musu labarin MUSKAN tun randa yatafi ya barta a bauchi har kadeta da Mum tayi da zamanta agidansu har kawo xuwa randa ya hadu da ita a airport”
Aliyu yace tab babbar magana a gaskiya na tausayamata abokina allah ya jikan iyayenta da rahma”
“Ameen” dukkansu suka amsa a tare Anwar da FARIS”
Anwar yace abokina kasan Allah ni duk tunanina Kai kadai kake hauka akanta na zata ita tuntuni ta mance da Kai”
.
FARIS yace ina wlhy idan za’atara Mata duka na duniya toh MUSKAN ta dabance tana sona kamar yadda nake sonta kumafa kar Ka manta yarinyace am her first and last love insha Allah da soyayyata ta tashi kuma da soyayyata zata rayu kamar yadda nima ban taba son wata ya`mace Ba face ita kuma insha Allah ita zata kasance mace ta karshe a rayuwata nayi alkawarin sonta a raina son dan Bana wa wata irin sa sai mahaipiyata da kannena, My lyf is all depend on her lobe I cannot do without her,she mean a lot to me, I lobe her so much”
Anwar da Aliyu dai sunsan gaskiya abokinsu ke fada Dan idan akoi waenda sukasan halin FARIS bayan iyayensa toh sai su biyunan they are childhood frnds, sun girma atare basa boyewa dayansu damuwarsu karatunsu iri daya suka yi dukkansu pilot ne tun suna kanana inka gansu zaka dauka yan uku ne, gidajensu Ba nisa duk suna anguwa daya wato maitama dake birnin tarayya yadda suke abokai yasa iyayensu kulla abota duka matan da mazan Anwar da Aliyu suma iyayensu Nada arxiki iya gorgodo,,,, wannan kenan”
Aliyu ne yakatsemusu tunani da fadin hey dudes lokacifa na tafiya har karfe 4:00 fa yakamata mu je gida wlhy ni yunwa nake ji”
FARIS yace ragon namiji kawai kai kullum yunwa “
Anwar yace gaskiya kafada Aliyu nima nan yunwa nake ji wlhy mu tafi gida, kuma gidan Ku zamu FARIS sai Ka nunama Baby boo din naka, koya kace”
Baza a jeba’ nifa Ba Wanda zai ganmin Mata yafada yana mikewa”
Sai kayi amma wlh sai mun ganta, nan kowannensu ya nufa motansa ya ja fuuuu sai gida”
MUSKAN ce dasu fareeda a kitchen suna dafa Dan wakensu ita MUSKAN na kwashemusu a ruwa sukuma sai zuba surutu suke sallamar su FARIS ne ya katse surutun da suke fareeda ta fita,tana amsa sallaman”
Sanda zuwanku ya Anwar da ya Aliyu,,, Yawwa fareeda ya kk? Lpy qalau,, Ya karatu? Tace alhamdulillah,, Toh Masha Allah”
Ke fareeda bamu abinci yunwa muke ji FARIS yake fadamata” ya FARIS sai dai a girka muku yanxu nan wasu sukazo wajen Dad muka juyemusu sauran abincin da ya saura”
Humaira da MUSKAN ne suka fito hannunsu dauda da bol na danwake yasha eggs da sauran kayan hadi suka tarar da su ya FARIS gakuma fareeda dake bayani, sannunku ina wuninku duka suka fada,, lpy suka amsa, suna kokarin hawa sama zuwa daki FARIS yace kai Ku dawo meye wanann acikin bol dinnan ya tambayesu,”
Suna karasawa sukace ya FARIS Dan wake ne fa suka fadamasa suna nuna masa cikin bol din, aiko yana hango cikin bol yasa hannu ya karbe tare da fafadin jeku kukawamanacruwan sanyi da drinks”
Ido suka zubamasa dukkansu badai ya FARIS cinye musu Dan wake zaiyiba basu ida tunaninsu sukaji yace dudes Ku sauko muci mana and Ku kuma ban aike Ku bane kun wani tsayamana a ka, TAFIYA suka soma kowa na gunguni su fareeda kam tana zuwa kitchen ta fashe da kuka wai ita ala dole ya FARIS ya cinyemata Dan wake, hk suna ji suna gani suka yi tasss da Dan waken, sai da suka sake dafa wani suka ci suma Dan cire kwad’ayi”
.
Bayan sun gamane FARIS ya gabatar wa su Aliyu MUSKAN ita ma ya gabatar mata su Anwar, sun sha hira sosai har sun saba da juna a dan kankanin lokaci, sunyaba da zaben abokinsu kuma vasu karyata shi Ba gaskiya yayi dacen Mace kamila,kunya,nitsuwa dakamun kai,sai maghriba suka bar gidan”
Nan suma suka gabatar da al’amuransu yadda suka saba aiwatarwa a kowani dare”
‘Lovers bird kam yau hira suka sha a waya kamar Ba gobe sai wajajen 11:00 na dare
.
_*one week later*_
Yanxu FARIS ya sami sati daya da zuwa 9ja komai yana tafiya daidai yadda ya kamata, MUSKAN ma sun kusa gama Waec, soyayya kam ba’a magana suna shan lo6e FARIS baya shakkun nunawa MUSKAN soyayya a gaban kowa ita har kunya yake sata wani sa’in Dan KO gaban su Mum ne sai yace Baby Boo kaza anjima princess kaza duk shi daya tun MUSKAN na faking tare dajin kunya yanxu km harta saba, Mum kam na ganin ikon Allah duk FARIS yazama maras kunya ynxu indai Baby Boo dinsa na wajen DA yake toh fa sai kunyi hkri dashi, su fareeda kam sai dai suyita tsokanan MUSKAN kan wai wani charming take anfani dashine ta sace xuciyan big bro haka, itakam saidai tayi dariya tace Ba abinda na mishi kawai Allah ne ya dasa masa soyayyata cikin zuciyarsa kamar yadda nima nake son sa, tabe baki suke suce bawani nan wlh ya FARIS yafi sonki fiye da yadda kike sonsa, hmmm kwafadi hk amma shi kansa yasan yadda ni nake sonsa haka dai xasu yita hiransu, suna dariya da wasa…
Yau takama Thursday (alhamis) Mum da yan matan ta na hango a parlorn su sun baje suna hira da yan matan ta abin birgewa, sallamarsa ce ta katsesu yshigo fuskansa dauke da murmushi ya karasa inda suke, Yana zuwa ya zuve kan couch na faLon yace wasshhh yana lumshe ido hade da matsa kafafunsa da hannnu mum wlh na gaji yau nayi yawo kuma duk Anwar da Aliyu ne suka jani if not ni Ba iya wannan yawonba yana fada yana langw6ar da Kai kamar karamin yaro”
.
“Ta6e vaki duka sukayi MUSKAN, fareeda da humaira hade da samasa dariya”
“Humaira tace pls ya FARIS kadaina langwabar da kankanan wlh u look like baby”
“Amsheta fareeda tayi dacewa wlh kuwa koba hk bane MUSKAN”
“Haka ne mana mutum kato dashi yaxo yana zubamana shagwa6a kamar wani Baby tana fada tana kannena masa ido(wink) hade da smiling”
“Gaskiya yaranan kun rainani dayawa jibi abinda kuke min ehh ni nake Abu kamar Baby yafada yana mikewa,aiko yana tashi yasawa fareeda rankwashi a Ka, rike wajen tayi idonta yakawo ruwa, yana shirin kaiwa humaira nata bugun tayi saurin buya a bayan Mum yakaiwa iska duka”
“Mum tace son karka biyewa wadannan mashirmatan barni dasu zanyi maganinsu, tafi daki Ka watsa ruwa karka kula su kaji”
” kallo yabisu dashi irin kallon xamu hadu dinnan har yayi gaba yana tafiya yajuya hade dacewa baby Boo ki hadamin snacks da drinks ki kaimin garden in na fita wanka yana Kai nan yayi hanyan part dinsa”
‘Fareeda da tundaxu tana rike da kanta ta murguda baki ()tace sai danbanzan mugunta ya iya”
“Dariya MUSKAN da humaira suka samata,Mum na kallon tace maginki ai Ku kuka rainashi”
“Sallamar ta ne yasu dagowa duka suna amsawa”
‘”Mum tace a’a wanake gani kamar fatiti”
“Ehh Mum nice yau musan man nakawo miki ziyara”
“Fatyn ce ta karaso ta zauna ta kwashi gaisuwa “
“Mum tace yasu hajiya Ina fatan lpyn su’
“Lpynsu tanama gaidake “
“Masha Allah Ina amsawa, fareeda Ku kawomata abin motsa vaki mana”
“Tana zungura baki ta je ta hadomata snacks da drinks tajiyemata a karamin glass stool agabanta”
“Thanks fareeda'”
“Mikewa sukayi dukkansu suka haura sama xuwa dakinsu aiko suna shiga kowa ya soma magananta, MUSKAN tace guys kunsan meye, a’a sai kinfada’
“Hmmm yau baku ga new face da mutuniyarba”
“Mungani maybe yau din she was kinda simple and happy shiysa”
“Oh nidai ita ya dama Bari naje na kaiwa sweet love snacks nasa karnayi laifi”
“Ke ta matsewa mtssww wai sweet love”
“Naji kwaji dashi tasa Kai tafice kitchen direct”
“Tahada komai yadda ya bukata ta nufi hanyan garden, taxo wucewa ta hango faty da Mum suna hira kamar Ba itace mai dagun kannanba tabe baki tayi ta wuce abinta”
“Xaune yake kan plastic chairs na garden din yana ta latsa wayoyinsa,sanye yake cikin wata farin T-shirt da 3quarter jeans nasa baisan ma ta karasoba kawai jiyayi an warce wayan hannunsa, da axama ya daga idanunsa da niyan matsifa kawai yayi tozali da abin kaunarsa baisan sanda yasaki murmushi Ba harsaida hakoransa suka bayyana sai kuma yasake hada rai kamar bashi yayi dariya yanxuba”
“Tasan laifinta Dan hk tayi murmushi itama tace sorry sweet nasan laifina amma am on my kneels asking for forgiveness”
“Uhmm ashema kinsan laifinki Ba ni kikawa dariya daxuba kuma hardacewa sweet love dinki yayi Abu kamar baby KO Zan Rama ai”
“Nidai kayi hakuri pls wlh sharrin shaid’an ne dasu fareeda amma ai ni duk yadda kayi yana maka kyau habibie”
“I trust u nasan kinfad’i gaskiya nan ya sawya hirantasu Dana soyayya uhmm lovers bird kenan suna ta shan love”….
.
“Faty ce tadubi Mum tace; mum wai yaushe FARIS zai dawo ne”
“Mum tace ai ya dawo KO baki sanibane”
“Ehh wlh bansanib”
“A toh hakane yanxu ma ai yana garden sai kije Ku gaisa “
“Toh tace tata shi tayi hanyan garden din”
“Suna hiransu abin burgewa sai murmushi da dariya zaka gani dauke kan fuskokinsu”
“Tun kan takarasa ta hango su nan zuciyarta ta harba tana bugaws da sauri wani Kishine ya kamata, haka ta daure ta karasa wajen Ba KO sallama tasoma Jan plastic chairs dake gefen FARIS da niyan zama”
Kamar ance ya juya ai ko yana juyawa ya ganta take annurin fuskasa da duk wata farinciki ta gushe”
“Faty ce tasoma magana kamar haka haba my FARIS yanxu duk son da nakemaka har zaka dawo 9ja kayi kusan week van saniba if not naxo yau u won’t cal and inform and kasan I miss u so much, I miss those eyes , those smile and every thing from you'”
“Hade rai yayi sosai kamar wadda aka aikowa sakon mutuwa yace what rubbish are u saying,how many times do I have to tell u dat am damn in love with you hun, kewai mai yasa bakida hankaline ,why meyesa kike Abu kamar va maceva can’t u take a look from others girls su haka suke ehe su basuda kamun kai ne are they not expensive huh kosu suke zuwa wajen maza suna tona asirin zuciyarsu pls Fateema be matured enough kisan what are u up to”
“Rausayar da Kai tayi gefe hade Kai hannunta ta kamo nasa hannu tace pls FARIS just knw how much I love you, just a chance zanyi proving my true love for u ,hannun NASA takai kirjinta saitin zuciyarta tace just feel how my heart beat just bcox of ur love,why meyesa baka tausayamin ne nan tafashe d kuka”
“MUSKAN kam tazama Yar kallo awajen”
“FARIS can’t stand watching faty crying, idan akoi abinda yatsana toh vai wuci yaga Mace na kukaba, bai San sanda ya dago fuskanta ya soma share Mata hawayenba”
“MUSKAN na ganin haka ta tashi fuuuuuu a zuciye tabar wajen gudu gudu take hade da sauri tana sharan hawaye tayi hanyan cikin gida'”
.
“MUSKAN!MUSKAN!!MUSKAN!!! FARIS ne yake kiranta amma Ina tuni ta shige cikin gida allah ya taimka Ba kowa a falon hakan yabata daman shigewa dakinsu tafada kan gado tasoma rusa kuka”
“Shimaa can FARIS ya rikice ganin Baby boo ta tafi rai bace gashi kuma tana kuka hakan yasasa binta amma kash yana zuwa yaji kofan dakinsu akulle dafe Kai yayi yace nashiga uku”
_hmmm FARIS Ba uku kashigaba tara kashiga inji neeratlurv lolz_
“Faty ma a zuciye tabar garden din ko shiga tawa Mum sallama batayiva tafigi motarta tabar gidan at 360”
.
Buga kofan yake yana kiran Baby Boo pls ki bude door din don’t get upset with me, wlh banyi haka Dan bata miki rai ba is not intensionally pls understand me, haka yata fad’a amma kamar Kara harxukata yake sai volume na kuka take karawa, shikam FARIS yanajin kukanta harcikin kogon zuciyarsa amma Ba yadda ya iya dole yabarta ta huce zuwa anjima”
“Jiki sanyaye yabar bakin kofan but his heart arch more feeling his own baby boo crying that make d thing worse”
“Duk wannan abinda suke su fareeda basu saniba kasancewar suna daga kitchen sai yanxu dasuka zo bakin kofan kuma suka jisa a datse”
“Buga kofan fareeda ta soma Ghamb! Ghamb!!’
“Waye MUSKAN tafad’a cikin muryanta daya dashe d’an kuka”
“Mune su fareeda ne da humaira open d door”
“Jin su fareeda ne yasata tashi taje tabud’e musu kofan, tana bud’ewa ta nufin gado ta zube kansa”
“Kansu suka kunsa cikin dakin suka nufin wajen MUSKAN dasuka ga ta zube kan gado”
“Humaira ce tad’ago da ita nan suka ga idanuwanta ja kamar gauta”
“Sis lpy? both exclaim fareeda and humaira”
“Meye sameki? Waya tab’aki? Ki gayamana”
“Ido ta zubamusu tana masu kallonsu, wani amsa zata Fara basu cikin tamvayarasu”
“Muna tambayanki kinyi shiru ki gayamana ko naje nakira Mum fareeda tafad’a cikin muryan da yanuna alamar damuwa tattare da ita”
“Mikewa humaira tayi tace bara nakira Mum sai kigayamata tunda u are not ready telling us”
“Dasauri MUSKAN tajata baya hade da zaunar da ita tace am ready zangayamuku wlh karki Kira Mum”
“Okay muna jinki”
“MUSKAN tace Ba ya FARIS bane ya…..nan ta k’washe musu labarin abinda yafaru'”
“Oh jealousy babe calm down,cool ur mind babe ke kanki kinsan u r d only girl who got ya FARIS heart huh, so why d worry, karki dami kanki kinji I knw he’s allergic of seeing women crying that’s why he intend of waping that brat tears fareeda tafad’a pleasing MUSKAN”
“Yes that’s it wlh nasan Broz hakan ne nufinsa inba haka meye zai kaisa taba Faty inji humaira”
“Nan dai sukasamu suka shawo kanta da kalamai masu dadi har ta ware kamar Ba itaba suna tashan firansu amma can kasan zuciyarta kuma tanata saka abinda zatama FARIS yaji zafi”..
FARIS!!!
.
“Yana shiga daki ya zube kan kujeran da ke dakin, ya furzar da wata zazzafan iska daga bakin yace “Gosh!, yadafe kansa”
“Idanunsa ya lumshe ahankankali yace why! Baby boo yazaki min haka?, bakinsan bacin ranki na iya sani cikin matsanaicin damuwa bane pls ki tausayamin.”
“Yana ta surutunsa shi kad’ai har aka Kira sallan maghriba, naushi ya kaiwa kushin d’in kan ya mike yashige bathroom ya d’auro alwala ya nufi masallaci d’an gudanar da sallah.”
Faty!!!
Tana fita gidansu FARIS kaitsaye gidan kawarta meemah ta nufa, Allah yasa ta isketa gida, a zuciye ta banke kofar d’akin ta shige tasami bakin katifar dakin ta zauna sai faman huci take kamar wata kumurci.”
“Babe lpy ki shigo azuciye haka? Waya b‘atamiki rai?”
“Gwaron numfashi taja hade da jan tsuka mtsswww.'”
“Meemah tace babe kin barni duhu ki fahimtar dani ba tsaki nace kiimin Ba”
‘Dallah kin daman ai kema kinsan Ba Wanda ya isa batamin sai FARIS, kinsan ina dak’on soyayyarsa kamar dan dako wlh yanxu daga gidansu nake vanma San ya dawoba sai tarar dashi nayi, nan ta k’washemata labarin yadda sukayi dashi .”
“Mtsswww kin vada ni wlh yoo yanxu d’an wannan kike tad’a hankalinki.”
“Babe taya hankalina bazai tashiba, wlh bakiga yarinyar bane kamar aljana fah take d’an kyau kuma duk yadda akayi yana sonta sosai, sabida yadda na Lura dayaga ranta ya b’aci, sai kinga yadda ya rikice da ta bar wajen ma, sai kiran sunan ta yake duk ya susuce .”
“Babe ki taimaka wlh kinsan inason FARIS kamar hauka wlh in na rasasa Zan iya rasa raina pls help me”
“Meemah ta dafata tace don’t worry babe ki kwantar da hankalinki kisha ruwa mai sanyi kid’auka FARIS yazama naki.”
“Are u serious Faty tafad’a tana kallonta.”
“Yes 100% sure! Zan kaiki wajen malamina dake min aiki, wlh aikinsa kamar yankan wuka take, nasan rannan karamar matsala ce taki and am very sure zamu semi nasara in munje.”
“Yeeeeh takai mata peck a check, tace shegiya kawata shiyasa nake sonki, I know u can do it ILY babe, yanxu yaushe zamuje”
“Dadina dake hanzari kifa vari bayanxu zamuba sai nan da sati daya d’an malam din yayi tafiya sai ya dawo sai muje ko ya kikace”
“Ehh hakan ma yayi duk da sati dayan yayi yawa amma Allah ya kaimu”
“Ameen”
“Nan suka sauya hirantasu ya koma na wata duniyar ta daban kuma .”
****•••°°••°°
_*8:30pm*_
Dukkansu a zaune suke suna kallo wani film da ake a MBC 2 _A good day to die hard_ .”
“Dukanninsu hankalinsu na akan film din illah FARIS da Rabin hankalinsa na’akan film din rabi nakan Baby Boo dinsa dake fushi dashi”
“Dad yayi gyran murya yace Son”
“FARIS dake kallo ya juya dan amsa kiran dad yace ma’am Dad”
“Dad yace daughter”
“MUSKAN ta juya tace na’am dad”
“Dad yace magana nake son yi daku dan haka kubani Aron kunnuwanku”
“Duk suka maida hankalinsu kan dad”
“Toh dama Ba wani Abu nake son gayamuku illah dama nida Mummy’n Ku mun yanke shawara munga it’s high tym ace kunyi aure tunda duk mun fahimci kuna son juna, kuma kai faris baka jin kunya ma kota2,kunga gwamma mu muku aure kawai mu huta tunda yanxu kana da aikin and u are good enough kazama magidanci, ke kuma daughter tunda kungama Waec kinga neco din inyaso ko da aurenki sai kiyi bayan nan in results suka fito sai a nema miki admission kiyi makarantar ki adakinki, meye kukace gameda da shawaran?.”
“FARIS da tunda dad yasoma bayani yake jin kamar anmasa busharan gidan aljannah yace Dad am ok with ur offer na yarda da duk abinda kuka yanke tunda Ku kuka haifan”
“Toh alhamdulillah, ke kumafa daughter?.'”
“Cike da jin kunya ta sadda kanta kasa tana wasa da yatsanta tace Dad, Mum duk hukuncinda kuka xartar mai kyau da Mara kyau toh ni duk a wajena yayi, kun kasance iyaye a wajena dan haka nasan baza kutab’a gudanar da abinda Ba alhairiba a tattare dani wlh na amince da hukuncin Ku.”
“Alhamdulillah Allah ya muku albarka haka dama akeson duk d’ana gari ya kasance, hakikanin gaskiya Ina alfahari da samun Ku matsayin ’ya’ya Allah yarayamin Ku baki daya.”
“Ameen dukkansu suka fad’a.”
“Mum da tunda aka Fara maganan bata sa bakiba sai Yanxu tayi magana fuskanta fal farinciki daya kasa buya tace.”
“Daughter na gode gaskiya yau kin nunamin ni uwacee gareki may god bless u.”
“Ameen Mum”
“Dad yad’aura da cewa yanxu insha allah jibi zamuje bauchi wajen baffanki sai mu nemi aurenki a wajensa tunda shine Wanda ya ragemiki a duniya, dollene sai da yardansu xakiyi aure, dan haka zaki ban address na gidan sai muje.”
“MUSKAN bata so Ba amma gudun b’atawa Dad rai yasa tace Ba matsala.”
“FARIS, fareeda, humaira sunfi kowa murna mussaman shi FARIS har ya kasa boyewa, ganin haka yasa su Dad barin falon suka nufi nasu d’akin.”
“Ai ko suna barin wajen yacewa su fareeda su basu waje zasuyi magana da baby Boo dinsa,haka ko akayi amma su fareeda na mikewa MUSKAN ta mike itama.’
“Gabanta FARIS yasha yace pls baby Boo kitsaya ki saurareni mana yakarasa maganar cikin tausayi, MUSKAN ganin haka yasata koma ta zauna.”
“Baby Boo pls ki yi hakuri I know I offended u but not intentionally, wlh banyi haka da niyan b’atamiki raiba understand pls.”
“Zakace haka mana bayan kana ganina Ka aikata hakan waya sani in abayan idanuna meye zakayi, tayi maganan in jealous voice.”
Oh gosh, ya dafe kansa, yace ok naji but understand ko vayan idonki I will do something bad, ina sonki bazantab’a cin amanarkiba trust me baby Boo.”
“Kalamai masu tausasa zuciya yarinka Mata yana calming dinta with his sweet love words, har ya shawo kanta suka shirya kamar basu tab’a fadaba.”
“Hira soyayyan su suka sha kamar Ba gobe, zuciyoyinsu na cike da farinciki, basu sukawa juna sai da safeba sai wajajen 11:30pm na dare kowannensu ya wuce daki cike da kyewar dan uwansa.”
“Koda MUSKAN taje daki su fareeda har sunyi bacci dan haka itama tashirya cikin kayan baccinta ta kwanta zuciyarta fal farinciki.”
“Haka bangaren FARIS shima yana shiga daki ya sauya kaya zuwa pajamas nasa ya kwanta shima zuciyarsa fal farinciki.”
*** ***
Washegari da sassafe bayan sunyi Karin kumallo FARIS yace musu su shirya zai kaisu shopping, rawa suka hau yi suna tsalle saida ya daka musu tsawa suka nutsu kuma yakara dacewa wlh cikin 10mins idan basu shiryaba zaiyi tafiyarsa fuuuu yafice xuwa motansa yana jiransu.”
‘”Gudu2 sauri2, suka je daki dama da shirinsu mayafi kawai suka dauko suka d’an gyra make up na fuskarsu basuyi wani makeover Ba illah light one dasukayi, dukkansu sanye suke cikin bakaken Arabian gown sunyi rolling d’in Kansu da d’ank’walin gown d’in sunyi kyau sosai barin ma MUSKAN datake blowing wani haske kamar balarabiya.”
“A mota suka samesa ya had’a giran sama data kasa bud’e motan sukayi suka shiga MUSKAN a gaba fareeda da humaira abaya, tunda suka shiga bai tanka musuba, sudai dariyane yake son gifta musu amma haka suka danne basuyiba gudun hukuncin da FARIS zai yanke musu.”
“Stupid girls, kun rainani ko? eh Zan had’une da Ku ai maras kunyan yara kawai , nama yi niyan tafiya buh Dan akoi Baby boo shiyasa I can’t go inba haka fitowa zakuyi Ku tarar bani ya bugawa musu wani dirty look dasuka sha jinin jikinsu, mota yaja da d’an banzan gudu yafita , basu tsaya KO inaba sai _shoprite_ na cikin garin abuja.”
“Sayayya yamusu sosai na kayan sawa, kayan makeup da kayan makuleshi, daga nan yawuce dasu ice cream shop ya saimu su .”
“Park ya wuce dasu shan iska, acan suka keb’e da Baby boo d’insa suka sha love sai yamma lis suka koma gida da gajiyan yawo.”
“Da dare suka sha hirannsu yadda suka Saba.”
*** *** ***
_*2days later*_
Kamar yadda Dad yafad’a toh hka akayi ya karb’i adreshin gidansu MUSKAN dake bauchi shida Dan uwansa da abokansa biyu suka isa garin bauchi,direct unguwarda MUSKAN ta basu adreshi sukaje basu wani sha wuyaba suka sami gidan nan suka aika yaro yamusu sallama da mai gidan.”
“A cikin gida yaro yace Ana sallama da Baffa, kasancewar bai fita aikiba yasa yaje har kofan gidan, KO da zuwansa yaga manyan mutane nan ya musu iso har cikin gida , a babban falon gidan ya ajiyesu aka kawo musu drinks da snacks.”
“Bayan sunci sunsha nan suka sanar dashi meye ke tafiya dasu sun zo nemarwa dansu ne auren MUSKAN kuma itama MUSKAN din na awajensu.”.
“Bud’an bakin Baffa yace sai mai intana wajenku, ai ni tuni na tsameta daga jinin na tunda yarinya yawon dandi taje ni Ba ubanta bane kuma Ba hadina da ita.”
“Ta inda yake shiga bata nan yake fitaba matsifa sosai yayiwa su Dad ya koresu kuma har da cewa daga rana ita yau karsu sake zuwar masa da maganar shegiyan yarinya nan.”
‘”Jiki a sanyaye su Dad suka bar garin bauchi , tun a hanya Dad ya rinka baiwa abokansa hakuri da gayamusu abinda ya faru da MUSKAN duk sun tausayamata kuma su sun yarje kanin Dad yace shi zai wakilci a matsayin uba.”
“Iya murna Dad yayi har suka karasa garin Abuja.”
“Sukayanke gobe su Dad su je gidan (Usman)Dan uwansa nemar auren MUSKAN wajensa.”
“Da wannan shawaran da suka yanke suka isa gida”.
.
“Sai bayan isha misalin 8:30 suna a zazzaune a falon kasa Dad yayi gyran murya ya kwashe duk yadda sukayi da Baffa da sukaje har da abinda abokansa da Dan uwansa yafad’a, ya Kara da cewa gobe zasu je Neman aurenta wajen Dan uwansa (Usaman) insha Allah.”
“Godia sosai MUSKAN tayiwa Dad, har Baba Usman akakira Mata suka gaisa ta masa godia hira sukayi dashi sosai kamar ta mahaifi da ‘da.”
“Baffa kam ko vayan tafiyarsu
Dad yashiga wajen matarsa yasanar da ita suwaye Dad da abinda yake tafe da su itama ta hau sababi wai Allah yarabasu da alakakai yanzu kuma saida suka soma cin arziki zata dawo tab ai baxai yibu nan suka ta zagi da matsifa.”
_ni dai neerat nace tirr da halayensu Baffa da matarsa_
Washegari!
Su Dad sunje neman aure anvasu har sun yanke aure bayan MUSKAN tagama neco da sati daya za’ayi aure.”
“Dad ya sanar dasu Mum abinda suka yanke “
“Nan aka soma shirye shirye kasancewar su MUSKAN sun Fara neco Ba kanta “
“Amma kullum suna manne a waya da FARIS wani’sain kuma suna tare a gida.”
_*Faty*_
Tun bayan da sukayi magana da kawarta meemah bata sake waiwayar FARIS Ba ko a waya bata kiransa amma can cikin zuciyarta kuma ta kudura niyan da zarar malamin ya dawo zasu wajensa.”
*** ***
A haka rayuwa taci gaba da gudana, MUSKAN na faman preparation na gama school da bikin candyn su wani bangare Nata kuma na shirye shiryen bikinta da FARIS.”
“Haka shima FARIS yana busy yanxu Sam baida lokaci yana can yana gyran gidan da zasu zauna da baby boo duk da ko anyi auren Ba nan zasu zaunaba can London zasu sabida aikin sa kuma bazai iya zuwa can Baby boo na nan Ba shiyasa su Dad suka yarje masa kan bayan aure zasu tare can da matarsa.”
_*Faty*_ sunje wajen malamin amma kash sun tarar baida lpy sosai nan suka baro gidansa suka dawo gida duk ran Faty a bace.”
“Dan Ba karamin tashin hankaliba Faty ta shiga jin ansa ran auren FARIS da MUSKAN shiyasa tasa meemah a gaba sai sunje wajen malam, kuma koda sukaje sai su Ka tarar baida lpy.”
“Meemah ce tayita k’wantar ma ta da rai kancewa ta barsu ai ko bayan auren sai su je inyaso su fitar da ita daga gidan, dan akoi wani hatsabibin boka a garin _Bebeji_ dake kano toh can zasu.”
” da wannan shawaran Faty tasama zuciyarta ruwan sanyi, takoma shanawa.”
_*sati biyu*_ ya rage auren MUSKAN yanxu ta gama neco har sunyi candy aurenta kawai take jira.”
“Mum ta tafi Dubai hado kayan lefe da kayan kitchen da furniture’s.”
*** *** ***
_*bayan sati daya*_
Mum taje Dubai tadawo lpy da kaya niki niki wanda ta sayo kama daga kayan lefe, kayan kitchen, furnitures da sauransu.”
“Gida duk ya cika da yan uwa sai shirye shirye ake tako ina.”
“gyra sosai MUSKAN ke sha dan wata yar Maiduguri Mum ta dauko tun ana saura 1week auren taxo, inka ga MUSKAN zaka rantse ba itabane dan ta canza fatanta ta kara laushi sai sheki take kuma dama tuncan itadin mai laushin fatane.”
“Tunda aka fara shirye shirye FARIS basu hadu da baby boo dinsa ba sam dan Mum tahanasa zuwa part dinsu sai dai suyi waya gashi yau ana saura 4days auren.”
“event Kala Kala suka hada akoi, kamu,fulani’s day &kauyawa day, sai Dinner da mothers night daza’ayi, saikuma walima daxasuyi before d’aurin auren ran Saturday a gidansu FARIS “
“yau takama Wednesday zasuyi fulani day, dan jiya suka yi kauyawa day, gobe kuma kamu.'”
“shiri su fareeda keyi da kawayensu cikin shiga irinta fulanin usul daga can gefe kuma MUSKAN ne da frnds d’inta na school kamar su meena da kubrah anata tsaramata make up cikin kayan fulani, make up artist dasuka dauka daga company’n Tara make up ita ke mata make up.”
“gefe daya kuma Young writers forum(Y.W.F),five stars ke zaune su Miss Mjay kenan.”
“daga dayan gefen kuma su yar mitsila (Faty axland) da huddallah(Mrs JH)sai kuma yan group na (Huddalah Bani inbaka) da sauran groups din da members duk cikin shiga ta fulani .”
“vayan angama makeup ne wayar muskan tafara neman agaji, hannu ta mika ta dauka _heartbeat_ tagani tubuce nan ta dauka cikin muryanta mai sanyi tayi sallama hade da gaishesa.”
“Amsawa yayi, yace baby boo i miss You so much, pls ki zo na ganki even for a minutes wlh zaki kasheni da missing dinki.”
“can kasa2 kamar munafuka tace Nawan yi hakuri wlh nima am damn missing ur handsome face and that ur huskyVoice buh mum tahanani fita and eyes nasu fareeda na akaina, in na fita xata gayawa mu…..m.”
“bata ida maganarba sanadiyar jin sallamar mum datayi yasata cusa wayan kasanta.”
“Mum ce tashigo hannunta rike da cup takarasa gabanta ta mika mata oya shanye yanxu kiban cup.”
“tana yatsine fuska ta karb’a tace mum wlh wannan akoi daci pls kiban d’ayan.”
“anki a bayar zaki shane ko yaya ko saina d’uramiki.”
“jin Mum tace zata d’uramata yasata kafa cup d’in a baki ta shanye tana kakarin amai.”
“kika amayar _Ni dake_ (pherty) Sha sha kawai bakisan anfanin taba shiyasa tasa kai ta fice.”
“dariyanda humaira ke boyewa ne ya fito saida tayi mai isarta tukun tace jibe kimana.”
“karamin bakinta ta cuno alamar zatayi kuka, fareeda ce takara wajenta da sauri tace baby boo karkiyi kuka pls zaki bata make up dinfa.”
“and u humaira you Are very stupid yazakisata kuka? ko kina so kib’ata mata make up ne.”
“folding hands d’inta tayi taka ce am sorry big sis, baby boo kiyi hakuri kinji.”
“kai ta gyda alamar ta hakura and taji dadin yadda suka kirata baby boo, sai lokacin ta lura da wayarta dabata kasheba dagawa tayi tasa kunnenta tace heartbeat baka kashe wayan ba.”
“eh baby boo ban kasheba ina jinku dont mind them zan hadu da su kinji.”
“ok naji tohm.”
“meye mum take baki mai daci da baki so.”
“uhmm ba komai.”
“naji toh tunda baxaki fad’aminba take care bye lo6e u muahh yayi hanging kiran.”
“wayar tabi da kallo tace ILYM.”
“Taro sukayi sun gama fulani day lpy aka watse.”
“Haka suka ci gaba da gudanar da event dinsu lpy sai ranar kamu FARIS yaga MUSKAN basuma samu sunyi magana sosaiba FARIS sai bin bin baby boo da kallo na So da Sha’awa dan yadda yaga ta canza.”
_*Friday 7:00AM*_
“gida ya kacame da Hayaniya sai shiga da fita ake kowa ka gansa cikin kwalliya na lemon sky blue da ratsin pink a jiki head pink da ke daure a kansu.”
“motocine birjik a kofan gidan manya manyan motoci kana gani kasan annarkar da naira wajen siyan motocin.”
“fareed ce tace kun gama make up d’inne itama tata fuskan dam da make up.”
“mun kusa head ne kawai ya rage muke gyrawa, artist make up ne ke maganar.”
“okay make hurry up suna can sunata damuna da waya.”
“inless than 10mins aka gama wa MUSKAN make up din nan suka jera dan fita zuwa mothers night.”
_wooohooo muskan tayi kyau words cannot say how beautiful she look make up din ya karbeta masu karatu kawai just imagine yadda zatayi kyau zan so ku ganta lolz_
“jerawa sukayi da kawayenta , suna sanye da blue and pink head while ita kuma dogon gown wanda aka rike ta baya if not zaija kasa pink in color gown d’inta ya kasance head dinta kuma sky blue.”
“a kofan gida suka yad’a zango sauran kawayen sun shiga sauran motocin, wajen wata bakar ford jeep suka nufa da MUSKAN nan suka bud’e suka zaunar da ita hade da kullo kofar suma sukaje suka shishiga aka ja motocin covoy aka hada.”
“kamshin turarensa ne da nata ya gawraye ga sanyin AC nan wani fitinanne kamshi ya mamaye motan.”
“hannu yasa ya jawota zuwa jikinsa ya rungumeta a kunne ya rad’amata I Miss you baby.”
“uhmm tace dan ita a takure take wani irin electrical spark ne yake ziyartarta.”
“uhm kawai zakice, shiru tayi har yanxu, ganin bata da niyar magana yasa shi rinka mata hira duk da bata amsawa baisa,yin shiruba har suka isa sharaton hotel dake Abuja.”
“Tare suka jera hannunsa rike cikin har suka shiga cikin hall, inda masu daukar foto da bidiyo suke aikinsu sa wutan flash ke haskasu, suna shiga MC ya sake kida mai sanyi.”
“bayan sun zazzauna aka soma gavatar da taro, Anwar ne yakaranta biography’n FARIS while Meena ta Karanta na MUSKAN.”
“Taro yayi taro anci ansha antiki rawa inda na hango su Aneelurv,cute xarah, yar ficika,mss mjay, faty axland,miemie bee,ayusha iliasu, Autar hajiya,Futh pinky durling, princess Amrah,baby mash,Zara b~b, Aneesa didi,Vasmer Er Lele,hamagee,Melody, da sauran waenda ban ambataba duk suna k’wasan Shoki ansa musu wakar _shake d bom bom sai karka d’awa ko suke.”
“Gefe guda kuma yan group na Neeralurv novels,Aneelurv novels,mss Mjay novels,little princess novels, futhalurv novels, Online hausa Writers,perfect hausa writers da sauransu duk suma k’wasan Shoki.”
“sai wajajen 12:00 na dare suka tashi a taro kowa yanufi gida a gajiye.”
.
_Rana bata karya saidai uwar diya taji kunya_ yau Asabar misalin 1:00 aka d’aura auren SALMAN FARIS DA MUSKAN akan sad’aki naira dubu 1000, Auren da manya manyan mutane na ciki nijeriya da wajen kasa, suka hallata daga abokan Dad har na FARIS na waje sunzo Dana gida 9ja .”
“cikin gida anyi walima antashi lpy inda aka gayyaci babba malami sheik kabiru Gombe ya wa’azantar da su sai 1:00 aka watse.”
“Nan aka cigava da gudanar da biki har yamma, waenda zasu kwana sunan ,waenda kuma zasu tafi suntafi.”
“shikuma faris da abokansa a wani pent house na dad suka taru can sukayi reception nasu.”
*** ***
Da dare bayan sallah’n magrib yawancin mutane sun watse daidai kune suka rage da dangi, suna shirye2 mika amarya gidanta.”
“MUSKAN na kwance bisa gadon idonta a lumshe tana cize lebbenta ta dafe kanta arrrrrhhh tace alamar kan na Mata ciwo.'”
“Sis lpy ko dai kanki ne ke ciwo fareeda ce tayi maganar.”
“Eh Sis kaina ke ciwo, ina ji kamar fadowa zai wlh.’
“Sorry bara na gayawa Mum toh , ta mike tare da ficewa dakin.”
“Meena ce ta matso kusa da MUSKAN cikn kunnenta ta rad’amata amarya mun kusa kaiki wajen angon zaki warke inkin kasance dashi ki daure ta kanne Mata ido (wink).”
“Dukan wasa MUSKAN ta kaimata ta turo dan karamin bakinta tace Allah meena Bana son hk fa.”
“Ai gsky na fad’a anyways mu bar zancen kawai.”
“Mum ce da wata Yar uwarta Aunty maijidda suka shigo dakin fareeda na’a biye da su, har bakin gado inda MUSKAN Take Mum taje ta zauna.”
“Daughter ciwon Kai ko? Nasan za’a Rina sabida yawan hayaniya da gajiya sannu yanxu Zan Kira FARIS d’in ya saimiki magani, yanzu ki tashi a shiryaki ga Aunty maijidda nan Zan turo Aunty Sis (ummu sultan ) su shiryaki kinji ki daure.”
“Aunty maijidda sai kuyi hanzari sabida kar yan daukar amarya su zo baku shiryaba yanzu as Aunty Sis zata shigo.”
“Tana fita Ba dadewa sai ga Aunty Sis, nan ita da Aunty maijidda suka shige ciki da MUSKAN.”
_naso binsu daga ciki dan dauko rohoto amma mommah (Aunty sis) ta zunguro kaina ta koroni waje wai nayi karama kar naga abin manya_
.
“Wanka suka Mata da ruwan turaruka, jikinta sai sheki take zubawa da kamshi ga shi kuma ta sha gyran amare wacce Yar Maiduguri ta Mata.”
“Cikin mintuna 30 su aunty sis suka shiryata cikin wata milk color lipaya jikin lipayan duk stones da flowers Wanda kalan flowers din golden color, MUSKAN ta fito daban kamar wata shuwa Arab ta zama ga wani fitinanen kamshi dake fita a jikinta.’
“Bayan an bata hadin amare taci takuma sha na sha nan Aunty sis suka ja hannunta zuwa falo inda su, Hauwa. M. Jabo, banaxir umar, ummu beenah, su batul mamnan, dasu Aunty Sdy Jegal, Ya hajja ce duk suke zaune dasu Mum.”
“Bayan an zaunar da ita aka ta zuba Mata nasihohi hade da sirrikan rike miji, kamar su tsabta, kissan magana, kissan tafiya na kwanciya, gyran jikin mace, kula da Miji, da sauransu.”
“Ita dai MUSKAN shiru tayi dan duk sun sata kunya kanta a kasa suka jera zuwa wajen Dad, dan yan daukar amarya tuni sun zo.”
“Bangaren Dad zaune yake da shi da FARIS nan Mum da MUSKAN suka zauna bayan sunyi sallama an musu iso.”
“Dad shima ya hada MUSKAN da FARIS duk ya musu nasiha sosai mai ratsa jiki, bayan yasake jaddadawa FARIS kan ya rike MUSKAN amana Dan ita amana ce wajensa, karka cutar da ita, kazamo mai faranta Mata da share Mata hawaye, banda cutarwa duk da nasan Baxakayi Ba but FARIS Ka kula.”
“Da irin wadannan nasihan yata musu anyavasa izinin tafiya da amaryarsa.”
“MUSKAN kuka ta soma ganin dad yace su tafi, shima Dad kwalla ya dinga shara FARIS ganin Baby boo na kuka kuma yanajii har cikin zuciyarsa yasa sa varin gidan gabadaya sabida he can’t stand watching his baby boo crying.”
“Har bakin mota Mum ta rakata hugging din Mum tayi tanata kuka su fareeda da humaira duk suka rufomata suna tayata da kyar aka ban bare ta jikin Mum aka sata mota nan aka dau hanyan gidanta dake unguwar game village.’
“Gidane dayaji kayan alatu Dana more rayuwa, upstairs ne, falon gidan guda uku daya na FARIS Wanda ya kasance komai nacikinsa blue and white har bedroom haka, sai kuma falon MUSKAN daya kasance pink and purple, falon baki kuma komai red and arsh color.’
“Bangaren kayan kitchen kuma ba’a magana komai daga Dubai akayi order duk wani abin yayi na kitchen Dad ya saimata kitchen dinta babba da store dinsa.”
“Dakuna 6 ne a gidan, daya na part na FARIS, daya na part na MUSKAN sai guda biyu kuma Wanda akayisa na yara, dakuma biyun na saukar baki,.”
“Komai na gidan yayi kyau duk waenda suka kawota sai sun yabatsarin gidan, sai 9:00 yan kawo amarya suka watse bayan Aunty sis tasake yiwa muskan durln dinta nasiha suka tafi, nan aka bar MUSKAN dasu fareeda, meena da kubrah, sai Yar rigamata Mjay dasu little, xubie, cute xarah, huddalah, yar fucika,da dai sauransu sunsa MUSKAN gaba sai tsokanar ta suke.”
“9:30pm dadai FARIS da abokansa Anwar da Aliyu, sai su Mr fauxy, Dr sameer ameer, Dr meerah, al’amin, el Bahrain, da dai sauransu suka rako ango FARIS.”
“Suna jiyo sallamar angwaye suka lullube fuskar nan suka sake sambada turaren wuta gaba daya gidan ya gwaraye da kamshi.”
.
“Da sallama suka shiga bayan an ansa musu suka gabatar da abinda zasu gabatar, su Mjay sai fari da ido ake dan anga mr fauxy har da kashe murya wai ita ala dole taga handsome lolx.”
“Nasiha su Mr fauxy sukawa ango da amarya bayan sun musu fatan samun zuri’a d’ayyiba suka musu sallama, har wajen motocin su FARIS ya rakasu.”
“A kunne cute xarah da huddallah suka rad’awa MUSKAN wani Abu Wanda duk jin gulmana ban Kai ga jiba sai da na hakura, hannu suke dagamata suna kanne Mata ido daya.”
“Bayan FARIS ya rakasu ya dawo ya rurrufe ko ina ya wuce dakin MUSKAN, a tsakiyar gado ya taddata Tasha lullubi, zuwa yayi har inda take ya yaye lullubin wani kamshine ya bugi hancinsa nan ya lumshe idanunsa yace.”
“Tsarki ya tabbata ga allah da mallakamin wannan kyakyyawar, yakuma vani ikon saminta matsayin matar aure hakika nayi dace.”
“Hannu bibbiyu tasa tana kare fuskarta dan wani fittinannen kallo da FARIS ke binta da shi.”
“Baby boo kunyata kike ji? Pls ki bud’e fuskarki, ko kina so kisani hawan jini ne, kinsan yadda na azbatu da rashin ganinki a kwanakin nan Ku pls kibud’e hannu yasa kan Nata hannun ya cire Nata daga fuskar.”
“Murmushi ta sakar masa shima maida Mata yayi yace ki tashi muje muyi alwala mu nuna gdyr mu wajen ubangiji.”
“Alwala yaje yayi bayan ya fito itama taje tayi, nan ya jasu sallah raka’a biyu vayan sun yi sallama ya dafa goshinta ya musu addu’oi da dama nasamun zaman lpy da zuri’a ta gari.”
“Kallonta yayi yace Baby boo tashi ki mikomin wancan ledar, tashi tayi ta d’auko ta mika masa, tashi yayi yaje ya dauko tray da tumblers cup ya dawo ya baxa Kazan kan tray ya bude fresh milk ya juye a cups.”
“Matso ki ci yace da ita Yana kaffeta da ido.”
“Uhmmm nifa a koshe nake.”
“A’a ban yardaba yaushe hid’ima ya barki kika ci abinci, wlh ko kizo kici kona d’uramiki.”
.
“Jin yace zai d’uramata yasata matsowa da sauri, can kasan zuciyarta tsoro ne ya cika dan su cute xarah sun gayamata ta sake taci kazar wlh shima sai yayi abun.”
“Jinta kawai tayi a cinyar mutum xatayi ihu taji yace shhhh nine FARIS oya bude bakin ki ki daina tsoro ba abinda Zan miki.”
“A tsorace ta bude bakin nan yata feeding dinta har saida ya tabbata ta koshi ya kyaleta, shima yaci nasa.’
“Bayan sun gama ci ya umar ceta da ta sauya kaya tazo su kwanta yabata wani sleeping dress yace tasa.”
“Toilet ta shiga ta kullo kofar ta sa kayan, amma ina bazata iya fita FARIS ya ganta da shigar nan Ba OMG ya zanyi, zama tayi kan seater’n toilet din.”
“FARIS dama yasan za’ayi haka, mikewa yayi yaje kofar toilet din yace Baby boo ki fito Ba abinda Zan miki kinji.”
“Shiru tayi can kuma tace toh Ka kulle idonka sai in fito.”
“Ok na kulle ki fito.”
“Bude kofar tayi ta leka saida ta tabbatar da baya ganinta tayi gudu sai kan gado ta shige cikin blanket din.”
“Dariya yayi yaje shima ya shige cikin blanket din ya ringino inda take ya rungumota.”
“Tanajin ya rungumeta jikinta ya dau rawa, FARIS ganin haka yace Baby Boo ki daina tsorona Ba abinda Zan miki kawai ina son jin dumin jikinki ne pls let me be Baby boo.”
“Ajiyan zuciya ta sauke, daga nan kuma batasake cewa komai Ba haka shima, a rungume sukayi bacci…….
.
_*MusFar*_ asuba ta gari………..
.
Washegari bayan sun idar da sallah’n Asuba suka sake komawa bacci nan ma FARIS saida ya rungumeta.”
“8:30am na safe MUSKAN ce ta farka ganin ta rungume da FARIS yasata murmusawa kawai a hankali ta soma janye jikinta daga nasa amma shi sake kankameta yake, tayi haka yafi a irga can dabara ta fadomata tadau filo ta cusamasa kan ta zame jikinta daga nasa, toilet ta fada don wanka.”
“koda tafito a toilet din bata hangosaba dadi taji ta soma shiryawa in less than 30mins ta shirya cikin wata blue materiel dinkin skirt ya kamata kamar ajikinta aka dinka mazauninta duk sun fito haka rigan breast cup din yafita Ba karya, Ba wata make up tayi va simple one tayi applying amma tayi kyau, tafeshe jikinta da turaruka masu kamshi ta gyra dakin Tass nan ta kunna turaren wuta ta fice. ”
“falo ta nufa nan ma ta jona turaren wutan gabadaya gidan ya gawraye da sansanyan kamshi, tana zaune kan couch na falon TV na aiki ta kunna tashar MBC Bollywood suna repeatation na madhubala shi take kallo aka soma kwankwasa kofa, koda taje ta bude drivern gidan Mum tagani bayan sun gaisa yabata basket yace inji mum ne amsa tayi tamasa godiya tace ya gaidamata yan gida.”
“ciki takoma bayan ta jera food flasks din kan dinning ta maida basket din kitchen, tafiya take zuwa falon amma tanaji kamar wani na kallonta, kamar ance ta juya takalli stairs din ido hudu sukayi yana Mata murmushi’n sa mai narkar da zuciya sanye yake cikin kananan kaya farin shirt din polo da denim jeans hannunsa sanye cikin aljihu yazubamata ido ko kiftawa bayayi tamatukar masa kyau.”
“muskan ganin yadda FARIS ke kallonta yasa tasoma takawa har inda yake taje baisaniba, hannu tasa tana waving face dinsa amma baijita Ba sam saida ta take masa kafa yayi Dan Kara Arrrhhh Baby Boo yaushe kikazonan? ya tambaya yana,shafa sajen sa da suka kwanta.”
.
“tundazu,and why d look na canza ne.”
“oh c’mon Baby Boo kinyi kyau sosaine yakai hannu zai rikota,da sauri taja baya tace Allah Bana so kasauko kayi breakfast, naki bazan saukoba sai kinzo kin rikemin hannu, dariya ta bushe dashi, ganin tana mai dariya yasasa nufota, tana ganinsa ai Ba shiri ta arce da gudu, shima binta yake haka sukayita zaga falon bai kamotaba da kyar ya kamota bayan sun zube kasan carpet sai haki suke ga FARIS ya danneta da duka hannayensa biyu tana kasa yana samanta, ita kam duk ta tsorata zuciyarta sai dukan Tara take.”
“can bayan numfashin su ya daidaita FARIS yaga yadda MUSKAN tayi wuki2 da ido ya yadda zuciyarta ke bugaawa dariya ya kwashe dashi saida yayi mai isarsa tukun yace fair fair baby boo, jibi yadda kike tsoro zuciyarta yanuna da yatsa yace nan duk bugawa yasake bushewa da dariya vayan ya sauko a kanta ya janyota zuwa kirjinsa ya kwantar da ita yace feel free Baby Boo Ba yanxu Zan miki wani abuba kunnenta yaje yacemata yarinya saimun bar 9ja tukun zakisan kin auri gwarzon namiji ya saketa yana mikewa yana Mata dariya.”
“up ya mikamata hannunsa, itakuma duk ta gama tsorata da kalamsa, ganin batada niyan mikamai hannun yasasa tsunkuyawa ya daukota kamar Baby, kafa take bubbugawa let me down, ya FARIS saukeni kasa zanyi tafiya da Kaina haka take fada amma shi ko ajikinsa har dining yaje kan ya direta yace am starving serve me.”
“karamin bakinta ta cuno gaba ta soma zuzzubamasa breakfast, soyayyen chips da koi, sai kuma peppe soup na kaza, tajiyemasa tajuya zuwa nata kujeran zata zauna yace xonan kizauna muci yanuna Mata laps (cinyansa).”
,
“Marairace fuska tayi a shagwabe tace pls ya FARIS let me sit here ta nuna sit dinta, I said no akan laps Dina zaki zauna and am d one to feed u so come and sit down. ”
“Kallona take amma bata je ta zaunaba, yace okay toh shikenan tunda bazaki zaunaba muje d’aki toh na karbi hakkina na fasa Bari muje London din yanxu zaki ban yayi maganar in a serious tone yana kuma binta da kallo yana son ganin reaction dinta.”
“jin abinda yace yasata tsurewa da sauri tace no pls am sorry wlh am gonna sit on ur laps amma karkamin komai ta kare maganar ready to cry.”
“ dariya yake son yi amma ya gimtse yace okay zo ki Zauna, Ba musu tazauna yarinka feeding dinta yana binta da wani mayen kallo har suka kammala cin abincin, Tare suka kwashe kwanukan suka Kai kitchen suka dawo falon da zama suna kallon TV ”
“Kamar 11:00 suka soma yin baki Dan haka FARIS ya fita daga gidan zuwa nasa yawon. ”
“Ranar currr gidan da baki ya cika su fareeda ma sun zo suna ta Mata tsiya. ”
“sai yamma liss mutane suka watse bayan ammata girki an kimsa gidan sai kamshi yake zubawa Dan turaren wutan da aka zuba.”
“ FARIS bai tashi dawowaba sai bayan sallah’n isha koda yazo bayan sunci abinci as usual suka Dan taba hira suka kwanta Ba abinda yamata kamar jiya haka sukayi bacci. ”
“ haka suka ci gaba da zama Ba abinda FARIS kema MUSKAN ya cika alkawari ko wassani bai Mata har ta soma sake jiki da shi bacci a rungume kam tasaba dashi da cin abinci kan laps dinsa, yanxu sun cika one week da aure kuma A yau din zasu koma London, duk sunbi gidajen yan uwa sun musu sallama waenda basa Abuja sun kirasu a waya, yau da dare zasu gidansu Mum daga can kuma su wuce airport Dan jirgin 12:00pm na dare zasu bi, komai sun shirya MUSKAN duk a tsorace take Dan tasan suna zuwa London Nata ya kare.”
“ bayan sunje gidan su Mum, nan Dad ya ajiyesu yasake musu nasiha sosai mai ratsa jijiyoyin jiki yakuma sake jaddadawa FARIS amanar MUSKAN dayabasa, haka itama Mum tamusu nata nasihar kan ta janye MUSKAN zuwa dakinta.”
,
“a can daki bayan Mum ta ajiye MUSKAN ta soma bata kissa kamar haka tace.”
“Abu na frko da Zan soma gayamiki daughter shine tsafta.”
TSAFTA yana daya daga cikin abinda ke sake janyo hankalin mijinki gareki, idan nace tsafta Bana nufin na jiki kawai harda muhalli nake nufi, KO da yaushe jikinki, gidanki, dakinki, sukasance a tsaftace kuma suna kamshi.”
“ Na biyu girki, nasan kiniya girki amma kisake dagewa ki goge da iya girki, dandanon abincinki kansa koda mijinki na cikin wani hali da zarar yaci abinci yaji duk damuwarsa ta yaye.”
“ sai kuma tafiya da lafazi, idan nace tafiya inaso kigane tafiya yakasu kashi kashi, toh fa dole kirinka canza salon tafiya kuma kina rankwasa kina karkadawa kina juyawa, saikuma lafazi kikasance mai tattausa lafazinki mussman ga mijinki, kina shagwa6a kina lankwasa harshe hakan Ba karamin burge maza keyiba.”
“kwalliya da shagwa6a, kirinka kwalliya kina sa kananan kaya dazasuja hankalin mijinki gareki, shagwa6a ma na sa miji ya susuce kanki.”
“kizama mai rike sirrin mijinki kada ki yarda wasu su ji kanki da mijinki, idan yabatamiki toh kisan ydd zaki gyra vasai kinje kina fadawa kawaye Ba.”
“mode of kwanciyar aure da sirrikansu duk Mum ta bata kissar sa shima.”
“Nan ta hadamata mayuka da turare masu kamshi da dai sauransu, ta hadamata nasha Dana ci dafawa da sauransu.”
,
“ godiya sosai tayiwa Mum harda kukanta, lallashinta Mum tayi tace am just lyk a mum to you feel free with me kigayamin duk matsalarki kar ki rinka biyemin and wannan abin danake miki is nothing daughter u deserve more than this.”
“ hira sukayi da Mum kan ta koma wajen su fareeda can dinma hiransu suke kamar Ba gobe ita dai MUSKAN surely tasan she’s gonna miss them.”
“Sai 10:30 suka tashi zuwa airport dukansu suka je 11:30 suka soma shrye shiryen tafiya nan fa MUSKAN hankali yasake tashi yanxu shikenan zata tafi tabar su mum dasu humaira she couldn’t imagine.”
“Lokacin saura 10mins jirginsu yatashi sukayi sallama tashin hankali kuka MUSKAN keyi tayi hugging din su Mum very tight tana kuka Mum ma duk iya karfin halin da tayi saida ta zubada hawaye su fareeda kam shabe shabe fuskarsu da hawaye, Dad na can gefe shima yana jin zafi rabuwa da MUSKAN daughter, FARIS duk tausayinsu yake ji yasan sun shaku da juna gashi MUSKAN tazama _*Jinin jikinsu*_ da kyar yasamu yaja MUSKAN zuwa jirgi suna dagawa su Mum hannu har suka shige cikin jirgin.”
“in less than 5mins jirgin su yadaga zuwa London, MUSKAN na kwance jikin FARIS tayi shiru tana sauke numfashi a hankali shikuma sai aikin bubbugamata baya yana calming dinta with his sweetest words and love har tasamu tayi bacci, ajiyan zuciya ya sauke shima yana kallon kyakyawan fuskarta yace sleeping beauty.”
.
“Haka sukata lulawa sararin samaniya har zuwa lokacinda zasu isa……
Tafiya mai nesa sukayi almost na 4-5hr kan suka isa garin _*London*_ duk a gaje suke liss Dan zaman jirgi, daga wajen aikinsu FARIS driver yazo daukar su zuwa gida.”
“ Tsakanin airport da gidan Ba wani nesa sosai bane a kalla zaikai kilometers 100, a haravar gidan driver yayi parking, gidane up stairs ginin turawa gidan Dan madaidaici Wanda yake dauke da part uku, part biyu a sama dayan a kasa, gidan yayi Ba karya danko a turai masu kudinsu ke mallakar gidaje kamar haka, akoi garden da swimming pool wajen hutawa duka akoi.”
“ gaba driver ya wuce da kayansu, MUSKAN sai kallon gidan take Dan yatafi da imaninta wajen kyau da tsaruwa ita kam wannan gidan yafi gidansu na 9ja tsaruwa, FARIS ne yadawo da ita duniyar tunani da ya rungumeta ta baya kansa bisa kafad’arta cikin husky voice dinsa yace baby boo gidan ya miki?.”
“ murmushi tayi ta juyo dashi tace sosaima gidan yamin.”
.
“ karan hancinta yaja yace gud gurl, muje ciki toh yaja hannunta a bakin falon ya danna wasu securities code sai kofan ya bude sai FARIS yace _*welcome to your home Baby Boo*_ Yana Mata murmushi, itama mayar masa tayi daga nan suka wuce ciki har sama driver ya wuce da kayansu nan suma suka haura, part dinta ya kaita bayan ya nunamata Nata dakin yace ta watsa ruwa shima zaije yayi wankan.”
“ Fita yayi tabi vayansa da kallo tana murmushi, tace My handsome tana rage kayan jiknta, toilet ta wuce ta shige jacuzzi tana sakewa kanta shawa cikin wannan yanayin ne maganar FARIS na sai sunzo London zata San shi cikekken namijine ya fad’o mata take zuciyarta ta buga tace nashiga uku nan tsoro ya rufeta a daddafe ta gama wanka ta fito ta shirya cikin English wears jeans da top, tana cikin feshe jikinta da perfumes ya shigo cikin 3quater jeans da armani top yayi kyau tunda taji kamshin turarensa taji takasa samun nutsuwa duk tasoma jin tsoro.”
.
“ chak ya dagata Yana jujjuyawa da ita kan ya direta yace My baby is looking beauty, taho muje kici abinci already nasa ankawomana, Ba musu ta bisa hannunta sarke cikin nasa har sukaje falon sa dinning table ya je da ita bayan yaja kujera ya zauna ya daurata kan cinyansa, jikinta duk rawa yake saida ya yacemata Baby ki nutsu Ba abinda zanmiki kinji just have your food, da taji maganarsa yasa ta d’an Sakin jiki dashi har suka kammala cin abincin.”
“ A falo suka yada zango bayan sun karasa cin abinci suna zauna almost 10:00 na safe a nan London, inda nijeriya kuma yake 7:00, kallo take na wata Indian film _Rajkumar_ shikuma FARIS yana dannedane cikin laptop dinsa sai misalin 12 suka Kira su Dad suka gaggaisa, wayan yabata suka sha hira da Mum dasu fareeda kusan 1hr tukun sukayi sallama, ta mikamasa wayansa, yace aikin kenan dama nasan idansu fareeda ne zakukai fiye da 1hr, baki ta murgud’a masa, yace zamu hadu ne ai dake yaci gaba da aikinsa, murmushi tayi a ranta tace bawani nan zamu hadu a Ina.”
.
“Ranar yini sukayi a gida Ba inda sukaje, misalin karfe 10:00pm na dare bayan MUSKAN ta shirya cikin night gown dinta ta haye gado, shima cikin pajamas dinsa ya shigo d’akin gadon ya haye ya jawota zuwa jikinsa, wasanni yasoma da ita yana aikamata sakonnin sa ta ko Ina na jikinta, duk jikinta rawa yake har tasoma matsar kwalla, FARIS duk ya fita hayyacinsa duk ya rabata da kayan jikinta yana Neman rabata da pant dinta ta fashe da kuka tana rike hannunsa tace pls karkayi Dan Allah, saketa yayi bayan ya koma gefe ya kwanta yana maida numfashi, itakuma ta dau riganta tasa da pant dinta takoma can karshen gado zuciyarta fal tsoro, bayan yakoma daidai ya ringino zuwa wajenta ya kwantar da kansa bayanta yazagaya Hanna’yensa a cikinta tana jinsa tayi shiru da haka bacci ya d’ebesu….
_Asuba ta gari musfar_
*** *** ***
_*1week later*_
kusan sati daya amma duk suna abu daya kullum saidai yayi wasanni da ita ya kyleta dan kuka take samasa themore yayi yunkurin yin sex da ita shikuma he pity and can’t stand seeing his own baby boo crying, dan kukanta na matukar damun sa baiso sam yaga shi yasata cikin damuwa, gashi yana cutar kansa dan ya kasance namiji mai sha’awa(desire) Maransa har yasoma masa ciwo,kullum yana cikin shan lemon tsami da lipton.”
“ Cikin week daya dasukayi FARIS yazaga gari da ita sunyi yawo sosai, kuma ya koma bakin aiki yanxu ita kadai ke yiniva gida sai 5:00pm yake dawowa gida,tun tana dan tsoro hartafara sabawa dazaran yafita, toh itakuma tana falo zaune ko ta fita garden tana shan iska.”
“Yau ma kamar kullum da safe bayan ta hada masa break yaci yafice dan tafiya office cikin shigarsa ya uniform na pilot wow! yayi kyau sosai hannunsu sarke da juna suka fita har haraban gidan wajen motarsa suka nufa marcedes benz kirar 4matic(300).”
“ Kallonta yake cike da sha’awa da so dan dreesing dinta ya tafi dashi matuka ,sanye take dawata lagis da top pink mai dogon hannu, baby boo ni zan tafi yace yana rike da habarta.”
“ fuska ta marairaice kamar zatayi kuka cikin tsigar shagwaba tace am gonna miss You and ni kadai kullum a gida wlh ba dadi ta kare maganar kamar mai shirin yin kuka.”
“ rungumeta yayi yana bubbuga bayanta yace am gonna miss u too baby boo, even me inbadan aiki yaxama dole injeba da zan zauna dake, karki damu kinkusa fara zuwa school maybe yau na taho miki da admission, and baxan yi dareba insha allah zan dawo yau da wuri kinji.”
“ kai ta gyd’amasa bayan tayi breaking hug din, tace safe trip sai ka,dawo ka kularmin da kanka kaji, insha allah kema haka baby boo yace oya goodluck kiss zakimin ya tsaya yana jiranta tayi.”
“ ido ta kulle ta kaimasa peck a cheek dinsa, shikuma ya jawota yabata nasa soft one a lips ,yashige mota yana dagamata hannu har ya fice daga gidn kan ta shige cikin gida tana missing dinsa.”
_*At office*_
“ FARIS Zaune yana danne danne cikin laptop gefensa ruwan lemon tsami da lipton duk hankalinsa na akan aikinda yake cikin laptop din , konkosa kofa akayi batare da dagoba yace come in.”
“Anwar da Aliyu ne suma sanye cikin uniform suka shigo har bakin desk din sukaje vayan sun zauna kan kujerun dake fuskantar na Faris, hey dudes ya akayine Faris ne yayi maganar amma har yanxu bai dagoba, lpy qalau angon Muskan baby boo fadar su, jin abinda suka fada yasasa dagowa yana musu murmushi,nan suka gaisa suka soma taba hira.”
“ Suna cikin hiranne Anwar ya kai hannu ya dau kofin gaban FARIS yana kokarin kaiwa bakin dan yasan FARIS da shan coffee, FARIS ne ya dago yaga Anwar yakai kofin bakinsa kanyayi magana tuni ya kafa a bakinsa har ya kurbe, dafe kai FARIS yayi cikin ransa yace shikenan Anwar yasan mai nake ciki oh gosh ya zanyi.”
.
“ Nuna FARIS yayi yace don’t tell me kana shan abinann dan rage ma sha’awa, dagowa Aliyu yayi , yayi exclaiming rage sha’awa, FARIS Anwar yakira sunansa yace kana nufin yanxu duk sonda kakema Muskan tana iya hanka hakkinka? .”
“ No thats not what u mean kawai ina shane but ba’abinda musk….. bai karasa ba Aliyu yace don’t speak the lie to us bakayo and karkasoma huh!, ko ka manta we are tripple frnd and brother bama boyewa dayan mu secrect c’mon munsan MUSKAN tana hanaka are we right?.”
“ Dagowa yayi ya kalli abokansa maganarsu gsky ne buh taya zai gayamusu baby boo taki ta amince dashi he think that not possible, amma wata zuciyar tace they Are your childhood frnds ,u never keep a secret from each other ka gayamusu maybe they had a way to solve your problem da wannan shawaran yake hukuncin sanar dasu, take ya fadamusu matsalarsa.”
“ Dariya sosai suka barke dashi har sun soma kular dashi sai da sukayi mai isarsu harda rike ciki tukun suka daidaita, Anwar yace Love ,shege dude yanxu dan kanasonta kana tausayinta yasaka kin karban hkkinka gashi yanxu kaxo kana shan lipton da lemon tsami chab ai kakusa ma kwanciya a gadon asibiti lolx yacigaba da dariya.”
.
“ Abin ya kular da FARIS yace look dan ta fadamuku problem dina it does not mean nace kumin dariya i want a advice from u guys yazanyi kunsan how am suffering.”
“Aliyu ne yace i had an idea tunda ita kullum cikin cewa tsoro take toh zama tagama tsurewa for the look i take to muskan nasan tanada tsoro, zo kuji yace nan duk suka hada kansu waje daya suna magana.”
_Duk jin gulmata sai da na hkura dajin wannan dan naso daukomuku rohoto amma Tureni FARIS yayi yace na cika jin gulma, koma menene ku viyoni dan ji meye idean su d’in_
“ Dariya suka bushe dashi dukka FARIS yace shege ashe kanka na ja lolx wannan haka zanyi is a good idea kuma nasan it will work.”
.
“ anwar yace yes ka gwada kawai dude, nan suka cigaba da hiransu suna tattauna kan aikinsu.”
_6:20pm_
Daidai wannan lokacin FARIS ya iso gida a gajiye ya iso koda yayi parking cikin gida ya nufa, a falonsa ya tarar da ita tana kallo, da sallama ya shiga, tasowa tayo taxo wajensa ta amsa masa tana kokarin karban briefcase na hannunsa, kallo yake binta da shi mai cike da tsansar so da sha’awa sanda dawo tace bakinta yabi da kallo yana cize lips dinsa baby boo sannu kinyi kyau, tasake wanka yanxu tana sanye dawata doguwar riga yar kanti purple yamata kyau, Tnz tace ,yace am starving muje nayi wanka kiban abinci i miss You so much, murmushi tayi tace me too handsome.”
“ Daki suka wuce ya rage kayan jikinsa ya shiga wanka , itakuma ta nininke kayansa ta sake ciremasa wasu kanana na shan iska,kan ta fice daga dakin.”
.
“ cikin minti 30 yagama wanka ya shirya bayan ya idar da sallah, yana cikin gyra suman kansa tashigo dakin,barin abinda yake ya je ya rungumeta kissing dinta ya fara yana aikamata sakonninsa masu rikitarwa gado sukafada sun dau kusan 5mins a haka kan ya kyaleta a kunnenta ya rad’amata cewa ta shirya yau zai karbi hakkinsa and no favour, ya mike yace muje am starving ba musu ta bisa , abinci suka ci kan suka dawo falo da zama suna kallo, can ya fita wajen gidan mai gadi yaje yasamu sukayi wata magana amma bansamu damar jiba yace in lessThan 30mins yakeson ya gudanar da aikin kudi yamikamasa kan shige ciki.”
.
“MUSKAN Na zaune duk ita tsoronsa takeji yau cikn ranta kuma ta kudiri niyan yau a dakinta zata kwana kuma ita kadai tana shiga zata sa lock kawai, tana cikin wanga tunanin FARIS,ya shigo kauda kai tayi gefe, shikuma ganin haka yasasa mazgewa dan yasan hujjanta nayin haka, zama sukayi suna kallo amma ko “A” basa cewa dan uwansu.”
.
” _10:30pm_ Mikewa MUSKAN tayi tace handsome zanje na kwanta sai da safe, Baby boo bazamuje tare bane? No a d’akina zan kwana yau kaima kaje d’akinka, Oh is that so haka kikace? eh , ok amma bakya jin tsoro i think vakya iya kwana ke daya? Eh but yau zan fara nidai kawai karkazomin daki, Dariya yakesonyi amma sai ya gimtse yace ok bazanzoba kinji jeki, yawwa daka kewta saida safe tacemasa bayan tasoma tfy, yace sound sleep and swtdreamx.”
“tana varin wajen ya varke da dariya yace see her zaki dawone ai yarinya shima daki yanufa ya sauya kaya zuwa pajamas ya kwanta yana dariya.”
.
“MUSKAN na shiga daki tasa lock tace tab ai bazan yardaba hka kawai ni wlh ban shiryaba tsoron sex din nake ancefa akoi wuya kuma wlh daga ganin FARIS zaiyi mugunta, surutu take ta rage kayan jikinta ta daura towel na wanka wanda yake rabin cinyanta ta baza gashin knta suka zubo a kafadarta toilet ta nufa tana karkadawa tana waka cikin ranta , jacuzzi ta shige take tasakarwa kanta ruwa idonta lumshe tanajin dadin ruwan.”
“ FARIS kwance sai juyi yake kan gado yana jiran yaji result daga dakin MUSKAN, cikin ransa kuma yace ko daniel gate man baiyimasa aikin daidai bane yace let see then.”
.
_10mins back to MUSKAN’S room_ ido a bude lokacinda tagama wanka mai zataji da gani? wata kulliya(cat) yake kuka meaoow yana kallonta ido ta waro waje hade da sake wata razanannen kara tasabi towel d’inta tayi hanya waje ihu take rusawa tana kiran HANDSOME,FARIS help kulliya zai cizeni.”
“ Daga dakin FARIS yana kwance yasoma jin ihun MUSKAN yes it work yafada ya mike zuwa dakinta.”
“Koda yaje kofan dakin ya tarar a kulle gashi tana ta ihu tana kiran sunansa, MUSKAN yace yana bubbguga kofar a a.m here kinji open the door , daga dakin tace i cant zai cizeni, noo ba abinda zaiti try and open the door babe, da kyar ta iya bude kofan, ai tana budewa ta rungumosa tace Handsome cat a toilet dina pls kakaini dakinka i can’t sleep here tana mammatsesa tana shigewa jikinsa ,duk tasaukar masa kasala da kyar yayi controlling kansa yace.”
.
“ ok naji but bazaki je dakinaba kizo muje ki nunamin kulliyar inciresa d’akinnan toh, no pls kaje kai kadai, what! a’a wlh nima ina tsoro saidai muje tare, no kakira daniel toh ya cire,tana rungume dashi suka kira daniel yazo yacire.”
“ Toh anciremiki sai ki koma ki kwanta nima kwanciya zanje nayi ya cireta a jikinsa ya juya yana barin wajen da sauri ta zo tasake rungumesa tace pls mu kwana tare inajin tsoro, no ni bazan kwana ananva saidai inke zaki bini, tuni ta manta da batun hakkinsa tace ehh zan bika muje, dariya yayi yace yarinya muje, haka suka jero har zuwa dakinsa , gado ya haye abinsa yace zo ki kwanta mana.”
“ Fuska ta mairairaice tace pls ka rakani indau kayan bacci ka kallifa tanunamasa jikin, idanuwansa ne sukayi tozali da santalasantalan cinyoyinta ga boobs, dinta da skin dinta mai daukar ido , yace bazanjeba nima ina tsoro ki zo ki kwanta a hka ya juyamata baya yayi kwanciyarsa.”
.
”tsayuwa taci gaba dayi can taje ta haye kan gadon tashige blanket, yana jinta ta kwanta ya mirgino zuwa inda take ya rungumota take jikinta ya dau rawa, shiko romancing dinta ya soma ba kakkawta , duk tagama tsorata da yanayin yadda yake tafiyar da ita yau sai kuka takemasa amma shi ko ajikinsa bata ankaraba taga ya kashe bed side lamp yana cire rigarsa take takara volume na kukanta tana basa hkr amma ko jinta bayayi, lokacinda yayi niyar shiganta yaji sautin kukanta yace idan bazakiyi shiruba just kibardakina toh, a ranta tace ina zanje in nabar dakinsa i had no choice than to stay here shiru tayi tace na daina kukan, good yanxu sai kiban hadin kai na tafiyar dake a hankali if not kikayi gardama na miki da karfi, shiru tayi yaci gaba da sarrafata.”
“ Can bayan duk yakashemata jiki ya soma kokarin shigarta amma ba hanya duk da a hankali yake tafiyar da ita, ido ya rufe kawai ya shigeta zuruff, Ihu tasake lokacinda taji abu cikin farjinta shikam ko ajinkisan ganin yasami hanya yasa sa soma cika aiki ina ganin haka naja daga waje na kullo musu kofan dakin.”
“ Daga waje ina jiyo ihun MUSKAN tana kiran Dad,mum,fareeda,humaira duk su kawomata dauki amma ina ba ko daya, FARIS kam duk ihun da take da kirayekiraye baisa sa sauraramataba bashi ya bartaba saida ya tabbatar ya gamsu tukun ya kyaleta, ya koma gefe ya kwanta yana maido numfashi.”
.
“ Ya dau kusan 5mins tukunna ya koma inda yabar MUSKAN kwance hawaye na fita daga idanunta suna bin kuncinta , Baby boo yakira in his husky voice, banza tayi dashi takiamsawa tama juyamasa baya, murmushi yayi dan yasan lefinsa, sukutota yayi kamar baby yayi hanyan toilet da ita tana bubbuga kirjinsa tanacewa ya sauketa amma yaki dan yasan bazata iya tafiya ba dan she sofer a lot da abinda ya mata.”
“ Cikin toilet ya direta ruwan xafi ya hadamata da dettol yasa ta aciki kara tasake tana neman ficewa cikin ruwan ya maidata yasoma gasa ta, kuka take kuma taki ta bude ido ta kallesa shi, saida yatabbata ta gasu tukun ya barta tayi wanka, shi da kansa ya nadeta a towel ya daukota kamar baby har gado ya direta bai dametaba ya kelleta ta kwanta a haka.”
.
“ haurowa yayi gadon ya rungumeta tsam a jikinsa yace MUSKAN allah ya miki albarka, hakika kin shayar dani zuman da ba’ika, ni’imarki ta dabance ,kuma kinyi kokari wajen kawon min budurcinki wannan shine babban kyauta dakikamin wanda bazan taba mantawa dashi, kin cancanci na yabamiki kuma tukwaicinki ta dabanne Ina sonki I love u so much baby boo namiki alkawarin kasancewa dake har abada cikin jin dadi ko wuya _*ina tare dake*_ zan zamo mai tausayi gareki da share kukanki, haka kuma mai saki farinciki Allah ya barmu tare, haka yacigabada kagayamata kallamai masu dadi da samata albarka yana shafa gashin kanta yana bubbuga bayanta har bacci ya debesu zuciyarsu fal farinciki dukkansu…….
*** *** ***
_*Washegari*_
Tunda sukayi sallar asuba MUSKAN ta gudu d’akinta taki hada ido Sam da FARIS.”
Koda tazo tfy ya tambayeta ko bazataji tsoroba, tace masa ta daina jin tsoro ta fice mar daga dakin, dariya FARIS ya kwashe da shi, yana jinjinawa MUSKAN, yana ganin yadda take d’ingisawa harta fice.”
“Tana faman d’ingisawa sabida yadda kasanta kemata rad’ad’i ga yadda take jin zazzabi na Neman rufeta, ga tsoron d’akinta datakeji amma haka tayi karfin hali tashige dakin hade da hayewa gado taja blanket ta ruhu dashi tana ta karatun Qur’an a ranta har bacci yasaceta.”
“Ba ita ta farkaba sai 9:00 na safe, da kyar ta iya tashi a daddafe ta yi wanka tagasa jikinta da ruwan dumi kan tadan ji dama dama, shiryawa tayi cikin wata farar shirt anyi rubutu da baki da manyan harufa kamar haka _*BE MY SWEET*_ da red pencil trouser tasa ta yane kanta da bakin d’ankwali tazubo da gashin kanta kadan a gaba, jikinta sai fitar da daddad’an kamshi yake sabida yadda tayi wanka da perfumes, hoda kadai tashafa da wet lips, sai idonta da tamasa ado da kwalli,tayi kyau duk da bawata makeup tayiba.”
” tana cikin gyra kan gadonta taji alamar Ana bud’e kofar d’akinta, gudu tayi ta shige cikin labule ta buya Dan ita kunyar abinda sukayi jiya da FARIS take.”
“FARIS ne yashigo shima cikin shigar kananar kaya Sun kasance farin shirt da blue jeans shima jikin shirt dinsa anyi rubutu da manyan harufa shima kamar haka _*FINALLY I GOT HER*_, murmushi yake yaduba cikin d’akin bai ganta yayi tsammanin toilet take d’an haka yasoma kiranta _*baby boo*_ yaji shiru can yace kardai har ta tashi amma ina taje badai kasa ta saukoba sabida daga can nake, huh maybe tana cikin toilet dinne, mikewa yayi da niyar bude toilet d’in ya tsinkayo kafarta a waje.”
“Inda take ya nufa yana killer smile dinsa, hannu yasa ya yane labulen sai ido hudu sukayi da MUSKAN, saurin runtse ido tayi, FARIS na ganin haka ya daga sama yana juyawa da ita daga nan ya direta kan gado yace so kin buya sabida Karna ganki kuma kike ji ina kiran sunarki amma kikaki ansani ko.”
” shiru tayi idonta still a rufe taki budewa kuma taki yin Magana.”
“Oh I see kunyana kike ji you won’t open your eyes and won’t talk ko, ok Bari nakara abun jiya toh maybe that would let you talk and open the eyes, yasoma cire rigansa Yana daddadaneta da hannayensa.”
“MUSKAN na jin haka tayi saurin bude idonta tace _*MUSFAR*_ na bude fa pls stop it don’t karkayi wlh akoi zafi.”
.
“Chak ya tsaya yana nanata sunan da takirasa dashi yanzu, yace na tsaya what a nice and unique name Baby Boo.”
” Uhm nidai Ka tashi a kaina Ka danne ni tace a shagwabe.”
“Toh na tashi, tell me what I ask you about.”
“Zama tayi tana kallonsa kallon So da kauna cike da _*SHAUKIN SO*_ ( Littafin NEERATLURV & AAJ ) tace _*MUSFAR*_ yana nufin MUSKAN-FARIS, yankesu nayi yazama haka.”
“Rungume ta yayi yana kaimata kiss yace thanks Baby boo the name was unique and I lyk it zanna kiranki dashi kinji.”
“Kai ta gydamasa tace na ji muje yanxu na hadamana breakfast kaga mun makara ta fad’a tana mikewa.”
“Hannu yasa yajawota sai kan cinyarsa ta zauna, yace you don’t have to namiki your breakfast is ready.”
.
“Don’t tell me tundazu Ka tashi har Ka yi breakfast.”
Kinawasa Dani yau zakici girkin MUSFAR yafada yana kanne Mata ido (wink).”
” oh MUSFAR naje dai naci jagwalgwalo MUSKAN tafada tana murmushi.”
“Ok naji but anyway I had a surprise for you muje tukunna.”
“A Jere sukayi falonta har dining area ya kaita ya zaunar da ita, abincin ya xubamata chips da soyayyen koi yahadomata shayi mai kauri,shima yahadawa kansa, suka soma ci cikin SO suke ci har suka kammala.”
“Tare suka kai k’wanukan kitchen suka wanke da suka gama jerawa, yace toh muje na nunamiki surprise d’in.”
“Hannunta yaja har zuwa waje inda ake parking na motoci, wajen wata mota suka nufa an rufesa da tampol.”
.
“Ido kawai take binsa dashi harya yaye tampol din yace this is for you MUSFAR, nakine kyauta namiki duniya da lahira kuma ga wannan envlope ya mikamata yace admission later ne nasamomiki gurbin karatu a Oxford university fannin physiotherapy zaki karanta.”
“She stand totally speechless takasa furta komai, ga new car benz 4matic (300) and her admission da kyar tayi gaining courage tasoma masa godiya with her sweetest words.”
Hanata yayi yace godiyan ya isa she deserve more than this awajensa Dan haka she should stop it.”
“Da murna takirasu mum tagayamusu, murna sosai sukayi sukamata addu’ar Allah sa a tsufar lpy, sukama FARIS gdy shima.”
“Su fareeda sunyi da ita tafadamusu wani abune ta baiwa FARIS yamata wanga kyauta, taki tace secret ne Nata da mijinta.”
.
“Ranar ko aiki FARIS bai jeba a gida suka yini suna zuba love.”
Ya kirasu anwar yasanar dasu bazai zo aikiba Baby boo Ba lpy, tsiya suka hau masa suna cewa plan dinsu has soccide , kuji dashi yace dasu…
*** ***
_Life moves on_ yanxu komai ya daidadita almost 2week Wanda yayi dadai da watan aurensu daya kenan.”
MUSKAN ta mulmule, harta soma zuwa school, yanxu bata da wata damuwa dayawuce makarantar ta da kula da mijinta saikuma addu’ar da takema iyayenta nasamun rahama da gidan aljannah.”
Kullum suna manne da FARIS duk inda take yana can shima, yana kula da nuna soyayyarsa gareta Ba laifi yanxu ya mulmule shima yasake cika yaxama cikkeken namiji.”
MUSKAN na kokari wajen farantawa FARIS, kuma tana kokari wajen biyamasa bukatarsa Coz FARIS Nada sha’awa kusan kwana bibbyu saiya kusanceta kuma tana daurewa bata taba nunawa FARIS gaxawartaba, shiyasa shima kullum yana cikin faranta Mata da kuma ji da ita.”
“Yanxu MUSKAN ta koya driving ita da kanta take Jan motarta zuwa school da sauran wajaje .”
Yawanci suna fita shakatawa ko kuma shopping, duk wajen aikinsu ansan MUSKAN.”
“Su Anwar Ba Wanda yakaisu jin dadi ganin there only Frnd cikin farinciki, yanxu kusan kullum gidan suke suna zuwa cin abinci.”
*** ***
_*Nigeria kauyen bebeji dake jahar kano*_
Faty ce da meemah ke shiga wata kuryan daji zasu wajen wani hatsabibin boka wai shi boka share kukanka.”
“Faty ce ta tsaya tace babe wlh na gaji jibi yadda mukayita tafy.”
“Meemah tace yo bakya son FARIS dinkenan, idan har kingaji toh mu koma gida kuma kin rasa FARIS.”
No am just kidding babe ai ko bangon duniyace sai munje mun tarar da boka share kukanka.”
” shegiya meemah ta kaimata duka, sukaci gaba da tafiya, can wajen wata jibgegen bishiyan gamji suka tsaya Faty tace babe nannefa akace bokan yake, meemah tace eh nan…….kan ta ida maganar sukaji wata murya tana dariiya Hhhhhhhhhhhh dukkansu sun razana suka kankame juna suna inalillahi wa’ina ilaihi raji’un.”
Wata katuwar babbaba murya yadaka musu tsawa yace kai waya fad’a muku Ana kiran sunar Allah anan.”
.
“Juyawa sukayi nan take sukasake tsurewa ganin wata baka mummunar halitta.”
“Kuntsaya kuna wani kallona ko kuna so na tarwatsa kune yafada cikin wannan babbabar muryansa.”
“A’a boka amana afuwa inji meemah da fadi, ta daidaita natsuwarta zata soma yiwa boka bayani, yace dakata nasan meke tafe daku Ku zauna yanxu.”
Ba mutsu suka zauna, take yasoma karanta wasu yarensa daban take wata iska ta buso sai ganin kulli Leda guda uku ya bayyana a hannusa, take kuma iskan ya bace.”
“Wata mahaukaciyar dariya ya bushe da ita, ya watsomusu kullin ledar, yace wannan maganine na vaki daya nacikin leda bakin zaki yi hayaki ne dashi kina kiran sunarsa, wannan kuma na farar ledan wanka zakiyi dashi Randa zaizo Dan cikin kwananan zaizo wajenki kuma zakuyi aure bada jimawaba amma kuma akoi matsala, nacikin wancan yellow da layin baki kuma a abinsha zaki zubamar inyazo.”
Matsala Dana cemiki akoi kuma zaki auresa kuma Ku zauna amma zaku rabu kuma rabuwarku bazatayi kyauba Hhhhhhhh ya kece da dariya.”
A rude tace boka haka za’ayi?.
Eh haka abin zai kasance.”
“Toh NAWA zamu bayar yanxu.”
Kubada koma mai kuma kusa anan yanuna musu wata kwarya.”
Dubu Dari suka samasa a kwarya kan suka mike sukabar wajen shikuma take ya bace battttt.”
Suma gida suka wuce Abuja, koda suka isa a gajiye suka isa suka Dan huta suna tattaunawa kan lamarin.”
***
10:00pm
FARIS kwance da Baby boo tayi ma kwanci da kirjinsa tana wasa da parks dinsa suna hira FARIS yasoma jin kamar Ana kiran sunarsa take ya mike zaune.”
FARIS! FARIS!! FARIS!!! Faty ce ke kiransa tana fadin kaxo gareni kazo gareni FARIS! FARIS!! FARIS!!! Haka taci gaba da kiransa.”
Baby Boo kaina yana rike da kansa dake juyawa yace arhhhhh baby Boo kaina Ana kiran sunana.”
.
MUSKAN ganin haka yasa rudewa take tasoma hawaye tarasa abinyi, sannu MUSFAR sorry haka take cewa.”
Faty kam kiransa tayi tayi har saida ta tabbatar yaiso garesa sakonta kan ta daina take ta bushe da wata mahaukaciyar dariya tace sorry but u must come FARIS.”
Muskan kuma a rude taji addu’oi sun zo bakinta take tasoma karanta masa har ya dawo hayyacinsa amma meye bazai iya cewa ga yadda akekiransa Ba da kyar da addu’oin da MUSKAN ke masa ya samun bacci, nan itama ta sauke ajiyan zuciya ta kwanta tana mai jin tausayin mijinta abinsonta.”
“Faty saida ta dau waya ta sanar da meemah abinda ake ciki, ita kam zuciyarta fal dadi fari tasss ta kwanta bacci…….
****
Washegari da safe bayan sunyi breakfast, FARIS ya shirya fita office amma Sam baijin dad’in jikinsa, karfin hali kawai yake haka kawai ya tsinci kansa da k’wadayin zuwa nijeriya, yana missing home, kuma yana missing Faty, duk rufe idonsa dayayi, ko ganin MUSKAN saiyaga kamar Faty ce, a daddafe ya mike baby boo a bayansa rike da briefcase dinsa tana masa rakiya, har bakin motarsa ta rakasa.”
Jingine yake a jikin motar Yana kallonta, murmushi takemasa, matsowa tayi inda yake ta rungumesa hade da k’wantowa a jikinsa tace.”
“MUSFAR meye yasamekane yau naga kamar akoi abindanke damunka tun tashiwarmu a bacci?. kodai abinda yafaru jiyane ke damunka? Tafada cike da damuwa.”
” cireta yayi daga jikinsa ya karbe briefcase din ya jefashi cikin motar, hannunsa bibbiyu yasa ya tallafo da fuskarta yana ganin k’yak’yawar fuskarta yace.”
MUSFAR Ba abinda ke damuna kawai ina missing nijeriya ne I feel lyk flying naje yanxu, that’s all yafad’a yana kannemata ido daya.”
” Are sure MUSFAR?”
.
” yes baby boo am very more sure, karkidamu it’ll be okay kinji.”
“Ok naji toh, yanxu kashiga mota katafi karkayi late a office, nima yanxu zan wuce school.”
“Ok ki kularmin da kanki sosai “
“Same goes to you MUSFAR, kaci abinci kaji.”
“Ok yafada, yabata peck a goshi, itama good luck kiss tabasa a lips, ya shige motar, ya tayarda shi, hannun yake dagamata haryabar gidan, itama hannu take daga masa saida ya fice a gate ta daina ganin motarsa, kan itama ta shige cikin gida.”
“Bata fi minti 30 Ba ta shirya itama ta fice zuwa tata makarantar (Oxford university).”
***
_*At office*_
Tunda FARIS ya shiga wajen aiki,bai tsinana komaiba, ya taba wancan ya Bari haka yayita fama.”
.
Koda su Anwar suka tambayesa ko lpy ganin yadda yau yake gudanar da Abu cemusu yayi Ba komai.”
” hira suke jansadashi amma amsar eh’ a’a kawai yake binsu dashi har suka hakura suka kyalesa.”
” misalin 2:00pm na Rana yana zaune duk tunanin Faty ya addabesa gashi yana jin muryanta na kiransa tazo garesa.”
“Rasa abinyi yayi haka kawai ya yanke shawaran kiranta a phone maybe idan yaji muryanta yasami peace of mind.”
Wayansa ya dauko kirar iPhone7 yasoma bincika contact, amma ya kasa samin number’nta sabida ko da datake kiransa baiyi saving Ba, OMG ya zanyi ina zan samo number’nta gosh ya dafe kansa.”
“Can wata idea tafadomasa msg ya shiga yasoma dubasu daya- bayan daya da kyar ya lalumo messages da ta turomasa, hamdallah yayi take yayi dialing number’r.”
****
_*nijeriya*_ Faty ce zaune ita da meeemah suna tattaunawa kan lamarin.”
“Meemaah tace shegiya yanxu aiki inaga yayi kiransa kawai zamu jira da zuwarsa babe.”
.
“Sosaima ai yanxu nasan duk inda yake zuciyarsa cike take da tunanina, kuma nasan yanxu yana cike da _*SHAUKIN SOYAYYATA*_.”
“Haka ne kam let just watch babe.”
” ah toh kina was……Bata ida fadar wasan Ba wayarta ya dau ruri.”
“Lekowatayi da ihu tace babe FARIS tana nunamata wayar.”
‘”Yeaaaaa dauka da wuri karya tsinke inji meemah.”
” baxan daukaba ki Bari yasake Kira tukunna.”
” eh hakana babe mu Bari toh.”
” FARIS yayita Kira kusan 5 missed calls tukunna ta dauka.”
.
“Hello tace kamar batason Magana.”
” FARIS da duk a matse yake yasoma Magana kamar haka.”
” Faty ya kike, hope kina lpy, yasu Daddy, ya 2days.”
” meye haka Ka nustsu mana FARIS, kana jeramin tambayoyi haka, wanne zan soma amsa maka.”
.
” Controlling kansa yayi tukun yace am sorry wlh I can’t control ne, zuciyata cike take da kewarki ina muradin jin muryanki da kasancewa dake pls Faty forget all our past wancan duk nasan banyimiki dadaiba but yanxu ki anshi soyayyata mai dadi da nutsuwa, namiki alkawarin kasancewa dake kuma mai farantamiki pls help yakare maganar kamar kuka zai Mata.”
“Naji toh amma zanyi tunani akai.”
“OMG! Noooo pls just say u accept me as your lover Faty ninefa FARIS har saikin yi wani tunani, pls just accept miee.”
“Yanga da Jan aji na duniya takare tukun tace ta yarda, nan ma saida yayita Mata magiya tukun.”
” hira sukasha kamar Ba gobe da kyar ya yarda ya bata if not shikam suyita wayan inso samune.”
.
“Suna tsinke wayar ta fashe da dariya tace shege yazo hannu ai.”
“Ai kuwa ki bar Dan banza inji meemah.”
” Hhhhhhhhh haka sukayita hirarsu suna shewa.”
.
FARIS kam suna tsinke wayar yaji kamar ansaukemasa wani gajiya da sukayi wayar, ga zuciyarsa cike take da begenta.”
_*9:00pm*_
Tunda FARIS yadawo gida misalin 7 na dare yazamawa MUSKAN wani irin not as yadda yasaba Dan da yadawo daki ya wuce not minding da welcoming datakemasa danshi Faty kadai yake son kasancewa da ita a halin yanxu.”
“Ko abinci ma kadan ya ci Dan jin kansa yake akoshe, duk abinda yake MUSKAN na Lura dashi tayi tambayar duniya tagaji Dan amsarsa dayane “Ba komai, Ba abinda ke damuna” kadai yake fad’a, haka ta hakura da tamvayarsa.”
” yanxu su na zaune ne suna ganin wani film a Bollywood _*bajirao mastani*_ amma shi FARIS hankalinsa ya tafiiya kan chatting da suke da Faty, daga yayi murmushi sai ya danyin dariya mai sauti kadan, haka yaketa yi.”
“Duk MUSKAN na Lura dashi, da taga abin ya isheta ta daure tace waini MUSFAR dawa kake chatting ne haka.”
“Karya yamata yace dasu Anwar yake.'”
“Sanyi taji aranta dayace dasu Anwar yake chatting, tace my regards to them.”
“Yace okay zasuji, yacigaba da chatting.”
Kusan 11:00pm MUSKAN ta gaji ga baccinda takeji, tace MUSFAR nifa inajin bacci yakamata muje mu kwanta, sabida kaima karkayi late wajen aiki gobe.”
“Noooo jeki kawai xan sameki akoi abinda zandan yi kadan.”
“Toh sai kazo, batajira mai zaiceba ta hate sama, sauya kaya tayi zuwa na bacci ta karanto addu’oin bacci ta shafe jikinta ta kwanta.”
” abun nema ya samu FARIS bajewa yayi ya bugowa Faty waya, sukayita hira.”
“Hira sosai sukayi na love, cikin hirar yake fad’amata in 2days dai zo nijeriya ya ganta inyaso daga nan ayi maganar aure danshi a matse yake ya mallaketa.”
“Dadi sosai taji a ranta finally burinta ya kusa cika tace toh tana sa raan ganinsa sai yazo.”
“Basu sukabar yin wayarba sai kusan 1:00 na dare ya Mata sai da safe badan ya soba.”
“Itama cike da missing dinsa dazatayi ta mishi saida safe.”
Daki ya wuce, MUSKAN ya Tatar tana bacci peacefully ga wani kyau da tayi sleeping beauty yace ya wuce ya sauya kayansa zuwa Pajama’s ya haye gadon hade da rungumota ya kwanta.”
.
” zuciyar sa fal Ba damuwa ya kwanta take bacci ya debesa…….
_*Two days later*_
“Cikin 2days dinnan FARIS ya canza kota2 yakoma kamar Ba FARIS na Baby Boo Ba.”
“MUSKAN tayi tambayar duniya tagaji Dan Ba amsata yakeba,gashi Yanxu kullum yana kan waya ko chatting, harta soma zargin kodai Mata FARIS yake nema, amma wata zuciyar cemata take kul karki zargi mijinki kan wata abinda bakida tabbas, da irin wadannan tunanin take yi kullum, amma haka ta hakura tanazubamasa I do, kullum cikin nafila take tana rokon Allah kan lamarin.”
“Cikin haka FARIS ya sami visa zai tafi nijeriya, lokacinda yafad’wa MUSKAN ciki daya tamasa fatan alheri bata kawo komai a ranta.”
“Shima ya hi dadin rashin kawo wani Abu ran MUSKAN dadi yaji da bata gane mai yake cikiba, yayi alkawari sai komai ya kankama yagama daidaita zaifad’awa MUSKAN maganar Faty.”
“Yau suke sa ran FARIS xai daga zuwa nijeriya, MUSKAN kamar ma zazzabi takeji ganin FARIS tafiya zaiyi, gashi yanxu tasaba k’wanciya a jikinsa, komai nasu tare suke, she’s gonna miss him a lot.”
“K’wance suke kan lallausar royal bed d’insu, kan MUSKAN na a kirjin FARIS wasa take da parks d’insa tayi lamo ajikinsa.”
“Baby boo yakira sunanata with his husky voice.”
.
“Na’am.”
“Bakiso ne nayi tafiyar? Ya tambayeta cikin sanyin murya.”
“No Ba hakabane kawai am gonna miss you, kusan yanxu masaba komai na tare muke, and ni tsoro nakeji wata ta kwace min Kai acan coz I feel it deep inside my heart tafiyarka nijeriya Ba alheri bane tafad’a tana shirin kuka.”
“Tashi yayi daga k’wanciyar yadaga fuskarta ya tallafo, yana ganin ta cikin ido, yace no Baby boo it won’t karki ce Ba alheribane ,I know it’s alherine, trust me Ba wacce zata kwaceni wajenki you are the only one huh!.”
“But why d sudden changes those days, Ka canxa MUSFAR I suspect there is something going terrible.”
“Not at all baby boo, nifa kibar maganar huh! Ko kinaso muna jani in jakane won’t you free your mind and had a trust in me.”
“I will ya wuce nayi shiru toh.’
‘That’s my Baby come here ya waro Mata hannayensa.”
“Ba musu tafada jikinsa, hugging dinta yayi tight, itama back hugging dinsa tayi, sakonni yasoma aikamata dasu masu rikitarwa cikin kwarewa da iya sarrafa mace yake Mata komai, take ta dauke wuta tasoma maidomasa da martani, sun dauki tsawon lokaci suna romancing junansu daga nan FARIS ya kashe arna.”
“Cikin farinciki kayan sun gamsar da junansu sukayi wanka, daga nan suka shirya.”
“Cikin 30mins suka kimsa, nan suka ja mota zuwa airport, MUSKAN ke driving dinsu, yanata Mata hirar sa mai dadi har suka isa airport.’
“Da isarsu basu fi 15mins Ba jirginsu ya daga, da kyar MUSKAN ta rabuda FARIS kwalla cike aidonta tana gani ya shige jirgi, yana dagamata hannu itama haka har saida yashige tukunna, saida taga jirginsu ya daga yasoma keta haxo tukun taja motar ta ta wuce gida jiki a sanyaye, data isa gidama kulle kanta tayi a daki ta kwanta take bacci yayi awon gaba da ita…
.
_*nijeriya*_
Faty sai Kai komo take a dinning tana shirya warmers, meemah na tayata.”
“Suna cikin hakane FARIS ya Kira wayarta yasanar da ita ya sauka yanxu amma zai biya gida tukunna inyaso daga baya yaxo.”
“Toh tace masa sai yaxo.”
“Suna gama wayar, tace wa meemah, babe FARIS fa ya iso.”
“Toh yi sauri muje ki shirya kiyi wanka da wancan maganin, kuma akoi wata turare da boka ya ban da na koma ya ce kishafasa a jikinki da zarar yaji kamshin toh fa hmmm sai kingani kawai.”
“Hannu ta bata suka kece da dariya ahayyeee nanayeee ai FARIS zaici ubansa ahannun Dani yake zance ai.”
“Yanxu yi sauri ki shiryo, da fatan kin zuba wancan maganin a juice din nan meemah ta tambaya.”
“Ehh na zuba amma ki kula dashi pls kar wani yazo yadauka ya kurbe aikin mu ya baci.”
“Lolz karki ji komai yanxu kije kawai.”
“Ok tafada, take ta wuce daki Dan shiryawa.”
****
FARIS ya isa nijeriya lpy, daga airport yasa wani Frnd dinsa dake Abuja zuwa ya daukosa yakaisa gida, yazo ya daukosa yakaisa gidansa dake game village.”
“Bayan ya saukesa ya masa sallama ya tafi, shiko FARIS cikin gidan ya shiga, kusan komai a kimtse ya tarar sabida matar gate man dinsa na sharemusu after 2-2days Ana biyanta monthly.”
“Dakin da yakasance nasa ya shiga, kura kadan ne a d’akin, ya tarar da kansa yayi dusting dakin komai yakoma daidai yadda yake bukata, wanka ya sheka ya shirya cikin wata dakakkiyar _wagambari sky blue_ hulansa ma yakasance irin ruwan kayan, agogon _Rolex_ ne daure a hannunsa, kafan sanye da sau ciki, yayi kyau abinsa, ya feshe jikinsa da perfumes masu kamshi sai wata uban kamshi ke tashi a jikinsa.”
.
” fita yayi already mai kula da motocinsa ya gogemasa motarsa kirar KIλ, key ya mikamasa nan take yaja motar gate man ya wangalo masa gate ya fice.”
“Hanyar gidansu ya nufa dake maitama.”
****
Mum zaune da ‘Yan matanta suna hira tace su gwada Mata layin baby doll dinta coz tundaxu take Kira amma Ana cemata a kashe.”
“Fareeda ta gwada tace Mum wlh wayar MUSKAN a kashe take har yanxu.”
“Humaira tace toh maybe tana skul ne shiyasa.”
“Eh zai yu hakanne toh kiranmi salman naji ko lpyr su qalau inji Mum.”
“Toh nan fareeda tashiga Neman layin sa amma Sam bata saminsa shima.”
“Mum shima fa haka Bana saminsa.”
“Toh ki Bari zuwa anjima mu sake gwadawa.”
“Rife bakinta keda wuya sukaji karar tsayuwar mota amma basu damuba kasancewar sunsan gidan kullum cike yake da baki.”
“FARIS ya fito cikin motar suka gaisa da gate man na gidan su, ya wuce cikin gidan.”
“Assala mu’alaikum yace yana kunsa kansa cikin falon.”
” Wa’alaikum salam suka amsa, mum tace Wanake jin muryansa kamar na salman kodai Dan inata tunaninsa ne yakemin giz…o not finishing what she want to say to her surprise taga FARIS yayi folding hands dinsa a kirji Yana sakar Mata murmushi.”
“LA YA FARIS su fareeda da humaira suka fada da karfi suna karasowa wajensa.”
“Wajensa suka nufa nan sukayi hugging dinsa shima hugging dinsu back yayi.”
“Mum wlh shine its him shiyazo fareeda tafada tana zamewa daga hugging dasukawa juna, ta karasa wajen Mum.”
“Hannunsa sarke da humaira suka karasa wajen Mum.”
“Gefen mum ya zauna ya kwashi gaisuwa, kansa ta shafa tace irin wannan zuwan Ba Kira kodai surprising dinmu kayi ne.”
.
“Eh mum is a surprise, kuma wani abin naxoyi anan nijeriya shiyasa.”
“Toh yanada kyau, ina MUSKAN din toh ko Ka barta acan ne?.”
“Eh tana can tana makaranta.”
“Ayyah tun dazufa nake kiranta a waya amma Bana saminta komai yasane oho.”
“Shi FARIS ma yamanta da kiranta wlh duk hankalinsa nakan yaje yaga Faty shiyasa ko MUSKAN yamanta kiranta yasanar da ita ya iso, karya ya shiryawa Mum yace shima ya nemeta amma bai sametaba yana ga ko ta kashe wayarne tana class.”
“Ayyah zaiyu hakanne, fareeda maza kutashi kuba yayanku abinci da abin sha.”
“No Mum ki barsu I will be out some where banajin yinwan yanxu.”
.
“Ok toh yayi kyau.”
“Ina dad ne mum?”
“Dad dinku yayi tfy zuwa kd jiya sunada wata programs da zaiyi attending acan.”
Ok ayyah Dad Allah ya taimaka masa.”
‘Ameen”
“Mikewa yayi yacewa mum anyway Bari nafita yanxu zuwa anjima zan dawo.”
“Toh saika dawo Allah ya kare.”
“Ameen Mum, and kukuma na tfy saina dawo dasu fareeda yake.”
“Ok yaya saika dawo, ac dawo lpy.”
“toh my lovely sisters.”
‘Waje ya nufa ya shige motarsa ya dau hanyar gidansu Faty yakirata a waya yasanar da ita gashinan tahowa, tace sai yaxo.”
“A hanyarsa na tfy ya kira baby boo yaci sa’awayanta ya shiga ya sanar da ita ya’isa lpy.”
“Hammadallah tayi tace toh ya kula da kansa,insha Allah yace da ita.”
.
Faty ta shirya cikin wata abaya red ta yane kanta da bakin gyale,fuskarta duk makeup yasha foundation, highlighting da contour, anfenta aishadow dasu janbaki lolz! Tayi kyau Ba laifi, tasahafe jikinta da turaren duk dakin ya dau kanshinsa, ga kanshin Ba dadi sam ko kadan, suna zaune da meemah.”
“Karar tsayuwan mota taji ta leka ra window FARIS ta gani yamatukar Mata kyau yasake haske yaxama babban mutum, tsalle tadaka tace he’s here babe.”
“Dadina dakefa kenan ki nutsumana haba tafada haushi yana building a face dinta.”
“Oh sorry na nutsu toh tace tana gyra kanta.”
“A waya yakira yasanar daita ya iso.”
“Fita tayi har inda yake taje tasamesa, sannun daxuwa tamasa ya amsata da yawwa yana Mata wani mayen kallo ga Ka.mshin tuarenta da ya Shaka yatafi dashi wata duniya,kallonta yake ko keftawa bayayi.”
“Waving face dinsa tayi da hand dinta tace honey kallonannfa.?
“Swthrt kinyi kyau ne ga kamshin tuarenki mai dadi Ba dole na kallekiva.”
“Oh c’mon tafada a shagwabe, yanxu isn’t time for this kaxo muje daga ciki tukunna.”
“Ok yace da ita.”
“Hannunsa ta rike tana jansa shikuma sai binta yake kamar rakumi har suka karasa falon saukar baki.”
” zaunar dashi tayi ta zauna a gefensa, tace su gaisa da meemah, gaisawa sukayi Ba yabo Ba fallasa.”
“Hira suka Dan taba duk Faty tagama rukitar dashi Dan wasu kissa take masa sai shi gemasa jiki take saida suka Dan jima tace suje suci abinci.”
“A dinning chair ta zaunar dashi taxubamasa miyan agushi dayasha nama, kifi da vegetables, sai tuwon semo da tuku mai kyau da kanta tayi feeding dinsa, ta shayar dashi lemon kwakwa mai sanyi Wanda surkullenta ke ciki.”
“Tunda ya hadiye lemon yaji duk duniya Ba wata mace dayake gani inba Faty Ba and yanajin sonta na building a zuciyarsa kamar ya fashe.”
“Dasukagama cin abincin suka koma falon suna hira love words masu dadi yarinka gayamata itama haka tarinka kashesa da love words dinta.”
“A gidan ya yini sai dare karfe 9 ya bar gidan full of Missing her itama haka Dan da kyar ta barsa ya tafi.”
“Ko gidansu Mum baiji jeba ya wuce gidansa Dan ya gaji,ga wani SHAUKIN SO na Faty na building a zuciyarsa karfin hali yake kawai Dan wannan turaren da yashaka da juice dayasha duk ya rikitar dashi.”
“MUSKAN nema ta kirasa waya Dan taji shiru, karya yamata yace ya gaji yana ma jin zazzabine shiyasa.”
“Abu da Mata da miji daga jin muryansa datayi ta yarda da zancensa, batasan duk karya ya shrgamata Ba.”
“Da haka sukayi sallama ta kwanta zuciyarta cike da tausayin mijinta….
Shikuma da tunanin Faty ya kwanta bacci……
***
ƁBayan wasu kwanaki FARIS yanzu sam hankalinsa bayakan baby boo kusan zance baya kiranta kullum itake kiransa, da takirasa saiya shirgamata karya kan aiki yamasa yawa yana gajiyane shiyasa baisamu ya kirata, abunka da mata da miji idan yafaɗamata haka saima tausayinsa datake ji ita a ganinta aikin ne yamasa yawa.”
“Hakafa rayuwarsu ke gudana yanxu a kalla faris yana neman shuɗe sati ɗaya a nijeriya.”
“Zuwansa gidansu baifi a irgaba kullum suna tareda Faty duk tahanasa sakewa saikara rura wutar tsafinta take kotakota yanxu faris baya hankalinsa itake controlling dashi, ga ta matsa masa kan suyi aure, yabata hakuri kan jiran Dad yake da zarar yadawo za’yi komai, da waɗannan kalaman yasamu ya kwantar mata hankali.”
“yauma kamar kullum suna tare suna hiransu cikida so da kauna, faris kenan da faty.”
“Wayarsa dake aje gefensa ne yaɗau ruri yana neman agaji,sharewa yayi not minding yadauka ko yasan mai kira.”
“Uhmmm honey kanajina faty ce ke faɗar haka.”
“ina jinki swthrt Faris yaceda ita.”
“Wannan kuɗin da kace zakaban ɗinnan 1million naira ko kamanta ne tana faɗa tana fari da ido.”
“No ban manta ba let transfer it now to your account kinji koh?.”
“Fari da ido tayi tace naji honey.”
“In less than 3mins Faty taji alert a wayarta, dake da E banking yayi amfani.”
“Full of suprise take kallonsa she could not believe it, idan ko hakane maganin boka share kukanka na aiki 1million naira tayi exclaiming, hugging ɗinsa tayi tabasa peck a cheek tace i loɓe you Faris, ina sonka, da sonka nunfashina ke fita kazamo wani gurbi na rayuwata i can’t live without you pls karka bar rayuwata kakasance dani har abada tana magana tana shishigewa jikinsa kamar mage.”
“fuskarta ya ɗago ya zubamata oily eyes ɗinsa yanamata wani shu’umin kallo haɗe da killer smile ɗinsa wanda ni Neerat nakasa fassara kallon mai wannan, faty yakira cikin muryansa mai sanyi.”
.
“ɗagowa tayi tana kallonsa itama danata salon kallon tace na’am.”
“Alkawari na miki xan kasance da ke no matter what kinji, kada kidami kankai wannan kyautar ba komai bane idande wake nayisa kai koma wa wani nayi, so yanxu kimanta da wannan muyi hiranmu kinji.”
“Kai ta gyaɗamasa alamar taji maganarsa, hiransu sukacigaba dayi kamar ba gobe.”
***
Mum ne da ‘yan matanta suna ta faman aiki tarar Dad kasancewar yau zai dawo.”
“Mum nikam ya faris ya komane humaira ce ke tambaya.”
“Fareeda tace banajin ya koma sabida munyi waya da Muskan jiya tace vai dawo.”
“Mum ce tayi saurin karɓan zancenda fareeda keyi tace kina nufin Faris yana nan amma baixuwa ko gaisuwa muyi anya lafiya kuwa? kuma yabar min daughter acan ita ɗaya kudaukomin waya nakirasa yanxu.”
“Wayan sukamikamata ta gwada kiransa saidai rashin sa’a takira kusan sau biyar amma ba’a ɗagawa, layin muskan takira cikin sa’a kuwa ta daga.”
“Gaisawa sukayi da mum, bayan sungama gaisawa ta tambayi lpyrta tace tana lpy, bawani matsala mum tasake tambayarta, tace ba komai, kunyi waya da faris inji mum, eh munyi tawa mum karya ɗan kare mijinta, toh yayi kyau ki kulla da kanki, kuma kimaida hankali kan karatu kinji, naji mum na gode, ba komai ‘yata ,hira suka ɗan taba kan sukayi sallama.”
“@2:00pm Dad yadawo family’nsa sunyi murnar dawowansa, tarɓansa sukayi cikin girmamawa, bayan ya huta yayi wanka suka cikamasa gabansa da abinci kala kala, dukka yaran da mamar kowa naso ya farantamishi, sosai yaco abincin sai albarka yaketa samusu yana kuma yaba abinci.”
“Daya gama cin abincin suka koma falo, nan yabaiwa kowa tsarabarsa, murna suka hauyi suna masu farinciki da kyutarda mahaifinsu yamusu ta sabuwat waya.”
.
“hira sukasomayi da matarsa dakuma ‘ya’yansa, cikin hiransu ne mum take sanar dashi zuwan Faris, yace toh yayi kyau, ina ita Muskan ɗin ya barta, mum tacemasa ai tana makaranta shiyasa basuma zo tareba, yace toh yayi kyau sunma yi kwana biyu basu gaisa da muskan ba ɗan baida lokaci.”
“Wayarsa yacire yakira muskan, sun gaisa lpy yamata nasiha sosai kan xaman rayuwa da kuma kab karatunta, godiya tawa Dad sukayi sallama.”
.
“FARIS @ 4:00pm daidai wannan lokacin suka rabu da faty, rabuwarma da kyar sukayi, sabida yana zaune hankalinsa na a kan giɗa yau yana son zuwa duba su mum.”
“Motarsa yake tukawa a hankali cikin nutsuwa, amma kuma yanajin kamar yayi missing ɗin wani abu daban, duk da idan suna tare da faty yakan manta kowa da komai amma yau yana ɗan tunawa da wata ko wani abin mai muhimmaci a wajensa.”
“Wayarsa ya ɗauko yana driving yana ɗan duddubawa can ya danna lambar baby boo.”
“Wayar na Hannunta tana game yasoma ringing, ganin handsome ɗinta ke kira yasata ɗagawa da sauri tace Assalamua’alikum mijina abin alfaharina.”
“wa’alaiki salam dafatan kin wuni lpy?
“Lpy mijina, ya aiki?
“Aiki alhmdullilah, ya karatu? da fatan kina kula da kanki? “
“Sosaima mijina, saidai zuciyata cike take da kewarka, i miss you my handsome pls kadawo gida mijina tafaɗa a sahagwaɓe.”
.
“Wani yarrrrr yaji duk tsigan jikinsa ya tashi wani iri yaji, ɗan maganarda tayi a shagwaɓen duk yaji jikinsa yayi sanyi, wani irin feelings yasoma ji na fusgarsa.”
“Uhmmmm baby boo zandawo ƙwannan karki Ji damuwa yafaɗa adan daɓurce, yakara da faɗin zankiraki anjima kinji.”
“Toh mijina ka kula da kanka tamasa blowing kiss ta waya haɗe da hanging ɗin wayar, tana murmushin jin daɗi.”
“Shikam duk ta rikitasa gashi ta kashe wayar, shima murmishin yayi yaji wani daɗi na shigarsa fiyeda in da faty yayi hira.”
“Cike da jin daɗi ya isa gidan, amma yana karasawa text na faty ya shigomasa waya, yana dubawa yaga text ɗin kamar haka.”
_*honey bayan tafiyarka yanxu Daddy’na yakefaɗamana tare suka dawo da Daddy’nka, Pls ka daure kasanardashi maganata da kai*_.
“yana gama karantawa yayi murmushi, ya fita cikin motar ya kullo, nufi cikin giɗa.”
***
Suna zaune dukkansu a falon kasa suna ganin wani series film a zee world _king of heart_ da ka gansu zakasan suna jin daɗin kallon, ana cikin haka suka jiyo sallamar Faris.”
“Assalamua’aikum”
“Wa’alaikum salam dukkansu suka amsa haɗe da basa izinin shigowa.”
“Sgowa yayi fuskarsa ɗauke da murmushi, yakarasa har inda suke zaune, zama yayi ya kwashi gaisuwa, nan su fareeda ma suka gaida shi ya amsa fuskarsa a sake.”
“Dad ashe ka dawo faris ne yayi tamvayar.”
“Eh son ɗazu na dawo, mummy’nku take sanardani kaxo bayan tafiyana.”
“Eh naxo yin wani aikin ne dama kai nake jiran zuwanka ma tuntuni.”
nikuma faris? Dad yayi tambayar very exclaimed.”
“Eh Dad.”
“ALLAH daiyasa lpy kake nemana.”
“Wata magana nakeso muyi ne shiyasa.”
“TOH inajinka faris faɗa toh.”
“Juyawa yayi ya kalli fareeda da humaira dake kallo abinsu, yace fareeda kutashi kubamu waje zamuyi magana da Dad.”
“baki suka turo gaba suna gunaguni suka mike, harara humaira ta wurgamai itakuma fareeda baki ta murguɗamasa, duk ya gansu amma ya share kamar bai gansuba.”
“Suna barin wajen ya juyo yace em..em…emm dama nace Dad sai kuma yayi shiru.”
“Ido Dad da Mum suka xubamasa suna sauraronsa, shiiru kusan na 3mins sukayi duka, shi faris yana tunanin ta’ina xai soma faɗawa dad yaje nemasa auren faty, sukuma dad da mum daban abinda suke sakawa a ransu.”
“Dad ya gusar da shirin nasu dacewa faris lpy kayi shiru? ko dai wani abinne ya faru tsakaninka da muskan? kayi magana kasamu a duhu.”
.
“Jin maganar dad ne ya dawo dashi duniyar tunaninda yake, gaining courage yayi yasoma magana.”
“Dama ba komai bane kuma muskan batayi wani abinba kawai Mum, Dad kunsan ina namiji allah ya halittamin auren mace 1,2,3,-4 shi………”
“DAKATA Mum tafaɗa cikim kakkawsar murya karka kuskura ina ruwanmu da wani 1,2,3,-4 dakake irgawa tsayama tukun ban fahimci mai kake nufi…..”
“DAD Ne ya tari nunfashinta ta hanyar dakatarda maganarta, yace haba zainab kya barsa ya karasa maganarsa tukun kikasan mai zai ce haba zainab ki rinka baiwa kanki hutumana.”
“TACE toh shikenan inajinsa yakarasa toh tafaɗa a kifule.”
“Yawwa son inajika kacigaba.”
“FARIS yace toh dad dama ba wani abin bane, nasan muna zaman lpy da muskan tana bayamin bukatuna da sauke dukkanin hakkina da ya rataya a kanta, tana farantamin kuma gsky ina alfahari da ita matsayin matarda na aura, banso ace zan iya rayuwa da wata bayan itaba amma kaddara ta riga fansa dad aure nake so nayi kuma fatima ce ‘yar wajen abokinka ita nakeso kanemamin aurenta, bawai zanyi aure ɗan banason muskan ba ko kuma cin fuskarta a’a kawai dai cika sunnah xanyi, yana kawowa nan yayi shiru yana mai tsunkuyar da kansa.”
“Ai kamar jira mum take ya gama ta amashesa tace lalle wuyarka yakai yanka nasan za’a rina wai anci zanen mahaukaciya, sabon salo gemu a kafaɗa, toh buɗe kunnuwarka da kyau kaji wlh middin ina raye bakai ba auren wannan ‘yar iskan yarinya maras kunya kawai tun wuri ka janye wannan kaxamin batunka dan baxai taɓa yuwa ba kadai jini da kyau, tana kaiwa nan ta tashi fuuuuuuuu ta bar wajen tana binsa da wani mugun kallo da yasa cikinsa ɗuran ruwa sabida abinda ya gani cikin idon mahaifiyartasa.”
“Mikewa dad yayi shima ya dafashi yace son kayi tunani idan ma baka hayyacinka kadawo tun wuri sabida nima ban goyi bayan aurenan ba, gajidai mai nace maka kuma idan dan wannan kakejirana toh gobe ka kama hanya kabar nijeriya ka koma london maganar nan ya mutu understand.”
“NOOOOOOOOO yafaɗa da karfi this house is hell, why? dad nazata zaka goyi bayana but kaima kayi turining back to mie,pls dad ku barni nayi auri faty i so much love her.”
“KA Mutu inji mum dake saukowa nace kama fita kabani waje i don’t want to see this your useless face and that your stupid mouth talking here kafita kuma baza ka auretaba.”
“Hanyan fita ta nunamasa, jiki sanyaye ya tashi ya kama hanyan fita har yakai bakin kofa Dad yace and gobe kabar nijeriya nace kadai jini da kyau.
“ko kulasu bai yiba yafita zuciyarsa namasa zafi zuciyan maza ya baci.”
“Motarsa yashiga not minding da gate man din horn yake dannawa kamar zai pasa kunuwar ‘yan gidan gateman na hangamemasa gate @360 ya ja motarsa.”
“Mum rai bace ta wuce dakinta……….
Hakama Dad bayan yabi shima NASA ran s bace……..
*****
“ɗaki Mum ta wuce rai bace, shima Dad biyota yayi.”
“A bakin gado ya ganta zaune tayi tagumi ta tafi duniyar tunani, zuwa yayi yazauna kusa da ita yayimata side hug sannan ya kira sunarta ZAINAB.”
“Na’am ta amsa sa amma bata ɗago ta kallesaba.”
“Look at mie we need to talk huh! “
“Alhj ina jinka ta ɗan ɗagowa a karonnan.”
“Kidaina ɗaga hankali kan abinda yaron nan yafaɗa bai isaba yayi kaɗan yace zaiyi wannan auren nasan matsalar ki muskan ce, toh ki kwantarda hankalinki ba’abinda zai faru da ita, ko kin manta nace itama ɗiyatace zan zamemata uwa kuma uba wannanfa alkawarine dana ɗauka kuma saina cika, ZAINAB idan harɗai ina nunfashi a doron kasa muskan bazata yaɓa yin kuka ba insha Allah Bazan bari FARIS ya sata bakin cikiba, wannan auren ban goyi bayansaba matata idan har hakan shine kwanciyar hankalinki da farincikinki kinji koh.”
“Fuskarta sake kuma ɗauke da murmushin jindaɗin zancen mijinta tace na goɗe mijina a kullum ina alfahari da kai kasancewarka matsayin mijina uban ‘ya’yana.”
“Bakomai matata ina son ganinki cikin farinciki, kwanciyar hankalinki shine nawa.”
“Peck ta kaimasa a cheek tace amma wani hanzari ba guduba nifa wannan al’amarin yaban mamaki.”
“Wani al’amari kenan inji dad da faɗa.”
“Gani nake kamar faris baya hayyacinsa anya kuwa ba wani abin a kasa.”
“Kai ya jinjina maganar ki gsky ne nima haka nake gani sabida bantaɓa tunanin faris zai iya furta waɗannan maganganun ba musamman yadda nasan yakeson muska da alama akoi abu a kasa.”
.
“tayani gani mijina nasanfa halin yaron nan kumafa dacan yarinyar na sonsa amma shi kullum cikin tsanarta yake, kai gsky da sake kasan mai hankali shiyake ganin ɗingishin ƙkwaɗo.”
“gasky kam karmuyi sake yanxi yakikeganin za’ayi sabida nace masa yatafi london a gobe kina tunanin zaitafi kuwa?.”
“Ina ai ban tunanin haka, wannan yarinyar fatima idonta a ɓuɗe suke nasan duk yadda za’ayi idan shi faris yaje yafaɗamata bamu yarda da zancenba, toh daga nan zatace zatayi wani abu akanmu kaga tunda dama gwanda mu mike tsaye, nafiloli zamu sake kan wanda muke a da sa’annan zamu sami malamai suyita saukar Qur’ani da yanka ana saɗaka koya kace.?”
“Excellent matata haka kawai zamuyi kuma muja shi faris jikinmu mununa mun yarda da auren kinga haka zaiyarda damu aikinmu zaitafi mai kyau.”
“Haka za’ayi, abuna kuma biyu muskan zamanta can ita ɗaya kaga ba daɗi nace ko zata dawo itama sai amata nata neman tsarin a amata saukar al qur’anin itama.”
Toh sai gobe zanwa su anwar magana su sata a jirgi saita dawo ko? “
“Eh haka za’ayi , nan suka sauya hiransu da tasu salon soyayyar.”
***
Allah ne kaɗai yakaisa giɗa sabida wani irin tukinda yake, koda yashiga gida da gate man ya hangamemasa gate ya shige @360 parking ɗinma yayisane kawai sabida akarkace yayi, rai ɓace yafita yanufi cikin gida, ɗakinsa direct yanufa, kayan jikinsa ya rage yashige toilet, shower yasakarwa kansa idonsa runtse yana cikin jacuzzi ruwa na sauka a dukkanin ilahirin jikinsa,yana jin daɗin ruwan, duk haushin su Dad yakeji kamar ya shakesu ya huta kawai haka yakeji a ransa yana ganin hakkan shizaifi samamasa farinciki a halin yanxu.”
“Ya ɗau tsawon lokaci a haka kan yayi wanka yafito, ya shirya cikin kananan kaya, fitayayi bayan yazari key yaɗau mota ya fice,hanyan gidansu faty yaɗauka dancan kaɗai yakeji idan yaje zai ji sanyi cikin ransa.”
“Ya isa gidan yasanar da faty ta shirya tasamesa kofan gidansu yanajiranta.”
“Cikin shirin wata doguwar rigar material blue ta fito tana rankwasa tana yauki harta karasa wajensa.”
“Shikam faris ganinta dayayi kawai ya nemi ɓacin ransa ya rasa sai ma murmushi dayake kamar bashibane wanda ya murtuke fuska ɗazu.”
.
“Gaisawa sukayi data shiga motar,ya amsa yacemata fita zasuyi zuwa gari, tace ba matsala suje.”
“Suna tfy suna hira abinsu anan ne ta tambayesa ko yasanar da Dad maganarsu yacemata eh yasanardashi yace daya kammala abinda yke zaisami daddy’nta suyi magana, farinciki tayi sosai harta kasa boyewa.”
“shidai kallonta yake batasan karya yamataba, shikuma yama rasa dalilinsa na mata karya.”
Da haka sukaje wajajen shakatawa dayawa sai dare sukadawo ya ajeta gidansu shima ya wuce gidansa…..
***
_*2 days later*_
Bayan kwana biyu Da maganarsu Dad kan ɗauko muskan da za’ayi, yasamu yakirasu Anwar yasanar dasu su sata d jirgi tadawo gida.”
“Sunyi komai shida aliyu yadda Dad ya bukata sunsama mata viza,.”
“FARIS kam tunranda su Dad sukaki amincewa su nemamasa auren faty yaɗaina zuwar musu gida ko kiransu a waya ya daina yi sam kuma su ko sunkira baya picking wai yana fushi dasu. kuji wani zancefa anan.”
“Fanin su Dad ma dasuga abin na faris yayi kamari suka kyalesa sunsan baya hayyacinsa ne, kuma har yau su fareeda basuda masaniya kan abinda yake faruwa a gidan.”
***
” Ranar Wata alhamis tana zaune a falo tayi tagumi tafi wata uwa duniya can tana tunani, ba komai take tunawa ba illah faris, ya canza kota kota gashi yaki yadawo, gashi kullum cikin kawomata korafi yake da zarar tace bayakiranta saiyace aikine yamasa yawa ita a gsky yanxu tasoma gajiya zuciryarta tasoma mata hasashe kan ba gasky faris ke faɗamata ba, takasa sakewa kwanan tana yawan yin mafarkai iri iri.”
.
“Tana yawan ganin faris dawata mata fuskarta baki kirin gashitana neman halakasa,itakuma muskan duk lokacin ta dososu wani farin haskene ke bayyana kuma da zarar ta dososu ko wancan matar tayi niyan kashe faris ɗin idan wannan hasken muskan ya bayyana saita kasa yin komai.”
“Toh fa muskan wannan abin shi kedamunta gashi takasa gane mai wannan mafarkin ke nufi, tana cikin wannan tunanin ne tajiyo sallamarsu Anwar, take ta komo hankalinta taɗan daidata nutsuwarta waje ɗaya ta amsa su haɗe da basu izinin shigowa.”
“izini tabasu suka zauna, bayan sun gaisa, tawuce taɗaukomusu abin motsa baki, hannunta ɗauke da tire da jug saikuma kofuna da plate cike da snacks ta zo dashi, a gaban kowannensu ta ɗirarmasa kan wasu kananan stools tace dasu bismillah.”
“Sai da suka ɗan taba abin da takawo musu tukun suka tamabayeta ya zaman kaɗaice? ya makaranta kuma? duk tace abgodewa Allah zaman kaɗaici kuma tana fama.”
“Anwar yace faris ya makale acan yaki yadowo kuwa, sai Aliyu yace nimadai abinda nagani.”
.
“Murmushi tayi tace zai dawo insha allah bada daɗewaba coz nasan yayi missing ɗina kamar yadda nima nayi missing ɗinsa kunga duk inda yake hankalinsa na gida na tabbata.”
“Suma murmushin sukayi Aliyu yace toh sarauniyar iya magana da soyayya kyafaɗamana haka ai dama tunda kika kasance matar faris kam.”
“Anwar ne ya amashesa da faɗin faɗi kanka tsaye abokina gori takemana da wayancewa.”
“la muskan tafaɗa tana mai rufe fuskarta da hannu biyu alamar taji kunya tace nifa ba gori nakemuba.”
“Toh muskan munji faɗar Anwar, yace dama gaidaki mukazo yi saikuma visa da muka tahomiki dashi inji Dad yace gobe zaki 9ja yana maganar ya ciro visa card ɗin yamikamata.”
.
“full of suprise take kallon card ɗin a ranta tace 9ja Allah dai yasa lafiya ne, murmushi ta kakaro tace musu na gode insha Allah yau zan shirya.”
“Toh suka amsata Aliyu yace gobe zamuzo mukaiki airpot insha Allah.”
“Toh ba komai sai kunzo Allah ya kaimu.”
“Ameen, muzamu wuce sukace da ita suna mikewa.”
“Har bakin kofa tarakasu ,tamusu godiya yadawo ciki, tana sake sake cikin ranta, waya taɗauko takira fareeda kozata bata information amma kash wayar baya shiga haka ta gwaɗa na Dad shima, duk saida ta gwada wayar ‘Yan gidan amma batasaminsu, hakura tayi kawai.”
“Tashi tayi taje ɗaki tasoma haɗa kayayyakinta na tafiya duk wani abinda tasan zata nema tahaɗa su a babban troley’nta cip cip.”
****
Washegari jumma’a kamar yadda su anwar sukace zasu zo ɗaukarta toh suncika alkawari sunzo sun ɗaukota sun kaita airpot.”
“Kafin jirginsu yaɗaga saida suka kira Dad a Waya suka haɗashi da muskan sukayi magana.”
_Readers karku manta duk wannan abinda ake faris baida masaniya akai_
“basuɗau lokaciba a maganar dadukayi da Dad wanda ni neerat banji abinda sukafaɗaba amma sai ganinta nayi tana murmushi alamar maganan da sukayi yamata daɗi kenan, wayar ta mikamusu lokacinda ake bukatar pasinja su shiga jirgi tamusu sallama tawuce abinta..”
“baifi 30mns ba jirginsu yaɗaga zuwa nijeriya.”
.
FARIS zaune gaban kanin mahaifinsa Usman duk ya korowa kawunsa bayanin komai game da son auren faty daya ke son yi dakuma yadda suka kaya dasu , kawu usman yaji jawabansa yakuma tambayesa kan yana son karin auren dawata manufa koko matarsa ce tamasa wani abin?,Kamar yadda yafadawa Dad yanason karin auren ne sabida cika sunnah kuma yana sha’awan yin mata Biyu haka yadafadawa Shiva kawun. Kawu yace toh masha Allah idan dai dan wannan ne zaiyiwa Dad magana,gdy FARIS yashiga jerowa kawu yasan idan dai kawu yawa dad m.agana zai iya amincewa shiko idan akamai haka angama masa komai na Rayuwa.
Kawu yace gdy ya isa ai yiwa kaine kuma FARIS ai kai dana ne kaima karkaji komai kaji. Toh yace kawune ya umarcesa da yatashi yatafi shima zasa wani gun yanxu daganan yawuce wajen dad din.”
‘farinciki ne ko murna duk FARIS na ciki yana driving yana..murmushi harda bude wakar backstreet boys yana marming din wakarsu ta _I want it that way_ har ya isa gida.”
“Faty da kawarta meemah yau sundau hanyar kauyen bebeji sabida itafa faty haka kawai take jin bata aminta da abinda FARIS ke fadamata game da maganar aurensuba gani take kamar karya yake mata idan yace wai aiki ne yawa dad yawa, shiyasa ta fadawa meemah su koma wajen boka share kukanka ko, zaisan *meke faruwa*(cute xarah ce ).”
“sun shiga cikin jejin kamar yadda suka saba yau ko tsoro babu tattare da faty, karkashin bishiyan da yake bullowa suka tsaya take sukasoma babbako ashar masu zafi, wata irin iska ce ta kada tana juyawa boka na a samarta yana saukowa kasa take suka jiyo dariyar boka hahahaha yana wani mugun dariya inda iskar ta tsaya shikuma sai gashi zaune yana wannan muguwar dariyarsa hakora duk sun rine gasa baki so irritating idan kungansa fans.
“shegu, marasa imani, hatsababbu abinda boka kefadi kenan wasu faty.”
“Sannunku dazuwa yanunamusu waje su zauna, ba musu suka zazzauna, boka yace.”
“nasan zaku dawo basai kunfadi mai ke tafe dakuba nasani ansami matsala wajen iyayen yaron wancan karon bamusamu munyi aiki kansuba amma yanxu zamuyi, wata kwarya yaja yakawo gabansa cike da ruwa ya umarci faty da ta matso ba musu ta matso kamar yadda ya bukata wasu yarensa yasoma karantowa wadda ni neerat bansan mai yakefadaba tsiiiiii wasu kibiya biyu suka wuntsilo bakin kwarya atsorace faty ke gwalo idanu tana ganin abin al’ajabi, dariya boka ya bushe da ita yace.”
“kinga wannan yanunamata cikin kwaryan waye wannan ya tambaya yana nunamata cikin kwaryan?.
“faty da tacika da mamaki tace.”wannan ai mummy ce mahafiyar FARIS tafada maganar na rawa abakinta.”
“wannan fa yanunamata dayan.”
“Dad ne ai tafada still getting suprise.”
“toh yayi kyau inji boka sa’anan yace wadannan suke kawomuku cikasss sabida a halin yanxu sun hana dansu auren ki amma yanxu zanyi maganunsu zuba ido ki gani.”
“kibiyar da ya ajiyesu guda biyun yadaga yajefa cikin ruwan take dayan ya sami dad a bakin zuciyarsa dayan kuma yasami mum gefen zuciyarta amma basu kula da hakanba boka yace .”
“kinga wadannan kibiyoyin dana harba musu yasamesu toh aiki yayi yanxu bazasu bijirewa auren kuba tashi ki tafi komai yayi daidai hahhhhhh yasake barkewa da dariya.”
“kudi masu yawa ta ajiyemasa cikin kwaryansa ta taso suka kama hanyan fita daga jejin da meemah.”
“saida suka fita cikin daji suka shiga cikin mota sun soma shiga gari tukun faty tasoma baywa meemah lbrn abinda ya wakana.”
**
Dad, mum zaune a falo tare dasu fareeda sun shirya tsabb zasu dauko MUSKAN takusa sauka, suna cikin hirane lokacinda boka ya harbo kibiyoyin kirjinsa ya rike a daidai lokacinda kibiyar ta samesa, mum madai taji abu ya dan tabata amma ba kamar ta dad ba.”
“ruwa dad yace humaira ta mikomasa a firij mai sanyi, saida yasha wannan ruwan yadanjin dama -dama yace su taso su tafi batare da yafadamusu abinda yaji bakin zuciyarsa.”
“isarsu airport yayi daidai da saukar jirgin su MUSKAN, lokacinda ta fita a jirgin ido tarinka warowa tana dudduba su mum, can nesa ta hangosu lokacin suma sun hangota da gudu ta nufesu hugging din mum tayi tace I miss you so much my mum, I miss you to daughter mum tafada itama, murmushi dad yayi wajen dad ta koma ta kama hannunsa tace i also miss you dad, kanta yashafa yace my daughter I miss you too, ke baki ganmu bane fareeda tafada tana wurgomata harara cikin wasa, sorry my sisters tamatso wajensu hannayensu takamo dukka tace.”
“You know i love you all babes kawai ganin dad da mum ne yasa nayi mantuwa ban fara hogging dinkuba, kun hakura ammatas? Murmushi sukayi tare da hugging dinta suna dariya duka.”
“da kyar Dad yasasu suka shiga mota, suka kama hanyan gida.”
“da isarsu.MUSKAN tawuce daki tawatsa ruwa sukuma sukaje shiryomusu abinci, bata dau lokaciba ta shirya tasamesu a falo dukkansu sukaci abincin suna hira harsuka kammala, koda suka kammala kamar rufe bakinsu dad akayi(kodashike ai rufewan akayi ) ko maganarda sukayi. Niyan sanar da ita sunkasa yi hira kawai sukayi tayi.”
“sai kusan bayan sallah’n magriba kawu usman yazo shi gidansu FARIS ya tarar da Dad a gida da fara’arsu suka tarbesa, bayan sun gaggaisa hardasu MUSKAN yake tambaya dama tare suke da FARIS ne? Mum ce tace dashi ai yau tazota ita, yace toh yana da kyau, cewa su MUSKAN yayi subasu waje zasuyi magana da dad, ba musu suka mimmike suka nufi nasu dakin.”
“bayan tafiyarsu ne kawu usman ya dubi yayansa da girma ya soma koramasa bayanin yadda sukayi da FARIS yakuma rokarwa FARIS dad yaje sunemasa auren faty tunda sunnah zai cika.”
“Ajiyan zuciya dad ya sauke yace ba matsala gobe ma kuwa zasu yanxu zai kira daddyn faty yasanar dashi batun.”
“mum dai najinsu amma itama bata jin zata iya hanasu auren, amma can kasar zuciyarta kuma tanajin zafin faruwar haka.”
“Gdy kawu usman yawa dad hade da musu sallama ya tafi.”
“Cikin mum da dad ba wanda ya yi yunkurin tambayan wani mai dalilin sa na barin ayi auren shiru kawai sukayi duka.”
“da kyar dad yayi gaining courage ya dau waya ya kira daddyn faty yasanar dashi abinda yakeso, daddyn faty dayafi kowa murna naganin zai aurar da diyarsa yace ba matsla sai sunzo, nan sukayi sallama.”
“kawu usman yakira faris ya fadamasa yadda sukayi da dad harma da amincewarsa wow! FARIS yakasa boye farincikinsa sai gdy yake zubawa kawu, kawu yace dashi yaje yasami dad yamasa gdy shima toh yace dashi.”
“suna gama waya da kawu yakira dad yanemin yafiyarsa hade damasa gdy yace zai shigo gobe insha Allah, dad yasanar dashi MUSKAN tama zo yasa su anwar susata jirgi tazo, FARIS yace ba komai sai ya shigo kawai.”
“lokacinda ya kira faty dan yasanar da ita already daddynta ya sanar da ita amma tayi birisss ta saurari shi FARIS din daya fadamata tayita murna kamar da gaske harda kukan munafunci, shikam dariyama ta basa da tayi kukan, hira suka sha ta love kamar su cinye kansu ko suzama tsuntsu su ga junansu. “
**
Washegari kamar yadda su dad suka fada haka akayi sunje sun nemawa FARIS auren faty an basu, take suka bada sadakinta naira dubu dari , akasa Rana sati daya mai zuwa za’a daura auren.”
“Alokacinda aka sanar da FARIS wane yasa ruwa akasa yasha dan murna kasa boyewa yayi a fuskarsa.”
“yaje sa gidansu bayan sun gaggaisa da mahaifansa da yan uwansa ya mike yace bara yaje su gaisa da MUSKAN, dad yace idan kaje kasanar da ita zance amma kamata yadda zata fahimta kaji son, FARIS yace insha Allah, yasa kai yawuce a dakinsu fareeda ya sameta zaune tana game a wayarta.”
“sallama yayi, ta amsasa ba tare da ta dago kallesaba, shikuma bai kulataba dan yasan fushi take dashi waje yasamu ya zauna kusa da ita jikinsu na gogar juna suna iya jiyo numfashin junansu ga Sansanyan kamshin turarensu da ya hade a dakin, kansa ya kwantar bisa kafadarta a hankali yamata whispering (rad’a) a kunnenta wanda ni dai neerat banji mai yaceba, haryanxu ignoring dinsa tayi, dayaga da gaske take yasa sa saukowa har kasa ya kama hannayenta yace.”
“Am sorry baby boo i know you have the right to ignore me but just know d fact that I so much love and miss you too as you did, kiyi hakuri gani gabanki ina mai neman yafiyarki matata, would you forgive me yatambaya yana kanne mata ido daya.”
“she couldn’t stand anymore denying it she miss him, all she can is that let her make him understand his fault but she loves him so much, baki ta murgud’a masa ta dauke kai daga ganinsa “
“Dariyane yaso kwace masa amma ya danne yace plss baby boo, har yanxu she’s not ready to talk to him, FARIS fa yaga idan ba using da love styles dinsa yayiba he could not get his baby boo bak, dan haka ya mike kamar fita zai yi ai bata ankareba taji saukar bakinsa a nata kissing dinta yashiga yi romantically yana sarrafata yadda yakeso duk iya kokarinta tayi ignoring abinda yake mata but takasa, itama shahada tayi kawai tashiga..maidamasa martani, sun ma manta inda suke harsaida FARIS yacimma burinsa suka fada duniyar ma’aurata.
“Alokacinda ya gamsu, ya dawo hankalinsa yace am sorry i don’t mean to do that kinji yi hakuri my baby boo, murmushi tayimasa kawai, umurtanta yayi da su yi wankan tsarki akoi maganar da zaiyi da ita, ba musu ta biyemasa shida kansa ya sabeta yakaita toilet wankan ma shiyamata yawa kansa, koda suka fito saida ya tabbata ta shirya yaja hannunta suka nufi part dinsa ta kofan baya sukabi sukaje su.”
“bayan ya canza kaya shima yadawo inda take yayi yazauna kusa da ita baby boo ya kira sunarta.”
“Na’am ta amsa sa cikin sanyin muryanta.”
.
“magana yasoma mata kamar haka, kinsan ina sonki kuma har cikin kundun zuciyata, kuma akidayaushe burin na bai wuci na faranta miki na ganninki cikin jindadi da Kwanciyar hankakiba, I never wish naga ranki a bace koba kya cikin kwaciyar hankali, so dayawa nakan cemiki ke kadai zuciyata ta aminta dake kuma ke kadai nake son rayuwa da ke karkashin inuwar aure daya kuma ki kasance uwar ‘ya’ya na you know it right that bantaba jin son wata diya mace cikin zuciyata idan ba keba banida burin naga ina rayuwa da wata idan ba keba, kinzama *jinin jikina* zuciyata da ruhina, numfashi yaja yayi shiru daya kawo nan yana mai jin tausayin baby boo baisan yadda zai sanar da ita ba OMG! ya furta cikin ransa how will i tell her this, how will I convince her, how will she know that wat am capable of doing is not intentionally gosh yadafe kansa yace c’mon be strong enough oya FARIS gain courage huh! Duk maganar nan a ransa yake shi kadai, iska ya furzar a bakinsa mai zafi hade da daci.”
“musfar i don’t understand what you are saying go straight to the point and said it clearly so that I will understand MUSKAN ce tayi wannan maganar.”
“oh baby listen to what i will say and just know is not intentionally huh!.”
“yeah ok all ears musfar inji MUSKAN.”
“uhmm em…emm gaining courage yayi yace dama aure nake so nakar… Makalewa maganarsa tayi sakamakon ganin MUSKAN ta mike a guje tayi hanyan waje da gudu.”
“MUSKAN! MUSKAN!! MUSKAN!!! FARIS ne ke kiranta yana binta amma ina tuni ta fice daga part dinsa, da gudu taxo tawucesu mum zaune a falo, suna ganin ta tawuce suma suka rufomata baya, itakuma tana fadawa dakin ta banko kofar da karfi ghamb! Ta fada gado tana rusa kuka mai tsuma zuciya.”
“d’akin suka shiga dukkansu harma dashi uban gayyan duka, a kid’ime mum tasoma tambayarta lpia? Tambayoyi tarinka jeromata amma kodaya bata sami amsar daga bakin MUSKAN ba a dole suka koma kan shi FARIS da tambayar nan ya sanar dasu abinda ya wakana tsakaninsa da MUSKAN, damn it! Mum ta furta you see huh! Now get out of here ta umarcesa dayabar dakin badan yasoba yafita amma yaso ace ya sami ya lallashi baby boo.”
“fareeda, humaira, totally speechless suka tsaya baki sake suna ganin, da jin ikon Allah yanxu Ya FARIS dama abinda yake shiryawa no wonder amma koma wacece zai aura zataci ubanta kwafa sukayi duka, Dad yace su fita zaiyi magana da MUSKAN fita sukayi ransu duk a dagule suka bar mum da Dad.”
“d’ago MUSKAN mum tayi daga kwanciyar tazaunar da ita tana mai fuskantarta zuciyarta cike da tausayin ‘Yar tata, haka shima Dad,.”
“Da kyar suka sami karfin guiwa suka soma mata da nasihohin suka sanar da ita yin wannan auren shine mafita daya garesu idan ba hakaba zata iya sa mijinta yasoma bibiyar matan banza idan ta hanasa auren yin haka kuma sam ba yida amfani Dan da kishiyar waje gomma ta gida, da ire -iren wadannan kalaman nasu da nasihanda sukamata hade da kalamai masu taushi da zagi dasukayi amfani dasu sukasamu suka shawo kanta ta fahimcesu hade da rage damuwa , dan sun nunamata itace tasu suna sonta kuma baxasutaba yarjewa FARIS ya musguna ko wulakanta ta sabida yayi amaryaba, duk da abune mai wuya gareta Dan mata akoi kishi mussaman idan akace kishiya za’amusu toh ita MUSKAN kishin mai zafine sabida jitake kamar mutuwa zatayi barinma dataji wacce FARIS zai aura wayyo tarasa inda zata sa kanta if only zata iya bijirewa maganarsu Dad da tayi hakan amma yazatayi da kauna da hallacin da sukamata a rayuwa hakika idan ta bijirewa maganarsu tazama butulu.”
“saida suka tabbatar da tadan sami nutsuwa tukun sukamata saida safe suka tafi nasu dakin.”
“ka.mar jira su fareeda suke su mum su fita suka fada dakin, tambayar.MUSKAN suka soma wacece FARIS zai aura, tana a kwance ko kallonsu batayiba tace dasu FATY, what! Suka hada baki wajen fada both fareeda and humaira, faty fa kikace lalle biri yayi kama da mutum but ya akayi su mum suka yarda da hakan no fareeda that girl is up to somthn bahaka su dad yarda kuna idon a tsatsaye she is a witch, an evil, monster zaginta fareeda da humaira sukayi tayi harsaida suka gaji dan kansu suka daina amma sun dau alkawarin sai tagane kurenta dasu take zance.”
“FARIS kam duk yarasa mai yakemasa dadi duk lissafinsa ya dagule haka ya kwanta da tunanin abin yi.”
.
_ranar yadda sukaga dare haka suka ga rana MUSKAN nacan takasa bacci kwana kuka tayi tajin zafin mijinta zai kasance karkashin inuwar aure da wata wayyo taci kuka ta koshi, FARIS ma kusan shima kwana zaune yayi dan zuciyarsa ba dadi sam yake ji, su mum ma haka bangarensu, haka su fareeda duk haushi ya cikasu da sunada yadda zasuyi apasa aurenan da sunyi, Amarya faty kuma cikin jin dadi da farinciki ta kwana Allah Allah take gari ya waye tasamu tasoma preparation danji take kamar sati dayan yamata yawa bazai Zo ba take ji_
.
Kwanaki sunata shudewa hakama ranaku abubuwa da dama sun faru cikin wadannan kwanakin har zuwa yanxu da ake gobe daurin auren FARIS da faty, duk iya kokarin MUSKAN na ganin ta had’iye mai ke damunta takasa kullum cikin kuka take dama -dama ma dasu fareeda ke dan debemata kewa suna tayata hira da k’wantar mata hankali da kalamai masu taushi, ba a bar su mum da dad a baya ba awajen kula da farantawa MUSKAN rai, tunda incident d’innan yafaru tsakanin MUSKAN da FARIS batasake kulasaba, duk hanyanda zata hadasu kauracewa take haka da zarar yashiga d’aki ta tabba shi dinne zata kwanta kamar mai bacci haka zai kare wa kyak’yawan fuskarta da jikinta kallo wani sa’in ya bata peck (light kiss )a kumatu ko a lip ko ya gyramata kwanciya yatafi.”
“Su faty amarya anyi events kala -kala na keche raini akayi duk event din ta hade da ita da angonta, ta gaiyato kawayenta daga kasashe daban -daban kuma duk yan duniya ne, haka shima FARIS ya gayyato abokansa amma basukai na faty yawa ciki harda su Anwar da Aliyu wanda da kyar yasamu suka yarda zuwa auren dan su afad’arsu suna yin MUSKAN ne ba faty ba.”
“events sunyi ba karya saidai dangin FARIS kodaya ba wanda ya hallaci event din kama daga mum, MUSKAN su fareeda da yan uwa sabida duk cikinsu ba wanda yake murna da wanga auren.”
“sanin ba wanda zai kulasa yasa bai ma yimusu maganar zuwaba, faty kam taji dadin rashin zuwan nasu ma hakkan shi Yafimata alheri a ganinta.”
“A gidanan 9ja zasu xauna FARIS yasake gina tangamemen gida tsarin gidan hak na turawa sabida mr fauzy ne yayi zanen gidan tsaya fadin tsaruwan gidan da girmansa bata lokacine amma gidan yakai gida kowacce mace da part dinta kuma gidan upstair ne, a nan nijeriya zasu tare da zama saidai shi FARIS idan yagama cin amarci zai koma bakin aiki ansamowa MUSKAN transfer daga can tadawo da karatu Nile University dake abuja fadar Dad abarta anan sabida zata fi samin nutsuwa.”
“Yau jumma’a misalin karfe 2:00pm aka daura auren faty da FARIS akan sadaki naira dubu dari auren da manya -manyan yan siyasa da kasuwa suka hallata sai dai ko kotan mutannenda suka hallacin daurin auren MUSKAN faty bata samuba.”
“Andaura aure lafiya lau ango sai washe hakora yake wani dadi yake ji wanda shi kansa baisan na meyeba, abokansa sai faman tsokanansa suke da yimasa tsiya.”
“A cikin guest house na daddy akayi reception na maza.”
“lokacinda MUSKAN taji an daura auren FARIS wani irin kukan bakin ciki ta rushe dashi duk yan uwa sunyita rarashinta da kyar ta tsaida kukan amma can cikin zuciyarta *Hawayen masoyi* (sis rabi’at sk mash &Mr smile ) shike zuba daga idanunta.”
“Wow! Amarya faty basai na tsaya fad’a muku yadda zata kasanceba danyin haka bata lkc ne amma baki haryakasa rufewa dan murna ko kunya bataji yadda take abu kamar ba amarya bane.”
“Da dare andauki amarya aka kaita gidan mijinta dake ashokoro, yadda part nata ya hadu hmmmm ba karya komai nata ja da baki kamadaga kushin, kayan kitchen, pent ds.”
“lokacinda kowa ya watse aka barta da kawayenta nan suka bude babin hira harda ita kamar ba itaceba amaryan sabida lullubinta ta yane tazauna acikinsu sunta shan hira kuma duk akan zaman da zatayi da MUSKAN suke munafunci iri -iri da abuba da dama suke kunsawa faty akai yadda zata maida MUSKAN mowa wajen FARIS suke fad’amata sai babbake dariya suke kamar gidan rawa haka gidan ya koma.”
“kafin FARIS yatafi wajen amaryansa dad yace yabiya yadau MUSKAN itama yau zata koma gida kuma yahad’ata da humaira sutafi tare sabida zaman kad’aici taji dad’in hakan dukda bason komawa takeba.”
“An ajiyesu ansake musu nasiha kamar sabon auren Dad yace yamasan MUSKAN batada matsala saidai kai FARIS ka kula kazama adali mai adalci tsakanin matanka, ire -ire wadannan nasihan yarinka masa, saida ya tabbata yamasa nasiha sosai yabasu izinin tafiya,yabawa MUSKAN key mota sabuwa pill kirar KIA Yacenatane kyauta yabata harda kuka dan murna tayitamasa gdy, ba’abar mum abayaba itama tayimusu nata nasihan ankai ruwa tukun akaraba MUSKAN da mum da fareeda tana matsar kwalla suka kama hanya taki zama a gaba a bayan mota tazauna tare da humaira.”
“kamar FARIS yasan *bad’akala* (kwaishe) da ake a gidansa baiyi gigin gayyatan abokai su rakasaba daga shi MUSKAN da humaira kadai suka hanyan gidansa.”
“lokacinda suka isa gidan tundaga waje har suka doshi falon suna jiyo muryansu, bangaren MUSKAN yanunawa humaira yace taje ta tajirasu itakuma MUSKAN babban falon gidan dake kasa yanuna mata yace tajirasa yana zuwa ba musu duk suka bi umarnin sa.”
“A lokacinda ya isa kofan d’akin faty kamar kunnensa ya fashe dan yadda suke ihu suna babbake dariya, rai yahada fuskarsa a murtuke ya bankaje kofar, a rayuwa ba abinda FARIS ya tsana kamar hayaniya, ido curu -curu suka a lokacinda suka hango FARIS ko wacce tasoma tattara kwarmatsonta suna shirin barin gidan, angrily yace faty tasamesa a falon kasa bai jira mai zataceba yajuya yabarta a d’akin, mchwww! Duk sukaja tsaki itakuma tabi mijinta, duk fita sukayi kowa tayi gidan ubanta.”
“Duk ya tarasu a falon tunda faty tashigo taga MUSKAN tasoma wani shu’umin murumushi tana wani rankwasa da juya ido,zama tayi kusa dashi jikin FARIS ta shige da gangan dan ta bakantawa MUSKAN rai amma ko kallon inda suke MUSKAN batayi, shikuma tunda faty ta shige jikinsa yaji wani rin yarrrrr a jikinsa gawani dan iskan kamshin turare dayake fitadaga jikinta rikitasa take yanemi nutsuwarsa yarasa da kyar ya daidaita yasoma musu nasiha kamar yadda addinin islama ta tadana a gurguje yasamu ya kammala bayan yace da zarar yagama sati daya a d’akin faty girki zai koma 2-2days, ba abinda MUSKAN tace dasu haryagama yatambayeta ko tana da wani abin fada tace babu, yace toh ta wuce d’akinta saida safe, baby mujemana faty tace dashi ok toh haka tana kallonsu suka wuce faty rungume dashi, dan bakin ciki dayawa MUSKAN yawa kasa kuka tayi kawai murmushin takaici tayi ta wuce nata part din.”
“wow! Part na MUSKAN yaci uban na faty nesa ba kusaba duk da iyayen faty sun narka arziki amma bai kai wanda aka narkawa MUSKAN ba ita kallon nata komai ligh purple da pink falo da kitchen d’akuna kuma Golden haka babban royal bed dinta na duka dakunan side dinta golden ne komai nata yayi wanne yar wata sarki ko shugaban kasa haka dakinta yake, ta sami humaira harta sauya kaya zuwa na bacci itama haka ta sauya ta dauro alwala tazo tayita nafiloli, saida ta idar suka soma dan taba hira da humaira ko abinda yafaru bata fadawa humaira bacci tasoma ji tacewa humaira su kwanta dan gobe zasu makaranta kasancewar itama humaira a nile University tuke karantu, kuma ita MUSKAN a goben zata fara fita School din.”
“Amarya da ango kam saidai muce sam barka sabida suna shiga d’aki ba kunya faty tasoma romancing din FARIS abunka da mai nema tuni ya biyemata da kyar yasasu sukayi sallah’n raka biyu da ya wajaba nan ma ita ta nemi yahada kwanciya da ita.”
.
_waiyazibullah ya Allah ka tsaremu daga irin halin mata kamarsu faty, ace anyi mace ba kamun kai ba aji, ko kunya, yaku yan mata da manya mata mu na lura muzama daya daga cikin matan da Allah s.w.t yake suffantasu da matan hurul ayn, mukance masu alkunya da kamun kai..Allah yasa mudace AMIN YA RABBI_
“Ango FARIS fa an angwance duk da ba a Virgin yasami faty ba but bayida nacewa sabida yadda tsafi ke dako dashi.”
“saida suka sami nutsuwa bayan sundibi kusan tsawon awa 2-3 suna abu daya, wanka ma duk tare sukayi suna zuba love abinsu.”
“ko da suka gama duk abinda zasuyi suka nemi lafiyar gado.”
Su amarsu ta ango saidai muce asuba ta gari…………
**
Washegari tun sallah’n asuba da sukayi MUSKAN batasake komawa kwanciyaba azkar tarinka yi harsaida taga gari yadanyi haske nan dinma ba baccin ta komaba kitchen ta nufa dake bangarenta tasoma had’a breakfast na gidan gaba daya, Irish potatoes ta fere ta soya sa da eggs dinta ga peppers soup nata na chicken sai shayinta dayasha kayan kamshi ta hada ta juyewa su FARIS a warmers tazuba nasu da humaira takaimusu dining suma FARIS takaimusu part din faty a bude ta tara suma a dining ta ajiyemusu tabar dakinsu.”
“data koma tahada komai na kitchen datayi amfani dashi ta wanke tasss tayi mopping haka falonta ta kunna turaren wuta na yan Maiduguri dana kaimata gudumawa duk gidan ya bulbule da kamshi, ganin har kusan 8:00 yasa bata koma bacciba dan dama 9:00takeda lectures, d’aki tawuce tayi wanka data fitone ta tada humaira tace tayi wanka itama, humaira da bacci bai ishetaba ta mike a wahale tayi wanka tafito tasami MUSKAN ta shirya tsabb cikin wata super lemon green dinki zamani akawa rigar tadaura zaninta kwass abinta tasha ado kamar wata amarya sai shining take like a star, baki wangale humaira take gininta tace mata kai aunty kinyi kyau, na gode tace da ita kiyi maza kishirya yanxu kusameni a falo toh ta bita dashi kawai, Itama atamfa tasa amma ita d’inki riga da skirt tayi kyau itama, a falo ta sami MUSKAN, dining MUSKAN taja suje suci abinci full of surprise tace MUSKAN yaushe kika tashi har kinyi breakfast and all those work, hmmm kekike bacci ni nagama komai nasu FARIS ma na kaimu-humaira bata bari ta karasa maganarba tace kardai kucemin ke kikamusu girki? Of course yes ni namusu ta bata amsa, you are stupid wlh yanxu har girki zaki musu Allah kinbatan rai nikam, sorry lil sis amma kinsan hakkina ne na musu and kinga ni fa duk abinda suke kansu sukewa kuma fadar ubangiji da nasu mum nake bi if not am not gonna do it babe.”
“Toh naji yanxu muci abincin mutafi school karmuyi missing lectures ko, toh MUSKAN tace bayan ta zuzzubamusu abincin da tea suka soma ci.,”
“inless than 20mins suka kammala komai suka fito a sabuwar motanta da dad ya siyomta KIA tajazu suka tafi school kota kansu FARIS basubiba.”
“toh su amarya kuma sai 11:00suka tashi wanka suka chaba ita da angonta dasuka fito sukaga warmers a kan dining nan suka baje suka kwashi girki abinsu.”
“koda suka gama garden na gidan suka fita shan iska suna zuba love wane su cinye junansu ko fita yau FARIS baida niyan yi idan baki sunzoma wajen amarya ma hira ka’dan suke taba ta sulale wajen mijinta .”
“FARIS baidamu daya duba MUSKAN ba kuma baiji motsintaba koda yamma dasuka dawo basu haduba suma basu nemesaba, nan ma indomie dinsu suka dafa da eggs sukayi pilling suka ci nayanxu kam basu kaiwa su faty ba.
•••••
Lives moved on haka rauywarsu ta kasance har 1week koda FARIS zai koma d’akin MUSKAN ranar ma faty bata kyalesaba har saida yabiya mata buka tarta taga ta mantar dashi MUSKAN har tasake jansa suka kwana tare, kullum haka take da zarar randa tasan girkin MUSKAN ne saitayi abinda FARIS bazasa wajen MUSKAN ba.”
“ita dai MUSKAN na gani ikon Allah amma ko ajikinta bata taba nunawa koda a fuskaba and bata sakewa humaira ta gane komai dake gudana, kuma ko mum takira ta tambayeta ya zamansu? da Matsala? Duk saidai tace masha Allah ba komai shiyasa mum ke kara son MUSKAN cikin ranta.”
“duk kwanakinda suke shudewa FARIS basu cika haduwa da MUSKAN ba watarana su hadu yaxo shiga gida tana fita ko yana fita tana shiga, girkima yanxu taciresu kowa shi ke nasa, karatu ya kankama yanxu suna second semester exams zasu fara duk hankalin MUSKAN na akan karatunta dad’inta ma daya course dinsu daya da humaira kuma aji daya suke shiyasa kullum zaka gansu da laptop ko test books agabansu suna karatu.”
“duk iya zamansu ba wanda ke zuwar musu gida sai zaryan kawayen faty dasuka maida gidan kamar gidan ubansu, kullum suna cikin zuwa gidan.”
“Abun FARIS fa sai addu’a sabida aikin ma yanxu saida suka yomasa transfer yadawo gidan Nigeria da aikin.”
Yanxu almost getting a month da aurensu faty while MUSKAN kuma tana 3month 2weeks da auren FARIS.”
“yau kamar kullum ba school humaira tafita unguwa while faty itama taje gidan wata kawarta, MUSKAN kadaice a gida tana zaune batama jin dadi 2days kasala da yawan bacci sun mata yawa ga yawan kwadayi tarasa mai yasameta tana cin gautanema yanxu dan tashin zuciyar da yake damunta karar tsayuwar mota taji cikin ranta tace Allah yasa humaira ce dan ni nagaji dazama ni daya wlh.”
“FARIS ne yashigo bayan ya Parker motarsa ya shiga cikin gida yunwa yakeji yaje part na faty bata nan duk iya bincike yayi amma ba abinci a part dinta, haushi duk ya cikasa har ya zauna komai ya tuna oho ya mike yayi hanyar dakin MUSKAN da sallamarsa yashiga ta amsa masa amma bata waiwayi inda yakeba.”
“gefenta yaje yasamu yazauna yace MUSK- bai karasa tamike a guje tayi hanyan kitchen sink tasamu tasoma kwarara amai wane hanjinta zasu fito waje kamshin turarensa kadai dataji shi yasata amai.”
“A guje yabiyota kitchen din bayanta yaje yatsaya duk ya kidime yanajin yadda take amai saiji yayi tausayinta ya darsu cikin ransa he cannot stand any more zuwa yayi, yayi hugging dinta yana bubbuga bayanta yanata fad’in sorry har saida tagama ta kuskure bakinta tana juyawa ta kwace jikinta daga hugging din da yamata binta yasoma dayaga tana tafiya yana kiranta amma ita ko juyawa batayi ba harta kai falo ta zauna.
“shima biyota yayi yasoma tambayarta bata da lapiyane taki amsasa dayaga haka yace ta tashi suje asibiti, tabb nan fa tace ba inda zata, dayaga da gaske take, yabata rai shima forcefully yasoma janta bayan yaja hijabinta dake kan kujera tana tirjewa yana janta saida yadakamata wani irin tsawa daya tsoratata ba shiri tayi tsitt haryasa a mota ya kama hanyar asibiti.”
“suna isa asibiti basu wani sha wuyaba suka sami ganin Doctor kasancewar FARIS yasansa, Doctor yama MUSKAN wasu yan tambayoyi duk ta amsamasa nan yasa wata nurse ta karbi fitsarinta a gwada.”
“in less than 30mins nurse din tadawo da result na fisarin, Doctor yana gani yakaranta yana ganawa yace wa FARIS congratulations matarka na dauke da juna biyu na wata daya da yan kwanaki.”
“FARIS daya tashi daga zaunenda yake yayi hugging na MUSKAN yana bata peck ta ko ina yama manta asibiti suke saida tadan cijesa a kunne yadawo hankalinsa, gdy da kyauta ya ma Doctor da nurse din, bayan doctor yakaranta musu jawabai da ya kamata suka kama hanya, yama rasa idanda xaisa kansa duk da FARIS ba a hankalinsa yakeba but yana son baby musamman daga MUSKAN wacce takasance *JININ JIKINA* he can’t deny it he loves it and yakasa boyewa.”
“tun a hanya yasoma sayesayen kayan kolama sabida Doctor yafadamasa mata masu ciki na kwadayi itadai MUSKAN ido take binsa dashi kawai bata magana.”
“kafin su karasa gida saida yayi siyesiye dayawa, suna Parker mota faty na shigowa gidan itama ganinsu tare kuma FARIS yazaga yana budewa MUSKAN kofa yasa faty fitowa a harzuge tayo wajensu da saurinta amma ina kafin takarasa MUSKAN takama hanyan shiga cikin gida FARIS kadai ta tarar ko sannu dazuwa babu tace baby daga ina?.”
“Daga asibiti yabata amsa.”
“doing what at hospital? Tasake tambaya “
“MUSKAN ce ba lafiya nakaita ganin Doctor.”
“And sukace mai yake damunta.”
“Enough! Ya kina ta min tambaya kamar wacce take a lawyer.”
“yes dole na tambaya i wanna know what happen to her.”
“okay fine kinaso kiji ko toh ciki ne da ita she’s taking my baby.”
“WHAT! Tafada da kakkausar murya CIKI Noooooo bazai yuba I have to do something bazata zauna da cikin nan ba da gudu tadau motarta ta fita a gidan @360.”
“shikam FARIS ko kallonta baiyiba yasa kai ya shige cikin gidan “.
@ 360 take sharara gudu a kan kwalata ita kadai tana magana kamar tabab’iya tace a yau -yau d’inan boka zai zubda cikin nan Cox wlh bazan bari ta haihu ba FARIS nawa ni kadai ne NEVER! Ta fad’a da karfi, ko meemah kawarta bata naimaba tadau hanyar bebeji .”
“FARIS dai kam yana shiga cikin gida part na MUSKAN yana nufa tare ya and tadda ta da humaira harma da fareeda duk suna hira abinsu shima fuskarsa dauke da murmushi mai kayatarwa yayi sallama.”
“Amsa masa sukayi duk fareeda dai da humaira they are full of suprise yadda FARIS ya canza kallo -kallo suka soma basuma gama ganin abin mamakiba saida sukaji yace.”
“Baby boo Hope bakya jin komai yanxu? yana maganar yana zama a kusa da ita.”
“Baki ta murgud’a tace nifa ka takurani wai wayace ma inajin wani abine.”
“Jawota yayi zuwa jikinsa tana tirjewa amma ina rikonda yama bana wasabane yace.”
“Ni nafada idan ma kinada lafiya what about my baby? yana nuna cikinta yace shi yaci abinci?.”
“pls ni kasani ko baka ganin su fareeda ne kake irin wannan abin.”
“Shi sai yanxuma yakula dasu, sukuma suman zaune sukayi suna jiyo abinda yake fad’a if har da gaske MUSKAN nada ciki toh ba wad’anda zasu kaisu murna, tunaninsu yakatse musu lokacinda ya gyra throat dinsa yace.”
“magulmata wato duk kunzo kun kasa kunne kunajin abinda muke da baby boo ko? Toh maza ku tashi yanxu ku dafomin indomie dan yinwa nakeji, yajuya wajen MUSKAN yace baby mai zakici su dafamiki kai ta girgiza tace ba abinda zan-.”
“ko kare maganar bata yiba FARIS ya amsheta yace bazai yuba sabida mai yanxu zaki barmin baby da yunwa no that’s not possible ku dafo indomie’n tare da ita.”
“Kuje mana yinwa fa nake ji yace dasu fareeda.”
“mikewa sukayi suna d’an tab’e baki.”
“Baby boo tun yaushe kike yin amai ‘n.”
“Bansaniba tafada angrily dama kadamu ne dani ko neman sani?.”
“Nadamu mana kuma neman sani tunda ina mijinki.”
“MIJI! Tayi exclaiming wow! Sai yau kake kiran kanka matsayin mijina lol you fooling yourself coz kana da matar da kafi so fiye da komai “
“wace mata nake dashi da har inaso fiye da ke?.”
.
“kana tambaya! FARIS i think you are dump bani zanbaka amsaba but kaje wajen Faty zata baka tana kaiwa nan tayi hanyar kitchen abinta tabarsa nan zaune.”
“Kansa ya dafe yace oh baby boo kishi, wayarsa yacire yakira mum.”
“lokacin mum na zaune da Dad suna hira wayarta yadau ruri hannu takai tad’au wayar tana ganin mai kiran tad’auka tasa a kunnenta.”
“Assala mu’alakum tace.”
“wa’alaiki salam, mum ina yini.”
“Lafiya kalau son ya kuke da iyalanka.”
“lapiya qalau muke.”
“masha Allah inji mum, nan suka shiga gaisawa FARIS yace mum i had a surprise for you albishirinki.”
“Goro tace.”
“Fari ko ja mum.”
“Fari kal “
“Ok mum your daughter in law is taking my baby.”
“Mum da FARIS yad’auremata kai tace wacece acikinsu.”
“kai mum your own daughter MUSKAN.”
“mum datake a zaune take tasauko kan kujerar tayi sujjadal shukur tana mai godewa Allah.”
“Son ina take bani ita na tambaye mai take so na dafamata.”
“mum bata nan fa tana kitchen dasu fareeda.”
“kaimata wayar toh.”
“Kai mum yana murmushi ya nufi hanyar kitchen d’in, yasamesu suna hira abinsu yace da MUSKAN ga waya mum nason magana dake ya mikamata ya bar kitchen din.”
“wayar ta sa a kunnenta suka gaisa da mum.”
“bayan sun gaisa ne mum tace daughter mai kikeso na dafamiki.?
“MUSKAN da kanta yagama kullewa tace a ranta kodai wannan mara kunya yafadawa mum inada cikene? Duk cikin zuciya take maganar a fili kuma tace mum kunun gyd’a nake so.”
“ok daughter yanxu zan kawomiki.”
“ok tnx mum.”
“you don’t have to.”
“daga nan suka tsinke wayar tayi hanyan kaiwa FARIS.”
“MUSKAN na zuwa tahau FARIS da matsifa ita lalle ya fallasata sai da tayi mai isarta ta wurgamasa wayarsa tayi gaba.”
“Shikam dariya ma taso basa amma ya gimste dan Doctor yafad’amasa mata masu ciki akoisu da matsifa wani sa’in shiyasa yakima kulata hartayi ta kare.”
“Kallo ya ke abinsa cikin kwanciyar hankali yau dinnan yanaji wani farinciki na mussaman yana shigarsa.”
“A lokacinda mum take fad’awa Dad MUSKAN na d’auke da ciki dasuka kare wayar, wani irin farinciki ne ya lullebesa shima saida yayi sujjadal shukr a wajen yayi ta godewa Allah yana kuma mata addu’ar Allah yaraba da cikin lpy.”
“Mum kam kitchen ta wuce tasoma girkawa daughter abinda take so.”
“MUSKAN dai zaman kitchen ya gund’areta sabida kamshin girkin da suke ita yana tada mata zuciya shiyasa ta wuce d’aki abinta ta kwanta.”
“FATY ta isa garin bebeji tasoma shiga kuryan dajin kusan hankalinta baya jikinta dan wani uban sauri datake ta zabgawa.”
“Tana isa ta tarar da boka kwance yanata shure -shure yana rike da makogoronsa wasu irin kumfa yana fita daga bakinsa idanunsa sun sauya sunzama ja jir dasu gawani bakin duhu daya mamaye wajen, a haka faty ta taddasa tana ganin sa haka amma ita ko a jikinta tasoma magana tana cewa.”
“BOKA! BOKA!! Katashi ka taimakeni wannan shegiyar tana d’auke da ciki, boka kaban maganin da zai barar da cikin kusan sau biyar take magana amma ina boka ko magana baya yi can akayi irin wata kara da ya tsoratata take kuma boka yadaina motsi wajen atake yakama wuta yasoma ci bal-bal.”
“Faty na ganin wutan ga kuma boka baya motsi ta d’iba @360 ta wuce motarta tana maida numfashi , duk a tsorace take tama kasa zama take ta tayar da motarta tadau hanyar gida.”
“A waya takira meemah tana fad’amata duk abinda yafaru kama daga abinda taji abakin FARIS, barinta gida, zuwanta wajen boka da yadda ta gansa tacemata gata a hanya yanxu, toh kawai meemah tace da ita.”
.
“some hours past, FARIS zaune dasu fareeda suna cin indomie ‘n su, mum tazo tasamesu duk suka k’washi gaisuwa a lokacinda tashiga dakin, bayan ta amsasu tace ina daughter ‘n ta, FARIS yace mum tana d’aki, ok fareeda je kikara tazo ta sha kunun, ok mum fareeda ta wuce d’aki.”
“Da kyar fareeda ta tashi MUSKAN bayan sunsha daru ita MUSKAN tace wai fareeda ta tasheta shiyasa taji haushi while fareeda tace ai mum ce tace na tasheki suna ta fad’a suka isa falon, mum ce ta lallashi MUSKAN, suka gaisa da ita tana tambayanta ya baby, duk kunya ya cika MUSKAN sai aikin harara datake aikawa FARIS ta gefen ido.”
“kunun gyd’a mai kamshi mum ta zubamata tace ta sha, Ba musu ta soma sha ita kanta taji dad’in kunun har da karawa.”
“FARIS kwadayi yace abasa kunun yasha shima mum ta hanasa tace na daughter ne ita kad’ai.”
“mum nimafa d’an kine.”
“A da amma ba yanxu ba danni yanxu daughter kadai nake da.”
“baki ya tab’e yayi shiru bai sake magana ba.”
“Suna zazzaune can FARIS yayi wani irin ihu yana dafe kansa, ahhhhh kaina mum, baby boo, duk yana kiran sunansu ahhhhh yasake cewa take yafad’i summeme?”
“Iya rud’ewa su mum sun rud’e tunba MUSKAN ba kuka ma tasoma, da kyar suka d’auki waya suka kira Dad suka fad’amasa maike faruwa, yace gasanan zuwa yanxu.”
“Zama sukayi darsham MUSKAN ta daura kan FARIS a laps dinta sai surutai take tana zubda hawaye su mum na gefe suma aikin kukan suke.”
“Suna cikin haka Dad ya iso da wani abokinsa suka zo, abokin irin uztazainan ne, daga yadda Dad ya tarar da iyalansa sai yaji zuciyarsa ta karaya shi a tuninsa FARIS ya mutu shima darsham ya zauna yayi shiru.”
“Abokinsa da yaga haka sai ya zo har inda FARIS yake yasa kansa a kirjinsa yaji ko yana numfashi, cikin sa’a yasamu FARIS na numfashi, da murmushi a fuskarsa ya sanar dasu hakan.”
“Alhmdullilah! Dukkansu suka fada suna masu sauke ajiyar zuciya dajin wanga good news.”
“Ruwa ya umarcesu da akawomasa mai kyau cikin kofi.”
“Da sauri mum takawomasa ya karba, addu’oiaddu’oi yasoma karantawa yana tofawa cikin ruwan can ya ajiye ya kama kan FARIS yasoma karanta addu’oi da karatun alkur’ani mai girma, yadau lokaci yana haka kamar jira FARIS yake ya farfad’o hade da yin wata irin atishawa sai amai ya soma nawani bakin abu, sannu kowa na wajen ke cemasa duk they are full of surprise na aman da yake, mutumin kuma bai bar karatunba har saida FARIS yagama aman, yasake cewa a kawomasa ruwa da bowl na wanke hannu , nan aka kawomasa FARIS ya baiwa yace ya kurskure bakinsa sai yazuba a bowl din, yadda yace haka FARIS yayi, sai yanxu mutumin yadau ruwanda yayi tofi a ciki yace FARIS ya shanye duka, ba musu FARIS yayi yadda yafada ai ko yana shanyewa yasoma zare idanunsa yana bin kowa na dakin da kallo, sunayensu daya -bayan daya yasoma kira can yace Mum yaushe kuka zo? Baby boo yawshe su mum suka zo bansaniba?.”
“Dukkansu cike suke da mamakin tambayarda FARIS yake musu.”
“Abokin dad na ganin yanayinsu yasan cewa duk basu san mai yafaruba dan haka yashiga yimusu bayanin kan sihiri aka masa duk yadda abin yake yakoramusu jawabi akai.”
.
“Daga FARIS din harsu na d’akin duk suncika da mamaki basu gama cika da mamakiba wayar FARIS ya dau ruri yana neman agaji.”
“hannu yasa ya dauka yace “Hello.”
“daga dayan bangaren akace hello ina fatan da SALMAN FARIS nake magana.”
“Eh dashi kake lpy ya dai ko? “
“Ba lpy ba gaskiya sabida a halinda ake ciki yanxu matarka na hannunmu tayi accident wanda taji rauni da dama rai a hannun Allah take, ita tace akiramata kai sabida akoi maganar da take son fad’amaka, zaka iya zuwa National hospital yanxu dake garin abuja kittt aka kashe wayar.”
“wayar yabi da kallo tukun ya korawa su dad bayani, take dad yace su tashi suje hospital din.”
“Gabaki daya gidan suka fita suka shige cikin motocinsu, sai hospital.’
“lokacinda suka isa asibitin direct d’akin da faty take aka wuce dasu, tana ganin FARIS tasoma kuka da neman yafiyarsa duk abinda ta aikata tasoma fad’a da bakinta wiwiwi! Take zubda hawayen nadama is too let to correct her mistakes tasani, bata gajiba tarinka rokon both MUSKAN da FARIS su yafemata, haka su Dad da Mum.”
“Tausayi iya tausayi tabawa kowa ga kuma alajabin abinda ta aikata ganin kada lokaci ya kure dad yace yaya femata. Haka mum, FARIS da MUSKAN suka biyo baya, wani hammdalla da ajiyan zuciya ta sauke tace ku tayani neman gafara wajen iyayena, I LOVE YOU FARIS tafada tana murmushi a haka fa Faty tace ga garinku ta cika kenan.”
“Duk iya dauriya da kowa na wajen yayi amma saida suka zubar da kwalla musamman FARIS dayake ganin is just because of the love she had for him that make her go through all this.”
“Jiki duk a sanyaye suka karbi gawan faty suka tafi gida.”
“lokacinda aka sanar da iyayenta ba karamin tashin hankali suka shigaba amma dashike dad namijin duniya ne yayita kwantar musu da hankali har suka samu nutsuwa.”
“Anyimata sutura ankaita gidanta na gsky, ni neerat nace Allah ya jikanki faty aunty sis ma haka tace sai fans na house of JININ JIKINA novel, da sauran groups duk sunce Allah ya jikanta kuma sunzo gaisuwa.”
“A wajen gaisuwa na hango su aneerlurv, miemie bee, faty azland, miss neerat, seemaluv, mjay, nafee anker, hamagee, yar mama, maryam s bello, Aisha iliasu, ayusha Muhammad, ehart tsafe, mum ihsan, cute xarah, RAZ, dimples, batul mamman,my rooky kaex ds.. duk sun zo gaisuwa harda dan matsan kwalla .”
.
“Anyita karban gaisuwa daga wajen gidan har cikin gidan mutane da dama sun hallacin rasuwar, anyi sadakan uku har da bakwai lpy, duk cikin kwanakin nan FARIS da MUSKAN basa haduwa sabida mutane.”
**
2 days dagama rasuwar dad ya tara familynsa duka ya ajiyesu yayita musu nasiha mussman FARIS da MUSKAN, yakuma ce su yawaita ibada kuma duk bayan 1-1week za’ana kewaye gidansu dasu kansu da Al Qur’ani mai girma.”
Kamar yadda Dad yafad’a saida aka kewaye gidan da al-qur’ani tukunna da daren laraba aka rakasu Gidansu.”
“kamar sabon aure haka suka kasance dan yadda ake kai amarya da abinda akewa amarya shi FARIS yawa MUSKAN.”
.
“karfe 11:00 na dare FARIS sanye da pajamas nasa ya nufi d’akin MUSKAN, a gaban madubi ya taddata sanye dawata arniyar baby pink sleeping dress wanda iya cinya ya tsaya mata.”
“Tana shafe jikinta da turare yashigo, ta gansa cikin madubi amma tayi ignoring kamar bata gansaba, shikuma karasawa yayi har inda take yaje ya kwantar da kansa a bayanta a hankali cikin Salonsa yajuyarda ita hannunsa danata ya hada yace.
“baby boo am sorry for everythi-.”
“Shhhhhh tasa yatsanta a lips dinsa tace you don’t have to everything is okay, past is past let face the present and continue tense handsome tana murmushi.”
“Is that so baby boo.”
“yeah ta d’aga masa kai.”
“I love you eternity my wife.”
“I love endlessly too my handsome.”
“Dagata yayi chakk sai kan gado, bakinsa yakai wuyanta yashiga kissing da duk ilahirin jikinta , batayi kasa a gwiwaba tasoma maidamasa martani she miss him so much, haka shima he miss her so much, wani irin romancing dinta yasoma wanda ba duka maza ne suka iyaba sai yan baiwa duk ya rudata da yanayinsa she could not say how she’s enjoying what he’s doing to her, sundau tsawon lokaci suna abu daya daga baya kuma suka lula duniyar ma ‘aurata.”
.
Wow! Ba sambatun da FARIS bai yiba sai dunbin albarka dayaketa samasa this night was a great full night in there life they could forget it never, dukkansu sun gamsar da juna and they enjoyed it.”
.
_After 2 weeks_
Bayan sati biyu nan abubuwa sun daidai ta kamar yadda akeso.”
“Kullum love bird din suna tare manne da juna suna zuba love kamar ba gobe.”
“Duk inda FARIS yake MUSKAN na wajen suna manne da juna.”
“MUSKAN takoma makaranta yanxu tana cikin k’wanciyan hankali, tana samun kula daga mijin iyayensa da ‘Yan uwansa itama tana iya kokarinta wajen kula da hakkin mijinta ba abinda FARIS ya nema MUSKAN tagaza yimasa haka itama bata nemi komai ba yagaxa yimata.”
“FARIS yamaida hankali sosai yanxu kan iyalinsa dakuma ibada, duk wani abu tare suke da MUSKAN kullum a gida suna zuba soyayya, ko kwak’waran motsi MUSKAN tayi saiya tambayeta lafiya, kullum kuma cikin sayomata kayan k’walama yake da k’wadayi yadauki son duniya yad’aurawa cikin da ke jikin MUSKAN duk randa yafita saiya sayowa own born stuffs kamar su kayan wasa ds.”
“Idan yana hka MUSKAN kallonsa kawai take ita dan bata isa hanasaba duk abubuwan sunyi yawa dayake saya amma ba hali.”
“Aikin sa ma sai MUSKAN tayi da gaske take sasa zuwa inba haka shiyace a gida zai zauna ya kula da’ita da babyn sa.”
“Idan yayi irin wad’annan magananganu MUSKAN kanyi dariya tace.”
“Musfar idan baka fita nema mana kudi ba da mai zamu zauna ko da mai zaka ciyar damu.”
“Cewa yayi ai ina da kudin da zan ciyar daku harzuwa nan da shekara hamsin.”
“Na yarda amma duk da haka kaje aiki kodan ka taimakawa aluumma.
“Naki baza niba o’o ni wayo kikemin.”
“See you! Wai babba dakai zanwa wayo? Please go for the sake of our own born baby.”
“Ba abinda FARIS yake so kamar wannan baby’n nasa dan haka yace yaji zaina zuwa wajen aikin is that ok with you.”
“Yeah I love you handsome.”
“I love you too beautiful.”
“Daga nan sai ya jawota jikinsa suna dan tab’a wasannni da sauransu.”
“Cikin MUSKAN kullum cikin girma yake dan kulawanda yake samu yanxu cikin yakai 8months ya girma sosai ga tayi jiki ta huru kamar cincin, kullum cikin tsokanarta FARIS yake akan jikinta idan yafara wani sa’in har kuka MUSKAN take ita bata so yace tayi jiki dayawa.”
“Cikin na bala’in bata wahala ba kadan ba dan irin cikinnan ne mai tsayi, bacci da kyar cin abinci da kyar, wanka komai ma da kyar take ga matsifa daga FARIS har su fareeda basu tsiraba .”
“Both humaira da fareeda suna taimaka mata kusanma sun tare a gidan da zama amma basu tsiraba MUSKAN matsifa take zazzaga musu sudai shiru suke sabida sunsan za’a rina shiyasa basa kulata.”
“FARIS yace suje ayi scanning amma MUSKAN taki badan yana soba yabarta tazauna abinta sabida kwanciyar hankalinsa shine nata.”
.
“Watan haihuwa fa yazo komai sun shirya dakin yara biyu FARIS ya gyra daya na baby boy daya na baby girl, na baby girl mai fentin pink da katon pics na Barbie, na baby boy kuma fenti blue da katon pics na Spider-Man.”
“Kayan wasa da duk wani abu daga Dubai yayi ordering dinsu aka xo aka zuba duk a d’akunan, idan Kaga d’akunan ba abin kasaceba dan tsabar kyau.”
“MUSKAN tayi farincikin yadda FARIS ya tsara wa own born baby dinta daki duk da batasan mai zata haifa ba amma taji dad’in ganin d’akuna biyu.”
“Yau Friday da dare misalin 10:00pm MUSKAN na kwance bisa kirjin FARIS tazaga hannayenta a cikinsa tana ta wasa da cikin nasa dakuma parks d’insa tayi shiru bata magana, shima FARIS kusan hakkan ne gashin kanta mai tsansi yake wasa dashi shima.”
“Murkuso murkuso take wani lokaci can bayanta ya amsa wani irin azabbaben ciwon mara da baya ne ya saukemota Arhhhhh bayana marana musfar wayyo zan mutu, mummy wayyo tanata ihu.”
“A kid’ime FARIS yasauko kan gadon d’agota tare da hugging d’inta tightly a jikinsa yace baby boo u won’t die, kidaina fad’an haka am here for you huh! “
“No musfar just call mum for mie it hurt ahhhhhh, take me to hospital tafada cikin wahalalen murya.”
“Da sauri ya ajiyeta yanufi hanyan waje d’akinsu fareeda yaje yasoma k’wank’wasawa kon..kon..”
“who is here knocking the door.”
“Sister came out baby boo “
“Suna jin haka suka fito a kidime suma d’akinnasu suka nufa sun tarar da MUSKAN duk ta galabaita sai gumi take had’a ba bata lokaci fareeda tad’au kayan haihuwa suka cincimeta suka fita.”
“A mota suka sata FARIS da kyar yake jin zai iya driving saida FARIS tace be strong bro kada ka karaya pls drive, maganar fareeda yabi suka kama hanyan hospital.”
“Fareeda da humaira a baya rike da MUSKAN sai sannu suke jeramata sun isa National hospital dake abuja nan da nan nurses suka karbi MUSKAN sukayi hanyan Labour room da ita.’
“Hannun FARIS sarke dana MUSKAN suka je har Labour room, saida nurses din sukayi da gaske FARIS yafita a d’akin badan yasoba hakan ma.”
“Yana fita yasami su fareeda zaune kowa yayi jingum, fareeda na ganinsa tace brother na kirasu mum nafad’amusu kasunan zuwa yanxu.”
“kansa ya kwantar ya jikin fareeda bai yi maganaba.”
“Fareeda na ganin haka tasoma bubbuga bayansa tana calming dinsa.”
“Su mum na isa asibitin reception suka wuce acan suka tarar da su FARIS a guje yayi wajenta hugging d’inta yayi wiwi kamar karamin yaro yake kuka yace.”
“Mum, baby boo please kifad’awa Doctor kar baby boo ta.mutu idan ta mutu mum nima mutuwa zanyi.”
“Shhhhhhhh mum tasa yatsanta a bakinsa tace stop saying that hun! Won’t you be strong? Ya kake abu kamar ba namijiba? Stop it please baby boo ain’t going to die.”
“Hawayensa Dad yashiga wiping da yatsansa saida yagama yajasa zuwa jikinsa wani kujera yasamu suka zauna Dad ya dubesa yace.”
“Son bansanka da hakaba, kai jarumin keep on being that jarumin maza kaji.”
“Kai FARIS ya gaid’awa Dad.”
“That’s my son yanxu tashi muje muyi nafila so I that zamu roki Allah ya sauketa lafiya.”
“Hannunsa Dad ya rike suka mike a tare suka wuce sunyi alwala suka soma sallah abinsu.”
.
” _Some hours later_ Kusan awanni 3 MUSKAN na Labour room tana ta fama duk ta galabaitu iya galabaita tama fita hayyacinta tana awa na hudun ne wanda yayi daidai karfe uku na dare tayi wani irin nishi sai ga kan santalelen d’an ta nurses na karba tasake nishi sai wani kan baby, basu gama da wancan ba sai ga kan wata ‘Ya mace ta fito, wani irin wahalallen ajiyan xuciya ta sauke nurses dinkuma take suka yanke cibiya sukayi abinda ya kamata cikin kankanin lokaci aka shirya su, nan aka wuce rest room dasu.”
“Wata nurse ce ta fito tasami su FARIS sai zirga -zirga yake a kofan reception din uhmmmm tayi gyran throat dinta, duk suka maido hankalinsu gareta.”
“Tace kune iyayen patient da take ciki ko.”
“Eh mune inji Dad, dasauri FARIS yazo yace what happen to my wife?.”
“Ka kwantar da hankalinka Allah ya sauki matarka lafiya ya azurtaku dasamun triplet twins.”
“WHAT! Are you kidding me? FARIS yafada full of exclaimed.”
“No am not kidding just come and see for yourself.”
“Dukkansu suka rufamata baya zuwa d’akin da MUSKAN take.”
“Suna shiga suka tarar da The biggest surprise in their life’s gabadayansu suka zube suna masu yin sujjadal shkr suna godiya wa Allah.”
“FARIS yad’au tsawon lokaci ahaka kafin yad’a kansa hawayen farinciki kwance a fuskarsa.”
“Daya bayan daya suka soma d’aukar baby’s din kowa zaka ga farinciki kwance fuskarsa sai murmushi suke, duk abinnan dasuke MUSKAN na bacci bata saniba sabida tsan -tsan wahalan da tasha yasata baccin dole.”
Zama yayi setin fuskar MUSKAN yana karemata kallo wutan sonta nasake ruruwa cikin zuciyarsa, ana haka MUSKAN ta bud’e idanunta karappp yasauka cikin na FARIS dasauri tajuyamasa baya, Baby boo yafada, hakan yadawo da hankalinsu mum gabadaya kansu.”
“Dasauri mum ta taso tazo wajen ta tace daughter Kintashi? Sannu my baby? Har yanxu taki juyawa ta kallesu, mum ta gane dan haka tace FARIS dan fita ina zuwa, ba musu ya fita yanata kallon MUSKAN kamar yaje ya rungumeta yake ji.”
“Dad ma ya fita dan haka MUSKAN tajuya hawaye take, dasauri mum ta soma sharemata tana fad’imata kalamai masu dad’i.”
“Saida mum tasamu ta kwantar mata hankali tukun nurse tace abawa yara nono.”
“Nan fa wani darun ya tashi sabida MUSKAN taki bawa yara nono harsaida mum ta tsawatar mata tukun tabasu daya bayan daya tanayi hawaye na kwarara a idonta sabida zafin da takeji ga yaran zuga suke kamar ba gobe.”
“saida mum ta tabbata nonon ya ishi yaran tukun takarb’esu ta k’wantar ta fita.”
“Kamar jira FARIS yake tana fita yashiga, har inda take yaje yazauna kusa da ita yace.”
“baby boo “
“Ignoring d’insa tayi tama juyamasa baya “
“Baby boo pls ko kina so na sauko a gwiwanane.”
“Jin zai sauko a gwiwa yasata yin magana da sauri tace no you don’t have to is okay.”
“Da gaske kike baby boo.”
“yeah da gaske nake.”
“Oh tnx god, yafad’a ya mike tare da hugging dinta yana sauke wani. Wahalallen ajiyan zuciya.”
“Sannu baby boo yace.”
“Uhmm nifa ba ruwana dakai tafada a shagwa6e.”
“Mai nayi kuma? “
“Ba kaibane ka – saikuma tayi shiru.’
“Kallonta yayi cikin ido ya gane mai take nufi dan haka yakai hannunsa cikinta yana shafawa slightly.”
“Stop it bana so.”
“Why? .”
“Kawai haka.’
“No i won’t ina shafawa ne naji ko akoi d’ayan baby na a cikinki shiyasa.”
“Dukan wasa takai masa a chest (kirji ) tace chap wazai sake haihuwa ai nagama haihuwa.”
“A ina kika gama ai after 1yrs ma xaki karomin triplet ko.”
“Kadai ji nafad’a ni nagama.”
“Fear fear baby boo kawai Yanxu sabida dan wannan abin zakice kingama Haihuwa? .”
“My words are done kadai ji, d’an fa kai baka jibane yadda naji shiyasa.”
“Oh sorry ILY.”
“ILY too but not going to deliver a baby again”
“Dariya ya k’washe dashi Yakaima kissing d’in days wuya, nose, cheek every where yana mata chak’walk’wali.”
“Dariya itama take ta kyal kyalawa, sai da ya tabba he make her happy tukun ya kyaleta.”
“D’ebo baby’s d’insu yayi ya kawosu, kallon yaran suke gasu farare k’yawawa dasu masha Allah komai nasu na FARIS ne macen ne kadai ke kama da MUSKAN kuma tanada gashi akanta tubarkallah.”
“FARIS yace baby boo kigani baby girl din na kama dake.”
“Same goes to you kaima mazan na kama dakai.”
“Murmushi yayi suka ci gaba da hira abinsu cikin so da kauna.”
“k’wanan su daya a asibiti aka sallamosu suka dawo gida.”
“Kulawa iya kulawa MUSKAN nasamu daga sirkanninta da mijinta.”
“Komai takeso shiya ake mata ba’a bari kowata k’wakwaran motsi tayi komai yimata ake har zuwa ranar suna.”
.
“Ranar suna yara maza sunci sunan kakaninsu maza mace kuma taci sunar kakarta tawajen uba.”
“Anakiran mazan ABID Da ABIDIN while macen kuma DANEEN.”
“Ansha shagalin suna wajen taro harnaga su Faty azland (mommah na ) Miss Mjay (sistoh na ) Miemiebee, Aneelurv, billylosh, Aisha iliasu, suhana, jannat, seemaluv, Rooky kaex, Rufaida, Dijawaziri Omg! You are just many cannot list y’all but you’re all there.”
“Aunty Sis manyan baki tazo da gayyanta kamarsu sdy jegals, aunty maijidda, hauwa m.jabo, benaxir, lubiee, ds.”
“Nagasu su Anker da cute xarah harma da hamagee, lilmeerahcute, Autar hajiya da RAZ har takeaway suke d’iba suna zubawa ajaka.”
“Wow! A gsky sunan yayi ba karya komai anyishi yadda ya kamata, baiyi over irin nawasu mahaukataba.”
“Angama suna lpy nan fa akaxo wajen da mum tace zata gida da MUSKAN amata wanka, tabb nan fa daru ya tashi dan tirjewa FARIS yayi yace sam baza a tafi da MUSKAN.”
“Saida mum ta daga masa tsawa tace wannan al’adace dole a tafi da ita.”
“Badan yasoba haka yana gani aka tafi da baby boo d’insa “
“Kussan kullum FARIS na gidan tare ake wankan arba’in dashi saidai sam mum bata barinsa shi daya da baby boo dan tsaro .”
.
“Kwana arba’in cipp akayi kan aka maida MUSKAN gidanta bayan tasha gyra wajen mum tafito sak amarya ga yara sai wayo suke yi.”
“Randa aka kaita saida FARIS ya fance duk kwanakin da yayi ba ita, tsaban dad’in da baby boo tayi har kukan dad’i saida yayi yata samata albarka ba adadi.”
.
_*AFTER FIVE (5) YEARS*_
“Su MUSKAN manyan mata angazama Big woman an kammala degree har ansoma aiki, ga kuma business da take na saro kaya daga Dubai zuwa nan gida 9ja.”
“Babban Plaza FARIS yabud’e musu da sunansu _*MUSFAR PLAZA*_ yana daya daga cikin plaza’s da’ake ji dashi a garin abuja, arziki ya bunkasa FARIS yasami karin girma a office yanxu yana da matsayi babba.”
“MUSKAN na kitchen tana girki abinta sauri sauri take ta kammala dan FARIS yakusa dawowa.”
“Ta gama komai ta jera a dining table, ta gyra ko’ina fes -fes sai sheki gidan yake ga wani ubansu kamshin turaren wuta dake tashi.”
“D’aki takama hanyasa tana kwalla wa DANEEN kira Emma taji shiru, tace were will that stupid girl be at this hour, ta bude d’akinta ta shige turus ta dakata daga inda take abinda ta gani shi ya mugun bata mamaki.”
“Daneen ce zaune gaban mirror tachaba ado kamar wata babba an daddabta counciler ga Foundation sai eye-shadow data bata fuskanta dashi.”
“Nufota MUSKAN tayi tace “what are you doing Daneen.”
“Ido ta zazzaro waje tace “babu “.
“You’re lying mai a fuskarki.”
“Mommy ba komaifa.”
“Zakiyi bayani ai,.”
“tana ganin MUSKAN na nufota da dib’a @360 ta bar d’akin, karo suka ci da FARIS yana shigowa shida Abid da Abidin, ga MUSKAN ta biyota.”
“Bayan FARIS tajeta buya tace plss daddy kafad’ama she shouldn’t beat me.”
“Zagayowa yayi da ita gabansa yace “Princess what have you done kuma now?.”
“Daddy kolliya nayi fa look ta nunamasa face d’inta.”
“Dariyarda yake shirin fitane ya kubce ya fito daga shi har brothers d’inta sukasa dariya.,”
“Rai Daneen ta had’a tace you’re laughing at me hun!.? “
“Dariyan FARIS ya tsaigaita kan yace “Princess wannan ai ba kolliyabane dodoniya kika zama look ya ciromata wayansa yana nunamata fuskarta a gaban wayar.”
“Nidai o’o kolliya nayi.”
“Rufemin baki mara kunya kawai zan zane kifa yau dinnan inji MUSKAN.”
“Daddy nifa kafada mata tadaina damuna da curutu.”
“kinji mummy kidaina damin Princess da surutu.”
Anki ayi din dama kai ke goyamata baya ai.”
“As you said madam but karkitab’a princess.”
“Kaji dashi ai kai da ita din Abidin abbana da abid kuzo mutafi abinmu mu barsu ku ai you’re a good boys.”
“Yeaaa mummy let go.”
“Tare suka tafi suka bar FARIS da Daneen.”
“Baki ta cuno gaba tace daddy ni mummy bata chona sai su abidin take cho.”
“Shhhh! Don’t say so tana sonki but sai kinfara jin magana zata nunamiki hun!.”
“Toh daddy zanfara jin magana ILY.”
“ILY too princess.”
“Muje yanxu na wanke miki fuska toh.”
“Ok daddy tafad’a bayan ta d’ale bayansa.”
“Dakinsa suka nufa yayi wanka yashirya cikin 3quater jeans da simple shirt, ya gyrawa Daneen fuska itama, suka kama hanyan falo.”
“Sun tarar dasu MUSKAN suna zaune suna kallo abinsu suna ta kyal-kyala dariya sai abin ya baiwa Daneen sha’awa da gudu tayi wajen MUSKAN, MUSKAN na ganinta tace tafi can wajen daddyn ki karkizo wajena, fuska ta marairaice tana Shirin kuka.”
“FARIS ne yace Princess say sorry to mommy.”
“Am sorry mummy I will never repeat it again.”
“Murmushi MUSKAN tayi tawaromata hannaye taxo.”
‘Da gudu tafada jikin MUSKAN, tace I love you my super amazing mum.”
“I love you too my princess.”
“kirinka jin magana kinji ko”
“yeah mum daga yau nazama good girl.”
“yawwa my baby boo tabata peck a forehead.”
“Tnx mummy.”
“Welcome my Princess.”
“FARIS dake tsaye tundazu yana kallonsu sai yanxu ya karasa wajensu yazauna.”
MUSKAN yajawota jikinsa a kunnenta yarad’amata am hungry babe.”
“itama a kunne tace muje kan dining nabaka abinci.”
“No bashi nake soba dayan zakiban.”
“ta ganesa sarai dan haka tadau tro pillow ta wurgamasa tace I won’t.”
“You must kota karfi sainayi shima yadau pillown ya wurgamata.
“Wasan wurge wurge suka soma yi dukkansu harda yaransu, can da suka gaji dukkansu FARIS yajawosu yayi hugging dinsu yace.”
“I LOVE YOU ALL GUYS.”
“WE LOVE YOU TOO DADDY.”
“Musfar Allah yabarmu tare inji MUSKAN.”
“Ameen baby boo ai kinriga da kinzama *JININ JIKINA*.”
“Kaima haka kazama *JININ JIKINA*”
Duk dariya sukasa abin sha’awa…….
.
ALHAMDULILAH Anan na kawo karshen littafina mai tattaken *JININ JIKINA*
Allah ‘n da yabani ikon farawa shi yabani ikon karasawa….