*Bissmillahirrah manirrahim* +
Fatan alkhairi ga kowa inafatan za ayimin hakuri abisa ga wasu kura kuran da kila zanyi
Gaisuwa da jinjina ga GOLDEN PEN WRITTERS
🅿AGE📕 1⃣
Gid’ane madai-daici dayike cike taf da jama’a idan kakalli kowa zaka fuskarsa dauke da farinciki da annashuwa banda wacce akayi taron da gayyar dominta
Datake makwabta tare da kawayenta anayimata lalle
Kallo daya zakamata kagano tashin hankali da tsananin fargaba atare da ita
Batawuce seconni batare data duba agogon wayarta ba faduwar gabanta na dada tsananta
Babbar aminiyarta ce tafahimci halin datake ciki ta matso gab da ita tafara magana ahankali
“Rauda please kikwantar da hankalinki banaso jama a sufahimci halin dakikeciki”
Kai kawai Rauda tagyada ma salma dantasan bazata fahimci tashin hankalin datakecikibane
Hakanma bakaramin dauriya takeyi ba
Tanaji kawayenta nayaba kyan lallen amma takasa tankamusu
Wata yar makarantarsuce tashigo tana sallama
Suka amsa salma nafadin”munyi fushi saiyanzu”
Tazauna kusa da rauda tana yar dariya”nabiya kasuwane salma yanzukuma danashigo layin dakyar na iya kutsowa
Jama a suncika layin tundaga farkonsa har karshensa”
Rauda tayi saurin tambayar jamila
“kinga umar?
Jamila ta girgiza kai”gaskiya ban lura ba kinsan mutanen dayawa”
Tajinjina kai tare da kara lalubar numbansa amma har lokacin akashe
Takara duba agogo karfe biyu saura hankalinta yakara tashi
Kallon me lallen tayi tace”dan allah kitakaita lallen haka”
“To”
Me lallen tace batafi minti biyar ba kuwa tace tagama
Mikewa tayi ganin mama tashigo suka shiga dakin matar gidan dasuke lallen
Mamar ma hankalinta atashe yike
Rauda da jikinta yagama yin sanyi ta dubi mama tanacewa
“mama wayar umar tundazu nike kira akashe kuma bana tunanin yazo gurin daurin aurannan gashi yanzu biyu dai dai”
Mama tasauke numfashi
Dan tama kasa cewa komai
Kasa rauda tayi dakanta hawaye na gangarowa
“mama idan aka fasa aurannan awannan karon bansan yaya zanyi da raina ba”
Mama takara sauke numfashi tare dacewa cikin kwantar da hankali
“insha allahu ba abunda zefaru”
Zaunawa kawai tayi amma ita ta riga da ta sadakar
Mama tafice zuciyarta cike da damuwa
Salma tashigo dakin tazauna kusa da ita tana karemata kallo
“haba Rauda meyasa bazaki kwantar da hankalinki bane bakisan wannan damuwar zata iya haifarmiki da wani ciwon na dabanba”
STORY CONTINUES BELOW
Wasu hawayenne suka kara gangarowa cikin shesshekar kuka tace
“Salma bansan yazanyi da rayuwata ba tundazu nike kiran wayar umar batashiga,gashi yanzu biyu harta gota amma banji alamun wani nasa yazoba bare maganar daurin aure ba
Salma inason umar bantaba son wani kamar yadda nike sonsa ba,idan narasasa bansan yazanyi da rayuwata ba……
Takarasa maganar cikin karyewar zuciya
Salma tasauke ajiyar zuciya hakika itama tagama karaya amma bataso ta nunama Raudan bataso hankalin raudan yakara tashi
Cikin karfafa gwiwa tajanyota jikinta tanadan bubbuga bayanta
“kawata kukannan ya isa haka dan allah insha allah ba abunda zefaru”
Kuka kawai takeyi me cin zuciya
Khadija ce tashigo dakin aguje fuskarta dauke da tsananin farinciki
Salma tace
“lafiya”
Cikin sauri khadija tace
“gasu umar can sunzo da tawagarsu”
Dasauri Rauda tamike
“dagaske khadija?
Khadija tadaga kai
“dagaske wallahi”
yaye labulen dakin tayi dasauri wanda ke fuskantar cikin layin tafara hange hangen inda zata hangosa
Daga can nesa tahangosa cikin abokanansa yasha wata purple din shadda abunka ga fari tas
Sai shaddar ta hausa kyawunsa yakara futowa
Kuramasa ido Rauda tayi da jikakkun idanunta
Tanajin wani sanyi da farinciki naratsa zuciyarta
Salma tadafa kafadunta tana dan murmushi
“kinga ni ba,bagashi yazo ba amma da duk kinbi kintada hankalinki nima kin tada nawa”
Kallon salma tayi tana yar dariya “karkiga laifina kawata kinsan yadda nike sonsa kuwa?
Dariya salma tayi itama sai lokacin hankalinnata yakwanta
“jibeki hawaye na zubowa kina kuma dariya, kuka da dariya alokaci daya”
Hannu tasa ta goge fuskarta dasauri tarasa
Ma mezatace saboda tsananin farinciki
“salma bazaki gane bane aure biyu anafasawa dole hankalina yatashi bare umar danike sonsa kamar raina”
Murmushi salma tayi tana girgiza kai
“allah dai yasa yadda kike son umar shima yana sonki haka”
Rauda ta jingina tana lumshe idanuwanta
“aganina salma ayanzu dai babu wanda yakai umar sona
Saboda kullum maganarsa batawuce idan babu ni baze iya rayuwa”
Dariya salma takuma yi
“lallaikam kunason junanku dayawa,amma dai kada wannan son yasa kibada kanki da ankaiki ehe
Kija aji kidan bashi wuya tukunna
Bude idanu rauda tayi tanayima salma wani irin kallo
“lallai salma bakida saiti,tunda nike aduniya bantaba yima umar musu ba
Ko bani da lafiya nakasa cin abinci idan yacemin inci sainaci kobadadi
Haka bacci ma kobanaji idan yace inyi dole nikeyi alokacin
Anguwa ma haka idan yace kar inje to ko inason zuwa fasawa nikeyi
Kekomai idan Umar yace inyi atake nikeyi bana bata lokaci
Bare kuma abunda ya dade yana muradi sai kawai in hanasa saboda wani ajin banza……
“Ya isa ya isa mamar soyayya”
Salma tafada tana mikewa
Sannan tacigaba dacewa
STORY CONTINUES BELOW
Yanzu nasan ko rijiya Umar yace kifada fadawa zakiyi wannan soyayyar taki tayi yawa wallahi
Dariya Rauda tayi
“najidai koma mezakice dan haka kigayawa wa’ancan
(sauran kawayen)
Dannaji suna zancen kwana babu wacce zata kwananmin agida”
Baki Rauda tarike
“eyyeh lallaima Rauda yazune bakinki yabude ko?
Amma dazu ko ihin kasa furtawa kikayi
To kwana ko zamuyi yazama dole”
Waro idanu Rauda tayi tanajin kamar mafarki takeyi
Yayinda taji ana sanarwa
“andaura auran umar da Rauda bisa ga sadaki naira dubu dari
Cinta,shanta,suturarta duk sunkoma kan umar
Jama a sunshaida
Fatiha
Runkunkume salma tayi tanfadin
“kinji abunda kunnuwa na sukaji salma”
Salma tadaga kai
“naji andaura auran Rauda da umar”
Durkushewa Rauda tayi,tayi sujada ga ubangiji
Tana fadin allah nagodemaka allah nagodemaka
Wayarta tafara kara tadago ahankali tana duban wayar
Salma tamikamata wayar tanufi hanyar fita tana cewa
“kinga bari naje muciga da shirye shirye tunda dai allah ya yadda”
Kallon wayar tayi ganin numban umar yasa tadauka
Cikin tattausar muryarsa mesata natsuwa aduk sanda tajita yace
“madam yadai”
Fashewa tayi da kuka wanda batasan ko namenene bane
“haba madam kukan kuma namene?
Yatambaya yana sassauta muryarsa
Cikin kukan tace
“yau tunda natashi nike kiranka amma wayarka akashe kasa hankalina yatashi…
Yakatseta”haba honey,kema kinsan hakanan dai bazan kashe wayata ba
Kinsan hidimar bikinnan jiya agajiye nakoma gida dasafe kuma mutanene suka addabeni da kira
Shiyasa nakashe”
Numfashi tasauke
“kasani cikin fargaba da tsoro bazan iya kwatantamaka tashin hankalin dashiga ba”
Murmushi yayi wanda tajiyo sautinsa
“kiyi hakuri bama jina kadai ba yanzu gabadayana nazama naki
Mallakinki ke kadai
Murmushi ya subucemata zuciyarta har harbawa takeyi saboda tsananin farinciki
“jaana”
(sunan datake kiransa kenan)
Takira sunan ahankali sannan tacigaba dacewa
“ina sonka bazan iya kwatanta kaunar danike maka ba…..
Ya katseta
“chuchu inasonki fiye da yadda kikesona,
Inasonki fiyeda yadda nikeson kaina
Zan iya yin komai akanki zan iya yin komai dan inga nakasance
Tare dake har abada
Kece farinciki
Lumshe idanuwanta tayi wasu hawayen farinciki masu dumi suka gangaromata
Anty larai ce tashigo dakin tana salallami
“wai dama amaryan tananan ko wanka batayi ba bare tashirya?
Ga jama a saikara cika sukeyi?
Murmushi Rauda tayi,tayi kasa da muryarta tare da kara matse wayar akunnenta
“jaana bari naje nayi wanka “
Yace to afito lafiya
Yarfillo
STORY CONTINUES BELOW
🌹JINNUL
AASHQUE🌹
NA
HARIRA ALIYU( *Yar Fillo*)
✍✍✍✍✍✍✍
*GOLDEL PEN WRITER’S ASSOCIATION*
✍✍✍✍✍✍✍
❄_We are bearers of sooo golden a pen We write assidiously percieven no pain Sooo magical Our creative golden pen Be hold our words A product of our pen Savour our words, for it will cause you no pain_❄
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
Dedicated to aisha a ibrahim
🅿AGE📕 2⃣
Cikin kankanin lokaci aka tsantsara mata kwalliya
Take kyawunta yakara fitowa
Farinciki agunta kuwa baya misaltuwa bakinta yakasa rufuwa
Haka mahaifiyarta ma itama farinciki gareta baya misaltuwa
Karfe hudu suka kammala shirin zuwa reception
Motocine manya masu tsadan gaske sukazo daukansu zuwa gurin reception din
ansha shagali sosai saikarfe bakwai akatashi Harsu salma sunshigo motar datake
Abokin umar yazo yace sukoma dayar motar
Wannan motar amarya da angone zasushiga
Basuyi musu ba suka koma dayar motar
Saida motocin suka gama tafiya sannan umar yashiga motar
Tanazaune tayi shuru tana tunani batasan yashiga motarba harsaida yashafamata wuya
Tadanyi firgigit tana kallonsa
Murmushi yayi yanafadin
“matsoraciya tunanin mekikeyi?
Girgiza kai tayi
“babu komai”
Ya gyada kai
“ook fadamin wani hotel kikeso muje mukwana”
Danzaro ido tayi tana kallonsa
“hotel kuma?
Yadaga gira
“yes hotel ko da aurena zan kwana nikadaine?
Ta rausayar da kai
“dan allah kabar wasa mutafi gida”
Ya gyara zamansa yana fuskantarta
“allah dagaske nikeyi da aurena bazan kwana nikadai ba idan bazaki zabi
Hotel din dakikeso ba nizanzaba”
Ganin dagaske yikeyi yasa ta marairaice fuska
“haba jaana kaima kasan abunda bazeyuwu bane…..
“mene bazeyuwuba?
Yakatseta ya na hade fuska
Tasauke numfashi
“tayaya bamu tare ba zamutafi hotel?
“keba matata bace?
Yawurgo mata tambayar
“matarka ce mana amma……
Yadaga mata hannu
“kinga dakata!
Banason wasu surutai marasa tushe ke matata ce ina da ikon dazanyi duk yadda naga dama dake
Zata kuma magana yakuma katseta
“nace taredake zan kwana idan kuma tunyanzu zakifara min gardamane sai inji”
Shuru tayi tana kallonsa tarasa tayadda zatamai magana yafahimta
Ganin zetada motar yasa tarike mai hannu tana langabar dakai
“jaana please kayi hakuri kasani bazantaba iya yima musu ba amma hakan badai dai bane
Duk da nasan ba haramun bane dan na kwana tare da kai
Amma surutun mutane nike gudu
Kaga za a daukeni marar kunya
STORY CONTINUES BELOW
Kayi hakuri gobe iyanzu inadakinka duk abinda kaga dama saikayi amma kayimin hakurin yau please”
Bekara cemata komai ba yatada motar ya nufi hanyar gida da ita
Kallonsa kawai takeyi tasan ransa yabaci itama saitaji zuciyarta babu dadi
kwata-kwata batason ganin bacin ransa
“jaana…..
Zatai magana yayi saurin dakatar da ita tahanyar daga mata hannu batare da ya ko dubeta ba
“inace gida kikace inkaiki?
Tadaga kai
Yacigaba da cewa”to yanzu hanyar gidan nikeyi ai dan haka banason surutu please”
Jikinta yayi sanyi takuma kai hannunta tarike nasa
“muje hotel din inhar zuwan zesaka farinciki”
Fakawa yayi agefen titi yazuba mata manyan idanuwansa masu juya mata lissafi
“bazantaba yimiki abunda bakyaso ba chuchu,danhaka kibari kawai ba fushi nayi ba kawai dai banji dadi bane”
“amma….
Shhhhhhh yadora yatsunsa biyu akan dan karamin bakinta
“nacemiki banyi fushi bakarki damu,dayau da goben ai duk na allah ne
Kuma goben kaman yaune”
Yakarasa maganar yana sakin fuskarsa
Sai lokacin taji hankalinta yakwanta bata kaunar bacin ransa kwata
“nagode mijina dakafahimceni”
Yasakarmata murmushi tare da shafa gefen fuskarta
“bar wani jindadi gobe zaki gane kurenki ne yarinya”
dariya tayi tana kauda kanta
Washegari karfe goma nasafe sukabar kaduna zuwa garin abuja
Iyayenta sunyimata fada da nasiha sosai
Taci kuka kamar ranta zefita dan tanada kawa zuci sosai ko tafiyar kwana biyu tayi allah allah takeyi takoma inko tayi sati to dama wajibine saitayi rashin lafiya
To bare wannan da tafiyar dun-dun-dunce saidai takaima gidansu ziyara
Saiwajen karfe shabiyu suka isa birnin tarayya
Cikin wata hadaddiyar unguwa suka shiga wani kayatacce fankacecen gida me kama da gidan sanator
ko nawani gomna gidan yatsaru sosai gaba d’aya wadanda suka rakota sakin baki sukayi suna kallon gidan
Wasu daga cikinsu suna fadin
“gaskiya Rauda ta dace”
Yan uwan Umar ne suka futo da ga ciki yayarsa me suna kaltum itace tazo tarungumota
Tana rangada buda
Nandanan sauran suka fara yan wake-wakensu na buzaye
Ahaka suka shiga kayataccen falon dayasha kayan alatu
Atsakiyar falon anty kaltum tazaunar da ita inda sauran suka zagayeta
Anty kaltum tayaye lullubin da ke kan rauda fuskarsa ta bayanna
“masha allah”
Sauran yan uwansa suka fara fada suna yaba kyanta
Kasa tayi dakanta dangani takeyi kaman zaginta sukeyi yadda sukeda tsananin kyau har zasu dubeta su kirata kyakkyawa
Ba abata lokaci ba aka cika gabansu da abinci kala kala
Saiwajen karfe biyar yan kaduna suka fara shirin komawa
STORY CONTINUES BELOW
Fada suka kara yimata sosai sannan suka juyo
Suma yan uwan umar din fashewa sukayi yan kaduna suka juyo yan niger suka nufi masaukinsu
Anty kaltum ce kawai tarage itama kuma tanajiran zuwan angwaye ne takama gabanta
Wanka tasa Rauda takumayi taciromata wani leshi rantsatsse tasa
Sannan tazauna tatsaramata kwalliya kasancewar ta kware afannin kwalliya
Saida akayi sallar issha sannan umar yashigo tare da babban abokinsa zayyad
Nan itama takarayimusu tata nasihar sannan tamusu sallama shima zayyad yayimusu nasa
Sannan yayimusu saida safe
Umar yarakasa yarufe kofofin
Tanazaune saman gado inda yabarta yashigo yana zuba kamshi
Yazauna kusa da ita yasa hannu ya tallabo fuskarta
Suka hada ido
Jitayi gabanta yafadi wanda batasan dalilin faduwar tasa ba
Yasakar mata murmushi
“yadai amarya kinwani yi shuru ko duk jimamin rabuwa da mamane?
Takakaro murmushi
“kaman kasani jinikeyi kaman intashi inkoma”
Yayi yar dariya har fararen hakoransa suka bayyana
“lallai yarinya bakiji dakyau ba keda zuwa kaduna saikin shekara kila ma da jariri zakijemusu”
Dariyar itama tayi
“ai inayin sati biyu zanje”
Ya jinjina kai
“lallai kam”
Tashi kidaukomana plate muci abinci dannasan yau bakici komai
Tamike tabude kofar dakin tafara saukowa daga step tana karema falon kallo
Azuciyarta tana yaba kyansa dakuma kokarin mijinnata
Ta murda kofar kicin din
Komai ashirye yike tsaf-tsaf
Tayi guntun murmushin jindadi
Lallai umar yanasonta dayawa dan ko tsinke kinyarda ayimata yayi shi yayi komai
Tazaro plate daya acikin kitchenwire
Tajuyo zata fita
“kwaram”
Taji karar wani plate din yafado
Tajuya tana cewa garin saurina banciro ahankali ba
Tagyara su tsaf sannan takuma juya
Hartakai bakin kofa takuma jin karar faduwar plates din
Dasauri tajuyo plates biyu tagani akasa
Gabanta yafadi take taji tsoro yafara kamata
Bata koma dauke plates dinba gaba kawai tayi tarufo kofar kicin din
Tafara tafiya dasauri tahau step.
Tahau daya biyu uku tatsaya cak.
Wani fargaba da tsoro yakuma kamata
Jitayi kaman ana bin sawunta
Tayi karfin halin juyawa amma bata ga kowa ba
Dasauri tacigaba da hawa harda tuntube gurin shiga dakin
Kallonta yayi yana fadin
“lafiya madam?
Zama tayi tana dan sauke numfashi
“jinayi kaman wani yanabina”
Dariya yayi
“oh my dear tsoronki yayi yawa wallahi waye zebiyoki?bayan kinsan gidannan dagani saike?
Hmmmmmmmm
Tasauke ajiyar zuciya
“nidai yanzu bazankara fita nikadai ba saidai muje tare”
STORY CONTINUES BELOW
Yagirgiza kai yana murmushi
“to madam ai duk yadda kikace haka za ayi”
Ya amshi plates din yajuye gasassun kaji biyu aciki
Sannan yafara bata abaki
Saida yaga takoshi dam sannan ya kyaleta
Yakwashe kayan yamaidasu gefe sannan yadauro alwala itama yace tadauro
Sallah raka a biyu sukayi yayimata tambayoyi game da addininta ta amsa mai
Sannan yadafa kanta ya dinga kwarara addu o i
Sunmike kenan yana ninke darduma wayarsa tafara kara
Ganin numban asibi ne yasa ya dauka
Magana uku yayi yace “ook kubashi taimakon gaggawa ganinan zuwa”
Ya ajiye wayar yana dubanta
“baby kirane daga asibiti wai ankawo wani emergency”
Kallonsa tayi sosai
“toyanzu mekake nufi?
“zuwa zanyimana chuchu ceton raine fa?
Waro idanuwanta tayi tana kallon agogo sannan tamaida idanuwanta kansa
“yanzufa karfe shabiyu”
Yadaga kai
“nasani ai amma ai komin dare dole infita tunda aikinane
“
Nan danan idanuwanta suka cicciko da kwalla
Matsowa yayi gab da ita yajanyota jikinsa
“please honey kiyi hakuri naje ance mutumin yana cikin wani hali please….
Dago kanta tayi daga jikinsa
Tazuba masa fararen idanuwanta
“amma kasan bazan iya kwana nikadai acikin gidan nan ba ko?saidai inmutafi tare”
Ya waro ido
“dawa?baze yuwu ba ba bu inda zakije acikin darannan
Nima dan yazamarmin dole ne
Danhaka kikwanta kiyi baccinki inagamawa zandawo
Zata kuma magana ya katseta
“chuchu bata lokacinnan danikeyi bawan allahn can ze iya rasa ransa da haka natafi
Yakarasa fada yana ficewa da sauri
Bin bayansa tayi da kallo cike da tsananin damuwa dan ita ko agida batasaba kwana itakadai
Bare awannan katoton gidan
Zama tayi turus gefen gado yayinda taji tashin motarsa
Tayi shuru tana tunanin yadda zatayi
Ga iskar hadari tanata kadawa
Mikewa tayi ta janyo windon dakin dayike abude iska nata kadashi
Rufe windon yayi dede da dauke wutar gidan
Kirjinta yabuga dam take matsanancin tsoro yakamata
Tayi karfin halin dawowa bakin gadon tasa hannu tana laluben wayarta
Jitayi antaba mata kafa dasauri tahaye gadon tana karanto duk addu o in da suka zo bakinta
Yarfillo.
🌹JINNUL
AASHIQUE🌹
NA
HARIRA ALIYU(yarfillo)
✍✍✍✍✍✍✍
*GOLDEL PEN WRITER’S ASSOCIATION*
✍✍✍✍✍✍✍
❄_We are bearers of sooo golden a pen We write assidiously percieven no pain Sooo magical Our creative golden pen Be hold our words A product of our pen Savour our words, for it will cause you no pain_❄
STORY CONTINUES BELOW
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
Dedicated to Aisha Ibrahim
🅿AGE📕 3⃣
Dakyar ta iya lalubo wayar gabadaya firgici da tsoro sungama kamata
Hannunta na rawa takunna fitilar wayar,tahaska tsakar dakin inda takejin kaman akwai wani atsaye
Saidai bataga kowaba,ajiyar zuciya tasauke me nawi
Tajingina da jikin gadon tana maida numfashi.
Amma idanuwanta sunkasa tsayawa wuri daya kalle-kallen dakin kawai takeyi
Azuciyarta kuma tana karanto addu’o in neman tsari.
Dai-dai lokacin akafara ruwan sama wanda yataho da karfi kaman da bakin kwarya
Hankalinta yakara tashi dantasan yadda ruwan yataho da karfi,to lallai sai anyi tsawa,itakuma allah ya jarabceta da jin tsoron tsawa
Takurewa tayi guri daya ko motsin kirki takasa yi
Ahankali taji karar bude kofar falon sannan taji anrufe
Daga bisani tajiyo karar tafiya kamar ana haurowa saman
Babu inda baya rawa ajikinta saboda tsabar tsorata,gabadaya ta daburce
Addu’o inma sunbace mata
Inbanda ayatul kursiyyu ba abunda bakinta ke iya furtawa,itama din bata kaiwa karshenta take dawowa farko.
Jin karar sawun tafiyan daf da kofar dakin datakeciki,yasa ta cusa kanta cikin gwiwo winta
Danbataso taga abunda ze shigo din tasan ba alheri bane
Murda kofar dakin akayi
Da karfi tafara karanta ayatul kursiyyu,amma har lokacin takasa dago kanta bare taga me shigowar,
Jitayi andafata,takwala ihu tana fadin
“inna lillahi wa inna ilaihi raji’un !
Muryar umar taji yana fadin
“lafiya madam meke faruwane haka?
Tabude idanuwanta da sauri,ganin shine yasa ta rungume sa dasauri gami da fashewa da kuka.
Zaunawa yayi tana rungume ajinkinsa
“meyake faruwane?fadamin mana”
Cikin kuka tafara magana tana girgiza kai
“bazan iya zama agidannan ba wallahi tsoro nikeji,bazan iyaba”
Yasauke numfashi yana dan bubbuga mata baya ahankali
Cikin sigar rarrashi yace
“ok..ok kiyi shuru hakanan banason kukannan please”
Saida tadan dauki lokaci sannan tadena kukan takomai sauke numfashi ahankali
Ya dagota daga jikinsa yazuba mata kyawawan idanuwansa
“chuchu,meyasa kikeda tsoro dayawane? Bakisan yawan tsoro babu kyau ba?
Ta ajiye numfashi tace
“to ba laifinka bane katafi kabarni a wannan daren,badole inji tsoro ba”
Shima numfashin yasauke
“toyanzu da bandawo ba fa?dole fa kikoyi rage tsoronnan saboda kinsan aikina,
Ana iya kirana ako wani lokaci”
Ta jinjina mai kawai sannan tace
“waima ya akayi kadawo?bakace zakaje kaduba mara lafiya bane,kuma ya akayi banji tsayuwar motarka ba?
Yayi dan murmushi
“wallahi inazuwa natadda doctor zubairu a asibitin,yanata yima nurse din data kirana fada
Wai akanme tasan yaune natare zata kirani,shine yacemin injuyo shi zeduba marar lafiyan
Karar mota kuma ya zayi kiji?bayan kin sama zuciyarki tsoro,sannan kuma kinmanta ruwa akeyi?
Tagyada kai
“hakane amma please jaana karka kara barina nikadai wallahi inajin tsoro sai intajin wasu abubuwan tsoro dayawa”
yayi murmushi dayakara bayyana kyan fuskarsa
“dama koda yaushe ni inatare dake,danhaka kirage tsoro kinji”
STORY CONTINUES BELOW
Ta gyada kai tana nata murmushin
“tom insha allahu zan rage”
Yakwanta gamida kwanto da ita jikinsa
“chuchu ina alkawarina na jiya?
Tadanzame
“tomiye nasauri jaana,nifa takace”
Dariya yayi ya kashe fitilar wayartata
Misalin karfe uku da rabi,suna rungume da juna yana shafa sumar kanta
“chuchu allah yayimiki albarka hakika ke tadabance kinsanyani farinciki mara misaltuwa”
Murmushi tayi tanajin wani sanyi acikin zuciyarta
“jaana inasonka,kayimin alkawarin bazaka taba rabuwa dani ba”
hannu yasa yadago fuskarta suna kallon juna
Tasauke ajiyar zuciya
“hmmmmmm hakika nayi dace da miji kyakkyawa wanda samun irinsa aduniya ze yi matukar wahala,amma ina fargaban kada watarana wata takwacemin kai”
ya girgiza kai
“bakisan irin son danakemiki ba chuchu,zan iyayin komai akanki kuma babu wacce ta isa takwace soyayyata agareki
Maganar yimiki alkawari kuwa,nayi ada kuma ayanzu ma zankuma yimiki
bazan taba rabuwa dake ba…..”
Ta lumshe idanuwanta ahankali farinciki yakuma lullubeta
Gani takeyi kamar ayanzu bata da wata sauran matsala arayuwarta
Kara shigewa jikinsa tayi bacci medadi yadauketa.
Washegari sai wajen karfe bakwai tafarka
ganin haske yagauraye dakin yasa ta kalli agogo
Karfe bakwai harda mintoci.
Takalli gefenta inda yakwanta, baya wurin
Mikewa tayi tashiga toilet tayi wanka tadauro alwala
Ta gabatar da sallar asuba,bayan ta idar ta ninke dardumar tanufi wardrop tanajin jikinta nayimata tsami dan gabadaya ciwo yikeyi.
Riga doguwa tadauko tasa,sannan tasauko daga saman dantasan yana kasan
Saidai bataganshi a falon ba,taduba kicin nanma baya ciki
“ina yaje”
Tayi wa kanta tambayar
Zuciyarta ce tabata amsa
“kila yaje siyomuku abun kari ne”
Tagyada kai dantasan baze wuce hakan ba
Falon tadawo tazauna adaya daga cikin kujerun
Tadanna kiran numban mama
Ringing biyu tadauka suka fara gaisawa.
Kwan-kwasa kofar akafara yi
Tamike da wayar akunnenta tabude
Umar ne tsaye rike da rigarsa ta likitoci
Suka sakarma juna murmushi
Katse wayar tayi tanacewa
“ina kwana”
Ya janyo hannunta tafada kan faffadan kirjinsa
“wayace miki haka ake tarban miji?kintsaya daga nesa kina wani cewa ina kwana”
Tayi kasa dakanta cike da jin kunyarsa
Suka karasa cikin falon yana rike da ita
A three seater suka zauna,ya ajiye rigar ahannun kujera yanacewa
“wallahi nagaji kokadan jiya ban runtsa ba,amma nasan ke barcinki kikai harda munshari”
Megadi ne yayi sallama
Ya miko ya miko wani kwando cike da kayan karin kumallo yace anty kaltum ce ta aiko dashi
Umar yamike
“kinga jera abincinnan akan dining bari in watso ruwa”
STORY CONTINUES BELOW
Tadauki kwandon ta kai kan dining din ta jejjera komai,tazauna tana jiransa.
Befi minti goma da shiga ba yafito sanye da three-quater da T-shirt
Yazauna a kujerar dake fuskantarta suka fara karyawa yana janta da fira
“shine ko kitambayeni ya me jiki ko?
Yafada yana kai kofin tea bakinsa
“yihakuri yanzu nike shirin intambayeka”
Ya gyada kai
“ook ai bawan allahnnan ya jigata dayawa motarsa karkashin traler fa tashige da kyar muka iya ceto ransa danni banyi zaton ma zeyi rai ba”
Tadakata daga kurban tea din datakeyi tana kallonsa dan bata fahimci abunda yike nufi ba
Shima kalonnata yayi ganin takafashe da ido yasa yace
“yadai?naga kinayimin wani irin kallo,kamar bakigane abunda nike cewa ba”
Ta jinjina kai
“to gani nayi ba kai kayi aikinnan ba,doctor zubairu ne yayi amma kana cewa da kyar kuka ceto rayuwarsa
Kallon rashin fahimtar shima yafara yimata
“bangane ba,wani doctor zubairu kuma?
“doctor zubairu na asibitin ku mana”
Tabashi amsa atakaice
Yagyara zamansa yana maida hankalinsa akanta
“wai wani doctor zubairun kike magana akansa?
Doctor zubairun da watansa biyu kenan a kasar china”
Takauda idanuwanta akansa,tamaida kan wayar ta, tana duba sakon da aka turo mata
“to nidai bansani ba,kaida bakinka jiya kace doctor zubairu yace kadawo gida bekamata kafita aiki a daren jiya ba”
Har lokacin idanuwansa nakanta
“ayaushe nace miki hakan?
“a jiya da kadawo mana”
Tabashi amsa cikin kosawa da zancen dan dan tafahimci so yike yamaida abun wasa
“nifa bandawo gidannan jiya ba”
Yafada
Tadago kanta daga kan wayar suka hada idanu
“mekace?
Ta tambaya dan tabbatar da jin abunda yace
“nace bandawo jiya bani,tunda mukai natafi asibiti bandawo gidannan ba sai a safiyarnan”
Ganin fuskarsa ba bu alamar wasa yasa tace
“wai meyasa kaketa wasu maganganu da bangane bane,jiya bakadawo ba,misalin shabiyu da rabi?
Ta girgiza kai
“saidai in mafarki kikayi danni lokacin ma ina emergency room”
Ta gyada kai
“dan allah kabar wasannan haka”
Hannunta yakama
“kedai zancema wa kibar wasan haka,nida na kwana asibiti zaki wani ce wai nadawo gida………..
Takatse shi
“jaana please wasan ya isa haka”
Ya jingina bayansa da kujerar dining yana kallonta
“chuchu i’m serious saidai in mafarki kikayi amma ni wallahi bandawo gidannan ba”
Jin yayi rantsuwa yasa gabanta yafara faduwa
“jaana harda rantsuwa?
Ya jinjina kai
“to nafadamiki mafarki kikayi baki yarda ba…….
“to dawaye na kwana jiya?
Takatsesa da sauri
“kwana kuma?banganeba”
Ta jinjina kai yanayinta yafara komawa na firgici
“jaana wallahi jiya kadawo kacemin doctor zubairu ya amsheka,kuma tare dakai muka kwana.”
Wani kallo yayimata gami da cewa
“kidawo hankalinki please,ban kwana agidannan ba…………..
STORY CONTINUES BELOW
Yarfillo.
🌹JINNUL
AASHIQUE🌹
NA
HARIRA ALIYU(yarfillo)
✍✍✍✍✍✍✍
*GOLDEL PEN WRITER’S ASSOCIATION*
✍✍✍✍✍✍✍
❄_We are bearers of sooo golden a pen We write assidiously percieven no pain Sooo magical Our creative golden pen Be hold our words A product of our pen Savour our words, for it will cause you no pain_❄
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
Dedicated to Aisha Ibrahim
Wannan page din nakine anty nabila ina godiya da kokarinki gareni allah yabar zumunci
🅿AGE📕 4⃣
Dire kofin tayi,ranta yadan soma baci,akanmene yikeso yayi mata wasa da hankali?
“wai meke damunka ne? Indawo hankalina kamar yaya?tayaya munkwana dakai zaka cemin kai ba a gidannan kakwana ba……..
Buga teburin yayi dan shima nashi ran yasoma bacin
“nace miki a asibiti nakwana!
Jikinta yasoma bari,zuciyarta tafara rawa
Zagayawa tayi inda yike ta durkusa tadafa gwiwowinsa
“jaana kasan bama irin wasannan ko?dan allah kafadamin dagaske ne baka kwana agidana?
Wani irin kallo yikemata nawacce tafara tabuwa
“chuchu wallahi a asibiti nakwana……
matsawa tayi arazane idanuwanta suka cicciko
Cikin rawar murya tace
“inna lillahi wa inna ilaihi ra’ji un…….
Kallonta kawai yikeyi
Maganar malan ce tadawo mata
“kirike wannan lemun tsamin kitabbatar dakin shiga dashi cikin gidanki
Aranar da kika kwana daya kibude kullin da lemun tsamin ke ciki
Idan kiga yananan akalarsa to tabbas munyi nasara a wannan aikin da mukayi na karshe
Idan kuma kiga yacanza kala zuwa ja,to tabbas akwai matsala
Wannan lemun tsamin yana dauke da magunguna masu karfin gaske kitabbata kinshiga dashi”
Mikewa tayi dasauri tafara hawa step dagudu
Tanajin umar yana kiranta bata tsaya ba,harsaida tashiga bedroom dinta
Handbag din ta tadauko ta zazzage kayan dake ciki
Hannunta na rawa tadauki kullin lemun tsamin tafara kwancewa
Gabanta nafaduwa
Saidai me,tana gama kwance kullin taga lemun tsamin yayi jawur
Ihu takwala ta wurgar dashi
Dai-dai lokacin umar yashigo dakin
“chuchu me kikeyi ne wai…….
Kankamesa tayi dasauri jikinta narawa
“Aasim!Aasim!”
Yadagota dasauri
“Aasim kuma?
Cikin kuka tafara cewa
“nashiga uku jaana Aasim yanatare dani haryanzu,wallahi jiya ba mafarki nayi ba shi yazomin a suffarka………
Kamata yayi suka zauna akan gadon yakura mata ido yana karantar yanayinta
“Aasim chuchu?ba malan yace anriga da ankullesa a kwalba ba?
STORY CONTINUES BELOW
Ta jinjina kai dasauri
“haka yace amma lemun tsamin dayabani yacanza kala kuma…..kuma jiya inatajin anatsoratani sannan yazomin asuffarka”
Rungumeta yayi yana shafa bayanta
“okay,okay,kwantar da hankalinki please bari inkira wayar malan din”
Yazaro wayarsa daga aljihu yadanna numban malan saidai kira biyu yana masa bedauka ba
Yakuma danna kiran a karo na uku,saida takusan tsinkewa sannan aka daga
Yayi sallama yana fadin
“ina kwana malan,antashi lafiya?
Daga can bangaren wani ne ya amsa
“ba malan bane,malan allah yayi masa rasuwa jiya da daddare yanzu haka muna shirin kaisa makwancinsa”
“inna lillahi wa inna ilaihi ra’ji un,ya rasu?hatsari yayi kome?
daga can bangaren ya amsa
“wallahi lafiyarsa lau ya kwanta saidai dubawa akayi akaga yarasu”
Ajiye wayar yayi yana share gumin da ke keto masa a goshi
Itako kuka tafashe dashi tana fadin
“wayyoh allah na,nashiga uku!!
Be hanata kukantaba,zura mata ido kawai yayi zuciyarsa cike da damuwa
Da tarin fargaba,me yike shirin faruwa da sune?
Jiyayi kansa yayi wani dum
“la ila ha’illa anta subhanaka inni kuntu minaz zalimin”
Bakinsa ya furta ahankali
Sannan
Ya kira sunanta a sanyaye
“Rauda…..
Sanin kankine kukannan ba bu maganin da zemana face yajanyo miki ciwon kai,
Kiyi shuru kidaina kukan haka,munemi mafita……
Dagaowa tayi tana kallonsa da jikakkun idanunta
“mafita?a ina zamu samo mafitar jaana?gurin malan isah ne kadai muka sa ran zamu sami mafita,
Amma gashi,sanadiyyar taimakona har ya rasa ransa nasan…….
Ya girgiza kai
“malan kwanan sa ne yakare,kuma na tabbata zamu samu waraka awani gurin.
Abinda nikeso dake,ki kwantar da hankalinki kinji?
Ta jinjina mai kai kawai amma ita kadai tasan tashin hankalin datake ciki.
Shima din dauriya yayi kawai amma zuciyar sa cike taf da da damuwa.
Yarasa wani irin al’amarine wannan me cike da rudani
Ya kalli fuskarta,tayi kuka harta gaji bacci yadauketa.
Kwantar da ita yayi
Ya mike,yana zagagaye acikin dakin yana tunanin ta inda ze bullo ma al’amarin
Itako Rauda mafarki takeyi cikin barcinta,malan isa tagani zaune yana lazumi
Saiga hayaki yafara shigowa dakin dayike,kan kace kwabo jijiyoyin wuyansa sun mummurde,idanuwansa sun kakkafe
Zuwa can taga yazame kasa,alamun numfashin sa yadauke
Dariya taji anfara yi me tsoratarwa daga bisani taga wani farin saurayi yabayanna
Dariyar ya cigaba dayi,lokaci daya kuma ya murtuke fuska kamar bashi yagama yin dariyar ba.
Yakalli malan isa yana nuna sa da da yatsa
“kallesa,wai shi ze ja dani,ni Aasim”
Ya girgiza kai yana cigaba dacewa
“bazaka iya ba! Bazaka iya ba!
Na gargadeka tun farko amma kayi taurin kai kana ganin kaman zaka iya ja dani……”
STORY CONTINUES BELOW
Yadan durkusa sai saitin malan isan
“tashi mana! Tashi kaciga ba da aikin da kakeyi………bazaka iya ba,bazaka iya ba ko?
Ya mike tsaye yana cigaba da yin dariyar sannan ya dubeta da razanannun idanunsa
“kinsa nayi abunda ban taba yi ba,tunda nike aduniya bantaba kisa ba
Amma gashi sanadinki kinsa nafara,kinsa naka sheshi…….
Yakara sa fada idanuwansa na kuma runewa
“Kiyi babban kuskure a rayuwanki,da kika karya sharuddan dana gindaya akanki
Mafi girman kuskuren da kikayi kuwa,shine dakika bari na kusanceki azahiri…”
“kisani daga yanzu kinrabu da farin ciki,kwanciyar hankali sannan abunda zance miki na karshe shine
Idan har kinason rayuwar mijinki to tabbas kada ki kuskura ya kusanceki dan duk ranar daya yi hakan to tabbas ze mutu kamar yadda wannan ya mutu!!!!!
Yakara sa fada yana nuna malan isa sannan yakuma fashewa da dariya
A razane tafarka jikinta nabari
Umar dake ta patrol acikin dakin yadawo bakin gadon dasauri
Rirrikesa tayi tana waige-waige
“shine yakashe shi,wayyoh allah na!!!
Bayi da bukatar tambayarta dan yasan mafarki tayi
Rungumeta yayi kawai,azuciyarsa yana jin tausayinta
“dan allah kada kabarni koda na minti dayane,cutar dani zeyi”
Tafada jikinta na kakkarwa
Ya jinjina kai
“zan kasance tare dake,akodayaushe,babu abunda zesameki da izinin allah”
Yarfillo.
🌹JINNUL
AASHIQUE🌹
NA
HARIRA ALIYU(yarfillo)
✍✍✍✍✍✍✍
*GOLDEL PEN WRITER’S ASSOCIATION*
✍✍✍✍✍✍✍
❄_We are bearers of sooo golden a pen We write assidiously percieven no pain Sooo magical Our creative golden pen Be hold our words A product of our pen Savour our words, for it will cause you no pain_❄
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
Dedicated to little Hajjo
*_A kullum forum dinmu Kara bunk’asa yakeyi,mutanen cikinsa Kara basira da fasaha sukeyi,ina jinjina ma golden writters Allah yabar zumunci a tsakaninmu_*
_GAISUWA Ga *MATAN K’WARAI* group *yar fillo* na godiya da addu’o inku gareta,ina Kuma Jin dadin yadda kuke yaba labarina,ina godiya sosai_
🅿AGE📕 5⃣
Hannunsa takama,Tana kallonsa da jik’akk’un idanuwanta da suka yi luhu-luhu
“Jaana,kayi min alkawarin duk rintsi bazaka taba rabuwa Dani ba,nasan matsala yanzu muka fara ganinta……
Ya sauke numfashi Yana kallon cikin idanuwanta
“Chuchu kina tunanin akwai abunda ze bani tsoro har yasa nai tunanin rabuwa dake?”
Ya girgiza Kai sannan yaciga ba da cewa
“Son Dana ke yimiki,ba k’aramin so bane,kuma bana tunanin akwai abunda ze razanani akanki,nasan yayi hakane Dan yasanya shakku da fitina atsakaninmu Amma ni ina k’aunarki Kuma ko me zeyi sai dai yayi Amma tarayya dake yanzu nafara Kuma ashirye Nike da indauki duk wani abun da zezo dashi”
Ta maida kanta kan k’irjinsa,tanajin zuciyarta babu dadi
“Nasan zaka iya jure komai,Amma ina Jin tsoro,nafi kowa sanin waye Aasim,abunda ze iya?da abunda baze iya ba.
STORY CONTINUES BELOW
Nasan ze iyayin komai domin yaga yarabani da kowa,baze cutar Dani ba,ina da tabbacin hakan Amma……..
Tadan dakata Tana share hawayen dake ambaliya a fuskarta,sannan tacigaba
“Kai ze iya cutar da Kai,banason wani Abu yasameka abunda Nike tsoro kenan”
Murmushi yayi me dauke da damuwa
“Kinmanta da cewa Allah Yana tare damu?idan har muka rike addu’a,to tabbas muna tare da kariyar Allah a kodayaushe.
Dan Haka kikwantar da hankalinki,zankira zayyad akwai wani malami dayace yasani a k’auyensu,sai muji yadda za’ayi”
“A’a,banaso wani yak’ara rasa ransa a sanadina”
Tafara cikin karyewar zuciya
“Hmmmmmmmmm!!
Yakuma sauke numfashi
“To Rauda zamu zauna hakane?dole mukuma neman mafita,tun abun beyi k’arfi ba”
Shuru tayimai kawai,Amma ita ta Riga da ta Gama karaya
Wunin ranar be leka ko kofar gida ba,Dan yasan a tsorace take,hatta salloli agida yayi.
Abincin Rana Dana dare duk anty kaltum ce ta aikomusu,Dan Basu da nisa sosai
Bawani cin abincin sukayi dayawa ba,Dan hankalinsu ba a kwance yike ba.
Suna zaune a kan kujera,da daddare,bayan sun kammala cin abinci,yamike Yana maida sauran kula
“bari in d’an watsa ruwa,yanzu zandawo”
Ta gyad’a mai,batare da tace komai ba.
Sama ya haura yashiga bedroom dinsa,yarage saura ita kadai a falon
Tunanin Daren jiya kawai takeyi da abunda ya wakana atsakaninta da Wanda ba jinsinta ba,
Zuciyarta ce take ta haskomata lokacin, gani takeyi Kamar mafarki takeyi.
Karar da TV d’in falon yikeyi ne yafara damunta,ganin hankalinta bama akan TV d’in yike ba,yasa tadauki remote d’in dake dake gefen kujerar takashe
Ko second biyu batayi da kashewa ba ya kunnu
Ta Kuma d’aukar remote d’in takuma kashewa,still ya sake kunnuwa.
Gajeren tsaki taja tamik’e ta zare socket din,tajuyo zata dawo kan kujerar
Karar TV d’inne yasa ta tsaya cak,tare da juyawa ahankali
Still TVn yasake kunnuwa
Takalli socket d’in da ta zare Yana nan akasa Amma Kuma TV Yana aiki
Tsoro yafara kamata,zuciyarta tafara rawa
Ta kalli cikin TVn,wasu mutane tagani a zazzaune sanye da bak’ak’en Kaya sunyi kasa da kansu suna karatu da wani yare
Zuwa can suka d’ago suka kalleta da manyan idanuwansu da yike bak’kk’irin babu wani alamar fari acikinsa.
Tayi baya dasauri jikinta yafara rawa
Hannayensu suka d’ago sunayimata alamar Kira
“Ta’al huna Rauda!
Ta’al huna Rauda!”
Zuciyarta tafara bugawa da k’arfi kaman zata fito waje saboda tsananin razana
Matsowa sukeyi suna Kuma fadin
“Ta’al huna!
A razane tajuya da gudu,Tafara hayewa saman,maganganunsu kawai ke yimata yawo akunne tanajin sautin muryarsu yana dad’a k’aruwa
Ta banka k’ofar bedroom dinsa da k’arfi,tare da tura k’ofar bayin
Yana tsaye jikin shower,Yana sakar ma kansa ruwan sanyi
STORY CONTINUES BELOW
K’an-k’amesa tayi jikinta na kyar-kyarwa
“gasu can…….kirana sukeyi,d’aukata zasuyi,kataimakeni kafitar Dani daga cikin gidannan……
“Suwaye?”
Yatambayeta dasauri
Kasa bashi amsa tayi Dan ta rud’e sosai
K’aramin towel ya d’aura yakamo hannunta suka fito daga bayin
Addu’o I yadinga tofa Mata,zuwa can tadena sambatun datakeyi, Takoma sauke ajiyar zuciya
Ya dauko wani tawul din yafara gogemata gashin kanta daya jike yayinda tashiga bayin
“Aduk sanda kika ga wani Abu na tsoratarwa,ki rinka ambaton sunan Allah kikuma dungayin addu’a,
Tsoratar dakikeyi shizeba masu tsoratar dake damar cutar dake”
tadago kanta tana kallonsa har lokacin jikinta bedena rawa ba
“Bazan iya zama agidannan ba,bazan iya ba,ka maidani gida Dan Allah”
Hmmmmmmmmm yasauke numfashi
“Ko zaki iya gaya min yanayin da mama take ciki a halin yanzu?
Nasan tana cikin farin ciki,da jin dadin kinyi aure,abunda tadade tanason tagani,
Me kike tunanin zataji idan har ta fuskanci kina cikin matsala a halin yanzu?
Yad’an numfasa sannan yacigaba da cewa
“Nasan zata shiga damuwa,da tashin hankali,wanda ze iya tado mata da ciwonta,sam komawarki gida ba mafita bane
Ta yayama daga yin auranki kwananki daya da tarewa ace kinkoma gida,me kike tunanin mutane zasu ce?
Nasan mak’iya dariya zasuyi,Dan haka kicire wannan tunanin a zuciyarki
Badai sai bana tare dake a ke tsorataki ba?
To bazan kara zuwa ko nan da can batare dake ba,ba abunda ze koma tsorataki ina tare dake”
Yak’arasa fada yana share mata hawayen dake gangarowa daga idanuwanta
Tabbas abunda yafada gaskiyane,mama tanacikin farin ciki a halin yanzu
Dole ta hak’ura ta danne damuwarta
Mik’ewa yayi yazaro mata rigar bacci ya mik’a Mata
“Kayan jikinki sun jik’e,kisanya wannan”
Amsa tayi tana dubansa,shid’inma ita yike kallo ganin nawin cire kayan takeyi agabansa yasa yace
“Kinajin kunya ko?to bari infita kisa kayan”
Yak’arasa fada yana juyawa
Da hanzari ta rik’o hannunsa
“Baka ce bakace bazaka k’ara barina nikadai ba?
Ya jinjina Kai
“Eh,Amma ai naga nawin cire kayan kikeji agabana,shiyasa zanfita”
“To nidai karkafita,zan canza ai”
Tafad’a tanayin k’asa da kanta
Ya gyad’a kai yana kafeta da kyawawan idanuwansa
“To canza”
D’ago kanta takumayi suka had’a ido
Ta marai-raice fuska
“To ka dena kallona”
“Aa,bari ma infita kawai”
Yafada Yana niyyar zame hannusa dake rik’e cikin nata
Kara matse hannun nasa tayi tana cewa
STORY CONTINUES BELOW
“Kayi hakuri”
Ya gyara tsayuwarsa yana k’ara kafeta da ido
Cikin sanyin jiki ta war-ware k’aramin gyalen da ke kanta tadan daura a k’irjinta
Sannan tafara yaye doguwar rigar dake jikinta,cikin sauri tacire rigar tasa hannu zata d’auki rigar baccin
Dakatar da ita yayi tahanyar rik’emata hannu
Kallonsa tayi da rinannun idanunta
“Menene kuma?
Ya sauke gauron numfashi tare dacewa
“Kitsaya ahaka,ina buk’atar ganinki ahaka”
Zatai magana,yajanyota tafad’a jikinsa
Gabanta yafara fad’uwa
“Jaana,kamanta damuwar da muke cikine wai?
Ya girgiza Kai
“Ina sane banmanta ba”
“Amma……
Yakuma katseta
“Chuchu duk wad’annan abubuwan dakika ga anayi,anayine dan ahanamu samun cikar burinmu,shiyasa aka biyo ta wannan hanyar dan aga ankauda tunaninmu akan abunda mukadad’e muna muradi”
Ta girgiza kai
“Amma ai ba ayau ba,kabari sai mundawo cikin natsuwar mu tukunna…….
Yatsunsa biyu yad’aura akan labb’anta
“Kada kibawa azzalumai damar cin galaba akan rayuwar auranmu,nasan da zarar mun cika burinmu to tabbas wannan tsoratakin da akeyi za Adena,Dan dama anayine Dan aga ancanza mana tunani
Maganganun Aasim ne suka fara dawo mata da yi mata yawo akunne
“Idan har kanason rayuwar mijinki to tabbas kada ki kuskura ya kusanceki Dan duk ranar da yayi hakan to tabbas ze mutu Kamar yadda wannan ya mutu”
Umar ya katsemata tunanin da takeyi
“Kada kibari maganganunsa suyi tasiri a zuciyarki,kibani dama zaki tabbatar da abunda Nike fadamiki…..
Yak’ara matseta a jikinsa
Hankalinta yak’ara tashi
“Aa kayi hak’uri Dan Allah,bazan iya ba!
Kallonta yayi sosai, daga bisani ya janye jikinsa ya kwanta agefen gadon yana juya mata baya
Hawaye ne yacigaba da gangaro mata,yaza tayi da rayuwarta ne?
Aduniya babu abunda ta tsana irin taga b’acin ran Umar,Amma yaza ayi ya fahimci irin abubuwan datake gani na razanarwa??
Durk’usawa tayi agaban gadon,cikin kuka tafara cewa
“Dan Allah kayi hak’uri…….
Juyowa yayi ahankali yana kallonta,ya sakar mata murmushin karfin Hali
“Kada kidamu kanki,ki hawo kikwanta,nima nasan ba dai-dai bane inbukaci hakan agareki awannan yanayin danike ciki
Amma idan muka ce zamu biyema wannan al’amarin haka zamuyita zama,kuma kimin uzuri kinfi kowa sanin hak’urin dana dad’e inayi”
Ta jinjina Kai
“Nasani,amma ka gafarceni tukunna Dan Allah”
Ya gyad’a kai yana kuma yimata murmushi tare da dagota
Suka kwanta suna fuskantar juna
“Karki damu,kiyi baccinki Amma kibari in rungumeki ki kwana ajikina,babu abunda zanmiki”
Ta jinjina mai Kai,ahaka suka kwana rungume da juna
Kowane da abunda yike sak’awa acikin zuciyarsa
STORY CONTINUES BELOW
Da Asuba,ita Tafara tashi,wani irin yunk’urin amai ne yatasheta
Bayi tashiga dasauri tanata kakarin amai
Sai dai babu amai babu labarinsa sai uban kakarin datakeyi
Tsayawa tayi tana maida numfashi
Ta kunna famfo Dan ta dauraye bakin da fuskarta
Sai dai me? A memakon taga ruwa saitaga jini nata bul-bulowa
Baya tayi dasauri tana murza idanuwanta Dan tabbatar da jinin datagani
Still jinin tagani harda guda-guda
JINNUL
AASHIQUE🌹 +
NA
HARIRA ALIYU (yarfillo)
✍✍✍✍✍✍✍
*GOLDEL PEN WRITER’S ASSOCIATION*
✍✍✍✍✍✍✍
❄_We are bearers of sooo golden a pen We write assidiously percieven no pain Sooo magical Our creative golden pen Be hold our words A product of our pen Savour our words, for it will cause you no pain_❄
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
Dedicated to little hajjo
Gisuwa da fatan alkhairi ga babbar Yaya hafsat aliyu
🅿AGE📕 6⃣
Bissmillahir rahmanin rahim
Hannunta na rawa takulle kan famfon tafito daga bayin
Ta zauna bakin gadon tana kallon fuskar Umar
Bacci yikeyi sosai,tafashe da kuka tana dafa kanta datakeji yanayimata wani irin ciwo Kamar ze rabe biyu
*** *** ***
Washegari
Anty kaltum da yaranta anan suka wuni,hakan yasa tad’an saki sai yamma suka tafi
Bayan sun dawo daga yimusu rakiya,umar yakalleta yanacewa
“Kishirya mufita yawo”
Tayi murmushin Jin dad’i Dan dama zaman gidan ya isheta jitakeyi kaman akan k’aya take
“Yanzu,ko anjima?
“Yanzu mana,”
Ya bata amsa
Ta gyad’a kai
“To muje karakani d’akin”
Dariya yayi had’i da cewa
“Matsoraciya zanga yadda zakiyi innafara fita aiki”
Tafiya tafara yi Tana cewa
“Tare zamu rink’a zuwa ai Dan bazan taba zama nikadai ba Allah”
Bedroom d’inta suka shiga tasauya kayan dake jikinta zuwa ga bak’ar jallabiya
Tayana gyalen rigar tana d’aukar wayarta
“Muje nagama”
Kallonsa tayi jin yayi shuru
“Yadai nace nagama muje”
Janyota yayi gab dashi suna shak’ar numfashin juna
“Chuchu!
Yakirata da wata kalar kasalalliyar murya
Suka kalli juna,yasauke numfashi me nawi
Tare da kama hannunta yad’aura akan k’irjinsa
“Chuchu,zuciyata tana bugawa da k’aunarki ne,a duk sanda nakalleki inajin k’aunarki na k’ara bin jinina da dukkanin jijiyoyina……
STORY CONTINUES BELOW
Tayi guntun murmushi tare da kama nasa hannun tad’aura akan nata k’irjin tace
“Nima haka, kodayaushe zuciyata bata wani abun da take ambato face sunanka,ina sonka fiye da yadda Nike son kaina,fiye da yadda nike son rayuwata,bazan iya rayuwa idan babu Kai na”
Rungumeta yayi yana k’ara sauke sassanyar ajiyar zuciya
“Ina alfahari da samunki danayi amatsayin Mata,zankasance tare dake har k’arshen rayuwata”
Har lokacin murmushi be bar fuskarta ba
“Muje,kada dare yayi”
Yakama hannunta suka jero zuciyoyinsu cike da begen juna
Saida suka shiga motar me gadi yabud’e suka hau Kan titi sannan yace
“Ina kikeson mujene,inda zesakaki nishadi?
Tad’an rausayar da fararen idanuwanta
“Uhm muje…….
Ya ketseta
“Wajen shan ice cream ko?
Dariya tayi tana kallonsa
“Ya akayi kasan abunda zanfad’a?
Hankalinsa nakan tuk’in yabata amsa
“Saboda nasan kinasan Ice cream sosai”
Ta jinjina Kai
“Hakane,kumafa na kwana biyu bansha ba,tun zuwan dakayi kaduna wancan karen dakazo mindashi”
Ya gyad’a Kai
“To yau zaki sha ki k’oshi harkiyi odarsa zuwa gida”
Basu dad’e suna tafiya ba suka isa katafaren wurin
Wuri me kyau suka zauna aka kawo musu ice cream d’in,suna sha suna fira cikin nishad’i
Duk da k’asan zuciyarta akwai damuwa amma tayi k’ok’ori ta danne.
Basu suka bar wurin ba sai tara saura
Suna shiga falo ko zama basuyi ba,ya fizgota jikinsa yana shisshin shina wuyanta cikin wani irin yanayi
K’ok’orin janye jikinta tafara yi tanacewa
“Jaana please”
Kuma matseta yayi yana k’ok’orin had’a bakinsa da nata
Yayi nasan cafkar labb’anta masu ban Sha’awa aduk sanda take motsasu gurin yin magana
Kissing d’inta yafarayi azafafe,yana shasshafata
Maganganun Aasim ne suka fara yimata yawo a kunne
K’arfinta tasa gabad’aya,ta turesa tare da janye jikinta tana maida numfashi
Yakuma janyota yana kallonta da idanuwansa dasuka canza launi
Cikin wata kalar murya me cike da buk’ata yace
“Rauda please kada kihanani,ayanzu ke matata ce babu wani shamaki atsakaninmu”
Girgiza kai tayi idanuwanta suka fara cikowa da hawaye
“Jaana dan Allah kayi hak’uri bazan iya ba……..
Ya k’ura mata ido zuciyarsa na bugawa dasauri
“Chuchu idan kika hanani yin abunda zuciyata take muradi ahalin yanzu,wallahi zanshiga wani Hali,kitausayamin please……
Zuciyarta tafara karyewa,hak’ik’a tana tsananin k’aunarsa tana son tafaranta Masa, Amma yazatayi?idan wani abu yasamesa fa?
Kuka tafarayi me cike da tsananin damuwa
STORY CONTINUES BELOW
Yasauke numfashi me nawi
Tare da jinjina kai
“Shikenan ya Isa,tunda bakyaso shikenan”
Yak’arasa fad’a Yana sakinta yakoma kan kujera yazauna,ya lumshe manyan idanuwansa shikad’ai yasan halin dayike ciki
Kuka takeyi sosai tarasa yadda zatayi da rayuwarta
Sun d’auki lokaci ahaka,daga bisani yataso yadawo inda take durk’ushe
Zatai magana ya katseta ta hanyar cewa
“Karkice komai,nafahimceki,bazan tab’a yimiki abunda bakyaso ba,akullum burina infarantamiki,danhaka kada kidami kanki zancigaba da hak’uri har zuwa sanda zakiyi niyya”
Takallesa da jik’akk’un idanunta da sukayi luhu-luhu tace
“Wallahi inason infaranta maka kaima kasani Amma………..
Yatsunsa biyu y d’aura akan lips d’inta
“Nace nafahimta,tashi muje kiwatsa
Ruwa kikwanta”
Tamik’e tanajin zuciyarta babu dad’i
Dakanshi yashiga yahad’amata ruwan wanka tashiga
Kafin tafito haryaciro mata kayan bacci,hakan yak’ara mata tausayinsa sosai
Bayan tasa kayan tazauna kusa da shi tare da kama hannunsa ta matse cikin nata
Cikin murya me taushi tafara magana
“Jaana kagafarceni,nasan hukuncin duk macen da tak’i zuwa shimfid’ar mijinta,nasan mala’iku ke tsinemata har gari yawaye
Amma…….
D’aga mata hannu yayi yace
“Nacemiki nafahimceki meyasa kikeson nanata abu d’ayane,alfarma d’aya kawai Nike so kimin”
Kallonsa tayi suka had’a ido
Yacigaba dacewa
“Inaso muraba d’aki wajen kwanciya,kikwana a naki in kwana anawa,saboda aduk sanda nike tare dake hankalina tashi yikeyi………
Ta katseshi
“Jaana amma kasan bazan iya kwana a d’aki ni kad’ai ba ko?
Ya jinjina kai
“Nasani amma hak’uri zakiyi, Kamar yadda kika rok’i alfarmar in k’yaleki nakuma k’yaleki
Nima kimin wannan alfarmar dan Allah ta wannan hanyarce kad’ai zansamu sa’ida”
Kasa cewa komai tayi, kallonsa kawai takeyi
Yamik’e Yana tambayarta
“Akwai wani abun da kike buk’ata ne?
Ta girgiza kai alamar aa
Yace
“To shikenan zanje inkwanta,kiyi addu a kafin kiyi bacci kinji?
Gyad’a Masa kai kawai tayi zuciyarta cike da fargaba
Ya durk’uso yanayimata murmushin k’arfin Hali tare da manna mata kiss a goshinta
“Good night”
Yafad’a yana ficewa daga d’akin tare da rufomata k’ofa
Ajiyar zuciya tasauke gabanta nafad’uwa,
Shiko Umar bedroom d’insa yashiga,yashiga toilet tare da sakar ma kansa ruwan sanyi
Dafa bangon bayin yayi ruwan na sauka ajikinsa
Ya runtse idanuwansa yana tunanin yadda ze b’ullo ma al’amarin,shikad’ai yasan irin feeling d’in da yikeyi akanta
Zuciyarsa ta haskomata kyakkyawar k’irarta
STORY CONTINUES BELOW
Yakuma runtse idon yana dun’k’ule hannunsa yabuga a bango
“Why Rauda?meyasa bazaki fahimci yadda kike araina bane?
Yafurta ahankali
Janyo tawul yayi yad’aura ya janyo wani yana goge gashin kansa
A gaggauce yasanya kayan bacci yafad’a Kan gado
Yayi rub da ciki,tsananin sha’awarta na kuma taso Masa.
Itako tana zaune gefen gadon tana rarraba idanu,dan gani takeyi kamar zataga wani abun tsoro
Kallon agogo tayi k’arfe shad’aya da minti arba’in
Haka tacigaba da zama tana dube-dube ahaka bacci yafara d’aukarata
Sama-sama taji andafa mata kafad’a,tabud’e ido cikin yanayin bacci tana kallon kafad’ar,wasu dogayen yatsu tagani bak’ak’e sid’ik tare da zak’o-zak’on k’umbuna
Wartsakewa tayi dasauri tana k’ara kallon kafad’ar
Still hannun yana kafad’ar ta
Azabure tamik’e tana kallon kan gadon,babu kowa akai
Motsi tafara ji ak’asan gadon, hakan yatabbatar mata abunda yatab’atan yana k’ark’ashin gadon
Hanyar fita d’akin tayi,ta murd’a hannun k’ofar amma gam tak’i bud’ewa,
Tafara jijjiga k’ofar da ka k’arfi gabanta na wani mugun fad’uwa
Shafata wuya akayi tabaya
Ta k’wala ihu tare da juyawa a razane
Wayam babu kowa,bubbuga k’ofar tayi tana kiran sunan Umar,amma shuru
Tazame k’asa tana numfarfashi,
Wani kalan gurnani tafaraji me tsoratarwa yana fitowo daga cikin bayi
Bam!
Aka banko k’ofar bayin,runtse idanuwanta tayi dasauri tana ambaton sunan Allah Dan tasan shikad’ai ze kawomata agaji
“Habibty!
Taji anfad’a cikin wani irin salo
Tabud’e idanuwanta dasauri tana kallon inda tajiyo Kiran
Aasim tagani kwance kan gadon ya kishingid’a da fulo
Yanayimata wani irin kallo da idanuwansa masu d’auke da k’wayar ido kalar golden
Yacigaba da cewa
“Barka dai habibty,barka da dare”
Yarrr yarrr tsigar jikinta ta tashi,ba bu inda baya rawa ajikinta
Addu’a kawai takeyi
Dariya yafarayi yanacewa
“Nazo tayaki kwana ne bazaki yimin maraba ba?
“Dan…..Dan…..Allah…kayi…. hak’uri’
Tace cikin rawar murya da tsananin razana
Dariya yakuma yi akaro na biyu
“Gabad’aya ni natsani kalmar hak’uri,dan haka kada kik’ara ambaton hak’uri agabana,kitaso ki hawo kan gadon”
Girgiza kai tayi jikinta na kyar-kyarwa kamar wacce akaciro daga cikin k’ank’ara
Yagyad’a kai yana murmushin k’asaita
“Kinfi kowa sanin bana nanata magana sau biyu,idan bazaki taso ba to akwai wad’anda zasu taso dake
Yana gama fad’a kuwa taji anciccib’eta and’agata sama amma kuma bata ganin wad’anda suka d’agatan
Tana ihu kuma amma ihun baya fita
STORY CONTINUES BELOW
Kan gadon aka direta, gabad’aya jikinta ya mutu bata da kuzarin dazata iya guduwa
Duk surar datazo bakinta karantawa takeyi
Yayi murmushi tare da cewa
“Tun kan asan za a haifeki nike karanta al’qur ani,yanzuma zanso ace ni nike karantamiki tunda naga arud’e kike wasu ayoyinma ba dede kike karantasu ba”
Cikin tsananin tsorata tace.
“Menayi maka ne da kake bibiyar rayuwata,meyasa bazaka k’yaleni nayi rayuwa kamar yadda sauran al’umma sukeyi ba,meyasa!
Yayi guntun murmushi
“Sabida ba’ayiki dan kowa ba,anyiki ne danni kad’ai,kuma dani kad’ai zaki rayu,ina sonki habibty bazan tab’a iya rayuwa babu keba………
Cikin kuka tace
“Wannan ba so bane,zalunci ne………
Bata k’arasa ba ya damk’o gashin kanta yana kallon fuskarta
“Kada ki kuskura,ki zageni,kinsan halina sarai”
Ya matso yana gogga fuskarsa me zagaye saje a wuyanta
“Hak’ik’a kinacin albarkacin son dankeyi Miki,shiyasa nike k’yaleki,amma da tuni na b’atar dake a duniya,Dan babu mahaluk’in da ya isa yafad’amin maka manciyar abubuwan dakike fad’amin batare dana shafe labarinsa ba!
Runtse idanuwanta tayi wasu hawaye masu zafi suna gangaro gefen kuncinta
“Rauda!!!!!!
Yakira sunanta
Tabud’e ido tana kallon sa
“Kicire tunanin cewa zanrabu dake arayuwa,Dan wallahi babu wani malamin da ya Isa yarabani dake”
Y’arfillo.
🌹 JINNUL
AASHIQUE🌹
NA
HARIRA ALIYU (y’arfillo)
✍✍✍✍✍✍✍
*GOLDEL PEN WRITER’S ASSOCIATION*
✍✍✍✍✍✍✍
❄_We are bearers of sooo golden a pen We write assidiously percieven no pain Sooo magical Our creative golden pen Be hold our words A product of our pen Savour our words, for it will cause you no pain_❄
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
Dedicated to little hajjo and my elder sister Hafsat aliyu
_Kuna a raina yan uwana yan *Golden Pen* hadin kanku na burgeni hakika kun cika Zinarai, kuma yan Amana, inama yan k’ungiyoyi zasuyi kuyi daku yan uwana, da tabbas zasu samu ci gaba, wlh *Golden Pen* kun hadu dari bisa milyoyi, bani da abunda zan baku shiyasa na baku wannan page kuyi yan da kukeso dashi na bakushi kyau ta,👌_
🅿AGE📕 7⃣
Bissmillahir rahmanin rahim
“Rauda!!!!!!
Yakira sunanta
Tabud’e ido tana kallon sa
“Kicire tunanin cewa zanrabu dake a rayuwa,Dan wallahi babu wani malamin da ya Isa yarabani dake”
Tanaso tayi magana amma taji bakinta yayi mata nawi takasa motsashi,kamar yadda takasa motsa koda d’an ya tsanta
Yakuma yin murmushi yana shafa lip’s d’inta da yatsansa
“Wani hukunci yakamata inyima wannan labb’an?dasuka bari wani ya tsotsesu”
Yad’an rausayar dakai cikin yanayin nishad’i
Bakisan cewa wa’annan kyawawan labb’an suna d’aya daga cikin manyan dalilan dana kasa rabuwa dake ba??
Hmmmmmm yasauke numfashi
Sannan yacigaba da cewa
STORY CONTINUES BELOW
“Kada ki sake,habibty kisani komai na jikinki mallakina ne nikad’ai”
Ya matso da fuskarta kusa da tasa,dan har lokacin gashin kanta na damk’e a hannunsa
Kallon lips d’inta yikeyi
“Hukunci d’aya zanyima labb’an Nan,zanta shansu har gari ya waye”
Tanaji yafara tsotsar lips d’in cikin wani salo na mugunta
Bata da ikon hanasa dan bata da yadda zatayi, in Banda rad’ad’i babu abunda lips d’in kemata
Wani kalan yanayi taji tafara shiga, ahankali tunaninta yafata tsayawa taji kanta yanayimata waiwayi take wani kalan bacci me cike da wahala ya d’auketa.
B’angaren Umar ko kai-kawo yike tayi acikin d’akin
Ahankali yaji mararsa tayi wani k’arfi tare da fara ciwo
Ya kwanta a k’asan kafet hannunsa dafe da mararsa
Da k’yar bacci ya d’aukesa
*** *** ***
Washegari,ana kiran assalatu tafarka, tabud’e idanuwanta dasukayi mata nawi tana kallon cikin d’akin
Babu kowa aciki,jitayi bakinta nayimata zugi ahankali k’wa-k’walwarta tafara tariyomata abunda yafaru
Ajiyar zuciya tasauke tatashi daga kwanciyar datake ta jingina da jikin gadon
Gani takeyi kamar mafarki take,amma kuma tasan ba mafarkin bane
Nannauyar ajiyar zuciya tasauke tana tunanin yadda zata cigaba da rayuwa da aljani amatsayin mijinta bayan kuma ga nata mijin yanaso yarabata dashi
Mik’ewa tayi tashiga bayi tad’auro alwala,tagabatar da sallar Asuba
Sannan tafito falon lokacin gari yafara haske, bedroom d’insa ta nufa dan bataji fitowarsa sallah ba
Ta tura k’ofar d’akin tana sallama
Yana kwance k’asan kafet yatakure guri d’aya
A sanyaye ta k’arasa inda yike ta durk’sa tana kallonsa cike da tausayinsa
“Na k’osa muyi aurannan chuchu,inhuta da kwanciya nikad’ai,yazamana kullum ina manne dake ina shak’ar daddad’an k’amshinki”
Maganar umar tadawo mata
Sassanyar ajiyar zuciya tasauke tasa hannu a gefen fuskarsa tana shafawa ahankali
Ya bud’e idanunsa ya watsasu akanta dama ba baccin yikeyi ba ya farka tuntuni
Kallon juna sukayi sosai
Daga bisani ya sakarmata guntun murmushi
“Madam har kintashi?
Ta d’aga masa kai alamar eh tare da cewa
“Kaima yakamata katashi kayi sallah”
Ya yunk’ura ya mik’e zetashi,mararsa tayi wani mugun k’ullewa
Dasauri yakoma yazauna yana d’an runtse idonsa alamar ciwon na damunsa
Rauda tace
“Lafiya jaana?
Guntun numfashi ya sauke yana bata amsa
“Cikinane ke ciwo”
Cikin tausayawa tace
“Sannu,tunyaushe yafara ma?
“Cikin dare amma nasha magani nasan zebari nan bada jimawa ba”
Ta gyad’a kai tare da mik’ewa
“Allah yak’ara sauki bari inhad’ama ruwan wankan”
Bayin tashiga tahad’a mai tafito tace ta had’a
Saida yashiga sannan tafito da ga d’akin tashiga kicin
STORY CONTINUES BELOW
A gurguje ta had’a abun kari,tana cikin jerawa,yasauko
Ya zauna yanayimata sannu
Itama tazauna suna fuskantar juna tafara tsiyaya ruwan zafi a Kofi
Kallonta yikeyi anatse ya lura da lips d’inta dasukayi ja
Yace
“Chuchu meyasami lips d’inki?
Kallonsa tayi tana ajiye kofin
“Babu komai”
Ze kuma magana mararsa takuma k’ullewa
Dasauri ya dafa cikinsa,tasowa tayi dasauri ta dawo inda yike tana tambayar
“Jaana cikinne?
Ya d’aga mata kai kawai
Hankalinta yatashi
“Fad’amin inda maganin yike in d’auko maka”
Ya girgiza Kai
“Aa,d’auko min wayata kawai inkira doctor zainab nasan yanzu bata wuce asibiti ba sai ta biyo takawomin allura”
Tad’auko mai wayar tamik’amai har lokacin yana dafe cikinsa
Ya lalubo numban doctor zainab yadanna
Ringing biyu tad’auka tana fad’in ango kasha k’amshi
“Kinwuce asibiti ne?
Tace aa
“Yace kibiyo please banad’an jin dad’i”
Daga can b’angaren doctor zainab tace
“Subhanallah meke damunka?
Yafad’a mata
Tace
“To shikenan ganinan zuwa yanzu insha Allah”
Ya ajiye wayar Yana mik’ewa da gyar
“Bari naje nakwanta kafin tazo,kibiyoni da Lipton d’aki”
Ta jinjina kai cikin damuwa tana bin bayansa da kallo haryashige
Sannan tasauke ajiyar zuciya,ta had’a Lipton d’in tabishi da shi
Ya amsa yana kurb’a kad’an-kad’an
Hannunta yakama ganin yadda duk tashi ga damuwa
“Chuchu bafa wani abu bane,inayin alluran zedena dama nasaba irin ciwon kada kid’aga hankalinki please”
Hmmmmmm tasauke doguwar ajiyar zuciya
Knocking d’in k’ofar falon akafarayi taje tabud’e
Doctor zainab ce,suka gaisa sannan tayimata jagora zuwa d’akinsa.
Sama-sama ya amsa gaisuwar doctor zainab dan ciwon ya matsamasa
Doctor zainab ta fahimci abunda yike damunsa tsaf hakan yasa data mai allura zata wuce tacema Rauda tana son magana da ita
A falo suka zauna,Rauda zata had’amata tee tacemata tabarshi ta k’oshi tazauna suyi maganar kawai
Bayan sun zauna doctor zainab takalleta sosai tace
“Kinayin al’ada ne?
Rauda takalleta tana mamakin tambayar
Doctor zainab tayi murmushi tare dacewa
“Kiyi hak’uri inason infahimci wani abune”
Girgiza mata kai Rauda tayi
“Aa banayi”
Doctor zainab ta jinjina Kai
“Amma meyasa kik’i yarda da mijinki?
Cikin rashin fahimta Rauda take kallonta
Doctor zainab tayi murmushi tana cigaba dacewa
“Nasani yawancin y’ammata idan akakawosu gidan auransu sukank’i yarda da angwayensu,badan komai ba sai dan tsoro
STORY CONTINUES BELOW
Kuma dama tsoro wajibine ga duk macen da takai budurcinta gidan mijinta
Amma yanzu kai ya waye andaina wannan k’in amincewar,kuma miyema abun gudu ga wanda yazama muharraminka?
Bakisan idan Sha’awa tayiwa namiji yawa tana iya halaka saba?
Wannan ciwon cikin dakikaga yanayi somin tab’i ne inhar bazaki yadda da mijinki ba
Tad’an dakata sannan tacigaba da cewa
“Dan allah ki ajiye wani tsoro da fargaba agefe ki bawa mijinki kulawa kinji?
Gyad’a mata kai kawai Rauda tayi tana nazarin maganganunta
Doctor zainab tamik’e tana d’aukar jakarta.
“Nizan wuce nasan yanzu yasamu bacci dan allurar tanasa bacci sai anjima”
Rauda tamik’e tayimata rakiya zuwa k’ofar falo sannan takoma d’akinsa
Ganin yasamu bacci yasa ta janyo mai k’ofar tadawo falo tana nazarin abunyi
Gabad’aya tarasa yadda zatayi,wayarta tad’auko tadanna numban aminiyarta Salma bugu d’aya salma ta d’auka tanacewa
“Amarya kinsha k’amshi,sai yau akatuna dani?anata ragargazar amarci?
Rauda tasauke ajiyar zuciya cikin damuwa tace
“Salma ina cikin matsala bansan ya zanyi ba”
Daga can b’angaren salma tace
“Subhanallah matsala kuma Rauda?
Rauda tafashe da kuka
“Salma bansan yazanyi da rayuwata ba,inaganin na tsallake rijiya da baya ashe bansani ba cikin rijiyar nafad’a”
Cikin tashin hankali Salma tace
“Nashiga uku ni Salma,me yafaru Kuma?
Rauda takwashe komai tafad’a mata
Hak’ik’a Salma ta kad’u da jin labarin
Tama rasa abunda zatace
Zuwa can tasauke numfashi tare da cewa
“Kenan Aasim kwantan b’auna yayi,yayi kaman yarabu dake ashe azzalumin yananan……
Rauda tayi saurin katseta
“Aa Salma karki zagesa wallahi ayanzu yawuce duk inda kike tunani”
Salma tasauke doguwar ajiyar zuciya
“Hmmmmmm yanzu miye abunyi Rauda?danni wallahi kaina ya kulle”
Itama Rauda ajiyar zuciyar tasauke
“Ni yanzu damuwata d’aya cewa dayayi Umar ze mutu idan har ya kusanceni,gashi umar yana matuk’ar buk’atata, kifad’a min yadda zanyi please Salma,ke kad’aice wacce nike iya gayama damuwata”
Salma tasauke numfashi
“Ina ganin kaman yafad’a miki hakane dan ya tsorataki, Amma baze iya kashesa ba, Dan ina tunanin umar yafi k’arfinsa tunda har yabari kika auresa”
Ta girgiza Kai
“Bana tunanin hakan”
Salma tace
“To yakamata munemi wani malamin Rauda,zan k’ara yin tunani anjima inga yadda za’ayi amma kafinnan kinsan y’ar dabaran dazakiyima umar d’in dan ki rage masa feeling d’in”
“Shikenan saina jiki anjiman”
Rauda tafad’a tare da aje wayar
Tanaciga da lulawa cikin tunani
Sai k’arfe biyun rana yatashi tana zaune agefen sa
Tasha fa gefen fuskarsa tana cewa da tausassar muryarta
“Jaana,yajikin?cikin yadena ciwo?
Yayi murmushi yana bata amsa
“Yadena chuchu,saidai kukan yunwa dayikeyi”
STORY CONTINUES BELOW
Tamaida mai martanin murmushin
“To alhamdulillah,kawatsa ruwa bari ind’auko ma ferfesun kifin danayima”
Yagyad’a kai yana mik’ewa
“To madam”
Fitowa daga d’akin tayi tashiga kicin tabud’e kular data zuba ferfesun kifin tare da d’auko plate zata zuba?
Saidai me a memakon taga kifin saitaga manyan b’eraye kwance acikin kular da alamu sun dahu sosai sai uban turiri sukeyi”
Mamakine ya kamata kodayike ba abun mamaki bane dantasan zata iya ganin abunda yafi hakama ayanzu
Rufe kular tayi tad’auka ta wurgata dustbin
Ruwan indomie ta maida tana tsaye har indomin ta nuna tajuye a plate
Tadawo d’akin lokacin yafito da wanka yana sallah
Tazauna tanajiran ya idar,yasallame sallar yana shafa addu’a
Sannan ya juyo yana dubanta
“Madam yadai?
“Dede”
Tafad’a tana ajiye plate d’in agabansa
Yayi murmushi tare da kamo hannunta yazaunar da ita a k’asa inda yike zaune
“Ai tare zamu ci,dannasan kema baki ci abincin rana ba”
Bata mai musu ba sukaci indomin tare
Bayan sunkammala yace
“D’azu bayan fitarki zayyad ya kirani akan maganar danamai na malaminnan,yace ze turomin numban malamin inyaso sai muyi masa bayani”
Tagyad’a kai
“To allah yasa mudace”
Ya amsa da amin
Daddare suna zaune a falo wuraren misalin shabiyu nadare
Yakalleta yana cewa
“Madam tashi inrakaki kije kikwanta”
Marai-raice fuska tayi tana kallon sa
“Allah yau bazan iya kwana nikad’ai ba,jiya nikad’ai nasan abunda nagani”
Hmmmmm yasauke numfashi
“To yanzu yakike so ayi?.
“Mukwana tare,wannan tsarin naraba d’aki a sokeshi please”
Yayi guntun murmushi
“To shikenan tashi muje,a wani bedroom d’in zamu kwana?naki ko nawa?
“Naka”
Tafad’a
Yace
“Ok tashi muje”
Yakashe kayan kallon
Bedroom d’inta yafara rakata dan tasa kayan bacci tabud’e wardrobe d’in kayan baccin tana tunanin wanda zata sa
Umar ya d’auko wata maroon d’in riga yamik’o Mata
“Naga sai ruwan ido kikeyi kisa wannan”
Murmushi tayi ta amsa
Yakauda kansa yayinda takesa rigar dan bayaso yaga abunda zetada mai hankali
Takammala sa rigan tace
“Muje”
Suka rufe bedroom d’inta suka shiga nasa
Zama tayi bakin gadon tana duba addu’o in da salma taturomata
Shiko canza kayan yikeyi yana kallonta,wani irin feeling d’inta na taso Masa
Tun yana kauda abun aransa haryaji baze iya ba
Jingina yayi da bangon d’akin yana maida numfashi ahankal
Tad’ago tana kallonsa
“Lafiya jaana?
Ya girgiza kai batare dayace mata komai ba
Ajiye wayar tayi tataso,tana k’ara tambayar sa
“Jaana cikinne?
STORY CONTINUES BELOW
Yabud’e idanuwansa ahankali yana kallonta
Rigar tabi jikinta sosai
Jiyayi wani abu na fizgarsa da k’arfi
Besan sanda ya janyota yamannata da jikinsa ba yafara kissing d’inta ta ko Ina
“Jaana!
Be saurareta ba ya sureta ya ajiyeta kan gadon yana cigaba da kissing d’inta
“Jaana please kabari sai munje gun malamin tukunna banaso wani abu yasameka…..
Rufe mata bakin yayi da nasa,takasa k’arasa abunda zatace
Shasshafata yashiga yi ta ko Ina yana sauke wani numfashi a wahalce
Bakinta dake cikin nasa yasaki yamaidasa kan wuyanta
Yanacigaba da kissing d’inta ta ko ina
Wata irin iskace da guguwa ta turniki’e d’akin
Lokaci d’aya, hankalinta yatashi jin batajin motsin Umar, tabud’e idanuwanta a firgice data rufe yayinda guguwar ta turnik’e d’akin
Aasim tagani tsaye idanuwansa sunyi jawur yana nuna wani abu da hannunsa
Dasauri takalli abunda yike nunawan, Umar ta hango can saman d’akin jijiyoyin wuyansa sun mummurd’e idanuwansa sun firfito waje
Ta zabura tamik’e jikinta yafara rawa
“Narok’eka kada ka kasheshi,dan girman allah”
Ko kallonta beyi ba,ta taso dasauri tana nufar inda yike
“Dan girman allah narok’eka……..
Da razanannun idanunsa yayimata wani kallo
Wani irin haske yafito daga cikin idonsa
Wata iskace tad’auketa tahad’a da bango wanda kanta yayi mugun buguwa
Durk’ushe wa tayi tana kuka tana cigaba da rok’onsa
“Wallahi bazan k’ara sab’a ma umarninka ba,duk abunda kace inyi zanyi amma dan allah kada karabasa da rayuwarsa
Kuma kallonta yayi idanuwansa nakuma rinewa
Yafara magana muryarsa nafita bibbiyu
“Kina ganin kamar bazan iya abunda nace ba ne ko,to yau zanbaki mamaki!!!!
“Wallahi bazan k’ara sab’a ma ka ba nayi alk’awari,kada ka kashesa dan allah”
Hannunsa yaja baya, umar yafad’o daga saman yazube a k’asa yana maida numfashi sama-sama dan ya wahala matuk’a
Dagudu tatashi ta isa gun Umar tana jijjigasa tana kiran sunansa
“Kisani ayanzu dama biyu zanbaki,ko kisa yasakeki ko kuma ki rasasa gabad’aya”
Yana gama fad’ar haka ya b’ace
Hankalinta yayi matuk’ar tashi jijjigasa kawai takeyi
“Jaana katashi karkata fi kabarni……
Yabud’e idanuwansa a wahalce yana kallonta
Ahankali yamaida idanunsa yarufe
Kuka takeyi sosai tana jijjigasa
“Ayanzu dama biyu tarage miki, ko kisa shi yasakeki kokuma kirasasa gaba d’aya”
Maganar Aasim tadawo mata
Hannunta tasa a k’irjinsa da sauri,jin yana numfashi yasa ta mik’e tad’auki wayarsa jikinta na rawa ta lalubo numban zayyad tadanna Kira
Zayyad naganin kiran yasan ba lafiya ba,ya d’auka Jin muryar Rauda yasa yace
STORY CONTINUES BELOW
“Lafiya Rauda?a darennan ina umar d’in?
Muryarta narawa tace
“Zayyad kazo kataimakeni Umar ze mutu”
Mik’ewa zayyad ya yi daga kujerar da yike na office dan ranar Yana asibiti duty d’in dare yikeyi
“What?meyasamesa
“Kazo yanzu dan Allah”
Kawai tafad’a tana ajiye wayar tana cigaba da kuka
Shima aje tashi wayar yayi yafito dasauri yashiga motarsa
Gudu yike yi sosai har ya kawo gidan,saidayayita horn sannan me gadi yabud’e dan shi baccinsa yikeyi besanma wainar da ake toyawa ba
A tsakar gidan yayi parking yafito dasauri yana bubbuga k’ofar falon
Tana rungume dashi tana kuka taji ana bubbuga k’ofar
Tasan zayyad ne ta tashi har lokacin jikinta narawa taje tabud’e k’ofar
Ganin yanayin datake ciki yasa zayyad tambayar ta dasauri
“Ina Umar d’in?
D’akinsa ta nunamai da hannu kawai dan tama kasa magana
Yashiga d’akin,ganin halin da umar ke ciki yatada mai hankali sosai
Ciccib’osa yayi yafito dashi tana tsaye gabad’aya ta firgice
“Maza d’auko mayafinki muwuce asibiti”
Hijabin datake sallah dashi dake gefen kujera tad’auko tazura,yashimfid’eshi abayan motar
Yatada,zata shiga baya yace aa tashiga gaba dan ba inda zata zauna abayan
Yafigi motar aguje yana kuma tambayarta
“Kifad’a min meyasamesa?
Bakinta narawa tace
“Aasim…Aasim….
Yakalleta da sauri dayike yasan duk abunda kefaruwa
“Aasim?
Ta jinjina mai kai
Yasauke numfashi yana cewa
“Shikenan idan munje asibiti koda za atambayeki ace meyasamesa kice accident yayi kinji?
Ta gyad’a mai kai kawai tanajin kanta kamar ze juye
Suna isa asibitin akabashi taimakon gaggawa
Lokacin da doctor zayyad da nurses suka fito biyu saura
Ta taso daga durk’usan datayi tana kallon zayyad
Kafin ta tambayesa yace
“Kikwantar da hankalinki yadawo cikin hayyacinsa yanzu amma yasamu bacci kina iya shiga”
Tatura k’ofar d’akin tashiga
Zayyad yabita da kallon tausayawa
A kujerar da ke gaban gadon tazauna tana kallonsa
Lokaci d’aya harya fad’a,tana zaune tana kallonsa har asuba inbanda kuka ba abunda takeyi
Lokacin yafarka,ganinsa a asibiti yasa k’wa-k’walwarsa ta tariyo masa abunda yafaru
Cikin kuka taruko hannunsa tanacewa
”kayi hak’uri,duk sanadina kashiga wannan halin…..
Ya girgiza kai yana cewa
“Hak’urin mekike bani chuchu?
Kuka yacigaba dayi cikin tsananin damuwa
Ajiyar zuciya yasauke me nawi
STORY CONTINUES BELOW
Tare da sa hannu ya share mata hawayen da suke bin fuskarta
“Saiyanzu nafahimceki chuchu, saiyanzu na fahimci abundance yasa kika k’i yarda Dani, Amma inaso kisani babu abunda zesa inrabu dake
Inatare dake duk runtsi duk wuya”
Y’arfillo.
🌹 *_JINNUL_*
*_AASHIQUE_*🌹
NA
HARIRA ALIYU (y’arfillo)
✍✍✍✍✍✍✍
*GOLDEL PEN WRITER’S ASSOCIATION*
✍✍✍✍✍✍✍
❄_We are bearers of sooo golden a pen We write assidiously percieven no pain Sooo magical Our creative golden pen Be hold our words A product of our pen Savour our words, for it will cause you no pain_❄
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
Dedicated to Little hajjo and my elder sister
🅿AGE📕 8⃣
_Wannan page d’in nakune masoya jinnul aashique,na sadaukar dashi gareku,saboda k’aunarku ga littafin,ina godiya ga yadda kuke son wannan labari allah yabar zumunci,sannan ina baku hak’uri akan dad’ewa danikeyi bana typing insha allahu zanyi k’ok’ori inga ina yin yadda yadace nagode._
*_GAISUWA ga Aishatu Babayo Jos,ina godiya da kulawarki gareni,ba irin su o’o ba @maman ummi,dan inbanda tsokana babu abunda ta iya ba😜 amma dai duk da haka kema ina gaisuwa_*
_ADDU’A Ga besty safiyya maina,allah yabaki lafiya yasa kaffarane_
Bissmillahir rahmanir rahim👏🏻
Ta girgiza Kai cikin kuka tace
“Yanzu inane keyimaka ciwo?
Ajiyar zuciya yasauke dan babu inda bayamasa ciwo ajikinsa amma dan kada yak’ara tada mata hankali yasa yace
“Chuchu nifa naji sauk’i yanzu,wuyanane kawai ked’an yimin zafi,kuma shima nasan zuwa anjima zedaina insha allahu”
Ta kwantar dakanta agaban gadon
“Jaana tunanina yafara raguwa,Ina tsoron watarana k’wak’walwata ta juye danjina nikeyi kamar na kusa haukacewa”
Numfashi yasauke me nawi zuciyarsa cike da tarin damuwa dan shima tunanin nasa ya tsaya yarasa ta inda ze b’ulloma al’amarin,ada yayi tunanin al’amarin mesauk’i ne amma daren jiya yatabbatar mai da al’amarin Aasim ba k’aramin babban al’amari bane
Idanuwansa ya runtse yana furta ya rabb!
Ahankali
K’arfe takwas doctor zayyad yashigo d’akin yana sallama
Umar ne ya amsa mai,dan ita Rauda baccine yad’auketa me tattare da ciwon kai me tsanani
Zayyad yajanyo wata kujera yazauna yana duban umar
“Yajikinnaka?
“Dasauk’i”
Ya amsa mai
Zayyad yace
“Jiya cikin dare Rauda takirani tace inje kana cikin wani Hali dana tambayeta meke faruwa sai tace min Aasim,wai meke faruwane Umar?
Umar yasauke numfashi yana cewa
“Zayyad yanzu ba lokacin dazanyima bayani bane amma aikasan bana b’oyemaka komai”
Zayyad ya jinjina Kai
“Hakane,to yanzu inane kedamunka ajikinka?
“Wuyana,yanamin zafi da ciwo sosai kad’auko alluran……. yafad’a mai sunan alluran sannan yacigaba da cewa
“Kayimin,koze d’an lafamin”
Zayyad yamik’e yafice daga office d’in batare da yakuma cewa komai ba amma zahiri yana cikin damuwa da ganin halin da abokinsa keciki
STORY CONTINUES BELOW
Allurar yad’auko yamasa bayan yagama yace
“Ni zanje gida na dawo”
Umar yace
“To amma da na tashi Rauda ka ajiyeta itama inzaka dawo sai kabiya kad’aukota”
Zayyad yagyad’a kai yatsaya yana dubansu.
Hannunsa yasa Yana d’an bubbuga bayanta yana kiran sunanta
A d’an razane tafarka dan gabad’aya atsorace take
“Chuchu calm down nine”
Umar yafad’a,tasauke numfashi tana kallonsa
“Jikinne?
Ya girgiza Kai
“Aa ni naji sauk’i kitashi zayyad ze wuce ya ajeki agida inze dawo sai ya biya yad’auko ki”
Girgiza kai tayi ahankali
“Ni ba inda zanje,bazan barka kai kad’ai ba”
Hmmmmm chuchu kinmanta da night gawn ne ajikinki kiyi hak’uri kije kicanza kaya ai ba dad’ewa zaki yi ba”
Umar yafad’a,shuru tayi Tana nazari dan gani takeyi kamar idan tatafi wani abunne zekuma samunsa
Gefen fuskarta yashafa
“Tashi kinji nima kitaho min da kaya kala d’aya tunda nasan zuwa dare ko gobe dasafe zamukoma gidan gabad’aya”
Mik’ewa tayi badan ranta yasoba tana tafiya tana waigensa
Harta fice daga d’akin
Tunda suka shiga motar babu wanda yayi magana harsuka iso gidan
Sannan zayyad yace
“Nan da awa nawa zaki kammala abunda zakiyi”
“Minti talatin ma yayi yawa”
Zayyad yayi murmushi
“Kidai shirya atsanake nan da awa d’aya zandawo”
Tagyad’a mai kai kawai tare da ficewa daga motar yaja yawuce.
Tunda ta doshi k’ofar falon ta tsinci kanta da fad’uwar gaba
Tatsaya a bakin k’ofar tanajin kamar kartashiga amma babu yadda ta iya yazamarmata dole
Murd’a k’ofar tayi ahankali gabanta na fad’uwa
Saida tatsaya tana k’arema falon kallo kamar yaune tafara ganinsa sannan tashiga tamaida k’ofar tarufe
Ahankali tafara takawa zuwa step tafara hawa step d’in ahankali
Jitayi k’arar sawun tafiyar bibbiyu
Tad’an dakata da tafiyar tana kallon gefenta
Babu kowa azahiri amma tasan a bad’ini akwai wani awurin
K’arfin halin cigaba da tafiya tayi tashiga d’akinta
Tana tunanin abunda zata farayi,tana tsoron yin wanka gashi Kuma yazama dole
Ahankali tacire hijabi da rigar dake jikinta tashiga bayin
Bata tsaya sa ruwan zafi ba,nasanyi ta tatara cikin k’an k’anin lokaci tayi wankan daba ta da tabbacin tafita.
Ko mai bata tsaya shafawa ba ta sanya atamfa riga da skirt d’akinsa ta nufa dan d’auko masa kayan
Ta bud’e wardrobe tana tunanin kayan dazata d’auka
Shesshekar kuka tafaraji sama-sama
Tad’an dakata da abunda takeyi tana k’ara kasa kunne dan tabbatar da abunda taji
Sautin shesshekar kukanne yacigaba da k’aruwa kuma da dukkanin alamu daga bayi shesshekar yike futowa
Gabanta yacigaba da fad’uwa
Kayan tad’auka da sauri tafita daga d’akin
STORY CONTINUES BELOW
Ajiyar zuciya tasauke mai nawi tana hamdala da bataga abunda ke kukanba dan tabbata ba alkhairi bane
Saidai me kukan tak’ara ji anayi a falon dake k’asa
Fargaba da tsoro suka k’ara kamata, ahankali tafara saukowa daga step k’irjinta na dukan uku-uku
Harta gama saukowa can gefe tahango wata tsohuwa kwance tana d’ago mata hannu tana cigaba da kukan
Wani irin lugude k’irjinta yacigaba dayi tana jin zuciyarta na rawa kamar zata fito waje saboda tsananin tsoro
Tama rasa inda zatayi dan dole saitabi gaban tsohuwar kafin tafita waje ita kuma ba abun takoma sama ba taga abinda yafi wanda takegani ayanzu
Sautin kukan tsohuwar nafita tsigar jikin Rauda na tashi
Jikinta na rawa tafara tafiya tana nufar hanyar fita
Idanun tsohuwar akanta tana cigaba da kukan
Tazo saitinta da addu a abakinta tana shirin rugawa
Tsohuwar tatashi tazauna gashin kanta ya barbazu a ajikinta
Dukda akwai tazara atsakaninsu sosai amma hannu kawai tsohuwar tasa tajanyo wuyanta
Tsananin tashin hankali da tsorata Rauda tashiga,hannunta tasa ta na k’ok’orin b’an-b’are na tsohuwar amma takasa
Dan gam ya manne da wuyanta
Cikin wata kalar murya me tsoratarwa tsohuwar tace
“Babu inda zakije ki gujemana,duk inda kikaje muna tare dake”
Runtse ido Rauda tayi dan kallon fuskar tsohuwar na k’ara razanata
Jin shuru yasa tabud’e idanuwan a tsorace saidai wayam bataga kowa ba babu tsohuwar
Abun mamaki kuma ganinta tayi a d’akin umar gaban wardrobe d’insa
Ita da har tad’auki kayan tafita falo ya akayi kuma taganta a d’aki
Jikinta narawa tabaro d’akin tana k’ara kallon inda taga tsohuwar
Amma babu kowa awurin
Ficewa tayi dasauri tamaida k’ofar tarufe sannan ta jingina da k’ofar tana maida numfashi
Ahaka zayyad yadawo yatadda ta
Tana ganinsa ta taso tashiga motar dan jinta takeyi kamar akan k’aya take
Kallon ta zayyad yayi sosai take yafahimci firgici atare da ita hakan yasa shi tambayarta yace
“Rauda lafiya naganki atsorace haka?
Ta jinjina mai kai
“Lafiya”
Yagyad’a nashi kan yana cigaba da tuk’in
Suna isa asibitin ko parking begama yiba tafito
Dan gani takeyi kaman wani abu ya samu umar.
Da hanzari ta ke tafiya har ta isa d’akin
Ganin sa jingine yasa tasauke ajiyar zuciya
Kallonta yayi ganin yadda tashigo a hargitse
“Lafiya madam?
K’arasawa tayi bakin gadon saikuma ta fashe da kuka
Hannunta yakama yazaunar da ita kusa dashi yace
“Mekuma yafaru chuchu?
Cikin kuka tace
“Bazan iya cigaba da zama agidannan ba,bazan iya ba……
Ya sauke numfashi me nawi,tare da fara rarrashinta
“To shikenan, kukan ya isa haka,ya isa”
Yafad’a yana d’an bubbuga bayanta
STORY CONTINUES BELOW
Saida tadena kukan,sannan ya k’ara tambayar ta
“Mekika gani yau Kuma?
Ta fad’a Masa,yayi ajiyar zuciya yana nazarin abunda tafad’a mai sannan yace
“Inaganin gobe idan allah yakaimu mutafi katsinan kawai gurin malamin da zayyad yace”
Ta jinjina Kai kawai batare data k’ara cewa komai ba
Daddare tana zaune kusa dashi yafarayin bacci, itama gyan-gyad’i ne yafara d’aukanta
Taji ana k’wan-k’wasa k’ofar
Ta mik’e taje tabud’e
Doctor zayyad tagani,yace
“Yihakuri kinfara bacci natasheki ko?
Tayi d’an murmushi tace
“Aa babu komai”
Yagyad’a kai
“Dama akwai allurar daban masa bane saiyanzu na tuna shine nazo inmasa”
Tad’an kallesa tanacewa
“Ba d’azu kayimasa ba?
Ya d’aga kai alamar eh sannan yace
“Wannan watace daban”
Shuru tad’an yi daga bisani tabashi hanya tanacewa
“Gashi kuma yayi bacci natashesa kenan?
Ya girgiza Kai
“Aa basai kintashesa ba,ai allurar bata baya bace ahannu za aimasa”
Tace to tare da zama tana kallon Umar d’in
Yakama hannun yana tsira mai allurar
Kallonsa tayi sosai ganin ko jijiya be nema ba amma yanayin allura
“Doctor dama ana allura ba a nemi jijiya ba?
Be bata amsa ba yacigaba da abunda yikeyi
Jin yayi mata shuru yasa takuma cewa
“Doctor magana nikeyi fa”
Still banza yayi da ita,cikin idanuwansa takalla taga k’wayar idonsa golden
Azabure tamik’e lokacin yagama allurar yazare yana wani mugun murmushi
Dede lokacin Umar yafarka
Jikin Rauda na rawa tace
“Allurar me kamasa zayyad…
Kasa k’arasawa tayi yayinda ya kauda fuskar zayyad dayayi amfani da ita fuskarsa ta bayyana
Subiyun duka suka zaro ido suna kallonsa
“A..asim”
Tafad’a cikin rawar murya
Yashafa gefensa da hannunsa saiga wata kujera tabayyana
Yazauna har lokacin da murmushin mugunta a fuskarsa
Zatai magana ya katseta tahanyar cewa
“Kafin kitambayeni bari ni na baki amsa,danna san tambayar ki bazata wuce”allurar mekamasa ba”
To allura ce wacce ruwan dake cikinta yike d’auke da abubuwa da dama,zanfad’a miki kad’an daga ciki
Dafarko dai tana d’auke da guba wacce bata kisa amma tana shiga cikin k’ashi da b’argo da kuma jijiyoyin mutum,ta rink’a rugurguza k’ashi tana tsittsinka jijiyoyi,abu nabiyu shine takan saka mutum ya cutar da kanshi yanaji yanagani batare da ya iya hana kansa ba,
Sannan tana d’auke da abubuwan dasuke canza halittar d’an adam”
Yad’an dakata sannan yacigaba dacewa
“Wannan kyauta ce daga gareni,kuma kinsan makarin wannan guba??
Magani ko wani abu baze tab’a karyata ba face saki
Yafad’a yana maida kallonsa ga Umar sannan yacigaba
“Kaga saika zab’a,ko lafiyarka kokuma zama da matarka”
STORY CONTINUES BELOW
Umar yatashi daga kwanciyar dayayi daky’ar yana dubansa cikin dakewar zuciya yace
“Duk wad’annan abubuwan kanayine dan karabani da matata,to kasani inason matata fiye da yadda nike son kaina,kuma babu wata barazanarka da zata sani naji Tsoro
Sannan inaso kasani kalmar saki bazata tab’a fitowa daga bakina ba
Dariya Aasim yayi sosai sannan yace
“Banga laifinka ba dan kafad’i haka ayanzu,saboda allurata batadad’e da shiga jikinka ba,nabaka sati biyu kacal dakanka,dabakinka zaka furta “
Yamaida kallonsa kan Rauda
Yana cigaba da dariyan ya b’ace
Zubewa Rauda tayi tana fashewa da kuka
Umar yasauko ahankali ya durk’usa agabanta yanajin kukanta harcikin zuciyarsa
“Rauda kisani inasonki babu abunda zesani fargaba akanki,ko kad’an kalamansa basu dameni ba Dan nasan be isa yamin abunda allah be minba,ki kwantar da hankalinki babu abunda zesameni kinji?
Ta jinjina Kai kawai tanacigaba dayin kukan tarasa wannan wace irin Jarabawa ce take bibiyarta takuma kasa rabuwa da ita
Ya d’aga ta suka kwanta akan gadon asibitin yana cigaba da kwantar mata da hankali
Washegari, yafarka jikinsa da sauk’i,hakan yasa yace sukoma gida
Zayyad yad’auko su, yadawo dasu,suna shigowa motar anty kaltum nashigowa
Suka fito atare
Suka gaisheta ta amsa had’i da cewa
“Kukan lafiya nike ta kiran wayoyinku basa shiga?
Umar ne yabata amsa
” Wayoyinne suka samu matsala amma lafiya Lau”
Kallonsa anty kaltum tayi ganin yadda yarame
“Meyasameka naga kafad’a?
Zayyad yace
“Habadai anty idonki ne amma babu ramar dayayi”
Jinjina kai tayi amma bata yarda ba dan tafi kowa sanin k’anin nata
Rauda ce takatsemata tunanin da datakeyi tahanyar cewa
“Anty kaltum mushiga daga ciki Mana”
Anty kaltum ta girgiza Kai
“Aa, office zani dama nabiyo ne inga lafiyarku tunda kuma kuna lafiya shikenan”
Tafad’a idanuwanta akan umar tana k’ara yin nazarinsa
Umar yace
“To sister gobe zamuzo amana girki medad’i”
Gyad’a mai kai kawai tayi tashiga motarta ta tada
Suka sauke numfashi lokaci d’aya
Zayyad yace
“Ni zan tafi daddare zanbiyo in k’ara duba jikinnaka mukuma k’ara tattaunawa akan zuwa katsinan”
Umar yagyad’a kai tare dacewa
“Shikenan sai anjiman”
Suka shiga falon bayan wucewar zayyad
Zama sukayi na y’an mintoci sannan Rauda tace
“Mezan had’a maka na karyawa”
“Kisa ruwan zafi kawai musha tea”
Tace to tare da shiga kicin
Shiko kwantawa yayi yanajin jikinsa nayimasa wani iri, ya lumshe idanunsa cike da damuwa da fargaba
Ahaka ta gama had’a abun karin tasamesa,tadad’e tsaye akansa tana magana amma bejiba dan yalula cikin tunani
Saida ta tatab’asa sannan tad’anyi firgigit yana kallonta
“Lafiya?ko jikinne?
Tatambayesa
Yakakaro murmushi yana tashi daga kwanciyar dayayi
STORY CONTINUES BELOW
“Aa lafiya lau harkin kammala”
Tad’aga masa Kai alamar eh
Sunfara karyawan yana shan tea hannunsa rik’e da Kofi
Jikinsa yafara rawa,yanajin cikin naman jikinsa kamar ana huramai wuta
Aje kofin hannunta tayi dasauri tana dubansa tare da amsar kofin hannunsa
“Jaana,meke faruwa?
Kasa bata amsa yayi dan zafin cikin jikinsa dad’a k’aruwa yikeyi
Daky’ar ya iya furta
“D’auko min ruwan sanyi kizubamin ajikina”
Dasauri tamik’e tabud’e fridge tad’auko goran ruwan tafara shafamai ajiki
Amma kamar k’aramai zafin takeyi
Yadakatar da ita tahanyar cewa
‘barshi haka ya isa”
Aje goran tayi hankalinta atashe
Jiyayi hannunsa yafara wani irin ciwo yarike hannun dasauri yana ambaton sunan Allah
Saida yakusan awa d’aya ahaka sannan hannun yalafa,amma still zafin jikin yananan
Y’arfillo.
🌹 JINNUL
AASHIQUE🌹
🧞♂🧞♂
🧞♂
NA
HARIRA ALIYU (y’arfillo)🧕🏻✍✍✍✍✍✍✍
*GOLDEL PEN WRITER’S ASSOCIATION*
✍✍✍✍✍✍✍
❄_We are bearers of sooo golden a pen We write assidiously percieven no pain Sooo magical Our creative golden pen Be hold our words A product of our pen Savour our words, for it will cause you no pain_❄
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
Dedicated to Little hajjo and my elder sister Hafsat Aliyu
🅿AGE📕 9⃣
Ina bawa masoyana hak’uri abisa ga jimawa dani keyi ban yi posting ba,nima ba da son raina bane,bank’i ace kullum naturo muku ba amma uzururruka sunyi min yawa inafatan zaku amshi uzurina,kuma zanyi k’ok’ari insha allahu inga ina yin posting akan lokaci nagode da k’aunarku gareni da kuma jinnul aashique.
GAISUWA
Ga y’an uwana y’an Golden pen writters allah yak’ara mana dank’on zumunci
FATAN ALKHAIRI
Ga aminiyata AISHA A IBRAHIM allah yazab’a miki abinda yafi alkhairi a rayuwarki Amin.
Wannan page d’in sadaukarwa ne gareka jarumi sadauki,AASIM na sadaukar dashi gareka ranka shi dad’e allah yak’ara girma👍🏻
Bissmillahir rahmanin rahim
Duk iya k’ok’orin da umar yayi,wajen ganin ya b’oye yadda yikeji ajikinsa dan gudun kada hankalinta ya tashi,kasawa yayi saboda tunda yike a duniya betab’a jin irin yadda yike ji ahalin yanzu ba,iya kuma karatunsa na likita da yayi betab’a karo da wannan irin ciwon da yikeji ajikinsa ba bare yasan wani magani ko allura ze ma kansa yaji sassauci.
Yasa ta k’ure AC d’in falon,takuma kawo mai fankar k’asa,badda wacce take sama tanata nata aikin
Amma a banza,a memakon yaji sanyi-sanyi sai ma yikejin zafin nakuma k’aruwa.
“Chuchu”
Ya kira sunanta ahankali ganin yadda tashiga damuwa sosai
Ta zare hannunta daga tagumin da tayi tana amsawa
“Na’am”
“Please karki d’aga hankalinki,naji ma jikin yafara lafamin”
Yafad’a cikin son kwantar mata da hankali
STORY CONTINUES BELOW
Ta sauke ajiyar zuciya hmmmmm
“Taya hankalina baze tashi ba,bayan ina ganin ka cikin wannan halin?
Jaana ina jin tsoro,jikina na bani wani babban al’amari yana shirin faruwa damu,bana so wani abu yasameka”
Tak’ara sa fad’a idanuwanta na ciccikowa da hawaye
Yayi murmushin k’arfin Hali Yana kama hannunta yace
“Banaso kina fad’in haka,babu abunda ze samemu da izinin Allah,kinji?
Ta d’aga mai kai kawai amma ita jikinta ya gama yin sanyi
“Yauwa chuchu na,mik’omin wayata inkira zayyad”
Yafad’a
Ta mik’amai wayar,yadanna numban zayyad bugu biyu ya d’auka
Yace mai yazo yaduba shi,ga abunda yikeji
Ba a jima ba kuwa zayyad yadawo gidan,gwaje-gwaje yayi masa amma bega komai ba
Cikin mamaki yadubi Umar
“A bayanin dakamin nayimaka gwaji akan abunda nike tunani yana damunka amma banga komai ba”
Hmmmmmm umar yasauke numfashi
“Dama banyi tunanin zaka komai d’in ba……
Sai kuma ya dakata yana duban Rauda dan ba ya so yayi maganar agabanta
“Madam had’a min ruwan wanka”
Ta mik’e ta hau sama,ya maida kallonsa kan zayyad Yana cigaba da cewa
“Zayyad,zafin dani keji a jikina yawuce yadda zan kwatanta maka,jini keyi kamar ana huramin wuta acikin jikina”
Zayyad yasauke numfashi yace
“Wai to meke faruwa haka?
Umar ya zayyana mishi abunda yafaru daren jiya a asibiti,da allurar da Aasim yayi masa
Zayyad zaro ido yayi zuciyarsa cike da tsoro
“Yayi shigata yayimaka allura?nashiga uku nikuma me yasakoni a al’amarinsa?
Umar shuru yayi yana kallon zayyad
Zayyad ya ciga ba da cewa
“Amma wannan al’mari akwai rud’ani da rikitar wa wallahi,kace ciwon maka ba na asibiti bane”
Umar ya yi ajiyar zuciya me nawi
“Hmmmmmm zayyad al’amarinnan yafara bani tsoro,duk inda kake tunanin Aasim wallahi ya wuce Nan,ina fargaban abun da ze iya faruwa gaba”
Zayyad ya jinjina kai cike da tsananin mamaki danshi tunda yike aduniya betab’a jin makamancin al’amari irin wannan ba Koda kuwa a littafi ballan tana a zahiri
“Gaskiya dole musan abunyi,inaga mushirya mutafi katsinan yanzu kawai”
Umar ya girgiza Kai yace
“Allah bazan iya tafiya me nisa ba,idan ka rok’esa baze yarda a turamai kud’i yazo ba?
Zayyad yad’an yi shuru yana tunani sannan yace
“Babban malami ne gaskiya,kuma koda yaushe gidan shi cike yike taf da jama’a bana tunanin ze iya barinsu yazo,amma bari na kirasa naji”
Yak’arasa fad’a yana zaro wayarsa a aljihu
Ya danna numban malamin bugu biyu ya d’auka suka gaisa,zayyad yasanar dashi buk’tarsu akan yazo tare da rok’onsa daya taimaka
Yace ba matsala gobe da safe ze taho
Zayyad yayi mai godiya sannan ya kashe wayar yana kallon Umar yace
“Bari yaturo account numban sai inmai transfer”
Acan bedroom kuwa Rauda,
Ta gama had’a ruwan,zata fito kenan taji wani k’ara
STORY CONTINUES BELOW
Ta waiga da sauri tana kallon cikin bayin,ruwan data had’a acikin kwamin wanka ne taga yana ta zakud’owa kamar dakwai wani abu aciki
Ta rufe idanuwanta da sauri jin tsigar jikinta na tashi bakinta na ambaton sunan Allah
“RAUDA!
Taji ankira sunanta da wata kalar murya me tsoratarwa
Tabud’e idanuwanta da sauri tana kallon cikin ruwan inda taji ankira sunannata
Wani mutumi tagani d’an k’arami shi ba wada ba shi ba yayan wada ba,d’an siriri,fatar jikinsa wata kala kamar gansa kuka,koriya shataf,idanuwansa wasu kala kamar na mage
Futowa yayi daga cikin ruwan yana tahowa inda take
Jikinta na rawa ta murd’a k’ofar bayin zata fita amma gam k’ofar ta rufe
Addu’o i tacigaba dayi dasauri tana jijjiga k’ofar
Ganin ya iso gab da ita yasa tayi sarranda
Ta runtse idanuwanta kawai,jitayi an damk’i hannunta ta ware idanun tana k’wala ihu
“Bazamu tab’a rabuwa dake ba”
Taji yafad’a
Tare da kecewa da wata kalar dariya
Takuma k’wala ihun tare da zubewa a sume,
Umar nafalo, yajuyo ihunta, zayyad ya dubesa yana fad’in
“Kamar ihun Rauda ko?
Umar ya d’aga kai yana mik’ewa
“Bari Naduba Ina zuwa”
Yafad’a yana hayewa sama da sauri
A dur k’ushe yasameta,ya d’agata dasauri yana kiran sunanta
“Rauda!Rauda!
Amma shuru,d’aukota yayi ya yo falo da ita, zayyad na hangosa ya mik’e yanacewa
“Subhanallah me yasameta?
“Wallahi bansani ba”
Umar yafad’a yana shimfid’ar da ita a kan doguwar kujera
Yazauna gefenta yana d’an girgiza ta,yana cigaba da kiran sunanta
Zayyad da ke tsaye yad’auko ruwa agora ya mik’ama umar yana cewa
“Ina ganin suma tayi,yayyafa mata mugani”
Ya amsa ruwan ya yayyaffa Mata,ko minti biyu beyi da yayyafa mata ruwan ba,tafarfad’o tana sauke ajiyar zuciya me nawi
Lokaci d’aya ta bud’e idanuwanta ahankali harta gama bud’e su akansa
Ahankali k’wa-k’walwarta ta tariyo mata abunda tagani a bayi
Tashi tayi a zabure ta fad’a jikinsa tare da fashewa da kuka
“So sukeyi su kasheni,sunce bazasu tab’a rabuwa dani ba wayyoh allahna na shiga uku!
Umar yasauke numfashi zuciyarsa cike da tsananin damuwa,
Kasa cewa komai yayi,ya rungume ta kawai yana sauke numfashi ahankali
Zayyad yayi jugum Yana kallonsu gabad’aya tausayinsu yikeji,lokaci d’aya yanayinsu ya sauya daga farin ciki zuwa tashin hankali
Be bar gidan ba sai da aka kira sallar magriba
Suko suna falon har lokacin,ba maganar neman abinci dan babu me jin yunwa acikinsu
Zuwa can dai ya dubeta tana kwance akan k’afafunsa yayinda yike zaune kan doguwar kujera yace
“Mekike buk’atar kici insa me gadi ya siyo Miki?
Girgiza masa kai tayi tace
“Ni banajin yunwa”
“Nasan bakyaji ai,nima baji nike yi ba amma yazama dole munemi wani abu musa acikin mu dan zama da yunwar itama babbar matsalar ce”
STORY CONTINUES BELOW
Ta jinjina Kai
“Shikenan kasa yakawo koma miye”
Koda me gadin yasiyo kuwa,kad’an suka tsakura, suka gabatar da sallar magriba da issha,sannan suka kunna karatun qur’ani acikin a falon
A haka bacci ya d’auke Rauda,shiko umar ko kad’an be runtsa ba dan jikeyi kamar ana d’add’aure jijiyoyin jikinsa,ga zafin da yike ji Yana dad’a k’aruwa.
Sai wajen asuba Rauda ta farka,taga yadda ya had’a zufa
“Ba kayi bacci bane?
Ta tambayesa da damuwa a fuskarta
Ya girgiza Kai yana k’ok’orin b’oye yanayin da yikeji
“A a nayi Mana kiran sallar da akayi ne ya tasheni”
Hmmmmm tasauke numfashi
“To muje muyi alwala ko”
Suka mik’e atare,jiyayi k’afarsa ta rik’e tana mai zugi
Yad’an tsaya yana kallon k’afar,kallon Rauda tayi tace
“Lafiya?
Yad’an k’ak’aro murmushi
“K’afata ce ta rik’e ina ganin Dan na kwana a zaune ne shiyasa”
Cikin tausaya wa tace
“Meyasa baka tasheni ba to,dana kwanta akan k’afafunka?
Ya kuma yin murmushi
“Taya zan tasheki?zan iya kwana a tsaye ma inhar ke zakiyi baccin cikin kwan ciyar hankali”
Sonsa da k’aunarsa da kuma tausayinsa suka k’ara shiga cikin zuciyarta
Wasu siraran hawaye ne suka biyo kuncinta
Cikin damuwa yace
“Miye kuma na kuka chuchu”
Hannu tasa tashare hawayen tana cewa
“Tabbas samunka matsayin miji agareni,wani babban rabo ne daga ubangiji,na tabbata da bakai na aura ba da yanzu wanda na aura ya maidani gidanmu danna tabbata babu me iya zama dani da wannan lalurar atare Dani”
Tak’arasa fad’a wasu sabbin hawayen na gangarowa daga idanunta
Ajiyar zuciya yasauke tare da kama hannayenta yana kallon cikin idonta
“Rauda,allah yayi nine mijinki shiyasa ma ya k’addaro miki wannan al’amarin,dan Allah ki kwantar da hankalinki banaso inga damuwa a fuskarki,wallahi nikad’ai nasan yadda Nike Jin zuciyata idan naganki acikin damuwa”
Tayi murmushi still hawaye nabin fuskarta
“Zan rink’a b’oye wa dan kawai hankalin naka ya kwanta amma kasan damuwata bazata tab’a ciruwa ba face na rabu da matsalar dake tattare Dani”
Har lokacin hannayenta na rik’e cikin nasa
“Jikina nabani kinkusa rabuwa da wannan matsalar,ko ince munkusa rabuwa da ita,insha allahu muna gab da fita daga cikinta”
Ta gyad’a kai kawai dan ita tasan yanzu ma suka fara shiga cikin matsala
“To allah yasa”
Tafad’a,suka shiga cikin bedroom suka d’auro alwala
Shiya jasu sallar, Allah-allah yikeyi ya idar sabida zugin da k’afarsa keyi masa
A daddafe ya sallame sallar,ya mik’ar da k’afar yana mamakin zugin da k’afar ke masa
Jikinta yayi sanyi dan ta fahimci ba kwanan dayayi azaune bane yasa k’afar tasa haka,k’ila abunda ke shiga cikin jikinsa ne
“Jaana haryanzu k’afar bata dena ba ko?
K’ak’aro murmushi yayi yace
“Aa ta Dena,kawai dai na mik’ar da ita ne”
Ajiyar zuciya tayi tana girgiza Kai,batasan me yasa yike son b’oye mata halin da yike ciki ba
STORY CONTINUES BELOW
“Jaana dan allah kadena min irin haka, at least in kanajin abu kafad’a min ko kana da wacce tafi nine?
Nida bani da wanda yafika ai komai naji saina sanar dakai amma Kai……
Ya katseta
“Chuchu kinsani babu abunda zan b’oye Miki,k’afar ta Dena tund’azu”
Ta kauda kanta gefe gudun kada yaga hawayen da ke Shirin zubo Mata
“Chuchu”
Yakira sunanta,saida tashare hawayen sannan ta juyo tana amsawa
“Na’am”
“Zonan”
Yafad’a,ta taso tak’arso gabansa ta durk’usa
Janyota yayi ya rungume ta yana sauke wani numfashi me nawi
“Kizauna ajikina,ko zanji sanyi acikin zuciyata”
Yafad’a yanajin yanayin sa na k’ara canzawa,k’afa da zafin jikin nakuma addabarsa
Runtse idanuwanta tayi wasu sababbin hawayen na ambaliya a fuskarta
Yakuma matseta ajikinsa bakinsa na ambaton
“La’ila ha illa anta subhanaka inni kuntu minaz zalumin”
Ta bud’e jik’akk’un idanunta tana kallon yadda ya runtse idonsa alamar yana jin rad’ad’i
Addu’o i tafara tofa Masa, idanuwanta na fitar da hawayen tausayi da tsantsar damuwa
K’arfe tara tayima zayyad a Tasha,Dan malam aminu ya sanar dashi sunkusa isowa
Ko minti goma beyi da zuwa ba,motarsu ta tsaya
Yafito cikin manyan kayansa da nad’in rawani akansa
Dattijone kamilalle me cike da natsuwa,ya mik’ama zayyad hannu sukai musa baha suka gaisa,sannan suka shiga motar zayyad d’in
Bayan zayyad yatada motar yace
“Malan sannu da hanya,gaskiya kun iso da wuri motar tayi gudu”
Malan yace
“Ai da wuri nafito ina idar da sallah danma motar tad’an tsaya mana amma da mun iso tund’azu”
Zayyad ya jinjina kai yana cewa
“Allah sarki,kayi hak’uri fa malan,muntasoka mu yakamata ace munzo da kanmu amma halin da abokinnawa ke ciki yasa nace bari dai kazo d’in”
Malan yayi d’an murmushi
“Babu komai”
Tunda suka iso get d’in gidan malan aminu ya fahimci akwai gagarumar matsala acikin gidan
Hakan yasa ya umarci zayyad da ya dakata da shiga cikin gidan
Sai da yayi addu’o I sosai sannan yace zayyad ya shiga
Zayyad ya shiga yayi parking,sannan suka fito zayyad yafara knocking d’in falon
Har lokacin suna rungume da juna, bakinta kuma bedena karanto addu’o in ba
K’wan-k’wasa k’ofar da zayyad yayine yasa suka bud’e idanuwansu atare
Dede lokacin wayar Umar tafara k’ara ganin numban zayyad yasa yace
“Ina ganin zayyad ne,mukoma falon”
Suka mik’e sukayo falon yana d’an ciccije bakinsa dan ciwon dad’a k’aruwa yikeyi
Kan kujera ya zauna,Rauda ta bud’e k’ofar
Ta gaishe da su tana kallon malan aminu Wanda shima ita yazuba ma ido
Ta basu hanya suka shiga sannan ta maida k’ofar tarufe,takoma kusa da Umar tazauna
Yayinda suma suka zauna suna gaisawa da Umar d’in
STORY CONTINUES BELOW
Malan aminu yatashi ya dafa kan umar yana nazartar abunda ke damunsa
Ya girgiza kai fuskarsa d’auke da damuwa yana duban Rauda sannan itama ya dafa nata kan
Janye hannunsa yayi dasauri yana kallonta fuskarsa d’auke da tsantsar mamaki
A fili yace
“Aasim bin ramzad?
Yasauke numfashi Yana kuma girgiza kai cike da tarin fargaba
“La haula wala k’uwwata illah billah”
Malan aminu yafurta yana komawa kan kujerar ya zauna
Gabad’aya sun zuba mai ido suna jiran suji abunda zece
Ya sauke numfashi yana kallonsu
“Zahiri kuna cikin babbar matsala,domin kuna tare da rauhanin da ba kowani malami bane ze iya ja dashi”
Yad’an numfasa sannan yacigaba dacewa
“Amma nayi mamaki,Aasim bin ramzad rauhanine,kuma a iya sanina rauhanai basa cutarwa,wani laifi kuka masa haka da ya tunzurasa yike azabtar daku?
Ya k’arasa maganar Yana kallonsu sosai
Ganin basu bashi amsa ba yasa yacigaba da cewa
“Tabbas akwai laifin dakuka masa mai girma wanda ya tunzurasa ya canza daga ainihinsa,kuma ni tabbas bazan iya ja dashi ba amma zan iya nemansa inji dalili inkuma jaraba rok’onsa ko ze iya hak’ura”
Har lokacin babu wanda yayi magana kallonsa kawai sukeyi,umar ne yakatse shurun ta hanyar cewa
“Malan dan Allah kataimaka kayi iya abunda zaka iya, wallahi muna cikin damuwar da bazamu iya kwatanta maka ba”
Malan aminu yagyad’a kai yaciro wani turare a aljihunsa ya fesa sannan yafara karanto addu’o I da basajin me yake fad’a illa bakinsa da suke gani yana motsawa
Ahankali d’akin yafara duhu,saiga shi ya bayyana cikin ainihin suffarsa ta yarima
Malan aminu nagani,yazube a k’asa yana faman jera kirari
“Allah yataimaki yarima,me martaba d’an sarki,basarake me dubbannin dawakuna”
Fuskarnar tasa a tamke ya watsawa malan aminu razanannun idanunsa cikin b’acin rai yace
“Kai wanene,da har ka kai matsayin da zaka nemeni”
Bakin malan aminu na rawa yace
“Ka gafarceni ranka shidad’e,tuba nike allah ya huci zuciyarka”
Ya kad’a kai yana cewa
“Fad’i kiran me kakemini,meke tafe dakai,me Kuma yashigo dakai matsalar da babu ruwanka,shin kanaso rayuwarka ta salwanta ne?
Jikin malan aminu na kyar-kyarwa yace
“Tuba nike ranka shidad’e,amsa Kira na dakayi kad’ai ya isheni,bakuma nanemeka bane dan na Isa,illa Dan na rok’eka da ka sassauta ma wad’annan bayin allahn…..
Da wata kalar tsawa ya katsesa
“Kai!
Kashiga taitayinka,kakuma tuna da wanda kake magana,kai baka isa ka nemar musu afuwa ba,kuma hukuncine nariga da na yanke,mafita ta rage garesu”
Malan aminu bakinsa na rawa saboda kid’imar da yayi
Yace
“Kagafarceni tuba nike allah ya huci zuciyarka”
Aasim ya kalli Rauda da umar yana yimusu wani kallo da shi kad’ai yasan ma anarsa
“Nafad’a kuma zansake fad’a muku,ko ku rabu da juna kokuma daga yanzu kicigaba da fuskantar barazana,kuma gubata akullum k’ara ratsaka zatayi wallahi sai ka gwammace mutuwarka da halin da zaka shiga
Ke Kuma….yanuna Rauda sannan yacigaba da cewa
“Yanzu ne zaki fahimci ko ni waye dakuma matsayin da nike dashi”
STORY CONTINUES BELOW
Yana gama fad’ar haka yab’a ce
Nan danan haske ya gauraye falon ya dawo yadda yike
Gabad’aya malan aminu ya jik’e sharkaf da zufa,shiko zayyad harda fitsari ya saki saboda tsananin tsorata
Malan aminu yasauke doguwar ajiyar zuciya yace
“Agaskiya bazan iya ba,ku gafarceni amma ya wuce k’arfin da kuke tunani,bazan iya ba dan allah karku sake nemana dan rayuwata zata iya shiga cikin hatsari”
Yak’arasa fad’a yana mik’ewa ze fita
Zayyad na kiransa amma be tsaya sauraronsa ba ya k’arasa ficewa daga falon dan gabad’aya ya firgita
Rauda ta runtse idanuwanta cikin tashin hankali maganganun malan aminu nayimata yawo acikin kunnuwanta
“Aasim bin ramzad rauhanine kuma rauhanai basa cutarwa tabbas kunyi masa laifin dakuka tunzurasa wanda yasa ya canza daga ainihinsa”
Wasu hawaye ne masu zafi suka cigaba da gangaro mata
Ahankali ta furta
“Tabbas ban kyauta ba maka ba,amma ban cancanci wannan hukuncin daga gareka ba”
Wanene Aasim? Menene had’insa da Rauda? Me suka masa da ya canza sa daga ainihinsa?
Muhad’u a page 🔟 dan jin yadda zata cigaba da kasancewa taku a kullum
Y’arfillo.
JINNUL
AASHIQUE🌹
🧞♂🧞♂
🧞♂
NA
HARIRA ALIYU (y’arfillo)
✍✍✍✍✍✍✍
*GOLDEL PEN WRITER’S ASSOCIATION*
✍✍✍✍✍✍✍
❄_We are bearers of sooo golden a pen We write assidiously percieven no pain Sooo magical Our creative golden pen Be hold our words A product of our pen Savour our words, for it will cause you no pain_❄
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
Dedicated to little hajjo and my elder sister Hafsat aliyu
🅿AGE📕 1⃣1⃣
Wannan Page d’in nakune jinnul aashique group,ina me k’ara baku hak’uri akan rashin typing d’in da banayi dawuri.
Gaisuwa da fatan alkhairi ga
Safnah
Maman ummi
Maman khalifa
Maman Khadijaa
Allah yabar zumunci
11:06 🕐am. TUE,APR 16 ✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
Bissmillahir rahmanin rahim
Ya murd’a k’ofar falo,yana cewa
“Ina y’an gidannan suke,kufito ga matata na kawo muku”
Yafad’a cikin d’aga murya yana k’arasa shiga cikin falon
Wata kyakkyawar budurwa ta taso daga cikin falon dasauri tana fad’in
“Dagaske?tare kuke?
Bata hanya yayi yanacewa
“Gatanan kuwa kina gani”
Budurwar da bazata wuce sa’ar Raudan ba ta k’an-k’anme Raudan cikin farinciki da jin dad’in ganinta
“Oyoyo sister”
Harararta Aasim yayi
“Kinga nazma,saketa daga zuwanta ko hutawa batayi ba zaki wani ruk’ur-k’usheta salan ki gajiyar min da ita”
STORY CONTINUES BELOW
Nazma ta zame daga jikin Raudan tana dariya
“Afuwan d’an uwa, sister mu shiga kizauna”
Tak’arasa fad’a tana jan hannun Raudan zuwa cikin falon
Itadai Rauda butun butumi tazama,dan takasa cewa komai kallonsu kawai takeyi,ga kuma tambayar dake zuciyarta
Jin Aasim yakirata da matarshi,shida ko maganar soyayya bata tab’a shiga tsakanin su ba,miye na kiranta da matarshi?
Nazma ta zaunar da ita akan kujera tana cewa
“Mekikeson infara kawo Miki?gasashhiyar kaza,ko gasasshen rago? Talo-talo ko kayan ciki?
Aasim yadafa kansa cikin damuwa da surutun nazma
“Kinga fad’ama ammi tafito su gaisa sannan kizo kiyi shirmen naki”
Dariya nazman tayi tana wucewa
Rauda da batace komai ba har lokacin,ganin nazman ta wuce yasa takalli Aasim da sauri tace
“Ina Nan?
Gyara zama yayi yana bata amsa
“Gidan mu Mana”
Tasauke numfashi dansai lokacin hankalinta ya kwanta
“Shine baka fad’amin ba tuntuni?
Yad’aga gira
“To ba gashi yanzu nafad’a Miki ba”
Harararsa tayi tana kallon kayan jikinta
“Ai sai ka fad’amin tun a makaranta nan zamuzo inje incanza Kaya Amma……
Shigowar wata farar mata ya sa tayi shuru
Da ka kalli fuskarta ka kalli ta Aasim zaka gane itace mahaifiyar shi
Matar tazauna akan kujera idanuwanta akan Rauda
Rauda tazame k’asa tana gaisheta
Matar ta amsa fuskarta a sake tana cewa
“Koma kizauna y’ata”
Takoma ta zauna tana duban Aasim daya tashi daga kujerar ya koma wacce mahaifiyar sa take yazauna yana kama hannunta
“Ammi,nayi missing d’inki sosai”
Ammi tayi murmushi tana shafa kansa
“Nima haka,kana lafiya dai ko?
Ya girgiza kai
“Aa ammi”
Nan da nan ko yana yinta yasauya zuwa damuwa tafara tattab’a jikinsa alamun tana so ta ji zafin jikinsa
“Me ke damunka,ina kema ka ciwo”
Yayi dariya yana kama hannunta yana matsawa
“Kwantar da hankalinki ammi,lafiya ta k’alau”
Ta sauke ajiyar zuciya
“Harkasa hankalina ya tashi,katabbata babu abunda ke damunka?
Ya gyad’a kai yana murmushi
Rauda ko Sha’awa suka bata,dan dukkanin alamu akwai soyayya da shak’uwa me k’arfi a tsakaninsu
Dede lokacin nazma tadawo falon d’auke da wani fankacecen tire
Wanda yike shak’e da takarcen kayan ciye-ciye dana lashe-lashe
Aasim yarik’e baki ganin yadda tad’auko tiren da k’yar
“Nazma duk wad’annan kayan ina zaki kaisu?
“Na antyna ne,ita na kawo mawa”
Dariya sukayi gabad’aya,ammi tace
STORY CONTINUES BELOW
“To kai mata sashensa,dannasan nan bazata iya sakewa ta ci ba”
Nazma tace to tana juyawa
Ammi tace tana kallon Aasim
“Yaro tashi kakaita sashenka”
Wata yarinya da bazata wuce shekaru biyu da rabi ba,ta tashigo falon rik’e da k’atuwar y’ar baby
Tafad’a jikin Aasim cike da jin dad’in ganinsa
Shima cikin farinciki yad’agata yana juyi da ita
Suna ta dariya,sannan ya rungume ta yanacewa
“Ina kika je banganki ba tunda nazo sai yanzu”
“Nade tallon wuwa”
Tafad’a da maganarta ta yara da bata gama iyawa ba
Ya dire ta a k’asa yana yimata nuni da Rauda dabata lura da ita ba
Aiko tana ganinta ta ruga aguje tayi wajenta
Rauda tad’auketa tana kallon yarinyar,farace k’ar kamar lantarki, kyakkyawa,ga gashi da aka kama mata da rimbom wanda yasauka har gadon bayanta
Lokaci d’aya taji yarinyar ta shiga ranta,
“Miye sunanki?
Rauda ta tambayeta tana kallonta
Cikin gwalantonta yarinyar tace
“Tatida”
“Tatida? Rauda ta nanata
Ammi tayi dariya tare da cewa
“Shahida ta ke so tace”
Rauda ta gyad’a kai tana murmushi
“Shahida,shekaraki nawa?
Hannu shahida ta d’aga tana nuni da yatsunta guda uku
“Shekararki uku?
Rauda ta tambaya tana mamakin wayon yarinyarShahida ta d’aga Kai
Alamar eh
Ammi tace
“Kinga y’ata karki biye ma shirmen shahida,tashi kuje kisa wani abu acikinki”
Rauda tayi dariya,tana mik’ewa rik’e da shahidan a hannunta
Aasim yayi gaba tana binsa a baya,wani madai-dai cin falo suka shiga
Komai na falon kalar golden ne,kama daga kan kujeru,kafet,labulaye kai komai na d’akin kalar golden akayi ado dashi
Yayi Mata nuni da kujera
“Bissmillah,zauna”
Ta zauna hankalinta na kan shahida gabad’aya k’aunar yarinyar ya shiga zuciyarta
Ta rasa dalilin hakan
Ko dan tanason fararen yarane oho
Aasim ya matso da zagayayyen tebur d’in da nazma ta d’aura tiren akansa gabanta yana cewa
“Madam ajeta fa zakiyi kici abinci”
Tad’an kallesa gami da cewa
“Nifa banajin yunwa”
Komawa yayi kan kujera ya zauna yana dubanta
“Kedai kice ganin shahida ya k’osar dake,da alamu tashiga ranki ko?
Rauda ta jinjina kai tana murmushi
“Kabari kawai,dan Allah ina mamanta take?
In tambayeta ta bani ita”
Ya rausayar dakai yace yana mik’ewa yad’auki shahida
“Bari inkaita gurin ammi,dan ba barinki zatayi kici abincin ba”
“Please Aasim kabarta,zanci Allah”
STORY CONTINUES BELOW
Be saurareta ba ya sab’a shahida a kafad’a ya yi hanyar fita
Shihada na d’aga mata hannu alamar bye bye
Ajiyar zuciya Rauda tasauke,azuciyarta tana addu’ar allah yabata irin shahida
Bayan yafice tamaida kallonta ga tiren dake gabanta,babu abunda babu akai,nama,nono,abinci ma kala-kala gashinan tarkace wasu ma bata tab’a ganin kalar su ba
Takuma sauke ajiyar zuciya tana tambayar zuciyarta,haryaushe daga zuwanta aka shirya mata wad’annan abubuwan?
Tunda a fahimtar da tayi basuma san da zatazo ba
Shigowar sa ne ya katse mata tunanin data fara,
“Wai haryanzu baki fara cin komai ba?
Ya tambaya yana zama a gefenta dayike kujerar da take kai three seeter ce
Bata ce mai komai ba,ya d’auko wani juice ya tsiyaya mata kofi yana mik’a Mata
Numfashi ta sauke tana kiran sunansa
“Aasim!
Yad’ago suka had’a ido
Tayi k’ok’orin cigaba da kallon cikin idonsa
“Meyasa kace y’an gidan ku ga matarka ka kawo?idan suka d’auka dagaske muna soyayya fa?
Hmmmmm ya sauke guntun numfashi
“Meyasa kika tambayeni?ko laifine dan nafad’i hakan?
Ta d’aga kai alamar eh tana kurb’ar juice d’in da ya mik’omata
Sannan tace
“Kadube kanka da kyau,kaduba irin baiwar kyau da allah yayi maka,sannan ka kalli gidan ku
Tafad’a tana zagaye falon da idanuwanta sannan tacigaba da cewa
“Kai ba k’aramin mutum bane,tayaya zaka dangantani da matar ka,kadubeni da kyau,ni ba kyakkyawa bace kuma ni ba y’ar babban gida bace,shin baka tunanin zasuji badad’i ayayinda kafad’i hakan?
Tak’ara sa maganar tana kallonsa
“Ina sonki”
Taji yafad’a,tayi y’ar dariya
“Ni maganar gaskiya Nike maka, please ka aje maganar wasa”
“Ina sonki”
Ya kuma fad’a
Ta ajiye kofin tana tambayar sa
“Wai kasan mekake cewa kuwa?
Akaro na uku ya kuma mai-maita wa
“Ina sonki”
Ta kallesa sosai tana nanata abunda yace
“Kana Sona?
Zamewa yayi daga kan kujeran yana kama hannunta
“Ina sonki Rauda,ina k’aunarki kece farin cikina”
Sororo tayi tana kallonsa tana kuma mamakin sa
Ya cigaba da cewa
“Meyasa baki fahimci cewa ina sonki ba tuntuni?
Ya kamata ace kin fahimci inasonki ko ta irin kallon da nike miki”
Ta zame hannunta daga rik’on da yayi mata tace
“Dan allah kabar maganar Nan, kaima kasan ba abu me yuwuwa bane”
“Miyene baze yuwu ba Rauda?
Ya tambaya da alamar damuwa a fuskarsa
Tasauke ajiyar zuciya tare da cewa
“Wai tayaya ma soyayya zata yuwu a tsakanina da Kai?
Nida kai sam ba mu dace da juna ba”
Mik’ewa yayi yana kama hannunta
“Tashi muje,infad’a agaban ammi,kisan cewa da gaske nikeyi”
Fizge hannunta tayi da sauri
STORY CONTINUES BELOW
“K’afad’a agaban ammi?dan allah karufamin asiri,ni muje ma ka maidani makaranta”
Tafad’a cikin zaro ido
Ya koma ya zauna yana sauke numfashi
“Shikenan,amma ki yarda ina sonki dagaske,dan Allah”
Dawowar nazma falon yasa suka bar zancen
“Haba antyna, kamar baki ci komai bafa nike gani”
Nazma tafad’a yayinda tak’ara sa shigowa falon
Rauda ta yi murmushi tace
“A k’oshe nike shiyasa”
Nazma ta gyad’a kai cikin nuna rashin jindad’i
“Shikenan Amma zan tattara miki su kitafi dasu,kuma dan Allah karkice aa”
Rauda ta gyad’a kai har lokacin da ragowar murmushi a fuskarta
“To shikenan nagode”
Ta k’arasa fad’a tana mik’ewa
“Muje kamaidani banaso dare yamin awaje”
Tafad’a tana kallon Aasim
Bece k’ala ba ya mik’e yana d’aukar wayoyinsa ya zuba su a aljihu
Yayi gaba,yayinda suka jera ita da nazma
Babban falo suka dawo,inda ammi take
“Badai har zaki tafi ba?
Ammi ta tambaya yayinda taga fitowarsu
Rauda ta durk’usa cikin girmamawa tace
“Eh zantafi,banaso nayi dare ne”
Ammi ta jinjina Kai
“Eh kinada gaskiya,jirani to inazuwa”
Tafad’a tana mik’ewa
Batafi minti biyar ba tadawo rik’e da k’atuwar leda
Tamik’a ma Aasim tace
“Gashi kasa mata amota,y’ata sai yaushe zamu sake ganinki?
“Insha’allah idan na samu lokaci”
“To shikenan nagode kinji”
Sukai sallama,Rauda na dube-duben inda zata hango shahida
Sai da suka fito zasu shiga mota,sannan ta hangota
“Shahida”
Ta kira sunanta,aiko tana jiyo kiran ta rugo a guje
Rauda tad’auketa tana cewa
“Ina ta nemanki muyi sallama ashe kina waje”
“Tafiya da tiyi?
Shahida ta tambaya tana kallonta
Rauda tad’aga kai alamar eh
Aiko Sai tayi narai-narai da ido zatayi kuka
Cikin d’an mamaki Rauda tace
“Shahida,baki so intafi ne?
Tad’aga kai alamar eh batason tatafi
Rauda tayi murmushi soyayyar yarinyar nak’ara shiga zuciyarta
“Karki damu zandawo nan bada jimawa ba”
Shahida ta girgiza Kai alamar bata yadda ba
“Nide kan titafi”
Rauda tayi shuru tana kallon ta sosai hakanan take jin zuciyarta wani iri,dan ita kanta bata son rabuwa da yarinyar
Aasim dake tsaye yana kallonsu ya mik’oma shahida hannu alamar tazo
STORY CONTINUES BELOW
“Shahida zo inkai ki gurin ammi kinji,nan da kwana biyu zanzo inkaiki gurinta kinji?
Ta mik’a mai nata hannun yad’auketa
Yace
“Yauwa Small habibty”
Wata kyakkyawar mata da bazata wuce shekara talatin ba tak’araso wurin
Suka gaisa da Rauda sannan ta amshi shahida a hannun Aasim ta juya
Basu dena kallon juna ba ita da shahida har saida matar ta sha kwanar falon
Rauda ta sauke ajiyar zuciya me nawi tana maida kallonta ga Aasim
“Wannan itace mamar shahida?
Aasim ya girgiza kai yace
“Aa me kula da itace”
“To ina mamarta take”
Be bata amsa ba ya zagaya ya bud’e motar ya shiga
Itama shiga tayi tana nanata tambayar ta
“Nace ina mamar shahidar fa?
Yatada motar yana cewa
“Meyasa kike tambaya akanta?
“Saboda kawai inaso inganta,dan ta iya haihuwa data haifo kyakkyawar yarinya irin haka,allah zuciyata ta kamu da son yarinyar”
Ya jinjina kai
“To nikuma fa?
Takallesa tace
“Kai kuma me?
“Zuciyarki bata kamu da sona ba?
Ta jingina da kujerar motar tana bashi amsa
“Dan Allah ka ajiye maganar wasa”
Ya jinjina kai yace.
“To shikenan tunda soyayya kin mai data wasa bari inyi miki ta gaske
Zaki aure ni?
“Miye?
Tatambaya tana d’an zaro ido
Yace
“To kince maganar soyayya wasace,aure kuma ai shi gaske ne ko?shine nace zaki aureni?
“Dan Allah ka rufamin asiri”
Tafad’a
Ya k’ara gudun motar yana cewa.
‘kamarya in rufa miki asiri?
Ta gyara zama tana dubansa
“In aureka?cap ai tsoratani zaka rink’ayi idan dare yayi”
Yayi dariya har fararen hak’oransa suka bayyana
“Nidai nace ina sonki,kisoni ko karki soni wannan matsalar ki,danni soyayya dake ba gudu ba ja da baya”
Dariya ta kuma yi
“Allah Aasim bazan iya soyayya dakai ba,kafi k’arfina Allah”
Ya tab’e baki
“Nagaya miki wannan matsalar kice,amma ni inkinga na ja da baya to nadena numfashi ne Allah”
Dariya tayi tana girgiza kai batare da tak’ara cemai komai ba
Ana kiraye-kirayen sallar magriba suka koma makarantar
Bayan tafito, yafito mata da k’atuwar ledar da ammi tabata ya mik’ama ta
“Masoyiya gashi”
Harararsa tayi
“Wacece masoyiyar taka?
“Ke Mana,kodayike matata yakamata ince tunda baki san kalmar wasa”
Yafad’a cikin tsokana yana gimtse dariya
Itama dariyar tayi ta amshi ledar tana juyawa
“Nagode saida safe”
Murmushi kawai yayi,saida tad’an yi nisa sannan yace da k’arfi
“I love you habibty”
Wai gowa tayi dasauri tana kallon mutanen dake kai da komowa
STORY CONTINUES BELOW
Ze kuma magana tayi mai nuni da yayi hak’uri dan tasan ba k’aramin aikin d’alubai bane su taru suna kallonsu
Murmushi yayi yana kuma fad’a k’asa-k’asa yadda motsin bakinsa kawai ta hango
Ta maida mai martanin murmushin tana juyawa da sauri
Tana shiga d’akinsu ta tadda salma na ta patrol a d’akin da alamu hankalinta atashe yike
Rauda na ganin haka ta rungume ta tabaya tana fad’in
“K’awalliya romon jab’a,nasan duk rashin ganina ne yasa aketa patrol,to gani na dawo”
Salma ta galla mata harara tana k’wace jikinta
“Sakeni ni,kinsa hankalina yatashi yadda y’an kidnapping d’innan sukayi yawa gabana nata fad’uwa,ina fargaban ko su sukayi awon gaba dake…..
Dariya Rauda tayi sosai,ta zauna gefen gado tana kallon salmar
“To da ba sai ki saido gonar ki kibiya a sakoni ba”
Salma takuma galla mata harara tace
“Wace gona?ai nairata baza tayi ciwon kai ba”
Dariya Rauda takuma yi
“Amma ai idonki ze yi ko,dannasan idan kika dunga rusa kuka sai hawayenki sun k’are”
Tsaki salma taja, tabud’e tukunyar girkin da take yi batare da ta sake kula ta ba
Rauda ta taso daga gefen gadon ta dawo kusa da ita ta zauna
“Kinga k’awata,kiyi hak’uri,wallahi ina fitowa daga lectures Aasim yajani wai muje yawo”
Salma tad’ago tana kallonta
“Yawo Kuma?kuma kika bishi,allah Rauda kiyi hankali da Aasim d’innan,dan wallahi y’ay’an masu kud’i ba kirki garesu ba”
Rauda ta girgiza kai had’i da cewa
“Aa shi ba haka yike ba,ba yadda kike tunani bane,gidan su yakaini,gidan iyayenshi kinga ma abunda mahaifiyar sa tabani”
Tak’arasa fad’a tana janyo ledar,tafito da kayan dake ciki
Atamfofi ne masu tsada guda uku,sai less da doguwar jallabiya,sannan turarruka da kayan kwalliya
Salma ta saki baki tana d’aga kayan
“Daga zuwa gaisheta shine ta baki wannan uban kayan”
Rauda ta jinjina kai tare da cewa
“Wallahi k’awa bakiga kirkin mutanen ba,yadda suke da kud’i da kyau,saiki rantse zasuyi wulak’anci
Amma sam abunda suke dashi be rufe musu ido ba,baki ga yadda suka tarbeni ba,kuma ma kinsan me?
Salma ta girgiza kai
“Inafa na sani ai sai kin fad’a”
“Wai cewa yayi yana Sona”
Rauda tafad’a
Salma ta zaro ido tace
“Wa? Aasim d’in?
Rauda tad’aga mata kai alamar eh
“Babbar magana,to ke mekika ce Masa?
Rauda ta mik’e tace
“Me ko zance masa,ce masa nayi ni bazan iya soyayya dashi ba dan sam bamu dace da juna ba”
Salma ta jinjina kai gami dacewa
“Gaskiya Kam,amma kuma da baki cemai haka ba k’ila rabon jindad’i ne ke kiranmu”
Girgiza Kai Rauda tayi tana dariya tashige toilet dan d’auro alwala
Da daddare,tana kwance bacci yakasa d’aukar ta,hakanan take jin zuciyarta cikin farinciki mussaman idan ta tuno maganganun sa
STORY CONTINUES BELOW
Ta duba agogo k’arfe d’aya saura
Gyara kwanciyar ta tayi tana rufe ido da niyyar bacci
Saidai a memakon baccin yad’auketa, zuciyarta ce ta hasko mata kyakkyawar fuskarsa alokacin da yike dariya
Ta matse filon dake hannunta a k’irjinta, ahankali bakinta ya furta
“Please zuciya ta kada kifara son Aasim, Aasim yafi k’arfinki ta ko ina ba sa’an ki bane please”
Wayarta ce tayi k’ara alamar shigowar message
Tajanyo wayar ta bud’e
Ganin numban Aasim yasa tayi saurin bud’e wa k’irjinta na d’an bugawa
“Amincin Allah ya tabbata ga tauraruwa ma’abociyar haske da k’yal-k’yali, hak’ik’a a yau dana bayyana miki sirrin dana dad’e ina b’oyewa acikin zuciyata,
Naji kaman na sauke wani nawi da ya rataya a kaina,bazan iya kwatanta miki irin k’aunar da nikeyi miki ba
Ina sonki habibty!
Murmushi tayi tana jin wani farinciki na ratsa zuciyarta ajiye wayar tayi tana lumshe idanuwanta
Wani bacci medad’i yad’auketa
Washegari bata da lectures,hakan yasa suka kwashi kayan su dayayi datti suka fara wanki
Suna cikin wankin kira yashigo wayarta,salma dake kusa da wayar tad’auka zata mik’o mata
“Aje ta mugama kawai”
Salma takalleta tace
“Aasim ne fa”
Rauda ta jinjina kai
“Nasani ai”
Salma ta ce
“Ya akayi kikasani bayan baki duba wayar ba?
Murmushi tayi tana bata amsa
“Saboda gabana yafad’i lokacin da kiran yashigo”
Salma ta rik’e baki
“Kai Rauda badai har kinfara sonshi ba?
Rauda ta girgiza kai
“Allah bawai yau kad’ai ba,tun farkon had’uwarmu,indai kiransa zeshigo wayata to sai naji gabana yafad’i
Haka ma ko ganinsa nayi”
Salma ta matse kayan dake hannunta tana cewa
“Kedai kice kinfara sonsa kawai”
Ganin bata yadda da abunda tace ba yasa tabar zancen
Bayan wata d’aya
Soyayya me k’arfi tashiga tsakaninta da Aasim tayadda inbata ji muryarsa ko ta gansa ba, bata jin dad’i sai taji gabad’aya ta rasa sukuni
Duk yadda tayi da karta sa soyayyar sa aranta kasawa tayi dan shi d’in na dabanne
Arana sai yakirata fin sau goma,kuma duk sanda yakira da irin zafafan kalaman da yike fad’a Mata masu matuk’ar rikita mata zuciya
Kamar kullum tana mak’ale da waya a kunnenta suna fira
Tace
“Ni fa yunwa nike ji kuma yau batajin cin abinci wallahi”
Daga can b’angaren yace
“To mekike son ci habibty, fad’a min ko menene shi zan nemomiki shi”
Ta girgiza kai kamar yana ganinta
“Dambu nike son ci kuma babu inda zaka samo dambu”
“Ina zuwa”
Kawai yace ya kashe wayar
STORY CONTINUES BELOW
Bayan minti talatin sai gashi yakuma kira tana d’auka
Yace
“Kifito ina wajen hostel”
Tace to,tana ajiye wayar
Kasancewar ana sanyi a lokacin rigar sanyi kawai tad’aura akan doguwar rigar dake jikinta
Tafito,yana tsaye ya jingina da wata bishiya
Tayi mai sallama ya amsa yana sakar mata murmushi me cike da so da k’auna
Ya mik’o mata ledar dake hannunsa yana cewa.
“Amsa maza kije kici,banason kirink’a zama da yunwa”
Amsa tayi tana tambayar sa
“Menene aciki?
“Ba dambu kikace kinason ci ba? shine aciki”
Kallonsa tayi da d’an mamaki
“Habadai?
Ya jinjina kai
“To kiduba kigani Mana”
Tako bud’e ledar ta duba take away d’in da yike ciki
Dambunne kuwa yaji zogale,sai zuba k’amshin man k’uli yikeyi
Mamakine ya kamata
“A ina kasamo dambu a darennan?
Yayi murmushi
“Kedai ba cine naki ba?dan haka kije kici”
Ta girgiza kai tace
“Aa saikafad’amin inda kasamo shi,dan a iya sanina ba inda ake saida dambu anan kusa-kusa kai ko da ranane
Ballantana da daddare, please kafad’a min”
Hak’ik’a naji dad’in comments d’inku,ina kuma k’ara godiya a gareku yawan comments d’in ku shike k’ara k’arfafamin gwiwa Page 12 yana zuwa insha Allah,taku akullum
Yarfillo.
🌹 JINNUL
AASHIQUE🌹
🧞♂ 🧞♂
🧞♂
NA
HARIRA ALIYU (y’arfillo)
Dedicated to Little hajjo and my elder sister Hafsat aliyu
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~*
*~❄We beare’s of soon golden We writer’s assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
🅿AGE📕 1⃣2⃣
Wannan Page d’in nakine mamana,allah ya k’ara miki lafiya yasa kaffarane, ina k’aunarki araina domin kin kasance uwa tagari me share min kuka na a kodayaushe.🥰
NA KASA MANTAWA DAKE😭
Dede da rana d’aya, kodayaushe cikin tuna ki nikeyi, hak’ik’a nayi babban rashi da na rasaki,y’ar uwata hajara aliyu allah Nike rok’o ya jik’anki da rahama,ya gafarta Miki,yasa aljannah ce makomarki Amin😭😭😭
8:57🕐am. SUN,APR 21✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
Bissmillahir rahmanin rahimYa sauke numfashi idanuwansa na kanta,yace
“Akwai wani sabon restaurant da aka bud’e babu kalar abincin gargajiyan da basa saidawa,kuma har dare suna kaiwa,anan na siyo”
Ta jinjina Kai
Ya cigaba da cewa
“Sannan dakike cewe a iya sanin ki babu inda ake saidawa a kusa -kusannan yawo kike yi? Keda sai kiyi sati ma wani zubin baki lek’a ko wajen makaranta ba”
STORY CONTINUES BELOW
Tayi dariya tana gyad’a Kai
“Hakane,to nagode allah ya k’ara bud’i “
Ya amsa da Amin
Taja iska alamar sanyi na ratsa jikinta sosai tana tana mammatse jikinta da yike rawa kad’an saboda sanyin dake kad’ata
“Wai shin kai baka jin sanyi ne?
Ya bata amsa
“Me kikagani?
Rauda tace
“Gani nayi bakasa rigan sanyi ba,kuma ko rawar sanyi bakayi”
Aasim yayi murmushi
“Kafinnazo nan inajin sanyi sosai,amma ina had’a ido dake,sai naji wani d’umi na ratsani, gabad’aya sai naji sanyin ya tafi”
Tayi dariya tana girgiza Kai
“Kai ko?
Shima dariyar yayi yana kwai-kwayar yadda take magana
“Ni me nayi?
Dariya takuma yi sosai tace
“Allah har fargaban ayi hutu nikeyi,saboda zanyi missing d’inka,da dariyar da kake sani,tunda nahad’u dakai ka kawarda duk wata damuwata kasanya ma zuciyata farin ciki ina godiya sosai”
Murmushi yayi me cike da abubuwa da yawa
“Kin can-canci komai habibty,zan iya yimiki komai,sannan zan iya yin komai akanki”
Itama murmushin takeyi
“Dagaske?zaka iya yin komai akaina?
Ya jinjina kai
“Dagaske habibty,zan iya bada rayuwata akanki”
Wata sassanyar ajiyar zuciya tasauke,tana jin wani farinciki na ratsa illahirin zuciyarta
Ta d’aga kai tana kallon saman bishiyar wacce iska ke kad’a ganyayyakinta,suna kad’awa ahankali
“Bansan meyasa kake sona ba,duk da nasan matsayina be kai ace ka soni ba”
Yad’an matso gab da ita suna kallon juna
Yace
“Nima kaina bansan meyasa ba,abu d’aya ne nasani na kuma yarda dashi,shine allah ne ya jarabceni da k’aunarki,habibty bazan iya rayuwa idan babu keba,kuma kada kiyi tunanin nafad’a mikine dan kawai soyayya
Wallahi dagaske nikeyi,ina k’aunar ki”
Ta kuma sauke ajiyar zuciya da yin shuru na y’an sakwanni sannan tace
“Nima ina sonka Aasim,kuma insha allahu zan rayu tare da Kai,dannasan zan rayu cikin farin ciki idan na kasance tare da Kai”
Aasim yayi murmushi da alamu maganar da ta fad’a tayi masa dad’i sosai
“Nagode habibty,bari nabarki kikoma ciki,tunda sanyin na damunki”
Ta gyad’a kai tace
“Shikenan nagode, Saida safe”
“To sai da safe”
Tafad’a tana juyawa,harta d’an yi nisa tajuyo
Yana tsaye inda tabarsa yana kallonta
Tace
“Yadai da magana ne indawo?
Ya girgiza kai yace
“Aa,kawai inaso inga shigarki ne tukunna sai inwuce”
Ta gyad’a Kai tana murmushi
Sannan taci gaba da tafiya
“Rauda!
Ya Kira sunanta,ta waigo tana kallonsa batare da ta amsa ba
“Ina sonki”
Yafad’a,takuma yin murmushi tare da juyawa dasauri,tashige ciki
STORY CONTINUES BELOW
Koda ta koma d’aki, murmushi be bar fuskarta ba,taci dambun sosai tasha Lipton sannan ta kwanta zuciyarta cike da tunaninsa
Washe gariDa wuri ta shirya zuwa lectures,tana tafiya tana tunanin meyasa be kirata ba yau,dan kullum da asuba sai ya kirata,shike tashin su sallah,
Haka ma idan gari yayi haske sai ya kirata yace ta tashi ta shirya
Ta ciro wayarta ta latsa numbansa taji a kashe
Ta maida wayar jaka taciga ba da tafiya
Wunin ranar wayar sa bata shiga ba,data kira sai taji a kashe
Tashiga damuwa sosai,dan bata tab’a kiran wayarsa taji a kashe ba
Har ta koma hostel, tana k’ara trying d’in kiran
Amma still a kashe
Ta yada jakar ta a k’asa tana zubewa a kan katifa
Salma dake zaune ta kalleta tana cewa
“Yadai?duk gajiyar ce?
Ta d’aga kai alamar eh tare da cewa
“Da gajiyar da kuma damuwa”
Salma tace
“Damuwa Kuma? Tamece?
Ta sauke numfashi tana tashi tazauna
“Yau tun safe Nike kiran wayar Aasim a kashe,shine duk hankalina ya tashi wallahi,dan bantab’a kiransa naji irin haka ba”
Salma ta jinjina kai
“Gaskiya dole kishiga damuwa,to ko wayar tasa ta fad’i ne?
“Nima nayi tunanin hakan,amma kuma da fad’uwa wayar tayi,da yazo yafad’a min kuma da na gansa acikin makaranta,amma fa banga alamunsa ba,har inda yasaba tsayawa naje bangansa ba, shiyasa nike tunanin ba lafiya ba”
Salma ta jinjina kai
“Gaskiya, to amma kik’ara gwadawa anjima insha’allah zata shiga,k’ila abubuwane suka mai yawa ya kashe”
Rauda tayi shuru kawai dan ita zuciyarta tafi bata ba lafiya ba
Daren ranar batayi wani baccin kirki ba,washegari ma haka takira wayar yafi sau d’ari amma abu d’aya ake gaya mata,akashe
Hankalinta ya tashi sosai,ko abinci takasa ci,bata tab’a sanin tana k’aunar sa ba sai a lokacin
Ahaka aka kwashe kwana uku, lokacin tagama jigata da rashin sa
Hakan yasa bayan tafito daga lectures tayanke shawarar zuwa department d’insu ta tambaya
Suka ci karo da salma ita ma tafito daga nata lectures d’in
“Yadai Rauda ina zakije?
Salma ta tambaya,
“Zan lek’a b’angaren su Aasim ne intambaya nagaji da zama cikin rashin sanin wani Hali yike ciki”
Salma ta jinjina Kai
“To muje inrakaki nima abun nadamuna wallahi”
Suka jera suka tafi,da isarsu suka tadda d’alubai na zaune suyi group-group sunata fira da shewa da alamu sunfito daga lectures ne,wasu kuma suna ta bitar karatu
Wani matashi suka gani a zaune shikad’ai da handout a hannunsa
Suka k’arasa gurin suka mai sallama
Ya amsa fuskarsa a sake suka gaisa,sannan Rauda tace
“Dan allah ina tambayar Aasim ne,kwana biyu bana ganinsa bansani ba ko lafiya?
“Aasim?
Matashin ya tambaya, Rauda ta d’aga kai tana fad’in
“Eh “
Yace
“Gaskiya bangane shi ba saidai ku tambayi wancan shine yike da list sunayen gabad’aya kuma shi ze iya saninshi,amma ni ba lallai insanshi ba saboda muna da yawa”
STORY CONTINUES BELOW
Yak’arasa fad’a yanayimata nuni da wani
Rauda ta jinjina kai
“Hakane,nagode sai anjima”
Tafad’a sannan suka k’arasa gurin wanda ya nuna musu suka mai sallama
Sannan suka tambayeshi
Shima mai-maita sunan yayi
“Aasim, Aasim,anya anan department d’in kuwa?Ta d’aga kai
“Eh”
Yad’an yi shuru yana nazari sannan yace
“Gaskiya bangane shi ba,abokina ko kasan me suna irin haka haka?
Yak’arasa fad’a yana kallon wanda yike kusa da shi
Shima girgiza kai yayi alamar be sani ba
Wanda suka fara tambayar yace
“To gaskiya bamu san wani me suna haka ba,sai dai inba a department d’inmu yike ba”
Rauda ta girgiza kai tace
“Anan fa yace yike,yananan zaka ganshi wani fari dogo haka”
Ya ajiye numfashi yace
“Nafad’a miki bansanshi ba gaskiya”
Ta gyad’a kai cike da damuwa a cikin zuciyata
“Shikenan nagode,mutafi Salma”
Suka juyo jiki babu k’wari
Salma tace
“To ya akayi haka Rauda?ni al’amarinnan yafara d’aure min kai fa,ace a department d’insu babu wanda yasansa?
Rauda ta sauke numfashi me nawi batare da ta ce komai ba, Dan gabad’aya jikinta yayi sanyi
Wata mota ce tasha gabansu,cikin b’acin rai salma Tafara fad’a
“Wannan wani irin wulak’anci ne zaka wani…….
Kasa k’arsawa tayi yayinda ya sauke Glass d’in motar
Rauda ko kanta na k’asa ko kallon motar batayi ba dan damuwar dake zuciyarta nema takeyi tafi k’arfinta
“Habibty…
Taji anfad’a, dasauri tad’ago kanta,suka had’a ido
Ya sakar mata lallausan murmushi
“Habibty,bazaki amsa kiran nawa bane,duk fushi dani d’inne ya jawo haka?
A memakon tabashi amsa,sai kawai idanunta suka cicciko da k’walla
Nan da nan hawaye yafara wanke mata fuska
Dasauri ya bud’e marfin motar,yafito yana fad’in
“Subhanallah,kuka habibty,me yake faruwa?
Ya tambaya hankalinsa a tashe
Ji tayi k’afafunta suna neman kasa d’aukarta,hakan yasa ta durk’usa tana cigaba da yin kukan
“Habibty please kiyi hak’uri,tashi kishiga mota, banaso hankalin mutane ya dawo kanki”
Kasa mik’ewa tayi saida Salma ta kamata tukunna,sannan tashiga motar
Salma tawuce tabarsu,itako Rauda kifa kanta tayi agaban motar tana cigaba da yin kukan da ta rasa ko na menene
Ya sauke numfashi yana cewa
“Dan girman Allah habibty,ki wa girman allah kiyi shuru,wallahi kukanki sosamin zuciya yike yi”
D’agowa tayi tana kallonsa da jik’akk’un idanunta
“Inyi shuru fa kace?kasa nashiga tashin hankali da tsananin damuwa,ina fargaban ko ba lafiya kake ba,inata fargaban ko wani abune ya sameka,ashe lafiyar ka k’alau…..
STORY CONTINUES BELOW
“Please kiyi hak’uri nasan nayi kuskure, Amma ba wai da niyya nai hakan ba,tafiya ce takamani kuma cikin gaggawa……
“Okay idan tafiya takamaka baka iya sanar min kafin katafi?
Ta katseshi,ya girgiza kai yace
“Naso insanar dake kafin intafi amma saboda yadda tafiyar tazo min bansamu daman kiranki ba”
“To dakaje fa,meyasa baka kirani ba?
Ta kuma tambaya still idanuwanta na kansa
Ya bata amsa da yanayin damuwa a fuskarsa
“Habibty inda naje waya bata shiga shiyasa”
Jingina tayi da kujerar motar batare da ta k’ara cewa komai baYa matso kusa da ita yana cigaba da cewa
“Abunda natsana a duniya shine inga hawaye a fuskarki, narok’eki habibty, ki tsayar da hawayennan haka”
Banza tayi dashi,ya gyad’a kai yana cewa
“To shikenan cikin biyu yanzu dole za ayi d’aya
Ko ki tsayar da hawayennan,ko kuma ki juyo da fuskar yana zubowa ina lashewa”
Harara ta galla Masa,yayi dariya yana kama kunnuwansa
“Please habibty I’m sorry”
Yadda ya lank’wasa muryar tasa taso tasata dariya
Ta share hawayen tana fuskantarsa,
“Dan Allah karka k’ara yimin irin haka,bakasan halin da na shigaba wallahi nikad’ai nasan tashin hankalin dana shiga”
Tafad’a cikin marai-raice fuska
Ya jinjina kai
“Shikenan, insha’allah bazan sake ba,kin hak’ura yanzu?
Ta d’aga kai alamar eh
Yayi murmushi
“Yauwa tawan Allah yabar minke,yanzu fad’amin ina kikeso muje,gurin shan ice cream,gurin cin tantabara ko gurin saida dambu?
Dariya tayi had’i da fad’in
“Sai dai gurin saida fate”
Shima dariyar yayi yana tada motar
Ita ko Rauda zuba mai fararen idanuwanta tayi tana sauke ajiyar zuciya
“Zahiri tana sonsa acikin zuciyarta, Wanda bata tab’a tunanin zata k’ara sa wani d’a namiji a cikin zuciyarta ba
Dan gabad’aya a rayuwarta ta tsani soyayya,takuma yi alk’awarin bazata sake yinta ba
Sai gashi Aasim ya canza mata tunani yasa ta k’ara komawa soyayya
Ajiyar zuciya ta sauke me nawi
Aasim ya juyo yad’an kalleta sannan yamaida kallonsa ga titi yace
“Yadai habibty,wannan ajiyar zuciya haka?
Ta kuma sauke wata a karo nabiyu sannan tace
“Aasim kasa na karya alk’awarin dana d’aukar ma kaina,na bazan sake yin soyayya ba,gashi yanzu zuciyata tagama amincewa dakai
Inada wata kalar zuciya da bata iya yin soyayya ba,idan harna fara son mutum to gabad’aya hankalina gushewa yikeyi
Dan allah kada kayi amfani da son danike maka,ka wahalar min da zuciyata,nasha wuya a baya banaso nasake mai-maita wa”
Ta k’arasa maganar idanuwanta na ciccikowa da hawaye
Da alamu jikinsa yayi sanyi da jin magan-ganunta
“Insha’allah habibty,bazan zama mesaki damuwa ba,abu d’aya nike so agareki…
Yad’an dakata, Rauda ko kallonsa takeyi
STORY CONTINUES BELOW
Yavcigaba da cewa
“Inaso kiyimin alk’awarin ko da nan gaba kin gano wani abu da baki san da shi ba a tare Dani,to kiyi min alk’awari bazaki rabu dani ba,ba kuma zaki dena sona ba, sannan kuma zaki gafarceni abisa b’oye mikin da nayi”
Kallonsa takeyi cikin rashin fahimta dan gabad’aya bata fahimci inda maganarsa ta dosa ba
“Bangane ba,dama kana b’oye min wani abu ne?to meyasa?kuma menene shi?
Yayi murmushin da ya tsaya masa iya labb’a kawai
“Lokaci na zuwa,da nasan dole zaki gane gaskiya,aduk lokacin dana tuna hakan sai inji hankalina ya tashi dan bansan wani hukunci zaki d’auka a lokacin ba”
Ta sauke guntun numfashi tace.
“To wai miye kake b’oyemin ne?
Sai kuma ta dakata alamar ta tuna wani abu, tacigaba da cewa
“Owo nafahimta,kana da aure ne ko?kana da mata shine ka b’oye kak’i fad’amin ko?
Ya murmushi yana girgiza kai
“Aa,wallahi bayan ke bani da wata Mata”
Tabud’e idanunta tana masa wani kallo
“Eyen,ni d’in ko?to yaushe na zama matarka?
Yad’an yi jim kaman ya naso ya tuna
“Eh to,kaman shekaru hud’u da suka wuce”
“Kai lokacin ma ko sanina kayi,duka-duka ko rabin shekara ma munyi da had’uwa ne?
Tafad’a tana k’walalomai ido
Yayi dariya yace
“Agurinki kenan amma ni agurina had’uwarmu tun bayan shekara ashirin ne?
Ta kuma bud’e idanuwanta sosai
“Kai, lokacin ma ko haihuwata anyi?ohhh na tuna anhaifeni lokacin kenan tun ina jaririya ko?
Ta tambayesa cikin yi galala da baki
Dariya yayi Yana paka motar a harabar gurin saida Ice cream
“Kinga habibty muje musiyo muyi mu koma,yanzu aka kirani akafad’a min muna da meeting”
Tace to,harzata bud’e motar kuma sai takoma tazauna
“Kace yanzu aka kiraka?da wace wayar to ince ga wayarnan a ajiye,kuma ni tunda nashigo motarnan banji ankirata ba?
Yayi k’ok’orin tsaida natsuwarsa guri d’aya yace
“D’azu nike son ince”
Gyad’a kai tayi tana tab’e baki
“Ook muje”
Basu wani b’ata lokaci ba,suna shiga tazab’i kalar ice cream d’in datake so suka fito
Bayan yatada motar sunfara tafiya tace
“Namanta ban tambayi shahida ba,tana lafiya? Ya ammi da nazma?
“Duk sunanan k’alau”
Yabata amsa a tak’aice
Gudu yayi sosai saboda meeting d’in da yace suna dashi
Yana ajiyeta ya juyaDa daddare bayan tayi shirin kwanciya,ta kira wayarsa,tagama ringing be d’auka ba
Tana ajiye wayar message na shigowa ta bud’e
“Habibty bamu gama meeting d’inba haryanzu,ki kwanta kiyi bacci ina sonki”
Murmushi tayi tare da rungume wayar a k’irjinta baccin da batayi kwana biyu ba kuwa yad’auketa
Bayan sati d’aya, hankalinta ya kwanta,dan suna tare soyayyar su nadad’a yin k’arfi
STORY CONTINUES BELOW
Ranar wata laraba,tashirya dan zuwa gurin saloon,dama sunyi dashi intaje shi zeje yad’aukota
Saboda yace yana da meeting a lokacin
Hakan yasa tafito bakin titi ta tari adai-daita sahu
Sun d’an yi nisa kad’an wata kyakkyawar budurwa ta tsaida a dai-daitan da Rauda ke ciki
Da sallama tashiga, Rauda ta amsa suka gaisa
Napep d’in tacigaba da tafiya
Budurwar da tashi ga napep d’in tace
“Rauda ko?
Da mamaki Rauda ta kalleta jin takira sunanta
“Eh itace”
Budurwar tayi murmushi
“Ni kuma saima”
Rauda tak’ara kallonta, bata tab’a ganinta ba,to a ina tasan ta?har tasan sunanta?
Saima ta katse mata tunanin da takeyi
“Kinyi mamakin kiran sunanki da nayi ko?
Rauda ta d’aga Kai
“Eh gaskiya danni bansanki ba,to ko makarantar mu kike?
Saima ta girgiza kai alamar aa
“Ba a makarantar ku nike ba malama Rauda”
Rauda ta jinjina Kai
“To ya akayi kikasan sunana?
Saima ta kuma yin murmushi,sunan ki ai sananne awurina,ke bama nikad’ai ba gabad’aya ahalina,babu wanda be sanki ba”
Mamaki yakuma kama Rauda
“Ahalinki? bangane ba”
Saima ta d’aga kai tace
“Eh,amma bawannan surutun ya kawoni ba,meyasa zuciyarki take saurin amincewa da mutane?
Baki san akwai wasu jinsi dazasu iya biyowa ta suffar mutane su cutar dake ba?
Cikin raahin fahimta Rauda ke kallonta amma takasa K’ara cewa komai
Dan ji tayi tsigar jikinta tafara tashi
Saima takuma yin murmushi,tana cigaba da cewa
“Ya kamata dai kirink’a ban-bance jinsin mutum da kuma na aljani,domin yana tare dake akodayaushe
Nabarki lafiya”
Tana gama fad’ar haka ta dire ko cewa me napep d’in ya tsaya batayi ba
Rauda tsoro ne yakamata, jikinta yayi sanyi sosai
Dede lokacin me napep d’in yatsaya a k’ofar shagon saloon d’in
Taciro kud’insa tabasa, dasauri tashiga shagon tazauna tana maida numfashi
Me saloon d’in me suna Amira tace
“Yadai customer?lafiya naganki wani iri?
Rauda ta girgiza Kai
“Aa bakomai”
Amma cikin zuciyarta mamaki da kuma al’ajabin saima ne,me take nufi da yakamata ta rink’a ban-bance jinsin mutum da na aljani?
Domin yana tare da ita a kodayaushe?
Maganar Amira ce ta katse mata tunanin data tafi
“Me za’amiki, retouching ko steaming?
“Steaming”
Tabata amsa a tak’aice
Har aka kammala mata bata dawo cikin natsuwarta ba,juyayin abunda yafaru kawai takeyi
STORY CONTINUES BELOW
Tana zaune ana taje mata kai, Aasim yayi sallama dayike yasan wurin ya tab’a kawota
Amira ce ta amsa tana bashi izinin shiga
Yashiga shagon da murmushi a fuskarsa yana kallon gashin kanta da yayi bak’i sid’ik yana ta shek’i
“Wow habibty kinga yadda gashin yayi kyau kuwa?
Amira tayi dariya tana fad’in
“Sai ka biyani da yawa”
Ya rausayar da Kai yace
“Baki da matsala, tunda kina gyara min matata”
Murmushi Rauda jeyi
“Ai nayi zaton bazaka zo ba”
Ya girgiza Kai yace
“Haba nina Isa?muna gama meeting d’in nan nayo direct”
Ta jinjina Kai tana janyo d’an kwalinta zata d’aura gaban makeken madubin da ke manne a bango
Gabanta ne yafad’i Ras, yayinda ta ga Aasim sanye da wasu kaya irin na sarakai ta cikin madubin kuma yayi wani bau farinsa da kyansa ya ninka wanda tasani
Tayi gaggawar kallonsa a fili
Yana tsaye yana bawa amira kud’i sanye da k’anan Kaya
Ta murza idanuwanta dasauri tana ganin kaman gizo idanun ke mata
Takuma kallon madubin, still da kayan sarautar ta k’ara ganinsa
Maganar saima ce tadawo Mata, gabanta yayi wani mugun fad’uwa
Tayi saurin kauda kanta a madubin ganin madubin yafara yimata dishi-dishi
Kallonta yayi yace
“Yadai naganki a daburce meyafaru?
Ta girgiza kai dasauri batare da tace komai ba
Amira tace
“Nima dai yau tunda tashigo haka naganta”
Yakuma kallonta sosai
“Habibty,lafiya?meke faruwa”
Kuma girgiza kai tayi alamar babu komai
Ya jinjina kai amma be yadda babu komai d’in ba
“Shikenan muje”
Yayi gaba yana yiwa amira sallama
Bin bayansa tayi da kallo gabanta na fad’uwa
Yad’an waigo yana dubanta ganin tana tsaye bata da niyyar tafiya
“Yadai,ko baki gama bane”
Ta girgiza kai tana d’aga k’afarta datayi mata nawi a tafito
Yabud’e mata motar tashiga,sannan ya shiga ya tada
Yana cewa
“Kifad’a min meke faruwa,ni nasan akwai wani abu hakanan dai bazan ganki a daburce ba”
Tayi k’arfin halin danne tarin fargaban da yike zuciyarta
“Aasim,intambaye ka zaka fad’amin gaskiya”
Ya kalleta
“Eh zanfad’a miki indai nasani”
Ta jinjina Kai tace
“Aasim kai mutum ne?
Ta jeho mai tambayar da be shirya jinta ba
“Eyeh,mene?mekika ce?
Yafad’a cikin sark’ewar murya
“Nace kai mutum ne?
Yayi shuru na y’an sakwanni sannan yace
STORY CONTINUES BELOW
“Me yasa kika yimin wannan tambayar?
Ta gyad’a kai fad’uwar gabanta na dad’a tsananta
“Akwai abunda nagani da nakasa fahimta, please k’afad’a min gaskiya kai mutum ne?
Ya sauke numfashi tare da cewa
“Eh ni mutum ne”
Girgiza kai tayi cikin rashin yadda
“Banyadda ba,idan kai mutum ne ya akayi siffarka,da kayan jikinka suka sauya acikin madubi?
Ya taka burki da sauri yana kallonta
“Suffata Kuma,ayaushe?saidai in gizo idanun ki suka Miki”
Ta gyad’a kai tana zage jakar ta ta ciro reza ta bud’e tare da sawa akan yatsanta ta danna
Sai ga jini b’ul-b’ul,
“Miye haka habibty,yanka kanki kikayi fa?
Yafad’a dasauri,ta jinjina
” kai nasani ai,kai ma inaso ka yanki yatsanka,saboda in tabbatar da abunda nike zargi”
Girgiza kai yayi
“Habibty baki yadda dani bane?
“Ko na yarda dakai inaso inga jini a jikinka,idan har kasan abunda kafad’a min gaskiya ne to ka amsa kayi abunda nace”
Tafad’a cikin wani irin yanayi na tashin hankali
“Habibty..,.
Katseshi tayi ta hanyar kama hannunsa zata danna rezar
Yayi saurin rik’e hannunta da d’ayan hannunsa
Sai dai ina,kafin yayi wani yunk’uri ta yanke sa
A memakon taga jini,wani kalar abu taga yana fitowa kore shataf
Ja baya tayi dasauri, k’irjinta yayi wani mugun bugawa
Hannunta tasa akai,ta k’wala ihu
Yayi saurin matsowa yana fad’in
“Habibty narok’eki ki kwantar da hankalinki”
K’ok’arin bud’e motar tafarayi da sauri amma Gam,tak’i bud’ewa
Tafara jijjigata da k’arfi tana cigaba da yin ihu
Ya k’ara matsowa yana kiran sunanta
Ganin k’ofar bata da alamun bud’ewa yasa ta juyo tana kallonsa tare da had’e hannun ta guri d’aya cikin kuka da tsananin firgici tace
“Narok’eka kada ka cutar Dani,kayi hak’uri idan laifi nemaka”
Hannunta yakama zeyi magana,ta fizge hannun da sauri
“Kada katab’ani kayiwa Allah kabud’emin infita”
Ajiyar zuciya yasauke tare dacewa
“Kiyi hak’uri ki fahimceni,ki natsu dan Allah”
“Nidai kabud’emin infita,karabu dani kayi hak’uri,kar ka cutar Dani wallahi banyi ma komai ba……
Tsawa ya daka mata
“Nace ki natsu ko!!!!!!
Shurun ko tayi dan tsawar ta k’ara razana ta, kyar-kyarwa kawai takeyi kamar anciro ta da ga cikin k’an-k’ara
Aasim ya cigaba da cewa
“Inda zan cutar dake da tuni na cutar dake,kinsan adadin shekarun da nayi ina tare ke ne?
Da zan cutar dake da tuni ban cutar dake ba,ko kinga al’amarin cutarwa a tare Dani?
Yafad’a cikin yanayin damuwa
STORY CONTINUES BELOW
Sannan ya sassauta murya
“Kiyi hak’uri na d’aga miki murya,amma dan allah ki kwantar da hankalinki,
Tunda Kingane gaskiya ai dole zanyi miki bayani”
Ta jinjina Kai tana kallonsa,ayanzu tsoron yafara raguwa dan ko tafahimci ba cutar da ita d’in zeyi ba
Ya numfasa sannan yace
“Ayanzu babu abunda zan b’oye Miki,
Zanyi miki bayanin komai,kuma inaso ki saurareni da kunnen basira
Ki kuma fahimci bayanin da zanyi miki kinji?
Tad’aga kai alamar taji
Yacigaba da cewa
“Ni ba mutum bane,kuma ni ba aljani bane amma ni rauhani ne,
Kamar yadda kikasani sunana Aasim, Aasim bin ramzad,
Mahaifina shine sarki ramzad dake mulkar masarautar rauhanai
Kuma ni mijinki ne,inada aure dake tun shekaru hud’u da suka wuce,sannan har da y’a a tsakanina dake”
Zaro ido tayi tana kallonsa
“Aure,harda y’a?kuma Dani?
Tafad’a cikin rawar murya da kuma mamaki
Ya jinjina Kai
“Eh Rauda,shahida da kika gani y’arki ce kece mahaifiyar ta”
Ta kuma zaro ido tana kallonsa
Yacigaba dacewa
“Zanyi miki bayanin ko ni waye,da kuma yadda akai na aure ki har kika haihu batare da kinsani ba”
🙎🏻
Typing dakwai wahala Allah, muhad’u a Page 13
Yarfillo.🌹 JINNUL
AASHIQUE🌹
🧞♂ 🧞♂
🧞♂
NA
HARIRA ALIYU (y’arfillo)
Dedicated to Little hajjo and my elder sister Hafsat aliyu
🅿AGE📕 1⃣2⃣
Wannan Page d’in nakine mamana,allah ya k’ara miki lafiya yasa kaffarane, ina k’aunarki araina domin kin kasance uwa tagari me share min kuka na a kodayaushe.🥰
NA KASA MANTAWA DAKE😭
Dede da rana d’aya, kodayaushe cikin tuna ki nikeyi, hak’ik’a nayi babban rashi da na rasaki,y’ar uwata hajara aliyu allah Nike rok’o ya jik’anki da rahama,ya gafarta Miki,yasa aljannah ce makomarki Amin😭😭😭
8:57🕐am. SUN,APR 21✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
Bissmillahir rahmanin rahimYa sauke numfashi idanuwansa na kanta,yace
“Akwai wani sabon restaurant da aka bud’e babu kalar abincin gargajiyan da basa saidawa,kuma har dare suna kaiwa,anan na siyo”
Ta jinjina Kai
Ya cigaba da cewa
“Sannan dakike cewe a iya sanin ki babu inda ake saidawa a kusa -kusannan yawo kike yi? Keda sai kiyi sati ma wani zubin baki lek’a ko wajen makaranta ba”
Tayi dariya tana gyad’a Kai
“Hakane,to nagode allah ya k’ara bud’i “
Ya amsa da Amin
Taja iska alamar sanyi na ratsa jikinta sosai tana tana mammatse jikinta da yike rawa kad’an saboda sanyin dake kad’ata
“Wai shin kai baka jin sanyi ne?
STORY CONTINUES BELOW
Ya bata amsa
“Me kikagani?
Rauda tace
“Gani nayi bakasa rigan sanyi ba,kuma ko rawar sanyi bakayi”
Aasim yayi murmushi
“Kafinnazo nan inajin sanyi sosai,amma ina had’a ido dake,sai naji wani d’umi na ratsani, gabad’aya sai naji sanyin ya tafi”
Tayi dariya tana girgiza Kai
“Kai ko?
Shima dariyar yayi yana kwai-kwayar yadda take magana
“Ni me nayi?
Dariya takuma yi sosai tace
“Allah har fargaban ayi hutu nikeyi,saboda zanyi missing d’inka,da dariyar da kake sani,tunda nahad’u dakai ka kawarda duk wata damuwata kasanya ma zuciyata farin ciki ina godiya sosai”
Murmushi yayi me cike da abubuwa da yawa
“Kin can-canci komai habibty,zan iya yimiki komai,sannan zan iya yin komai akanki”
Itama murmushin takeyi
“Dagaske?zaka iya yin komai akaina?
Ya jinjina kai
“Dagaske habibty,zan iya bada rayuwata akanki”
Wata sassanyar ajiyar zuciya tasauke,tana jin wani farinciki na ratsa illahirin zuciyarta
Ta d’aga kai tana kallon saman bishiyar wacce iska ke kad’a ganyayyakinta,suna kad’awa ahankali
“Bansan meyasa kake sona ba,duk da nasan matsayina be kai ace ka soni ba”
Yad’an matso gab da ita suna kallon juna
Yace
“Nima kaina bansan meyasa ba,abu d’aya ne nasani na kuma yarda dashi,shine allah ne ya jarabceni da k’aunarki,habibty bazan iya rayuwa idan babu keba,kuma kada kiyi tunanin nafad’a mikine dan kawai soyayya
Wallahi dagaske nikeyi,ina k’aunar ki”
Ta kuma sauke ajiyar zuciya da yin shuru na y’an sakwanni sannan tace
“Nima ina sonka Aasim,kuma insha allahu zan rayu tare da Kai,dannasan zan rayu cikin farin ciki idan na kasance tare da Kai”
Aasim yayi murmushi da alamu maganar da ta fad’a tayi masa dad’i sosai
“Nagode habibty,bari nabarki kikoma ciki,tunda sanyin na damunki”
Ta gyad’a kai tace
“Shikenan nagode, Saida safe”
“To sai da safe”
Tafad’a tana juyawa,harta d’an yi nisa tajuyo
Yana tsaye inda tabarsa yana kallonta
Tace
“Yadai da magana ne indawo?
Ya girgiza kai yace
“Aa,kawai inaso inga shigarki ne tukunna sai inwuce”
Ta gyad’a Kai tana murmushi
Sannan taci gaba da tafiya
“Rauda!
Ya Kira sunanta,ta waigo tana kallonsa batare da ta amsa ba
“Ina sonki”
Yafad’a,takuma yin murmushi tare da juyawa dasauri,tashige ciki
Koda ta koma d’aki, murmushi be bar fuskarta ba,taci dambun sosai tasha Lipton sannan ta kwanta zuciyarta cike da tunaninsa
Washe gariDa wuri ta shirya zuwa lectures,tana tafiya tana tunanin meyasa be kirata ba yau,dan kullum da asuba sai ya kirata,shike tashin su sallah,
Haka ma idan gari yayi haske sai ya kirata yace ta tashi ta shirya
Ta ciro wayarta ta latsa numbansa taji a kashe
STORY CONTINUES BELOW
Ta maida wayar jaka taciga ba da tafiya
Wunin ranar wayar sa bata shiga ba,data kira sai taji a kashe
Tashiga damuwa sosai,dan bata tab’a kiran wayarsa taji a kashe ba
Har ta koma hostel, tana k’ara trying d’in kiran
Amma still a kashe
Ta yada jakar ta a k’asa tana zubewa a kan katifa
Salma dake zaune ta kalleta tana cewa
“Yadai?duk gajiyar ce?
Ta d’aga kai alamar eh tare da cewa
“Da gajiyar da kuma damuwa”
Salma tace
“Damuwa Kuma? Tamece?
Ta sauke numfashi tana tashi tazauna
“Yau tun safe Nike kiran wayar Aasim a kashe,shine duk hankalina ya tashi wallahi,dan bantab’a kiransa naji irin haka ba”
Salma ta jinjina kai
“Gaskiya dole kishiga damuwa,to ko wayar tasa ta fad’i ne?
“Nima nayi tunanin hakan,amma kuma da fad’uwa wayar tayi,da yazo yafad’a min kuma da na gansa acikin makaranta,amma fa banga alamunsa ba,har inda yasaba tsayawa naje bangansa ba, shiyasa nike tunanin ba lafiya ba”
Salma ta jinjina kai
“Gaskiya, to amma kik’ara gwadawa anjima insha’allah zata shiga,k’ila abubuwane suka mai yawa ya kashe”
Rauda tayi shuru kawai dan ita zuciyarta tafi bata ba lafiya ba
Daren ranar batayi wani baccin kirki ba,washegari ma haka takira wayar yafi sau d’ari amma abu d’aya ake gaya mata,akashe
Hankalinta ya tashi sosai,ko abinci takasa ci,bata tab’a sanin tana k’aunar sa ba sai a lokacin
Ahaka aka kwashe kwana uku, lokacin tagama jigata da rashin sa
Hakan yasa bayan tafito daga lectures tayanke shawarar zuwa department d’insu ta tambaya
Suka ci karo da salma ita ma tafito daga nata lectures d’in
“Yadai Rauda ina zakije?
Salma ta tambaya,
“Zan lek’a b’angaren su Aasim ne intambaya nagaji da zama cikin rashin sanin wani Hali yike ciki”
Salma ta jinjina Kai
“To muje inrakaki nima abun nadamuna wallahi”
Suka jera suka tafi,da isarsu suka tadda d’alubai na zaune suyi group-group sunata fira da shewa da alamu sunfito daga lectures ne,wasu kuma suna ta bitar karatu
Wani matashi suka gani a zaune shikad’ai da handout a hannunsa
Suka k’arasa gurin suka mai sallama
Ya amsa fuskarsa a sake suka gaisa,sannan Rauda tace
“Dan allah ina tambayar Aasim ne,kwana biyu bana ganinsa bansani ba ko lafiya?
“Aasim?
Matashin ya tambaya, Rauda ta d’aga kai tana fad’in
“Eh “
Yace
“Gaskiya bangane shi ba saidai ku tambayi wancan shine yike da list sunayen gabad’aya kuma shi ze iya saninshi,amma ni ba lallai insanshi ba saboda muna da yawa”
Yak’arasa fad’a yanayimata nuni da wani
Rauda ta jinjina kai
“Hakane,nagode sai anjima”
Tafad’a sannan suka k’arasa gurin wanda ya nuna musu suka mai sallama
Sannan suka tambayeshi
Shima mai-maita sunan yayi
“Aasim, Aasim,anya anan department d’in kuwa?Ta d’aga kai
“Eh”
STORY CONTINUES BELOW
Yad’an yi shuru yana nazari sannan yace
“Gaskiya bangane shi ba,abokina ko kasan me suna irin haka haka?
Yak’arasa fad’a yana kallon wanda yike kusa da shi
Shima girgiza kai yayi alamar be sani ba
Wanda suka fara tambayar yace
“To gaskiya bamu san wani me suna haka ba,sai dai inba a department d’inmu yike ba”
Rauda ta girgiza kai tace
“Anan fa yace yike,yananan zaka ganshi wani fari dogo haka”
Ya ajiye numfashi yace
“Nafad’a miki bansanshi ba gaskiya”
Ta gyad’a kai cike da damuwa a cikin zuciyata
“Shikenan nagode,mutafi Salma”
Suka juyo jiki babu k’wari
Salma tace
“To ya akayi haka Rauda?ni al’amarinnan yafara d’aure min kai fa,ace a department d’insu babu wanda yasansa?
Rauda ta sauke numfashi me nawi batare da ta ce komai ba, Dan gabad’aya jikinta yayi sanyi
Wata mota ce tasha gabansu,cikin b’acin rai salma Tafara fad’a
“Wannan wani irin wulak’anci ne zaka wani…….
Kasa k’arsawa tayi yayinda ya sauke Glass d’in motar
Rauda ko kanta na k’asa ko kallon motar batayi ba dan damuwar dake zuciyarta nema takeyi tafi k’arfinta
“Habibty…
Taji anfad’a, dasauri tad’ago kanta,suka had’a ido
Ya sakar mata lallausan murmushi
“Habibty,bazaki amsa kiran nawa bane,duk fushi dani d’inne ya jawo haka?
A memakon tabashi amsa,sai kawai idanunta suka cicciko da k’walla
Nan da nan hawaye yafara wanke mata fuska
Dasauri ya bud’e marfin motar,yafito yana fad’in
“Subhanallah,kuka habibty,me yake faruwa?
Ya tambaya hankalinsa a tashe
Ji tayi k’afafunta suna neman kasa d’aukarta,hakan yasa ta durk’usa tana cigaba da yin kukan
“Habibty please kiyi hak’uri,tashi kishiga mota, banaso hankalin mutane ya dawo kanki”
Kasa mik’ewa tayi saida Salma ta kamata tukunna,sannan tashiga motar
Salma tawuce tabarsu,itako Rauda kifa kanta tayi agaban motar tana cigaba da yin kukan da ta rasa ko na menene
Ya sauke numfashi yana cewa
“Dan girman Allah habibty,ki wa girman allah kiyi shuru,wallahi kukanki sosamin zuciya yike yi”
D’agowa tayi tana kallonsa da jik’akk’un idanunta
“Inyi shuru fa kace?kasa nashiga tashin hankali da tsananin damuwa,ina fargaban ko ba lafiya kake ba,inata fargaban ko wani abune ya sameka,ashe lafiyar ka k’alau…..
“Please kiyi hak’uri nasan nayi kuskure, Amma ba wai da niyya nai hakan ba,tafiya ce takamani kuma cikin gaggawa……
“Okay idan tafiya takamaka baka iya sanar min kafin katafi?
Ta katseshi,ya girgiza kai yace
“Naso insanar dake kafin intafi amma saboda yadda tafiyar tazo min bansamu daman kiranki ba”
“To dakaje fa,meyasa baka kirani ba?
Ta kuma tambaya still idanuwanta na kansa
Ya bata amsa da yanayin damuwa a fuskarsa
STORY CONTINUES BELOW
“Habibty inda naje waya bata shiga shiyasa”
Jingina tayi da kujerar motar batare da ta k’ara cewa komai baYa matso kusa da ita yana cigaba da cewa
“Abunda natsana a duniya shine inga hawaye a fuskarki, narok’eki habibty, ki tsayar da hawayennan haka”
Banza tayi dashi,ya gyad’a kai yana cewa
“To shikenan cikin biyu yanzu dole za ayi d’aya
Ko ki tsayar da hawayennan,ko kuma ki juyo da fuskar yana zubowa ina lashewa”
Harara ta galla Masa,yayi dariya yana kama kunnuwansa
“Please habibty I’m sorry”
Yadda ya lank’wasa muryar tasa taso tasata dariya
Ta share hawayen tana fuskantarsa,
“Dan Allah karka k’ara yimin irin haka,bakasan halin da na shigaba wallahi nikad’ai nasan tashin hankalin dana shiga”
Tafad’a cikin marai-raice fuska
Ya jinjina kai
“Shikenan, insha’allah bazan sake ba,kin hak’ura yanzu?
Ta d’aga kai alamar eh
Yayi murmushi
“Yauwa tawan Allah yabar minke,yanzu fad’amin ina kikeso muje,gurin shan ice cream,gurin cin tantabara ko gurin saida dambu?
Dariya tayi had’i da fad’in
“Sai dai gurin saida fate”
Shima dariyar yayi yana tada motar
Ita ko Rauda zuba mai fararen idanuwanta tayi tana sauke ajiyar zuciya
“Zahiri tana sonsa acikin zuciyarta, Wanda bata tab’a tunanin zata k’ara sa wani d’a namiji a cikin zuciyarta ba
Dan gabad’aya a rayuwarta ta tsani soyayya,takuma yi alk’awarin bazata sake yinta ba
Sai gashi Aasim ya canza mata tunani yasa ta k’ara komawa soyayya
Ajiyar zuciya ta sauke me nawi
Aasim ya juyo yad’an kalleta sannan yamaida kallonsa ga titi yace
“Yadai habibty,wannan ajiyar zuciya haka?
Ta kuma sauke wata a karo nabiyu sannan tace
“Aasim kasa na karya alk’awarin dana d’aukar ma kaina,na bazan sake yin soyayya ba,gashi yanzu zuciyata tagama amincewa dakai
Inada wata kalar zuciya da bata iya yin soyayya ba,idan harna fara son mutum to gabad’aya hankalina gushewa yikeyi
Dan allah kada kayi amfani da son danike maka,ka wahalar min da zuciyata,nasha wuya a baya banaso nasake mai-maita wa”
Ta k’arasa maganar idanuwanta na ciccikowa da hawaye
Da alamu jikinsa yayi sanyi da jin magan-ganunta
“Insha’allah habibty,bazan zama mesaki damuwa ba,abu d’aya nike so agareki…
Yad’an dakata, Rauda ko kallonsa takeyi
Yavcigaba da cewa
“Inaso kiyimin alk’awarin ko da nan gaba kin gano wani abu da baki san da shi ba a tare Dani,to kiyi min alk’awari bazaki rabu dani ba,ba kuma zaki dena sona ba, sannan kuma zaki gafarceni abisa b’oye mikin da nayi”
Kallonsa takeyi cikin rashin fahimta dan gabad’aya bata fahimci inda maganarsa ta dosa ba
“Bangane ba,dama kana b’oye min wani abu ne?to meyasa?kuma menene shi?
Yayi murmushin da ya tsaya masa iya labb’a kawai
“Lokaci na zuwa,da nasan dole zaki gane gaskiya,aduk lokacin dana tuna hakan sai inji hankalina ya tashi dan bansan wani hukunci zaki d’auka a lokacin ba”
STORY CONTINUES BELOW
Ta sauke guntun numfashi tace.
“To wai miye kake b’oyemin ne?
Sai kuma ta dakata alamar ta tuna wani abu, tacigaba da cewa
“Owo nafahimta,kana da aure ne ko?kana da mata shine ka b’oye kak’i fad’amin ko?
Ya murmushi yana girgiza kai
“Aa,wallahi bayan ke bani da wata Mata”
Tabud’e idanunta tana masa wani kallo
“Eyen,ni d’in ko?to yaushe na zama matarka?
Yad’an yi jim kaman ya naso ya tuna
“Eh to,kaman shekaru hud’u da suka wuce”
“Kai lokacin ma ko sanina kayi,duka-duka ko rabin shekara ma munyi da had’uwa ne?
Tafad’a tana k’walalomai ido
Yayi dariya yace
“Agurinki kenan amma ni agurina had’uwarmu tun bayan shekara ashirin ne?
Ta kuma bud’e idanuwanta sosai
“Kai, lokacin ma ko haihuwata anyi?ohhh na tuna anhaifeni lokacin kenan tun ina jaririya ko?
Ta tambayesa cikin yi galala da baki
Dariya yayi Yana paka motar a harabar gurin saida Ice cream
“Kinga habibty muje musiyo muyi mu koma,yanzu aka kirani akafad’a min muna da meeting”
Tace to,harzata bud’e motar kuma sai takoma tazauna
“Kace yanzu aka kiraka?da wace wayar to ince ga wayarnan a ajiye,kuma ni tunda nashigo motarnan banji ankirata ba?
Yayi k’ok’orin tsaida natsuwarsa guri d’aya yace
“D’azu nike son ince”
Gyad’a kai tayi tana tab’e baki
“Ook muje”
Basu wani b’ata lokaci ba,suna shiga tazab’i kalar ice cream d’in datake so suka fito
Bayan yatada motar sunfara tafiya tace
“Namanta ban tambayi shahida ba,tana lafiya? Ya ammi da nazma?
“Duk sunanan k’alau”
Yabata amsa a tak’aice
Gudu yayi sosai saboda meeting d’in da yace suna dashi
Yana ajiyeta ya juyaDa daddare bayan tayi shirin kwanciya,ta kira wayarsa,tagama ringing be d’auka ba
Tana ajiye wayar message na shigowa ta bud’e
“Habibty bamu gama meeting d’inba haryanzu,ki kwanta kiyi bacci ina sonki”
Murmushi tayi tare da rungume wayar a k’irjinta baccin da batayi kwana biyu ba kuwa yad’auketa
Bayan sati d’aya, hankalinta ya kwanta,dan suna tare soyayyar su nadad’a yin k’arfi
Ranar wata laraba,tashirya dan zuwa gurin saloon,dama sunyi dashi intaje shi zeje yad’aukota
Saboda yace yana da meeting a lokacin
Hakan yasa tafito bakin titi ta tari adai-daita sahu
Sun d’an yi nisa kad’an wata kyakkyawar budurwa ta tsaida a dai-daitan da Rauda ke ciki
Da sallama tashiga, Rauda ta amsa suka gaisa
Napep d’in tacigaba da tafiya
Budurwar da tashi ga napep d’in tace
“Rauda ko?
Da mamaki Rauda ta kalleta jin takira sunanta
“Eh itace”
STORY CONTINUES BELOW
Budurwar tayi murmushi
“Ni kuma saima”
Rauda tak’ara kallonta, bata tab’a ganinta ba,to a ina tasan ta?har tasan sunanta?
Saima ta katse mata tunanin da takeyi
“Kinyi mamakin kiran sunanki da nayi ko?
Rauda ta d’aga Kai
“Eh gaskiya danni bansanki ba,to ko makarantar mu kike?
Saima ta girgiza kai alamar aa
“Ba a makarantar ku nike ba malama Rauda”
Rauda ta jinjina Kai
“To ya akayi kikasan sunana?
Saima ta kuma yin murmushi,sunan ki ai sananne awurina,ke bama nikad’ai ba gabad’aya ahalina,babu wanda be sanki ba”
Mamaki yakuma kama Rauda
“Ahalinki? bangane ba”
Saima ta d’aga kai tace
“Eh,amma bawannan surutun ya kawoni ba,meyasa zuciyarki take saurin amincewa da mutane?
Baki san akwai wasu jinsi dazasu iya biyowa ta suffar mutane su cutar dake ba?
Cikin raahin fahimta Rauda ke kallonta amma takasa K’ara cewa komai
Dan ji tayi tsigar jikinta tafara tashi
Saima takuma yin murmushi,tana cigaba da cewa
“Ya kamata dai kirink’a ban-bance jinsin mutum da kuma na aljani,domin yana tare dake akodayaushe
Nabarki lafiya”
Tana gama fad’ar haka ta dire ko cewa me napep d’in ya tsaya batayi ba
Rauda tsoro ne yakamata, jikinta yayi sanyi sosai
Dede lokacin me napep d’in yatsaya a k’ofar shagon saloon d’in
Taciro kud’insa tabasa, dasauri tashiga shagon tazauna tana maida numfashi
Me saloon d’in me suna Amira tace
“Yadai customer?lafiya naganki wani iri?
Rauda ta girgiza Kai
“Aa bakomai”
Amma cikin zuciyarta mamaki da kuma al’ajabin saima ne,me take nufi da yakamata ta rink’a ban-bance jinsin mutum da na aljani?
Domin yana tare da ita a kodayaushe?
Maganar Amira ce ta katse mata tunanin data tafi
“Me za’amiki, retouching ko steaming?
“Steaming”
Tabata amsa a tak’aice
Har aka kammala mata bata dawo cikin natsuwarta ba,juyayin abunda yafaru kawai takeyi
Tana zaune ana taje mata kai, Aasim yayi sallama dayike yasan wurin ya tab’a kawota
Amira ce ta amsa tana bashi izinin shiga
Yashiga shagon da murmushi a fuskarsa yana kallon gashin kanta da yayi bak’i sid’ik yana ta shek’i
“Wow habibty kinga yadda gashin yayi kyau kuwa?
Amira tayi dariya tana fad’in
“Sai ka biyani da yawa”
Ya rausayar da Kai yace
“Baki da matsala, tunda kina gyara min matata”
Murmushi Rauda jeyi
“Ai nayi zaton bazaka zo ba”
Ya girgiza Kai yace
STORY CONTINUES BELOW
“Haba nina Isa?muna gama meeting d’in nan nayo direct”
Ta jinjina Kai tana janyo d’an kwalinta zata d’aura gaban makeken madubin da ke manne a bango
Gabanta ne yafad’i Ras, yayinda ta ga Aasim sanye da wasu kaya irin na sarakai ta cikin madubin kuma yayi wani bau farinsa da kyansa ya ninka wanda tasani
Tayi gaggawar kallonsa a fili
Yana tsaye yana bawa amira kud’i sanye da k’anan Kaya
Ta murza idanuwanta dasauri tana ganin kaman gizo idanun ke mata
Takuma kallon madubin, still da kayan sarautar ta k’ara ganinsa
Maganar saima ce tadawo Mata, gabanta yayi wani mugun fad’uwa
Tayi saurin kauda kanta a madubin ganin madubin yafara yimata dishi-dishi
Kallonta yayi yace
“Yadai naganki a daburce meyafaru?
Ta girgiza kai dasauri batare da tace komai ba
Amira tace
“Nima dai yau tunda tashigo haka naganta”
Yakuma kallonta sosai
“Habibty,lafiya?meke faruwa”
Kuma girgiza kai tayi alamar babu komai
Ya jinjina kai amma be yadda babu komai d’in ba
“Shikenan muje”
Yayi gaba yana yiwa amira sallama
Bin bayansa tayi da kallo gabanta na fad’uwa
Yad’an waigo yana dubanta ganin tana tsaye bata da niyyar tafiya
“Yadai,ko baki gama bane”
Ta girgiza kai tana d’aga k’afarta datayi mata nawi a tafito
Yabud’e mata motar tashiga,sannan ya shiga ya tada
Yana cewa
“Kifad’a min meke faruwa,ni nasan akwai wani abu hakanan dai bazan ganki a daburce ba”
Tayi k’arfin halin danne tarin fargaban da yike zuciyarta
“Aasim,intambaye ka zaka fad’amin gaskiya”
Ya kalleta
“Eh zanfad’a miki indai nasani”
Ta jinjina Kai tace
“Aasim kai mutum ne?
Ta jeho mai tambayar da be shirya jinta ba
“Eyeh,mene?mekika ce?
Yafad’a cikin sark’ewar murya
“Nace kai mutum ne?
Yayi shuru na y’an sakwanni sannan yace
“Me yasa kika yimin wannan tambayar?
Ta gyad’a kai fad’uwar gabanta na dad’a tsananta
“Akwai abunda nagani da nakasa fahimta, please k’afad’a min gaskiya kai mutum ne?
Ya sauke numfashi tare da cewa
“Eh ni mutum ne”
Girgiza kai tayi cikin rashin yadda
“Banyadda ba,idan kai mutum ne ya akayi siffarka,da kayan jikinka suka sauya acikin madubi?
Ya taka burki da sauri yana kallonta
“Suffata Kuma,ayaushe?saidai in gizo idanun ki suka Miki”
Ta gyad’a kai tana zage jakar ta ta ciro reza ta bud’e tare da sawa akan yatsanta ta danna
STORY CONTINUES BELOW
Sai ga jini b’ul-b’ul,
“Miye haka habibty,yanka kanki kikayi fa?
Yafad’a dasauri,ta jinjina
” kai nasani ai,kai ma inaso ka yanki yatsanka,saboda in tabbatar da abunda nike zargi”
Girgiza kai yayi
“Habibty baki yadda dani bane?
“Ko na yarda dakai inaso inga jini a jikinka,idan har kasan abunda kafad’a min gaskiya ne to ka amsa kayi abunda nace”
Tafad’a cikin wani irin yanayi na tashin hankali
“Habibty..,.
Katseshi tayi ta hanyar kama hannunsa zata danna rezar
Yayi saurin rik’e hannunta da d’ayan hannunsa
Sai dai ina,kafin yayi wani yunk’uri ta yanke sa
A memakon taga jini,wani kalar abu taga yana fitowa kore shataf
Ja baya tayi dasauri, k’irjinta yayi wani mugun bugawa
Hannunta tasa akai,ta k’wala ihu
Yayi saurin matsowa yana fad’in
“Habibty narok’eki ki kwantar da hankalinki”
K’ok’arin bud’e motar tafarayi da sauri amma Gam,tak’i bud’ewa
Tafara jijjigata da k’arfi tana cigaba da yin ihu
Ya k’ara matsowa yana kiran sunanta
Ganin k’ofar bata da alamun bud’ewa yasa ta juyo tana kallonsa tare da had’e hannun ta guri d’aya cikin kuka da tsananin firgici tace
“Narok’eka kada ka cutar Dani,kayi hak’uri idan laifi nemaka”
Hannunta yakama zeyi magana,ta fizge hannun da sauri
“Kada katab’ani kayiwa Allah kabud’emin infita”
Ajiyar zuciya yasauke tare dacewa
“Kiyi hak’uri ki fahimceni,ki natsu dan Allah”
“Nidai kabud’emin infita,karabu dani kayi hak’uri,kar ka cutar Dani wallahi banyi ma komai ba……
Tsawa ya daka mata
“Nace ki natsu ko!!!!!!
Shurun ko tayi dan tsawar ta k’ara razana ta, kyar-kyarwa kawai takeyi kamar anciro ta da ga cikin k’an-k’ara
Aasim ya cigaba da cewa
“Inda zan cutar dake da tuni na cutar dake,kinsan adadin shekarun da nayi ina tare ke ne?
Da zan cutar dake da tuni ban cutar dake ba,ko kinga al’amarin cutarwa a tare Dani?
Yafad’a cikin yanayin damuwa
Sannan ya sassauta murya
“Kiyi hak’uri na d’aga miki murya,amma dan allah ki kwantar da hankalinki,
Tunda Kingane gaskiya ai dole zanyi miki bayani”
Ta jinjina Kai tana kallonsa,ayanzu tsoron yafara raguwa dan ko tafahimci ba cutar da ita d’in zeyi ba
Ya numfasa sannan yace
“Ayanzu babu abunda zan b’oye Miki,
Zanyi miki bayanin komai,kuma inaso ki saurareni da kunnen basira
Ki kuma fahimci bayanin da zanyi miki kinji?
Tad’aga kai alamar taji
Yacigaba da cewa
“Ni ba mutum bane,kuma ni ba aljani bane amma ni rauhani ne,
Kamar yadda kikasani sunana Aasim, Aasim bin ramzad,
STORY CONTINUES BELOW
Mahaifina shine sarki ramzad dake mulkar masarautar rauhanai
Kuma ni mijinki ne,inada aure dake tun shekaru hud’u da suka wuce,sannan har da y’a a tsakanina dake”
Zaro ido tayi tana kallonsa
“Aure,harda y’a?kuma Dani?
Tafad’a cikin rawar murya da kuma mamaki
Ya jinjina Kai
“Eh Rauda,shahida da kika gani y’arki ce kece mahaifiyar ta”
Ta kuma zaro ido tana kallonsa
Yacigaba dacewa
“Zanyi miki bayanin ko ni waye,da kuma yadda akai na aure ki har kika haihu batare da kinsani ba” +
🙎🏻
Typing dakwai wahala Allah, muhad’u a Page 13
Yarfillo.
JINNUL
AASHIQUE🌹 +
🧞♂ 🧞♂
🧞♂
NA
HARIRA ALIYU (y’arfillo)
Dedicated to Little hajjo and my elder sister Hafsat aliyu
🅿AGE📕 1⃣2⃣
Wannan Page d’in nakine mamana,allah ya k’ara miki lafiya yasa kaffarane, ina k’aunarki araina domin kin kasance uwa tagari me share min kuka na a kodayaushe.🥰
NA KASA MANTAWA DAKE😭
Dede da rana d’aya, kodayaushe cikin tuna ki nikeyi, hak’ik’a nayi babban rashi da na rasaki,y’ar uwata hajara aliyu allah Nike rok’o ya jik’anki da rahama,ya gafarta Miki,yasa aljannah ce makomarki Amin😭😭😭
8:57🕐am. SUN,APR 21✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
Bissmillahir rahmanin rahimYa sauke numfashi idanuwansa na kanta,yace
“Akwai wani sabon restaurant da aka bud’e babu kalar abincin gargajiyan da basa saidawa,kuma har dare suna kaiwa,anan na siyo”
Ta jinjina Kai
Ya cigaba da cewa
“Sannan dakike cewe a iya sanin ki babu inda ake saidawa a kusa -kusannan yawo kike yi? Keda sai kiyi sati ma wani zubin baki lek’a ko wajen makaranta ba”
Tayi dariya tana gyad’a Kai
“Hakane,to nagode allah ya k’ara bud’i “
Ya amsa da Amin
Taja iska alamar sanyi na ratsa jikinta sosai tana tana mammatse jikinta da yike rawa kad’an saboda sanyin dake kad’ata
“Wai shin kai baka jin sanyi ne?
STORY CONTINUES BELOW
Ya bata amsa
“Me kikagani?
Rauda tace
“Gani nayi bakasa rigan sanyi ba,kuma ko rawar sanyi bakayi”
Aasim yayi murmushi
“Kafinnazo nan inajin sanyi sosai,amma ina had’a ido dake,sai naji wani d’umi na ratsani, gabad’aya sai naji sanyin ya tafi”
Tayi dariya tana girgiza Kai
“Kai ko?
Shima dariyar yayi yana kwai-kwayar yadda take magana
“Ni me nayi?
Dariya takuma yi sosai tace
“Allah har fargaban ayi hutu nikeyi,saboda zanyi missing d’inka,da dariyar da kake sani,tunda nahad’u dakai ka kawarda duk wata damuwata kasanya ma zuciyata farin ciki ina godiya sosai”
Murmushi yayi me cike da abubuwa da yawa
“Kin can-canci komai habibty,zan iya yimiki komai,sannan zan iya yin komai akanki”
Itama murmushin takeyi
“Dagaske?zaka iya yin komai akaina?
Ya jinjina kai
“Dagaske habibty,zan iya bada rayuwata akanki”
Wata sassanyar ajiyar zuciya tasauke,tana jin wani farinciki na ratsa illahirin zuciyarta
Ta d’aga kai tana kallon saman bishiyar wacce iska ke kad’a ganyayyakinta,suna kad’awa ahankali
“Bansan meyasa kake sona ba,duk da nasan matsayina be kai ace ka soni ba”
Yad’an matso gab da ita suna kallon juna
Yace
“Nima kaina bansan meyasa ba,abu d’aya ne nasani na kuma yarda dashi,shine allah ne ya jarabceni da k’aunarki,habibty bazan iya rayuwa idan babu keba,kuma kada kiyi tunanin nafad’a mikine dan kawai soyayya
Wallahi dagaske nikeyi,ina k’aunar ki”
Ta kuma sauke ajiyar zuciya da yin shuru na y’an sakwanni sannan tace
“Nima ina sonka Aasim,kuma insha allahu zan rayu tare da Kai,dannasan zan rayu cikin farin ciki idan na kasance tare da Kai”
Aasim yayi murmushi da alamu maganar da ta fad’a tayi masa dad’i sosai
“Nagode habibty,bari nabarki kikoma ciki,tunda sanyin na damunki”
Ta gyad’a kai tace
“Shikenan nagode, Saida safe”
“To sai da safe”
Tafad’a tana juyawa,harta d’an yi nisa tajuyo
Yana tsaye inda tabarsa yana kallonta
Tace
“Yadai da magana ne indawo?
Ya girgiza kai yace
“Aa,kawai inaso inga shigarki ne tukunna sai inwuce”
Ta gyad’a Kai tana murmushi
Sannan taci gaba da tafiya
“Rauda!
Ya Kira sunanta,ta waigo tana kallonsa batare da ta amsa ba
“Ina sonki”
Yafad’a,takuma yin murmushi tare da juyawa dasauri,tashige ciki
Koda ta koma d’aki, murmushi be bar fuskarta ba,taci dambun sosai tasha Lipton sannan ta kwanta zuciyarta cike da tunaninsa
Washe gariDa wuri ta shirya zuwa lectures,tana tafiya tana tunanin meyasa be kirata ba yau,dan kullum da asuba sai ya kirata,shike tashin su sallah,
Haka ma idan gari yayi haske sai ya kirata yace ta tashi ta shirya
Ta ciro wayarta ta latsa numbansa taji a kashe
STORY CONTINUES BELOW
Ta maida wayar jaka taciga ba da tafiya
Wunin ranar wayar sa bata shiga ba,data kira sai taji a kashe
Tashiga damuwa sosai,dan bata tab’a kiran wayarsa taji a kashe ba
Har ta koma hostel, tana k’ara trying d’in kiran
Amma still a kashe
Ta yada jakar ta a k’asa tana zubewa a kan katifa
Salma dake zaune ta kalleta tana cewa
“Yadai?duk gajiyar ce?
Ta d’aga kai alamar eh tare da cewa
“Da gajiyar da kuma damuwa”
Salma tace
“Damuwa Kuma? Tamece?
Ta sauke numfashi tana tashi tazauna
“Yau tun safe Nike kiran wayar Aasim a kashe,shine duk hankalina ya tashi wallahi,dan bantab’a kiransa naji irin haka ba”
Salma ta jinjina kai
“Gaskiya dole kishiga damuwa,to ko wayar tasa ta fad’i ne?
“Nima nayi tunanin hakan,amma kuma da fad’uwa wayar tayi,da yazo yafad’a min kuma da na gansa acikin makaranta,amma fa banga alamunsa ba,har inda yasaba tsayawa naje bangansa ba, shiyasa nike tunanin ba lafiya ba”
Salma ta jinjina kai
“Gaskiya, to amma kik’ara gwadawa anjima insha’allah zata shiga,k’ila abubuwane suka mai yawa ya kashe”
Rauda tayi shuru kawai dan ita zuciyarta tafi bata ba lafiya ba
Daren ranar batayi wani baccin kirki ba,washegari ma haka takira wayar yafi sau d’ari amma abu d’aya ake gaya mata,akashe
Hankalinta ya tashi sosai,ko abinci takasa ci,bata tab’a sanin tana k’aunar sa ba sai a lokacin
Ahaka aka kwashe kwana uku, lokacin tagama jigata da rashin sa
Hakan yasa bayan tafito daga lectures tayanke shawarar zuwa department d’insu ta tambaya
Suka ci karo da salma ita ma tafito daga nata lectures d’in
“Yadai Rauda ina zakije?
Salma ta tambaya,
“Zan lek’a b’angaren su Aasim ne intambaya nagaji da zama cikin rashin sanin wani Hali yike ciki”
Salma ta jinjina Kai
“To muje inrakaki nima abun nadamuna wallahi”
Suka jera suka tafi,da isarsu suka tadda d’alubai na zaune suyi group-group sunata fira da shewa da alamu sunfito daga lectures ne,wasu kuma suna ta bitar karatu
Wani matashi suka gani a zaune shikad’ai da handout a hannunsa
Suka k’arasa gurin suka mai sallama
Ya amsa fuskarsa a sake suka gaisa,sannan Rauda tace
“Dan allah ina tambayar Aasim ne,kwana biyu bana ganinsa bansani ba ko lafiya?
“Aasim?
Matashin ya tambaya, Rauda ta d’aga kai tana fad’in
“Eh “
Yace
“Gaskiya bangane shi ba saidai ku tambayi wancan shine yike da list sunayen gabad’aya kuma shi ze iya saninshi,amma ni ba lallai insanshi ba saboda muna da yawa”
Yak’arasa fad’a yanayimata nuni da wani
Rauda ta jinjina kai
“Hakane,nagode sai anjima”
Tafad’a sannan suka k’arasa gurin wanda ya nuna musu suka mai sallama
Sannan suka tambayeshi
Shima mai-maita sunan yayi
“Aasim, Aasim,anya anan department d’in kuwa?Ta d’aga kai
“Eh”
STORY CONTINUES BELOW
Yad’an yi shuru yana nazari sannan yace
“Gaskiya bangane shi ba,abokina ko kasan me suna irin haka haka?
Yak’arasa fad’a yana kallon wanda yike kusa da shi
Shima girgiza kai yayi alamar be sani ba
Wanda suka fara tambayar yace
“To gaskiya bamu san wani me suna haka ba,sai dai inba a department d’inmu yike ba”
Rauda ta girgiza kai tace
“Anan fa yace yike,yananan zaka ganshi wani fari dogo haka”
Ya ajiye numfashi yace
“Nafad’a miki bansanshi ba gaskiya”
Ta gyad’a kai cike da damuwa a cikin zuciyata
“Shikenan nagode,mutafi Salma”
Suka juyo jiki babu k’wari
Salma tace
“To ya akayi haka Rauda?ni al’amarinnan yafara d’aure min kai fa,ace a department d’insu babu wanda yasansa?
Rauda ta sauke numfashi me nawi batare da ta ce komai ba, Dan gabad’aya jikinta yayi sanyi
Wata mota ce tasha gabansu,cikin b’acin rai salma Tafara fad’a
“Wannan wani irin wulak’anci ne zaka wani…….
Kasa k’arsawa tayi yayinda ya sauke Glass d’in motar
Rauda ko kanta na k’asa ko kallon motar batayi ba dan damuwar dake zuciyarta nema takeyi tafi k’arfinta
“Habibty…
Taji anfad’a, dasauri tad’ago kanta,suka had’a ido
Ya sakar mata lallausan murmushi
“Habibty,bazaki amsa kiran nawa bane,duk fushi dani d’inne ya jawo haka?
A memakon tabashi amsa,sai kawai idanunta suka cicciko da k’walla
Nan da nan hawaye yafara wanke mata fuska
Dasauri ya bud’e marfin motar,yafito yana fad’in
“Subhanallah,kuka habibty,me yake faruwa?
Ya tambaya hankalinsa a tashe
Ji tayi k’afafunta suna neman kasa d’aukarta,hakan yasa ta durk’usa tana cigaba da yin kukan
“Habibty please kiyi hak’uri,tashi kishiga mota, banaso hankalin mutane ya dawo kanki”
Kasa mik’ewa tayi saida Salma ta kamata tukunna,sannan tashiga motar
Salma tawuce tabarsu,itako Rauda kifa kanta tayi agaban motar tana cigaba da yin kukan da ta rasa ko na menene
Ya sauke numfashi yana cewa
“Dan girman Allah habibty,ki wa girman allah kiyi shuru,wallahi kukanki sosamin zuciya yike yi”
D’agowa tayi tana kallonsa da jik’akk’un idanunta
“Inyi shuru fa kace?kasa nashiga tashin hankali da tsananin damuwa,ina fargaban ko ba lafiya kake ba,inata fargaban ko wani abune ya sameka,ashe lafiyar ka k’alau…..
“Please kiyi hak’uri nasan nayi kuskure, Amma ba wai da niyya nai hakan ba,tafiya ce takamani kuma cikin gaggawa……
“Okay idan tafiya takamaka baka iya sanar min kafin katafi?
Ta katseshi,ya girgiza kai yace
“Naso insanar dake kafin intafi amma saboda yadda tafiyar tazo min bansamu daman kiranki ba”
“To dakaje fa,meyasa baka kirani ba?
Ta kuma tambaya still idanuwanta na kansa
Ya bata amsa da yanayin damuwa a fuskarsa
STORY CONTINUES BELOW
“Habibty inda naje waya bata shiga shiyasa”
Jingina tayi da kujerar motar batare da ta k’ara cewa komai baYa matso kusa da ita yana cigaba da cewa
“Abunda natsana a duniya shine inga hawaye a fuskarki, narok’eki habibty, ki tsayar da hawayennan haka”
Banza tayi dashi,ya gyad’a kai yana cewa
“To shikenan cikin biyu yanzu dole za ayi d’aya
Ko ki tsayar da hawayennan,ko kuma ki juyo da fuskar yana zubowa ina lashewa”
Harara ta galla Masa,yayi dariya yana kama kunnuwansa
“Please habibty I’m sorry”
Yadda ya lank’wasa muryar tasa taso tasata dariya
Ta share hawayen tana fuskantarsa,
“Dan Allah karka k’ara yimin irin haka,bakasan halin da na shigaba wallahi nikad’ai nasan tashin hankalin dana shiga”
Tafad’a cikin marai-raice fuska
Ya jinjina kai
“Shikenan, insha’allah bazan sake ba,kin hak’ura yanzu?
Ta d’aga kai alamar eh
Yayi murmushi
“Yauwa tawan Allah yabar minke,yanzu fad’amin ina kikeso muje,gurin shan ice cream,gurin cin tantabara ko gurin saida dambu?
Dariya tayi had’i da fad’in
“Sai dai gurin saida fate”
Shima dariyar yayi yana tada motar
Ita ko Rauda zuba mai fararen idanuwanta tayi tana sauke ajiyar zuciya
“Zahiri tana sonsa acikin zuciyarta, Wanda bata tab’a tunanin zata k’ara sa wani d’a namiji a cikin zuciyarta ba
Dan gabad’aya a rayuwarta ta tsani soyayya,takuma yi alk’awarin bazata sake yinta ba
Sai gashi Aasim ya canza mata tunani yasa ta k’ara komawa soyayya
Ajiyar zuciya ta sauke me nawi
Aasim ya juyo yad’an kalleta sannan yamaida kallonsa ga titi yace
“Yadai habibty,wannan ajiyar zuciya haka?
Ta kuma sauke wata a karo nabiyu sannan tace
“Aasim kasa na karya alk’awarin dana d’aukar ma kaina,na bazan sake yin soyayya ba,gashi yanzu zuciyata tagama amincewa dakai
Inada wata kalar zuciya da bata iya yin soyayya ba,idan harna fara son mutum to gabad’aya hankalina gushewa yikeyi
Dan allah kada kayi amfani da son danike maka,ka wahalar min da zuciyata,nasha wuya a baya banaso nasake mai-maita wa”
Ta k’arasa maganar idanuwanta na ciccikowa da hawaye
Da alamu jikinsa yayi sanyi da jin magan-ganunta
“Insha’allah habibty,bazan zama mesaki damuwa ba,abu d’aya nike so agareki…
Yad’an dakata, Rauda ko kallonsa takeyi
Yavcigaba da cewa
“Inaso kiyimin alk’awarin ko da nan gaba kin gano wani abu da baki san da shi ba a tare Dani,to kiyi min alk’awari bazaki rabu dani ba,ba kuma zaki dena sona ba, sannan kuma zaki gafarceni abisa b’oye mikin da nayi”
Kallonsa takeyi cikin rashin fahimta dan gabad’aya bata fahimci inda maganarsa ta dosa ba
“Bangane ba,dama kana b’oye min wani abu ne?to meyasa?kuma menene shi?
Yayi murmushin da ya tsaya masa iya labb’a kawai
“Lokaci na zuwa,da nasan dole zaki gane gaskiya,aduk lokacin dana tuna hakan sai inji hankalina ya tashi dan bansan wani hukunci zaki d’auka a lokacin ba”
STORY CONTINUES BELOW
Ta sauke guntun numfashi tace.
“To wai miye kake b’oyemin ne?
Sai kuma ta dakata alamar ta tuna wani abu, tacigaba da cewa
“Owo nafahimta,kana da aure ne ko?kana da mata shine ka b’oye kak’i fad’amin ko?
Ya murmushi yana girgiza kai
“Aa,wallahi bayan ke bani da wata Mata”
Tabud’e idanunta tana masa wani kallo
“Eyen,ni d’in ko?to yaushe na zama matarka?
Yad’an yi jim kaman ya naso ya tuna
“Eh to,kaman shekaru hud’u da suka wuce”
“Kai lokacin ma ko sanina kayi,duka-duka ko rabin shekara ma munyi da had’uwa ne?
Tafad’a tana k’walalomai ido
Yayi dariya yace
“Agurinki kenan amma ni agurina had’uwarmu tun bayan shekara ashirin ne?
Ta kuma bud’e idanuwanta sosai
“Kai, lokacin ma ko haihuwata anyi?ohhh na tuna anhaifeni lokacin kenan tun ina jaririya ko?
Ta tambayesa cikin yi galala da baki
Dariya yayi Yana paka motar a harabar gurin saida Ice cream
“Kinga habibty muje musiyo muyi mu koma,yanzu aka kirani akafad’a min muna da meeting”
Tace to,harzata bud’e motar kuma sai takoma tazauna
“Kace yanzu aka kiraka?da wace wayar to ince ga wayarnan a ajiye,kuma ni tunda nashigo motarnan banji ankirata ba?
Yayi k’ok’orin tsaida natsuwarsa guri d’aya yace
“D’azu nike son ince”
Gyad’a kai tayi tana tab’e baki
“Ook muje”
Basu wani b’ata lokaci ba,suna shiga tazab’i kalar ice cream d’in datake so suka fito
Bayan yatada motar sunfara tafiya tace
“Namanta ban tambayi shahida ba,tana lafiya? Ya ammi da nazma?
“Duk sunanan k’alau”
Yabata amsa a tak’aice
Gudu yayi sosai saboda meeting d’in da yace suna dashi
Yana ajiyeta ya juyaDa daddare bayan tayi shirin kwanciya,ta kira wayarsa,tagama ringing be d’auka ba
Tana ajiye wayar message na shigowa ta bud’e
“Habibty bamu gama meeting d’inba haryanzu,ki kwanta kiyi bacci ina sonki”
Murmushi tayi tare da rungume wayar a k’irjinta baccin da batayi kwana biyu ba kuwa yad’auketa
Bayan sati d’aya, hankalinta ya kwanta,dan suna tare soyayyar su nadad’a yin k’arfi
Ranar wata laraba,tashirya dan zuwa gurin saloon,dama sunyi dashi intaje shi zeje yad’aukota
Saboda yace yana da meeting a lokacin
Hakan yasa tafito bakin titi ta tari adai-daita sahu
Sun d’an yi nisa kad’an wata kyakkyawar budurwa ta tsaida a dai-daitan da Rauda ke ciki
Da sallama tashiga, Rauda ta amsa suka gaisa
Napep d’in tacigaba da tafiya
Budurwar da tashi ga napep d’in tace
“Rauda ko?
Da mamaki Rauda ta kalleta jin takira sunanta
“Eh itace”
STORY CONTINUES BELOW
Budurwar tayi murmushi
“Ni kuma saima”
Rauda tak’ara kallonta, bata tab’a ganinta ba,to a ina tasan ta?har tasan sunanta?
Saima ta katse mata tunanin da takeyi
“Kinyi mamakin kiran sunanki da nayi ko?
Rauda ta d’aga Kai
“Eh gaskiya danni bansanki ba,to ko makarantar mu kike?
Saima ta girgiza kai alamar aa
“Ba a makarantar ku nike ba malama Rauda”
Rauda ta jinjina Kai
“To ya akayi kikasan sunana?
Saima ta kuma yin murmushi,sunan ki ai sananne awurina,ke bama nikad’ai ba gabad’aya ahalina,babu wanda be sanki ba”
Mamaki yakuma kama Rauda
“Ahalinki? bangane ba”
Saima ta d’aga kai tace
“Eh,amma bawannan surutun ya kawoni ba,meyasa zuciyarki take saurin amincewa da mutane?
Baki san akwai wasu jinsi dazasu iya biyowa ta suffar mutane su cutar dake ba?
Cikin raahin fahimta Rauda ke kallonta amma takasa K’ara cewa komai
Dan ji tayi tsigar jikinta tafara tashi
Saima takuma yin murmushi,tana cigaba da cewa
“Ya kamata dai kirink’a ban-bance jinsin mutum da kuma na aljani,domin yana tare dake akodayaushe
Nabarki lafiya”
Tana gama fad’ar haka ta dire ko cewa me napep d’in ya tsaya batayi ba
Rauda tsoro ne yakamata, jikinta yayi sanyi sosai
Dede lokacin me napep d’in yatsaya a k’ofar shagon saloon d’in
Taciro kud’insa tabasa, dasauri tashiga shagon tazauna tana maida numfashi
Me saloon d’in me suna Amira tace
“Yadai customer?lafiya naganki wani iri?
Rauda ta girgiza Kai
“Aa bakomai”
Amma cikin zuciyarta mamaki da kuma al’ajabin saima ne,me take nufi da yakamata ta rink’a ban-bance jinsin mutum da na aljani?
Domin yana tare da ita a kodayaushe?
Maganar Amira ce ta katse mata tunanin data tafi
“Me za’amiki, retouching ko steaming?
“Steaming”
Tabata amsa a tak’aice
Har aka kammala mata bata dawo cikin natsuwarta ba,juyayin abunda yafaru kawai takeyi
Tana zaune ana taje mata kai, Aasim yayi sallama dayike yasan wurin ya tab’a kawota
Amira ce ta amsa tana bashi izinin shiga
Yashiga shagon da murmushi a fuskarsa yana kallon gashin kanta da yayi bak’i sid’ik yana ta shek’i
“Wow habibty kinga yadda gashin yayi kyau kuwa?
Amira tayi dariya tana fad’in
“Sai ka biyani da yawa”
Ya rausayar da Kai yace
“Baki da matsala, tunda kina gyara min matata”
Murmushi Rauda jeyi
“Ai nayi zaton bazaka zo ba”
Ya girgiza Kai yace
STORY CONTINUES BELOW
“Haba nina Isa?muna gama meeting d’in nan nayo direct”
Ta jinjina Kai tana janyo d’an kwalinta zata d’aura gaban makeken madubin da ke manne a bango
Gabanta ne yafad’i Ras, yayinda ta ga Aasim sanye da wasu kaya irin na sarakai ta cikin madubin kuma yayi wani bau farinsa da kyansa ya ninka wanda tasani
Tayi gaggawar kallonsa a fili
Yana tsaye yana bawa amira kud’i sanye da k’anan Kaya
Ta murza idanuwanta dasauri tana ganin kaman gizo idanun ke mata
Takuma kallon madubin, still da kayan sarautar ta k’ara ganinsa
Maganar saima ce tadawo Mata, gabanta yayi wani mugun fad’uwa
Tayi saurin kauda kanta a madubin ganin madubin yafara yimata dishi-dishi
Kallonta yayi yace
“Yadai naganki a daburce meyafaru?
Ta girgiza kai dasauri batare da tace komai ba
Amira tace
“Nima dai yau tunda tashigo haka naganta”
Yakuma kallonta sosai
“Habibty,lafiya?meke faruwa”
Kuma girgiza kai tayi alamar babu komai
Ya jinjina kai amma be yadda babu komai d’in ba
“Shikenan muje”
Yayi gaba yana yiwa amira sallama
Bin bayansa tayi da kallo gabanta na fad’uwa
Yad’an waigo yana dubanta ganin tana tsaye bata da niyyar tafiya
“Yadai,ko baki gama bane”
Ta girgiza kai tana d’aga k’afarta datayi mata nawi a tafito
Yabud’e mata motar tashiga,sannan ya shiga ya tada
Yana cewa
“Kifad’a min meke faruwa,ni nasan akwai wani abu hakanan dai bazan ganki a daburce ba”
Tayi k’arfin halin danne tarin fargaban da yike zuciyarta
“Aasim,intambaye ka zaka fad’amin gaskiya”
Ya kalleta
“Eh zanfad’a miki indai nasani”
Ta jinjina Kai tace
“Aasim kai mutum ne?
Ta jeho mai tambayar da be shirya jinta ba
“Eyeh,mene?mekika ce?
Yafad’a cikin sark’ewar murya
“Nace kai mutum ne?
Yayi shuru na y’an sakwanni sannan yace
“Me yasa kika yimin wannan tambayar?
Ta gyad’a kai fad’uwar gabanta na dad’a tsananta
“Akwai abunda nagani da nakasa fahimta, please k’afad’a min gaskiya kai mutum ne?
Ya sauke numfashi tare da cewa
“Eh ni mutum ne”
Girgiza kai tayi cikin rashin yadda
“Banyadda ba,idan kai mutum ne ya akayi siffarka,da kayan jikinka suka sauya acikin madubi?
Ya taka burki da sauri yana kallonta
“Suffata Kuma,ayaushe?saidai in gizo idanun ki suka Miki”
Ta gyad’a kai tana zage jakar ta ta ciro reza ta bud’e tare da sawa akan yatsanta ta danna
STORY CONTINUES BELOW
Sai ga jini b’ul-b’ul,
“Miye haka habibty,yanka kanki kikayi fa?
Yafad’a dasauri,ta jinjina
” kai nasani ai,kai ma inaso ka yanki yatsanka,saboda in tabbatar da abunda nike zargi”
Girgiza kai yayi
“Habibty baki yadda dani bane?
“Ko na yarda dakai inaso inga jini a jikinka,idan har kasan abunda kafad’a min gaskiya ne to ka amsa kayi abunda nace”
Tafad’a cikin wani irin yanayi na tashin hankali
“Habibty..,.
Katseshi tayi ta hanyar kama hannunsa zata danna rezar
Yayi saurin rik’e hannunta da d’ayan hannunsa
Sai dai ina,kafin yayi wani yunk’uri ta yanke sa
A memakon taga jini,wani kalar abu taga yana fitowa kore shataf
Ja baya tayi dasauri, k’irjinta yayi wani mugun bugawa
Hannunta tasa akai,ta k’wala ihu
Yayi saurin matsowa yana fad’in
“Habibty narok’eki ki kwantar da hankalinki”
K’ok’arin bud’e motar tafarayi da sauri amma Gam,tak’i bud’ewa
Tafara jijjigata da k’arfi tana cigaba da yin ihu
Ya k’ara matsowa yana kiran sunanta
Ganin k’ofar bata da alamun bud’ewa yasa ta juyo tana kallonsa tare da had’e hannun ta guri d’aya cikin kuka da tsananin firgici tace
“Narok’eka kada ka cutar Dani,kayi hak’uri idan laifi nemaka”
Hannunta yakama zeyi magana,ta fizge hannun da sauri
“Kada katab’ani kayiwa Allah kabud’emin infita”
Ajiyar zuciya yasauke tare dacewa
“Kiyi hak’uri ki fahimceni,ki natsu dan Allah”
“Nidai kabud’emin infita,karabu dani kayi hak’uri,kar ka cutar Dani wallahi banyi ma komai ba……
Tsawa ya daka mata
“Nace ki natsu ko!!!!!!
Shurun ko tayi dan tsawar ta k’ara razana ta, kyar-kyarwa kawai takeyi kamar anciro ta da ga cikin k’an-k’ara
Aasim ya cigaba da cewa
“Inda zan cutar dake da tuni na cutar dake,kinsan adadin shekarun da nayi ina tare ke ne?
Da zan cutar dake da tuni ban cutar dake ba,ko kinga al’amarin cutarwa a tare Dani?
Yafad’a cikin yanayin damuwa
Sannan ya sassauta murya
“Kiyi hak’uri na d’aga miki murya,amma dan allah ki kwantar da hankalinki,
Tunda Kingane gaskiya ai dole zanyi miki bayani”
Ta jinjina Kai tana kallonsa,ayanzu tsoron yafara raguwa dan ko tafahimci ba cutar da ita d’in zeyi ba
Ya numfasa sannan yace
“Ayanzu babu abunda zan b’oye Miki,
Zanyi miki bayanin komai,kuma inaso ki saurareni da kunnen basira
Ki kuma fahimci bayanin da zanyi miki kinji?
Tad’aga kai alamar taji
Yacigaba da cewa
“Ni ba mutum bane,kuma ni ba aljani bane amma ni rauhani ne,
Kamar yadda kikasani sunana Aasim, Aasim bin ramzad,
STORY CONTINUES BELOW
Mahaifina shine sarki ramzad dake mulkar masarautar rauhanai
Kuma ni mijinki ne,inada aure dake tun shekaru hud’u da suka wuce,sannan har da y’a a tsakanina dake”
Zaro ido tayi tana kallonsa
“Aure,harda y’a?kuma Dani?
Tafad’a cikin rawar murya da kuma mamaki
Ya jinjina Kai
“Eh Rauda,shahida da kika gani y’arki ce kece mahaifiyar ta”
Ta kuma zaro ido tana kallonsa
Yacigaba dacewa
“Zanyi miki bayanin ko ni waye,da kuma yadda akai na aure ki har kika haihu batare da kinsani ba”
🙎🏻
Typing dakwai wahala Allah, muhad’u a Page 13
Yarfillo.
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~*
*~❄We beare’s of soon golden We writer’s assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
🌹 JINNUL
AASHIQUE🌹
🧞♂ 🧞♂
🧞♂
NA
HARIRA ALIYU (y’arfillo)🧕🏻
Dedicated to Little hajjo and my elder sister Hafsat Aliyu
🅿AGE📕 1⃣4⃣
Wannan page d’innaki ne sis maman haidar,allah yak’ara mana k’arfin zumunci atsakaninmu💛💛
Fatan alkhairi ga kowa,allah ya bamu ikon ganin wannan azumi dake gabato mu,ya kuma bamu ikon aikata ayyuka acikinsa,masu ulcer allah yabamu lafiya👏🏻
Sis nabila allah yak’ara lafiya,naji dad’i dakika fara warwarewa allah kawo sauk’i gabad’aya kiyi gyam dan bazamu barki kisha azumi ba ehe🤪🤪🤪
11:09🕒pm
SUN,APR 28✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
Bissmillahir rahmanin rahim👏🏻👏🏻👏🏻
Gefen had’add’en gadon ya zauna,yana kallon kafet d’in dake malale gaban gadon.
Ita ko tana tsaye,tana kallonsa,sai kuma taji babu dad’i ganin yadda yana yinsa ya sauya zuwa damuwa
K’arasawa tayi gabansa,tadurk’usa har lokacin idanuwanta na kansa
“Aasim”
Ta kira sunansa cikin sassanyar murya
Yad’ago suka had’a ido
“Nayi wani abunda ya b’ata maka Raine?
Ya girgiza kai yana k’ak’aro murmushi
“Aa,ko d’aya mekika gani?
Ta kauda idanuwanta da ga ga kansa jin tsigar jikinta nayi mata wani yarrr
“To meyasa yanayinka ya canza?
Ya juyo sosai yana fuskantarta
“Habibty bakiyi min komai ba,kawai dai inajin zuciyata babu dad’i ne,nasan bazaki tab’a min kwatan son danike yimiki ba
Koda na kasance a jinsin d’an adam,bare kuma jinsin rauhan,shiyasa nike jin babu dad’i danna tabbata da ace nakasance a cikin jinsin ki,da zanji dad’i domin ko bakomai zuciyarki zata natsu dani koda baki soni kamar yadda Nike son kiba
STORY CONTINUES BELOW
Amma yanzu zuciyarki ba a natse take dani ba,ina tsoron wata rana ragowar sona daya rage a zuciyarki shima yatafi kamar yadda natsuwar tatafi”
Yak’arasa maganar idanuwansa na rinewa
Tausayinsa taji ya mamaye zuciyarta,shin wani irin so yike mata ne har haka?
Ta tambayi zuciyarta
Murmushin damuwa yayi yana K’ara kallonta
“Wani irin so nikeyi miki kike tunani ko?
Ta kallesa sosai tace
“Ya akayi kasan abunda ke zuciyata?
Ya kuma yin murmushi yana kauda kallonsa akanta
“Ya akayi fa kikace?hmmmmm,
Yad’an numfasa sannan yacigaba dacewa
“Nima kaina bansan dalilin dayasa nike miki irin wannan son me tsanani ba,
Wani zubin har mamakin kaina nikeyi,amma abu d’aya nasani nakuma yarda dashi Allah ne ya jarabceni da k’aunarki,
Rauda dan Allah kitaimakeni koda kwatan son da nike yimiki ne kiyimin,wallahi ina sonki bansan tayaya zan fahimtar dake irin son da nikeyi miki ba”
Yak’arasa maganar yana kama hannunta
Zuciyar tace ta k’ara yin rauni, cikin kwantar mai da hankali tace
“Aasim,ba kace min in kwantar da hankalina ba?kai ma ka kwantar da naka dan Allah,tabbas ayanzu bana cikin natsuwata
Saboda bantab’a tunin al’amarin ka haka yike ba,amma nasan nan da wani d’an lokaci,komai zeyi dede insha’allahu”
Ya sauke gauron numfashi yana kad’a kai
“Shikenan,me kike da buk’ata yanzu?
“Buk’ata??? Kamarya”
Tatambaya cikin rashin fahimta
“Mekike buk’ata,miye kikeso, kifad’a min”
Shuru tayi tana kallonsa dan bata gane me yike nufi ba
Ya mik’e ya bud’e wata durowa yad’auko kwalin waya,sannan yadawo yazauna yana mik’amata
“Nasan kina buk’atar waya,tundaKinfasa taki,ga wannan kiduba idan tayi miki to,idan kuma batayi ba sai a canzo ta yanzu”
Amsar kwalin wayar tayi tana juyawa,wayace iPhone me tsadar gaske
Ta girgiza kai tana mik’amai
“Batayi miki ba?to wace kala kikeso?
Ta kuma girgiza kai a karo na biyu
“Bawai batamin bane,tayi danyi saidai idan aka ganni da ita a gida fa,wa zance yabani?
Yad’an yi shuru sannan yace
“Sai kice saurayin ki ne ya Baki”
“Hmmmmmmmm,wayar dubu d’ari biyun?wani saurayine ze bani kyautarta?ai Sai su tuhumeni,dan kasan yanzu awannan zamanin samari ba sa yin kyauta dan allah”
Ya jinjina kai yace
“Hakane,to fad’i wacce kike ganin babu matsala idan anganki da ita”
Tad’an yi shuru tana nazari daga bisani tace
“Infinix note”
Ya gyad’a kai
“Ook,bayan waya fa sai me kikeso?
“Babu komai”
Tace,ya jinjina kai
“Shikenan,ina ganin muje inkaiki yanzu,naga sak’on ammi tana son ganina”
STORY CONTINUES BELOW
Rauda ta mik’e tana cewa
“To”
Shima mik’ewar yayi yana kallonta
“To haka zaki tafi,babu abunda zaki bani?
Ta kallesa tace
“Babu abunda zanbaka?to mekakeso”
Matsowa yayi gab da ita,yana kallon cikin idonta
“Duk abunda kikaga yadace Dani”
Tayi k’asa da kanta dan bata iya jure kallon cikin idanunsa
“To ni bansan me ya dace dakai ba”
Hmmmmmm yasauke ajiyar zuciya yana d’ago hab’arta
“To shikenan,kibani wad’annan labb’an kawai,masu kama da jar tufa,na minti uku kawai”
“Labb’a?kayi me dasu??
Ta tambaya,be bata amsa ba illa sunkuyo da fuskarsa da yayi dede tata
Ta gane abunda yike Shirin yi, dasauri tak’ara sun kuyar da kanta tana k’ok’orin ja baya
Rik’ota yayi dasauri
“Please habibty,wannan k’aramin abunne bazaki iya min ba”
Ta marai-raice fuska tace
“Nidai ban iya ba,kabari please”
Yayi guntun murmushi
“To ai banace kin iya bane dama,kuma bance kiyi min ba,nida kaina zanyi”
“Nidai…nidai……..
Bata k’arasa ba,taji bakinta cikin nasa
Wani irin yarrrrr taji jikinta nayi,ta lumshe idanuwanta a hankali tanajin gab’ob’inta nafara sarewa
“Habibty!”
Ya kirata,da sassanyar muryarsa data fara taushi
Tabud’e idanuwanta ahankali ta zubasu akansa,amma takasa amsawa
Dan ji tayi illahirin jikinta yayi mata wani iri
Ya kuma yin murmushi
“Ina sonki habibty”
Yafad’a yana rungume ta
K’ara lumshe idanuwanta tayi, tanajin zuciyarta na harbawa da sauri
“Ki kula min da kanki,anjima zamuyi magana”
Tabud’e idanunta zatayi magana,saidai wayam babu shi,takalli inda take
Zauren gidansu ne,gefenta kuma akwatinta ne
Tasauke ajiyar zuciya me nawi,tana jingina da jikin katangar zauren dan har lokacin bata koma dede ba
Maganar wani k’aramin yarone yasa tad’ago daga jinginar da tayi
“Laaa anty Rauda, oyoyo”
Ta yi murmushi tana d’aga shi sama
“Oyoyo my hanif,yaushe kukazo”
Hanif yace
“D’azu nida mummyna”
Ta dire shi k’asa tana jan akwatinta,d’ayan hannunta kuma takama hannunsa suka nufi cikin gida
“Dagaske?ina hanifa?
“Tana d’akin mama tana bacci”
“Eyyeh,tadaina rigima ko haryanzu tanayi?
Dede lokacin suka shiga cikin gidan,da umma tafara cin karo,tana zaune kan tabarma tana gyara wake
“Ina wuni umma?mun same ku lafiya?
STORY CONTINUES BELOW
Umma tad’ago tana yimata wani kallo,sannan ta amsa a dak’ile
“Lafiya”
Bata damu ba dan dama tasaba,tayi gaba
Har zata shiga d’akinsu ta hango inna a kicin, gudun kartayi laifi yasa takoma baya ta tsaya daga bakin k’ofar tana gaisheta
“Ita d’inma a dak’ilen ta amsa,juyawa Rauda tayi ta shiga d’akinsu tana sallama
Mama da anty ummi suka amsa cike da jindad’in ganinta
“Oyoyo auta,oyoyo autana”
Mama tafad’a fuskarta cike da annashuwa
Kusa da maman ta zauna tana kwantar da kanta a kan kafad’ar maman
“Mama wallahi nayi missing d’inki sosai”
Anty ummi ta galla mata harara,cikin wasa
“Dallah jibeki k’atuwa dake kin wani shige jikinta ko kunya bakyaji”
Rauda tayi dariya
“Kedai kice kawai kinji haushi ne,baki zo a auta ba,kuma mama tafi sona a kanki”
Anty ummi takuma harararta
“Ohon miki dai”
Mama dai dariya kawai takeyi
“Kinga ummi zubo mata abinci,kibar min auta ta huta daga isowarta har kinfara damunta?
Anty ummi tayi galala da baki
“Lallaima wannan yarinyar zanzuboma abinci,allah mama ke kike k’ara shawab’ata”
Rauda ta girgiza kai tana dariya
“K’yaleta mama bama najin yunwa,idan naji zan zuba”
Haka suka dinga barkwanci a tsakaninsu
Wacece Rauda?
Cikakken sunanta shine Rauda isma’il
Mahaifinta malan isma’il cikakken ba fulatani ne,yana kasuwancin saida hatsi,
Yana da mata uku,jummai(umma)
Itace uwargida,sai salamatu(inna)
Sannan Maryam (mama),allah ya azurtashi da yara dan umma yaranta takwas uku maza biyar Mata
Inna kuma tana da bakwai,ita kuma duka nata matane
Sai mama,wacce take da uku,dan tayi haihuwa takwas amma uku ne kawai suka tsaya
Kabir, Fatima (ummi) sai Rauda wacce takasance auta
Umma da inna kansu ahad’e yike dan komai tare sukeyi sun had’e ma mama kai babu abunda ke shiga tsakaninsu face kyara da hantara
Mussaman da suka ga tana da hak’uri dan duk abunda zasuyi mata bata tab’a d’aga ido ta kallesu bare tamaida musu martani
Haka suma y’ay’an sun tsani yaran d’akin mama,domin sun fisu kyau nesa ba kusa ba
Hakan yasa sauran y’ammatan suke tsananin jin haushin ummi da rauda dan duk inda suka shiga sai an kallesu
Haka aka dinga aurar dasu duk wad’anda aka ga girmansu yazo d’aya kuma sunsami masu neman auransu
Sai ahad’a su a aurar dasu,sau biyu ana fasa auran Rauda,kuma duka biyun sai ranar d’aurin ake fasawa
Hakan yasa yazama abun Gori,dansu gabad’aya babu wata y’a data rage a gabansu,kullum cikin yada habaici sukeyi
Rauda ganin yadda al’amarin aure yike kasancewa agareta yasa taciresa aranta, ta k’udiri niyyar yin karatu
Mahafinta be hanata ba yabata goyon baya d’ari bisa d’ari dan yana matuk’ar ji da ita acikin y’ay’ansa
STORY CONTINUES BELOW
Hakanko ba k’aramin k’ara basu haushi yayi ba dan su yaransu babu wanda yawuce secondary.
Cigaban labari
Sai yamma anty ummi tafara Shirin tafiya,suna zaune a falon rauda tashiga da akwatinta d’aki dan ta canza kayan jikinta da hanifa tab’ata da tumbud’i
Ta ajiye akwatin tana zaunawa a k’asa ta zage,bandir d’in kud’i tagani rafa na y’an dubu-dubu
Gabanta ne yafad’i,tad’auki kud’in tana juyawa da kuma mamakinsu dan tasan bata ajiye ko biyar acikin akwatin ba
Lokaci d’aya Zuciyarta ta tuno mata da Aasim,takuma fara jin maganar sa acikin zuciyarta
“Habibty,nasan kina buk’atar kud’i shiyasa na ajiye Miki,idan basu isheki ba kisanar Dani,sannan kisanya layinki awayar tana cikin k’aramar jakarki”
Jin motsin za’a shigo yasa tayi saurin rufe akwatin
Anty ummi ce da kwalin wayar a hannunta
“Rauda waya baki sabuwar waya me kyau haka?
Tad’an daburce,dan ganin kud’in ya rud’ata
“Am,am waya…
Anty ummi takalleta sosai tace
“Ke,miye na daburcewa daga tambayarki?
Rauda tayi k’ok’orin dai-daita natsuwarta tace
“Wani sabon saurayi nane”
Anty ummi ya k’walalo ido
“Dagaske?yaushe kuka had’u?
“Watanni takwas kenan”
Wani tsallen murna anty ummi tayi tare da k’arasawa kusa da Rauda ta tsugunna
“Kuma yana zuwa be dena zuwa ba?
(Dayike tun bayan fasa auranta,duk saurayin dayazo baya yin sati biyu yike tafiya,daganan bazata sake ganinsa bama bare wata maganar aure tashiga tsakaninsu)
Rauda ta d’aga kai alamar eh
Wani irin farin ciki ne ya mamaye zuciyar anty ummi
“Kai alhamdulillah kenan,wannan shegen jinnul aashiquen beyi nasara akansa ba,allah yasa shine mijin”
Rauda tasauke ajiyar zuciya tana jin tausayin y’ar uwar tata ganin yadda lokaci d’aya tashiga farin ciki dagajin tasamu saurayin da ya dad’e,bata san cewa shine jinnul aashiquen ba
Maganar anty ummin ce ta katse mata tunanin data tafi
“Miye sunansa?ya kamanninsa suke?kyakkyawane?
Danna sanki da son kyakkyawan mutum
Lokaci d’aya ta yi mata tambayoyin ajere
Shuru Rauda tayi zuciyarta nayi mata wani iri
“Miye sunansa kifad’a min Mana”
Anty ummi ta kuma fad’a cikin zak’uwa
Rauda ta kuma sauke numfashi tana bata amsa cikin sanyin jiki
“Aasim”
Anty ummi tad’ago ido tana kallonta
“Mene?
“Aasim,sunan sa Aasim”
“Aasim?
Anty ummi ta mai-maita sunan fuskarta da d’an alamar mamaki
“Wani kalan sunane wannan?
Rauda ta gyad’a kai alamar bata sani ba
Anty ummi ta ce
STORY CONTINUES BELOW
“Koma dai miye sunansa nidai nayi farin ciki,yaushe zezo?
Kuma acan katsinan yike?
Cikin k’osawa da tambayoyin Rauda tace
“Anty ummi please yanzu kaina ciwo yikeyi,zanzo har gida inbaki labari”
Anty ummi ta mik’e tana tab’e baki
“Ke kenan ai dama,yau ciwon kaza gobe ciwon kaza”
Banza Rauda tayi da ita,ta zura hijabi tana dubanta
“Ni in yanzu zaki tafi muje inrakaki”
Goya hanifa anty ummi tayi tana ma mama sallama
Suka fito,a k’ofar gida suka ci karo da baba yadawoDaga kasuwa,suka rusuna suna gaisheshi
Cikin farin ciki ya amsa yana duban Rauda
“Y’ar albarka,isowar yaushe?
“D’azu baba”
Tabashi amsa cikin ladabi
“Masha Allah,ya karatun? anayi dai sosai ko?
Ta d’aga kai
“Eh baba”
Baba yace
“To Masha’allahu,tashi kirakata,kar duhu yayi,hanif kagaida gida ko”
Suka mik’e anty ummi na mai sallama
Bayan ta dawo daga rakata,tasanya layi a wayar ta kunna
Sak’onninsa ne suka fara shigowa,masu d’auke da kalaman soyayya
Ta na gama karantawa ta ajiye wayar taje takwanta, zuciyarta cike da sak’e-sak’e
Washegari tana gyara falo,mama na zaune tana karatu,ta kwashi kayan da ta wanke tashiga d’aki dan sawa a drower
Tana shiga taji anjanyo ta,kallon sa tayi da sauri
Yana tsaye hannunsa sak’ale da k’ugunta
Zaro ido tayi tana kallon k’ofar d’akin
“Miye haka,idan mama tashigo fa?
Tafad’a cikin murya k’asa-k’asa
Murmushi yayi yana girgiza kai
“Babu wanda ze shigo ayanzu,kuma koma tashigo bazata ganni ba”
“To amma meyasa baka fad’amin zakazo ba?
Ta fad’a
Yasauke guntun numfashi tare da cewa
“Saboda a buk’ace nike da inganki”
Ta sauke numfashi tace
“To nidai kadena zuwa please,banaso a fahimci wani Abu,kabari har inkoma makaranta sai mucigaba da had’uwa”
Zaro ido yayi tare da cewa
“Mene?kema kinsan bazan iya ba,bazan iya ko kwana d’aya batare dake ba”
“Hmmmmm bazaka gane ba,idan kai ba’a ganinka,aini wani zubin za’aga ina magana nikad’ai idan inayi dakai,basai ayi tunanin k’wa-k’walwata tafara samun matsala ba?
Ya jinjina kai
“Hakane,amma kema kinsan baze yuwu indena zuwa gurinki ba,sai dai inkin yadda murink’a had’uwa a gida”
“Gida?
Ta tambaya cikin rashin fahimta
“Eh,inda mukaje jiya”
“Shima kasan baze yuwu ba”
Ya kuma matso da ita jikinsa yana cewa
“Ze yuwu Mana,banace da rana ba ai,da daddare babu wanda ze fahimta”
STORY CONTINUES BELOW
Ajiyar zuciya tasauke
“Naji shikenan,sai anjima”
Tafad’a a gaggauce dan taji motsin mama alamar tana tahowa
Ya gyad’a kai tare da b’acewa
“Ke kuma ke da wa kike magana,nike jiyo magana k’asa-k’asa”
Mama tafad’a yayinda tashiga d’akin
Wuri-wuri da idanu tayi tana neman abunda zatace
“Am,en,waya nayi da y’ar makarantar mu”
Tafad’a tana mata nuni da wayar
Mama bata k’ara cewa komai ba ta koma falo
Dafe k’irjinta tayi dayike dukan uku-uku tana sauke ajiyar zuciya
Da daddare tagama Shirin kwanciya dan mama tuni tayi bacci
Fulo ta janyo ta d’aura kanta tana rufe ido,jitayi iska na kad’a ta ahankali
Ta bud’e ido sai dai a me makon taganta a gadon mama,awannan k’aya taccen gadon taganta
Tashi tayi dasauri tazauna,dede lokacin Aasim yafito daga bayin yana goge ruwan jikinsa daga shi sai k’aramin towel
K’irjinta ne ya buga dam, Dan karo nafarko kenan da tab’a ganin na miji ahaka,gashi babu inda babu gashi ajikinsa yana kwance kan farar fatar dake jikinsa
Murmushi yayi mata yana k’arasowa ya zauna bakin gadon
“Habibty”
“Idan mama tafarka bata ganni bafa”
Abunda tafara cewa kenan
Ya kuma yin murmushi
“Mama bazata farka ba sai asuba,ki kwantar da hankalinki”
“Nidai gaskiya tsoro Nike ji kamaidani dan Allah,sai muyi maganar da zamuyi acan tunda tayi bacci”
“Habibty nace miki bazata ta tashi ba…….
“Nidai kamaidani”
Ta katseshi, kallonta yayi da idanuwansa da cikinsu yafara canzawa
“Banason musu,bazan mai d’aki ba sai asuba”
Shuru tayi tana yin k’asa da kanta
Ya mik’e ya hura mata iskar bakinsa a fuskarta
Jitayi tafara shiga wani yanayi,kamar na bacci kamar na suma,daga nan bata k’ara sanin inda kanta yike ba sai wajen k’arfe uku nadare tafarka
Akwance kusa da ita taganshi,ya zuba mata manyan idanuwansa
Tayi saurin rufe idanuwanta jin jikinta na amsawa
“Rauda!”
Ya kira sunanta,ta bud’e idon ahankali amma bata bari tak’ara kallon cikin idonsa ba
“Rauda ina sonki,rauda ina k’aunar ki,zan iya yin komai akanki”
Tasauke ajiyar zuciya tana mamakin yadda baya gajiya wajen fad’an wad’annan kalmomin
Sai lokacin ta lura da kayan ta dake gefe, tad’an zaro ido gabanta na fad’uwa tace
“Aasim,me kayimin?meyasa kicire min Kaya?
“Me na Miki?abunda nasaba yi dake”
Yabata amsa a tak’aice
Runtse idanuwanta tayi,cikin tsananin damuwa
“Amma meyasa?kenan da inason Abu da banaso zaka rink’a yimin?
Tafad’a cikin dashewar murya
Yasauke gauron numfashi yace
“Rauda baki yadda dani bane?
STORY CONTINUES BELOW
Tabud’e idanuwanta tana k’ok’orin d’aura su akan fuskarsa
“Amma badai-dai bane hakan,nidakai ba jinsi d’aya bane,kuma allah be halatta aure a tsakaninmu ba…….
Katseta yayi ta hanyar rufe mata baki
“Shhhhhh, bantab’a kusantar ki ba,saida aka d’aura aurena dake”
“Amma wayace maka auran ya d’auru?
Juya mata baya yi,dan baya buk’atar jin wad’annan kalaman nata,sosa masa zuciya suke yi
Ita d’inma juya mai bayan tayi,tana mamakin irin wannan al’amari
Saida suka kwashe minti goma ahaka,sannan ya juyo ya na kiran sunanta
Saukowa yayi yadawo gabanta ya durk’usa, idanuwansa sun rine sosai
“Rauda kitaimaki rayuwata kidaina fad’a min irin wad’annan maganganun,nidai ina sonki koma me zakice bazan iya rabuwa dake ba”
Kallonsa kawai takeyi, idanuwanta sun cicciko da hawaye
Wata k’aramar fulawa ce tasauka a hannunsa
Yayi saurin damk’eta yana rufe idanuwansa
“Ya Salam”
Yafad’a cikin tashin hankali
Ita dai kallon sa kawai takeyi,
Yabud’e idanuwan a wahalce yana zuba su akanta
“Sak’one daga sarki,yace yana son ganinmu ni dake gobe”
Mik’ewa tayi da sauri tace
“Mene?Ni,wallahi ba inda zani,nan ma a tsorace nake bare zuwa wata duniya, narok’eka ka taimakeni bakomai k’wa-k’walwata zata iya d’auka ba,kada inga wani abunda ze haukatar Dani”
Tafad’a cikin gigita
Zaunawa yayi yana kama hannunta
“Zuwa ya zama dole Rauda,dan ko ki yarda,ko kar ki yarda ya zamar miki dole kije,babu abunda ze sameki ina tare dake”
Girgiza kai tayi cikin tashin hankali da tsananin tsorata
“Nidai aa, duniyar aljanu fa? kataimakeni indai kana sona kada ka kaini dan Allah”
Ajiyar zuciya yasauke yana k’ara kama wata fulawar da ta sauko daga saman d’akin yakuma runtsewa a hannunsa
Kallonsa takeyi tana jiran jin abunda ze kuma cewa
“Sak’on ammi ne,tace inje yanzu tana son ganina”
Kama hannunsa tayi tana d’an jijjigawa
“Nidai bazan je ba,ka fad’a mishi bazan je ba”
Jitayi ana jijjigata
Dasauri ta bud’e ido,mama tagani zaune ta zuba mata ido
“Ina ne bazaki ba?
Mama ta jeho mata tambayar
Tashi tayi dasauri tafad’a jikinta tana fashewa da kuka
Mama tasauke numfashi tana tofa mata addu’o i
Maman isqah ina godiya,harda k’arfafa gwiwarki yike sawa nike daurewa Allah,amma typing akwai wuya😒
Y’arfillo
JINNUL
AASHIQUE🌹 +
🧞♂ 🧞♂
🧞♂
NA
HARIRA ALIYU (y’arfillo)🧕🏻
Dedicated to Little hajjo and my elder sister Hafsat Aliyu
🅿AGE📕 1⃣4⃣
Wannan page d’innaki ne sis maman haidar,allah yak’ara mana k’arfin zumunci atsakaninmu💛💛
Fatan alkhairi ga kowa,allah ya bamu ikon ganin wannan azumi dake gabato mu,ya kuma bamu ikon aikata ayyuka acikinsa,masu ulcer allah yabamu lafiya👏🏻
Sis nabila allah yak’ara lafiya,naji dad’i dakika fara warwarewa allah kawo sauk’i gabad’aya kiyi gyam dan bazamu barki kisha azumi ba ehe🤪🤪🤪
11:09🕒pm
SUN,APR 28✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
Bissmillahir rahmanin rahim👏🏻👏🏻👏🏻
Gefen had’add’en gadon ya zauna,yana kallon kafet d’in dake malale gaban gadon.
Ita ko tana tsaye,tana kallonsa,sai kuma taji babu dad’i ganin yadda yana yinsa ya sauya zuwa damuwa
K’arasawa tayi gabansa,tadurk’usa har lokacin idanuwanta na kansa
“Aasim”
Ta kira sunansa cikin sassanyar murya
Yad’ago suka had’a ido
“Nayi wani abunda ya b’ata maka Raine?
Ya girgiza kai yana k’ak’aro murmushi
“Aa,ko d’aya mekika gani?
Ta kauda idanuwanta da ga ga kansa jin tsigar jikinta nayi mata wani yarrr
“To meyasa yanayinka ya canza?
Ya juyo sosai yana fuskantarta
“Habibty bakiyi min komai ba,kawai dai inajin zuciyata babu dad’i ne,nasan bazaki tab’a min kwatan son danike yimiki ba
Koda na kasance a jinsin d’an adam,bare kuma jinsin rauhan,shiyasa nike jin babu dad’i danna tabbata da ace nakasance a cikin jinsin ki,da zanji dad’i domin ko bakomai zuciyarki zata natsu dani koda baki soni kamar yadda Nike son kiba
STORY CONTINUES BELOW
Amma yanzu zuciyarki ba a natse take dani ba,ina tsoron wata rana ragowar sona daya rage a zuciyarki shima yatafi kamar yadda natsuwar tatafi”
Yak’arasa maganar idanuwansa na rinewa
Tausayinsa taji ya mamaye zuciyarta,shin wani irin so yike mata ne har haka?
Ta tambayi zuciyarta
Murmushin damuwa yayi yana K’ara kallonta
“Wani irin so nikeyi miki kike tunani ko?
Ta kallesa sosai tace
“Ya akayi kasan abunda ke zuciyata?
Ya kuma yin murmushi yana kauda kallonsa akanta
“Ya akayi fa kikace?hmmmmm,
Yad’an numfasa sannan yacigaba dacewa
“Nima kaina bansan dalilin dayasa nike miki irin wannan son me tsanani ba,
Wani zubin har mamakin kaina nikeyi,amma abu d’aya nasani nakuma yarda dashi Allah ne ya jarabceni da k’aunarki,
Rauda dan Allah kitaimakeni koda kwatan son da nike yimiki ne kiyimin,wallahi ina sonki bansan tayaya zan fahimtar dake irin son da nikeyi miki ba”
Yak’arasa maganar yana kama hannunta
Zuciyar tace ta k’ara yin rauni, cikin kwantar mai da hankali tace
“Aasim,ba kace min in kwantar da hankalina ba?kai ma ka kwantar da naka dan Allah,tabbas ayanzu bana cikin natsuwata
Saboda bantab’a tunin al’amarin ka haka yike ba,amma nasan nan da wani d’an lokaci,komai zeyi dede insha’allahu”
Ya sauke gauron numfashi yana kad’a kai
“Shikenan,me kike da buk’ata yanzu?
“Buk’ata??? Kamarya”
Tatambaya cikin rashin fahimta
“Mekike buk’ata,miye kikeso, kifad’a min”
Shuru tayi tana kallonsa dan bata gane me yike nufi ba
Ya mik’e ya bud’e wata durowa yad’auko kwalin waya,sannan yadawo yazauna yana mik’amata
“Nasan kina buk’atar waya,tundaKinfasa taki,ga wannan kiduba idan tayi miki to,idan kuma batayi ba sai a canzo ta yanzu”
Amsar kwalin wayar tayi tana juyawa,wayace iPhone me tsadar gaske
Ta girgiza kai tana mik’amai
“Batayi miki ba?to wace kala kikeso?
Ta kuma girgiza kai a karo na biyu
“Bawai batamin bane,tayi danyi saidai idan aka ganni da ita a gida fa,wa zance yabani?
Yad’an yi shuru sannan yace
“Sai kice saurayin ki ne ya Baki”
“Hmmmmmmmm,wayar dubu d’ari biyun?wani saurayine ze bani kyautarta?ai Sai su tuhumeni,dan kasan yanzu awannan zamanin samari ba sa yin kyauta dan allah”
Ya jinjina kai yace
“Hakane,to fad’i wacce kike ganin babu matsala idan anganki da ita”
Tad’an yi shuru tana nazari daga bisani tace
“Infinix note”
Ya gyad’a kai
“Ook,bayan waya fa sai me kikeso?
“Babu komai”
Tace,ya jinjina kai
“Shikenan,ina ganin muje inkaiki yanzu,naga sak’on ammi tana son ganina”
STORY CONTINUES BELOW
Rauda ta mik’e tana cewa
“To”
Shima mik’ewar yayi yana kallonta
“To haka zaki tafi,babu abunda zaki bani?
Ta kallesa tace
“Babu abunda zanbaka?to mekakeso”
Matsowa yayi gab da ita,yana kallon cikin idonta
“Duk abunda kikaga yadace Dani”
Tayi k’asa da kanta dan bata iya jure kallon cikin idanunsa
“To ni bansan me ya dace dakai ba”
Hmmmmmm yasauke ajiyar zuciya yana d’ago hab’arta
“To shikenan,kibani wad’annan labb’an kawai,masu kama da jar tufa,na minti uku kawai”
“Labb’a?kayi me dasu??
Ta tambaya,be bata amsa ba illa sunkuyo da fuskarsa da yayi dede tata
Ta gane abunda yike Shirin yi, dasauri tak’ara sun kuyar da kanta tana k’ok’orin ja baya
Rik’ota yayi dasauri
“Please habibty,wannan k’aramin abunne bazaki iya min ba”
Ta marai-raice fuska tace
“Nidai ban iya ba,kabari please”
Yayi guntun murmushi
“To ai banace kin iya bane dama,kuma bance kiyi min ba,nida kaina zanyi”
“Nidai…nidai……..
Bata k’arasa ba,taji bakinta cikin nasa
Wani irin yarrrrr taji jikinta nayi,ta lumshe idanuwanta a hankali tanajin gab’ob’inta nafara sarewa
“Habibty!”
Ya kirata,da sassanyar muryarsa data fara taushi
Tabud’e idanuwanta ahankali ta zubasu akansa,amma takasa amsawa
Dan ji tayi illahirin jikinta yayi mata wani iri
Ya kuma yin murmushi
“Ina sonki habibty”
Yafad’a yana rungume ta
K’ara lumshe idanuwanta tayi, tanajin zuciyarta na harbawa da sauri
“Ki kula min da kanki,anjima zamuyi magana”
Tabud’e idanunta zatayi magana,saidai wayam babu shi,takalli inda take
Zauren gidansu ne,gefenta kuma akwatinta ne
Tasauke ajiyar zuciya me nawi,tana jingina da jikin katangar zauren dan har lokacin bata koma dede ba
Maganar wani k’aramin yarone yasa tad’ago daga jinginar da tayi
“Laaa anty Rauda, oyoyo”
Ta yi murmushi tana d’aga shi sama
“Oyoyo my hanif,yaushe kukazo”
Hanif yace
“D’azu nida mummyna”
Ta dire shi k’asa tana jan akwatinta,d’ayan hannunta kuma takama hannunsa suka nufi cikin gida
“Dagaske?ina hanifa?
“Tana d’akin mama tana bacci”
“Eyyeh,tadaina rigima ko haryanzu tanayi?
Dede lokacin suka shiga cikin gidan,da umma tafara cin karo,tana zaune kan tabarma tana gyara wake
“Ina wuni umma?mun same ku lafiya?
STORY CONTINUES BELOW
Umma tad’ago tana yimata wani kallo,sannan ta amsa a dak’ile
“Lafiya”
Bata damu ba dan dama tasaba,tayi gaba
Har zata shiga d’akinsu ta hango inna a kicin, gudun kartayi laifi yasa takoma baya ta tsaya daga bakin k’ofar tana gaisheta
“Ita d’inma a dak’ilen ta amsa,juyawa Rauda tayi ta shiga d’akinsu tana sallama
Mama da anty ummi suka amsa cike da jindad’in ganinta
“Oyoyo auta,oyoyo autana”
Mama tafad’a fuskarta cike da annashuwa
Kusa da maman ta zauna tana kwantar da kanta a kan kafad’ar maman
“Mama wallahi nayi missing d’inki sosai”
Anty ummi ta galla mata harara,cikin wasa
“Dallah jibeki k’atuwa dake kin wani shige jikinta ko kunya bakyaji”
Rauda tayi dariya
“Kedai kice kawai kinji haushi ne,baki zo a auta ba,kuma mama tafi sona a kanki”
Anty ummi takuma harararta
“Ohon miki dai”
Mama dai dariya kawai takeyi
“Kinga ummi zubo mata abinci,kibar min auta ta huta daga isowarta har kinfara damunta?
Anty ummi tayi galala da baki
“Lallaima wannan yarinyar zanzuboma abinci,allah mama ke kike k’ara shawab’ata”
Rauda ta girgiza kai tana dariya
“K’yaleta mama bama najin yunwa,idan naji zan zuba”
Haka suka dinga barkwanci a tsakaninsu
Wacece Rauda?
Cikakken sunanta shine Rauda isma’il
Mahaifinta malan isma’il cikakken ba fulatani ne,yana kasuwancin saida hatsi,
Yana da mata uku,jummai(umma)
Itace uwargida,sai salamatu(inna)
Sannan Maryam (mama),allah ya azurtashi da yara dan umma yaranta takwas uku maza biyar Mata
Inna kuma tana da bakwai,ita kuma duka nata matane
Sai mama,wacce take da uku,dan tayi haihuwa takwas amma uku ne kawai suka tsaya
Kabir, Fatima (ummi) sai Rauda wacce takasance auta
Umma da inna kansu ahad’e yike dan komai tare sukeyi sun had’e ma mama kai babu abunda ke shiga tsakaninsu face kyara da hantara
Mussaman da suka ga tana da hak’uri dan duk abunda zasuyi mata bata tab’a d’aga ido ta kallesu bare tamaida musu martani
Haka suma y’ay’an sun tsani yaran d’akin mama,domin sun fisu kyau nesa ba kusa ba
Hakan yasa sauran y’ammatan suke tsananin jin haushin ummi da rauda dan duk inda suka shiga sai an kallesu
Haka aka dinga aurar dasu duk wad’anda aka ga girmansu yazo d’aya kuma sunsami masu neman auransu
Sai ahad’a su a aurar dasu,sau biyu ana fasa auran Rauda,kuma duka biyun sai ranar d’aurin ake fasawa
Hakan yasa yazama abun Gori,dansu gabad’aya babu wata y’a data rage a gabansu,kullum cikin yada habaici sukeyi
Rauda ganin yadda al’amarin aure yike kasancewa agareta yasa taciresa aranta, ta k’udiri niyyar yin karatu
Mahafinta be hanata ba yabata goyon baya d’ari bisa d’ari dan yana matuk’ar ji da ita acikin y’ay’ansa
STORY CONTINUES BELOW
Hakanko ba k’aramin k’ara basu haushi yayi ba dan su yaransu babu wanda yawuce secondary.
Cigaban labari
Sai yamma anty ummi tafara Shirin tafiya,suna zaune a falon rauda tashiga da akwatinta d’aki dan ta canza kayan jikinta da hanifa tab’ata da tumbud’i
Ta ajiye akwatin tana zaunawa a k’asa ta zage,bandir d’in kud’i tagani rafa na y’an dubu-dubu
Gabanta ne yafad’i,tad’auki kud’in tana juyawa da kuma mamakinsu dan tasan bata ajiye ko biyar acikin akwatin ba
Lokaci d’aya Zuciyarta ta tuno mata da Aasim,takuma fara jin maganar sa acikin zuciyarta
“Habibty,nasan kina buk’atar kud’i shiyasa na ajiye Miki,idan basu isheki ba kisanar Dani,sannan kisanya layinki awayar tana cikin k’aramar jakarki”
Jin motsin za’a shigo yasa tayi saurin rufe akwatin
Anty ummi ce da kwalin wayar a hannunta
“Rauda waya baki sabuwar waya me kyau haka?
Tad’an daburce,dan ganin kud’in ya rud’ata
“Am,am waya…
Anty ummi takalleta sosai tace
“Ke,miye na daburcewa daga tambayarki?
Rauda tayi k’ok’orin dai-daita natsuwarta tace
“Wani sabon saurayi nane”
Anty ummi ya k’walalo ido
“Dagaske?yaushe kuka had’u?
“Watanni takwas kenan”
Wani tsallen murna anty ummi tayi tare da k’arasawa kusa da Rauda ta tsugunna
“Kuma yana zuwa be dena zuwa ba?
(Dayike tun bayan fasa auranta,duk saurayin dayazo baya yin sati biyu yike tafiya,daganan bazata sake ganinsa bama bare wata maganar aure tashiga tsakaninsu)
Rauda ta d’aga kai alamar eh
Wani irin farin ciki ne ya mamaye zuciyar anty ummi
“Kai alhamdulillah kenan,wannan shegen jinnul aashiquen beyi nasara akansa ba,allah yasa shine mijin”
Rauda tasauke ajiyar zuciya tana jin tausayin y’ar uwar tata ganin yadda lokaci d’aya tashiga farin ciki dagajin tasamu saurayin da ya dad’e,bata san cewa shine jinnul aashiquen ba
Maganar anty ummin ce ta katse mata tunanin data tafi
“Miye sunansa?ya kamanninsa suke?kyakkyawane?
Danna sanki da son kyakkyawan mutum
Lokaci d’aya ta yi mata tambayoyin ajere
Shuru Rauda tayi zuciyarta nayi mata wani iri
“Miye sunansa kifad’a min Mana”
Anty ummi ta kuma fad’a cikin zak’uwa
Rauda ta kuma sauke numfashi tana bata amsa cikin sanyin jiki
“Aasim”
Anty ummi tad’ago ido tana kallonta
“Mene?
“Aasim,sunan sa Aasim”
“Aasim?
Anty ummi ta mai-maita sunan fuskarta da d’an alamar mamaki
“Wani kalan sunane wannan?
Rauda ta gyad’a kai alamar bata sani ba
Anty ummi ta ce
STORY CONTINUES BELOW
“Koma dai miye sunansa nidai nayi farin ciki,yaushe zezo?
Kuma acan katsinan yike?
Cikin k’osawa da tambayoyin Rauda tace
“Anty ummi please yanzu kaina ciwo yikeyi,zanzo har gida inbaki labari”
Anty ummi ta mik’e tana tab’e baki
“Ke kenan ai dama,yau ciwon kaza gobe ciwon kaza”
Banza Rauda tayi da ita,ta zura hijabi tana dubanta
“Ni in yanzu zaki tafi muje inrakaki”
Goya hanifa anty ummi tayi tana ma mama sallama
Suka fito,a k’ofar gida suka ci karo da baba yadawoDaga kasuwa,suka rusuna suna gaisheshi
Cikin farin ciki ya amsa yana duban Rauda
“Y’ar albarka,isowar yaushe?
“D’azu baba”
Tabashi amsa cikin ladabi
“Masha Allah,ya karatun? anayi dai sosai ko?
Ta d’aga kai
“Eh baba”
Baba yace
“To Masha’allahu,tashi kirakata,kar duhu yayi,hanif kagaida gida ko”
Suka mik’e anty ummi na mai sallama
Bayan ta dawo daga rakata,tasanya layi a wayar ta kunna
Sak’onninsa ne suka fara shigowa,masu d’auke da kalaman soyayya
Ta na gama karantawa ta ajiye wayar taje takwanta, zuciyarta cike da sak’e-sak’e
Washegari tana gyara falo,mama na zaune tana karatu,ta kwashi kayan da ta wanke tashiga d’aki dan sawa a drower
Tana shiga taji anjanyo ta,kallon sa tayi da sauri
Yana tsaye hannunsa sak’ale da k’ugunta
Zaro ido tayi tana kallon k’ofar d’akin
“Miye haka,idan mama tashigo fa?
Tafad’a cikin murya k’asa-k’asa
Murmushi yayi yana girgiza kai
“Babu wanda ze shigo ayanzu,kuma koma tashigo bazata ganni ba”
“To amma meyasa baka fad’amin zakazo ba?
Ta fad’a
Yasauke guntun numfashi tare da cewa
“Saboda a buk’ace nike da inganki”
Ta sauke numfashi tace
“To nidai kadena zuwa please,banaso a fahimci wani Abu,kabari har inkoma makaranta sai mucigaba da had’uwa”
Zaro ido yayi tare da cewa
“Mene?kema kinsan bazan iya ba,bazan iya ko kwana d’aya batare dake ba”
“Hmmmmm bazaka gane ba,idan kai ba’a ganinka,aini wani zubin za’aga ina magana nikad’ai idan inayi dakai,basai ayi tunanin k’wa-k’walwata tafara samun matsala ba?
Ya jinjina kai
“Hakane,amma kema kinsan baze yuwu indena zuwa gurinki ba,sai dai inkin yadda murink’a had’uwa a gida”
“Gida?
Ta tambaya cikin rashin fahimta
“Eh,inda mukaje jiya”
“Shima kasan baze yuwu ba”
Ya kuma matso da ita jikinsa yana cewa
“Ze yuwu Mana,banace da rana ba ai,da daddare babu wanda ze fahimta”
STORY CONTINUES BELOW
Ajiyar zuciya tasauke
“Naji shikenan,sai anjima”
Tafad’a a gaggauce dan taji motsin mama alamar tana tahowa
Ya gyad’a kai tare da b’acewa
“Ke kuma ke da wa kike magana,nike jiyo magana k’asa-k’asa”
Mama tafad’a yayinda tashiga d’akin
Wuri-wuri da idanu tayi tana neman abunda zatace
“Am,en,waya nayi da y’ar makarantar mu”
Tafad’a tana mata nuni da wayar
Mama bata k’ara cewa komai ba ta koma falo
Dafe k’irjinta tayi dayike dukan uku-uku tana sauke ajiyar zuciya
Da daddare tagama Shirin kwanciya dan mama tuni tayi bacci
Fulo ta janyo ta d’aura kanta tana rufe ido,jitayi iska na kad’a ta ahankali
Ta bud’e ido sai dai a me makon taganta a gadon mama,awannan k’aya taccen gadon taganta
Tashi tayi dasauri tazauna,dede lokacin Aasim yafito daga bayin yana goge ruwan jikinsa daga shi sai k’aramin towel
K’irjinta ne ya buga dam, Dan karo nafarko kenan da tab’a ganin na miji ahaka,gashi babu inda babu gashi ajikinsa yana kwance kan farar fatar dake jikinsa
Murmushi yayi mata yana k’arasowa ya zauna bakin gadon
“Habibty”
“Idan mama tafarka bata ganni bafa”
Abunda tafara cewa kenan
Ya kuma yin murmushi
“Mama bazata farka ba sai asuba,ki kwantar da hankalinki”
“Nidai gaskiya tsoro Nike ji kamaidani dan Allah,sai muyi maganar da zamuyi acan tunda tayi bacci”
“Habibty nace miki bazata ta tashi ba…….
“Nidai kamaidani”
Ta katseshi, kallonta yayi da idanuwansa da cikinsu yafara canzawa
“Banason musu,bazan mai d’aki ba sai asuba”
Shuru tayi tana yin k’asa da kanta
Ya mik’e ya hura mata iskar bakinsa a fuskarta
Jitayi tafara shiga wani yanayi,kamar na bacci kamar na suma,daga nan bata k’ara sanin inda kanta yike ba sai wajen k’arfe uku nadare tafarka
Akwance kusa da ita taganshi,ya zuba mata manyan idanuwansa
Tayi saurin rufe idanuwanta jin jikinta na amsawa
“Rauda!”
Ya kira sunanta,ta bud’e idon ahankali amma bata bari tak’ara kallon cikin idonsa ba
“Rauda ina sonki,rauda ina k’aunar ki,zan iya yin komai akanki”
Tasauke ajiyar zuciya tana mamakin yadda baya gajiya wajen fad’an wad’annan kalmomin
Sai lokacin ta lura da kayan ta dake gefe, tad’an zaro ido gabanta na fad’uwa tace
“Aasim,me kayimin?meyasa kicire min Kaya?
“Me na Miki?abunda nasaba yi dake”
Yabata amsa a tak’aice
Runtse idanuwanta tayi,cikin tsananin damuwa
“Amma meyasa?kenan da inason Abu da banaso zaka rink’a yimin?
Tafad’a cikin dashewar murya
Yasauke gauron numfashi yace
“Rauda baki yadda dani bane?
STORY CONTINUES BELOW
Tabud’e idanuwanta tana k’ok’orin d’aura su akan fuskarsa
“Amma badai-dai bane hakan,nidakai ba jinsi d’aya bane,kuma allah be halatta aure a tsakaninmu ba…….
Katseta yayi ta hanyar rufe mata baki
“Shhhhhh, bantab’a kusantar ki ba,saida aka d’aura aurena dake”
“Amma wayace maka auran ya d’auru?
Juya mata baya yi,dan baya buk’atar jin wad’annan kalaman nata,sosa masa zuciya suke yi
Ita d’inma juya mai bayan tayi,tana mamakin irin wannan al’amari
Saida suka kwashe minti goma ahaka,sannan ya juyo ya na kiran sunanta
Saukowa yayi yadawo gabanta ya durk’usa, idanuwansa sun rine sosai
“Rauda kitaimaki rayuwata kidaina fad’a min irin wad’annan maganganun,nidai ina sonki koma me zakice bazan iya rabuwa dake ba”
Kallonsa kawai takeyi, idanuwanta sun cicciko da hawaye
Wata k’aramar fulawa ce tasauka a hannunsa
Yayi saurin damk’eta yana rufe idanuwansa
“Ya Salam”
Yafad’a cikin tashin hankali
Ita dai kallon sa kawai takeyi,
Yabud’e idanuwan a wahalce yana zuba su akanta
“Sak’one daga sarki,yace yana son ganinmu ni dake gobe”
Mik’ewa tayi da sauri tace
“Mene?Ni,wallahi ba inda zani,nan ma a tsorace nake bare zuwa wata duniya, narok’eka ka taimakeni bakomai k’wa-k’walwata zata iya d’auka ba,kada inga wani abunda ze haukatar Dani”
Tafad’a cikin gigita
Zaunawa yayi yana kama hannunta
“Zuwa ya zama dole Rauda,dan ko ki yarda,ko kar ki yarda ya zamar miki dole kije,babu abunda ze sameki ina tare dake”
Girgiza kai tayi cikin tashin hankali da tsananin tsorata
“Nidai aa, duniyar aljanu fa? kataimakeni indai kana sona kada ka kaini dan Allah”
Ajiyar zuciya yasauke yana k’ara kama wata fulawar da ta sauko daga saman d’akin yakuma runtsewa a hannunsa
Kallonsa takeyi tana jiran jin abunda ze kuma cewa
“Sak’on ammi ne,tace inje yanzu tana son ganina”
Kama hannunsa tayi tana d’an jijjigawa
“Nidai bazan je ba,ka fad’a mishi bazan je ba”
Jitayi ana jijjigata
Dasauri ta bud’e ido,mama tagani zaune ta zuba mata ido
“Ina ne bazaki ba?
Mama ta jeho mata tambayar
Tashi tayi dasauri tafad’a jikinta tana fashewa da kuka
Mama tasauke numfashi tana tofa mata addu’o i
Maman isqah ina godiya,harda k’arfafa gwiwarki yike sawa nike daurewa Allah,amma typing akwai wuya😒
Y’arfillo
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~*
*~❄We beare’s of soon golden We writer’s assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
STORY CONTINUES BELOW
🌹 JINNUL
AASHIQUE🌹
🧞♂ 🧞♂
🧞♂
NA
HARIRA ALIYU (y’arfillo)🧕🏻
Dedicated to Little hajjo and my elder sister Hafsat Aliyu
🅿AGE📕 1⃣5⃣
Wannan page d’in nakune y’an golden forum,na sadaukar dashi gareku kuyi yadda kukeso da shi🧡🧡
8:00🕒 Am
FRI,MAY 3
Bissmillahir rahmanin rahim👏🏻👏🏻👏🏻
Mama bata k’ara tambayar ta ba,dan tafi kowa sanin matsalar y’arta
Addu’a taci gaba da tofa Mata,bata bari ba harsai da tadawo cikin natsuwata
Lokacin ana kiraye-kirayen sallar asuba
“Kina yin wasa da azkar ko Rauda?
Mama tafad’a tana kallonta
Rauda ta girgiza kai alamar aa
Mama ta cigaba da cewa
“Aa kina wasa dashi banace miki duk sanda zakiyi bacci kiyi alwala ba, sannan kitofa ma jikinki addu’o i?yaushe rabon da kiyi hakan?
Rauda ta yi shuru tana tunani,dan ita rabonta da tayi alwala ko azkar d’in bacci har ta manta
Mama ta girgiza kai cikin damuwa
“Karatun al’qur ani ma kin rabu da yi ko?
Shuru Rauda tayi nanma mik’ewa mama tayi tafice daga d’akin dan d’auro alwala
Rauda ta jingina da jikin gado kanta nawani irin sarawa, gabad’aya yanzu tunanin ta nema yikeyi ya tsaya jitayi kamar ba ita ba
B’angaren Aasim,atsaye ya tadda ammi jikin wata k’atuwar bishiyar da ke cikin sahara
Wacce take gefen shiga masarautar
Kallo d’aya yamata yagano tashin hankali da tsananin damuwa a tare da ita
Kama hannunsa tayi suka zauna suna kallon juna
“Ammi,wai meke faruwa ne naga sak’on me martaba”
Ammi ta sauke numfashi tana bashi amsa
“Akan tarayyarka da Rauda ne,kasan tun bayan haihuwar shahida be kuma cewa komai ba,to jiya abu saima yaje fada
Yike cewa abunda kakeyi sam be dace ba,saboda da wanine yike aikata hakan da tuni an d’auki mataki akansa
Amma saboda kai d’an sarki ne,sai azuba maka ido ak’i cemaka uffan
Shine sarki yaturama sak’on Kira,kafin na turama nawa sak’on sai da naje na sami me martaban akan wani mataki yike shirin d’auka
Shine yace bega laifin abu saima ba,dan tabbas ba adalci bane,kana d’an da ya haifa kana aikata laifuka wanda kaine jigon masarautar,kuma ya zamar maka dole ka rabu da ita,domin auran jinsin d’an adam baya daga cikin tsarin masarauta”
Numfashi Aasim ya sauke,ya na kad’a kai
“Inbanda munafurci meya ruwan abu saima da rayuwata,nafahimcesa tunda nak’i auran y’arsa na nuna banason ta yashiga bak’in ciki Dani”
Ammi tadafasa cikin damuwa tare da cewa
“Nidai duk wannan bashi bane,abunda nikeso da Kai dan Allah ka amince ka rabu da ita, banaso ka bijirewa umarnin da mahaifinka ze baka,nayi maka alk’awarin tara maka kyawawan mata a jinsinka kazab’i wacce tafi maka……..
STORY CONTINUES BELOW
Katseta yayi ta hanyar girgiza kai
“Bazan iya ba ammi,wallahi bazan iya ba,bazan iya rabuwa da ita ba”
Ammi tayi shuru tana kallonsa,durk’usawa yayi agabanta yana kama hannayenta
“Ammi kitaimaki rayuwata dan Allah,ammi bazan iya rayuwa inba tare da ita ba,idan da abunda zaki iya yi kiyi dan Allah”
Yafad’a cikin tsananin damuwa
Ajiyar zuciya ta sauke tana kallon cikin idonsa
“Aasim babu abunda zan iyayi,kasani kai kad’ai gareni bayan kai banida wani d’a aduniya, narok’eka kada ka fusata mahaifinka dan nasan ze iya d’aukar ko wani hukunci akanka,bar ganin yana sonka amma yafi son kimarsa da darajarsa fiye dakai kuma zeyi komai ne abisa adalci”
Aasim ze kuma magana ta had’e mai hannunta guri d’aya
“Kaga dai nice na haifeka amma narok’eka daka bi umarnin da ze baka,banaso wani abu ya sameka kai kad’ai nike dashi aduniya”
Ta k’arasa fad’a hawayen daya cika idanuwanta na gangarowa
Runtse idanuwansa yayi yana cize leb’ansa
Ammi ta mik’e tana kallonsa tare da cewa
“Zan wuce,gobe katabbata dakazo a lokacin da ya baka”
Jingina yayi da jikin bishiyar wasu zafafan hawaye na gangaro Masa
Ya bud’e idanuwansa yana kallon sararin samaniya
“Bazan iya rabuwa da ita ba,ya allah kataimakeni”
Yafad’a cikin damuwa da rashin sanin abunyi
Ita ko Rauda kasa komawa ta kwanta tayi,tunda tayi sallar asuba tana kan darduman
Gabad’aya jinta takeyi cikin damuwa,da kuma tsananin fargaba
Har mama ta kammala abun kari ta dawo d’akin bata tashi daga kan darduman ba
“Wai ke lafiyan ki k’alau kuwa? kintashi bazaki je kigaida baban ku ba”
Mik’ewa tayi jikinta babu k’wari,ta ninke dar duman tana yin hanyar waje
Mama ta dakatar da ita ta hanyar kiran sunanta
“Rauda”
Rauda ta juyo tana amsawa
“Na’am”
“Meke damunki?
Mama ta tambaya tana tsare ta ido
Girgiza mata kai Rauda tayi
“Babu komai,banjin dad’ine kawai kai na ke ciwo”
Mama ta gyad’a kai had’i da cewa
“Shikenan jeki gaishe sa kidawo kisha magani”
Jinjina kai tayi tare da ficewa
Da sallama ta shiga d’akin Abba
Ya amsa,ta tsugunna tana gaishesa
Amsawa yayi yana kallon ta a tsanake
“Raudatu baki da lafiya ne?
Ta k’ak’aro murmushi tana cewa
“Aa baba,kaina ne ked’an min ciwo,shima kuma ba sosai ba”
Ya kad’a kai yace
“To tashi kije ki karya kisha magani,idan bedena ba anjima idan nadawo kasuwa sai inkaiki chemist”
“To”
Tace tare da mik’ewa tafito daga d’akin
Kan gadon mama tadawo takwanta
Tana jin maganar sa a cikin zuciyarta
STORY CONTINUES BELOW
“Habibty,anjima da daddare zamu tafi”
Shuru tayi tana lumshe idanuwanta,mama tadawo d’akin hannunta rik’e da kofin tea da paracetamol
Ta amsa tasha,tasha maganin sannan ta koma ta kwanta
Ranar mama ce da girkiDan haka bata zauna ba,tana ta ayyuka, Rauda tayi k’ok’orin fitowa ta tayata amma tace aa taje takwanta tunda bata jin dad’i
Wunin ranar haka Rauda tayi shi sukuku
Da yamma, tana bayi zatayi wanka ta tasa ruwan agaba tana kallo
Wani haske tagani ya b’ullo cikin bayin,sai ga Aasim ya bayyanaKallo d’aya suka ma juna suka gano damuwar da kowanensu yike ciki
Kauda kanta tayi daga kansa, gabanta na fad’uwa
Shiko wani kalar abune ya k’ara sukar sa,Wanda yasan tsan-tsar k’aunar tane
Tayaya ze iya rabuwa da wannan kyakkyawar halittan?
Yasan akwai kyawawan mata a duniya amma bega tamkar ta ba, tabbas baze iya rabuwa da ita ba
Gab da ita ya tsaya,dan tana jingine ne da bangon bayin
“Rauda”
Ya kira sunanta,ta juyo da kanta tana kallonsa ba tare da ta amsa ba
Shima shuru yayi suka kalli juna na y’an wasu sakwanni sannan yace
“Meyasa kika tada hankalinki?ba wani abun tsoro zaki gani ba idan munje,zaki ga kowane a suffar mutane kamar yadda kike ganina,kuma sannan ina tare dake,babu wani abun da zesa meki”
Juyawa tayi da niyyar fita daga bayin
Yasa hannu ya dafe bangon ya tare mata hanyar
“Rauda ki yarda dani, wallahi bazan cutar da ke ba”
Kallonsa tayi da idanuwanta da suka fara cikowa da hawaye
“Aasim,dan allah ka rabu Dani, kabarni inji da abunda yike damuna please”
Tak’ara sa fad’a tana tana juyawa da sauri ta d’ayan gefen
Jitayi ya rungumo ta tabaya,tayi saurin runtse idonta danji tayi illahirin jikinta ya amsa
Nannauyan numfashi yasauke yana sak’alo kansa ta gefen wuyanta
“Rauda,ina sonki,nasan kema kina sona dan allah kada kik’ara ambaton in rabu da ke”
Juyowa tayi dasauri,still Tana rungume a jikinsa,suna fuskantar juna
“To in ina sonka fa?yazanyi, zanciga ba da rayuwa dakai ne ahaka?
Meyasa kakasance a wani jinsi meyasa?
Tak’arasa fad’a tana fashewa da kuka
“Aasim ina sonka,dan girman allah idan mafarki nikeyi cewa kai ba mutum bane ka tasheni,nayi alk’awarin bazan sake yin baccin ba bare inkuma yin makamancin irinsa”
Tausayinta had’i da k’aunarta suka sake mamaye mai zuciya
K’ara rungumeta yayi yana runtse idanuwansa,cikin tsananin damuwa
Sai da suka kwashi minti biyar ahaka,sannan ya d’agota yana kallon kyakkyawar fuskarta data jik’e sharkaf da hawaye
“Rauda,nayi alk’awarin zan rayu dake ako wani irin yanayi, zanyi miki komai kamar yadda jinsin ki zeyi Miki,dan allah ki kwantar da hankalinki kinji?
Ta bud’e jik’akk’un idanunta tana kallonsa kawai batare da ta ka’ra cewa wani abu ba
Hannunsa yasa yana share mata hawayen
STORY CONTINUES BELOW
“Kinsan abunda natsana shine ganin hawayenki,shine abunda ke tada min da hankali,kibar yimin asarar su please”
Ya d’an numfasa sannan yacigaba da cewa
“Kinsan ya fuskarki take komawa idan kina kuka?
Ta tsaresa da kyawawan idanuwanta tana kallon yadda yike ya mutsa fuskarsa alamar haka tata fuskar take komawa idan tana kuka
Murmushi tayi,duk da batayi niyyar yi ba
Ya dafa kafad’unta yace
“Yauwa kokefa, Baki ga kinfi kyau ba”
Ya k’arasa fad’a yana sauke ajiyar zuciya
“Bari inbarki kiyi wankan,anjima dai kar ki manta”
Gyad’a masa kai kawai tayi,yayi murmushi tare da manna mata kiss a goshi
Ta sauke doguwar ajiyar zuciya bayan b’ace warsa sannan tayi wankan a sanyaye
Da daddare,misalin k’arfe goma,mama tagama Shirin ta tana mik’ewa
“Kisamin sakata a k’ofa,kada kibar min k’ofa ta kwana a bud’e sannan kiyi addu’a kafin ki kwanta”
“To”
Rauda tace,mama ta fice daga d’akin tana janyo mata k’ofa
Rauda tamik’e ta sa sakata a k’ofar falon sannan ta dawo ta zauna tana d’aukar wayarta dake k’ara
Numban Salma tagani,ta d’auka tana sallama
Daga can b’angaren salma tace
“Mara kirki,tunda baki kira kinji ya na sauka ba nina kiraki”
Rauda ta yi murmushi
“K’awa kina Raina,ya kike”
“Habibty”
Taji an fad’a abayan ta,ta waiga Aasim tagani
Ajiyar zuciya ta sauke tana cewa salma
“Bari zankira ki ina zuwa”
Ta katse wayar tana kallon sa
“Muna iya tafiya?
Yatambaya,ta jinjina masa Kai alamar eh
A cikin y’an sakwanni taganta acikin sahara,babu gida gaba babu gida baya
Kallonsa tayi k’irjinta na dukan uku-uku
Amma takasa yin magana
“Abun hawa na hanyar zuwa yad’auke mu”
Begama rufe baki ba saiga wasu dokuna guda biyu,d’aure da wata kujera ta zaman mutum biyu da rumfa a samanta
Saurin rik’esa tayi,dan girman dokunan ya wuce misali,wani irin tsoro yafara d’arsuwa acikin zuciyarta
Aasim ya lura da hakan,ya yi mata murmushi cikin k’arfafa mata gwiwa
“Habibty kada kiji tsoro kinji?muje”
Yak’arasa fad’a yana kama hannunta,babu yadda ta iya suka shiga suka zauna,dokunan suka juya inda suka fito a guje
Rauda ko mamakine da aljabi ya dabai-bayeta
Gabad’aya gurin Sahara ne,amma kuma ga wasu bishiyoyi masu shegen kyau dasukayi ma wurin ado
Daga nesa ta hango wani katafaren gari wanda katanga ta za gayesa
Jitayi tsigar jikinta ta tashi yarrr
Ta yi saurin runtse ido tana ambaton sunan allah
Kallonta Aasim yayi ganin yanayin data fara shiga
STORY CONTINUES BELOW
Yasa ya kama hannunta ya damk’e cikin nasa
Ahankali taji tsigar jikin ta dena tashi,suka kalli juna yayi mata murmushin k’arfin Hali dan gabad’aya hankalinsa a tashe yike
A k’ofar garin dokunan suka tsaya,wacce take a kulle
K’ofar tana da fad’in gaske,tsayawar dokunan keda wuya k’ofar tabud’e
Wasu zabga-zabgan mutane Rauda tagani masu matuk’ar girma sanye da bak’ak’en kaya da wasu manyan takobi ahannayensu
Idanuwannasu jawur kamar gauta,tayi saurin rufe idanuwanta k’irjinta nawani mugun bugawa
Maganar su ce tasa tabud’e idon dasauri jin muryoyinsu a kausheshe
Gabad’ayan su zubewa sukayi a k’asa suna fad’in
“Barka da isowa,yarima,allah shi baka nasara”
Ya d’aga masu hannu yanayi musu magana da wani yare
Nan da nan suka basu hanya,dokunan suka cigaba da tafiya
Rauda sakin baki tayi tana kallon cikin masarautar,da tsayawa fasalta ta b’ata lokacine
Ga mutane kala-kala iri-iri kuma duk inda suka gifta sai sun zube suna kwasar gaisuwa
Kallonsa tayi taga kayan jikinsa sun sauya zuwa kayan sarauta,idanuwansa ma k’wayar ciki sun tashi daga bak’in dasuke sun koma wani kala
Shima d’in tsoro yabata,ta k’an-k’anme jikinta tana ambaton sunan allah
Cikin sauri yace
“Rauda,yazamarmin dole inkoma yadda nikene,ki kwantar da hankalinki dan allah,”
Bata sauraresa ba tacigaba da karantasu addu’o i, jikinta na kakkarwa
Bata yadda tak’ara bud’e idanuwanta ba harsaida taji dokunan sun tsaya
Tabud’e idanuwanta a tsorace tana kallon inda suke
Wani k’ayataccen wurine me shegen kyau daga can gabansa kuma wata k’atuwar fada ce
Inda take hango wasu sanye da fararen kaya zazzaune
Ta kuma runtse idanuwanta tana fad’in
“Aasim,kataimakeni kamayar dani”
Hannunta yakama yana karanto wasu abubuwa da batasan ko menene ba
Take taji tsoron da takeji yatafi,sai abunda ba a za rasa ba
Takuma bud’e idanuwan ahankali tana watsasu akansa
“Habibty babu abunda zesameki,mutafi fada,kuma idan munje duk abunda kiga nayi kiyi irinsa kinji?
Gyad’a masa kai tayi tana bin bayansa
Har k’ofar fada, gabad’aya wad’anda ke zazzaune rusuna masa sukayi suna kwasar gaisuwa
Banda wani me kama da larabawa da ya hakimce a kan wata kujerar zinari
Aasim ya rusuna agabansa,itama Raudan ta rusuna kamar yadda taga yayi
Aasim yace
“Allah ya taimaki me martaba”
Sarki Ramzad ya kad’a kai batare da ya amsa ba
Mik’ewa Aasim yayi suka d’anyo baya sannan ya zauna,itama ta zauna kamar yadda yayi
“Yarinya!
Sarki Ramzad yafad’a yana kallon Rauda
Ta kallesa batare da ta amsa ba, gabanta na fad’uwa
“Shin kinsan waye Aasim?
Ya tambaya still idanuwansa na kanta
Nan ma shuru tayi,dan bata da bakin magana
STORY CONTINUES BELOW
Sarki Ramzad ya cigaba da cewa
“Aasim d’ane,kuma magaji a wannan masarauta,sannan kuma rauhani”
Ya d’an numfasa kad’an,sannan ya cigaba da cewa
“Amma duk da sanin hakan,kika amince zaki cigaba da rayuwa da shi?
Nayi miki uzuri,awancan lokacin domin ko kina cikin rashin sani,amma ayanzu zan yanke hukunci a bisa saninki”
Ya maida kallonsa kan Aasim yana ambaton sunan sa,
Aasim yad’ago da kansa k’irjinsa na bugawa
“Ina buk’atar ka furta kalmar saki,ayanzunnan sannan kayi alk’awarin rabuwa da ita,taje ta auri jinsinta”
Cikin kad’uwa da jin kalaman mahaifinsa ya zube,cikin tashin hankali yace
“Kayi min afuwa,abi bazan iya furta kalmar saki a gareta ba”
Sarki Ramzad ya had’e fuska ya kuma mai-maita abunda yace
Nan d’inma kuma zubewar yayi
“Abi kataimaki rayuwata, wallahi ita kad’ai nikeso bazan iya rayuwa idan babu ita ba”
Sarki Ramzad ya kad’a kai yace
“Amma kasan a dokar masarautar mu babu auran jinsin bil’adama ko?
Aasim ya jinjina kai
“Nasani abi,amma kayimin rai kabarni naciga ba da rayuwa tare da ita”
Sarki Ramzad ya girgiza kai
“Abune da baze tab’a yuwuwa ba kana d’an dana haifa inbarka ka sab’awa shari’ar masarauta,dan haka ka furta saki agareta”
Ammi dake gefe ta taso cikin tashin hankali ta wanka masa mari
“Baka da hankali ne Aasim?da mahaifinka kake jayayya?
Sarki Ramzad ya d’aga mata hannu
“Ya Isa,ki k’yaleshi zanga iya kafiyarsa dakuma taurin kansa”
Komawa tayi inda take,tanayi ma Aasim wani kallo me cike da bada umarnin ya aikata abunda akace Masa
“Na baka minti biyar,ka aiwatar da abunda nace”
Sarki Ramzad yafad’a cike da k’asaita
Aasim ji yayi kamar kansa ze juye saboda tsananin tashin hankali
Gabad’aya fadar tayi tsit,kowa maganar Aasim yike jira
Ahaka har minti biyar d’in tayi
Sarki Ramzad ya sauke numfashi tare da cewa
“Bazaka bi umarnina ba kenan?
Aasim jan gwiwowinsa yayi zuwa gabansa ya fashe da kuka
“Abi, kagafarceni bazan iya rabuwa da ita ba”
Runtse ido sarki Ramzad yayi,cike da tsananin takaici
Yabud’e su ya watsa su akansa
“Aasim akan bil’adama kake jayayya Dani?
Aasim ya kuma fashewa da kuka
“Ni me biyayya ne agareka abi,amma ina rok’onka da ka yimin agaji”
Sarki Ramzad ya jinjina kai yana kallon me fad’an hukunci
“Miye hukuncin duk wanda ya karya dokar masarauta?kuma akace ya bari ya yak’i bari”
Me fad’an hukunci yayi shuru,yana tunanin abunda zece ganin d’an sarki ne dakansa
Sarki Ramzad ya katse mai tunani ta hanyar cewa
“Kada kayi la’akari da wai d’anane,kafad’i hukuncin da ya rataya akanshi”
STORY CONTINUES BELOW
Me fad’an hukunci yasauke numfashi tare da cewa
“Za’a koresa daga masarautar gabad’aya”
Sarki Ramzad ya jinjina kai yana kallon Aasim yace
“Kaji hukuncin da ya rataya akan duk wanda ya aikata laifi irinnaka,dan haka sai ka zab’a cikin biyu,
Ko kasaketa karabu da ita,ko kuma ka bar masarautar gabad’aya”
“Abi ni d’anka ne,kaji tausayina……..
Sarki Ramzad ya katsesa
“Tunda ni amatsayina na mahaifinka ban isa inbaka umarni kabi ba,yazamar min dole ind’auki hukunci akanka,dan haka fad’i ina jiranka,wane kazab’a”
Yak’arasa fad’a cikin d’aga murya
“abi,kayi hak’uri ka gafarceni……..
“Nace kazab’a d’aya ko?
Sarki Ramzad ya katsesa a fusace
Kallon Rauda yayi wacce gabad’aya itama hankalinta ya gama ta shi
Ya maida kallonsa ga me martaba da yike cewa
“Zan irga uku,idan har na irga uku baka saketa ka rabu da ita ba,to tabbas zaka bar min masarauta”
“D’aya…..
Biyu……..
Cikin tashin hankali Aasim yace
“Abi dan girman allah………
Sarki Ramzad ya d’an dakata yana jiran jin abunda zece
Amma kuma sai yayi shuru,yana cize leb’ansa da k’arfi tare da runtse idanuwansa
“Uku”
Me martaba yafad’a,ammi ta taso da sauri tana jijjiga Aasim
“Aasim,kadawo hayyacinka,takan mace,macen ma bil’adama zaka zab’i rabuwa da ahalin ka,maza ka rok’i gafarar mahaifinka ka aiwatar da abunda yace”
Tafad’a a zafafe cikin kid’ima
Bud’e idanuwan sa Aasim yayi yana zuba su akanta
“Ammi kigafarceni,bazan iya rabuwa da ita ba…”
Yafad’a cikin zafin zuciya
Ammi baya tafara ja tana girgiza kai
“Aa,aa, Aasim kada kayi min haka”
Abu saima ne ya mik’e shima cikin tashin hankali dan betab’a zaton Aasim ze zab’i barin masarautar akan Rauda ba,ga saima can tana kukan inda babu shi bazata iya rayuwa ba,kuma shi yayi hakanne dan sama ma y’arshi farin ciki dan yasan idan Aasim yarabu da Rauda dole ze auri saima
“Yarima kasan hukuncin duk wanda ya zab’i barin masarauta kuwa? Dole fa sai ka bi ta tauran
(Tauran wani wurine zagayayye,da yike da k’unci da zafi, Wanda duk bayan minti biyu yike fitar da wani k’ara me kama da sautin tsawa,wanda duk wanda yike ciki sai hucin k’arannan ya tsattsaga jikinsa)
Abu saima ya cigaba da cewa
“Wanda sanin kankane sai rauhan yatsaya acikin tauran har sai ya tsallake k’arar tauran guda arba’in da tara,shin kamanta da azabar dake cikin tauran ne?
Aasim yayi masa wani kallo me cike da tsana dan inba da din munafuncinsa ba da yanzu wannan abubuwan basu faru ba
“Nasani,kuma na amince ko da hakan zeyi sanadiyyar rasa rayuwata ne”
Gabad’aya fadar zaro ido sukayi cike da al’ajabi
Rauda da jikinta ya gama mutuwa hawaye suka gama wanke mata fuska saboda tsananin tausayin Aasim,shin wani irin so yike mata da ze zab’i rabuwa da ahalinsa saboda ita?
STORY CONTINUES BELOW
Cikin kuka ta matsa kusa dashi tana fad’in
“Aa Aasim,kada ka bijirewa umarnin iyayenka akaina”
Girgiza kai yayi yana kallonta da idanuwansa da suka rine
“Rauda ina k’aunar ki,zan iya hak’ura da komai inhar zan rayu dake”
Sarki Ramzad da jikinsa yagama yin sanyi duk da b’acin ran dayike ciki kukan d’annasa na tab’a masa zuciya
“Na baka daganan zuwa gobe,kaje kanatsu kayanke wa kanka abunda yafi maka,wannan ne adalci na k’arshe da zan maka
Idan har ka amince da rabuwa da ita,to kazab’i ko y’ar sarkin wace k’asa ce zan aura ma ita
Idan kuma har kakai goben kana kan bakanka na k’in rabuwa da ita to tabbas zaka bar min masarauta
Sannan kuma zaka tsallake tauran ninki biyu, d’aya na barin masarauta d’aya kuma na jayayya dani”
Bubbuga k’ofar da akayine ya sa Rauda ta tashi,akan gadon mama ta ganta
Tana jiyo muryar maman tana cewa
“Kitashi kiyi sallah”
Dafa kanta tayi da yike sarawa kamar ze rabe biyu tana girgiza shi
“Aasim,kada kayi haka dan Allah”
Y’arfillo.
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~*
*~❄We beare’s of soon golden We writer’s assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
JINNUL*
*AASHIQUE*🌹 +
🧞♂ 🧞♂
🧞♂
NA
HARIRA ALIYU _(y’arfillo)_🧕🏻
_Dedicated to little hajjo and my elder sister Hafsat Aliyu_
🅿AGE📕 1⃣6⃣
Ina yima ɗaukancin masoyana barka da sallah, dafatan anyi sallah lafiya, wannan Page na baku shi amatsayin barka da sallah, sannan ina me baku haƙuri akan jina shuru da kuka yi bani da lafiya ne ina buƙatar addu’arku
_7:32_🕒 PM
FRI, JUN 7
_Bissmillahir rahmanin rahim_
“Aasim kada kayi haka,kada kayi haka dan Allah”
Tafad’a cikin tsananin damuwa
Bubbuga k’ofar mama ta kuma yi akaro na biyu
Cikin rashin k’warin jiki ta mik’e jiri na d’ibarta,ga kanta da yayi mata mugun nawi tana jin kamar an d’aura mata gingimemen dutse
Ta zare sakatar falon tana jingina da bango da sauri,dan ji tayi tana neman fad’uwa
Mama ta kalleta sosai tace
“Haryanzu kan bedena ciwon bane?
D’aga mata kai kawai tayi batare da tayi magana ba
Mama tasauke numfashi cikin damuwa tace
“Sannu,ina ganin idan gari yayi haske kawai zamu je k’aramin asibiti adubaki, k’ilan harda typhoid,kidaure kiyi sallan”
To Rauda tace tafito ta d’au buta tayi alwala,tana rawar sanyi
Lokaci d’aya zazzab’i me zafi ya rufeta,
A gaggauce tayi sallar saboda sanyin datake ji sosai,tana idar da sallar ta koma kan gado ta lullub’e
B’angaren Aasim kuwa,tunda taron fada ya tashi,yashige d’akinsa tare da kullewa dan gabad’aya baya son a damesa
STORY CONTINUES BELOW
Yana jiyo muryar ammi daga bakin k’ofar tana fad’in ya bud’e
Amma yak’i saboda baya son yaga tashin hankalin dake tare da ita,harta gaji ta wuce
Ya na zaune a k’asa kawai, cikin tsananin tashin hankali
K’wan-k’wasa k’ofar aka kuma yi,yaja gajeren tsaki tare da kifa kansa
Daga can k’ofar d’akin muryar mus’ab yaji Wanda ya kasance babban amininsa
Hannunsa ya d’aga yayi nuni da k’ofar, tabud’e
Mus’ab ya shiga d’akin Yana fad’in
“Wai meke damunka ne Aasim? Ace tun daren jiya ka kulle kanka a d’aki kakuma sawa d’akin takunkumi tayadda bawanda ze iya shigowa”
Aasim numfashi ya sauke yana d’auke kansa da ga kan mus’ab
“Kawai banaso a dameni ne,ina buk’atar natsuwa ne”
Mus’ab ya jinjina kai yace
“Hakan yayi kyau,inafatan a natsuwar da kasamu ka canza abunda ke zuciyarka,
Dan nasan jiya kana cikin rud’ani ne,shiyasa kak’i yin abunda me martaba ya umarce ka”
Aasim Ya sauke gauron numfashi tare da lumshe idanuwansa wad’anda suka kad’a sukayi ja
Mus’ab ya gyara tsugunnuwar da yayi yana k’ara fuskantar Aasim d’in
“Kayi shuru,ba kace komai ba,ko haryanzu kana kan bakannaka?
Ya bud’e idanuwansa yana d’aura su akan mus’ab
“Mus’ab,bazan iya rabuwa da ita ba,bazan iya ba”
Yafad’a cikin wani irin yanayi
Zaro ido mus’ab yayi yana kallonsa cike da mamaki
“Mekake nufi Aasim?kana nufin kazab’i rabuwa da ahalinka,takan bil’adama?
Yad’an numfasa sannan ya cigaba da cewa
“Ni wallahi banga abunda kagani agurin waccan bil’adamar ba,da yasa gabad’aya ka rikita tunaninka,
Dan allah kadawo cikin hankalinka,akwai kyawawan mata aduniya,ga kuma saima……….
Katsesa yayi ta hanyar d’aga masa hannu
“Dan allah kada ka k’ara b’ata min Rai,ni ita nike so kuma ita na zab’a zanyi rayuwa da ita,abunda nagani da ya rikita min tunani akanta kuma
Wannan ba damuwar ka bane,idan zaka bani shawara a matsayinka na aboki na kabani,idan kuma maganganun banza kazo kafad’a min ga hanya”
Ya k’arasa fad’a yana nuna mai hanyar fita
Mus’ab ya sauke ajiyar zuciya cike da juyayin al’amarin abokinnasa
“Aasim nikake fad’a ma haka?
Aasim ya d’aga kai yace
“To mekake so ince maka? A matsayinka na aminina kamata yayi kabani shawarar yadda zanyi insamu mafita amma kazo kana fad’a min abunda kasan ze k’ara min b’acin ran danike ciki”
Mus’ab yakuma sauke numfashi yana kad’a kai
“Shikenan,allah ya baka hak’uri”
Yafad’a yana mik’e wa ze fita
Sannan yace
“Bazan takuraka ba,akan fasa abunda kayi niyya,amma ina me baka shawara da kada ka bijirewa umarnin mahaifinka,katuna da haihuwar ka da yayi,da kuma rainonka har izuwa girmanka ko ba komai yaci wannan arzik’in “
Yana gama fad’ar haka ya fice
Doguwar ajiyar zuciya Aasim ya sauke tare da jinginar da kanshi
Tabbas yasan abunda yike shirin yi ba dai-dai bane,to amma ya zeyi? Ya zeyi da muradin zuciyarshi?
STORY CONTINUES BELOW
Ya runtse idanuwansa yana hango kyakkyawar fuskarta
“Bazan iya rayuwa babu keba *Rauda*”
Yafad’a tare da furzar da wata iska me zafi
Mik’ewa yayi yana fad’in
“Nasan zaka fahimceni abi,idan nak’ara yimaka bayanin yadda nike jinta a cikin zuciyata”
B’acewa yayi,be bayyana a ko ina ba sai abakin falon sarki inda yike hutawa
Kallo d’aya yayima kuyangin dake tsattsaye bakin k’ofar ya kauda kai tare da cewa
“Ku isar da zuwa na”
D’aya da ga cikinsu wacce take daf da k’ofar tace
“Yarima Aasim na buk’atar iso ranka shi dad’e”
Tafad’a cikin d’aga murya
Daga ciki aka basu izinin su bud’e k’ofar
Suka bud’e suna rusunawa
Gabanshi na fad’uwa ya shiga k’asaitaccen falon da akayi masa ado da zinarai kala-kala
Sarki Ramzad na zaune kan wata kujera me d’an fad’i ya jingina idanuwansa a lumshe
Shigowar Aasim d’inne yasa ya bud’e idanuwansa yana zubasu akansa
Cikin ladabi Aasim ya rusuna yana fad’in
“Barka me martaba,ina fatan kana cikin k’oshin lafiya”
Sarki Ramzad ya ce
“Lafiya,Ina fatan kaima haka?
Aasim yace
“Nima ina lafiya”
Sarki Ramzad ya gyad’a kai yana kauda kansa daga kallonsa
“Me ke tafe dakai?
Aasim ya d’an yi shuru sannan yace
“Inason magana dakai ne”
Jinjina kai sarki Ramzad yayi yana yima wazirin sa nuni da hannu alamar yafita ya basu guri
Cikin girmamawa wazirin ya rusuna tare da b’acewa
Sarki Ramzad ya maida hankalinsa kan Aasim yana cewa
“To ina jinka,fad’amin abunda kayanke ko sai munje fada tukunna?
Aasim ya sauke numfashi yana mik’e wa ya k’arasa gaban sa
Ya durk’usa tare da d’aura kansa a kan k’afafuwan mahaifinsa
Wasu hawaye masu zafi suka shiga gangarowa daga idanuwansa
Sarki Ramzad ya sauke numfashi tare dasa hannunsa yadafa bayan sa
Tabbas babu abunda yi keso sama da Aasim, yana matuƙar jinsa acikin zuciyarsa
Kuma babu abunda yafiso irin yaga Aasim cikin farin ciki
Amma dole ne ya dakatar dashi
Cikin kwantar da hankali yace
“Aasim, ka sani bawai na hanaka abunda kake so bane, dan jin daɗina
A’a, saboda adalci ne, domin babu wani rauhani daya isa yayi haka a ƙyalesa, Kaga ko bekamata na ƙyaleka ba dan kana ɗan dana haifa
Kasani da zarar akace babu ni, to kaine mai mulkin wannan masarautar
Ya kamata ka fahimce ni, nayi maka alƙawarin ko ƴar gidan wacece idan Kaga tayi maka zan auramaka in har a jinsin ka ce
Amma baze yuwu in barka ka cigaba da rayuwa da bil adama ba bazeyu ba”
STORY CONTINUES BELOW
Aasim ya ɗago kansa cikin muryarsa da ta dishe yace
“Abi,dan Allah kabarni nayi rayuwa tare da ita,ita kaɗai nike so banajin zan iya rayuwa da wata mace a duniya in ba ita ba……..
” dakata!
Sarki ramzad ya katse sa, sannan ya cigaba da cewa
“nabika ta faɗa bakaji ba, na bika ta lallami nanma bakaji ba
To kasani bazan takura ka ba, tunda har ban isa dakai ba, nan da awa ɗaya zamu je fada, duk abunda kayanke kafaɗa acan”
Aasim ze kuma magana ya dakatar dashi ta hanyar ɗaga masa hannu
“bana son na kuma jin komai daga gareka, tashi ka bani wuri”
“Abi…..
Be ƙarasa ba, sarki ramzad yasa hannu ya ɓatar dashi
Ƙarfe takwas suka isa ƙaramin asibitin gwamnatin, sun tadda mutane da yawa akan Layin ganin likita
Hakan yasa suka zauna suna jiran layi yazo kansu
Kallo ɗaya zakama Rauda, kagano ramar da tayi acikin kwana ɗaya kacal
Kallon jama’ar dake wurin kawai take yi amma zahiri hankalinta baya gurin
Damuwarta ta kuma ƙaruwa yayin da taga har zuwa lokacin bata ji wani alamun Aasim ba,
Me ya faru dashi, bayan dawowarta? Shin ya amince ya rabu da itanne ko yaya?
Tambayar da tayi ma kanta kenan wacce bata da amsar ta
Maganar sa ce ta dawo mata
_”Rauda ina ƙaunarki, zan iya haƙura da komai inhar zan rayu dake”_
“baze amince ya rabu dani ba nasani”
Tafaɗa a fili batare da tasan maganar ta fito filin ba
Mama dake zaune kusa da ita ta kalleta cikin rashin fahimta tace
“mene?
Kallon maman tayi itama cikin rashin fahimtar
” waye baze amince ya rabu dake ba?
Mama ta jefo mata Tambayar tana kafeta da ido
Daburcewa Rauda tayi, dan ita bata san maganar da tayi a zuciya ta fito fili ba, ta rasa me zata ce
Numfashi mama ta sauke tana kaɗa kai, lokacin layi yazo kansu tamiƙe tayi gaba batare da ta kuma cewa komai ba
Rauda tabi bayan ta, gwajin farko da likita yayi ya gano BP ɗinta yayi ƙasa sosai
Kallon ta yayi yana cewa
“meke damunki? Da BP ɗinki yayi ƙasa haka?
Shuru Rauda tayi, likitan ya cigaba da cewa
” BP ɗinki yayi ƙasa sosai, shi yasa kike jin ciwon kai da kuma jiri, zan rubuta miki magunguna Asiya kisha, sannan kidena barin kina shiga cikin tunani Allah ya ƙara lafiya”
Mama ta amshi takaddar maganin suka, fito kowanne zuciyarsa babu daɗi
Napep suka hau ta kawo su gida suna gab da tsayawa taji maganar Aasim
_”kisameni a bayi yanzu”_
ko tsayawa bata bari mai nepep ɗin ya gama yi ba ta diro
Cikin faɗa mama tace
“wani irin ganganci ne wannan? miye kikema sauri da ba zaki tsaya yagama tsayawa ba?
Cikin sauri Rauda tace
STORY CONTINUES BELOW
” bayi nikeso na shiga”
guntun tsaki mama ta ja,tana zage Jakarta zata ba mai Napep ɗin kuɗi
itako Rauda ta ƙagara tagansa,juyawa tayi da sauri ta shige cikin gidan
Ko buta bata tsaya ɗauka ba ta shiga bayin
A tsaye tagansa,rufe ƙofar bayin tayi da sauri tare da ƙarasawa inda yike
“Aasim, kana lafiya? Me ya faru na jika shuru? Ince dai ba wani abu a kayi maka ba?
Ta jero mai tambayoyin cikin zaƙuwa da son jin abunda ta tambaye sa
Be bata amsa ba, illa rungumeta da yayi,yana sauke wata nannauyar ajiyar zuciya
Ita ɗinma ajiyar zuciyar ta sauke, tana jin sonsa na bin duk wani sassa na jikin ta
“kabani amsa mana Aasim”
Ɗagota yayi ya zuba ma fuskar ta ido amma kuma har lokacin beyi magana ba
Kawai yana hango yadda za ace yayi rayuwa babu ita ne
Girgiza kai yayi yana ƙara rungumeta sosai
“baze yuwu ba, baze yuwu ba”
Yafaɗa cikin tsananin damuwa
“miye baze yuwu ba, kayi min magana yadda zan fahimta dan Allah”
Kuma Ɗagota yayi yasa hannayensa duka biyu ya tallabo fuskarta yace
“Rauda inaso kiyimin alƙawarin cewa ba zaki taɓa rabuwa dani ba,har ƙarshen rayuwarki”
Kallon sa ta keyi sosai,
“Aasim kasani ai, bazan iya rabuwa dakai ba”
Girgiza kai yayi, yace
“nasani a yanzu, amma bansan meze iya faruwa nan gaba ba, shi yasa nikeso kiɗaukar min alƙawari da kanki da kuma bakinki”
Kaɗa kai tayi tare da cewa
“shi kenan nayi alƙawari bazan taɓa rabuwa da kai ba”
Gauron numfashi ya sauke yana gyaɗa kai
“nagode, wannan alƙawarin da kika ɗauka a yanzu ya kuma ƙarfafamin gwiwa,zanje in sanar dasu abunda na yanke”
“amma Aasim, bekamata…….
Katseta yayi
” kinga Rauda kada kice komai,na san watarana zamu dai-daita dasu, amma ke bazan iya jurar rashinki dai-dai da rana ɗaya ba”
Be jira jin mezata ce ya ɓace
Ajiyar zuciya ta sauke me nawi, tare da fitowa daga bayin, ɗaki ta shiga ta zauna akan gado
Maganar daya faɗa ce kawai take yi mata yawo a kunne
_”kinga Rauda kada kice komai nasan wata rana zamu dai-daita dasu amma ke bazan iya jurar rashinki dai dai da rana ɗaya ba”_
Sauke ajiyar zuciya tayi, ta janyo filo ta ɗaura kanta
Meyasa ze zaɓi rabuwa da ahalinsa saboda ita? Me yasa?
Tayi wa kanta tambayar
Lumshe idanuwan ta tayi, tana fatan ace har yanzu Mafarki take yi
Dan har lokacin ta kasa gasgata abunda ke faruwa
Ɓangaren Aasim kuwa, lokacin da ya koma masarauta saura ƴan mintoci a tafi fada
Yana zaune a ɗakinsa ya zuba tagumi, fulawar saƙo ta shigo ɗakin
Hannu yasa ya damƙe, saƙon ammi ne tana son ganin sa
STORY CONTINUES BELOW
Kamar baze je ba, sai kuma yaga rashin dacewar Hakan
Miƙewa yayi ya bayyana a ƙofar sashenta
“ku isar da zuwa na”
Yace ma kuyangin dake bakin ƙofar
Tun kan su kai gayin magana aka basu izinin buɗewa
Shiga yayi da sallama yana rusunawa
Ammi tayi ma jakadiyarta nuni data fita sannan ta dawo da kallon ta kansa
“Aasim ni kake wulaƙantawa ko? Ace tun jiya nikeson yin magana da kai amma ka sawa Ɓangaren ka takun kumi ko?
Ƙasa yayi da kansa
” kiyi haƙuri ammi, ba nayi Hakan danna ɓata miki bane, nayi ne dan nasamu natsuwa”
Ta jinjina kai tace
“yayi kyau, saura minti biyar taron fada, me ka yanke a zaɓin da aka baka?
Shuru yayi yana nazarin abunda zece
” tambayar ka nikeyi kayi min shuru”
Cikin fargaba yace
“ammi ki gafarceni, amma banajin zan iya haƙura da duka zaɓi biyu”
Kaɗa kai tayi cike da ɓacin rai da kuma tashin hankali
“kadai ce kawai ka zaɓe ta a kanmu, ka fifita bil adama akan iyayenka
Wai shin Aasim lafiyar ka ƙalau kuwa? Ko ko taɓin hankali ne yasa meka?
Taɗan numfasa sannan ta cigaba da cewa
” shin kana tunanin bil adama zata sama ma dauwamamman farin ciki ne?
Kayi babban kuskure Aasim, ko da yike laifi na ne da na goyama baya tun farko
Amma ina so ka sani nadama da danasani zasu biyo bayan ka inhar kazaɓi rayuwa da ita sannan……..
Ƙarar sanar wa data Kaɗa ita ta dakatar da ita
Numfashi ta sauke tana ɗauke idanuwan ta a kansa
“lokaci yayi, zaɓi ya rage gareka, abu na ƙarshe da nike so kasani shine. Idan har kazaɓi rayuwa da ita to kada ka ƙara zuwa inda nike,kaje inayi maka fatan alheri”
Tana gama faɗar haka ta ɓace daga gurin
Aasim numfashi ya sauke Yana Miƙewa cike da tsananin ruɗani tabbas ya san ze aikata babban kuskure amma yana da yaƙinin iyayen sa ba zasu iya jurar rashin sa ba, nan da wani ɗan lokaci zasu nemesa kuma ma ya san da wuya Abi ya zartar da hukuncin kora a kansa ƙilan yafaɗi Hakan ne dan ya tsorata sa ya rabu da rauda
Ɓacewa yayi ya bayyana a fada, kamar kullum fadar cike take da manyan rauhanai
Suna zazzaune, Aasim na bayyana suka rusuna suna gaishe sa
Saida Aasim ɗin ya zauna a kujerar sa sannan suka ɗago
Shuru ya biyo baya na wasu mintoci, sannan sarki ramzad yayi gyaran murya
Hakan yasa fadar yin tsit
“Aasim, kafaɗa ma fada abunda ka yanke, shin ka haƙura zaka rabu da itanne? Ko ko kana kan bakanka na rayuwa da ita?
Aasim yayi shuru cike da tsananin fargaba
Sarki ramzad ya kuma mai-maita tambayar sa sannan ya ƙara da cewa
” bana buƙatar jin shurun ka, rayuwa da mu kazaɓa ko rayuwa da ita?
Aasim saukowa yayi daga kan kujerar ya durƙursa
” Abi ka gafarceni, har yanzu nakasa yanke komai, bana jin zan iya Haƙura da duka zaɓi ɓiyun da ka bani”
Sarki ramzad ya jinjina kai yace
STORY CONTINUES BELOW
“kenan har yanzu kana kan bakanka na ƙin rabuwa da ita?
Aasim ya ƙara dur ƙurshewa
” Abi dan Allah, kayi haƙuri kabarni na cigaba da rayuwa da ita, nayi maka alƙawari bazan sake aikata kuskure ba…….
Ɗaga mai hannu sarki ramzad yayi cike da ƙunar zuciya
” ya isa, ka riga da ka bani amsar tambaya ta, dan haka kada ka ƙara cewa komai”
Aasim ya runtse idanuwan sa yana ambaton sunan Allah
Sarki ramzad ya maida kallon sa ga rauhanan da suka yi jugum jugum saboda mamakin kafiyar da Aasim yayi
Yace
“tunda abunda ya zaɓa kenan, to bazan fasa hukuncin dana yanke ba, dan haka aje a shirya tauran zuwa jibi za a zartar da hukuncin”
Ɗaya daga cikin manyan fadawanne ya durƙusa cike da tashin hankali yace
“mai martaba, Aasim ɗan kane, be kamata ayi masa hukuncin kora ba, a sassauta masa ranka shidaɗe”
Shima wani ba faden zubewar yayi yana faɗin
“a sassauta masa ranka shidaɗe, a canza masa wannan hukuncin”
Sarki ramzad ya girgiza kai
“babu ruwan ku da matsayinsa, na riga da na yanke hukunci kuma wannan hukuncin shine adalci dan haka bana so na ƙara jin wani daga cikin ku ya furta komai, aje a shirya tauran kamar yadda na bada umarni”
Gabaɗaya jikin Aasim ya gama mutuwa, amma ya kasa ƙara furta komai
Hawaye kawai yikeyi, a haka aka watse daga fadar cike da juyayin al’amarin
Tunda Aasim ya koma Ɓangaren sa ya kwanta, yana ta tunanin bijire ma mahaifinsa da yayi
Tabbas yayi kuskure kuma be kyauta ma kansa ba
Buɗe ƙofar ɗakin aka yi aka shigo
Ya ɗago yana duban me shigowan, shaida ce
Ya tashi ya zauna yana kamo hannunta
“shahida, lafiya na ganki wani iri? Baki da lafiya ne?
Cikin gwaran cinta tace
” ba kai bane,kake ta yin kuka ɗazu”
ƴarfillo.
JINNUL*
*AASHIQUE🌹* +
🧞♂ 🧞♂
🧞♂
NA
HARIRA ALIYU _(y’arfillo)_ 🧕🏻
Dedicated to _little hajjo_ and my elder sister _Hafsat Aliyu_
🅿AGE 📕 1⃣7⃣
Wannan Page nakane……… Ina alfahari da kai a ko da yaushe
_9:15_🕒 PM
SAT, JUN 8
_Bissmillahir rahmaninr Rahim_
Murmushin ƙarfin hali yayi yana ɗaukan ta ya ɗaura ta ajikinsa
“dan kinga ina kuka, shi ya sa kika yi wani iri? Ba kyaso kiga ina kuka ne?
Shahida ta ɗaga kai alamar eh
Murmushi ya kuma yi yana tallabo kyakkyawar fuskarta
“shi kenan farin ciki na, daga yau bazan sake yin kuka ba, kinsan Abi ɗinki na sonki da yawa baya so ya ganki cikin damuwa”
STORY CONTINUES BELOW
Shahida tayi murmushi tana kwanta wa a jikin sa
“abbi,ina ammi na?
Aasim yayi shuru, yana kallon ta
Shahida ta ɗago kanta tana kallon sa tare da nanata tambayar da tayi
Yayi ƙoƙorin kauda damuwar dake fuskar sa yace
” kinaso kiganta ne?
Shahida ta ɗaga kai da sauri
Ya rungume ta ajikinsa yana sauke numfashi
” shi kenan, ki ƙara haƙuri kinji? Zaki ganta har sai kin gaji, yanzu faɗamin me kikaci yau?
Haka ya dinga lallaɓata har tayi barci, sannan ya kwantar da ita
Ya tsura mata ido yana jin tausayinta, kullum bata da maganar da ta wuce ina amminta?
Gashi da wuya ta rayu da ita yadda take so numfashi ya sauke tare da nuni da hannun sa
Wani ƙaton madubi ya bayyana, ya sake yin nuni da hannun sa
Sai ga Rauda ta bayyana a ciki, har lokacin tana kwance akan gado tana rawar sanyi
Ta duƙunƙune da bargo
“Rauda!
Ya kira sunan ta, ta buɗe idanuwan ta a hankali tana duba inda ta jiyo muryarsa amma bata ga kowa ba
Ya sauke ajiyar zuciya yana jin ƙaunarta na ƙara ratsasa
Hannu yasa ta cikin madubin ya ɗaura a wuyan ta yaji zafi rau
Ita ko zabura tayi dan bata ga kowa ba ta kuma ji antaɓata
Guntun murmushi yayi tare da faɗin
“matsoraci ya, nine”
Ta ƙara duba kan gadon bata ganshi ba, a hankali tace
“to kana ina? Ya aka yi bana ganin ka?
” ina masarauta, nima banajin daɗine bazan iya zuwa ba, kinsan duk abunda kikeji ajikinki inaji ajikina,ga kuma damuwar da nike ci”
Ta maida idanuwan ta ta Lumshe tare da cewa
“da gaske kana jin yadda nikeji a yanzu?
Ya ɗaga kai kamar tana ganin sa
” sosai habibty,zafin jikin ki yayi yawa,kinsha magani?
Ta ɗaga kai alamar eh
Ya jinjina kai
“sannu Allah ya baki lafiya,nan da ƙan-ƙanin lokaci zakiji sauƙi in sha Allahu”
“yanzu me kake yi? Ina so in ganka”
Ya gyara zamansa yana dai-dai ta saitin madubin
“to shi kenan rufe idanuwan ki ki natsu sosai”
Ta rufe kamar yadda yace, amma ba ta ganshi ba har zata buɗe, sai taga duhun dake cikin idanuwan ta ya fara yayewa
Ahankali Ahankali har duhun ya yaye gaba ɗaya ya bayyana
Guntun numfashi ta sauke tana cewa a zuciyar ta
“wannan kyawun naka dama ai sai jinsin aljanu”
“habibty”
Ya kira ta,ta amsa na’am
“kinyi mafarki ɗazu ko?
Ta ɗaga kai alamar eh
Ya jinjina kai
” to ba mafarki bane, abunda ya faru a fada ne kika gani”
Jikinta yayi sanyi
“amma Aasim Meyasa zaka yi haka, Hakan ba dede bane, Meyasa bazaka bi umarnin su ka rabu dani ba?
STORY CONTINUES BELOW
Ya sauke nannauyan numfashi, tare da dafa ƙirjinsa
” ba zaki gane yadda nike jinki a nan ɗina ba, wallahi Rauda bansan dalilin da yasa nike miki irin wannan son me zafi ba, jini keyi kamar idan na rasa ki zan iya rasa rayuwa ta, nima ba da son raina na bijire wa umarnin su ba, amma nasan ba zamu jima ba zamu dai-daita dasu”
Ajiyar zuciya ta sauke tana jinjina girman ƙaunar da yike mata
“amma ya maganar tsallake tauran da Naji anyi magana?
Ya sauke gauron numfashi yace
“zan tsallake jibi”
Jikinta ya ƙara yin sanyi
“Aasim dan Allah inda hanyar da zaka bi kabi, bana so kasha wahala”
Yayi murmushi yana sa hannu ta cikin madubin ya kama hannun ta tare da matsewa cikin nasa
“kar ki damu habibty, tabbas nasan tsallake tauran akwai wahala kuma nima hankalina na tashi idan na tuna azabar dake ciki
Amma kuma hankalina ya kan kwanta idan na tuna cewa zan samu ƴancin yin rayuwa dake bayan wannan wahalar, fatana dai kiriƙe min alƙawarin da kika ɗaukar min”
Haƙiƙa ta ƙara jin ya shiga zuciyar ta to me ma zesa ta karya alƙawarin data ɗaukar mai?
Ta tambayi zuciyar ta tana ganin babu, Guntun murmushi yayi tare da katse mata gajeren tunanin da ta tafi
“ki tuna ke mutum ce, kuma halin mutanen yanzu sai Allah, zasu ɗaukar ma alƙawari amma daga baya su nuna su basu ma san da maganar wani alƙawari ba, amma dai ke na yarda dake na kuma san ba zaki taɓa juyamin baya ba”
Hmmmm Ta sauke ajiyar zuciya kawai batare da ce komai ba
Murmushi ya kuma yi yanayi mata nuni da gefen sa
“baki ga wacce take kusa dani bane?
Sai lokacin ta lura da Shahida dake kwance gefen sa
Ta ƙura ma yarinyar ido tana jin ƙaunar ta acikin zuciyarta
” na tashe tane? Dan ɗazu ta gama tambaya ta ina amminta”
Girgiza kai Rauda tayi alamar a’a tana cigaba da kallon ta
“Meyasa?
Ya tambaya
“saboda kanta ze iya yin ciwo idan ka tashe ta”
Dariya yayi yana duban Shahida dake ta baccinta
“wa yace miki muma rauhanai irin ku ne mutane ragwaye,babu abunda kanta zeyi”
Ta gyaɗa kai tace
“shi kenan tashe ta”
Ya durƙuso sai tin fuskarta yana shafa fuskarta da ambaton sunan ta
Sai ko tabuɗe idon
“Shahida tashi ga amminki”
Tashi zaune Shahida tayi da sauri tana rarraba idanu
Yayi murmushi tare da nuna mata madubin
Haka suka cigaba da fira har saida barci ya fara ɗaukar Rauda sannan ya kaudar da madubin
Yana jin kamar bashi da wata damuwa, dan firar da yayi da ita yasa hankalinsa ya ɗan kwanta
Miƙewa yayi ya isa sashen ammi, sai dai kuyangin ƙin buɗe masa ƙofa suka yi dan sunce tace bata buƙatar ganawa da kowa
*Ranar tsallake tauran*
Duk wani masoyin Aasim da ke cikin masarauta hankalinsa a tashe yike, musamman ammi da gaba ɗaya ta fita hayyacinta
STORY CONTINUES BELOW
Haka Shima sarki ramzad dauriya kawai yikeyi yana nuna kamar abun Be dame shi ba, amma zahiri ƙasan zuciyarsa cike take da tashin hankali
Ammi kasa haƙuri tayi saura minti goma sha biyar ta shiga Ɓangaren sarki ramzad
Umarni ta bawa waziri da ya fita sannan ta ƙarasa gaban sa ta durƙusa
Cikin tashin hankali da tsananin damuwa ta fara magana
“na roƙeka ka janye wannan hukuncin akan ɗana, shi kaɗai gareni”
Sarki ramzad yayi mata wani kallo yace
“in janye hukunci fa kika ce? Kema kinsan abunda baze taɓa yuwu wa ba kenan,akwai sauran minti sha biyar, kina iya zuwa kisa ɗanki ya bi abunda nace mai, dan shine kika isa dashi.
Amma ni baki isa kisani in canza abunda na yanke ba
Yadda bawa zeyi laifi in hukunta sa, haka zan hukunta abunda na haifa dan haka babu maganar janyewa”
Kuka ta fashe dashi
“amma kasan bayan Aasim bani da wani ɗa a duniya ko?
Gyara zama yayi cike da ƙaguwa da kukannata dan tashin hankalin da yike ciki kaɗai ya ishesa
“kinga Samira,bana buƙatar jin wannan kukan naki, ki tashi ki ɓace min da gani”
Miƙewa tayi cike da ɓacin rai
“na fahimci ni kaɗai nike son Aasim, kai wahalar da ze shiga ko ajikinka, to shi kenan zan tafi amma ka sani duk abunda ya sami ɗana da kai zanyi kuka”
Shima miƙewar yayi a fusace
“ki dakata min da waɗannan kalaman naki, duk ba laifinki bane da Ace tun farko baki basa goyon baya ba da munkawo wannan matakin?
Juya wa ammi tayi ta fice tana kuka bata zame a ko ina ba sai Ɓangaren Aasim
Yana tsaye jikin bango, ya Lumshe idanuwan sa da suka kaɗa sosai
Jin kukan ta yasa ya buɗe su da sauri
Ganin halin da ta shiga ya ƙara ɗaga mai hankali
Durƙushewa tayi a wurin tana cigaba dayin kukan
Ya ƙarasa gaban ta da sauri ze ɗaga ta
Dakatar dashi tayi ta hanyar ɗaga masa hannu
Ya durƙusa yana tambayar ta
“ammi me yafaru?
” idan kai baka son rayuwar ka ni ina so, ka duba wahalar da za kasha idan ka shiga tauran”
Ammi tafaɗa
Aasim ya sauke numfashi yana kama hannun ta
“ammi indai tsallake tauran ne,ki kwantar da hankalinki zan tsallake lafiya insha Allahu Babu abunda ze same ni”
Ta kallesa da jiƙaƙƙun idanunta
“Aasim……
Katseta yayi ta hanyar cewa
” ammi dan Allah kada ki ƙara cewa komai, ammi Rauda itace farin ciki na na kuma son kina son duk wani abu da ze faranta min
Kinsan kema bazan taɓa yin nisa dake ba, dan haka ki kwantar da hankalinki dan Allah, kada ki karya min gwiwa”
Miƙewa tayi tana jinjina kai
“shi kenan, tunda abunda ka zaɓa kenan, Allah ya baka sa’a”
Tana gama faɗar haka ta ɓace
Ajiyar zuciya Aasim ya sauke cike da tausayin mahaifiyar tasa
Sai dai baya jin ze fasa abunda yayi niyya
STORY CONTINUES BELOW
*filin tauran*
Wurin ya cika sosai da rauhanai, Aasim na tsaye daga gefe inda babban ba fade yike
“Yarima Aasim, shin da gaske ka amince da barin masarauta ta hanyar tsalle ke tauran??
Me faɗar hukunci ya tambaya
Aasim ya ɗaga kai
” na amince “
” ka tabbata?
Me faɗan hukunci ya kuma tambaya
Aasim ya jinjina kai
“na tabbata”
Sarki ramzad ya runtse idanuwan sa cike da tsananin takaici
Babban ba fade yayi nuni da tauran take ƙofarta ta buɗe
Kai tsaye Aasim ya dumfareta
Yana kallon yadda haya ƙin hucinta ke fita
Runtse idanuwan sa yayi yayin da ya isa ƙofar, ya ɗan tsaya ya karanto wasu abubuwa sannan ya kutsa kai
Yana shiga ƙofar ta rufe
Nan da nan garin yayi duhu, iska ta fara kaɗawa da ƙarfi
Wani baƙin hayaƙi ne ya dunƙule yayi tsawo baka iya ganin ƙarshensa a saman tauran ɗin
Wasu kibiyoyi masu haske suna shiga cikin hayaƙin
Zuwa can hayaƙin ya fitar da wata ƙara me razanar wa wanda ta sauka a jikin Aasim
Faɗuwa yayi a ƙasa saboda tsananin azaba,gashi ba a so a kwanta dan danne mutum take yi
Yun ƙurawa yayi ya tashi da ƙyar yana duban jikinsa daya fara huhhujewa
Haka ƙarar ta dinga sauka a jikinsa har sau arba’in da tara
Iya jigatuwa Aasim ya jigatu
Gaba ɗaya jikinsa ya huhhuje,lokacin da ƙofar ta buɗe faɗowa yayi
Mus’ab ne ya ruga da gudu ya taro sa yana Kiran sunansa cikin kaɗuwa da halin da ya shiga
Aasim be kuma sanin inda kansa yike ba, har saida yayi kwana biyu
Sannan ya farfaɗo, lokacin da ya farfaɗo mus’ab ya gani a kusa dashi
Mus’ab na ganin ya buɗe ido ya matso kusa dashi sosai yana faɗin
“sannu Aasim ka tashi? Yaya jikinnaka?
Aasim ya kaɗa mai kai kawai ba tare da yace komai ba
“sannu, ga magani ammi ta aiko maka, tace da ka farka kasha ze taimaka gurin komawar jikin ka dai-dai”
“Allah sarki ammi”
Aasim ya faɗa a cikin zuciyar sa, yunƙurawa yayi ze tashi
Mus’ab ya dakatar dashi
“kada ka tashi, baka ga halin da kake ciki bane?
Aasim ya girgiza kai
” mus’ab barni na tashi, taimaka min dai in jingina”
Mus’ab ya jinjina kai tare da tallafa masa ya jinginan
“amma ya kake ji yanzu? Da kwai wani guri da yike ma ciwo?
Mus’ab ya kuma tambayansa
Aasim yayi murmushin ƙarfin hali yana sake girgiza mai kai
” a’a abokina, ka kwantar da hankalinka babu inda ke min ciwo”
Ya faɗa da muryarsa da ta dashe sosai
Mus’ab ya jinjina kai,yana miƙa mai maganin da ke cikin wani kofin silver
STORY CONTINUES BELOW
“gashi kasha, me kake buƙatar kaci?
Jar abarba ko koriyarta?
Aasim ya girgiza kai yana kai kofin bakin sa
Sai da ya sha rabin maganin sannan ya ajiye yana kallon yana yin garin
” yau kwana nawa anan?
“kwanan ka biyu da yini”
Mus’ab ya bashi amsa
Ya ɗan zaro ido
“kwana biyu??
” eh kwana biyu me ya faru?
Mus’ab ya tambaya yana kafesa da ido
Cikin ƴar damuwa Aasim yace
“Rauda mana, Nasan tana cikin damuwa da jina shuru da tayi”
Mus’ab ya kauda kansa da ga kan Aasim yana mamakin irin ƙaunar da yike wa wannan bil’adamar
“to Meyasa zata damu, bayan ta juya ma tunani, ta san yanzu ka zama nata ita kaɗai”
Yana yin fuskar sa ya sauya
“Kaga mus’ab bana so kana faɗan magan ganu marasa daɗi a kanta”
Mus’ab yace
“to maida wuƙar angon bil’adama”
Guntun tsaki Aasim ya ja tare da yin nuni da hannun sa madubi ya bayyana
Ya kuma nuna sa da hannu, sai ga Rauda zaune ta zuba uban tagumi
Kallon mus’ab yayi yace
“ka nemomin ko ma miye ina jin yunwa”
Mus’ab yayi murmushi tare da faɗin
“kadai ce kana son ganawa da tauraruwar mata”
Ya faɗa yana Miƙewa
Aasim banza yayi dashi, sai da ya fice sannan yaja gajeren tsaki
Tare da fuskantar madubin sosai
” *habibty!*
Ya kira ta, ta ɗago kai da sauri tana kalle-kalle
” Aasim kana inane, me ya faru da kai najika shuru?
Ta tambaya a ƙagare
“ina nan lafiya habibty, ki kwantar da hankalinki”
Hmmmm ta sauke nannauyar ajiyar zuciya
“inaso inganka yanzu please”
Ya kalli jikinsa yadda ya huhhuje tare da sauke numfashi
“habibty kiyi haƙuri baza ki iya ganina ba”
“amma Meyasa? Ka san damuwar da na shiga kuwa? A sanadin na Dena jinka, na Dena ganin ka”
Ya kuma sauke numfashi yace
“da gaske habibty?
Ɗaga kai tayi da sauri
” da gaske Mana, nidai Ina son inganka yanzu dan allah”
“habibty bana so kiganni a yana yin da nike ciki ne, kiyi haƙuri a kwana biyu tukunna”
Ya faɗa
Ta jingina da kujerar da take kai tana sauke ajiyar zuciya
“ni ko a yaya kake Ina son ganin ka ahaka”
Yayi Guntun murmushi tare da cewa
“to bazan iya zuwa ba, sai dai in janyo ki ta cikin inda nike kallon ki, amma kafinnan ina mama?
STORY CONTINUES BELOW
” Mama bata nan”
Ya jinjina kai
“shi kenan”
Cikin minti biyu ta ganta a ɗakinsa
Sai dai yana yin data gansa ya yi mugun ɗaga mata hankali ta tsorata sosai
Gaba ɗaya tsigar jikin ta tashi take yi
Cikin kiɗima ta ja da baya tana kallon sa
A tsorace
“A…a..sim”
Ta Kira sunansa cikin rawar murya
Miƙewa yayi daƙyar ya ƙara sa inda take, dan har lokacin yana jin jiki
“kingani ba, shiyasa banso kika ganni ba”
Ya faɗa yayin da ya isa gabanta
Kallon sa kawai take yi cike da al’ajabi
“me yasa Meka haka? Ya aka yi kakoma haka?
Yayi murmushin ƙarfin hali yace
” tauran, ko kin manta?
Idanuwan ta ne suka cicciko da hawaye
“Aasim, saboda ni ka koma haka?
Ta faɗa hawayen da suka ciko idanuwan ta suna gangarowa
Murmushi ya kuma yi
“dan Allah kada kiyi kukannan, kinsan dai abunda bana so na gani a fuskar ki kenan ko?
Ji tayi zuciyar ta ta karye, Bata damu da yanayin data gansa ba ta rungume sa
Cikin shesshekar kuka tace
” duk a sanadina Aasim? Yanzu ahaka zaka cigaba da zama kenan?
Ajiyar zuciya ya sauke me nawi yana jin guguwar ƙaunarta na daɗa lulluɓesa
Ɗago ta yayi yana kallon kyakkyawar fuskarta
“a’a habibty, nan da wani ɗan lokaci zan koma yadda nike, ki kwantar da hankalinki kinji?
Mai da kanta tayi kan ƙirjinsa tana cigaba dza yin kukan
Ya Lumshe idanuwan sa yana jin kukan ta har cikin ransa
“ki yi shuru hakanan dan Allah, ko kinaso Nima in fara ne?
Girgiza kai tayi tana share fuskarta
Ƴarfillo.
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~*
*~❄We beare’s of soon golden We writer’s assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
*🌹JINNUL*
*AASHIQUE*
🧞♂🧞♂
🧞♂
NA
HARIRA ALIYU _(ƴarfillo)_🧕🏻
Dedicated to _little hajjo_ and my elder sister _Hafsat Aliyu_
🅿AGE📕 1⃣8⃣
_wannan Page nakune ƴan golden forum, haƙiƙa bana gajiya da yabonku domin kun can-canta Allah nike roƙo ya ƙara mana basira da fasaha ya kuma ƙara mana danƙon zumunci a wannan gida na mu me albarka amin_
_8:52_🕒 AM
SUN, JUN 9
_Bissmillahir rahmaninr Rahim_✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
Ya kuma yin murmushi ya na kama hannun ta zuwa bakin gadon suka zauna suna fuskantar juna
STORY CONTINUES BELOW
“to shi kenan ya isa haka,Nasha faɗa miki cewa idan kina kuka bakya yin kyau amma kinƙi yarda”
Ƙarasa goge ragowan hawayen tayi tana zuba masa fararen idanuwan ta
“ni dama bani da kyau, ko banyi kuka ba”
Ya ɗan fito da idanuwan sa waje tare da faɗin
“inji wa ya faɗa miki? Ai ke idan akwai abunda ya wuce kyakkyawa dashi ya kamata a kira ki, domin kyawun ki na daban ne”
Murmushi tayi tana girgiza kai
“zan iya yadda da Hakan amma a gurinka, dan nasan son da kake min ze iya sawa Kaga kyau na fiye da kima, amma ni nasan ni ba kyakkyawa bace”
Ya kama hannun ta yana matsewa cikin nasa
“da gaske habibty kina da kyau, bawai idona rufe wa yayi ba”
Ta kaɗa kai tace
“to shi kenan Naji, amma ya kake ji ajikinka nasan ko ina yima ciwo yike yi ko?
Ta Ƙarasa faɗa idanuwan ta na kuma yin rau-rau da ƙwalla
” ya ilah, habibty baki ji abunda nace miki ba ko? Kina so raina ya ɓaci ko?
Girgiza kai
Yace
“oook idan bakya so raina ya ɓaci ki maida hawayen nan kada ki bari su zubo”
Tayi ƙoƙorin maida hawayen amma ina kafin tayi wani yunƙuri su biyo kumatun ta
Hannayen sa yasa ya tare hawayen suka ɗiga akai
“bazan taɓa bari hawayenki su zuba a ƙasa ba, indai ina tare da ke Rauda, dan Allah ki bari”
Kwantawa tayi a jikinsa tana haɗiye wani ƙullutun damuwa da ya dunƙule mata maƙogoro
“ka barni inyi kukan dan Allah,in banyi ba ina jinsa yana dunƙule min a ƙirji”
Hmmmm ya sauke numfashi tare da cewa
“to wai kukan me kike yi ne? Faɗa min,indai kukan halin da nike ciki ne kibari, nan da wasu kwanaki zaki ga na koma dai-dai”
Dai de lokacin mus’ab ya shigo ɗakin ɗauke da tiren abinci
Ganin su a tare ya sa ya shigo da sallama
Aasim ne ya amsa yana tambayar har ya dawo?
Be bashi amsa ba illa ajiye tiren da yayi ya fice
Cike da takaicin ganin ta da yayi, dan shi gaba ɗaya haushinta yike ji
Dama ya san ze ganta Aida da ainihin suffarsa ze shiga ɗakin dan ya razana ta
Ƙwafa yayi tare da ɓacewa
Ita ko Rauda bayan fitar mus’ab ɗago wa tayi tana duban Aasim dan a kallon da mus’ab ya yi mata ta hango tsanarta ƙarara a tare dashi
“wanene wannan da ya shigo?
“abokina ne”
Ya bata amsa
Ta ɗanyi shuru sannan tace
“amma nayi masa wani laifi ne?
Girgiza kai yayi yana murmushi
” kinga ƙyalesa akwai abunda ya ɓata masa rai ne kawai”
Jinjina kai tayi tana duban tiren da ya ajiye
Wasu kalar abinci ta gani da bata san dasu ba a duniya
Abu ɗaya ta fahimta a tiren itace arbaba, kuma abarbar ma ja
Mamaki ne ya kamata dan ita a sanin ta abarba ba ja bace
STORY CONTINUES BELOW
Ganin yadda take kallon tiren yasa yace
“yadai, me kike mamaki ne?
“dama akwai abarba Jane?
” eh akwai amma anan duniyar mu”
Ta jinjina kai tana duban madubin
Mama ta gani ta dawo
Zaro ido tayi cikin fargaba
“mama ta dawo”
Ya kalli madubin yace
“to yanzu yaza ayi? Ta ina kike so in maida ki?
A gaggauce tace
” bayi, sai in yi kamar daga bayi nike”
Duba bayin yayi yaga akwai mutum a ciki
“da akwai mutum a bayin”
Dafa kai tayi cikin damuwa
“maidani uwar ɗaka kawai tunda tana falo”
Jinjina kai yayi ya maida ta yana cigaba da kallon madubin
Ita ko tana ganin ta a ɗaki ta miƙe ta yo falo
Ganin ta ba ƙaramin faɗar mama da gaba yayi ba
“ke ta ina kika ɓullo?
Rauda tayi saurin ɓoye fargaban da take ciki tace
” daga uwar ɗaka mana mama”
Mama mamakine ya bayyana a fuskarta
“bangane daga uwar ɗaka ba, ba yanzu na shiga na ajiye hijabi ba, ya aka yi ban ganki ba?
Tayi mata tambayar tana kafeta da idanu
Gaban Rauda ya cigaba da faɗuwa
“baki dai lura bane, ina kan gado,”
Ta faɗa cikin dake wa
Mama ta jinjina kai tace
“to gaskiya zanje adubamin hawan jinana ƙila ya hau da yawa da ni banga kowa ba a ɗaki wallahi”
Ajiyar zuciya Rauda ta sauke ganin mama ta yarda
Ƙarasowa kan kujera tayi ta zauna kusa da maman tana dariya
“mama Bawani hawan jini fa, tsufa ne kawai da kika fara”
Mama tace
“gidan ku, dudu nawa nike? Bari kiga kiyi aure kibani wuri yadda zan koma yarinya shataf, dan gayu zan dinga ci”
Dariya Rauda tayi sosai
“Haba ainasan babu wani gayu da zaki rinƙayi, ni da baba ze ji shawara ta ma da ya ƙaro muku ƴar budurwa”
Mama kai mata duka tayi
Ta goce tana cigaba da yin dariyar
Bayan sati biyu,hankalin Rauda ya kwanta sosai bata da wata damuwa musamman data ga Aasim ya warware ya koma yadda yike
Uwa uba ga soyayyar da suke yi me zafi, wacce tasa ko da yaushe bata rabo da tunanin sa
Kamar ko wani dare bayan mama tayi bacci
Rauda na zaune a falo tana guga
Maganar sa taji
“habibty ina son ganin ki”
Ɗan ɗagowa tayi tace
“kabari in gama guga please….
Kafin ta Ƙarasa maganar taji wata iska me daɗi ta lulluɓeta tana janta
STORY CONTINUES BELOW
Lumshe ido tayi tana faɗin
“oh Aasim kasan fa Bama samun wuta sosai yanzu waze Ƙarasa min gugar”
Jin iskar ta lafa yasa ta buɗe idon, a kwance tagansa gefen gado
Kanne mata ido ɗaya yayi yana faɗin
“ba dai guga bace? To juya kigani”
Juyawan ko tayi tana duban madubin
Abun mamaki ion ɗin da kansa taga yana yin gugan
Ta zaro ido cike da mamaki
Dariya yayi yana janyo ta ta faɗa jikin sa
“miye na wani zare idanu, abunda yafi haka ma zaki gani, zaki wani ce in bari ki gama guga, kinsan yadda na matsu in ganki kuwa?
Ta marai-raice fuska tace
” to ni yanzu me zan maka?
Murgina wa yayi da ita, ya zama itace a kwancen
“me ma zaki min kike tambaya na?
” to ni bacci nike son nayi”
Ta faɗa a shagwaɓe
Yadda tayi maganar ya ƙara rikita sa
Ya tsa yasa yana zagaye gefen fuskarta
“bacci? To kiyi mana aiban hanaki ba”
Ji tayi wani abu ya fara taso mata ta Lumshe idanuwan ta daga kallon sa da take yi
Shiko sun kuyowa yayi daf da fuskarta yana kallon ɗan ƙaramin bakin ta
Yatsan sa ya dawo dashi yana zagaye tausasan lips ɗinta wanda Hakan ke ƙara sa tana shiga wani yanayi
Kissing ɗinta ya fara Ahankali yana bin duk wani sassan jikin ta
Gaba ɗaya jin ta take yi a wata duniya da bazata iya fasalta irin ta ba
Haka ya cigaba da sarrafa ta bata masan sanda ta shiga duniyar bacci ba
Shi ko Hakan ya bashi damar aiwata muradin zuciyar sa
Sai wuraren ƙarfe uku ta farka, yana kwance kusa da ita ya zuba mata ido
“habibty!
Ya faɗa cikin shauƙin ƙaunarta
Ɗago da kanta tayi tana kallon sa ba tare da ta amsa ba
“habibty ina sonki ina ƙaunar ki”
Murmushi tayi idanuwan su na cigaba da sarƙewa da juna
“Nima Ina son ka Aasim”
Ya rungume ta tsam a jikinsa
“ki faɗi,duk abunda kike so, nayi miki alƙawarin zanyi miki shi a take batare da ɓata loka ci ba”
Murmushi ta kuma yi
“babu”
Ya ɗago ta yana kuma kallon fuskarta
“mu cigaba da rayuwa a haka dan Allah habibty”
Gyaɗa mai kai tayi
“shi kenan”
Washegari
Bayan ta fito daga wanka tana zaune tana shafa
Bayan tagama ta ɗauko doguwar riga ta saka tana zage zip ɗin
Ji tayi zip ɗin ya kuma zagewa, ta kuma zagewa still ya kuma
Juya wa tayi dan tasan shine
Aiko shi ɗin ta gani ya harɗe hannayesa yana murmushi
STORY CONTINUES BELOW
Ta maida mai martanin murmushin tana cewa
“nifa bana son tsokana”
Ya matso gab da ita yana mai-maita abunda tafaɗa
“nifa bana son tsokana”
Dariya tayi dan yadda yayi maganar shi a dole ya kwai-kwaye ta
“ka ganka ko? To me ya faru na ganka da rana haka”
Wani zobe yaciro yana nuna mata
“wallahi kin gansa nan, nazo wucewa ta wata kasuwa nagansa naga ze yi miki kyau a hannun ki shine na siyo miki”
Murmushi tayi tana duba siririn zoben zinarin
“wow gaskiya yayi kyau kamar kasan kuwa ina son siririn zobe”
Ya kama yatsanta yana zura mata zoben
“yaza’ai bazan san abunda matata take so ba?
Har lokacin da ragowar murmushi a fuskar ta
“na gode, abban Shahida”
“shhhhh”
Yayi yana ɗaura Yatsan sa akan bakin ta
“kar in ƙara jin kalmar godiya abakinki, dan babu ita a tsakanin mu”
Sallamar da aka yi a falon ce tasa ya sumbace ta a goshi
“kije kunyi baƙuwa,sai mun haɗu anjima”
Gyaɗa kai tayi tana murmushi
Ya ɓace ƙara zage zip ɗin tayi ta fito falon
Anty ummi ce
“zama tayi kan kujera cike da nisha ɗi tana duban Anty ummin
“kune da rana haka?
Anty ummi kallon ta tayi tace
” eh me ya faru a gidan ne?
Cikin rashin fahimta Rauda tace
“bangane ba”
“gani nayi kina ta farin ciki”
Anty ummi ta faɗa
Dariya Rauda tayi tana girgiza kai
“to babu abunda ya faru kinsan wata ran zakiji ki cikin annashuwa”
Anty ummi ta jinjina kai tana kallon zoben hannun ta
“wannan zoben fa, kamar zinari, ina kika samoshi?
Rauda ta girgiza kai tace
” a’a ba zinari bane, ɓarawon zinari ne, a makarantar mu wata take saida wa dubu ɗaya to tunda na siya ma ban taɓa sawa ba sai yau”
Anty ummi ta jinjina kai
“aiko kamar zinari wallahi,zan baki kuɗi idan kun koma
Kisiyomin, ina mama?
” ta shiga gidan maman murja anyi haihuwa”
Anty ummi ta miƙe
“dama hanif zanɗauko a makaranta nace bari in biyo, kince zakizo har yanzu baki zo ba”
Rauda ta miƙe itama tana yafa ɗan kwalin ta dan ta rakata
“kinsan banji daɗi ba kwana biyu amma zan zo jibi in Allah ya kai mu”
Anty ummi tace
“shi kenan in maman ta dawo ki gaishe ta”
Washe gari suna zaune a tsakar gida gabaɗayan su suna gyara masarar da baba ya kawo
Suna cikin gyaran aisha ta shigo yarinyar umma da ƙaramin akwati a hannun ta idanuwan nan nata sun yi jawur da alamu kuka taci
Tana shigowa umma tace
STORY CONTINUES BELOW
“me zan gani Aisha, yau ma ya jin kikayo”
Aisha ta tsugunna tana fashewa da kuka
“umma ni wallahi na gaji,Ace kullum nasiru sai yayi waya da ƴammata”
Umma maka ta kai mata cike da harzuƙa
“ubanki kenan, nace ubanki kenan Aisha, dan yayi waya da ƴammata shine abun yaji?
Mazan yanzu ba haƙuri ake yi da su ba, ina farin ciki hankalina ya kwanta na gama aurar da ku shine kike kike so ki tattago naki auran?
Ga wasu nan auran ma ya gagare su suna neman mazan ruwa a jallo basu samu ba”
Inna ta jinjina kai tace
“ƙwarai kuwa jummai, a zamaninnan in ka samu ka aurar da ƴaƴanka ai ka gama hajji da ummara”
Umma tace
“faɗa mata dai, wata ma sau biyu ana fasa auran ta kuma babu wanda ya ƙara shinshinar ta, sai ke da Allah ya tarfa ma garin ki nono ya rufa miki asiri kikayi auran zaki rinƙayin yaji
Maza tashi ki ɓace min da gani in ba kinaso in rufe ki da duka ba, sakarya kawai”
Mama Miƙewa tayi ta shige ɗaki dan tasan da ita suke yada haibaicin
Rauda ma Miƙewa tayi tabi bayan maman
A zaune tasa meta ta zuba uban ta gumi
Ta zauna gefen ta tace
“mama dan Allah kada abunda suka faɗa ya ɓata miki rai”
Mama ta sauke ajiyar zuciya tana jingina da kujerar
“dole ya dameni Rauda, kullum fatana Allah ya kawo miki miji kiyi aure amma har yanzu shuru, yanzu ankai matakin da babu me sallama wa yace yana kiranki
Addu’a nike, maganin nike nemar miki amma shuru”
Ta Ƙarasa maganar cike da tsananin damuwa
Jikin Rauda yayi sanyi sosai, tausayin mama take ji, anya wannan rayuwar da tekeyi a ɓoye da Aasim tayi wa kanta da mama adalci kuwa?
Ya zamar mata dole ta yi masa magana dan ta samu mafita
Dan tasan yana da hannu wajen ɗaukewar mane manta
Guntun numfashi ta sauke
Tace
“komai lokaci ne mama, kuma komai yayi farko yana da ƙarshe ki kwantar da hankalinki ai da banyi auran ba ba a zaune nike ba, karatu nikeyi”
Mama ta girgiza kai
“aure ai mutuncin ƴa mace ne, hankali na zefi kwanciya idan Naga kinyi auran kina cigaba da karatun”
Rauda tayi shuru kawai tana ƙara yin nazari
Allah Allah take yi dare yayi
A gaggauce tagama ayyukan da zata taya mama dan ranar itace da girki
Ƙarfe goma mama tayi mata sallama taja mata ƙofar da yike hadari ya taso sosai
Tana fita Aasim na bayyana a ɗakin
Cikin sauri Rauda tace
“yauwa dama yanzu nike shirin kiranka”
Kama hannun ta yayi yana ƙoƙarin janyo ta jikinsa
Ta dakatar dashi
“a’a Aasim, magana nike so muyi dan Allah”
Ganin yana yin fuskarta yasa ya gane da gaske take yi
Hakan yasa ya zauna a kan kujera itama ta zauna
STORY CONTINUES BELOW
“maganar me kike so muyi habibty?
Ta gyara zaman ta tana fuskantar sa
” ina so muyi wata muhimmi yar magana, kuma dan Allah inaso ka fahimce ni, ka kuma yarda da abunda zan faɗa ma”
Ya kaɗa kai
“to insha Allah ina jinki”
Ta sauke numfashi sannan ta fara cewa
“a gaskiya babu abunda nike so sama da kwanciyar hankalin mama, kuma hankalin ta baze kwanta ba har sai taga nayi aure sannan………..
Katseta yayi
” sannan me? Faɗamin kawai me kike so kice”
Ta kuma sauke numfashi a karo na biyu
“ina so kadena korar min mane mana kabar su su cigaba da zuwa….
” sannan me?
Ya tambaya cikin tsare gida da ɗaure fuska
“sannan kabarni inyi aure……..
” dakata dakata Rauda, kin san me kike cewa kuwa?
Ya faɗa cikin ɓacin rai
Jinjina kai tayi tace
“na sani Aasim, kuma kai ma ka san baze yuwu In cigaba da zama a haka ba, idan ni nasan ina tare da kai ai mutane basu sani ba…….
“kinga kima dakatar da waɗannan shirmamman maganganun naki”
Yafa ɗa yana kauda kansa
“magan ganun nawa ne shirme?
Ya jinjina kai yace
“eh shirmammu ne mana, ina so ki sani bazan taɓa barin wani ɗa namiji ya raɓeki ba, dan haka ki ma cire maganar aure a rayuwarki duk wani abun da ɗan adam zeyi miki nayi alƙawarin zanyi miki ninkin shi”
Kallon sa kawai take yi yadda ya tamke fuska kamar be taɓa dariya ba
Durƙusawa tayi a gaban sa idanuwan ta suka cicciko
“Aasim dan Allah na roƙeka,Hakan shine kwanciyar hankalin mama, ka riga da ka san a yanzu babu wanda nike so sama da kai, kuma bawai ina nufin kabar ni in yi aure dan inyi nisa da kai bane, a’a…
“kinga Rauda idan kinji abunda nafaɗamiki to, idan kuma baki ji ba bari in sake nanata miki
Bazan taɓa barin wani ɗa namiji ya raɓeki ba”
Runtse idanuwan ta tayi wasu siraran hawaye na gangarowa
“kenan haka kake so incigaba da rayuwa?
Ɓacewa yayi ransa a ɓace batare da ya ƙara ce mata komai ba
Ita ko Rauda fashewa tayi da kuka cike da tsananin damuwa
Haka ta kwana bata runtsa ba
Sai da suka yi kwana biyu be kuma zuwa inda take ba,bata damu ba dan haushin sa take ji sosai dan ta fahimci ba zasu daidaita dashi ba dan baze yuwu ta cigaba da rayuwa mutane suna yada Mata habai ci ba
Rana na ukun tana tsaye a ɗaki tana ninke kayan da ta kwaso akan igiya
Ɗagowar da zata yi suka haɗa ido
Maida kanta tayi kamar Bata gansa ba cigaba dayin abunda take yi
Hakan ya sosa masa rai amma sai ya danne ya ƙara so tare da rungume ta ta baya
“habibty fushi kike yi dani?
Janye jikin ta tayi tana kallon sa
” dan Allah ka rabu dani,ka ƙyaleni”
STORY CONTINUES BELOW
Ta faɗa cikin dakiya
Ajiyar zuciya ya sauke yana matsowa gab da ita
“shi kenan Naji nayi miki laifi, amma kiyi haƙuri”
“nayi”
Tafaɗa tana cigaba da ninke kayan
Cikin damuwa yace
“miye haka Rauda,? Nine fa?
Ta ɗaga ta watsa mai fararen idanuwan ta
“to inkaine sai mene Aasim? Me kake so ince maka? Tunda ka kasa fahimtata”
Ya girgiza kai yace
“ba haka bane, dan Allah ki saurareni, ranar ma raina ne ya ɓaci, kinsan ina ƙaunar ki, kishin ki da sonki ne suka hanani fahimtar ki a ranar”
Ta ajiye kayan tana faɗin
“shi kenan ina sauraron ka”
“amma ai ba atsaye zamuyi maganar ba ko?
Ta zauna bakin gado batare da ta sake magana ba
Ajiyar zuciya ya sauke yana zauna wa a kusa da ita
“to dan Allah ki saki ranki kinji? Ba na son ganin ki a yana yin ɓacin rai”
Ta sassauta ɗaurin da tayi ma fuskarta tana duban sa kawai
Gauron numfashi ya sauke yana kama hannun ta
“kinsan irin son da nike miki ba zaki taɓa neman wani abu agurina ban miki ba, amma gaskiya kamar yadda na faɗa miki bazan iya barin wani ɗa namiji ya raɓeki ba sai dai ina da wata mafita guda ɗaya”
Ta kallesa sosai
“mafita? To wace kalar mafita? Faɗi inji”
Ya gyara zama yana kuma fuskantar ta
“kinga ƙarfin da nike dashi idan na bayyana ga mutane da yawa ba zasu iya ganina ba
Ƙarfin da nike dashi mutum biyar ne zasu iya ganina,
To akwai wani kogo da ake zuwa a ƙasar Iraq inda wani tsohon rauhani yike
Idan rauhan yayi training awurinsa na tsawon watanni ƙarfin sa ze ƙaru ta yadda ze iya bayyana a bainar mutane da yawa
Kinga idan nayi sai inbayyana a gidan ku a matsayin mutum in kuma auranki kinga shi kenan baki da wata damuwa”
Kallon sa tayi da mamaki
“da gaske ana yin Hakan?
Ya jin jina kai
” da gaske, dan haka ina ganin jibi zantafi”
Jinjina kai tayi da sauri dan dama burinta be wuce ta rayu dashi ba, kuma tunda ga hanyar da babu wanda ze gane ai shi kenan
“dama ka san da wannan hanyar shine bakayi ba tun tuni?
” yanzu ai zanyi dole na”
Ya faɗa
Kama ɗayan hannun sa tayi cike farin ciki
“dan Allah ka tafi yanzu, wallahi ina son ka da kai kaɗai nike so nayi rayuwa a yanzu”
Murmushi yayi
“kwantar da hankalinki, jibi in Allah ya kai mu zan tafi,sai dai innata fi babu wata hanya da zata sa damu har sai na gama watannin da zanyi”
Kaɗa kai tayi tace
“to miye abun damuwa? In ka dawo ba shi kenan ba”
Ya jinjina kai
“shi kenan, yanzu hankalinki ya kwanta ko?
Ta ɗaga kai tana murmushi
Bayan kwana biyu suna tsaye suna sallama dan ranar ze tafi
” habibty dan Allah ki kula da kanki,na ajiye miki kuɗi a cikin akwatinki duk abunda zaki buƙata kiyi dasu,inda zan shiga bani da damar koda ganin ki ta madubi dan haka ki kula min da kanki”
Jinjina kai tayi tana ɗan murmushi
“baka da matsala, zan kiyaye insha Allah, kaima ka kula da kanka sosai”
Ya sumbace ta a goshi
“shi kenan ni zan wuce”
“Allah ya kiyaye hanya ta faɗa”
Ya ɓace, zama tayi zuciyar ta cike da kewarsa da ƙaunar ta
Bayan sati ɗaya lokacin komawarta makaranta yayi
Dan haka ta gama shirin ta tsaf, motar rana zata bi
Mama nasiha ta mata sosai akan ta cigaba da tsare mutuncin ta
Baba da kanshi ya kai ta tasha
Sai da yaga motar su ta tashi sannan ya tafi
Ita ko Rauda kallon gefen hanya take tayi zuciyar ta cike da tunanin Aasim
Ƙarfe biyar ta sauka a bakin makaranta
Inda Salma ke tsaye tana jiran ta dan ta riga ta dawowa
Tana ganin ta suka rungume juna cike da kewar juna, salmar ce ta ɗauki akwatinta tana tambayar ya hanya
“lafiya lau”
Ta bata amsa suna tsallakawa
Wata rantsattsiyar mota ce ta shanyo kwana a guje
Salma ta Ƙarasa tsallakawa da gudu yayin da takalmin Rauda ya turguɗe
Kafin tayi wani yunƙuri tuni motar ta bugeta
Faɗuwa tayi tana ambaton sunan Allah tare da tashi da sauri tana kallon motar
Ganin motar ta tsaya yasa ta duba ƙafarta inda take jin zafi da alamu anan ne taji ciwon
Wanda yike tuƙa motar ya fito hankalinsa a tashe
Fari ne tas, dogo kyakkyawan gaske
Da hanzari ya isa gabanta
Ganin ta durƙusa tana duba ƙafarta yasa shima ya durƙusa yana faɗin
“sannu baiwar Allah, kinji ciwo haka? Tashi mu tafi asibiti wallahi bada niyya ta na buge ki ba, saurin da nike yi ne”
Ƙirjinta ne ya fara bugawa yayin da taji tausassar muryarsa
“dan Allah tashi inkaiki asibiti, kinga jini na zuba a ƙafarki”
Gabanta ne ya sake faɗuwa,ƙarfin hali ɗagowa tayi ta kallesa suka haɗa ido
Atare gabansu yayi mummunan faɗuwa
Kallon-kallo kawai suke yi
Shine ya katse ɗauke wutar da suka yi ta hanyar kiran sunan ta
*”Rauda”*
Ƙirjinta ne yaci gaba da bugawa, zuciyar ta ta fara harbawa da sauri
Ganin wanda bata taɓa sa ran zata gansa a duniya ba
Har zata amsa sai magan-ganunsa na baya suka dawo mata
_”kada ki ƙara kirana ko nemana, kisa a ranki cewa baki taɓa sanina ba a duniya, ki gogeni daga rayuwarki”_
Nan da nan ɓacin ran shekarun da suka wuce ya dawo mata sabo fil
Miƙewa tayi tana jin raɗaɗin dake ƙafarta ya tafi sakamakon tuno wa da maganar sa da tayi
shi ko jikinsa na rawa ya kuma kiran sunan ta
“Rauda ba zaki amsa min ba?
Wani kallo tamasa tare da haɗe fuskarta
“ba sunana Rauda ba”
Tana gama faɗar haka tayi gaba
Yayi saurin shan gabanta
“Haba Rauda, nasan kece ki tsaya inkai ki asibiti”
Ranta ya soma ɓaci
“nace maka ni ba sunana Rauda ba, ka tafi ka ƙyaleni”
Ƴarfillo.
JINNUL*
*AASHIQUE🌹*
🧞♂🧞♂
🧞♂ +
NA
HARIRA ALIYU _(ƴarfillo)_🧕🏻
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer’s of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
Dedicated to _little hajjo_ and my elder sister _hafsat aliyu_
🅿AGE📕 3⃣7⃣
_Wannan page nakine *ummu sayyid* ina godiya da ƙaunarki ga jinnul aasshique_
_11:38_🕒 PM
WED, OCT 23
_Bissmillahir rahmanin rahim_✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
*Daga Cikin Ayyukan Alheri Da Kyawawan Halaye*
*Jabir bn Abdullahi, Allah ya yarda da shi, ya ce; Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce; “Idan duhun dare ya gabato – ko kuma almuru ta yi – to ku hana ‘ya’yanku fita, domin shaidanu suna bazuwa a wannan lokacin. Idan sa’a ta gota a cikin dare, to sai ku bar su. Ku rufe kofofi, kuma ku ambaci sunan Allah (yayin da kuke rufewa), domin Shaidan ba ya bude kofa rufaffiya. Ku zuge bakin salkunan ruwanku, kuma ku ambaci sunan Allah (yayin da kuke zugewa), kuma ku rufe kwanukan abincinku, ku ambaci sunan Allah (yayin da kuke rufewa); ko da ku dora wani abu ne a kan kwanukan. Kuma ku kashe fitilinku na a-ci-balbal.*
*Allah ya yi tsira da Aminci da albarka ga Annabinmu Muhammadu, da alayensa da Sahabbansa baki daya.*
Shin wai meke damunka ne Umar? Kana cikin hayyacin ka kuwa?
Ɗaga mata kai yayi yace
“nadai faɗa miki kada ki sake ki taɓani”
Ajiyar zuciya ta sauke me nauyi tare da miƙewa ta juya zata fita har ta kai bakin ƙofa ya kira sunan ta dan yadda yaga yanayin ta ya sauya Sam sai yaji beji daɗi ba
“Rauda!
Dakatawa tayi batare da ta juya ba
” kiyi haƙuri kinji?
Hmmmm ta sauke guntun numfashi tana cigaba da tafiya
“Rauda!
Ya kira sunan ta a karo na biyu
Juyowa tayi tana jingina da jikin ƙofar ta zuba mai ido kawai batare da ta amsa ba
Umar ya yunƙura ya tashi da ƙyar ya koma kan gadon har lokacin idanuwansa na kanta
” Rauda ina so ki ɗaukar min alƙawari tare da yin rantsuwar cewa ba zaki taɓa aikata abunda Aasim ya saki ba”
Sai lokacin ta gane dalilin da yasa yaƙi yadda ta taɓasa
Tsananin tausayin sa ne ya ƙara kanannaɗe zuciyar ta
Take hawaye suka ciko idanuwanta
“ina sonki Rauda, kisani idan kika aikata abunda ya saki yayi nasara wallahi ba tausayin rayuwa ta kika yi ba, ki sani zan kasance acikin farin ciki idan har zan cigaba da rayuwa da ke,ki taimaki zuciyata da ƙaunar da nike miki ki bar mu mu cigaba da rayuwa a haka “
Ya ƙarasa faɗa muryar sa na ƙara raunanewa
Komawa cikin ɗakin tayi ta zauna nesa kaɗan dashi
STORY CONTINUES BELOW
” shikenan ka kwantar da hankalin ka babu abunda zanyi Insha Allah “
” kinyi alƙawari?
Ya tambaya yana kafeta da ido
Ɗaga masa kai kawai tayi, amma a zuciyar ta bata fasa abunda tayi niyya ba
Hannu ya miƙo mata yana murmushin ƙarfin hali
Matsawa tayi ta kwantar da kanta a jikin sa
Gauron numfashi ya sauke yana lumshe idanuwansa a hankali
“kece kwanciyar hankali na Rauda ina sonki”
Ya faɗa a sanyaye
Aasim yana tsaye yana kallon su ta cikin madubin sa, wani irin baƙin ciki da kishi ne suka dunƙule suka tarun masa a wuri ɗaya
Wai Raudan sace kwance jikin wani yana faɗa mata kalaman soyayya, da ransa da lafiyar sa
Zagaye ɗakin ya fara yi yana furzar da wata iska me zafi dan shi kaɗai ya san yadda yike ji a ransa
Baze yuwu ba, baze yuwu in zuba muku ido ba na baki kwana biyu kacal wallahi idan baki aiwatar da abunda nace ba zakiga abunda zanyi
Ya faɗa a zafafe
Rauda taji maganar da yayi, gabanta ne ya faɗi
Aasim ya cigaba da cewa
“ki tashi daga jikin sa inba haka ba yanzu na illa ta shi”
Ta shi tayi da sauri ta ɗan ja baya kaɗan tana zazzare ido
Kallon ta umar yayi yace
“lafiya chuchu?
Girgiza kai tayi tace
” babu komai “
Ya gyaɗa kai ba tare da ya ƙara cewa komai ba
Aasim numfashi ya sauke me nawi dan sai lokacin ya ɗanji raɗaɗin da yike ji aransa ya ragu
Fulawar saƙo ce ta sauka a hannun sa ya buɗe ta
Saƙon ammi ne cewa tana son ganin sa ya same ta a iyakar shiga masarauta
Bayyana yayi a wurin, tana tsaye jikin bishiyar da suka saba haɗuwa a wurin, dan bayi da ikon shiga masarauta tun bayan tsalle ke tauran da yayi
Kallon sa ammi take yi cike da tsananin damuwa a fuskar ta ganin yadda ya lalace duk akan bil’adama
Cikin girmamawa ya gaishe ta, bata amsa mai ba illa zuba mai ido da tayi
Zuwa can ta kira sunan sa
“Aasim!
” na’am ammi”
Ya amsa yayin da yike ɗagowa yana duban ta
“yanzu kana ganin rayuwar da zaɓarma kanka ta dace da kai kenan?
Ta tambaya tana yi masa wani irin kallo
Ƙaƙaro murmushi Aasim yayi yace
” ammi nafaɗamiki kidena damuwa a kaina ina cikin farin ciki…
“ƙarya kake yi Aasim, dubi yadda ka lalace ka sauya kamar ba yarima ɗan babban sarki ba,da gatan ka da komai Aasim ka zauna kana wahala akan mace macen ma bil’adama wacce tayi maka butulci”
Ta ɗan tsaya sannan ta cigaba da cewa
“me yasa bazaka cire ta a ranka ba? Ga mata nan bila adadin a duniya Aasim zaka samu wacce tafi ta ka dawo masarauta ka nemi gafarar mahaifin ka ka dawo cikin gatan ka inda ake tarai-rayar ka Sam bana jin daɗin yadda nike ganin ka a haka”
Murmushin takaici yayi dan ya san ammi bazata taɓa ganewa ba, da zata gane son da yike ma Rauda da Sam bazata rinƙa faɗin maganganu haka ba shi kansa besan dalilin da yasa yike mata so me tsanani ba ya kuma kasa haƙura da ita
Guntun numfashi ya sauke har lokacin kansa na ƙasa
Ganin bayi da niyyar magana yasa ta girgiza kai cikin damuwa
“shikenan tunda har yau bani da matsayin da zance kayi abu kayi, nagode”
Matsowa yayi kusa da ita ya kamo hannun ta suka zauna still hannun ta na riƙe cikin nasa
Sam ya kasa danne hawayen da suka ciko kwarmin idanunsa
Cikin muryar sa me taushi yace
“ki gafarceni ammi,nasan ni me laifi ne tunda har na bijire wa umarnin ku, amma kimin uzuri dan Allah ammi, ammi nikaɗai nasan yadda nike ji acikin raina bazan iya rabuwa da ita ba”
Ammi tausayin sa ne ya ƙara ka mata dan tasan duk abunda zesa sa kuka ba ƙaramin abu bane
Nisawa tayi tana ajiye Gauron numfashi
“shikenan Aasim, Allah ya kawo ma mafita amma ka rage sanya ranka cikin damuwa kaji?
Gyaɗa mata kai yayi ba tare da yace komai ba
Magana tayi wa jakadiyar ta dake can gefe sai gata ta bayyana hannun ta ɗauke da shahida
Shahida na ganin sa ta faɗa jikin sa a guje cike da tsananin farin ciki
Aasim ya ɗagota cike da jin daɗin ganin ta dan tunda ya bar masarauta rabon shi da ya sake ganin ta dan sarki ramzad ya hana a fita da ita ko ina
“shahida na!
Ya faɗa yana kallon ta, cikin murna ta ƙara shige wa cikin jikin sa
Ammi dake kallon su cikin tausayawa tace
” kullum maganar ta baya wuce ina abban ta, amma me martaba ya hana fita da ita ko nanda can yau ma dan yayi tafiya ne Shine na samu na ɗauko ta”
Aasim yayi murmushi dan ganin ƴar tasa yasa yaji sanyi
“yaushe ze dawo ammi?
” kwana uku zeyi”
Ta bashi amsa
Aasim yace
“ammi to dan Allah Kibari in tafi da ita inyaso jibi da sassafe sai in maido da ita”
Ammi ta ɗan yi shuru tana nazari
“dan Allah ammi”
Ya faɗa cikin marai-raicewar murya
“shikenan kutafi”
Ƙarfe sha biyu saura ya dawo gida, kan kujera ya zaunar da ita ya cika mata gabanta da kayan tanɗe-tanɗe
Sai da ya tabbatar ta ƙoshi sannan ya tasa a gaba tana ta yi masa surutu
Dariya yike yi sosai, harda riƙe ciki abunda rabon shi da yayi har ya manta
Shahida yarinya ce me wayau da basira, sai da suka kwanta zasu yi barci sannan tace
“Abi ina ammina?
Danne abunda yaji a zuciyar sa yayi da ya tuna inda take ya ƙaƙaro murmushi yace
” kina son ki ganta ne?
Ɗaga mai kai tayi, ya ɗago yace
“to gobe zan kaiki wurin ta kinji, yanzu ki kwanta kiyi barci kinji?
Murmushin jin daɗi tayi, ta kwanta a Jikinsa bata daɗe ba barci ya ɗauke ta
Sai da ya tabbatar da baccin nata yayi nisa sannan ya kwantar da ita ya tsura ma fuskar ta ido yana jin ƙaunar ta a cikin ƙoƙon ransa
Madubin sa ya saita zuwa wurin Rauda
Tana kwance tana bacci fuskar nan tata tayi fayau kamar wacce ta yi watanni tana ciwo
A hankali yasa hannu ya shafi gefen fuskar ta cikin kalar wani yana yi na shauƙin ta, da yanzu suna tare suna soyayya amma wannan banzan ya ruguza masa tsarin sa
Lumshe idanuwan sa yayi yana ƙissima abubuwa da yawa a cikin ransa
Ɗan murmush yayi yabuɗe idanun yana kuma ɗaura su a kanta
“Rauda ke tawa ce nikaɗai”
Ya faɗa cikin wata kalar murya
*~Ƴarfillo.~*
JINNUL*
*AASHIQUE🌹*
🧞♂🧞♂
🧞♂ +
NA
HARIRA ALIYU _(ƴarfillo)_🧕🏻
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer’s of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
*Addu’ar Sallar Istihara (Neman Zabin Allah Idan Mutum Zai AikaTa Wani Abu).*
*Jabir Ibn Abdullah, Allah ya yarda da shi da mahaifinsa, ya ce; Manzon Allah (SAW), tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya kasance yana koya mana yin istihara (neman zabin Allah) a Cikin dukkan al’amura kamar yadda yake koya mana sura daga Cikin Alkur’ani, yakan ce, “Idan dayanku ya yi niyyar yin wani al’amari to ya yi sallah raka’a biyu ba ta farilla ba, sannan ya ce;*
اَللَّهُمَّ إِنِّي أَسْتَخِيرُكَ بِعِلْمِكَ، وَأسْتَقْدِرُكَ بِقُدْرَتِكَ، وَأَسْألُكَ مِنْ فَضْلِكَ الْعَظِيم، فَإِنَّكَ تَقْدِرُ وَلا أَقْدِر، وَتَعْلَمُ وَلا أَعْلَم، وَأَنْتَ عَلاّمُ الغُيوبِ، اللّهُمَّ إِنْ كُنْتَ تَعْلَمُ أَنَّ هَذَا اْلأَمْرَ- وَيُسَمِّي حَاجَتَهُ – خَيْرٌ لِي فِي دِينِي وَمَعَاشِي وَعَاقِبَةِ أَمْرِي، عَاجِلِهِ وَأَجِلِهِ فَاقْدُرْهُ لِي وَيَسِّرْهُ لِي ثُمَّ بَارِكْ لِي فِيهِ، وَإِنْ كُنْتَ تَعْلَمُ أَنَّ هَذَا اْلأَمْرَ شَرٌ لِي فِي دِينِي وَمَعَاشِي وَعَاقِبَةِ أَمْرِي، فَاصْرِفْهُ وَاصْرِفْنِي عَنْهُ وَاقْدُرْ لِي الْخَيْرَ حَيْثُ كَانَ ثُمَّ أَرْضِنِي بِهِ.
*Allahumma innee astakheeruka bi’ilmik, wa-astaqdiruka biqudratik, wa-as-aluka min fadlikal-‘azeem, fa-innaka taqdiru wala aqdir, wata’lamu wala a’lam ,wa-anta ‘allamul ghuyoob, allahumma in kunta ta’lamu anna hazal-amr (say your need) khayrun lee fee deenee wama’ashee wa’akibati amree fakqurhu lee, wayassirhu lee, thumma barik lee feeh, wa-in kunta ta’lamu anna hazal-amr sharrun lee fee deenee wama’ashee wa’aqibati amree fasrifhu ‘annee wasrifnee ‘anh, waqdur liyal-khayra haythu kan, thumma ardinee bihi.*
*Ya Allah! Ina neman zabinka domin iliminka, kuma ina neman Ka ba ni iko domin Ikonka, kuma ina rokonka daga falalarka Mai girma; domin Kai ne mai iko ni kuwa ba ni iko, kuma Kai ne Masani, ni kuwa ban sani ba, kuma Kai ne masanin abubuwan fake. Ya Allah! Idan ka san cewa wannan al’amari sai ya ambaci bukata tasa alheri ne gare ni a cikin addinina, da rayuwata, da kuma karshen al’amarina a wata rayuwar; da magaggaucin ala’marina da majinkircinsa Ka kaddara mini shi, kuma Ka saukake mini shi, sannan Ka albarkance ni a cikin sa. Kuma idan Ka san wannan al’amari sharri ne gare ni a cikin addinina, da rayuwata da karshen al’amarina a wata ruwayar; da magaggaucin al’amarina da majinkircinsa – Ka kawar da shi daga gare ni, kuma Ka kawar da ni daga gare shi, kuma Ka kaddara mini alherin a duk inda yake, kuma Ka sanya ni in yarda da shi”.*
*Duk wanda ya nemi zabin mahalicci, kuma ya yi shawara da talikai muminai, kuma ya yi azama a Cikin lamarinsa, to ba zai yi nadama ba, domin Allah madaukakin sarki Ya ce;*
(وَشَاوِرْهُمْ فِي اْلأَمْرِ فَإِذَا عَزَمْتَ فَتَوَكَّلْ عَلَى اللهِ)
*(Washawirhum Fiyl Amri Fa’iza Azamta Fatawakkal Alallahi).*
STORY CONTINUES BELOW
*”Kuma ka shawarce su cikin lamarinka, idan kuma ka kuduri aniya, to ka dogara ga Allah”.*
Dedicated to _little hajjo_ and my elder sister _hafsat aliyu_
🅿AGE📕 3⃣8⃣
_wannan page nakine *jamila Aliyu* masoyiyar Aasim, Aasim yana yinki irin sosai ɗinnan_
_10:23_🕒PM
Sun, Oct 27
_Bissmillahir rahmanin rahim_✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
_(mu yawaita karatun al qur’ani,mu maida al a marin mu ga ubangiji dan shi ze yi mana maganin komai, Allah ya tsarkake zuciyar mu ya biya mana buƙatun mu amin)_
Tun cikin dare umar ya farka sakamakon wani azazzaben ciwon ciki da ya farkar dashi
Zamowa ƙasa yayi yana riƙe cikin, cikin tsananin wahala
Sai da yayi ta karanto addu’a sannan yaji cikin ya lafa masa, gumi ne kawai ke ta keto masa duk da ac ɗin da yike ƙure kuwa
_”ya Allah ka kawo min agaji, ka fitar dani daga cikin wannan ƙangin”_
Ya faɗa a hankali,komawa yayi kan gadon ya tsura ma fuskar ta ido,ko kaɗan baya jin a ransa cewa ze iya rabuwa da ita, ko da kuwa wannan ciwon zeyi ajalin sa ne
Shin wace irin ƙauna ce yike mata, Meyasa yike jinta a cikin jinin jikin sa?
Tabbas ita ɗin ta dabance,haka yayi ta saƙe-saƙe
Washegari jikinsa ya kuma tsanani sosai dan magana ma da ƙyar yike iya yi
Tana tsaye a gefen gadon tana kallon sa, gabaɗaya ya fita hayyacin sa zayyad ne zaune gefen sa yana goge masa jikin sa da towel
Fita tayi daga ɗakin jin kuka na neman ƙwace mata, ɗakin ta ta shiga ta zauna takifa kanta akan gwiwarta wasu hawaye masu ciwo suna gangaro mata
Motsi taji a gefen ta, ta ɗago kanta a hankali,shahida tagani a gefen ta
Zuba mata ido tayi taka sa ce mata komai
“ammi”
Shahida ta faɗa cikin murmushi, Rauda tayi ƙoƙarin ƙaƙaro nata murmushin tana faɗin
“shahida, kece? Waya kawo ki?
“abbi”
Ta bata amsa a taƙaice,kallon ta Rauda ta cigaba da yi tana mamakin irin kyan yarinyar
Shahida ta kwantar da kanta kan cinyar ta tana faɗin
“kullum-kullum sai na cema Ammi babba takawoni inganki sai taƙi, Ammi ina son ganin ki kullum kice ma abi ya barni anan kinji?
Ɗan murmushi Rauda tayi tare da ɗagota tace
” kina son ki zauna tare dani shahida?
Shahida ta ɗaga kai
“shikenan Kibari nan gaba zan sa a dawo min dake nan kinji?
Cikin murna da jin daɗi Shahida tace
” to ammina”
Rungume ta Rauda tayi tana ɗan shafa bayan ta
“ina babanki?
“yana can gida yace ina gama ganin ki ze zo ya ɗaukeni”
Rauda ta gyaɗa kai
Sai bayan awa ɗaya sannan Aasim ya bayyana a cikin ɗakin
Kallo ɗaya yayi ma Rauda ya ɗauke kansa yana duban Shahida
“tuffah zo mu tafi ko?
Maƙale kafaɗa tayi
” nidai anan zan zauna”
“tuffah bakya so na kawo ki gobene? Taso mu tafi kinji?
STORY CONTINUES BELOW
Shahida ta marairaice fuska tana duban Rauda
“ki tashi ku tafi kinji, baki ji yace ze kawo ki gobe ba”
Rauda ta faɗa, Shahida ta mayar da kallon ta ga Aasim tace
“to abi kace ammi ta tashi mu tafi tare”
Durƙusawa Aasim yayi ya kama hannun ta yana murmushin takaici
“Shahida na anmin ki bazata bimu ba, bata son rayuwa damu kiyi haƙuri kinji”
Shahida zata kuma magana ya girgiza mata kai
“kada ki ƙara cewa komai”
Ya ƙarasa faɗa yana miƙewa tare da ɗaukar ta
Juyawa yayi zetafi batare da ya ƙara duban inda Rauda take ba
“ina son yin magana da kai”
Ta faɗa idanuwanta a kansa
Tsayawa yayi batare da ya juya ba
“inajin ki”
Ajiyar zuciya ta sauke tare da miƙewa ta zagayo gabansa
Kallon cikin ido su kayi ma juna, daga bisani ta zame nata idanun
“gobe ne zan aiwatar da abunda kace saboda na zaɓi lafiyar sa akan zamana dashi”
Ta ɗan numfasa tana ɗago idanuwanta ta kuma ɗaura su akan sa
“zan rabu dashi kamar yadda ka umar ta, amma inaso kasani bazan cigaba da yin tarayya da kai ba, zan yi rayuwa ta ni kaɗai”
Be bata amsa ba sai da yaɓattar da Shahida zuwa can gida dan baya so yayi magana a gaban ta
Sannan ya matso gab da ita yana kallon ta da idanuwansa da suka fara canza launi
“ni kike faɗa mawa ba zaki cigaba da yin tarayya dani ba?
Ki tuna cewa kinyi alƙawarin yin rayuwa dani har abada, dan haka baki isa ki janye wannan alƙawarin ba ki shirya ma cigaba da rayuwa dani har zuwa tsufanki”
Be jira yaji abunda zata ƙara cewa ba ya ɓace
Dafa kanta tayi da yike mugun sarawa,ta lalubo layin anty ummi ta sanar mata halin da ake ciki da kuma abunda zata yi
Cikin kuka take mata magana, ta ƙara da cewa
“kije gida ki sanar ma su mama dan zuwa nan da kwana uku zan taho”
Anty ummi cikin damuwa tace
“amma Rauda aganina karki aikata wannan abun,ki ƙara jira aƙara gwada na wasu malamai”
Girgiza kai Rauda tayi tace
“dan baki ga halin da yike ciki bane anty, yaufa ko magana baya iya yi, haka Allah ya so kawai”
Katse wayar tayi tana cigaba da yin kuka
Anty kaltum da ta daɗe tsaye a bakin ƙofa ta sauke numfashi tana ƙarasa shigowa cikin ɗakin
Zaunawa tayi gefen ta tace
“Rauda dan Allah ki kwantar da hankalin ki,ki dena kukannan haka dan ba maganin da ze yi miki”
Cikin shesshekar kuka tace
“shi kaɗai yike ragemin raɗaɗin da nike ji anty”
Anty kaltum ta kuma sauke numfashi a karo na biyu
“bana so kina sawa ranki damuwa,ina da yaƙinin komai ze wuce ya zama tarihi Insha Allahu”
Kaɗa kai kawai Rauda tayi,suka yi shuru naɗan lokaci sannan anty kaltum tace
STORY CONTINUES BELOW
“nida zayyad mun gama shirya komai, gobe idan Allah ya kai mu sai kiyi abunda yace ɗin, amma duk da haka ba zamu zauna ba dan ma yadda jikinna sa yayi tsanani ne da ba zaki yi abunda yace ba,amma nan da sati ɗaya zantafi Sudan wata ƙawata ta cemin akwai wani malami ƙwararre acan,zanje gurin sa”
Rauda ta jinjina kai kawai dan a yanzu itama maganar wahala take yi mata
Yana zaune ƙasan wata bishiya yana kallon shahida dake ta tsalle-tsallenta dan ita ta matsa sai ya fito da ita
Gabaɗaya ya Lula cikin tunani maganar ta ce kawai take yi masa yawo a kunne
_”zan rabu dashi kamar yadda ka umar ta, amma inaso kasani bazan cigaba da yin tarayya da kai ba, zan yi rayuwa ta ni kaɗai”_
Ajiyar zuciya ya sauke,tare da miƙewa ya kama hannun shahida
“tuffah mu tafi gida ko, kinga anfara kiran sallah”
Shahida ta ajiye sandar da take wasa da ita suka fara tafiya, sun zo wuce wa ta wani gida wata yarinya ta watso ruwan zafi sai a ƙafar shahida
Ƙara shida ta saki, Aasim yayi saurin durƙusawa yana duba ƙafar
Ita ko wacce ta watso ruwan ko a jikinta harkokin ta ma ta cigaba da yi dan ita bata san akwai wasu bayin Allah a wurin ba
Mahaifiyar ta dake zaune nesa kaɗan da ita tace
“wai bana hanaki zubar da ruwan zafi ƙasa bane?
Aasim numfashi ya sauke ya ɗauki shahida ya wuce
Kan kujera ya zaunar da ita yana sa mata ruwan sanyi a ƙafa
Sai da taci kukan ta sosai yana lallashin ta sannan tayi shuru
Zuwa can tace
” abi Meyasa baka yi mata magana ba, ƙonani fa tayi kuma naji zafi”
Murmushi Aasim yayi yana kama hannun ta yace
“shahida na,ki sani mu halitta ne da Muke rayuwa a ɓoye dole ne sai mun sa haƙuri a zuciyar mu, kinga ita bata san mun zo wuce wa ta wurin ba tunda bata ganin mu,kiyi haƙuri kinji?
_(mu kiyayi watsar da ruwan zafi a ƙasa,domin muna iya watsawa a kansu kuma idan ba aci sa’a ba aka watsa ma marasa haƙuri sai kuga sun shafi lafiyar mutum,mu kiyaye dan Allah)_
Shahida ta jinjina kai
“yauwa yarinyar kirki Allah yayi miki albarka”
Ya faɗa yana janyo ta jikin sa
Washe gari,Rauda na zaune gefen sa, shi ko yana kwance kamar matacce
Share guntun hawayen da ya zubo mata tayi ta shafa hannun ta sai ga ƙaramar wuƙar ta fito
Kamar anfaɗa masa ya buɗe idanuwansa ya tsura mata ido
“Rauda na faɗa miki, bazan yafe miki ba idan har kika aikata hakan”
Umar ya faɗa da ƙyar
“ka gafarce ni umar,ka gafarce ni……..
Ta faɗa tana caka mai wuƙar
Runtse idanuwansa yayi jin wani sabon raɗaɗi a ƙirjin sa ahanakali yaji tunanin sa ya fara gushewa
Ita ko kuka ta fashe da shi,daidai lokacin su anty kaltum suka shigo
Minti arba’in ya kwashe a sume,abun har ya fara basu tsoro ganin har lokacin ko alamar motsi baya yi
Sai da ya kwashe awa ɗaya a haka sannan ya sauke numfashi tare da yin miƙa yana karanto addu’ar farkawa daga barci
STORY CONTINUES BELOW
_alhamdulillahil lazi ah yana, ba’a dama a matana wa ilaihin nushur_
Ya ƙarasa faɗa yana buɗe idanuwansa gaba ɗaya
Ɗai-ɗaiya ya fara kallon su, dan shi ji yayi kamar daga barci ya tashi
Ganin yadda suka mai ƙuri-ƙuri da ido ya sa ya tashi zaune yana kuma ƙare musu kallo
Ɓangaren Aasim kuwa jiya yi zuciyar sa tayi fes,ajiyar zuciya ya sauke me nawi yana kishin giɗa a kujera
*~ƴarfillo~*.
*🌹JINNUL*
*AASHIQUE🌹*
🧞♂🧞♂
🧞♂
NA
HARIRA ALIYU _(ƴarfillo)_🧕🏻
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer’s of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
*Daga Addu’o’in neman tsayar da ruwan sama*
اَللَّهُمَّ حَوالَيْنَا وَلاَ عَلَيْنَا، اَللَّهُمَّ عَلَى اْلآكَامِ وَالظِّرَابِ، وَبُطُونِ اْلأَوْدِيَةَ، وَمَنَابِتِ الشَّجَرِ.
*Allahumma hawalayna wala ‘alayna, allahumma ‘alal-akami wazzirab, wabutoonil-awdiyah, wamanabitish-shajar.*
*Ya Allah! Ka sanya shi ya zuba a kewayenmu ba a kanmu ba. ya Allah! Ka sanya shi a kan jigayi da duwatsu, da cikin rafuka, da wajen saiwoyin itatuwa.*
Dedicated to _little hajjo_ and my elder sister _hafsat aliyu_
🅿AGE📕 3⃣9⃣
_Wannan page nakune masoya na masu haƙuri da daɗewa da nike yi amma still suna biye dani ina roƙon Allah da ya bar mu tare ya kuma ƙara danƙon zumunci a tsakanin mu_
_9:34_🕒 AM
Sun, Nov 3
_Bissmillahir rahmanin rahim_✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
Sai da yayi wanka ya sauya kaya zuwa blue jeans da farar t-shirt sannan ya sauko ƙasa
A kan dining ya same su, anty kaltum da mijinta, hajiya,da kuma zayyad
Ya zauna yana faɗin
“wai hajiya yaushe kika zo ƙasar ne? Sam ni na kasa fahimta ga yana yin gidannan duk ya Sauya kamar bashi ba”
Kasa bashi amsa suka yi dan basu san me zasu ce mishi ba
Amsar plate ɗin da anty kaltum ta miƙo mai yayi, har ɗiba a cokali ze kai bakin sa idanuwansa suka sauka kan zayyad,a iya sanin sa da zayyad baya ƙaunar gashi a fuska amma gashi duk ya bar sake da gemu
Aje cokalin yayi da mamaki sosai a fuskar sa
“zayyad yau Kaine da saje? Shekaran jiya fa da muka rabu babu komai a fuskar ka”
Zayyad ya ɗan daburce yana tunanin amsar da ze basa
Tsura musu ido umar yayi tabbas akwai abunda suke ɓoye masa cikin yanayin damuwa yace
“wai dan Allah me yike faruwa ne? me kuke ɓoye min?
Alh sadik(mijin anty kaltum) shine dabara ta faɗo masa yace
STORY CONTINUES BELOW
“umar dole fa zaka sauye-sauye da yawa,domin yau shekarunka biyar kenan kana barci sai yau Allah yasa ka farka”
Zaro ido umar yayi yana kallon Alh sadik, daga bisani kuma ya kece da dariya
Ido kawai suka zuba masa, sai da yayi dariyar sa me isar sa sannan yace
“wani irin bacci ne kuma na shekara biyar?dan Allah baban Salim ka ajiye wasannan a gefe ku faɗamin me yike faruwa?
Hajiya tace
” da gaske ne abunda ya faɗa ma,Allah ya jarabce ka da lalura kuma dai tunda ya yaye maka banason yawan tambayoyi”
Shuru umar yayi yana kallon hajiya, dan Sam be yarda da maganar su ba,amma ganin yanayin da suka shiga yasa yace
“shikenan hajiya, kice inji tsoron ƙara kwantawa barci kada insake yin na shekara goma”
Ya ƙarasa faɗa yana guntse dariya
Zayyad ya miƙe yana faɗin
“ni ina ganin zan wuce”
Umar shima ya miƙe yace
“bari mu fita tare,inga gari dan nasan abubuwa sun caccanza shekaru biyar ba wasa bane”
Ya faɗa cikin tsokana da dariya
Anty kaltum ta girgiza kai tace
“bafa inda zaka je umar dan baka gama warware wa ba kabari ka ƙarasa jin sauƙi tukunna”
Be saurare ta ba yayi gaba yana ɗan jijjiga jikin sa
“anty ni wallahi ƙalau nike,sai na dawo”
A tsakar gida ma, motocin da ya sani basu ya gani ba har ze yi magana sai kuma ya fasa yana faɗin
“komai ya canza, hajiya tace banda yawan tambaya, zayyad wacece motar ka a ciki?
Ya ƙarasa faɗa yana kallon zayyad
” banzo da mota ba”
Zayyad ya bashi amsa
“Ok mu shiga waccan Naga kamar da makulli a ciki”
Shiga suka yi ya tada motar,tunda suka hau titi babu wanda yayi magana, jefi-jefi dai umar kan kalli zayyad ya tun tsire da dariya
Abun ya fara ba zayyad haushi cikin ƙufula yace
“wai mahaukaci na zamar ma ne?
Umar ya kuma yin dariya har da buga sitiyari
” no abokina sajennan ne naga yayi ma kyau sosai, sai yasa ka zama kamar wani ustaz wallahi”
Tsaki zayyad yayi yana maida kallon sa gefe
Umar ya kuma dariya
“yi haƙuri abokina, faɗamin yanzu ina zamuje?
“ka ajeni a gida inyaso duk inda zaka je sai kaje”
“ai baka isa ba wallahi, tare muka saba fita kuma dolenka yanzu ma mu je da kai”
Sanin halin sa da zayyad yayi yasa marai-raice fuska yace
“please umar wallahi kaina ciwo yike yi”
Umar gyaɗa kai yayi yana canza hanya zuwa hanyar gidan su
A ƙofar gida ya ajesa sannan ya dinga zagaye gari bashi ya koma gida ba sai sha ɗaya da rabi
Lokacin duk sun kwanta,Rauda na tsaye a kitchen tana tsiyaya ruwan zafi a kofi dan sai lokacin taji tana jin yunwa
Bayan ta gama haɗa tea ta fito zata koma ɗaki
Dai-dai lokacin shi kuma umar ya shigo be kula da ita ba dan babu haske sosai a ɗakin suka ci karo
Kofin hannun ta ya faɗi ƙasa tean ya zube,ɗan ja baya tayi da sauri gudun kar ya fallatsan mata a ƙafa
Ido umar ya zuba mata,yana so ya tuna a inda ya Santa
STORY CONTINUES BELOW
Duk da babu wadataccen haske falon ne hana ta ganin kyakkyawar fuskar sa kasancewar sa fari sosai
Hannu ya kai ya kunna glop ɗin falon, still idanuwansa na kanta
Ji tayi kamar kar ta ɗauke nata idanun dan gani tayi yayi mata wani irin kyau
Jin hawaye na neman cika mata ido ya sa tayi saurin sadda kanta ƙasa
A hankali ya fara taka wa zuwa inda take sai da ya rage be fi taku ɗaya tsakanin su ba sannan ya tsaya
Ɗago kanta tayi, karaf idanuwan su suka sarƙe da juna
Yarrr yaji wani abu ya tsarga a jikin sa,yayi saurin lumshe idanuwan sa zuciyar sa ta fara bugawa a hankali
Ganin haka yasa tayi saurin hayewa sama, buɗe idanuwansa yayi yana bin bayan ta da kallo
Har ta shige sannan ya sauke idanuwan sa tare da zama kan kujera
Wacece ita?Meyasa yaji zuciyar sa na bugawa a sanda ya kalli cikin idanuwan ta?
Ya jero ma kansa tambayoyin da ya bayi da amsar su
Miƙewa yayi jikin sa babu ƙwari, wani ɗaki anty kaltum take? Dole yaje ya tambaye ta
Sama ya hau ya buɗe ɗakin farko,hajiya ya gani kwance tana ta munshari
Ya maida mata ƙofar ya rufe a hankali sannan ya wuto ze dawo ƙasa
Shesshekar kuka ya fara ji a hankali a ɗakin da ke kusa da wanda hajiya take
Murɗa ƙofar yayi a hankali tare da turawa
Gefen gado ya hango ta ta kifa kanta tana kuka
Runtse ido yayi dan jin kukan nata yayi har cikin ƙoƙon ransa
Murɗa ƙofar da taji anyi ne yasa ta ɗago kanta
Tayi ƙoƙarin mai da ragowar kukan tare da share fuskar ta da sauri
A jiyar zuciya ya sauke
“wani ɗaki anty kaltum take?
” tana ɗakin ƙasa”
Ta bashi amsa,juyawa yayi ya maida mata ƙofar ya rufe
Sai da ya ƙwanƙwasa ƙofar sannan ta buɗe dan ta rufe
Ganin sa yasa taɗan yi mamaki
“umar baka kwanta ba? Ba dai jikin bane ba ko?
Girgiza kai yayi yace
” a’a lafiya ta ƙalau, inaso muyi magana ne”
Bashi hanya tayi ya shige sannan ta bi bayan sa, a gefen gado suka zauna
“inajin ka”
Sai da ya sauke numfashi sannan yace
“anty wacece wannan dana gani?
Ta san Rauda yike nufi kuma dama ta tanaji amsar da zata bashi dan ta san dole ze tambaya
“ƴar’uwar baban Salim ce,ya ɗauko ta ta dawo wurina da zama”
“amma meyasa Naga tana kuka, akwai wani abu dake damun tane?
Manage plz banda caji
*~ƴarfillo~*.
*🌹JINNUL*
*AASHIQUE🌹*
🧞♂🧞♂
🧞♂
NA
HARIRA ALIYU _(ƴarfillo)_🧕🏻
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
STORY CONTINUES BELOW
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer’s of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
Dedicated to _little hajjo_ and my elder sister _hafsat aliyu_
🅿AGE📕 4⃣0⃣
_wannan Page nakine fretu muna godiya da yabawa ma rubuta golden pen da kike yi muma muna yinki kuma muna tare dake irin sosai ɗinnan_
_10:19_🕒 AM
Thu, Nov 7
_Bissmillahir rahmanin rahim_✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
Addu’a Yayin Da Aka ga Tumu,
اَللَّهُمَّ بَارِكْ لَنَا فِي ثَمَرِنَا، وَبَارِكْ لَنَا فِي مَدِينَتِنَا، وَبَارِكْ لَنَا فِي صَاعِنَا، وَبَارِكْ لَنَا فِي مُدِّنَا.
Allahumma barik lana fee thamarina, wabarik lana fee madeenatina, wabarik lana fee sa’ina wabarik lana fee muddina.
Ya Allah! Ka albarka ce mu a cikin kayan gonarmu, ka albarkan ce mu a garinmu, Ka alabarkance mu a kwanon awonmu, Ka albarkan ce mu a mudun awonmu.
Washe gari
Tana tsaye saman bene ta tsakar gida,ta dafa jikin zagayayyen ƙarfen da yayi ma wurin gajeruwar katanga,wasu tsuntsaye biyu ta tsura ma ido da suke ta shawagi a jikin bishiyar gidan
Jikin ta ne ya bata ana kallon ta, ta sauko da kallon ta ƙasa
Umar ta gani tsaye ya harɗe hannayen sa a ƙirji ya zuba mata dara-daran idanuwansa
Tsawon minti biyu suna kallon juna daga bisani ta janye nata idanun ta maida su gurin bishiyar
Numfashi umar ya ajiye sannan ya fara taka matakalar a hankali, duk da tana jin sawun hawowar sa besa ta kuma juyawa ba
Har sai da ya ƙarasa hawowar, kamar yadda tayi shima haka yayi dafa ƙarfen yayi da hannayen sa duka biyu
“barka da yammaci”
Umar ya faɗa yana ƙoƙarin saisaita idanuwansa a kanta
“yauwa barka”
Ta amsa mai a taƙaice
Yayi ɗan shuru yana tunanin abunda ze ce mata,ita ko gaban tane ya fara faɗuwa dan gani take kamar yana gab da dawowa cikin tunanin sa
“anty ta cemin gobe zaki koma garin ku ko?
Ya tambaya
Ɗaga masa kai kawai tayi alamar eh batare da tayi magana ba
Ya sauke guntun numfashi tare da faɗin
“shin bakya jin daɗin zama damu ne?
Shuru bata amsa mai ba,ya lumshe idanuwansa na ƴan sakwanni sannan ya sake buɗesu ya kuma ɗaura su akan ta
“bansan me yasa nike jin zuciya ta na bugawa ba a duk sanda na ganki,dan Allah kada kiyi nisa dani”
Yana yin yadda ya ƙarasa maganar ya sa jikinta ya ƙara yin sanyi
Tabbas ƙaunar da yike mata ba kaɗan bace,tunda har yanzu ya kasa dena jinta a cikin ransa duk da tuggun da Aasim yayi a tsakanin su
Take idanuwanta suka ciko da hawaye,matso wa yayi gab da ita yana ci gaba da cewa
STORY CONTINUES BELOW
“ki ci gaba da zama a nan please”
Sai lokacin ta ɗago ta zuba mai idanuwanta wanda suke cike taf da hawaye
A hankali hawayen suka fara gangarowa daga kurmin idanun ta
Juyawa tayi tabar wurin da sauri dan bazata iya jurar tsayawa a wurin ba
Ɗakin ta ta faɗa tana fashewa da kuka me ciwo,ya zamar mata dole tayi gaggawar barin gidan dan inbahaka ba ta san al’amarin yana gab da kuma jagulewa
Kayan ta ta fara haɗawa a akwati,tana haɗawa tana kuka
A haka anty kaltum ta shigo ta same ta, gabaɗaya tausayin ta ya gama cika zuciyar anty kaltum
Nasiha tayi mata sosai da kuma cewa ta kwantar da hankalin ta dan sauran kwanaki tafiyar ta Sudan
Cikin dare,Rauda ta kasa runtsawa ko kaɗan,tana zaune kan darduma bayan ta idar da nafiloli
Hakanan taji tana son taga umar,har ta miƙe wani sashi na zuciyar ta ya haneta
“yanzu idan kika tafi kinsan ranar da zaki ƙara ganin sa?
Wata zuciyar ta tambaye ta,jikinta ba kuzari ta kalli agogon ɗakin
Ƙarfe biyu na dare, tasan yanzu yayi barci hakan yasa ta fito daga ɗakin ta, ta murɗa ƙofar bedroom ɗinsa a hankali
Kwance ta hango sa yana bacci,ta maida ƙofar ta rufe sannan ta taka a hankali zuwa bakin gadon
Durƙusawa tayi sai tin fuskar sa ta tsura mai ido
Tunda take a duniya bata taɓa ganin me kyan umar ba, yana da wani irin sihirtaccen kyau me cike da haiba
“karki tafi please ki zauna tare dani”
Ya faɗa cikin barci da alamu mafarki yike yi
Ɗan murmushi tayi me cike da damuwa tare da kama hannun sa a hankali cikin murya ƙasa-ƙasa tace
“zantafi ne ba dan inaso ba jaana,zan barka a zahiri amma kasani zuciya ta na gare ka gangar jikina ce kaɗai zata yi nisa da kai..
Ta numfasa tana kai bakin ta dai-dai goshin sa ta sumbata
Hawaye ne masu ɗumi suka fara gangaro mata
Tayi saurin kauda fuskar ta daga tasa tare da miƙewa tabar ɗakin
Asubar fari tayi wa su anty da hajiya sallama dan bata so umar ya dawo masallaci ya same ta
Dama driver na jiran ta, ta shiga motar tana hawaye
Basu ɓata lokaci ba driver yaja suka wuce
Suna tafe tana tunanin yadda rayuwar ta zata cigaba da kasancewa
A haka bacci ɓarawo ya sace ta tunda dama bata runtsa ba ko kaɗan
Sanda ta farka mamaki ne ya kamata ganin ita da tasan tana cikin mota suna tafiya amma ta ganta kwance kan wani ƙayataccen gado
Yunƙurawa tayi ta zauna tana ƙare ma ɗakin kallo, babu shakka gidan Aasim ne
Ta dafa kanta cikin damuwa,dan tasan su mama zasu shiga tashin hankali tunda sun san ta taho
A haka Aasim ya shigo fuskar sa ɗauke da walwala da nishaɗi
“habibty sannu kin farka”
Bata bashi amsa ba illa zuba mai ido da tayi,ya ƙara so ya zauna yana sakar mata lallausan murmushi
Kallon sa ta cigaba da tayi, cikin tsananin damuwa tace
“Meyasa kake yimin haka ne, duk abunda kace inyi nayi me yasa ba zaka barni in samu natsuwa ba tukun?
STORY CONTINUES BELOW
Aasim ya sauke ajiyar zuciya yace
“duk natsuwar da kika samu ta kusan shekara bata isheki ba, wata kuma kike buƙata?
Kinga habibty a yanzu bazan iya jurar rashin ki ko da na misƙala zarratun ba,bazan kuma yarda nayi sakacin da nayi a baya ba”
Guntun numfashi ta sauke me cike da takaici
“me kake nufi kenan,ka rabani da mijina iyayena suma rabani da su zaka yi?
Ya ɗan kauda kansa da ga kallon ta garin irin kallon da take masa
” bance Hakan ba”
Ta sauke gauron numfashi tana saukowa daga gadon ta durƙusa a gaban sa
“dan girman Allah ka mai dani nasan mama tana can hankalin ta ya tashi in ya so daga baya duk yadda kake so sai inmaka”
Ta ƙarasa faɗa idanuwanta na ci kowa da hawaye
Numfashi ya sauke tare da ɗago kyakkyawar fuskarta
“habibty ki kwantar da hankalin ki,ki kalli can”
Yayi mata nuni da madubin sa,mama ta gani dasu anty ummi,tsakiyar su kuma wata Rauda ce tunda dai ita gata anan
Mamaki sosai ya bayyana a fuskar ta,ta mai kallon rashin fahimta tare da cewa
“waccan kuma wacece?
” wata rauhaniya ce nasa tayi shigar ki, zata ci gaba da zama tare dasu mama a madadin ki har zuwa wani lokaci dan gaskiya bazan yadda in kuma rasa ki ba”
Kallon sa kawai ta cigaba da tayi, ya sauko shima ƙasan yana janyo ta jikin sa
“habibty nayi rashi da kewar ki sosai, dan Allah ki rayu dani ni kaɗai”
Janye jikin ta tayi tana ɗaga mai hannu
“ina buƙatar natsuwa kabarni da Allah”
Ajiyar zuciya ya sauke tare da miƙewa ya fice daga ɗakin
Ita ko jingina tayi da gadon wasu siraran hawaye na biyo kuncin ta
Be kuma dawowa ɗakin ba falo ya koma ya kwanta kan kujera
Iyaka dai ya tura mata tire shaƙe da abinci,bata kula abincin ba sai bayan wasu awanni da taji cikin ta na neman agaji sannan ta tsakuri kaɗan
Sai dare ya dawo ɗakin, Rauda na tsaye jikin window ta zuba ma dogayen bishiyoyin dake dokar dajin ido
A bayan ta ya tsaya,bata wai ga ta kallesa ba,hannu yasa ya fara zage zip ɗin rigar ta ta baya
Tayi saurin waigowa a ɗan tsorace,murmushin nan nasa ƙasaitacce yayi yasa hannu ya saƙalo ta taba ya tare da manna ta da jikin sa
“miye ne na wannan tsoron, bafa wani abu zan miki ba wanka ne”
Ta riƙe zip ɗin tana girgiza mai kai
“ka bari zanyi da kaina”
Ya matso da fuskar ta gab da tata dan karan hancin su ma yana gogan juna
“da raina da lafiya ta inbar matata tayi wanka da kanta?ki sani a yanzu zan nuna miki tsantsar soyayyar da tafi tada ta yadda zaki yadda cewa zan iya yin abunda ze ninka wanda ɗan adam ze miki”
Zata kuma magana ya ɗaura yatsun sa biyu kan ƙaramin bakin ta
“shhhhhh kar ki ce komai”
Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tana kallon idanuwansa wanda kalar ƙwayar ciki take caccanzawa
Ya ci gaba da zage zip ɗin har ya kai ƙarshe sannan ya zame rigar
Runtse idanuwanta tayi da sauri, yayin da ya cigaba da kallon ta yana tambayar kansa
STORY CONTINUES BELOW
“ta yaya ze yadda ya rasa Rauda, ina!!!!
Bata ankara ba taji ya ɗauke ta cak,sai da ya tsundu mata a ruwa sannan ta buɗe idanun ta
Ruwane me ɗumi wanda saman sa yike mamaye da pink ɗin fulawowi
“kabarni nace zan yi da kaina”
Bece mata komai ba yaci gaba da abunda yike yi, da kansa yayi mata wankan ya naɗo ta da tawul sannan ya zaunar da ita a gaban madubi
Yana sunkuyo da kansa dai-dai wuyan ta
Ta cikin madubin suke kallon juna,gaba ɗaya idanuwansa sun narke da tsananin ƙaunar ta
“Rauda wallahi ina sonki”
Ya faɗa cikin wata murya me cike da shauƙin ta
Wani mai ya ɗauko ya shafe ta da shi sannan ya shafa gefen gadon sai ga wata rigar bacci me kyau ta bayyana sai da ya zura mata rigar sannan ya zame tawul ɗin
Ya kama hannun ta ya miƙar da ita tare da rungume ta sosai a jikin sa
Tabbas yayi kewar farin cikin rayuwar sa
Itako gabaɗaya jikin ta ya mutu,lumshe idanuwanta tayi kawai
Sai da suka kwashi minti biyar a haka sannan ya ɗago ta,ya na sunyo da fuskar sa zuwa bakin ta
Ta gane abunda yike shirin yi a kasalance tace
“hakan ba daidai bane kasan……….
Yayi saurin haɗa bakin su guri ɗaya dan baya so ta ƙarasa abunda zata faɗa
Minti uku baya ta janye jikin ta da ƙyar tana sa mai kuka
Bakin gadon ya zauna yana zuba mata ido cike da yanayi na galabai ta
Be lallasheta ba sai da tayi kukan ta me isar ta sannan ya kamo hannun ta ya zaunar da ita kusa dashi yana fuskantar ta
“habibty tunda bakya so bazan yi miki komai ba, ki dena kuka kinji?
Ya ƙarasa faɗa yana share mata hawayen fuskarta
” kwanta kiyi barci bazan yi miki abunda ranki ba ya so ba”
Kwantawar ko tayi,tana ɗan rawar sanyi wani lallausan bargo me taushi yasa ya lulluɓe ta
*~ƴarfillo~*.
*🌹JINNUL*
*AASHIQUE🌹*
🧞♂🧞♂
🧞♂
NA
HARIRA ALIYU _(ƴarfillo)_🧕🏻
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer’s of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
*Addu’a Idan Mutum Ya yi fushi.*
أَعُوذُ بِاللهِ مِنَ الشَّيْطَانِ الرَّجِيمِ.
*A’oothu billahi minash-shaytanir-rajeem.*
*Ina neman tsarin Allah daga shaidan tsinanne.*
Dedicated to _little hajjo_ and my elder sister _hafsat aliyu_
STORY CONTINUES BELOW
🅿AGE📕 4⃣1⃣
*_wannan Page ɗin nakine JAMILA ALIYU dake sa group ɗin ku masu ƙaunar jinnul aashique ina yin ku irin sosai ɗinnan_*
_7:45_🕒 AM
Wed, Nov 13
_Bissmillahir rahmanin rahim_✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
Bayan sati ɗaya
Umar ya jigata ƙwarai tun bayan tafiyar ta yike jin kamar ya rasa wani sashi na jikin sa ya rasa meke faruwa da ake ɓoye masa
Dan yanzu ma anty kaltum ta tilasta masa komawa gidan ta wai har sai ya ƙarasa samun lafiya
Ya rasa gane abunda ke faruwa kuma wanda ya tambaya baya samun gamsasshiyar amsa
Yana zaune cikin mota gaban wani shagon turaruka yana jiran mutanen da suka cika shagon su ɗan ragu sannan ya shiga
Gabaɗaya ya shiga cikin rikitaccen tunani dan ranar da ta shiga ɗakin sa idanuwansa biyu ba barci yike yi ba
“zantafi ne ba dan inaso ba jaana,zan barka a zahiri amma kasani zuciya ta na gare ka gangar jikina ce kaɗai zata yi nisa da kai..
Ya rasa gane abunda take nufi a cikin maganar ta,ya dafa kansa da yike jin yana ɗan sa rawa kaɗan
Da ƙyar ya iya fitowa ya shiga shagon yana tsaye yana duba turaren da yike son siya yaji ance
“Doctor umar dama talaka na ganin ku?
Umar ya juya inda yaji maganar yana kallon mutumin,tsayin sakwan uku yana so ya tuna a inda ya san mutumin
Be kai ga gama tunani ba mutumin ya ƙara so yana miƙamai hannu
Bayan sunyi musabaha mutumin yace
“doctor mutanen Allah,ya gida ya iyali? Ko ince amarya kayi haƙuri sanda aka yi auren ka bana ƙasar kuma naso na kira ka nayi maka Allah ya sanya alkhairi ashe numban ka na cikin Layina da ya ɓata”
Umar yayi sororo ya na kallon sa dan Sam be fahimci abunda mutumin ke faɗa ba
“nasan yanzu ƙila amarya ta haihu ko? Samin numban ka dan Allah zanzo har gida na ga amarya”
Mutumin ya ƙarasa faɗa yana miƙa mai faskekiyar wayar sa
Sa mai numban kawai yayi batare da ya ƙarasa sa numban ba ya fice daga shagon motar sa ya faɗa ya kifa kan sa akan sitiyari
“to yaushe yayi aure be sani ba? Kuma wacece wacce ya aura?
Yayi ma kansa tambayoyin a jere,
“zantafi ne ba dan inaso ba jaana,zan barka a zahiri amma kasani zuciya ta na gare ka gangar jikina ce kaɗai zata yi nisa da kai..
Maganar ta ta kuma yi masa yawo a kunne,tabbas idan ya kasance yayi aure to itace matar sa
Ya girgiza kai cikin dagulewar tunani, dole ne ya san abunda ake ɓoye sa
Tada motar yayi ya nufi gidan sa kai tsaye
A tsakar gida yayi parking ya zaro makullin gidan ya buɗe falon
Ya daɗe tsaye yana kallon cikin falon kamar yau ne karo na farko da ya fara ganin sa
Daga bisani ya shiga ya zauna akan kujera
Nan ma ya daɗe ƙwaƙwalwarsa naso ta tuno masa wani abu amma sai yaji kan sa ya cushe
Bedroom ɗin sa ya shiga ya zauna gefen gado idanuwansa suka sauka kan laptop ɗin sa
Jikin sa ba ƙwari ya miƙe ya ɗauko laptop ɗin dan ya san baze rasa wani abu da ze taimaka masa wajen gano abun da yike so ya gano ba
A can Kaduna kuwa gidan su mama mamaki da ban al’ajabi ne yike ta kama su
STORY CONTINUES BELOW
Dan tun bayan zuwan Rauda ta bogi suke shiga jimami, dan da farko kishiyoyin mama habaici da gori suka fara yima mama da faɗan maganganu masu ciwo
Farha wacce itace Aasim ya turo a madadin Rauda rauhaniya ce Mara haƙuri hakan yasa duk ranar da wani yayi ma mama habaici ko ita ɗin kanta to idan dare fa yayi mutum ya dinga tsala ihu kenan
Dan abubuwan tsoro take tura masa,tun basu Fahim ta ba har suka fara fahimta
Hakan yasa suka shiga ɗari-ɗari da ita,ga aiki dan idan ta soma aiki Sam bata gajiya
Abun yayi ta bawa mamaki sanin Rauda da tayi sam bata son aiki, aiki kaɗan zata yi tace ta gaji amma yanzu har so take ma ace ga aiki
Mama tasha jinin jikin ta sosai dan taga canje-canje da yawa wanda yasa ta fara zargin anya ba canza mata ƴar ta aka yi ba?
Amma dai tayi shuru tana cigaba da zubawa sarautar Allah ido
Ɓangaren Rauda kuwa a yanzu duk wani tsoro ya fita daga ranta dan zuciyar ta ta ƙeƙeshe wuni take da kwana tunanin umar
Wani zubin idan Aasim ya fita ta kan je wurin madubin sa ta ambaci sunan umar tayi ta kallon sa
Yana yin data ga yana shiga na damuwa da kuma tunani shine abun da ya ƙara sanya ta cikin damuwa
Ta rasa inda zata sa kanta,kamar kullum tana tsaye jikin bishiyar gidan tana kallon da jin
Taga Aasim ya bayyana a gaban ta dan tun safe ya fita
Kallon sa tayi yana yi mata murmushi
“habibty”
Duƙar da kanta tayi ƙasa batare da ta amsa ba
Ya matso gab da ita yace
“baza kimin sannu da zuwa ba ko?
Nan ma bata amsa ba
Ya sauke ajiyar zuciya yana fito da kayayyakin da ya siyo mata
Manyan sarƙoƙin lu’u-lu’u ne da awarwaron su
Dan a yanzu duk abunda ze sa ta farin ciki ƙoƙari yike yi yayi mata
” kinga habibty nasan zasu yi miki kyau shine na siyo miki duba kigani”
Kallo ɗaya tayi musu ta ɗauke kanta, gaba ɗaya sai yaji yadda tayi masa babu daɗi
Zama yayi a ƙasan bishiyar yana jin wani iri
Sun jima a haka daga bisani ya juyo yana kallon ta
Zaunar da ita yayi tare da kama hannayen ta cikin damuwa yace
“na rasa yadda zan yi miki Rauda,dan Allah ki faɗamin me kike so sam bana son ganin ki a irin wannan yanayin”
Hawayen da suka maƙale a idanuwanta suka gangaro a hankali
“ya Salaam,kinsani na tsani Naga kukan ki ko?
Cikin muryar ta da tayi san yi tace
“to ya kake so inyi Aasim?duk wani roƙo da ya dace in maka nayi amma ka kasa tausaya min,babu yadda zanyi zan cigaba da rayuwa da kai kamar yadda kake so amma kasani bazan taɓa ci gaba da farin ciki ba”
Ya lumshe idanuwansa da suka canza launi
Ya daɗe a haka yana tunani sannan ya buɗe su ya ɗaura su a kanta
Har lokacin kuka take yi mara sauti
“kin kasance komai na rayuwa ta,na kuma baki dukkanin amanar kaina ban taɓa tunanin zaki juya min baya ba Rauda sai gashi ni kike gudu ni kike kuka dan ina tare da ke”
STORY CONTINUES BELOW
Ya ɗan dakata yana jin wani dunƙulen baƙin ciki na taso masa
“tunda kin zaɓi rayuwa da umar a kaina zan barki ki cigaba da rayuwa da shi amma da sharaɗi guda ɗaya”
Tayi saurin kallon sa yayin da ya cigaba da cewa
“kamar yadda na sadaukar da rayuwa ta dan in rayu dake na tsalle ke tauran to shima ze tsallake”
Wani irin kallo ta ci gaba da yi masa dan tasan ba abu bane da ze taɓa yuwuwa ba,shi rauhani ma ya ya ƙare da ya tsallake bare mutum
“amma kasan dai hakan baze yuwu ba,taya ya yana ɗan adam ze tsallake tauran ya kuma rayu?
Aasim ya sauke numfashi yace
“bazan taɓa manta wahalar da na sha a lokacin dana tsallake ba,kuma na amince dan in rayu dake a yanzu kuma da kike son rabuwa dani to wannan shine abunda ze sa in haƙura da ke, nayi alƙawari idan har ya tsallake zan rabu dake har abada zan bar ku ku cigaba da rayuwar ku cikin kwanciyar hankali”
Zata yi magana ya dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu
“bana son na kuma jin komai daga wurin ki wannan shine alfarmar da zan iya yi miki,tun da kinzaɓi rabuwa dani”
Umar yana zaune ya tsura ma hoton da ke cikin laptop ɗin ido hoton sa ne da ita sun saƙale juna suna murmushi
A hankali ƙwaƙwalwar sa ta fara tariyo masa komai
Ya dafa kansa da sauri jin yayi wani mugun sarawa kamar an buga mai guduma
Jikin sa ne ya fara rawa ya runtse idanuwansa cikin tashin hankali
“kina ina Rauda?me yasa zaki yi nisa dani?
Karaf abunda ya faɗa a kunnen Aasim, mamaki ne ya kama Aasim ganin yadda cikin ƙanƙanin lokaci umar ya dawo cikin tunanin sa
Cikin hanzari ya ɓace daga wurin da yike ya bayyana a ɗakin da umar yike
Kallon tsana suka ma juna lokaci ɗaya yayin da umar ya miƙe cikin dakewar zuciya yace
“ina mata ta?ina ka kai min ita?
Aasim yayi murmushin takaici yace
“matar ka ko matata?kayi nasarar dawowa cikin tunanin ka amma kasani ba zaka taɓa nasara a kaina ba”
“ban damu akan yin nasara ko rashin ta akan ka ba,damuwa ta akan matata ne ka gaya min tana ina dan nasan tana tare da kai”
Aasim ya kuma yin murmushi yace
“haka ne matata tana tare dani sai dai kash zuciyar ta na tare da kai,kasani ban taɓa tsanar wani ɗan adam kamar yadda na tsanake ba Kaine wanda ka ruguza min farin cikina,idan naso zan kuma mantar da kai ko kai waye zan iya zautar da ƙwaƙwalwar ka amma bazan yi hakan ba kasan me yasa?
Ya ɗan dakata yana furzar da wata iska me zafi,sannan ya cigaba
“saboda bana son na cigaba da ganin damuwa a fuskar farin cikina,nazo ne na baka zaɓi idan har kana son Rauda ka na kuma son ka ci gaba da rayuwa da ita to zaka tsallake tauran ni kuma nayi alƙawari idan har ka tsallake to zan bar maka ita har abada”
Umar ya rausayar da kai yace
“idan har tsallake tauran ɗin ze sa kabar min matata ka kuma nisan ce ta na amince zan tsallake”
Aasim yayi wani mugun murmushi yana jinjina kai
“tsallake tauran ba abu bane me sauƙi, na baka kwana biyu kaje kayi tunani a kai”
Kafin umar ya kuma yin magana tuni ya ɓace
JINNUL*
*AASHIQUE🌹*
🧞♂🧞♂
🧞♂ +
STORY CONTINUES BELOW
NA
HARIRA ALIYU _(ƴarfillo)_🧕🏻
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer’s of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
Addu’ar Kin shu’umci
اَللَّهُمَّ لاَ طَيْرَ إِلاَّ طَيْرُكَ، وَلاَ خَيْرَ إِلاَّ خَيْرُكَ، وَلاَ إِلَهَ غَيْرُكَ.
Allahumma la tayra illa tayruk, wala khayra illa khayruk, wala ilaha ghayruk.
Ya Allah! Babu shu’umci sai abin da Ka halitta, kuma babu alheri sai alherinka, kuma babu abin bautawa da gaskiya ba Kai ba.
Dedicated to _little hajjo_ and my elder sister _hafsat aliyu_
🅿AGE📕 4⃣2⃣
_Wannan page nakune masoya na masu haƙuri dani Allah ya bar ƙauna😄_
_gaisuwa ga *Fatima batula* ina taya ki murnan kammala littafin ki wanda ya faɗakar damu sosai Allah ya baki lada ya ƙara basira da fasaha_
_8:26_🕒 PM
Thu, Nov 28
_Bissmillahir rahmanin rahim_✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
Bayan kwana biyu umar yana tsaye jikin window ya ji motsi a bayan sa
Ya waigo a hankali Aasim ya gani
“kwanaki biyun da na baka sun cika shin ka gama shawarar?
Aasim ya tambaya yana zuba masa razana nun idanun sa
Umar ya jinjina kai yace
“shawara tun a lokacin na yanke ta na amince”
Aasim yayi murmushi yana jinjina kai
“da kyau amma Naga baka nemi shawarar iyayen ka ba,kuma dole akan idon su zaka tsallake tauran”
Umar yayi murmushi da ya tsaya masa iya laɓe kawai
“wannan ba damuwar ka bace zan tsallake ko da amince warsu ko bada amince warsu ba tunda Naga kaima lokacin daka tsallake bada amincewar naka iyayen ba dan da kabi shawarar su da hakan duk be kasance ba”
Aasim ya kaɗa kai cikin yanayi na ɓacin rai
“shikenan kafaɗa ma shaƙiƙan ka nan da kwana uku zaka tsallake tauran
Ka kuma yi sallama da duk wanda ya kamata dan walau ka rayu walau a kasin haka na barka lafiya”
Umar ya zauna shuru bayan ɓacewar Aasim gabaɗaya tunanin sa ya tsaya sai dai baya jin ze fasa abunda yayi niyya dan ko da ya rasa ransa yasan Rauda zata gane cewa yana yi mata so na haƙiƙa
Miƙewa yayi ya nufi gidan anty kaltum
A falo ya tadda ta ita da hajiya
Bayan ya gaishe su ya zauna shuru
Anty kaltum ta dawo kujerar da yike ta zauna tana tambayar sa
“ya dai umar na ganka wani iri ko jikin ne?
Ya girgiza mata kai a hankali
” to menene? Banason ina ganin ka a haka kasan bana son ganin ka cikin damuwa ko?
STORY CONTINUES BELOW
Ya kalle ta da idanuwansa da suka canza launi yace
“anty jarabawar da Allah ya ɗauro min kenan dole kiganni a haka, anty na dawo cikin tunani na meyasa kika ba Rauda goyon baya ta aikata min haka Meyasa?
Kefa ƴar uwata ce kuma auran ta da rayuwa da ita shine farin cikina shin bakya son farin cikin ɗan uwan ki ne?
Jikin anty kaltum yayi sanyi hajiya ko zuba mai ido tayi kawai cike da al’ajabi
“Sam ba haka bane umar…….
Ya dakatar da ita ta hanyar cewa
“na fahimci komai ba sai kinyi min bayani ba, yanzu abu ɗaya nike so a gare ku ina so ku bani goyon baya koda kuwa zan rasa raina ne”
Kallon sa kawai suka cigaba da yi yayin da ya zayyane musu abunda Aasim yace game da tsallake tauran
Shuru suka yi dan sun rasa abun da zasu ce
Durƙusawa yayi gaban hajiya idanuwansa na zubar da hawaye
“hajiya dan Allah ki bani goyon baya Rauda ita ce farin cikina dan Allah hajiya”
Hajiya itama hawayen ta fara yi
“tabbas soyayyar ka a gareta daga Allah ce,akwai wata hikima da ubangiji ya ɓoye a tsakanin ku na baka goyon baya umar ubangiji Allah ya baka sa’a Insha Allah zaka tsallake lafiya kaci gaba da rayuwa da matar ka”
Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke yana hamdala a zuciyar sa dan beyi tunanin zasu amince mai ta sauƙi ba
Hannun ta ya kama yana ɗan murmushi
“nagode hajiya”
Rauda kuwa tana zaune ta Lula cikin tunani bata ma san Aasim ya dawo ɗakin ba sai da taji gyaran murya
A hankali ta zare tagumin da tayi tana kallon sa da lunshasshun idanun ta wanda suka yi luhu-luhu saboda kukan da taci
Kallon juna suka yi na ƴan sakwanni daga bisani ta ɗauke idanuwan ta a kansa ta maida su ƙasa
Shi ko kallon ta yaci gaba da yi yana jin wani irin yana yi na daban
Ya sauke numfashi me nawi yana matso wa kusa da ita a hankali
_”Rauda”_
Ya kira sunan cikin yana yi na damuwa
Ta ɗago ta kuma kallon sa, gabaɗaya ya koma yana yin tausayi ya canza kamar ba shi ba
Kuma sauke idanun ta tayi dan ba zata iya jurar ci gaba da kallon sa ba
“shin ko da sau ɗaya ne ni ba zaki tausaya min ba?
Ya faɗa yana ruƙo hannun ta sannan ya cigaba da cewa
“Sam ni bakya tunanin halin da zan shiga a yayin da zan rabu dake?me yasa ki ka kasa yimin adalci ne?
Ki tuna abubuwan da na rasa a sanadin ki
A da bana komai sai abunda bayi da fadawa suka min,Sam bansan wani abu wahala ba a rayuwa babu gatan da bana samu
Amma a sanadin ki,ki duba wahalar da nasha Rauda na rasa muƙami na na yarima narasa soyayyar iyaye na duk dai akanki
Amma ke…….
Be ƙarasa ba ta faɗa jikin sa tana fashewa da wani kuka me tsuma zuciya
Dan gabaɗaya tausayin sa ya cika mata zuciya
Ya runtse idanuwansa dan yana jin kukan ta har cikin ƙoƙon ransa
Sun kwashi minti biyar a haka ya kasa lallashin ta dan jikin sa yayi sanyi ƙalau
STORY CONTINUES BELOW
Ɗago kanta tayi tana kallon sa cikin kuka take faɗin
“na sani banma adalci ba Aasim tabbas na cika me son zuciya amma yadda rayuwar mu tazo dole mu amshe ta a haka
Baze yuwu mu cigaba da rayuwa…….
Dakatar da ita yayi ta hanyar ɗaga mata hannu
Yana murmushin takaici
“ya isa haka Rauda,nasan dama bani da kalaman da zan sa ki fahimta babu damuwa har a bada ni me ƙaunar ki ne zan rabu dake a jibi idan har umar ya tsallake tauran kar ki damu”
Ya faɗa cike da takaici
Zata kuma magana ya miƙe ya bar mata ɗakin
Kifa kanta tayi kan gwiwar ta wani sabon kuka na ƙwace mata
Shin ya za tayi da ranta ne,anya idan ta rabu da Aasim tayi ma kanta adalci kuwa?
Rayuwar da suka yi da shi ce tayi ta dawo mata da irin yadda ya nuna mata tsantsar ƙauna
_”habibty nace ba ina sonki”_
Kalaman da yike faɗa kullum idan zasu yi sallama a makaranta
_”Rauda ina sonki zan iya haƙura da komai nawa in har zan rayu dake”_
Zuciyar ta ta cigaba da hasko mata fuskar sa yana murmushi cike da nishaɗi
“tabbas ban maka adalci ba ka cancanci na rayu da kai har a bada amma umar fa?
Ta tambaya a fili tana juya idanun ta cikin yanayi na fara fitar gayyaci
Duk wahalar ya sha ta gubar nan besa yaji ƙaunar ta ta ragu a ransa ba ta san inda wani ne da idan ana saki ɗari yayi mata dan ya samu lafiya
Amma shi ko kaɗan be nuna gajiyawar sa ba illa ma ƙarfafa mata gwiwa da kwantar mata da hankali
_”chuchu ina tsananin ƙaunar ki ba zan taɓa iya rabuwa dake ba,na amince na cigaba da rayuwa a haka in har zan ci gaba da kasancewa tare dake”_
“ya Allah”
Ta faɗa cikin tsananin tashin hankali dan jin kanta take yi kamar zeyi bindiga
Daren ranar bata yi barci ba kamar yadda Aasim da umar ma ko kaɗan basu runtsa ba
Washegari tana zaune bayan ta idar da sallah taga tiren abinci ya shigo shaƙe da kayan kari
Shafa cikin ta tayi da ya laƙume dan rabon da taci abinci har ta manta
Bata bi ta kan abincin ba ta miƙe ta fito
A tsaye tagan sa yana shirin fita
Tayi sauran tarar sa tana faɗin
“ina son Magana da kai”
Be kalle ta ba ya ci gaba da abunda yike yi
“faɗi inaji”
Ya faɗa a taƙaice
Tayi shuru tana tunanin yadda zata mai maganar
Ɗagowa yayi ya kalle ta
“ke nike saurare”
Sai da ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce
“dan Allah kabani dama ina so inyi magana da umar”
Ya ɗan yi shuru yana cigaba da kallon ta kamar ba ze sake yin magana ba sai kuma yace
“shikenan na baki minti goma”
Yana gama faɗar haka ya ɓace
Zura ma wurin da ya ɓace ido tayi tana tunanin to ina zata fita daga dajin
STORY CONTINUES BELOW
Bata kai ga gama tunanin ba ta ganta a bedroom ɗin umar
Babu kowa a ciki sai iskar fanka dake ta kaɗawa
Numfashi ta sauke tana faɗin
Ƙiri-ƙiri a maida mutum aljanin ƙarfi da yaji
Umar ya turo ƙofar dan dawowar sa daga masallaci kenan
Da kyakkyawar fuskar ta yayi karo
Ƙarasa shiga ɗakin yayi da sauri
Ya nufe ta da nufin rungume ta sai kuma ya fasa dan be san wani abun Aasim yace ta kuma yi ba
Ɗan murmushi tayi dan ta fahimce sa
“Jaana guduna kake yi ne?
Ajiyar zuciya ya sauke tare da ƙarasa wa gaban ta
Ya kasa magana illa tsura mata ido da yayi
Gabaɗaya gani yayi ta rame masa
Wani irin tausayi da son ta ne ya kuma dabaibaye sa
Besan sanda ya rungume ta sosai a ƙirjin sa ba
Wasu siraran hawaye ne suka biyo kuncin ta wanda bata san na menene ba
Na kewarsa ne ko kuma na ƙaunar sa
Sun kwashi minti uku a haka tunawa da minti goma Aasim ya bata yasa tayi saurin janye jikin ta
Tana faɗin
“minti goma kaɗai ya bani zauna muyi magana”
Ta ƙarasa faɗa tana jan hannun sa zuwa gefen gadon
Bayan sun zauna tace
“Jaana dan Allah ka janye maganar tsallake tauran da ba abune da zaka iya ba, mu ci gaba da addu’a kawai…….
Girgiza kai yayi yace
“Rauda kisa aranki kamar na tsallake ne dan bazan fasa ba”
Cikin damuwa take kallon sa
“shi kanshi rauhani fa jikin sa huhhujewa yayi ina ga kai mutum? Idan har ba so kakeyi in rasa ka ba dan Allah ka fasa”
Ta ƙarasa faɗa idanuwan ta na ci kowa
Yayi ɗan murmushi ya na dafa kafaɗun ta
“yace idan har na tsallake ze rabu dake ze barki kiyi rayuwa cikin kwanciyar hankali dan haka koda na mutu bani da faɗuwa tunda zaki cigaba da rayuwa babu takurawar sa”
Ta kasa ƙara magana
Umar ya cigaba da cewa
“ki kwantar da hankalin ki chuchu abu ɗaya nike so dake idan Allah ya sa na rasa rayuwa ta kada kisa ranki a ƙunci kiyi rayuwa cikin farin ciki….
Toshe mai baki tayi da sauri tare da faɗawa jikin sa
” umar dan Allah ka janye na tabbata idan babu kai nima bazan iya ci gaba da rayuwa ba”
Ya kuma yin murmushi wanda yike tattare da ɗumbin damuwa
“chuchu a baya kin taɓa kuka a sanadina kin faɗi cewa ke kaɗai ke sona ni bana sonki
Nasan idan har na tsallake zaki yarda da cewa son da nike miki ya ninka wanda kike min”
Tayi saurin girgiza kai
“nasan kana sona umar dan Allah……….
Bata ƙarasa ba tagan ta akan kujerar falon Aasim
Kuka ta cigaba da yi dan tabbatar da baze shiga tauran ya fito da ran sa ba
STORY CONTINUES BELOW
Shiko umar zuba tagumi yayi,bayan ɓacewar ta
Ɓangaren Aasim kuwa can wurin tauran ya je
Mus’ab ya tarar a wurin hannun sa riƙe da wani haske me tartsatsi yana ta nuni ga tauran
Ya yin idan tartsatsin ya dake cikin ta take ƙara fitar da wani hayaƙi me zafin gaske
Aasim yayi saurin dakatar dashi
“Mus’ab me kake yi haka? Ƙarama tauran zafi fa kake yi”
Mus’ab ya jinjina kai
“eh mana yarima saboda ina so wannan bil’adaman ya gane yayi babban kuskure
Aasim ya girgiza kai yace
“shifa mutum ne taya kake tunani idan ya shiga ze kasance?
Mus’ab yayi ma Aasim wani irin kallo
” wai kai har ma tausayin sa kake ji?
Aasim yayi ɗan murmushi tare da zaunawa a kan kujera yana kallon yadda hucin tauran ke fita
Mus’ab ya kuma faɗin
“tambayar ka nike yi Aasim, mutumin da ya jagula ma rayuwar ka shine kake tausayi?
Aini wallahi so nike ko ɓurɓushin naman sa kar a gani”
Aasim ya kuma yin murmushi a karo na biyu sannan ya maida kallon sa ga babban abokin nasa
“Mus’ab ka sanyaya ranka kaji? Nasan kafini jin zafi amma inaso ka dawo da natsuwar ka mubi komai a hankali”
Mus’ab ya furzar da wata iska me zafi yace
“ni banga abun bi a hankali ba anan”
Wani irin ƙamshi me daɗi ne ya zagaye wurin
Aasim ya ɗago kansa da sauri dan yasan mahaifin sa ne kaɗai ke amfani da kalar turaren
Ga mamakin sa kuwa sarki ramzad ya gani cikin shigar sa ta ƙasaita
Mus’ab yayi saurin rusunawa cikin girmamawa yayin da Aasim ya cigaba da kallon mahaifin sa cike da tsananin kewar sa dan ya manta rabon da yayi tozali da shi
Sarki ramzad ya ƙara so wurin fuskar sa ɗauke da guntun murmushi
Mus’ab yayi gaggawar barin wurin ya rage daga Aasim sai me martaba
“Kaga yadda halin bil’adama yike koh? Aasim naji daɗi ƙwarai da suka koya maka hankali
Na zo ne na kuma baka zaɓi idan gobe bil’adaman nan ya tsallake tauran to fa kasani ba ka isa ka karya alƙawarin da kayi na rabuwa da matar sa ba, dan haka ka ka kiyaye”
Yana kaiwa nan ya bar wurin
Aasim shuru yayi zuciyar sa na yi masa wani iri kallon tauran ya kuma yi sai kuma yaɗan yi murmushi dan yana da yaƙinin sai dai gawar umar ta fita badai da ransa ba
*~ƴarfillo~*c
*🌹JINNUL*
*AASHIQUE🌹*
🧞♂🧞♂
🧞♂
NA
HARIRA ALIYU _(ƴarfillo)_🧕🏻
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer’s of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
STORY CONTINUES BELOW
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
Dedicated to _little hajjo_ and my elder sister _hafsat aliyu_
🅿AGE📕 4⃣3⃣
Wannan page nakine nabiha kiyi yadda kike so dashi.
*Addu’ar Da Mutum Zai Fada Idan Wani Al’amari Ya zo Masa na Farin Ciki ko na Bakin Ciki*
الْحَمْدُ للهِ الَّذِي بِنِعْمَتِهِ تَتِمُّ الصَّالِحَاتِ .
Alhamdu lillahil-lazee bini’imatihi tatimmus-salihat.
Godiya ta tabbata ga Allah wanda saboda ni’imarsa ce kyawawan ayyuka suke cika.
اَلْحَمْدُ ِللهِ عَلَى كُلِّ حَالٍ.
Alhamdu lillahi ala kulli halin
Godiya ta tabbata ga Allah a cikin kowane hali.
_2:02_🕒 PM
Mon,Dec 16
_Bissmillahir rahmanin rahim_✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
Kiran sallar assalatu yayi dai-dai da bugawar ƙirjin ta.
Tashi tayi da sauri ƙirjin ta na ci gaba da bugawa.
“yau ne, umar bazai iya ba”.
Abunda zuciyar ta ta tunatar da ita kenan.
Tashi tayi ta fito falo bata ga Aasim ba. ta duba ɗakin sa nan ma baya nan.
Zamewa tayi ta zauna a ƙasa tana dafa kanta cikin tsantsar damuwa.
Ta lumshe idanuwan ta, zuciyar ta na hasko mata tauran.
Tabbas ta san yau zata rasa Umar, rashi na har abada.
Wasu siraran hawaye masu zafi suka biyo kwarmin idanun ta.
“kin manta da cewa Allah ya na nan kuma shi ke maganin komai? Addu’a tafi ƙarfin komai”.
Wani sashe na zuciyar ta ya tunatar da ita.
Miƙewa tayi da sauri ta ɗauro alwala, bayan ta idar da sallah ta ɗaga hannayen ta sama.
Cikin kuka take faɗin;
“Ya Allah, Kaine sarkin da ka halicci sarakuna, kai ke da iko a kan dukkan halittun ka, ya ubangiji ka duba lamarinmu ka taimaki Umar ka kare sa daga sharrin tauran da sharrin duk wani halitta, ka taimake sa ya ubangiji”
Ta ƙarasa faɗa, zuciyar ta na ƙara raunane wa.
Aasim yana tsaye yana kallon ta, jin jikin sa yike yi wani iri.
Ƙarfe sha ɗaya dai-dai manyan rauhanai abokanan Aasim suka hallara a wajen tauran.
Anty kaltum, hajiya, da kuma zayyad, suma suna zaune a falo suka ga wata iska ta zagaye su kan kace kwabo suka gansu a wata kalar duniya.
Sun tsorata sosai ganin yadda tauran ke fitar da wani tartsatsi.
Addu’a kawai suke karantawa dan sun rikice.
Can kaduna ma, mama ce zaune da anty Ummi suna tattauna wa ƙasa-ƙasa akan Rauda ta bogi, dan gaba ɗaya basu yarda da ita ba.
Suna cikin tattauna war Farha ta fito ta zauna tana kallon su.
Da ɗan murmushi a fuskar ta tace;
“kuna yin tantama a kaina koh?”.
Basu bata amsa ba illa kallon ta da suka ci gaba da yi.
Ta kuma yin murmushi tana ci gaba da cewa;
“To a yau tantamar ku zata ƙare insha’allah, kamar yadda kuke zargi hakane ni ba Rauda bace”.
STORY CONTINUES BELOW
Ta ƙarasa faɗa tana shafa fuskar ta sai ga fuskar Rauda ta ɓace, ainihin fuskar ta ta bayyana.
Anty damƙe hannun mama tayi cike da tsananin tsorata.
Mama ko bata yi mamaki ba dan dama tayi tunanin hakan.
“ina ƴata ina kuka kaimin ita?!”.
Mama ta tambaya, zuciyar ta a dake.
Farha tayi murmushi tace;
” ƴarki tana duniyar aljanu a yanzu haka, ana can ana shirye-shirye dan yau ne mijin ta yace zai tsallake tauran, dan haka kuma yanzu zan tafi daku dan dole ayi komai a kan idon ku”.
Basu kai ga yin magana ba suka gansu a wani kalan wuri.
Babu inda baya rawa a jikin anty ummi dan har fitsari sai da tayi.
Banda mama da zuciyar ta take a dake.
Kallon kallo suka wa juna da su anty Kaltum amma babu wanda ya iya ma wani magana a cikin su.
Umar da tun cikin dare yake kan darduma har lokacin yana kai.
Ya ɗaga hannaye sa yana ta kai kukan sa ga ubangiji.
Motsin Aasim da yaji a ɗakin yasa ya shafa addu’ar tare da waigowa a hankali.
Yana tsaye ya harɗa hannuwan sa a ƙirji.
Ɗan murmushi Umar ya sakar masa tare da cewa, cikin dakiyar zuciya;
“muna iya tafiya yanzu koh?”,
Aasim gyaɗa masa kai kawai yayi ba tare da yace komai ba.
Cikin sakwanni suka isa, tabbas hankalin Umar ya tashi da yaga yadda tauran take.
Amma tunawa da yayi Allah yana tare da shi yasa yaji tashin hankalin ya ɗan ragu.
Anty kaltum na ganin umar ta ƙara so gurin sa da sauri ta riƙe sa
Cikin tashin hankali da tsananin tsorata tace
“umar dan girman Allah ka haƙura da yarin yar nan kadu ba inda zaka shiga fa”
Umar ya sake kallon tauran sannan ya mai da kallon sa ga anty kaltum
Cikin ƙoƙarin kwantar mata da hankali yace
“Anty na riƙe Allah na kuma san insha’allah ze bani nasara ki ci gaba da yi min addu’a kinji?
Kuka kawai ta fashe zata kuma magana Rauda ta riga ta dan isowar ta wurin kenan
Ita ma a gigice take gabaɗaya ta daburce
“umar ka kalli inda kake son shiga fa? Na roƙe ka ka janye
Umar ya dafa kafaɗun ta yana yi mata guntun murmushi
“Rauda ba zan taɓa janye wa ba koda ko hakan ze yi sanadiyyar rasa raina ne, bare ma insha’allah zan tsallake lafiya ki kwantar da hankalin ki kinji?
Ganin bayi da niyyar fahimtar ta yasa ta juya gurin Aasim cikin tashin hankali take yi masa magiya
“Aasim ka ɗaukeni mu tafi can wata duniya inda ma baza a ƙara ganina ba na amince zan ci gaba da rayuwa da kai amma kar ka barsa ya shiga tauran dan Allah ka taimake ni idan na rasa sa bansan ya zanyi da rayuwa ta ba”
Aasim da fuskar sa ba annuri idanuwan nan nasa sunyi jawur ba wata alamar ƙwaya aciki dan dama duk sanda ransa ya ɓaci haka idanuwansa ke komawa
Zuba mata idanun yayi masu firgita duk wanda aka kalla dasu
“ni ba rai bane kenen da na tsallake a baya? Tsallakewa ya zama dole tunda ya gani da idonsa kuma be janye da kansa ba idan har ya shiga ya tsallake ya fito kuma da ransa to da ga yau na barki har a bada!!!
STORY CONTINUES BELOW
Ya ƙarasa faɗa cikin ƙaraji
Mus’ab dake tsaye yace yana duba umar
Yayin da tauran tayi wani baƙin hayaƙi a Samanta cikin ta kuma wasu siraran wuƙaƙe ne masu kafin gaske wanda iska take ta kaɗa su da ƙarfin gaske ta yadda duk wani abu da ya shiga ciki zasu yayyanke jikin sa
“tauran tana yi maka marhaba dan a yanzu ta shirya tsaf da tarbanka”
Mus’ab ya ƙara sa faɗa yana yi masa nuni da ita fuskar sa ɗauke da wani mugun murmushi
Umar jinjina kai yayi yana kuma kallon tauran a hankali ya juya ze fara tafiya
Rauda ta ƙanƙame sa tana kuka tana faɗin
“umar kar kaje dan Allah mutuwa zaka yi”
Aasim ne ya fizgo a fusace
Ya yin da umar ya ci gaba da tafiya
A gigice ta kuma rugowa sai kafin ta ƙarasa inda umar Aasim yayi nuni da hannun sa wani kalar abu me kama da glass ya zagaye wurin gabaɗaya
Jita yi taci karo da abu gashi taku befi biyu ba tsakanin ta da umar amma wannan abun da Aasim yasa yayi shamaki a tsakanin su
Cikin kuka take bubbugawa tana kiran umar
A hankali ya juyo yana kallon ta
Tsananin tausayin ta ya ƙara za gaye zuciyar sa ya ɗauki tsayin biyu yana kallon ta daga bisani ya juya ya ci gaba da tafiya
Sai da ya karanta adduo i sosai sannan ya fara taka mata kalar wani kalan huci me zafi yaji yana dososa
Addu’ar dake bakin sa ya cigaba da karantawa har ya isa ƙofar tauran
Gaban sa ne ya fara faɗuwa yayin da yaga yadda wa’annan wuƙoƙin suke kaɗawa da ƙarfi
Jiyayi kamar ana fizgar sa yayi ƙarfin halin zura ƙafar sa ciki
Sai dai me? Jiyayi wani raɗaɗi ya mamaye sa yayi saurin kallon inda ya taka
Wasu mugayen allurai ne a caccake gabaɗaya kuma haka ƙasan wurin yike
Yayi shahada ya ƙarasa shiga yana ci gaba da ambaton sunan Allah
Cikin sakwanni wuƙaƙennan suka yo kansa ya runtse idanuwansa da sauri dan baya so yaga sanda zasu iso jikin nasa
Sai dai a me makon yaji yanka sai yaji ƙarar wuƙaƙen
Yayi saurin buɗe idon sa abun mamaki duk wuƙar da zo jikin sa sai ta lauye
Take sai ga wuƙaƙe birjik sun zube a ƙasa
“Allahu Akbar!!”.
Ya faɗa, take wata izza me ƙarfi tazo masa ya ci gaba da tafiya duk da raɗaɗin da yake ji a ƙafafun sa.
Cikin mintuna biyu ya fara ganin duhu yayin da saman tauran ya ƙara baƙinƙirin.
Murmushi Aasim yayi dan yasan ƙarar farko da tauran zata yi zata halaka sa.
Daram!!
Wata kalar ƙara me razanar wa ta fita.
Sai da aka kwashi minti biyu sannan haske ya fara gauraye cikin tauran ɗin ta yadda suke iya hango cikin ta.
Umar suka hango kwance a ƙasa jini na malala a jikin sa.
Cikin farin ciki Mus’ab ya kalli Rauda yace;
“kingani ko, ƙara ɗaya ta tauran ji yadda ta mayar dashi, nasan a yanzu kuma sai dai wani Umar ɗin ba dai wannan ba”.
Ya ƙarasa faɗa yana fashewa da dariya.
STORY CONTINUES BELOW
Su anty Kaltum kuka suke yi kamar ransu zai fita, yayin da Rauda ta zama kamar wata butumbutumi dan ko motsin kirki ta kasa yi, hawaye ne kawai ke bin fuskar ta.
Cikin hukuncin Allah Umar ya farfaɗo daga gajeruwar Suman da yayi.
Da sunan Allah ya farfaɗo a bakin sa.
Ya yunƙura ya tashi cikin juriya ya cigaba da tafiya.
Mamaki ne ya kama rauhanan dake wurin, suka saki baki suna kallon sa.
Rauda da sai lokacin ta samu damar magana ta kalli Mus’ab tace;
“Miye naka na sakin baki kuma? kana mamaki da ikon Allah ne??”.
Mus’ab yayi ɗan murmushi tare da cewa;
“Me kike ma sauri? Duka-duka ƙarar tauran ɗaya ce fa amma ji yadda ta maida shi, ƙarar ta guda arba’in da takwas ta rage, ki ci gaba da zuba ido”.
Dai-dai lokacin duhu ya ƙara mamaye tauran alamar ƙara na biyu na zuwa.
Jikin Rauda ya ƙara yin sanyi, zamewa tayi a wurin idanuwanta na ci gaba da zubar da hawaye.
Bayan minti talatin wanda yayi dai-dai da ƙarar tauran sau ashirin.
Umar ne kwance a ƙasa ya galabaita iya galabaituwa, amma duk da haka da ragowar ƙarfin sa sakamakon ƙarfin addu’ar da yake yi, kuma har lokacin ko wuƙa ɗaya ta kasa yankar sa.
Aasim yana tsaye yana kallon Rauda da taci kuka har ta gode Allah.
Tauran zata kuma sakin wata ƙarar yayi nuni da hannu ya dakatar da ita.
Mus’ab ya kallesa cikin sauri yace;
“me kayi haka yarima? Dakatar da ita fa kayi?”.
Aasim ya jinjina kai kawai.
Mus’ab zai kuma magana ya dakatar dashi ta hanyar faɗin;
“sanin kanka ne ba wani mahaluki me rai da zai shiga cikin Tauran da wannan zafi da aka ƙara mata face ya mutu, ni kaina da nike jinsin rauhan sai da me martaba ya sanyaya ta sannan na iya tsallakewa, amma shi ka duba har yanzu ba alamar karaya a tare dashi, har yanzu babu wuƙar da tayi nasarar yankar sa bare ta illata sa, tabbas nayi kuskure da na manta cewa addu’a ma karin mumuni ce, idan har nace zan bar sa ya cigaba zanyi babban kuskure domin ko kamar na ja da hukuncin Allah ne”.
Rauda ta kallesa da sauri jin abunda yace.
Shima kallon nata yayi idanuwansa na cikowa da hawaye.
A hankali ya rusuna inda take yana kallon ta cikin ido.
“kamar yadda na miki alƙawari yau zan barki, bazan ƙara bibiyar rayuwar ku ke da mijin ki ba, domin duk wanda ya sadaukar da rayuwar sa akanka ba ƙaramar ƙauna yake maka ba, abu ɗaya nike so ki sani ki kuma sa a ranki, ina sonki, kuma zan ci gaba da son ki har zuwa ranar da zanyi numfashi na na ƙarshe….”,
Ya ƙara sa maganar cikin wani irin yanayi, tare da miƙewa ya juya da sauri.
Washegari Rauda ce zaune gaban gadon asibiti, Inda umar ke kwance, tana zaune kawai ta rasa meke mata daɗi.
A hankali Umar ya buɗe idanun sa.
Cikin rashin kuzari ta matso da kujerar da take zaune a kai gaban gadon, tare da ɗaura hannun ta saman nasa.
“ka farfaɗo?”.
Tambayar da ta mai kenan tana kallon kyakkyawar fuskar sa.
Guntun murmushi ya sakar mata.
“na farfaɗo chuchu, alhamdulillahi mu gode ma Allah”.
Siraran hawaye ne suka biyo kwarmin idanun ta.
STORY CONTINUES BELOW
Ta kwantar da kanta jikin gadon saitin fuskar sa ta yadda suke kallon juna ido cikin ido.
“yanzu kin yarda cewa ina miki so me tsanani chuchu?”.
Ɗaga mai kai tayi tare da fara magana cikin sanyin murya.
” na yarda Umar, bansan kuma da me zan saka maka irin ƙaunar da ka nuna min ba”.
Murmushi ya kuma yi tare da shafa gefen fuskar ta.
“Idan baki sani ba ni zan faɗa miki, yanzu tunda hankalin mu ya kwanta sai ki fara shirin biyana bashin da na daɗe ina binki”.
Cikin rashin fahimta tace;
“bashi fa?”.
Ya ɗaga kai.
“Eh ko baki san ina binki bashi ba?”.
Ta ɗaga kai alamar eh.
Ya ɗan yi shuru yana tsura ma kyakkyawar fuskar ta ido.
“faɗamin bashin miye?”.
“lallai ma yarinyar nan, wato da gaske baki sani ba, to bashin angoncewa na ko kin manta?”.
Murmushi tayi cikin jin kunya.
“kana gadon asibiti kake wani maganar angoncewa, ai kabari ka samu lafiya ko?”.
Shima murmushin yayi.
“Eh wai dama ina faɗa miki ne saboda ki shirya dan zaki gwaguru yarinya kamar ba gobe”.
Ƴar dariya tayi har fararen haƙoranta suka bayyana.
“zan gwaguru sai kace wata goruba?”.
“yaushe rabon da inga dariyar ki?har na manta?”.
Ya faɗa idanuwansa na kanta.
“kana son ka rinƙa ganin dariya ta ne?”.
Ya jinjina kai.
“sosai ma kuwa, dan idan kika yi tana ƙara miki kyau kuma tana sani farin ciki”.
Tayi murmushi tace;
“shikenan Jaana, bari in kira zayyad ya duba ka ko?”.
Ta ƙarasa faɗa tana miƙewa. Hannun ta ya janyo ta faɗo jikin sa.
Da sauri ta yunƙura zata tashi dan gudun kada ƙarin ruwan dake jikin sa ya goce, ya dakatar da ita ta hanyar faɗin;
“Please ki tsaya Ina son inji ɗuminki ne”.
Ta ɗan ƙwalalo ido tare da faɗin;
“A asibiti kake fa, kuma ka duba yana yin da kake ciki”.
“Dan a asibiti nike sai me? Ai ɗumin ki nace ko?”.
Ta ɗan girgiza kai, dai-dai lokacin da Zayyad ya turo ƙofa.
Tashi tayi da sauri tana matsawa.
Zayyad yayi murmushi.
“A lallai abokina sauki ya samu, ashe ka farfaɗo har ka fara soyewa! Allah ya taimake ka da yanzu kana lahira”.
dariya suka yi gaba ɗaya.
Bayan sati biyu
Umar ya samu sauƙi sosai dan har sun dawo gida
Tunda ga bakin get Rauda ta saki baki tana kallon gidan,dan a canza mai feti bata ƙara shiga mamaki ba saida suka shiga falon
An canza komai na gidan, ta maida kallon ta ga umar fuskar ta cike da mamaki
“Jaana Naga gidannan ya canza, Anya ba ɓatan hanya muka yi ba?
Yayi murmushi yana matso wa kusa da ita sosai, kyawawan idanuwan sa ya zuba Mata
Cikin murya me taushi yace
STORY CONTINUES BELOW
“gidan ki ne chuchu Bawani ɓatan hanya,nine nasa aka canza komai”
Ta sauke ajiyar zuciya tace
“amma gani nayi kayan gidan nan sababbi ne ba abunda suka yi”
Umar ya ɗaga kai yace
“nasani chuchu, rayuwar da mukayi a gidannan rayuwa ce me cike d firgici da tashin hankali, shiyasa na sa aka canza komai saboda banason muna ganin duk abunda ze rinƙa tuna mana da waccan rayuwar, na kuma sa anyi saukar alqur’ani me girma saboda kariya”
Murmushin jindaɗi tayi,tana kallon fuskar sa
“nayi farin ciki sosai,nagode”
Ya girgiza kai
“A’a fa ba anan ya kamata ki nuna farin cikin ki ba?
Har lokacin da ragowar murmushi a fuskar ta
” to a ina ya kamata in nuna ranka shidaɗe?
Surar ta yayi, yayi mata ɗaukar jarirai
“bari in kai ki, kigani”
Sama ya fara hawa ya nufi bedroom
Dariya ta fara yi tana zullo da ƙafafun ta
“nagane wayo kake so kamin, to banyar da ba ka sauke ni”
Shima dariyar yike yi cike da nishaɗi, ya tura ƙofar bedroom ɗin tare da kwantar da ita a kan gadon
Tayi saurin yunƙurawa zata tashi,ya hana ta hanyar yi mata rufa d faffaɗan ƙirjin sa
Kallon cikin ido suka fara yi ma juna,saboda shauƙin soyayya har basa ƙyaftawa
Sunyi minti uku a haka daga bisani ta mirgina,ya koma ƙasa ita kuma ta koma sama
Sunkoyo da fuskar ta tayi daidai tasa,yayin da karan hancin su yike gogan juna
“in faɗa ma wani abu??
Tayi tambayar cikin maƙoshi
Da ido ya bata amsar alamar eh
“ina sonka fiye da yadda kake sona”
Ya ɗan zaro ido yace
“kambu, wallahi banyar da ba,nafiki”
Tayi dariya har farare haƙoran ta suka bayyana
“to shikenan bari dare yayi zamu gani”
Ta faɗa cikin tsokana
Matseta yayi a jiginsa yace
“eyyeh wato har zumuɗin dare yayi kike? Ai ba sai da daddare ake yi ba bari ma kigani….
Ya ƙarasa faɗa yana yunƙurawa
Tashi tayi da gudu ta fice daga ɗakin tana dariya
Washegari da safe
Tana kwance Jikinsa tayi luf
Yana shafa Suman kanta da ta baje a bayan ta
_”chuchu”_
Ya kira sunan ta, ta buɗe idanuwanta da suka yi mata nawi, batare da ta amsa ba ta kalle sa kawai
Lallausan murmushi ya sakar mata
“Allah yayi maki albarka ya saka miki da gidan aljanna, kinsani farin cikin da ban taɓa shiga irin sa a rayuwa ta ba nagode”
Ta maida mai martanin murmushin tana jin ta cikin wata kalar sabuwar rayuwa me cike da natsuwa
Maida idanuwan ta tayi ta rufe dan sam bata jin ƙarfi
Da kanshi yayi mata wanka ya haɗa musu abun kari, be yarda taci da kanta ba a baki ya dinga bata bayan sun gama suka dawo cikin falon
Shagwaɓe masa tayi sosai ita ta gaji bacci take so ta sake yi
STORY CONTINUES BELOW
Ya zauna akan doguwar kujera sannan ta kwanta tayi matashi da cinyar sa
Lallaɓata ya dinga yi kamar ƙwai
Bayan wata biyu
Basu da wata matsala soyayyar su kawai suke sha,umar ya koma bakin aikin sa
Ranar wata Laraba yana zaune gefen gado yayin da take sanya kaya dan fitowar ta daga wanka kenan
Kallon ta yike tayi,ta ɗan tsaya hannun ta riƙe da riga tana kallon sa tace
“wai Jaana baka gajiya da kallona ne?
Murmushi yayi yana miƙewa idanuwansa akan ƙirjin ta
“kem kinsan har abada bazan taɓa gajiya da kallon ki ba”
Baya ta ɗan fara ja tana faɗin
“Jaana dan Allah kayi haƙuri ka bari muje siyan ice cream ɗinnan MU dawo”
Dariya yayi yana girgiza kai
“raguwa kawai, ba wani abu zanyi miki ba ni, gani nayi duk kin canza anya ba ciki ne dake ba kuwa?
Ta ɗan waro ido
“ciki?
Ta faɗa, umar ya jinjina kai
“eh haka nike zargi dan duk kin sauya amma bari mu bincika mu gani”
Gwaji na farko ko da yayi ya gano ciki ne
Farin ciki a gurin sa baya misaltuwa ɗaga ta yayi yayita juyi da ita
Har sai da ta fara ganin jiri
“Jaana ka saukeni dan Allah jiri nike gani”
Ajeta yayi a gefen gado ya durƙusa gaban gadon yana zuba ma kyakkyawar fuskar ta ido
“chuchu me kike so, me kike buƙatar kiga kin mallaka da ze saki farin ciki kifaɗamin zanyi miki shi yanzu”
Rauda tayi murmushi tana rusuno da fuskar ta kusa da tasa
“burina ɗaya ne a rayuwa inga na mallake ka,na riga da na samu Allah ya bani kai a matsayin miji bani da wani buri bayan wannan kasance wa dakai shine farin cikina”
Umar ya lumshe idanuwansa saboda daɗin kalaman ta da suka ratsa masa zuciya
“nagode Rauda, yanzu bari inje in siyo miki ice cream ɗin ki kwanta ki huta bayan shi kina buƙatar asiyo wani abu ne?
Girgiza masa kai tayi alamar A’a
Ya miƙe yana manna mata kiss a goshi
“sai na dawo”
Jinjina mai kai tayi, sai da ya kai bakin ƙofa sannan ta kira sa
Tsayawa yayi tare da juyowa
“ya aka yi madam?
Rauda tayi murmushi tace
” ka kula min da kanka sosai”
Shima murmushin yayi yace
“angama Ranki shidaɗe”
Bayan fitar sa, sujada tayi ga ubangiji na nuna godiyar ta garesa
Shafa cikin kawai take yi tana ayyano abunda zata haifa
Tunda ga wannan lokaci umar ya ƙara ƙaimi gurin nuna mata tsantsar kulawa.
Bayan wata tara
Cikin ta ya tsufa sosai dan da ƙyar take iya tafiya
Ranar ya shirya ze tafi aiki yaga yanayin ta sai a hankali ya fasa
Ashe ko haihuwa zata yi
Abunka ga likita da kanshi ya karɓi haihuwar abarsa
STORY CONTINUES BELOW
Tasha wuya sosai, shi ko ya shiga damuwa ya ƙara tausayawa mata
Cikin hukuncin Allah ta haifo kyakkyawan yaro namiji
Sai da ya tabbatar ta dawo cikin hayyacinta sannan ya sanar da anty kaltum
Ba afi minti goma ba sai gata ta ƙara so
Cikin farin ciki take faɗin
“ah Lallai sannu wato dan kana likita shine ba zaka sanar damu tun tana na ƙuda bako?
Dariya umar yayi yana miƙa mata jaririn
“ga ɗanki nan sai ki shirya sa, ki barmini mata ta zan kintsa abata da kaina”
Anty kaltum ta amshi Yaron tana faɗin
“masha Allah sannu da ƙoƙari da Rauda”
Rauda dai ba bakin magana dan anji yadda mata keji
Da kansa ya kira anty ummi da mama ya faɗa musu
Sunyi murna sosai anty ummi tace tana nan tahowa Washegari
Da daddare Rauda na zaune kan gado ta tsura ma jaririn ta ido
Ji take ƙaunar sa na ratsa zuciyar ta ba abunda ya bari na mahaifin sa, har ma yaso yafi sa kyau
Bata san umar ya shigo ba sai da ya ɗan zungure ta
Ta ɗago ta kalle sa
Murmushi yayi tare da zaunawa
“sannu Maman baby, babyn ake ta kallo haka?
Ta maida mai martanin murmushin tace
” ina kallon kamannin ka daya kwaso ne ba abunda ya ɗauko nawa”
Ƴar dariya yayi me bayyana tsananin farin cikin da yike ciki
“Haba dai wannan ƙaramin bakin ai irin naki ne”
Ta maida kallon ta ga Yaron tana faɗin
“Bawani nan,kadai yimin wayo bari Allah ya kaimu next time idan nasamu ciki bazan sake kallon ka ba har sai na haihu, dan ina ganin kallon ka da na dinga yi ne yasa”
Dariya yayi sosai
“tofah to Allah ya kaimu,wani suna kike ganin ya dace mu saka masa?
Tayi ɗan shuru tana nazari
“ni ina ganin Musaka masa Aasim”
Rauda tayi saurin kallon umar jin abunda yace
“Aasim fa kace?
Umar ya jinjina kai
” eh, miƙo sa ma inmasa huɗuba”
Rauda ta girgiza kai tace
“A’a Jaana kadai duba wani sunan….
Murmushi umar yayi tare da faɗin
” Aasim be cancanci Musaka sunan sa bane?
Shuru tayi tana cigaba da kallon sa
Umar ya cigaba da cewa
“Aasim masoyin ki ne na haƙiƙa wanda a yanzu ya sadaukar da soyayyar sa dan dai ki kasance cikin farin ciki,kisani da ace yana yana da mugun hali da tuni ya halaka ni, ya sha matuƙar wahala akan ki,ya sadaukar da abubuwa da yawa duk dai akan ƙaunar ki,bantaɓa jin tsanar sa a raina koda sau ɗaya ba saboda duk me sonki masoyi na ne,dan haka babu sunan da ya dace musa sai nasa”
Rauda ta kasa magana dan gabaɗaya jikin ta yayi sanyi
Lokaci ɗaya soyayyar ta da Aasim ta dawo mata
STORY CONTINUES BELOW
Umar ya ɗauki jaririn yayi Masa huɗuba sannan ya maida mata shi kan cinyar ta
“Allah ya Raya Aasim, bari inje in watsa ruwa”
Har lokacin ta kasa cewa komai
Ya ɗan tsaya yana kallon ta
“wai miye kika wani sauya, Haba madam smile mana”
Ajiyar zuciya ta sauke kawai
Dariya yayi yana ficewa daga ɗakin
Shimfiɗar da yaron tayi, ta kwanta tare rufe idanun ta
_”zan barki kamar yadda nayi alƙawari bazan sake bibiyar rayuwar ki, amma kisani bazan taɓa dena sonki ba har ƙarshen rayuwa ta”_
Kalaman shi na ƙarshe suka dawo mata
_haba habibty, kiyi murmushi mana idan kiƙa ƙi yifa zanyi kuka_
_Ina son ki fiye da yadda nike son kaina Rauda_
_Na amince na rasa komai inhar zan rayu dake_
Kalaman sa suka yi ta yi mata yawo a kunne
Ta shi tayi ta zauna, tana jin babu daɗi
Yanzu ko wani hali yike ciki oho, ya datse duk wata hanya da zata sa dashi da ita, yanzu shikenan ba zata ƙara ganin sa ba har abada?
Tayi wa kanta tambayar, sake rungume jaririn tayi tana jin wata sabuwar ƙaunar sa sakamakon sunan da aka sa masa
_matsayin ka a raina baze taɓa canza wa ba Aasim Allah yasa kana cikin farin ciki_
Ta faɗa cikin zuciyar ta
Ranar suna dangi sun taru sosai anci ansha anyi wadaƙa da kuɗi
Jariri ko ya samu kyaututtuka
Bayan wata huɗu Aasim ƙarami yayi wayau sosai dan har ya fara zama
Yaro ne me farin jini kowa sonsa yike yi
Yarima shine sunan da Rauda take kiran shi dashi
Ranar suna zaune tana ma yarima wasa yana ta dariya
Umar kallon su yike yi cikin farin ciki da nishaɗi
Miƙewa tayi ta ɗaura ma umar yarima aji kinsa
“Kaga idan na biye wa wannan yaron bazan je inyi wanka ba”
Umar ya ɗaga shi sama yana faɗin
“daɗin ta ga ubanshi a kusa bari na cigaba da ma wasan kaji ɗan albarka”
Dariya tayi ta haye sama, ta faɗa toilet tayi wanka
Shirin shadda pink tayi, tayi kyau sosai tana cikin ɗaura ɗan kwali ta lura da mutum a ɗakin
A ɗan tsorace ta ɗago, umar ta gani tsaye ya zuba mata idanun sa hannayen sa harɗe a ƙirji
“kai Jaana kabani tsoro wlhi yaushe ka shigo ban sani ba”
Ƙasaitaccen murmushi yayi yace
“ya za ai kisan na shigo hankalin ki ya tafi gurin kwalliya”
Ta sauke ajiyar zuciya
“hmmm to ai dan kai nike yi koh”
Jinjina kai kawai yayi, ya ware mata hannayen sa
“zo inji ɗumin ki plz“
Aje ɗan kwalin tayi ta shige ƙirjin sa
Ajiyar zuciya ya sauke me nawi tare da rungume ta sosai
STORY CONTINUES BELOW
murmushi tayi tana faɗin
“wannan irin ajiyar zuciya haka? Sai kace ka shekara batare dani ba, banfa fi minti ashirin da baroka ba”
“ba zaki gane ba,yanzu dai baki da wata matsala koh?
Ta jinjina kai
“bani da wata matsala mijina,nagode da kulawarka gare ni ina sonka”
Murmushi yayi tare da faɗin
“Nima ina sonki habibty”
Lumshe idanuwan ta tayi cikin farin ciki
“kasan wani abu…….
Kasa ƙarasa wa tayi, tare da saurin buɗe idanun ta
Idan batai kuskure ba habibty taji yace
“me kafaɗa yanzu? Mai maita”
Ta faɗa tana kallon cikin idanun sa,tabbas ze iya canza komai amma baze taɓa iya canza idanun sa ba
“Aasim……
Ta faɗa cikin rawar murya
“na’am habibty”
Ya amsa yana shafa fuskar sa kamannin sa suka bayyana
Baya taja da sauri tana faɗin
“innalillahi wa inna ilaihi raji’un”
Yana yin fuskar sa ta canza zuwa damuwa
“sai kace kinga sheɗani Rauda?
Zubewa tayi a kan gwiwowin ta nan da nan idanuwan ta suka ciko da hawaye
” Aasim alƙawari fa ka ɗauka Meyasa ka karya? Dan Allah kada ka cutar min da mijina kada ka cutar min da ɗana……..
Shhhh
Ya faɗa yayin da ya durƙusa gabanta
“ba wannan ya kawoni ba Rauda, tsakanina da mijin ki sai dai kariya ba dai cutar wa ba,ɗanki kuma ɗana ne bazan taɓa bari wani abu ya samesa ba, ki kwantar da hankalin ki dan Allah”
Kallon sa tayi da mamaki sosai tana tantamar abunda ya faɗa
“wallahi da gaske nike yi Rauda kiyarda dani”
Numfashi ta sauke tana jinjina kai
“shikenan me ya kawo ka gareni?
” zamu iya zama muyi magana?
Ya faɗa yana tsare ta da idanun sa
Gyaɗa kai tayi, bayan sun zauna yace
“Yanzu ba da bane Rauda, Bawani cutarwa da ze ƙara shiga tsakanin mu, tun ranar da umar ya shiga tauran na tabbatar da yana miki so me tsanani bazan ƙara yunƙurin raba shi dake ba,a shekara ɗaya da rabin da nayi ba tare dake ba na shiga tsananin ɗimuwa na koma rayuwa a ƙasan ruwa da ƙyar na yarda na koma masarauta
Rayuwa bata min daɗi Sam, bana shiga cikin ƴan uwana sai dai na kulle kaina a ɗaki
Ganin halin da na shiga me martaba ya auro min wata ƴar sarki
Amma bantaɓa jinta a raina koda sau ɗaya ba, Rauda bazan iya rayuwa babu ke ba kinkasance wani sashe na rayuwa ta
Ki amince kiciga da rayuwa dani nayi miki alƙawarin babu abunda ze faru da izinin Allah”
Rauda ta sauke ajiyar zuciya tace
“wace kalar rayuwa kenan Aasim amma dai ba irin wacce muka yi a baya ba koh?
“nidai ki amince min inrinƙa zuwa ina ganin ki, ko hakan ma ya isheni”
Kaɗa kai tayi tana ɗan murmushi dan sai lokacin hankalin ta ya kwanta
“nagode sosai habibty”
Da daddare suna kwance ita da Umar yana shafa gashin kanta ta kira sunan sa
Ya amsa, tace ɗazu fa Aasim yazo”
Umar yayi murmushi
“nasani ai,zan shigo ɗakin naji maganar ku”
Ta kalle sa da mamaki
“amma shine ranka be ɓaci ba?
“kan me raina ze ɓaci chuchu? Yariga ya zubar da makaman sa yanzu ya zama ɗan uwa agurina”
Ajiyar zuciya Rauda ta sauke ta jinjina kai kawai
Rayuwa ta canza,Maganar rikici ya ƙare
dan anriga anzama ɗaya, Aasim da umar sun koma kamar abokai musamman Aasim ya kan ɗauke su zuwa duniyar su
Rauda Sam bata da wata matsala dan bata aikin komai Aasim ya ajiye rauhanai mata masu yi mata,umar arziƙi ya ƙara haɓaka dan ya gina ƙaton asibiti na sa na kansa
Sukan haɗu su biyar, Aasim, umar, Rauda shahida da kuma da kuma Aasim ƙarami
Ayi ta nishaɗi su suna hira shahida na wasa da yarima
Ranar ma hakan ta kasance
Suna zaune a falo,yarima yayi bacci yayin da umar suke ta wasa da shahida
Aasim kallon Rauda yike tayi, ta cikin zuciyar sa ya aika mata da magana
“ina son ki Rauda”
Murmushi tayi tana kallon su gaba ɗaya wani farin ciki na ratsa zuciyar ta.
Alhamdulillahi anan na kawo ƙarshen wannan labari na jinnul aashique
Babban abunda nike so na isar shine,rayuwa ta kan zo ma mutum a yadda ubangiji ya tsara masa
Labarin jinnul aashique kashi talatin cikin ɗari 30/100 ya faru da gaske a zahiri
Dan Aasim akwai shi a zahiri yayi soyayya da wata budurwa wacce kuma saurayin ta shine umar
Amma sauran labarin na tsara shi ne dan na faɗakar na nishaɗantar
Aduk halittun da ubangiji yayi babu halitta me kyau kamar ta bil’adama
Shiyasa aljanu suke bibiyar mu,ya kamata mu kula sosai musamman ƴammata dan sunfi samun irin wannan matsalar
Murinƙa azkar, yayin shiga bayi, lokacin kwanciya da sauran su
Dan ba kowani aljani bane yike jin tsoron Allah akwai mugaye akwai kuma na kirki
Jinnul aashique shine matsalar da yawancin ƴammata suke fama da ita, zaka ga yarinya da saurayi yazo indai maganar aure ne sai ka ga ya dena zuwa ko kuma ita taji bata son kowa
Irin wannan matsalar tana da wuyar sha’ani,sai mun kula sosai mun dage da addu’a.
Allah ubangiji ya ƙara karemu da zuri’ar mu baki ɗaya.