JUYIN RAYUWA CHAPTER C KARSHE
……. Babu wanda yabi ta kanta sukaci gaba da harko kinsu , hatta d’iyar ta Kuluwa bata wani damu ba , domin itama zuwa yanzu k’wak’walwar ta tafara samun matsala saboda yawan shaye shaye da take yi .+
D’aya daga cikin dangin Malam Habu ne tayi magana , “ai wallahi saidai ki mutu amma Zainabu ta miki nisa can sama wajen da bazaki iso taba , ko a y’ar aikin ta zaiyi wuya a d’aukeki , danman hausawa sunce abunda ka suka shi zaka girba , toh wallahi saidai ki mutu….
Haka suka watse suka bar mata gidan , kwanan ta biyu acikin mawuyacin hali shima Malam Habu ya dank’ara mata saki sannan yabar gidan , domin kuwa tinin Sultan ya saya masa wani gida a garin tunda yace bazai koma birni da zama ba yafison nan .
Zainabu bayan da ta iya dole ta hak’ura tabi mijin ta badon tana sonshi bah , saidai ba yanda ta iya yin hakan ya zama dole a gareta , awani 6angaren kuma tana gani kaman Sultan ne ya kashe masoyin ta , tawani wajen kuma dole ta kwantar da kai donmin kuwa Allah ne ya k’wata mata da k’arfi tunda Sultan yafi k’arfin ta tako ina , sannan ta futa da azaban Lantana amma bazatabar kukan rashin Ahmad ba , danma yawancin abun da Sultan yake mata yana kama dana Ahmed.
Sultan 6ari yakeyi sosai akan Zainabu kamar zai cinyeya , saidai a nata 6angaren hakan bawai ya dameta bane Sam baya gabanta tanadai d’aurewa ne tunda mijin tane bayanda ta iya tunda tanada ilimin addini.
Kwanan Zainabu biyu a gidan , Sultan ya samo masu aiki kala daban daban , akwai masu kula da gyaran gidan , akwai mai wanke wanke da shara , akwai mai girki , sannan akwai wanda ya d’auko musanman dan kula da kwalliyan Zainabu , haka suka shigo falon ya ringa lissafa mata aikin su , bata tari nunfashin saba saida ta Bari ya gama gabatar dasu sannan ta d’aga ido tana kallonsa , cikin muryan ta mai dad’in sauraro ta fara magana , ” na gode da wannan k’ok’arin naka saidai magana ta gaskiya duk bana buk’atar su zan iya komai da kaina , idan na kwanta sukayi ni meye amfani na?” , Gaskiya Nima ina buk’atar samun ladan zan iya da kaina…
“A’a Zainaba kar muyi hara.
“Munyi angama indai wannan ne , zan iya komai da kaina kabarshi kawai.
STORY CONTINUES BELOW

“Kinsan fa girkin birni ba kaman na k’auye bane.
Hmmm! “Sultan kenan.
“Eh magana zakiyi zance ne na gaskiya.
“Nifa bance muyi dogon magana ba kawai banida buk’atan masu aiki, tana kaiwa nan ta mik’e tabar falon.
Sultan kai kawai ya dafe , domin kuwa yasan akwai matsala , taya zata fara sarrafa wannan kayan da aka zuba a gidan, sannan kwalliya ma takawo mai koya mata tace batasoo yanzu shi ya zai yi kuma yana matuk’ar yarinyan, tare da sha’awan ta mai tsanani saidai tak’i bashi fiska ya rasa ya zaiyi.
Babu yanda ya iya dole ya sallami masu aikin nan .
Zainabu d’aki ta wuce ta fad’a saman gado , wayan ta tajawo tanata faman juyata a hanunta , can dabara ya fad’o mata number din K’awar ta ma’eesha , tafara Kira saidai har 2miscalls ba ad’au wayan ba tsaki tad’an ja tayi jifa da wayan gefen tah , sai faman lunshe ido takeyi tana tinanin abunyi a yanzu , taga alaman ya d’auketa y’ar K’auye gara ta nunamar tasan me takeyi domin kuwa suma yan k’auye mutane ne saidai talauci ya hanasu walwala har a ringa ganin k’auyancin su , zatabashi mamaki dan shi a zatonsa ko boko batayi bah , hakama da yan uwan sa sukazo tanajin suka juya harce da turanci suna kusheta wai shi ya Sultan yarasa wazai aura sai yar k’auye gaskiya yaci baya ko boko fa batayi ba , kuma yar talakawa duk da zancen su ya mata ciwo Amma dole ta d’aure bata nuna musu hakan bah , Amma a yanzu zata cire kunya ta bashi mamaki , gara ta rungumi mijinta kowa kagani a duniya da nashi k’addaran kitama auren Sultan shine nata k’addaran.
Wayan ta ne ya katse mata tinanin da takeyi ta hanya k’aran da ya shiga yi , jawowa tayi taga ma’eesha ceh da sauri ta d’auka tare dayin sallama “hello ma’eesha kinajina?”.
Ma’eesha shiru tad’an yi tana son tina wannan muryan , dan ko a mafarki batayi tinanin k’awarta Zainaba bace.
Zainabu ce tasake magana a karo na biyu” baki gane me magana bako” toh Mrs Ahmed ceh…
Ma’eesha wani k’ara ta saki! “wooww kece ?” Zainaba Allah sarki wallahi nayi missing d’in ki , nayiwa Daddy magana akan za’akaini gunki amma haryanzu baice komai bah , Ina fatan kina lafiya?”.
“Lafiya lau wallahi , Nima nayi missing dinki , yasu mamah?”.
Suna lafiya gatanan ma muna tare ne .
“Please ki gaisheta .
Zataji insha Allah.
“Ma’eesha neman kifa nakeyi , zan iya ganin ki yanzu?”.
“Zainaba yanzu kuma?” Kinsan dole sai idan an barni tunda gun bawai kusa bane , ina fatan lafiya ko bikin ne yazo mata a gidan Ahmed?”.
Hmmm! “Nifa nayi aure 2days kenan kuma inanan acikin kaduna.
“Kai haba banason zolaya yaushe muka fara hakan?.
“Wallahi ba wasa nakeyi ba , nayi aure ina kaduna so nake kizo gida nah….
“Zainaba are you sure?”.
“Wallahi ina kd nayi aure.
Wani irin tsalle ma’eesha ta buga kamar wata k’aramar yarinya , nanfa taringa yiwa Zainabu tanbayoyi ganin hakan bazai kaita ba yasa tace a mata kwatancen gidan zatazoo, take Zainabu ta bata address din gidan , sukayi sallama akan sai tazo din…
Ma’eesha bata wani d’au lokaci ba tazo gidan da Zainabu take ta hanyar yin waya harta isoo.
Azahirin gaskiya bata wani yarda ba tadai zone ta k’ure Zainabu, ga mamakin ta saita ga fa da gaske ne Zainaba ce a gidan kuma ga duk kan alamu gidan tane.
Nanda tasa Zainabu gaba da tanbayoyi akan meya faru har tayi aure , kuma ina Ahmed , Zainabu ta bata labarin duk abunda ya faru , taji bbu dadi game da lamarin da ya faru na mutuwar Ahmed saidai tamata murna da samun *Juyin Rayuwa* dan Zainaba ta jima tanashan wuya Allah yasa hakan shine mafi alkairi….
Aranan ta shigawa Zainabu kasuwa ta had’o mata duk wani kayan gyaran jiki da zatayi amfani dashi , sannan ta dawo gidan tare suka shiga kitchen hadawa Sultan abinchi.
Lafiyayyen girki suka had’amar , da lemukan sha na gargajiya , lemon kwakwa , na dinger , sai kunun zakin aya , tuwon sakwara miyan egusi wanda yaji kaza aciki ba kadan ba , farfesun kayan ciki , saikuma fruits da akayan ka akajeresu akan wani k’ayatatten tire, saida suka shirya komai a daining sannan suka shiga gyaran gidan lokaci daya ko ina yadau kanshi bbu inda basu gyara ba har d’akin sa.
D’akin suka koma , Ma’eesha ce ta za6o mata kayan da zata sa yanzu , sannan ta za6a mata wanda zata sa lokacin bacci , wanka Zainabu tashiga yi kafin ta fito Ma’eesha ta gama hada mata wani kayan k’arin ni’ima jira takeyi tazo tashanye a gabanta dan tasan k’awarta da gudun magani duk yanda take, bata wani d’au lokaci ba ta fito tana ta faman zuba k’anshi saboda wasu turaruka da suka hada cikin ruwan wankan, dole tasata saida ta shanye abunda ta had’a , kwalliya Zainabu ta tsara lokaci daya ta sanja kamar ba ita ba.
“Ni kam zanwuce gida sai wani lokacin idan wani abu ya shige miki duhu saiki nemeni , kiringa kula da kanki karkiyi wasa da daman da Allah ya baki ki rik’e tsatta kwalliya , ki girmama dangin mijin ki , banda rowa ki mutunta uwar mijin ki k’annen mijin ki dangin sa , ki kula da mijin ki lokaci zuwa lokaci ki ringa hadawa kanki kayan gyara da kanki.
*KI KARAWA KANKI DADI*
*Kisamu dan bashana da gyadar mata da yayan kankana da fara biya rana da yayan zogale da bazar kwaila ki hadasu waje daya ki dakasu kirinka sha da madarar shanu zakiga yanda me gida zaiyi…*
*smile emoticon*
Sallama ma’eesha ta mata akan zata wuce gida , godiya sosai Zainabu tayi tare da mata kyauta , harda bata sak’o zuwa wajen mamah….
Bayan dawowan Sultan gaba d’aya gidan ya sanja mar , yana bud’e k’ofan falon yayi wani ajiyan zuciya saboda sanyin dad’in da yaji , d’an lunshe ido yayi , be Ankara ba yaji an kama jakan hanun sa , hankali ta furta “sannu da zuwa , k’aran muryan ne ya daki dodon kunnesa ga kuma wani k’anshin ya sake k’aruwa ahankali ya shiga bud’e idon sa tare da sauk’ewa akan kyakkyawan fiskanta zare ido yayi yaja baya yana sake murza ido , anya ba gamo yayi ba” Zainaba ya furta ahankali, yana cigaba da k’are mata kalloh…
“Na am , sannu da zuwa ta bashi amsa .
“Da gaske kene ?”.
“Nice man , ta furta tare da kama hanunsa tsnufi kujera .
“Allah na gode maka dakaban mata gakyau ga hankali da nitsuwa , inason ki Zainaba Soo marar misaltuwa , hanunta ya kamo tare da furta dan Allah ki soni ko ba yawa , bazan iya rayuwa bbu keba kece rayuwa tah….