K’ADDARA CE CHAPTER 1

  K’ADDARA CE CHAPTER 1

Wasu mutane zaune a cikin wani kango dake tsakiyar wani daji k’aramin gidane, mutum ukku ne xaune suna shan giya suna surutai da alama sunajin dadin yanayin da suke ciki, chan gefe d’aya nesa dasu kad’an wani mutum ne zaune bisa wani dutsi hannunsa rike da taba yana zuk’a yana kallon gefe daya da alama tunani yake,+

wani k’aton mutum ne yadoso cikin dajin fuskarsa a murtuke da ka gansa ka san babu alamun imani a tare dashi hannunsa rik’e yake da wata kular abinci wajen mutanen yanufa wani dan siririn mutum ne ya mik’e yanufi wajensa yana layi kamar zai fadi, kular hannun mutumin ya kar6a yace sannu da dawowa ogah me muka samu yau? Wanda aka kira da ogah ransa a 6ace yace hmm bari cha6o wai ni yau akaci mutuncina a kasuwa harda mari sauran mutane biyun dake zaune suka mik’e sukace mari kuma ogah! Wanene wannan Wanda yagaji da duniya yamareka kafada manashi yanzu muje mugama dashi,

kallonsu ogan yayi yace kwaro kubar aikin nan ba na yau bane sai gobe zamu aiwatar dashi domin yau inada appointment da uban daba, toh wai ogah mekayi masa har yayima irin wannan cin mutuncin? Inji wani guntun mutum bakki dake gefen ogan numfasawa ogah yayi hannu yasa a aljihunsa yadauko taba yakunna yafara zuka sannan yace wai dan na mari indo mai abinci shine shi yazo yarama mata yahau ni da fada wai akanme zan mari mace banda tarbiya,

ogah kuma shine baka cire masa hannuba kakyalesa ogah yakalli mutumin yace cinnaka kunfi kowa sanin halina ba na yafiya ba na jiran bashi ai saida nabishi daga baya ba tare da ya saniba naga gidanshi sannan nadawo gobe munada babban aiki daman munkwana biyu bamuyi irin wannan aikinba inji kwaro a’ah kar kumanta gobe ina cikin farin cikin zagayowar ranar haihuwata dan haka ba zamuyi kisaba saidai zamuyi masa tabon da ba zai ta6a warkewaba a xuciyarsa, yanzu dae kuzo muci abinci,

kallonsu suka maida wajen saurayin da yake zaune nesa dasu kadan ya daina zuk’ar tabar saidai yana riqe da ita hayaki duk ya turnik’e wajen kansa yana k’asa da alama har yanzu tunanin yake baisan wainar da suke toyawaba, cha6o yace wlh ogah babban yaro yana bani haushi ya cika miskilanci kuma kullum cikin tunani yake kuma ko sana’ar mu ta sata bai binmu saidai mu muje musamo muciyar dashi kwata-kwata bai dace da zama cikinmu ba kuma ogah ka hana mukoreshi,

murmushi ogah yayi yace kar kumanta kudinsa damukaci aqallah sunkai dubu dari ukku bai dace mukoreshiba alhalin muncinye mai kudi akwai a binda nake shiryawa dan aikin da zamuyi gobe shi nakeso ya aiwatar dashi dan nima ba zan yarda ace mukadai muke harkan nan ba shi bandashi,

ogah kar fa kamanta yau shekararmu daya tare dashi ammah komai sai dai mu muyi masa inji kwaro, haba kwaro da kaga babban yaro ka san yana cikin damuwa akwai abinda ke damunsa a cikin zuciyarsa domin kullum cikin tunani yake kuma munce yadinga shan kayan maye ammah ya qi saidai taba kawai yake sha,

kukwantar da hankalinku domin na San yadda zanyi dashi, bai jira yaji mi zasuceba yawuce yanufi wajen da babban yaro yake zaune dafa kafadarsa ogah yayi  firgit yadago kansa yayi manyan idanuwansa sun danyi ja wani kyakkyawan saurayine dogo fari wanda wahala ta dasar dashi ammah duk dahaka ana ganin dan haskensa yana da doguwar fuska wadda take dauke da dogon hanci da bakinsa dan madaidaici idanuwansa manyane sosai yana da dan siririn saje a gefen fuskarsa gashin kansa baqi ne sosai koda ba ya samun gyara ammah hakan bai hana bayyanar kyawunsaba,

murmushi ogah yayi yace babban yaro ya kamata karage tunani kar kajawo ma kanka wani ciwon na ce kadinga shan giya domin zata rage maka damuwa ammah ka qi kamaida giya tazama abokiyar hirarka zakaji dadin rayuwarka sosai, shidai babban yaro baice komai ba ganin haka yasa ogah yace kataso muci abinci, tabar hannunsa yayadda tare da murjeta miqewa yayi tsaye yabi bayan ogah suka shiga daki dan tuni su cha6o suna ciki suna jiran shigowarsu domin suci abincin.

  ****   ****  ****

Amina ! Amina!! Amina!!!  Firgit tayi tatashi daga baccin da take dasauri tasafko daga saman gado ummah tagani tsaye bakin kofa tana banka mata harara dasauri ta isa kusa da ummah tare da tsugunnawa tace ummah gani, ke dan ubanki wa kika barma wanchan wanke-wanken yayi maki akwai bawankine, kasa tayi da kanta tace kiyi hkr ummah wallahi da nagama sallah nadan kwanta saboda kaina danaji yanamin ciwo daman idan natashi zanyi, eh sannu ‘yar gata toh bari kiji bakida wani gata a gidannan yadda uwarki tayi min bauta kafin tamutu kema haka zakicigaba dayimin ko bakijiniba toh Amina tace tashare hawayen da suka zubo mata fita ummah tayi daga dakin tace kuma kar kifito yanzu kigani kuma inkingama kidaura min girki toh tace dasauri tatashi bayan ummah tabi,,,

kitchen tashiga wanke-wanken tatattaro tazo tayi tana gamawa tashare gidan sannan tadaura girkin dare kasancewar marece ya yi kuma yau bata samu damar zuwa islamiyyah tunda ta makara sai gab da magrib tagama girkin alwallah tayi tashiga dakinta tagabatar da sallah addu’o’i tayi tashafa,,

daidai lokacin akayi sallama dasauri tafito daga dakinta tana amsa sallamar wajen mai sallamar ta iso tana murmurshi kayan dake hannunsa takar6a tare dacewa abbah sannu da hanya ya kasuwa? Yauwa mamana kasuwa Alhmdllh ya gidan dafatan kina lpy, lpy lou Abbanah dakinsa yawuce tabi bayansa ta aje masa kayan da yadawo dasu kitchen taje ta dauko masa ruwan sanyi takawo masa, kar6a yayi yace Allah yayimiki albarka mamana, Ameen Abbanah,,

fitowa tayi kitchen tanufa ta tadda ummah harara ummah tabuga mata tace munafuka ubanmi kikace ma uban naki, wlh ummah ba abinda nace mai ruwa kawai nakai mashi, banza mai mugun hali irin na uwarta abincinta tamiqo mata dan kadan acikin plate bata damuba daman ta saba jin wannan kalaman daga bakin ummah, kar6a tayi tatafi dakinta abincin taci,,

Da tagama taje tawanke duk kwanonin da ta 6ata sannan tadawo daki sallar isha’i tayi data gama tilawar alqur’ani tayi sai wajen tara tatashi wanka tashiga tayi data fito tasaka kayan bacci tafeshe jikinta da turare kasancewar Amina tana da son kamshi gado tahau takwanta tana tunanin rayuwarta.

”’SHIN WACECE AMINA”’Alh Ahmad shine mahaifin Amina d’an kasuwane yana da rufin asirinsa daidai gwargwado suna zaune a garin mashi dake cikin garin katsina a unguwar….. A madaidaicin gidansa mai dauke da d’akuna ukku manya palor nd bedroom kowane daki akwai toilet  a cikinsa sai kitchen a tsakar gida sai flowers masu kyau daga tsakiyar gidan.

yana da mata biyu Zainab da Hannatu, Zainab itace uwar gida bata ta6a haihuwaba shekarsu takwas da aure sannan ya auri Hannatu,

Hannatu ta kasance bafullatana ce tana siyar da kindirmo wajenta yake siya daga nan suka fara soyayya har ya aureta.

tunda ya auri hannatu take wahala a wajen zainab duk ayyukan gidan kanta suka dawo hannatu tana da hakuri sosai ga ta da kunya kasancewarta bafullatana ta usuli, a haka har tasamu ciki tunda Zainab tagano hannatu tana da ciki nan hankalinta yaqara tashi duk da haka bata daina azabtar da itaba wajen ayyukan gida.

Akwana atashi cikin hannatu yacika wata tara tahaifo diyarta kyakkyawa mai kama da ita,  ranar suna yarinya taci sunan marigayiya mahaifiyar Alh Ahmad wato Amina,

hakadai rayuwa taci gaba da tafiya komai bai chanza ba, Amina tanada shekara ukku mahaifiyarta tak’ara samun ciki wajen haihuwa hannatu tarasu. Mutuwarta ta girgiza kowa Alh Ahmad har kusan zaucewa yayi domin ya san ya yi rashin mace tagari,

hatta Zainab saida mutuwar tarazanata bayan kwana biyu takoma daida. Bayan sadakar arba’in dangin hannatu sunso Abbah yabasu Amina ammah yak’i yace shima yana buk’atar d’iyarsa a kusa dashi daganan sukayi fushi basu k’ara zuwa gidan ba.

Daganan rik’on Amina yakoma hannun ummah tana azabtar da ita sosai ammah idan gaban abbah ne tana nuna tanason Amina sosai ganin haka yasa hankalin Abbah yakwanta.

Amina tana da shekara hudu Abbah yasata makarantar islamiyyah da Boko kasancewar Amina ta tashi yarinyace mai wayo, a haka har tagama primary school dinta.

Zaman gidan da tayi kafin tacigaba da karatu yasa duk wani aikin gidan ummah tasakar matashi tamaidata kamar baiwarta hatta wankin ummah ita takeyi, zuwan da takeyi islamiyyah shine take samun hutu.

Ahaka har taci gaba da karatunta, kullum kafin tatafi makaranta sai ta gyara gida ta yi wanke-wanke ta had’a masu breakfast sannan take tafiya, idan tadawo ma haka za tayi ummah ba ta aikin komai.

A haka rayuwar Amina tacigaba da tafiya tana da shekara sha bakwai tayi S.S.C.E, ynz batada sauran hutu daman zuwa school dinne yake dan debe mata kewa toh ynz babu, gashi ummah ba ta barinta yin k’awaye.

Ba ta samun hutu sai ummah ta tafi unguwa kokuma idan Abbah ya dawo kasuwa dawuri take samu suna d’anyin fira dashi.

  *CIGABAN LABARI*

Tun dasafe Amina tatashi kasancewar yau lahadi akwai islamiyyar safe wanke-wanke tayi tagyara gidan tashiga kitchen tahad’a breakfast tashirya tatafi islamiyyah,

karfe 10:00am tadawo lokacin abbah har ya fita, dakin ummah tawuce ta taddata tana breakfast gaisheta tayi harara ummah ta banka mata amsawa tayi k’asa-k’asa tace har andawo daga yawon karuwancin? Kallonta Amina tayi hawaye suna zubowa daga idonta tace wlg Ummah islamiyyah naje, ke ni tashi kiban waje ni zaki ma k’arya?  tashi tayi taje dakinta tacire uniform dinta, fitowa tayi domin d’aura girkin rana.

****      ****     *****   ****

Yauma kamar kullum zaune suke suna ‘yan shaye-shayensu duk kayan mayene a gabansu domin taya ogansu murnar zagayowar ranar haihuwarsa chan nahango babban yaro gefe daya zaune rik’e da taba yana zuk’a.

Kofi ogah yadauka yazuba giya yatashi yatafi wajen babban yaro yana sha yace babban yaro yau fa muna da aiki cikin dare kuma muna bukatarka a cikin aikin kallonsa babban yaro yayi zaiyi magana ogah yad’a masa hannu yace wannan alfarmar da na nema kar kak’i kar6arta pls, yau shekara daya ammah ban ta6a neman alfarma wajenka nasamuba,

Murmushi babban yaro yayi wanda baikai zuciba iyakarsa baki yace shikenan ogah  na Amince.

Dafa kafad’arsa ogah yayi yace dakyau babban yaro.

****  ****    ****    *****

Sauri take ta   isa gida kasancewar magrib ta gabato yau basu tashi islamiyya da wuri ba saboda malam mai fiqhu baizo dawuriba, tana shiga gida ana kiran sallah,

Da sallamah tashiga, ummah na zaune tsakar gida bisa tabarma tana yanke farce ahankali ta isa wajenta tare da tsugunnawa tace ummah sannu da gida, ba tare da ummah ta d’ago ta kalletaba tace sai yanzu k’warton naki yasallameki? Bata jira amsar da zata bataba tace kije ga cus-cus chan kitchen kiyi  jalop dinsa,

Toh tace, d’aki tashiga tacire uniform dinta tashiga toilet tad’auro alwallah tazo tagabatar da sallar magrib, da tagama sallah yau ko tulawar alk’ur’ani bata tsaya yi ba tayi addu’a tatashi tashiga kitchen,

Ana kiran sallar isha’i tagama girkin tawanke duk abinda ta6ata tagyara kitchen din, d’akin ummah taje tace mata ta gama ko kallon inda take ummah batayiba,

‘Dakinta takoma taje tagabatar da sallar isha’i, sannan tafito tanufi kitchen tatadda har ummah ta zuba mata abincinta d’auka tayi tazauna kitchen din taci tawanke plate din,

Daidai lokacin abbah yadawo daga kasuwa wajensa taje tana murmushi ta amshi ledar dake hannunsa sannu da zuwa abbah, shima murmushin yayi yace yauwa Mamanah ya gidan? Lafiya lou abbah,

‘Dakinsa yawuce tana biye dashi a baya ledar ta aje mai tare dayi mai sai dasafe za ta fita yakirata chocolates ne yad’auko daga cikin jakkar yamik’o mata kar6a tayi tayime godia, daidai zata fita sai ga ummah za ta shigo d’akin harara ummah tabanka mata sannan taja tsoki tashige d’akin.

‘Dakinta takoma tacire kayan jikinta yashiga wanka bayan ta fito tashirya cikin rigar bacci fara daidai gwiwa turare tad’auka tafeshe jikinta dashi sannan tayi addu’a takwanta.

****  ****    ****     *****

Wajen karfe biyun dare wasu mutanene su biyar suka haura katangar gidan Alh Ahmad mutum ukku hannunsu rik’e da bundiga, mutum d’aya kuma rik’e yake da shar6e6iyar wuka, mutum daya kuma bai rik’e komai ba duk sunsha bak’ak’en kaya sun kulle fuskarsu idanuwansu kawai ake gani,

‘Dakin da yayi masu kama da na mai gidan suka nufa harbin k’ofar sukayi da k’afa tabud’e,

Wuri ogah yasamu yazauna yace kushiga kufito min dashi, bedroom din Abbah suka shiga daidai lokacin yafarka sbd motsin da yaji salati yafarayi ganin mutane riqe da bundiga sun nunasa daidai lokacin ummah tafarka tace munshiga ukku bayin Allah lafiya?

Alh Ahmad yace me kukeso? Basuce komaiba suka tasa su gaba sukafito falo ummah tana rik’e da Abbah, mutum biyu ne zaune saman kujera d’aya hannunsa da bundiga d’ayan kuma bai rik’e komai ba ya kunna T.V yana kallo, duk’ar dasu akayi gaban ogah,

Abbah addu’oi yakeyi, Ummah kuma kuka take tana rok’onsu tsawa suka daka mata saida tafirgita tak’ara shigewa jikin Abbah, kallon mutanen ogah yayi yace kuje kufiddo min duk wani mutum dake cikin gidan nan, angama ogah

Bincika gidan suka shigayi basuga kowaba har sukazo d’akin da Amina take tura d’akin sukayi sukajishi a kulle, bubbugawa suka shigayi, daidai nan Amina tafarka bacci a tsorace murya tajiyo ana cewa ko a bud’e d’akin ko mu6alla k’ofar mushigo,

Jin haka yasa Amina tasafko daga saman gadon jikinta sai kyarma yake addu’a kawai takeyi zuwa tayi tabud’e d’akin mutum ukku tagani a tsaye, mutum biyu da bundiga mutum d’aya da wuk’a rikicewa tayi tace bayin Allah lafiya?

Basu ce mata komai ba suka tisata a gaba har d’akin Abbah, wasu mutanen tagani zaune dasauri ta isa wajen Abbah tafad’a jikinsa tana kuka tace Abbah mi mukayi masu? Tsawa suka daka mata sukace tayi masu shiru nan Amina tayi shiru tana kyarma.

Ogah ita kad’ai ce muka samu a gidan, kallon Alh Ahmad ogah yayi yace ka tuna wanda kaci mutuncinsa har ka mareshi a kasuwa jiya? Eh Abbah yace toh nine kuma munzo d’aukar fansa K’ADDARA CE za ta fad’a a kan d’iyarka,

Kallonsu Abbah yayi hankalinsa a tashe..

Kallonsu Abbah yayi hankalinsa a tashe yace dan Allah kayi hakuri kar kuyima iyalina komai ni yakamata kud’au fansa a kaina, a’a dan Allah kar kuyi ma Abbah na komai kuyi mana hakuri duk abinda kukeso zamu baku inji Amina, kallonta ogah yayi yabushe da dariya yace ya yi kyau ‘yar budurwa ashe kina son Abbanki dayawa haka toh ba damuwa kar ki damu daman ai kanki zamu d’au fansar,

Kallonsa yamaida wajen mutumin da tunda suka shigo baice komaiba kamar baisan abinda suke aikatawa ba hankalinsa na wajen T.V yana kallo, yace babban yaro wannan fa aikinkane,

ba tare da ya juyoba yace aikina kuma? Miye had’ina da abinda kukeyi?

Murmushi ogah yayi yace eh inaso kakusanci wannan yarinyar domin shine kawai fansar da zan d’auka, juyowa yayi a firgice yakalli ogah yace ban ta6a zinaba kuma ba zan faraba,

da su cha6o kasa tunda su sun saba bin ‘yanmata daman, ni ba zan iyaba.

Mik’ewa tsaye ogah yayi yace ni kai nakeso ka aikata inkuma ba hakaba toh shikenan jawo gashin Amina yayi dak’arfi kasancewar kanta babu kallabi yace zamu kasheta.

Rintse idonta tayi saboda zafin damk’ar da yayi ma gashinta hawaye suna zuba daga idonta.

Kallonsa babban yaro yayi hankalinsa a tashe yace kisa kuma? Eh ogah yace, 

Kallonsa yamaida wajen yarinyar da ogah yake rik’e da ita ba zata wuce 19yrs ba, chocolate colour ce tana da fad’in fuska da dogon hanci idanuwanta sunada girma ammah ba sosai ba, bakinta dan k’aramine tana da tsayi ba laifi, tana da ‘yar k’iba dai-dai jikinta Nightgown din da ke jikinta ta taimaka wajen bayyanar kakkyawar surar jikinta.

Kukan Abbah ne yadawo dashi daga tunanin da yake, Dan Allah kuyi hak’uri kar kukashe min yarinya wlh ita kad’ai gareni ni ku kasheni,

Runtse idonsa babban yaro yayi tausayinsu yakamashi ganin babban mutum yana kuka wannan wace kalar K’ADDARA CE take shirin k’ara fad’amin yafad’a a cikin zuciyarsa, bud’e idonsa yayi Jin ogah ya ce k’waro inason ganin kan yarinyar nan a k’asa yanzu,

Dasauri babban yaro yace kar ku kasheta na amince zan kwanta da ita ammah da sharad’i d’aya, ogah yana jinka wane sharad’ine inji k’waro,

Saidai a d’aura min aure da ita, Jin haka yasa Amina tabud’e idonta hankali a tashe Kallon mutumin da ya ambaci aurenta tayi saidai kuma fuskarsa a kulle take, kuka tafashe dashi tace dan Allah kuyi hak’uri kukyaleni.

Dariya sauran mutanen suka bushe da ita sukace aure kuma babban yaro? Basuyi mamakin hakanba kasancewar sunsan halin babban yaro yana da tausayi sosai.

Bai ko kallesuba hannu yasa cikin aljihun wandonsa yad’auko wallet dinsa kud’in dake ciki yaxaro yan dubu-dubu ne dubu 20 yazara yaje gaban abbah da mamakin jin kalaman mutumin yasa ya kasa motsin kirki yamik’a masa yace kar6i sadakin d’iyarka kar6a abbah yayi jikinsa duk ya yi sanyi.

Ogah yace nine waliyyin ango kaikuma cha6o waliyyin amarya nan sukasa Alh Ahmad yad’aura auren akan sadaki naira dubu ishirin.

Ummah da tun da aka hanata magana bata k’ara cewa komai sai a lokacin tace wannan wane kalar aurene ba shedu? Harararta k’waro yayi yace ke yi mana shuru muma ai shedu ne koke baki shedaba? Jikinta yana kyarma tace wlh na sheda kayi hakuri.

Amina tunda akafara maganar kuka take wajenta cha6o yaje yajawota yakawota kusa da Babban yaro yace ga matar kanan,

Sai kaje ka aikata abinda ogah ya umurceka dashi idan kuma ba hakaba wlh har iyayenta sai mun kashe.

STORY CONTINUES BELOW

Ogah yace kuje duk d’akin da yayi muku a cikin gidan nan, ku kuma cha6o kai da cinnaka kubisu kuzama sheda.

Jin ance za a kashe har iyayenta yasa tawuce gaba tana kuka, bayanta babban yaro yabi hankalinsa a tashe su cha6o suna biye dasu a baya.

‘Dakinta tanufa tashiga shima shiga yayi yamaida k’ofar yakulle, su cha6o suka tsaya bakin k’ofar d’akin, jingina yayi jikin k’ofar idonsa a lumshe,

Ahankali yabud’e idonsa yasafkesu akan Amina da take waje d’aya sai kuka take tausayi tabashi ji yake ba zai iya aikata hakan ba,

Tunowa yayi da maganar ogah da yace sai ankashe har iyayenta idan dai har bai kusancetaba.

Ahankali yataka yanufi inda take a tsaye tana ganinsa nan hankalinta yak’ara tashi,

Da baya-baya take tafiya tana kuka tana rok’onsa binta yakeyi har tazo bakin gado batasaniba tana k’ara ja da baya tafad’a saman gadon dasauri tarintse idonta tana addu’oi.

Max din dake fuskarsa yacire, Ahankali shima yahau gadon jawota yayi jikinsa, dasauri tabud’e idonta,

gabantane yafad’i datayi arba da fuskar kyakkyawan saurayin kallonshi take hankali tashe.

Bai damu da kalar kallon da take mashiba yad’aure fuska yace taimakonki fa zanyi kema kin sani, bakinsu yahad’e waje guda yafara kissing dinta kamar yana tsotsar lollipop, idanuwanta talumshe sai da sukayi kusan minti goma a haka ahankali yazage zip din rigarta yayi qasa da rigar.

Itadai Amina tuni ta fita hayyacinta kyarma kawai takeyi, hannunsa yamik’a yafara shafo k’irjinta ahankali yazare rigar da take jikinta tare da kwantar da ita, bakinshi yazare daga cikin nata,

saida gabansa yafad’i da yayi tozali da k’irjinta.

Idanuwanta tak’ara runtsewa gam tana hawaye,

Tashi yayi yacire kayan jikinsa.

Kuka take tana rok’onsa yak’aleta ammah ina baisan inda kansa yakeba, ba shi yakyaletaba sai da yaji ya samu nutsuwa hankalinsa ya dawo jikinsa sannan yaga abinda ya aikata.

Mirginawa yayi gefe guda yana maida numfashi saida yayi kusan minti goma a kwance daidai lokacin aka fara buga k’ofar,

Tashi yayi yashiga toilet d’inta cikin sauri yatsaftace jikinsa sannan yahad’a ruwa masu d’umi.

‘Dakin yadawo yasaka kayansa wajen Amina yanufa a inda yabarta nan take bata motsaba kuka kawai take,

‘Daukarta yayi yanufi toilet din da  ita cikin ruwan yasakata, k’ara tasaki tare da rirrik’eshi,

Zare jikinsa yayi daga ruk’on da tayi mashi fitowa yayi daga toilet d’in,

Max dinsa yad’auka yamaida a fuskarsa yaje yabud’e k’ofar, cha6o yace haba babban yaro ka san muna jiranka shine zaka dad’e haka kusan awa d’aya, dariya k’waro yayi yace ya samu amarya ai dole yake mantawa da kowa.

Bai ko kalli inda sukeba yawuce binsa sukayi a baya suka nufi d’akin abbah suna shiga ogah yakalli cha6o, cha6o yace angama komai ogah kallonsa yamaida wajen k’waro d’aga mashi kai k’waro yayi alamar eh hakane.

Hawayen bak’in cikine suka zuboma abbah jin abinda aka aikatama d’iyarshi

Murmushi ogah yayi yakalli abbah yace aiki ya yi kyau ko da wannan nabarka dashi ya isheka domin mun cusa maka bak’in cikin da ba zaka ta6a mantawa dashiba,

Ammah duk da haka saura abu d’aya yarage shine inyanke hannun da ka mareni dashi dan haka cinnaka mik’omin wuk’ar nan.

Hankalin Abbah yak’ara tashi nan yafara basu hak’uri ummah da take raku6e waje d’aya hawaye kawai take ta kasa motsin kirki.

Daidai lokacin cinnaka yamik’a ma ogah wuk’ar sai shek’i take.

Tashi ogah yayi yanufi inda Abbah yake,

Tunda yashigo yana bakin k’ofar tsaye ya jingine kansa a bango idanuwansa a lumshe suke bai tankaba,

sai a lokacin yabud’e idonsa ganin abinda ogah yake shirin yi dasauri yaje yashiga tsakanin ogah da abbah yakalli ogah yace haba ogah me kuma kake shirin aikatawa haka,

dan Allah kakyalesa hakanan kaduba fa irin aika-aikan da kasa nayi ma d’iyarsa wannan bai isa ba?

Babban yaro wannan da kud’i ka aiwatar dashi wannan kuma ladan marin da yayi min ne.

Pls na rok’eka kayi hak’uri kar kayi hakan saboda ni ba dan halinsaba.

Kasancewar ogah yanason babban yaro sosai shiyasa yahak’ura yace shikenan na hak’ura ammah dole yak’wanta yabani hak’urin marin da yayi min.

Tun kafin yakulle bakinsa tuni abbah da ummah sun zube gaban ogah suna bashi hak’uri sun kusan minti biyar sannan ogah yace guys kuxo mutafi lokaci yana k’urewa gobe in halinsane yak’ara yagani idan zai kwana a raye, fita sukayi daga d’akin,

Ammah shi babban yaro bai fitaba saida yad’ago abbah daga kwancen da yake, sannan yafita daga d’akin da sauri.

Gidan suka bud’e suka fita ta k’ofa suka shiga motarsu sukabar unguwar dasauri Kasancewar asuba ta gabato.

jin k’arar tafiyarsu yasa ummah tayi sauri tatashi daga kwancen da take kallon abbah tayi da yake zaune sai hawaye suke fita daga idonsa, harara ta wurga mashi tace wai Alhaji me kayi masu haka har sukazo d’aukar fansa akanmu?

Hawayen fuskarsa yagoge yace wlh zainab K’ADDARA CE kawai tahad’ani dasu nan yakwashe komai yafad’a mata.

Harara tawurga mashi a karo na biyu tace sannu wanda yafi kowa tausayi toh gobema sai kak’ara aikatawa kaga in sun tashi kawai kasheka zasuyi, kallon ummah yayi hankalinsa a tashe yace Amina fa,

Dasauri suka tashi suka nufi d’akinta.

A 6angaren Amina kuma tunda yafita yabarta gasa jikinta tayi sosai kusan 20 minutes tayi tana gasa jikinta da ta ji ruwan sun huce sai tacanza wasu ruwan tunani takeyi wane kalan tashin hankali Abbanta zai shiga,

Kuka takeyi sosai tace wannan wace kalar K’ADDARA CE jin kanta yana ciwo sosai yasa tafita daga cikin ruwan wankan tsarki tayi tad’auro towel dakyar tafito daga toilet d’in direct wajen wardrobe dinta tanufa,

Doguwar riga har k’asa tad’auko tasa, zanen gadon tacire taje toilet tajik’ashi , dawowa tayi d’aki tashimfid’a wani bedsheet d’in gadon tahau takwanta,

Kukan tanema tarasa saidai hawaye kawai suke zubo mata, meyasa irin wannan k’addarar tafad’a a kaina innalillahi wa inna”ilaihirraji’un idanuwanta tarintse tana jin zazza6i yana neman rufeta…

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *