K’ADDARA CE CHAPTER 11
Tsorone duk ya baibaye zuciyarta tace na shiga ukku malam lafiya? Mi yakawo ka d’akina bakaga dare bane? Please katashi kafitar min daga d’aki,
Shidai fahad kallonta kawai yake, takaicine ya isheta ganin tana ta magana ammah ya shareta sai faman kallonta yake, harararsa tayi tace malam baka ji ina maka magana nace kafita kabar min d’aki,
murmushi yayi yace d’akinki ko d’akinmu? K’ara d’aure fuska tayi tace d’akina dai kai d’akinka ai yana chan, d’auke kai yayi daga kallonta yace nikuma nan naga damar kwana yau, zaro ido Amina tayi tace karufamin asiri please katashi kafita kar ashigo aganka,
Dariya yayi ganin yadda duk tabi tagigice yace kikwantar da hankalinki babu wanda zai shigo dan na kulle k’ofar,
Amina nan tak’ara firgicewa idanuwanta suka cika da k’wallah tace fahad dan Allah kafitar min daga d’aki,
Murmushi yayi yace kar kidamu ni bacci kawai nazo muyi kar kimance da sharad’inmu na d’azun na ce dole kiyi min biyayya,
Share kwallar idonta tayi tace ammah yaya fahad hakan da zakayi ai bai daceba,
Kifad’amin abinda yadace kar kimance ke fa matatace ina da iko da ke,
Hararasa tayi a karo na biyu tace wlh bakada iko da ni kuma kar kak’ara kirana da sunan matarka,
Tashi yayi zaune yace nikuma zan gwada miki ikona akanki hannu yakai yafizgo towel d’in dake jikinta dasauri takai hannu tadafe k’irjinta dan ma Allah yaso akwai pant a jikinta rikicewa tayi tarasa ina zata nufa juyawa tayi zata gudu tanufi toilet, cikin zafin nama fahad yajawota tafad’o jikinsa.
Amina fashewa tayi da kuka tace dan girman Allah kayi hak’uri kakyaleni kar kayimin komai karufa min asiri
Fahad duk ya fita hayyacisa shafata kawai yake ta ko’ina ahankali yakwantar da ita saman gadon, rik’esa Amina tayi tana girgiza mashi kai dakyar tabud’e baki cikin kuka tace wlh period nake dan Allah kakyaleni fahad,
Batare da ya kalletaba yacigaba da abinda yake,
Cikin sheshek’ar kuka tak’ara maimaita mashi
Dakyar ya iya bud’e baki cikin kasalalliyar murya yace i know that, don’t worry baby babu abinda zan miki kikwantar da hankalinki,
Toh kakyaleni dan Allah wlh bani so, shuru yayi yacigaba da abinda yake, cikin kuka tace please fahad kadai……… bata k’arasa fad’aba yahad’e bakinsu waje guda, romance d’inta yake son ransa itama Amina saida tafita hayyacinta kasa hanasa tayi saida yagaji dan kansa sannan yakyaleta batare da ya yi sex da itaba,
STORY CONTINUES BELOW

Gefenta yamirgina tare da lumshe idonsa yanajin wani nishad’i atare dashi, Amina kasa motsi tayi duk kunya tabi takamata duk yadda taso taji haushinsa ammah ta kasa saima son fahad da yake k’aruwa a cikin zuciyarta lallai ta yarda fahad gwarzon namijine komai nasa cikin aji yake yinsa, dakyar takai hannu tajawo blanket ta lullu6e jikinta tajuya mashi baya saboda wata irin kunyarsa da takeji, saida yasamu nutsuwa sannan shima yajawo blanket d’in yashiga yanjota jikinsa yayi yarungume k’ok’arin janye jikinta daga nashi tashiga yi k’ara matseta yayi cikin kunnanta yayi mata rad’a cikin muryarsa mai sanyi yace kikwantar da hankalinki babu abinda zanyi miki bacci kawai zamuyi, lumshe idonta tayi tana murmushi ta ji dad’in kwanciyar nan da nan bacci yayi awon gaba da ita, fahad yana jin ta yi bacci k’ara gyara mata kwanciya yayi yak’ara rungumeta sannan shima bacci yayi awon gaba da shi,
Karfe hud’u da rabi Amina tafarka jinta tayi jikin mutum nan tatuno da abinda yafaru shirin tashi take ammah taji ya matseta gam ahankali tad’ago kai tasafke idonta akan kyakkyawar fuskarsa baccinsa yake hankalinsa a kwance fuskarsa d’auke da murmushi, murmushi itama tayi ahankali takai hannunta saman fuskarsa tashafi sajen da ke gefen fuskarsa dasauri tajanye hannunta ganin yana shirin farkawa, ahankali yabud’e idonsa ganin haka yasa Amina tad’aure fuska tace katashi katafi d’akinka please kaga asuba ta kusa kar afito aganka nan,
K’ara rungumeta yayi yace Toh saime dan anganni ni ai nafison agannin.
Zaro ido Amina tayi tace karufa min asiri dan Allah katashi katafi,
Janyeta yayi daga jikinsa ya kwantar da ita dasauri tak’ara janyo blanket tarufe k’irjinta,
Murmushi fahad yayi yatashi yajawo rigarsa yasaka batare da ya k’ara kallontaba yaficce daga d’akin.
Ko da yafito gidan shuru kowa yana d’akinsa dasauri yanufi hanyar d’akinsa yabud’e yashiga toilet yashiga yayi wanka yatsarkake jikinsa sannan yad’auro alwallah cikin sauri yashirya yanufi masallaci dan ya san daddy tuni ya tafi dan tun yana wanka yajiyo yana kwankwasa masa k’ofa.
Yaye bargon tayi tajawo towel d’inta tad’aura dasauri taje tasa ma k’ofarta key, toilet tafad’a tayi wanka tagyara jikinta sannan tadawo takoma saman gadon takwanta pillow tajanyo tarungume tana ta murmushi tana tuno yanayin da suka shiga jiya ahaka har bacci yayi awon gaba da ita.
Fahad ko da suka gama sallah basu dawo gidaba suna masallaci suna azkar har gari yafara haske sannan suka dawo gida direct d’akinsa yawuce shima kwanciya yayi yakoma bacci.
Ba ita tafarkaba sai wajen k’arfe goma gyara d’akinta tayi fas takunna turaren wuta sannan tashiga wanka, bayan ta fito simple makeup tayi tashirya cikin material pink ta yi kyau sosai, bud’e d’akin tayi tafito tanufi d’akin babah mairo dasallama tashiga babah mairo suna zaune da Ameerah suna breakfast cikin fara’a babah mairo ta amsa mata dagudu Ameerah tataso tafad’a jikin Amina tace oyoyoo momo, Amina tana dariya tad’agata sama tace oyoyoo my daughter, zama tayi tagaishe da babah mairo cikin girmamawa cikin sakin fuska baba mairo ta amsa mata bayan sun gama gaisawa tatashi tabar Ameerah nan babah mairo tana cigaba da bata breakfast,
parlour tanufa dasallamarta tashiga a dining table tahangosu mummy zaune daidai lokacin su salma suma suka fito daga room d’insu atare suka nufi wajen su mummy kowa kujera yajawo yazauna nan suka gaishe da su daddy sannan suma suka shiga gaisawa da juna,
Mummy ce tace my son halan har ynz baccin yake bai tashiba saisa bai fitoba fatima kije kikirashi, bata gama rufe bakiba sai gashi ya shigo d’akin da sallamarsa,
Amsa masa sukayi daddy cikin fara’a yace d’an mummy yanzu mummynka take shirin aikawa agano mata lafiyar d’an nata, murmushi yayi yace Allah sarki my mummy na hutar da ku gani nazo, tafowa yayi yanufo dining d’in cikin tafiyarsa ta k’asaita jawo kujera yayi wadda take opposite d’in ta Amina yazauna cikin girmamawa yagaishe da iyayensa suka amsa mashi cikin fara’a, fatima ce takalli yayan nata tana murmushi tace gud morning my bro, mrng too,
STORY CONTINUES BELOW

Salma da tunda yashigo tatsaresa da ido ta ji haushin zaman da yayi opposite d’in Amina da bai zauna nataba ammah ta d’anji sauk’i da yazauna gefenta ahankali tace yaya fahad ina kwana? Batare da ya kalletaba yace kin tashi lafiya? Lafiya lou tace.
Amina da tunda yashigo kanta a sunkuye yake k’amshin turarensa mai dad’ine duk yacika wajen lumshe idonta tayi ba tare da ta d’agoba cikin muryarta mai dad’i tace yaya fahad antashi lafiya? Tunda yazauna kallonta kawai yake batare da ya d’auke idonsaba a kanta yace lafiya, y Ameerah tatashi?
Ta ji haushin yanayin amsar da yabata abinda ma yafi bata haushi ita bai tambayi yarda tatashiba sai lafiyar d’iyarsa yatambaya d’ago kai tayi takallesa saida gabanta yafad’i domin ya yi kyau sosai cikin k’ananun kaya dasauri tamaida kanta tasunkuyar saboda kunyarsa da takeji dakyar tabud’e baki tace lafiya lau.
Salma ce tayi serving d’in kowa nan suka fara breakfast ita dai Amina duk a takure take domin guy d’in duk ya tsareta da idanuwansa duk wani motsi da zatayi akan idonsa, shidai breakfast d’insa yake hankalinsa a kwance,
gajiya tayi da kallon tatashi mummy tace Amina ba dai kin k’oshiba, murmushi tayi tace mummy Allah na k’oshi, fatima tayi karaf tace sis ba fa abinda kika ci, harararta Amina tayi tace wanda naci ke kika ci min?
Dariya su mummy sukayi, mummy tace gaskiya kizauna kik’ara cin ko kad’an ne batayi musuba takoma tazauna ba dan ta so ba, juya spoon d’in kawai take tana yamutsa Irish, wayarsa yajawo yafara dannawa,
Amina jawo wayarta tayi jin alamun message ya shigo mata tana dubawa taga number ce nan tafara karantawa _kisaki jikinki kiyi breakfast inkuma ba hakaba zan miki d’ure agaban su mummy dan naga kamar bakison cin abinci kina wasa da cikinki_
zaro ido tayi dasauri tatura mashi _dan Allah karufa min asiri wlh zan ci_
Murmushi yayi ganin abinda taturo shima reply yamaida mata yace _oya ci mugani_
tana gama karantawa dasauri tad’auki spoon d’in tafara ci, saida yaga ta ci sosai sannan yatashi daman tuni su mummy sun tashi saura su hud’u, batare da ya tanka musuba yawuce yatafi, kallon plate d’insa tayi taga shima bai ci abin kirkiba cikin ranta tace hakanan yamatsamin ashe shima bai ci ba ai shi yafi kamata ayi ma d’ure,
turo baki tayi tatashi suka tatattare kayan suka kai kitchen saida suka gyara wajen fes sannan kowa tanufi d’akinta,
Saman 3 seater da take cikin d’akinta takwanta tajawo wayarta tahau chart kiran wayar fahad ne takatseta daga chart d’in sharewa tayi kamar ba zata d’aukaba saida takusa tsinkewa sannan tayi picking shuru tayi bata tankaba, shima a 6angaren fahad tunda tad’aga wayar shuru yayi yana jiran tafara magana saida sukayi kusan 5 minutes,
Amina takaici duk ya isheta ganin ankirata kuma anyi shuru ank’i magana kashe wayar tayi taja tsoki, tana ajewa wani sabon kiran yashigo picking tayi tak’arayin shuru batayi magana ba saida suka k’ara Kusan minti biyu Amina taga indai tabiyema wannan d’an jin kan toh ba zai fara maganaba daurewa tayi tafara sallama,
Lumshe idonsa yayi jin muryarta yadda tadoki dodon kunnansa amsa mata yayi daga nan shuru yak’ara biyo baya, saida akayi kusan 3 minutes sannan yace ya kike?
Takaici duk yacika Amina dakyar tabud’e baki tace lafiya lau,
ya my daughter? dafatan ta yi breakfast?
Eh ta yi tun d’azun,
Ohk, bata wayar inji lafiyarta,
A gadarance tace ai tana chan d’akin babah mairo,
Toh shikenan, kihad’a min kunun aya kisaka a fridge dan bazan dawo dawuri ba.
Bai jira jin amsar taba yakashe wayarsa, tsoki taja tace mutum sai jin kan tsiya cigaba tayi da chart d’inta saida taga 12pm ta kusa sannan tatashi tanufi kitchen nan ta tadda babah mairo tana girki kama mata tayi ta amsa tayi pepper sannan tahad’a kunun aya mai kwakwa wanda yasha madara ta saka ciikin freezer.
tare suka gama aikin itada babah mairo saida suka gyara komai sannan tatafi d’akinta domin tawatsa ruwa,
Bayan ta yi wanka shiryawa tayi cikin wata gown sky blue ta amsheta sosai simple makeup tayi tafeshe jikinta da turare ganin har k’arfe biyu darabi ta yi yasa cikin hanzari tasaka flat shoes d’inta tanufi parlour domin ta san jiranta ake,
STORY CONTINUES BELOW

kasancewar su mummy basunan zama su Amina sukayi su ukku suka fara cin lunch d’insu kowa yayi shuru, salma ce tace yaya fahad bai dawoba ne?
Fatima tace nima ban ganshiba mayb bai dawoba.
Amina dai bata tankasuba daga nan shuru yabiyo baya suka cigaba da cin abinci.
Bayan sallar la’asar zaune suke a parlour dukansu suna kallo fahad ne yashigo d’akin da sallamarsa, amsa masa sukayi tare da yi mashi sannu da zuwa ita dai Amina T.V tayi ma zuru tanuna kamar batasan shigowarsaba,
kallon fatima yayi yace mummy fa tana d’akinta? Karaf salma tayi tace ta je anguwa, ko inda take bai k’ara kalloba, kallon Amina yayi da taketa kallon t.v yace ke kizo kizuba min abinci, shuru tayi kamar ba da ita yakeba,salma tace bari inje inzuba maka.
no barshi, dake nake Amina,
Fatima ce tace sis yaya fahad yana magana.
Tashi tayi tana sun6uro baki tawuce tanufi dining area binta yayi a baya yaja kujera yazauna jawo kular Amina tayi tafara serving d’insa duk ta bi ta kicin cine fuska, murmushi yayi yace baki iya sannu da zuwaba? Shuru tayi masa, sai chan tace ya hanya dafatan andawo lafiya,
hmm sai da narok’a?
Shuru tayi masa sai chan tace ammah ga su fatima maimakon kasa suyi serving d’inka kuma ina ji salma ta ce zata zuba maka ammah kak’i ni dan katakurani shine kace ni
Murmushi yayi yace shine yasa kike fushi? Toh ai ke matatace ke yakamata kiban abinci.
Harararsa tayi tace mata kuma?
Eh mana ai har yanzu ke matatace har sai nan da wata shidda ko?
Shuru tayi mashi
Yace Ina kunun ayan?
Yana fridge, wucewa tayi tad’auko tazo tazuba mashi bayan ta gama serving d’insa tawuce zata tatafi rik”o hannunta yayi yace kizauna muci, dasauri takai kallonta chan gefensu fatima taga fatima ce kawai take kallon film, salma kuma ta shiga room d’inta,
Numfashi Amina taja tace dan Allah kasakeni kaga kar aganmu,
Kafeta yayi da ido yace Toh sai me dan anganmu ni da matata, kizauna kawai muci, hannu yakai saman cikinta yace da alama baki ci abinciba.
Ture hannunsa tayi daga kan cikinta tace Allah na ci sosai,
Ohk, ina my daughter?
Tana d’aki bacci take, dasauri tawuce tabar wajen takoma wajen fatima suka cigaba da kallonsu.
Murmushi fahad yayi sannan yacigaba da cin abincinsa..
Bayan ya gama bai bi ta kansuba yaficce daga d’akin, kallon Amina fatima tayi tace sis sai kinyi hak’uri da halin yaya fahad haka yake takura mu kema yanzu kinbi layi.
Murmushi Amina tayi tace ai nima yayanane komai yayi mana ai dan yana da iko da mu ne kar kidamu my sis.
Daganan suka cigaba da kallonsu.
Wajen k’arfe goman dare kwance take d’akinta har ta fara bacci wayarta tafara ringing dakyar tabud’e idonta batare da ta duba ba tad’auka cikin muryar bacci tayi sallama, amsa mata fahad yayi yace kikawo min maltina iina d’akina.
Sun6uro baki tayi tashagwa6e fuska kamar yana kallonta tace har fa na fara bacci katasheni.
toh ya kika iya ya za ayi kiyi bacci baki sallami mijinki ba? Please kiyi sauri kikawo min ina jiranki , inkuma ba hakaba yanzu kiganni d’akinki, bai jira Jin amsartaba yakashe wayarsa.
Dasauri tatashi daga kwancen da take dafe kanta tayi tace nashiga ukku k’addarace tahad’ani da wannan bawan Allahn sai takurani yake, safkowa tayi daga saman gadon kallon rigar baccin da take jikinta tayi taga iyakarta gwiwa, hijab tajawo har k’asa tasanya tace tunda ba dad’ewa zanyiba da na kai masa zan dawo ai ba sai nasa wani zaneba,
Fitowa tayi tajawo d’akinta kasancewar Ameerah yau ma tana d’akin babah mairo dan tunda aka yayeta ta fi kwana wajenta, kitchen tanufa tabud”e fridge tad”auko maltina tahad’o da cup sannan tanufi part d’insa, kwankwasa k’ofar tayi, saida tayi kusan 4 minutes har ta gaji sannan fahad yazo yabud’e mata, mik’a masa tayi, k’in kar6a yayi yace kishiga mana,
Kallonsa tayi tace sauri nake bacci nakeji ka amsa sai kashiga da shi,
Wani kallo da yawatsa mata saida ta tsorata dasauri tanufi cikin d’akin har tana turesa,
Maida k’ofar yayi yakulle, sannan yakoma bakin gado yazauna yacigaba da danna laptop d’insa, kusa dashi tazo tace ga shi.
cigaba yayi da dannar laptop d’insa kamar bai ji me taceba.
Ahankali tak’ara cewa gashi.
Ba tare da ya kalletaba yace haka ake ba miji abu? Ni zan zuba da kai na?
Sun6uro baki tayi sannan tabud’e tazuba mashi tamik”a mai.
Kar6a yayi yakur6a sannan ya aje saman bed side.
Tsaye Amina tayi tanaso yabata izini tatafi.
saida yayi kusan 2 minutes sannan yace ki zauna mana kin min tsaye a ka.
Zama Amina tayi nesa dashi kad’an haushine yacikata gashi bata d’auko wayartaba bare tayi chart ko ta rage.
Chan tagaji da zaman ga bacci tana ji kallonsa tayi taga aikin gabansa kawai yake ya ma mance da zamanta, ahankali tace yaya fahad zan tafi.
Shuru yayi yakyaleta,
Harararsa tayi ckin ranta tace mutum sai miskilancin tsiya, k’ara maimaitawa tayi.
A dak’ile yace ban baki iziniba.
Marairaicewa tayi kamar zatayi kuka tace yaya fahad wlh bacci nakeji.
Kiyi shi a nan akwai wanda ya hanaki?
Gabantane yafad’i domin bata mance wahalar da tasha jiyaba…….
Kwallace tacika mata ido tace dan Allah kabarni in…. wani kallo da yayi mata yasa maganar da take tamak’ale a bakinta, bai tankata ba yacigaba da abinda yake,
Hawayene yafara zarya a idonta tana gogewa a haka tafara gyangyad’i ganin baccin yana nema yaci k’arfinta yasa takwanta chan nesa da shi tare da takure jikinta duk a tsorace take, dan ta san ko ta k’ara magana toh a banza zatayi ba zai kulataba.
Sai wajen sha d’aya da rabi na dare sannan fahad yagama abinda yake, kallonta yayi yaga duk ta takure waje d’aya tana ta baccinta, dariya ma abin yaso yabashi, ahankali yasamu yarabata da hijab d’in rungumeta yayi yajawo blanket ya lullu6esu.
Cikin bacci suka jiyo ana knocking d’in k’ofa fahad ne yabud’e ido jin kiran sallah yatabbatar masa da daddyne yazo tadasa, dakyar yace daddy na tashi, cikin dubara ya janye Amina daga jikinsa yagyara mata kwanciya sannan yanufi toilet yad’auro alwallah cikin sauri yacanza kaya yanufi masallaci.
Kulle k’ofar da yayi yasa Amina tafarka dasauri tad’auki hijab d’inta tasaka tafito cikin sand’a tanufi d’akinta, tana shiga tamurza ma k’ofar key takoma saman gadonta ta kwanta.
Wajen k’arfe takwas tafarka toilet tashiga tayo brush sannan tafito tanufi kitchen doya tafere ta dafa sannan tasoya da kwai, kunun shinkafa tahad’a masu Wanda yasha madara,
ko da babah mairo tazo Amina hanata tayi kan dole babah mairo tabar mata aikin takoma d’akinta.
Had’a kayan tayi waje guda tad’ibar ma babah mairo nata takai mata d’aki, ganin Ameerah ta farka yasa tad’aukota tatafi d’aki da ita, wanka tayi ma Ameerah saida tashirya ta sannan itama tashiga wanka.
Ko da tafito ta tadda Ameerah ta bar d’akin bata damuba domin ta san halinta ba ta son zama waje d’aya, shiryawa tayi cikin shadda doguwar riga orange colour.
Duba clock tayi ganin goma har tayi yasa dasauri tafito tanufi kitchen takwaso breakfast d’in parlour tashiga da sallamarta, nan ta tadda su mummy su ma suna saukowa daga saman step, dining tahango su fatima zaune kowace da waya a hannunta tana dannawa da alama chart suke, dasauri fatima tazo takama mata suka kai saman table d’in,
Fahad ne yashigo d’akin d’auke da Ameerah tana ta zuba masa gwarancinta.
Cikin girmamawa suka gaishe da iyayen nasu da yaya fahad, daga nan suka d’unguma suka nufi dining, salma ganin fahad ya zauna cikin sauri tazauna opposite d’insa,
Haushi Amina taji ganin yadda salma take shigema fahad, d’aure fuska tayi tajawo kujerar gefensa tazauna itakuma fatima tazauna gefen salma.
Shidai fahad yana rik’e da d’iyarsa baima san dramar da akeba, Amina ce tatashi tafara serving d’insu mummy tace yau wane kalan better zamu ci? she hung her head murmushi tayi tacigaba da zuba masu, bayan ta gama takalli fahad tace kakawota inbata sai kayi breakfast d’in,
Batare da ya kalleta yace no kibarta kawai zanyi feeding d’inta.
Fatima ce tayi dariya tace yaya fahad kana ji da Ameerah gaskiya dayawa ni har ‘yar kama naga kunayi dan dai ita yarinyace, mummy tace aikam dai suna kama dandai my son ya fi kishiyata hanci da kyau, dariya daddy yayi yace kodai kina jealous ne? Gaba d’ansu suka sa dariya ammah banda Amina da gabanta yake faman fad’uwa su mummy basu kawo komai a ransuba suka cigaba da cin abincinsu.
STORY CONTINUES BELOW

Zama Amina tayi tafara cin nata, wurin yayi shuru ba ka jin muryar kowa sai ta Ameerah da take ta gwarancinta, Amina satar kallonsa take yadda yake feeding d’in Ameerah ammah shi ba wani ci sosai yake ba kunun gyad’ar kawai yake sha, Ameerah tana ji ta k’oshi tazame daga jikin fahad taficce dagudu,
Fakar idonsu mummy yayi yaduk’o saitin kunnanta yace ba laifi kunun ya yi dad’i, tsayawa tayi da taunar doyar da take. Murmushi kawai tayi.
Salmace talura da su takaici duk yacikata haushin Amina yakamata, kasa cigaba da jin abincin tayi mik’ewa tayi kallonta sukayi mummy tace salma ya dai, murmushi salma tayi tace mummy na k’oshine,
Toh shikenan ai ke ban jin ki dan nasan inda baki k’oshiba da ba zaki tashiba dan baki wasa da cikinki.
Murmushi tayi batare da ta tankaba tawuce tanufi d’akinta, saman gadonta tafad’a tafashe da kuka me yaya fahad yake nufi ne kar dai ace son wacchan bagidajiyar yarinyar yake, girgiza kai tayi tace kai no it can’t be possible, ya za ayi yaso bazawara duk ajinsa da kyaunsa, ko dai wata maganar ce yafad’a mata nice dai idona yanuna min ba daidai ba, tashi zaune tayi tace dole insa ido akansu domin ingano gaskiyar al’amari.
Su mummy suka fara tashi daddy yakalli fahad yace my son if u finished i want talk with you, fahad yace ohk daddy.
Amina tana shirin tashi fahad yakai hannu yarik’o hannunta ya girgiza mata kai alamun a’a, komawa tayi tazauna janye hannunta taso tayi ammah ya k’i sakinta, k’ara k’asa tayi da hannun dan kar Fatima tagansu kallonsa tayi ta marairaice fuska, k’in sakinta yayi yacigaba da shan kununsa,
Fatima ce aka kira waya dasauri tatashi tayi picking d’in call d’in tanufi room d’inta.
kallonsa Amina tayi she said lamely, please kakyaleni intafi na fa k’oshi, batare da ya kalletaba yace naga bakici sosai ba shine zanyi feeding d’inki, zaro ido Amina tayi tace karufa min asiri wlh na ci sosai,
Bangani ba ai, idanuwanta suka cika da kwallah tace wlh na ci kuma na k’oshi, d’aga kafad’a yayi yace shikenan ai cikinki, sakinta yayi yatashi, ahankali tace saikace wani ya ce cikinsa, juyowa yayi yace mi kikace, girgiza kai tayi tace babu abinda nace,
Bai dai yarda da amsar da tabashiba kawai wucewa yayi yatafi kiran da daddy yake mashi.
Tashi Amina tayi tatattara kayan takai kitchen sannan tawuce d’akinta.
Yau ma da daddare fahad d’akin Amina yazo lokacin har ta kulle d’akinta wayarta yakira tazo tabud’e mashi lokacin ma har ta fara bacci haka tataso tana sun6uro baki tana gunguni tazo tabud’e cikin sauri da tsoron kar wani yagani, ko da yashigo Ameerah ce yahango kwance tsakiyar gadon kusa da ita yaje yakwanta, tsaye Amina tayi tana kallonsa, shima kallonta yake yace kizo ki kwanta mana kin tsareni da ido,
‘Dauke kai tayi daga kallonsa tace ammah yaya fahad hakan bai daceba, kwallace tacika mata ido tace baka tsoro wata ran aganmu? Ya kakeso inyi idan su mummy suka gano hakan? Dan Allah karufa min asiri kadaina zuwa nan tafara sharar hawaye.
Shidai fahad kallonta yake yana mamakin yadda take da saurin kuka haka, bai ce mata komai ba yajuya yayi kwanciyarsa,
Haushine yakama Amina ganin yadda yashareta ko matsayin samun amsa daga garesa bata da shi, chan k’arshen gadon takoma takwanta itama tajuya kowa yakalli gefensa,
dasafe ko da Amina tafarka bata ganshi ba, ta6e baki tayi tajuya tacigaba da baccinta.
Haka fahad yacigaba da kwana d’akin Amina ammah kowa yana gefe d’aya a haka suke bacci yanzu Amina ta fara sakin jikinta da shi ganin bai nuna yana son wani abu daga gareta.
Daddy asibiti yasa aka fara gina ma fahad ya saki kud’i sosai wajen ginin, materials d’in aikin duk a waje akayo order d’insu.
Soyayya ake a 6oye tsakanin Fatima da yusuf abokin fahad, babu wanda yasani a gdn sai salma da Amina ne kawai suka san suna soyayyar,
STORY CONTINUES BELOW

Duk lokacin da yusuf zai mata magana tabashi izini ammah sai tai tayi mashi kwana-kwana ganin haka yasa ysuf yayi ma fahad magana akan Fatima dan shi har ga Allah aurenta yakeson yayi.
Fahad ya ji dad’i sosai dan ya yarda da halin abokin nasa, shi yayi mashi jagora wajen daddy aka bashi izinin nemanta.
Yau fahad tunda yaje gano ginin da ke dakyar yamaido kansa gida saboda wani irin ciwon kai da zazza6i da yakeji ko da yayi parking d’in motar bai tsaya rufewa ba yafito yanufi d’akinsa, kwanciya yayi yalullu6e jikinsa da blanket saboda wani irin sanyi da yakeji nan da nan zazza6i ya ida rufesa.
Mummy ce taji shurun ya yi yawa dan ko lunch bai fito yaci ba, ganin haka yasa tanufi d’akinsa da kanta, tana shiga tahango sa k’udindine cikin bargo yana rawar d’ari dasauri ta isa inda yake ta yaye bargon hankalinta ne yatashi ganin cikin d’an k’an-k’anin lokaci ya canza idanuwansa a rufe, rik’osa tayi taji jikinsa da zafi cikin tashin hankali tace my son zazza6i kake? Dakyar yanuna mata kansa dan bai iya magana nan mummy ta ida rikicewa sannu tashiga yi masa, wayarsa ce tajawo tayi dialing d’in number d”in daddy bugu biyu yad’auka ko sallama bata yi ba tace Alhaji kazo fahad baida lafiya, daddy yace subhanallah me yake damunsa,
Zazza6i da ciwon kai
Toh ganinan zuwa bari inkira family doctor.
Daddy kusan tare suka iso shi da Dr zubairu, nan yadubasa yatabbatar masu da fever ce take damunsa magunguna da injection yarubuta masa ita dai mummy tana zaune gefen d’anta,
Driver daddy yaba takardar maganin yaje yasiyo, mummy ce takira Fatima taje tahad’o masa tea mai kauri tare da salma sukazo suka dubasa,
Dakyar yad’ansha tea d’in sannan Dr zubairu yayi masa allura aka bashi magani yasha nan da nan bacci yad’aukesa.
Ita dai Amina batasan wainar da ake toya wa ba tana d’akinta ita kad’ai ga Ameerah tana gidan Aunty khairat d’azun da babah mairo taje tabarota wajensu jawahir,
Sai da suka had’u wajen yin dinner ne tasamu labarin rashin lafiyarsa, hankalinta tashi yayi kasa cin abun kirki tayi.
Ko da takoma d’akinta kasa bacci tayi juyi kawai take saman gadonta ji take kamar taje taganosa ammah ina she can’t do that, juyi kawai take saman gadon inda yake kwanciya takoma takwanta tare da jawo pillow tarungume ahaka har tayi bacci.
Da asuba ko da tayi sallah bata koma bacci ba kitchen tashiga tahad’a masu breakfast tadawo d’akinta tayi wanka tashirya, tana so taje taganosa ammah ta kasa dan tana jin nauyin su mummy, kusan sau ukku tana kiran number d’insa ammah ba ayi picking,
Salma ce takai masa breakfast d’insa mummy ta taimaka mashi yad’an ci yasha magani ganin jikinsa ya d’anyi k’arfi yasa mummy tahad’a mashi ruwan wanka yashiga yayi tafitar masa da kayan shan iska,
Ko da yashirya saman gadonsa yakoma yakwanta takaici duk ya cikasa ganin kowa yana zuwa yayi mashi sannu da jiki ammah banda Amina cikin ransa yace wannan wace irin tsanace take min haka runtse idonsa yayi jin zuciyarsa tana bugawa.
Salma a d’akinsa ta tare ita da fatima duk wani abu da yake buk’ata su suke yi masa,
Lunch ma Amina dakanta tashirya masu dan tana so taga halin da fahad yake, har ta had’a nashi zata je takai salma tazo takar6a tace tabarshi ita zata kai mashi, Amina ta ji haushin hakan ammah ba yarda ta iya, fatima ce tace sis yakamata kema kizo muje kiyi masa ya jiki.
Dad’i Amina taji tace toh tabisu, salma bata ji dad’iba dan ba haka taso ba,
Ko da suka shiga d’akin yana kwance yakallonsu yayi one by one ahankali yasafke idonsa akan Amina gani yayi itama duk ta fad’a kamar wadda tayi ciwo, itama Amina kallonsa take tana jin wani abu a ranta tausayinsa yakamata ganin yadda duk yafita hayyacinsa da ka gansa ka san ya ji jiki, dakyar rabud’e baki kamar zatayi kuka tace yaya fahad sannu ya jikin,
Lumshe idonsa yayi dakyar yace dasauki, jikin Amina duk yayi sanyi coz she knew from his tone dat he was angry, itama duk sai taji ba dad’i bata kyautaba, kwallace tacika mata ido dasauri taficce daga d’akin,
Salma tana lura da su takaici da haushin Amina yak’ara kamata dan taga abinda take zargi shi yake shirin faruwa.
Ko da takoma d’akinta saman gadonta tafad’a tarushe da kuka mai ban tausayi tana jin haushin kanta dan gani take fushi yake da ita, saida taci kuka tagaji dakanta ta lallashi kanta tayi shuru,
Su Fatima suka taimaka mashi yad’anci abincin kad’an,
Bayan sallar isha’i bayan ya gama sallarsa saman gadonsa yakoma yakwanta sai lokacin yad’auko wayarsa tun jiya rabonsa da ita 10 missed call yagani kasancewar wayar silent take, number d’in Amina yayi dialing, bugu d’aya tad’auka tace hello yaya fahad, lumshe idonsa yayi jin yadda muryarta tabugi dodon kunnansa, saida tak’ara cewa hello, dakyar yabud’e bakinsa yace kihad’o min coffee kikawo min d’aki, muryarta tana rawa tace toh.
Kitchen tashiga tahad’a mashi coffee sannan tafito tanufi hanyar part d’insa, had’ewa sukayi da salma itama ta fito zata dubosa kallon Amina tayi a wulak’ance tace ina zakije? Murmushi Amina tayi tace yaya fahad ne zan kai ma coffee, harararta salma tayi tace toh uwar shishigi shi yace kikai masa? Jikin Amina yayi sanyi tace eh.
Mik’o hannu salma tayi tace kawo ai nima d’akin nanufa sai inkai masa,
Bata Amina tayi tajuya takoma d’akinta cikin jin haushi dan ta so tak’ara gano fahad.
Bud’e k’ofar d”akin d’s akayi yasa yabud’e idonsa da suke lumshe he tot Amina ce ammah sai yaga akasin haka, juyar da kansa yayi gefe, salma tana murmurshi takashe muryarta tace sannu yaya fahad ga coffeen, haushin Amina yakamashi ganin ya sata maimakon takawo mashi shine zata ba salma takawo,
Cikin shagwa6a salma tace please yaya fahad kakar6a kasha tashi yayi zaune ya kar6a ya aje saman side bed kallonta yayi yace ba Amina nace ta had’o min ba?
Haushi yakama salma tace ita ai tahad’a maka, jin haka yasa yad’auka yafara sha itakuma tana tsaye tana kallonsa saida yasha kusan rabin cup sannan yamik’a mata, murmushi tayi tace yaya fahad sai dasafe, batare da ya kalletaba yace Allah yakaimu har ta juya zata tafi yace am idan kinje kice ma Amina takawo min yoghurt, murmushi salma tayi tace bari inje ind’auko maka, harararta yayi yace ita nace kice takawo min,
Wucewa salma tayi fuuu tanufi d’akin Amina tana jin tsanarta a ranta ko sallama batayiba tafad’a, Amina da take kwance tatashi zaune, hararta Salma tayi tace kije kikai masa yoghurt yace, Amina toh tace tare da mik’ewa tsaye, kallonta salma tayi tace inma kina tunanin gani abu game da yaya fahad toh kidaina domin ya fi k’arfin fi bata jira jin abinda Amina zata ce ba taficce daga d’akin ranta a 6ace.
Murmushin takaici Amina tayi ammah bata ji haushin maganar da salma tafad’a mataba dan itama kanta ta san fahad ya fi k’arfinta k’addara ce kawai tasa sonsa tashiga ranta.
Wucewa tayi taje tad’auko yoghurt d’in tanufi d’akinsa lokacin goma da rabi na dare, tura k’ofar tayi tashiga tana jin sanyi a ranta, kwance ta taddasa kansa yana kallon silin, k’amshin turarenta da yaji yasa yalumshe ido, ahankali ta tako inda yake tana jin sonsa yana k’aruwa a ranta………..
Gefen gadon Amina tazauna ahankali tace yaya fahad ya jikin batare da ya bud’e idonsaba yace dasauk’i,
Allah yak’ara sauk’i
Daga nan shuru yabiyo baya na d’an wani lokaci, Chan dai Amina tace yaya fahad ga yogurt d’in katashi kasha, dakyar yabud’e idonsa yasafkesu akan fuskarta, gani yayi ta yi wata fayau da ita, hannu yakai yashafi fuskarta lumshe ido Amina tayi, muryarsa chan k’asa kamar mai rad’a yace me yasameki bakida lafiya ne? Kwallah ce tacika mata ido girgiza mashi kai tayi alamun a’ah, dogon numfashi yaja ahankali yakai hannu yarabata da hijab d’in da take jikinta,
Sanye take cikin nyt gown doguwar riga pink colour, hannunsa yakai saman k’ashin wuyanta yashafa yace baby duk kin rame sai kace kina jiyya,
Cikin ranta tace jiyyar sonka take d’awainiya da ni,
Shafa jikinta yashiga yi ahankali har hannunsa yakai cikin rigarta, ita dai Amina batayi gigin hanasa ba,
Kwantar da ita yayi gefensa yashiga romance d’inta yashiga yi cikin salon soyayyar da shima baisan zai iya hakanba nan da nan yarikita Amina batasan lokacin da tafara maida mashiba cikin dabara yasamu yarabata da rigar jikinta nan hankalin Amina yafara tashi dan ta ga alama yau kamar ba zai raga mata ba nan ido yaraina fata magiya tashiga yi mashi ammah bai san ma tana yi ba…….
Amina kuka takeyi kamar ranta zai fita ita takaicinta fahad ya ci galaba akanta ya yi sex da ita a cikin gidan iyayensa a matsayinta na *YAR RIK’O* a wanchan karan kuma a gidan iyayenta lallai *YARAN ZAMANI* sai a slow, amatsayinta na *’YA MACE* Taso ace ta ja ajinta a garesa har sai yanuna yana sonta kafin yak’ara Kwanciya da ita ammah ina k’addara ta riga fata ni kuma nawa *SALON K’ADDARAR* kenan, ko kuma ni najama kaina da na amince nazo d’akinsa gashinan ya nuna mani halin *’YAN NIGER😜* *(DOMIN ‘YAN NIGER)*
Babbban abinda yafi bata takaici da batasan ko yana sontaba ko kuma baisonta k’ilama jikinta yake so ammah yanzu gashinan ya sameta cikin sauk’i ita ta san sonsane yaja mata har ta bashi had’inkai daman *DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA* shi ruwa kan doka, cigaba tayi da kukanta kamar wadda aka aiko ma da sak’on mutuwa har muryarta tafara dashewa.
fahad kuma yana gefenta yana ta maida numfashi saida yayi kusan 5 minutes sannan
yasamu yatattaro nutsuwarsa jawota yayi jikinsa yarungume yana d’an bubbuga bayanta alamun lallashi dakyar yabud’e baki yace nagode sosai Amina Allah yasaki aljannah firdausi kin sani farin cikin da ba wanda yata6a sani irinsa nagode nagode bansan kalar godiyan da zan mikiba,
Amina k’ara fashewa da kuka tayi takaici duk ya cikata haushin fahad ne taji domin gani take kamar jikinta daman yakeso,
Fahad k’ara matseta yayi a jikinsa kamar wani ya ce zai k’wace masa ita cikin muryarsa da tadashe yace kiyi hak’uri nima na san ban kyauta miki ba wlh *BA LAIFINA BANE* laifin zuciyata ne inaso kisan wani sirri da ba wanda nata6a fad’a mawa Amina ina sonki kece macen da nafara so a rayuwata , Amina saida gabanta yafad’i lumshe ido tayi hawaye suna cigaba da kwaranya daga idonta fahad yacigaba da cewa na san zakiyi mamakin jin hakan daga gareni inaso kisan cewa a kullum kece *MAFARKI NA* burina *KIYARDA DA NI* kamar yarda *NI DA ZUCIYATA* muka yarda dake kibani dama innuna miki soyayya fiye da yarda *BARKIN’DO* yanuna ma hunayya, ina so kikasance *TUDUN DAFAWA* ta arayuwar mu zan nuna miki gatan da ko *GIMBIYA LINDA* bata samesaba bare ma azo kan *MUHIBBAT* ko *JALILA* Amina soyayyata da ke *HA’DIN ALLAH NE* kamar yarda *K’ADDARA CE* takaini garinku har nahad’u da ke, numfashi fahad yaja sannan yacigaba da cewa kidaina tunanin wani zai iya rabamu soyayyata da ke *DAGA ALLAH NE* fahad surutu kawai yakeyi sai kace wanda yazauce, Amina dai babu abinda ta fahimta baccine yayi awon gaba da ita saboda rabon da tasamu baccin kirki kusan kwana biyu, saida taja numfashi sannan yafahimci bacci take, murmushi yayi yagyara mata kwanciyarta sannan shima ya lumshe idonsa yana jin wani nishad’i aransa ahaka bacci yayi awon gaba da shi,
STORY CONTINUES BELOW

Wajen k’arfe hud’u Amina tafarka dakyar tabud’e idanuwanta da suka kumbura saboda tsananin kukan da tasha jinta tayi jikin mutum ahankali abinda yafaru jiya yafad’o mata a rai,
‘Dago kai tayi taga fahad sai baccinsa yake hankali kwance, ahankali tazame jikinta daga nasa, kayanta tad’auka tasanya lalla6awa tayi tabud’e k’ofar ahankali taficce cikin sand’a tatafi d’akinta.
Wanka tashiga tayi saida tagasa jikinta sosai bayan ta fito shiryawa tayi, raka’atanil fajr tayi tazauna tana lazimi har aka tayar da sallah sannan tatashi tagabatar da ita bayan ta gama saman gadonta takoma takwanta maganganun fahad suka dinga fad’o mata a rai wani irin sanyi taji a ranta da tatuno wai fahad ne yafurta mata kalmar so har da hawayensa, murmushi tayi sonsane taji yana k’aruwa a cikin zuciyarta kamar zai fito waje lumshe idonta tayi cikin ranta tace lallai na yarda *CIKI DA GASKIYA wuk’a bata huda sa* a cikin idon fahad ta hango soyayya zallah murmushi tayi tace ko da yakasance d’an saurayi ta san ko *MATAR DATTIJO* bata kaita more mijiba😜, tana tunowa da salma saida gabanta yafad’i nan da nan novel d’in *NI DA MIJIN YAYATA* yafad’o mata a rai, numfashi taja ahankali tace fahad d’ina mutumin kirkine, saidai kash na san na yaudari kaina da na amince masa amatsayina na YAR RIK’O a gidansu kuma ga ‘yar uwarsa tana sonsa, dawane ido zan kalli iyayensa idan suka gano gaskiya? Zuciyarta ce taji ta tunkushe Kuka takeyi sosai har saida kanta yafara ciwo sannan tayi shuru ahaka bacci yayi awon gaba da ita.
A 6angaren fahad baccinsa yake hankalinsa kwance saida daddy yakwankwasa masa k’ofa da asuba sannan yafarka lo da yaga ba Amina, bai damuba yatashi yashiga wanka,
cikin sauri yashirya yatafi masallaci raka’ar k’arshe kawai yasamu, ko da yagama sallah yau bai tsaya gari yafara wayewaba yadawo gida idanuwansa duk sunyi nauyi, kwanciya yayi yahau rama baccin da ake binsa,
Amina sai wajen k’arfe goma tafarka kantane taji yana sarawa sosai dafe kan tayi duk yadda taso ta tashi ammah ta kasa har wajen 11 tana kwance ga wata irin yunwa da takeji, Fatima ce tashigo d’akin domin taga ko lafiya bata fito akayi breakfast ba kuma wayanta a kashe,
Dasauri fatima ta iso inda take saman gadon tahau cikin rud’ewa takalli Amina tace sis me yake damunki? Bakida lafiya ne? Lokaci guda fatima tajera mata tambayoyin,
Murmushin k’arfin hali Amina tayi dakyar tabud’e baki tace bakomai sis kawai d’an ciwon kai ne,
Subhanallah sannu sis bari inje inhad’o miki breakfast kiyi sai kisha magani,
Fita fatima tayi da sauri tanufi parlour kallonta su mummy sukayi sukace lafiya?
Fatima tace mummy wlh Amina ce batada lafiya kuma daga gani tana jin jiki.
Fahad da yake zaune yake ta faman juya spoon a cikin cup ya kasa sa saboda rashin ganin Amina ta fito jin abinda fatima tace yasa shi lumshe idonsa yana jin wani iri a ransa.
Muryar mummy ce yatsinkayo tana cewa Subhanallah Allah yabata lafiya yi sauri kihad’a mata tea mai kauri kikawo mata bari inje induba ta,
da sauri mummy tafita daga d’akin tanufi d’akin Amina, fatima ma tana gama had’a mata tea d’in tawuce tabi bayan mummy, wajen yakoma saura su biyu, salma tana lura da fahad tun da akace Amina ba tada lafiya yabi yacanza, tsanar Amina tak’ara ji a ranta daidai lokacin fatima tashigo d’akin tace yaya fahad mummy ta ce kazo kadubata karubuta mata magani, baice komai ba yatashi yabi bayanta. Takaici duk ya ida kama salma kasa cigaba da breakfast d’in tayi tatashi tashige room d’inta.
Ko da yashiga d’akin hango tayi a zaune tsakiyar gadon hannunta dafe a kanta mummy tana gefenta tana bata tea tana yi mata sannu, ganinta a wannan halin yasa yaji babu dad’i a ransa dan shine silar komai, muryar mummy yajiyo tana cewa k’araso mana my son ka yi tsaye.
Ahankali yataka ya isa bakin gadon kallonta yayi yace sannu ya jikin? Idanuwanta suna lumshe batare da ta bud’eba tace dasauk’i,
Me yake damunki ne?
Haushine yakamata cikin ranta tace kafi kowa sanin abinda yake damuna, muryar Mummy ce tajiyo tace kifad’i mashi abinda yake damunki dota, dakyar tace ciwon kai ne kawai, babu kuma abinda yake damunki?
Eh.
Kallon mummy yayi yace bari inje insamo mata magani, mummy tace toh my son please kayi sauri.
Bai fi 15 minutes da fitaba yadawo hannunsa d’auke da leda a parlour yatadda su mummy, kallonsa mummy tayi tace har ka dawo?
Yace eh mummy,
Toh kaje kayi mata bayanin yadda zata sha maganin,
Toh yace sannan yawuce yanufi d’akinta,
Kwance yahangota tsakiyar gadon ahankali ya isa yahau gadon kusa da ita yazauna duk tausayinta yak’ara kamashi cikin muryarsa mai sanyi yace sannu Amina kitashi kisha maganin,
Shuru tayi mashi kamar bata ji saba, murmushi yayi dan yasan fushi take da shi, yace kiyi hak’uri na amshi laifina ba zan k’araba kitashi kisha maganin ko kinsamu relief d’in ciwon
Dak’yar Amina tabud’e baki tace ba zan sha ba kabarni inmutu mana ina ruwanka,
Maganarta ta so tabashi dariya rik’ota yayi yace please my princess kitashi kisha, fizgewa Amina tayi tafashe da kuka tace yaya fahad karabu da ni miye ruwanka da ni, tunda ka samu abinda kake so ai sai ka kyaleni,
Kallonta yayi cikin mamaki yace Amina na ta6a cewa ina son jikinki ni tsakani ga Allah nake son ki kuma na fad”a miki duk wani sirri da yake cikin zuciyata ? Harararsa tayi tace kar kayaudari kanka fahad ni nasan ba sona kakeba jikina ne kawai kake so ko baka ceba ai ga alama nan…….
Kallonta fahad yayi yace Amina kidaina cewa haka kibani dama innuna miki kalar k’aunar da nake miki zannuna miki tsantsan so wlh ke ta dabance a cikin zuciyata fiye da yadda basma take a cikin zuciyar *BASSAM*
Hawayene suka cigaba da zarya a idanun Amina, kasa ce masa komai tayi
Ganin haka yasa fahad yacigaba da cewa Amina kema na san kina sona .
Gaban Amina saida yafad’i dasauri tad’ago kai takallesa cikin mamaki tace so kuma? Dariya yak’e tayi tace yaya fahad kenan ko d’aya kar kayi tunanin ina sonka ko da sau d’aya ban ta6a jin sonka a cikin raina ba,
Shima fahad d’in kallonta yake cikin mamaki nan da nan idanuwansa suka kad’a sukayi jawur runtse idonsa yayi jin wani abu ya tokaresa masa mak’ogwaro ahankali yabud’e idonsa yace Amina kar ki yaudari kan ki na san kina sona dan idanuwanki tuni suka bayyanar da sirrin da yake 6oye cikin ranki meyasa kikeso kiyi min k’arya? Meyasa bazaki ba zuciyoyinmu dama ba susamu sassafcin abinda sukeso ba?
Fashewa Amina tayi da kuka tabbas ta san fahad gaskiya yafad’a ammah ba ta jin zata bashi wannan damar dan ita burinta tasamu wannan *AUREN SIRRIN* yawarware batare da wata matsala ba, Cikin d’aga murya tace fahad ko d’aya kar ka k’ara tunanin ina sonka dan yaudarar kanka kake dan ni zuciyata tuni na bayar da ita ga wani na daban,
Ba fahad ba hatta ita kanta Amina da tayi maganar saida gabanta yafad’i ta tsorata sosai da ganin yadda hankalin fahad yak’ara tashi, kin ba wani na daban fa kikace? dariyar yak’e yayi wadda tafi kuka ciwo cikin d’aga murya yace idan har da gaske kike baki sona toh kikalli cikin k’wayar idona kifad’a min baki sona, kasa kallonsa tayi tace fahad na fad’a maka bana sonka dan Allah kafita kaban waje, rik’e fuskarta yayi da hannu biyu dasauri Amina ta rintse idonta, yace nace kikalleni kice baki sona, janye fuskarta tayi gefe d’aya, cikin d’aga murya yace kifad’a mana!! K’ara rintse idonta tayi yace kibud’e idonki nace kikalli cikin idona Amina kifad’a min idan har da gaske kike,
k’ara fashewa tayi da kuka tafizge kanta takoma chan k’arshen gado tad’ago kai takallesa suka had’a ido nan zuciyoyinsu suka dinga bugawa a lokaci guda tace fahad kafita daga rayuwata kakyaleni bana son… kasa k’arasa fad’a tayi nan ta kife kanta tana mai cigaba da kuka,
Murmushi yayi wanda yafi kuka ciwo yace kin gani ko Amina na fad’a miki kina so na ammah na yi miki alk’awali duk ranar da kika kalli cikin idona kikace baki sona toh zan rabu da ke ko da hakan yana nufin zan rasa rayuwata kin san *KYAN ALK’AWALI* acikasa toh nikuma zan cika miki Wannan alk’awalin da nad’aukar miki, domin da ni da ke duk munsan matsayin Alk’awali a addininmu kuma ko da ba garinmu d’ayaba bamuda *BANBANCIN AL’ADU* ‘Daga mashi hannu Amina tayi tare da d’aura fuska tace please let me stay in peace don’t give me more worries
Takaici yacika fahad yad’anyi murmushi yace ohk na barki lafiya, tashi yayi yana jin zuciyarsa ba dad’i yaficce daga d’akin ya yi sa’a ba kowa wajen direct d’akinsa yanufa yana shiga yamaida d’akin yarufe saman gadonsa yafad’a lumshe idonsa yayi tare da jin takaicin maganganun da Amina tafad’a mashi,
STORY CONTINUES BELOW

Cikin ransa yace tabbas ko da zan rasa rayuwata nikuma sai na rabu da ke a duk lokacin da kika fad’a min Amina, dakyar yatashi yashiga toilet yasakar ma kansa shower ko zai samu sauk’in abinda yake damunsa saida yayi kusan minti goma sannan yafito yashirya yad’auki key d’in motarsa yaficce yabar gidan domin yasamu sassafcin abinda yake damunsa.
Ko da yafita Amina sake fashewa tayi da wani sabon kukan mai ban tausayi tana jin son fahad yana k’aruwa a cikin zuciyarta ammah ba yadda ta iya dan gani take ko da ace zata mutu ba zata tona mashi *SIRRIN da YAKE RANTA* ba dan tana gani ba ita tadace da fahad ba ‘yar uwarsa ce tadace ta shi ahankali tace fahad *KAINE ZA’BINA* ammah kayi hak’uri ba yadda zanyi dole inbarka domin warware wannan *SARK’AK’K’IYA* r saida taci kuka mai isarta sannan tatashi dakyar tajawo ledar maganin tare da ruwa tasha sannan takoma takwanta tana ta juyi saman gadon har bacci yasaceta.
Sai gab da azahar sannan tatashi dakyar ammah ciwon kan ya safka wanka tayi tad’auro alwallah bayan ta shirya tagabatar da sallah, babah mairo dakanta tazo takawo mata abinci saida tatsareta sannan tad’anci tak’ara shan magani.
Mummy da fatima ma tun tana bacci suke ta zarya d’akinta dan dubata, bayan ta gama cin abincin suka dawo suka k’ara yi mata ya jiki.
Fahad ko tunda yafita daga gidan gidansu yusuf sukaje suka sha hira bayan sunyi sallah sunci abinci sai suka kama hanyar asibitin fahad da ake cikin aikin ginawa.
Salma tunda tashiga d’akinta saman gadonta tafad’a saida taci kuka mai isarta sannan tafara tunanin mafita, shawarar da ta yankece taji ta kwanta mata a rai, tashi tayi tanufi d’akin fatima ko da tashiga tsakiyar gadonta tahangota a kwance tana ta waya da yusuf bakin gadon taje tazauna tana kallonta cike da sha’awar yadda suke soyayyarsu ji tayi ina ma ace itace da yaya fahad suke haka, ta6ota fatima tayi tace my blood ina ta magana ammah sai tunani kike, kallonta Salma tayi tace kin gama wayar ne my blood? Hararar wasa fatima tayi mata tace tun d’azun ai naga tunani kawai kike,
Murmushi Salma tayi tace wlh soyayyarki da yaya yusuf tana burgeni, dariya fatima tayi tace toh ai kece my blood kin k’i kasamo mana suruki kin tsaya ruwan ido duk masoyanki ammah kin kasa za6o mana d’aya ni da zaki ban za6i da na za6ar maki Faruk abokin yaya fahad wlh yana sonki sosai kece dai kike mai wulak’anci.
Murmushi Salma tayi hawaye suka cika mata ido tace fatima ba zaki gane bane wlh na yi zurfi wajen son wani ammah shi ya nuna man bai ma san ina yi ba.
Kallonta fatima tayi cikin mamaki tace wanene shi? My blood toh kifito fili kifad’a mashi na san zai soki tunda kina da kyau sosai.
Salma tace a’a ba zan iya ba my bood..
fatima tace toh ni kifad’a min kowanene zan je insamesa infahimtar da shi.
Murmushi Salma tayi tace ba zaki iyaba fatima, cikin mamaki fatima takalleta tace saboda mi kika ce haka? Please kifito fili kifad’a min komai ni zan taimaka miki,
K’wallace tacika ma Salma idanuwa tace fatima ba kowa bane nakeso sai yaya fahad, fatima kasa motsi tayi saboda mamakin abinda Salma tafad’a,
Ganin haka yasa Salma tayi Murmushi tace kina mamaki ko? Wlh nima kaina ban san wace kalar K’addara bace take shirin faruwa da ni dan na yi zurfi sosai wajen sonsa.
Dakyar fatima tahad’e miyau dan gani take yaya fahad indai bai ra’ayin abu babu wanda ya isa yasanya shi kuma gashi iyayensu basa da burin yi ma ‘ya’yansu auren dole, lallai ta rasa wace *K’ADDARA CE* tasa Salma tafad’a *TARKON SO* n yaya fahad, kuma a ganinta ko sun fad’a ma mummy dakyar ta amince indai yaya fahad ba yaso ba zata ta6a yi masa doleba domin tsakanin *UWA DA ‘DA* sai Allah.
ta6ota Salma tayi tace sis kinyi shuru please kiban shawarar yadda zanyi ko da na san yaya fahad ya wuce ajina ammah ina so in jaraba sa’ata.
Numfashi fatima taja tace my blood nima mafita nakeso insamo yadda zamu bi abun cikin ruwan sanyi dan nima zan ji dad’i kikasance matar yayana burina dai Allah yasa yaya fahad baida wadda suke soyayya,
Kallonta salma tayi tace ko yana da ita ba zan damuba Indai zai ban dama nima in nuna mashi kalar son da nake mashi.
Eh kuma sis maganarki gaskiya ce toh me zai hana kije kisamesa kuyi maganar?
Murmushi Salma tayi tace na ga kunfi shiri da ke kika fara samunsa kika fad’a masa, you hv to help me,
Zaro ido fatima tayi tace wane ni? Dan Allah kirufa min asiri idan ba so kike yadaka ni ba a cikin gidan nan, yauwa dabara tafad’o min ga shawara.
Cikin zak’uwa fatima tace wace kalar shawarace my sis?
Yauwa musamu lokaci muje gidan Aunty khairat sai mufad’a mata ita sai tayi mashi magana da kanta.
Cikin jin dad’i Salma tace wow sis wlh brain d’inki tana ja dan kin iya kawo gud idea, toh yanzu yaushe zamuje?
Fatima tace saidai upper week idan ta dawo dan na ji d’azun suna waya da mummy tana cewa yaya fahad yaje yad’auko Ameerah dan gobe zasu tafi bauchi saboda bikkin k’anwar mijinta da za ayi next week, kinga da ta dawo sai muje kuma kinga on Monday d’innan zamu koma school da mun bi ta munje bikkin ammah yanzu ba damar zuwa.
Dogon numfashi salma taja tace toh Allah yakaimu, gaskiya nima naso ace munje bikkin.
Fahad bai dawo gidan ba sai bayan sallar magrib sannan yadawo sa6e da Ameerah tana ta faman bacci parlour yawuce da ita yakwantar da ita sannan suka gaisa da mummy, tace my son ina kashiga tun d’azun naketa cigiyarka?
Murmushi yayi yace mummy na je dubo gini daga chan nawuce gidan Maman jawahir (kasancewar haka yake ce ma Aunty khairat)
Mummy tace toh ya ginin yana ta mik’awa ko? Murmushi yayi yace mummy sai kinga hospital d’in sai kace a turai gaskiya ya had’u sosai yakamata inkaiki kigano, Murmushi mummy tayi tace indai angama ginin munje,
Mummy ai ankusan gamawa, toh Allah yasa agama lafiya my son.
Ameen suka ce gaba d’ayansu.
Kallon fatima yayi yace zo kid’auki Ameerah kikaita d’aki tunda bacci take, tasowa tayi tad’auketa mummy tace kiwuce da ita d’akinki kawai tunda mamanta batada lafiya kar ta je ta dameta, dariya fatima tayi tace ga kuma Ameerah ba bayaba wajen rashin ji.
Agurguje After 2 days suka koma school Amina ta shiga 200L su fatima kuma suna final year d’insu, tsakanin Amina da fahad ko saidai gaisuwa take had’asu shima d’in wajen cin abincine ake had’uwa kowa yana jin ba dad’i a ransa saidai ba maiji zai fara kula d’an uwansa, saidai Ameerah kullum yana manne da abunsa inko kagansa d’akin Amina toh Ameerah ce zai maida.
Bayan sati biyu Amina na kwance saman kujera 3 seater a d’akinta tana karatun C.A test d’in da zasuyi ran Monday kasancewar yau asabar, gashi tun jiya Ameerah da fahad yafita da ita bai maidotaba kuma bai fad’a mata inda yakaitaba itakuma ba ta jin za ta iya tambayarsa.
fatima ce tashigo da sallamarta tashi Amina tayi daga kwancen da take tana murmushi ta amsa mata zama kusa da ita fatima tayi tace my sis karatu ake?
Eh wlh dayake C.A zamuyi ran Monday,
Ayyah sis Allah yabaku sa’a, Amina tace Ameen sis.
Yauwa sis da anjima bayan la’asar kishirya zamuje gidan Aunty khairat, cikin jin dad’i Amina tace toh Allah yakaimu daman na kwana biyu ban je ba.
Wajen k’arfe ukku Amina tashiga wanka, bayan ta yi sallah tayi kwalliya cikin shadda maroon colour wadda akayi ma aiki pink, d’aurin kallabi tamurza nan da nan kyaunta yak’ara fitowa ko da ba wata kwalliyar kirki tayi ba,
Wayartace tafara ringing tana dubawa taga Fatima ce murmushi tayi tayi picking d’in call d’in tace my sis ya dae, fatima tace please kifito mutafi,
Ohk ganinan zuwa,
Veil pink tad’auko tayafa tasaka pink d’in shoe’s, tajawo hand bag d’inta tafito tanufi parlour, zaune ta tadda fahad shi kad’ai yana kallo, saida gabanta yafad’i da ta ganshi, shima kallonta yake cikin mamaki,
Juyawa tayi zata tafi d’akin fatima muryarsa tajiyo yana cewa ina zakije? Batare da ta juyoba ta ce gidan Aunty khairat,
‘Daure fuska yayi yace da izinin wa?
Juyowa tayi takallesa itama tad’aure fuska tace da izini mummy,
Dariyar rainin wayau yayi mata yace aren’t you ashamed to say dat? Mummy ita take aurenki ko ni? Dan haka babu inda zakije
Harararsa tayi tace kadaina ik’irarin aurenka akaina, auren da yakasance na d’an lokaci? Idan najefa me zakayi?
Wata irin harara yawurga mata har saida tatsorata ahankali yataso cikin tafiyarsa ta tak’ama ya iso inda take har suna jin numfashin juna yace kikwatanta fita daga gidan nan ba da iziniba wlh zan baki mamaki, hmm don’t never try to do dis mistake, murmushi yayi yace ga kuma tsinuwar mala’iku, ta gefenta yara6a ya wuce.
Tsaye yabar Amina ta rasa yadda zatayi kokwanto tashiga yi shin tatafi ko takoma………