K’ADDARA CE CHAPTER 13
Dasauri Mummy tanufo inda take tafara jijjigata tana kiran sunanta, Fatima ma da basu dad’e da dawowa daga school ba k’arar da tayi ta tsoratasu dagudu suka fito d’akin hankalinsu a tashe,
Ganin Amina azube k’asa kamar gawa yasa hankalin fatima ya ida tashi tafad’a jikinta tana kuka tana cewa sis dan Allah kitashi ganin bata ko motsi yasa tatashi dagudu tanufi kitchen domin tad’ebo ruwa, salma da take tsaye tana kallonta jikinta duk ya yi sanyi ganin Amina a wannan yanayin, kallon k’asan tayi taga duk jina nan tarud’e tace mummy jini fa take zubar wa,
Babah mairo jin hayaniya yasa tafito itama domin tagane ma idonta meke faruwa a gidan, salati tashiga yi hankalinta duk ya tashi,
Fatima ce tarugo dagu da ruwa a hannunta tazo ta watsa mata ammah ina bata ko motsaba ganin haka yasa mummy takalli salma tace yi sauri kije d’akina kid’auko min key d’in motata da hijab, dagudu salma tanufi d’akin ummah dan tad’auko key, mummy da Fatima da babah mairo suka kamata salma tabud’e masu bayan mota aka sakata sannan fatima da salma suka shiga mummy taba motar wuta ganin yadda mummy tatuk’o motar yasa getman dasauri yabud’e mata gate tana fita dai-dai lokacin daddy yadawo daga sallar juma’a yana shawo kwana yaga wuce war motar mummy yanayin yadda yaga tana tuk’in yasan ba lafiya ba dagudu shima yabi bayanta wayarta yadinga kira ammah ba ayi picking ba. Cigaba yayi da binsu har sukazo wata private hospital, tana yin parking shima daddy yayi.
Dasauri yafito yanufi inda suke kallon mummy yayi da take k’ok’arin bud’e mota lokacin anzo za a d’auki Amina, yace hafsat me yake faruwa nuni mummy tayi masa da Amina da ake fitowa da ita daga cikin motar kamar matatta,
Kallonta daddy yayi yace me yake faruwa da ita daga mummy har fatima rasa bakin magana sukayi dasauri suka d’unguma suka bi gadon da aka d’auki Amina saida sukaje har d’akin da za a shigar da ita sannan aka ce sutsaya waje,
Daddy shima duk jikinsa ya mutu Cikin tashin hankali yace kufad’a min me yasameta, salma ce tayi k’ok’arin fad’a masa abinda yafaru nan shima daddy hankalinsa ya ida tashi, nan sukayi zaune cirko-cirko suna jiran doctors d’in sufito.
daddy har yaje masallaci yadawo ammah basu fito ba a motor sa yad’auko ma su mummy darduma sukayi sallah,
Wajen k’arfe biyar doctor d’in yafito, dasauri duk suka taso suka nufo inda yake daddy ne yakalli doctor d’in yace doctor ya jikin nata,
Kallon daddy yayi yace kasameni a office har doctor ya juya sai kuma yajiyo yakalli mummy yace kema haka hajiya, doctor yana gaba su daddy suna biye da shi a baya har suka shiga kujera doctor yanuna ma su daddy da take opposite d’insa yace have a sit mana Alhaji.
STORY CONTINUES BELOW

Zama su daddy sukayi, doctor yazare glass d’in da yake fuskarsa yakalli daddy yace Alhaji ya akai kuka bari hakan tafaru da ita? Dan Allah yataimaka kun kawota hospital d’in da wuri da ba cikin da yake jikintaba har ita kanta sai kun rasata,
Ammah ynz Alhmdllh mun samu mun ceto rayuwarta da ta cikin da yake jikinta saboda bata bari maganin yabi jikintaba da ace ta bari ya bi jikinta toh da cikin ya zube.
Daddy da mummy Kallon doctor kawai suke duk basu fahimci abinda yake nufiba daddy ne yayi k’arfin halin cewa doctor bafa ciki bane da ita kawai fad’uwa tayi ko Hajiya? Dasauri mummy ta gyad’a kai tace eh.
Murmushi doctor yayi yad’auko takarda yamik’a ma daddy yace kuduba kugani a iya bin cikenmu mun gano tana d’auke da cikin wata d’aya da sati d’aya ne, ta sha maganin zubar da ciki ne shine takasance cikin wannan condition d’in,
Kallon kallo aka shiga yi tsakanin mummy da daddy kusan a tare sukace ciki kuma? Murmushi daddy yayi yace shikenan doctor mun gode, magani doctor yarubuta yamik’a ma daddy yace gashi asiyo mata domin tasamu k’arfin jikinta sannan yanzu nasa ankaita d’akin hutu idan tafarka akwai injection d’in da za ayi mata in yaso zuwa ran Monday sai ayi discharging d’inku, jikin daddy duk ya yi sanyi dakyar yakar6i takardar yayi ma doctor godia sannan yakalli mummy ta yi mutuwar zaune yace taso muje.
Dakyar mummy tatashi tabi bayansa suna fitowa dasauri su fatima suka iso wajensu suna tambayarsu halin da Amina take ciki domin sunga yadda jikin iyayen nasu yayi sanyi.
Daddy yakalli mummy yace hafsat yaushe hakan takasance a cikin gidana batare da na saniba?
Mummy dakyar tabud’e baki tace Alhaji wlh nima kaina ban san inda Amina tasamo ciki ba, gaskiya ni ban yarda ba acanza hospital,
Daddy yace tunda dai har doctor d’innan yafad’a toh na yarda saboda kwararren likitane, ya akayi wannan abun kunyar yafaru a gidana?
Fatima da salma Kallon iyayen suke cikin rashin fahimtar abinda suka fad’a fatima tace mummy wa yake da ciki?
Mummy d’auke kanta tayi daga kallonsu tace Amina mana, atare salma da fatima suka ce what!! Mummy ciki kuma? Fatima tace ina tasamo ciki toh?
Mummy tace amsar da bamu saniba kenan sai ta farka sai muji daga gareta, salma tace lallai tsintattiyar mage bata mage, shuru kowa yayi suna jimamun abun.
d’akin da take suka shiga sukayi cirko-cirko kallonta fatima tayi cikin tausayi ganin yadda duk tafita hayyacinta, har akayi sallar magrib Amina bata farka ba, kad’an-kad’an nurses sun lek’o suga ko ta farka.
Aunty khairat da takira mummy domin sugaisa nan take samun labarin suna asibiti dasauri tashigo motarta tatafo itama nan take samun labarin abinda yake faruwa maganar taji ta girgizata domin bata ta6a tunanin hakan daga Amina ba,
Mummy tace wlh nima na yarda da nutsuwarta a yadda nayarda da yarinyar nan gani nake ko yatsa aka sanya mata a baki ba zata cizaba ashe ba hakaba.
Daddy girgiza kai yayi yace Allah dai yakyauta.
Gaba d’ayansu suka amsa da ameen.
Babah mairo taba idi driver abinci yakawo masu a hospital d’in, har wajen k’arfe 10 Amina bata farka ba ganin haka yasa daddy yace sutashi sutafi gida mummy ita sai takwana wajen Amina,
Ko da suka koma gida zugum sukayi kowa abun yana damunsa, Aunty khairat ma bata koma gidan ta ba kasancewar mijinta ba ya nan, dan haka gidansu takwana.
Fahad tunda yafita hospital d’insa yawuce kife kansa yayi a desk takaicin marin da yayi ma Amina ya ishesa tunowa yayi da cikin da tace zata zubar dasauri yadafe kansa yace meyasa Amina kike so kiga kin 6ata min rai? Lallai dole su mummy susan wannan maganar ko ma menene zai faru saidai yafaru domin hakan shine kawai mafita.
STORY CONTINUES BELOW

takardun da aka aje masa a office na masu neman aiki a hospital d’insa yad’auka yana dubawa ammah duk ransa a 6ace yake, Ko da sakatare yashigo ganin ogan nasa cikin wannan hali yasa yafasa fad’a mashi abinda yakawosa gaishesa kawai yayi yafita yana mamaki domin bai ta6a ganin Fahad a wannan yanayin ba.
Sai wajen 11 sannan Fahad yafito yadawo gida, salma da ta kasa tsaye da zaune kowa ya tafi ya kwanta ammah ita tana nan jira take Fahad yadawo tafad’a mashi abinda yake faruwa, tana jin tsayuwar motarsa tayi hamdala.
Jira take taji shigowarsa ammah shuru har ta fitar da rai tana shirin tafiya room d’inta sai taji shigowarsa d’age labulen parlour tayi tagansa direct d’akin Amina yanufa nan kishi yak’ara kama salma ammah tana tunowa da idan yaya Fahad yaji labarin cikin Amina shima tsanarta zaiyi sai taji wani sanyi a ranta,
Dasauri tafito tanufo inda Fahad yake shirin bud’e d’akin Amina, tace yaya Fahad, dasauri yajuyo yakalleta yana mamakin ganinta yace me kike nan?
Murmushi salma tayi tace yaya Fahad daman jira nake kadawo infad’a maka abunda yake faruwa a gidan nan, hankalinsa yamaido gareta yace ina saurarenki me yake faruwa?
Gyara tsayuwarta salma tayi tace ashe Amina “yar iskace wajen yawon iskancinta tayo cikin shege, fahad runtse idonsa yayi yana mai jin takaicin kiran Amina da salma tayi ‘yar iska kuma cikinsa ne yazama na shege,
Ahankali yabud’e idonsa da suka canza kala saboda 6acin rai harara yawurga ma salma da tasa saida salma ta tsorata, yace uban waye yace miki tana da ciki?
Cikin in ina salma tace wlh yaya ciki gareta shine taje tasha maganin zubar da ciki….. nan takwashe komai tafad’a ma fahad.
Ran fahad in yayi dubu toh ya 6aci nan haushin Amina ya Ida kamasa daman zuwan da zaiyi d’akinta lallashinta zaiyi, cikin ransa yace wato da yahanata tasha maganin ashe saida taje tasha dan ta rainasa na,
Cikin 6acin rai yajuya yanufi hanyar d’akinsa batare da ya ce ma salma komai ba, nan salma tadinga murna domin ta san yanzu fahad ya tsani Amina ba zai ta6a aurentaba, tsalle tayi sannan tajuya takoma d’akinta takwanta zuciyarta fal da farin ciki dan gani take yanzu yaya fahad dole yahak’ura da Amina yasota.
Fahad tunda yakoma d’akinsa jingina yayi da bango maganganun da salma tafad’a mashi suka dinga yawo a k’walwarsa dakyar yaje yazauna tare da dafe kansa yana mai jin takaicin abinda Amina tayi tsaki yaja yace Lallai wannan yarinyar dole innuna mata kuskurenta,
Tashi yayi yashiga toilet yasakar ma kansa shower, saida yayi kusan 10 minutes sannan yafito yashirya yakwanta ammah har lokacin zuciyarsa a tunkushe take adaren fahad baiyi baccin kirki ba saidai jin dad’insa da cikin bai zube ba.
Babah mairo koda tasamu labarin abinda yake faruwa itama hankalinta ya tashi duk sai tausayin Amina yakamata domin bata yi kama da ‘yar iska ba saidai akwai wani 6oyayyen al’amari take tunani atare da ita.
Tun da safe Aunty khairat tashiga kitchen tare da babah mairo suka had’a breakfast wajen k’arfe goma suka gama shiri suka nufi hospital, Aunty khairat Ko da tayi ma fahad maganar bai ce komai ba tace yataso suje hospital d’in yace suje kawai babu inda zai je, ganin Aunty khairat tana shirin damunsa yasa yace tafad’a masa hospital d’in yana nan zuwa, ahaka suka tafi suka barsa,
Aunty khairat tare da daddy suka tafi.
Koda suka isa mummy suka tadda a zaune ta tisa Amina gaba da take ta faman bacci tana kallo,
Daddy cikin mamaki yace kar dai ace yarinyar nan bata farfad’oba, mummy tace eh ko motsawa batayiba ni na tsorata kuma da doctor yazo allura yayi mata ya ce bacci take akyaleta sai ta farka da kanta.
Daddy yace Allah yatasheta lafiya. Sallama daddy yayi masu yatafi yabarsu duk sunyi zugum.
Fahad da yake d’akinsa babah mairo ce tashigo d’auke da Ameerah tana ta kuka, dasauri yatashi yakar6eta talafe a kafad’arsa babah mairo tace wlh tun d’azun take min kuka wai mummynta shine nace bari inkawo maka ita, murmushi Fahad yayi yakalli Ameerah da take ta ajiyar zuciya yace my angel kina zuwa wajen mummy? ‘Daga mashi kai Ameerah tayi yace gud gurl bari inyi wanka sai inkaiki,
Kallon babah mairo yayi yace tayi breakfast? Babah mairo tace eh, yace toh shikenan babah, nan babah mairo tafito daga d’akin tanufi kitchen domin tad’aura girkin rana.
Fahad chocolate yad’auko yaba Ameerah sannan yatashi yashiga wanka,
Bayan ya shirya d’aukar Ameerah yayi yabar gidan,
Wajen k’arfe biyu daddy yadawo gida yaci abinci sannan ya amshi na ‘yan asibiti yatafi yakai masu har lokacin Amina bata farka ba,
Bayan sallar la’asar mummy tana zaune saman darduma idanuwanta suna a kan Amina ahankali taga ta fara motsa hannuwanta dasauri tata6o daddy tagwada mashi, duk zuba mata ido sukayi,
Ahankali tabud’e idonta tasafkesu a saman ceiling tana kallon fanka da take juyawa, maida idonta tayi tarufe abinda yafaru da ita yafara dawo mata a brain dasauri tabud’e idonta,
Fatima da tunda tafara motsa hannu taruga domin takira doctor, daidai lokacin suka shigo tare da doctor, dubata yak’ara yi yayi mata allura yatambayeta akwai inda yake mata ciwo? Hawaye zarya kawai suke daga idanuwanta ahankali tagirgiza masa kai,
Kallon su daddy yayi yace Alhamdulillah komai normal saidai ba za ayi discharging d’inku yau ba saboda allurar da za a ida yi mata cikin dare.
Yanzu ahad’a mata tea mai kauri abata tasha in tagama sai abata magani, daddy yace toh.
Su mummy sannu suka dinga yi mata tea aka had’a mata dakyar mummy tasamu tatashi tasha sannan tasha magani, Aunty khairat ta taimaka mata tayi wanka.
Bayan ta shirya saman gadon takoma tazauna tare da jingine kanta a bango su mummy duk sun zuba mata ido kowa maganace d’auke a bakinsa, runtse idonta tayi Hawaye suna zuba domin tabbas tasan yau k’aryarta ta k’are asirinta ya tonu.
Muryar mummy tajiyo ta kira sunanta ahankali tabud’e idonta tare da amsawa,
Mummy tace Amina ashe yadda muka d’aukeki ba haka kika d’auke mu ba kifad’a min menene kika ta6a nema kika rasa a tare da mu? Ashe bakida wayau da har zaki iya ba wani namiji kanki bata hanyar aureba wlh kin bani kunya lallai na yarda tsintacciyar mage bata mage, dasauri Amina tad’ago kai takalli mummy har ta bud’e baki zatayi magana sai kuma tayi shuru hawaye suka cigaba da zarya a idonta.
Daddy takaici ya ishesa yace uban wa yayi miki ciki? Shuru Amina tayi takasa magana saidai kuka da take.
Aunty khairat tace idan ba zata fad’aba kukyaleta ammah wlh ba zata cigaba da zama cikin zuri’ar muba, Amina kin bamu kunya ashe ke ba d’iyar arzik’i bace.
Mummy cikin d’aga murya tace nace kifad’a min uban wa yayi miki ciki?ke wai ma wacece ke, daga ina kika fito? Ni ban ma yarda da auren da kika ce kin ta6a yi ba, Amina dai kuka kawai take ta kasa cewa komai, Takaici yacika fatima tace Allah yakyauta daman ai ramin k’arya k’urarrene.
Tsaki salma taja tace munafukar banza ashe karuwa muke tare da ita bamu saniba wa ma yasani wacchan d’iyartata itama shegiya ce wajen yawon karuwancinta aka haif……
Wani irin mari da salma taji yahanata k’arasa maganar da take bakinta gigicewa tayi, kowa d’agowa yayi domin yaga waye yayi marin hatta ita kanta Amina saida tafirgita tad’ago kai takallah cike da mamaki suke bin Fahad da Kallo da idanuwansa suka rine suka canza kala, Ameerah dagudu tanufi wajen mummynta tana murna ammah sai taja tatsaya ta ta6e fuska kamar zatayi kuka saboda ganin Amina da tayi tana kuka.
Batare da tsoro ko fargaba cikin 6acin rai da basu ta6a ganinsa da shiba fahad yace kar kisaki kik’ara kiramin mata karuwa kuma kar kisaki kiyi gigin ce ma d’iyata shegiya idan ba hakaba ranki sai ya 6aci, kowa kallonsa yake fuskokinsu d’auke da mamaki maganar da yayi ta girgizasu sosai dasauri mummy tatashi tsaye daga zaunen da take, daddy zufa yafara yi, cikin had’in baki sukace matarka, d’iyarka?………
Mummy tace fahad kana da hankali kuwa? ka san abinda kake fad’a, Anya kana cikin hayyacinka? Miye had’inka da Amina da har kakeso kakareta? Mayasa kakeso kad’aura ma kanka laifin da ba nakaba? Lokaci guda mummy tajero masa tambayoyin.
Fahad yace mummy tabbas nasan abinda nake fad’a, Amina matatace kuma tabbas cikin da yake jikinta na…… wani gigitaccen mari da daddy yad’aukesa da shi yasa maganar ta ida mak’alewa a bakinsa,
Mamakine yakama fahad domin tunda yataso da wayonsa daddy bai ta6a d’aga hannu ya dokesaba sai yau, cikin 6acin rai daddy yace kar kasaki kad’aura ma kanka Abinda bakayiba domin naga alama so kake kakare yarinyar nan.
Mummy cikin 6acin rai tace har kake Iya d’aga hannu kamari ‘yar uwarka dan ta fad’i gaskiya fahad, ya kamata kadawo cikin hankalinka
Fahad yana rik’e da k’uncinsa yace daddy ba k’arya nake mukuba ina so infad’a muku wani sirri da baku sansaba, tabbas labarin da Amina tabaku game da ita ba gaskiya bane, ta 6oye muku gaskiya game da rayuwarta kamar yadda nima lokacin da k’addara tarabani da ku, acikinku akwai wanda ya tambayeni kalar rayuwar da nayi a chan bayan na dawo?
‘Dakin shuru yayi dukkansu sunyi mutuwar tsaye sun zuba masa ido fuskarsu kawai zaka kalla zaka gane suna cikin matsanancin tashin hankali, murmushi fahad yayi bai damu da rashin samun amsa daga garesuba yacigaba da cewa nima kuma babu wanda nafad’a mawa na bar sirrin ne kawai a raina domin bana so intayar muku da hankali ammah yanzu zan warware muku komai domin ina so kusan cewa *k’addara ce* tarabani da ku har naje katsina,
Murmushin takaici yayi yace ammah saidai banyi rayuwa da mutanen kirki ba, na yi rayuwa da ‘yan fashi,
Nan d’akin ya ida rud’ewa, mummy da Aunty khairat sukace fashi kuma fahad? wece irin *K’addara ce* tafad’a maka haka? daddy zufa yashiga gogewa duk A.C d’in da take d’akin ammah bai hanashi yin zufa ba,
Salma da tunda taji ya fad’i Amina matarsace daskarewa tayi daina jin zafin marin da yayi mata tayi ji take ina ma ace mafarki take hakan ba gaske bane.
Fatima ahankali tasulale tazauna k’asa tare da buga tagumi.
Amina kuka kawai take tana rungume da d’iyarta, cikin kuka tace fahad kar kayi min haka dan Allah kar kad’aura ma kanka laifin da ba nakaba. Wata harara da yawurga mata ita tasa tayi shuru.
Ahankali yataka yaje saman sick bed d’in da take zaune ya zauna shima, yace miyasa kikeso kiyi k’arya alhali k’arya bata dace dakeba? dasauri Amina tafad’a jikinsa tare da fashewa da sabon kuka tace fahad bana son kasamu matsala da iyayenka kamar yadda nasamu matsala nima, runtse idanuwansa fahad yayi yana jin wani iri a ransa.
Su mummy kallonsu suke duk mamaki ya ida kashesu jira kawai suke suji anwarware masu wannan bak’in duhun da suke ciki, Aunty khairat ce tayi k’arfin halin cewa ya kamata kufitar da mu bak’in duhun da kuka sakamu a ciki domin duk kun d’aure mana kai,
STORY CONTINUES BELOW

ahankali fahad yad’ago kai yakallesu batare da tsoro ko fargaba ba Yace kusaurareni koma minene zakuji a cikin labarina, bayan na bar gidan nan cikin tashin hankali da tsoron abinda zai biyo baya daga gareku daddy domin nasan ba zaku ta6a yarda da abinda zan fad’a mukuba, direct tashar mota naje saidai na rasa wane gari zan je kawai sai naza6i inje garin katsina saboda chan ne nasan bamuda kowa, motar zuwa katsina nashiga ko da muka isa katsina ban san ina zan nufa ba, waje nasamu nazauna ina tunanin ina zan je, wani mutum da muka shiga mota d’aya da shi duk yanayin da nake ciki yana lura da ni shine yazo yataimaka min yatafi da ni garinsu dake k’ark’ashin jahar katsina ana kiran garin mashi ashe gahurtacce d’an fashi ne yana da yaransa ukku………… nan fahad yakwashe labarin rayuwar da yayi duka yafad’a masu har zuwan da sukayi gidansu Amina da labarin auren da sukayi bai 6oye musuba kai har labarin tarihin Amina da tafad’a masa saida yabasu, da dawowar da yayi yasamu Amina a gidansu.
Amina k’ara shigewa tayi jikinsa tana kuka domin gani take kamar k’arshen tarayyarta da fahad ta zo idan aka rabasu batasan yadda zatayi da rayuwarta ba.
Aunty khairat ma da su fatima kuka suke, Mummy ma kanta kuka take,
Daddy ne kawai mai k’arfin hali a cikinsu shima kansa labarin ya firgitasa girgiza kansa kawai yake yana jimamin abun dakyar yabud’e baki yace tabbas Amina kinga rayuwa kin had’u da mutane kala-kala a rayuwarki, Allah yajik’an mahaifanki, Fahad ne kawai yace Ameen,
Daddy yacigaba da cewa tabbas wannan *K’ADDARA CE* da jarabta babu wanda ya isa ya tsallake abinda Allah yak’addara masa, wannan auren naku *HADIN ALLAH NE* fahad ka burgeni da kanuna jarumtarka a nan saidai abu d’aya ne banji dad’insa ba da ka6oye mana komai, har kana da d’iya kamar wannan batare da mun saniba kuma dan ta ce karkafad’a mana shine kabiye mata kuka 6oye mana, shin mu ba musulmai bane? Ko bamusan k’addara ba? Acikinmu akwai wanda zai iya gujema k’addarar sa?
Fahad janye Amina yayi daga jikinsa yatashi yanufi inda daddy yake cikin ladabi yace daddy dan Allah kayafe min insha Allahu hakan ba zai k’ara faruwa ba nasan na yi laifi daddyna inaso kuyafe min.
Murmushi daddy yayi yace shikenan my son tunda ka gane kuskurenka,daman ita rayuwa anaso idan mutum ya aikata kuskure yagane kuskurenta toh ayafe masa, Allah yayafe mana gaba d’aya Allah yayi muku albarka, cikin Jin daddy fahad yace Ameen daddy na.
Fahad wajen da mummy take yanufa rungumota yayi yace mummyna dan Allah kiyafe min insha Allahu ba zan k’ara aikata wannan kuskuren ba,
mummy goge hawayen fuskarta tayi tajanye jikinta daga nasa cikin 6acin rai tace wlh fahad baka kyauta min ba, ka ban mamaki da har hakan takasance batare da ka shaida mana ba lallai abinda kayanke a ranka shi kake aiwatarwa baka d’aukemu a bakin komai ba, dan haka kaje kayi yadda duk kake ganin shine daidai a wajenka, Fahad marairaicewa yayi yace please mummy pardon me I promise you i would never do it again, juya masa baya mummy tayi tare da tashi tajawo jakkarta taficce daga d’akin cikin 6acin rai,
tashi fahad yayi cikin damuwa zai bita nan daddy yad’aga masa hannu yace yabarta yanzu tana cikin 6acin rai ba zata sauraresaba, jikin fahad duk ya yi sanyi yakoma wajen Aunty khairat dasauri tarungumesa tana kuka cike da tausayin k’anen nata tace my bro kayi hak’uri da miss understanding d’inka da mukayi tabbas munyi kuskure.. murmushin k’arfin hali yayi dasauri yakatseta daga maganar da takeyi yace bakomai my sis wlh na fahimceku.
Janye jikinta Aunty khairat tayi tanufi wajen Amina da taketa kuka rungumeta tayi tace kiyi hak’uri kiyafe mana abinda mukayi miki Amina tabbas munsan munyi kuskure kuma….., dasauri Amina ta girgiza kai tare da toshe ma Aunty khairat baki tace Aunty khairat kidaina cewa haka ni bakuyi min komai ba sai alkhairain da kuka yi min alokacin da wasu suka gujeni ku kuma alokacin kuka jawoni a jikinku kuka rik’eni hannu bibbi…. kukane yaci k’arfin Amina takasa k’arasa maganar, ahankali takwantar da Ameerah da take ta faman bacci dakyar tatashi tana jin jikinta duk wani iri takawa tayi taje wajen da daddy yake zaune ya dafe kansa, ahankali tatsugunna cikin kuka tace daddy dan Allah kuyafemin nasan ban kyauta muku ba nice silar sakaku cikin wannan matsalar, kuyi hak’uri; daman irin wannan ranar ita nake gudu k’ara fashewa da kuka Amina tayi
Kallonta daddy yayi tare da murmushi yace bakomai Amina Allah yayi muku albarka, kidaina d’aura ma kanki laifi kar kimance da k’addara ce kuma tana akan kowa kikwantar da hankalinki kinji ko?
Cikin kuka Amina tace toh daddy nagode Allah yasaka da alkhairi Allah yak’ara girma Allah yasaka muku da gidan aljannah, cikin jin dad’i daddy yace Ameen,
Ahankali tatashi tanufi inda su fatima suke zaune kunya duk ta kamasu ganinta yasa suka saddar da kansu k’asa, tsugunnawa tayi gabansu dasauri fatima itama tatsugunna Amina tana shirin yin magana dasauri Fatima tarigata cikin kuka tace dan Allah kiyafemin sis wlh sharrin shaid’anne yaja nai miki haka, ashe ke ba “yar uwa kawai bace matar yayana ce gaskiya naji dad’in kasancewarki a cikin family d’inmu,
murmushi Amina tayi tare da rungumota tana rarrashinta tace bakomai fatima ni bakuyi min komai ba sai alkhairi kun rik’eni hannu bibbiyu tsakani na daku saidai addu’a dan haka kikwantar da hankalinki ai anzama d’aya, murmushin jin dad’i Fatima tayi tace nagode sis.
Kallon Salma tayi da tatakure waje d’aya sai kuka take,
dasauri Amina ta matsa wajenta jikin Amina duk ya yi sanyi tace Salma kiyafe min nasan nice silar fad’awarki na wannan yanayin nasan menene so tunda nima ya yi d’awainiya da shi kikwantar da hankalinki insha Allahu yaya fahad nakine saboda kece kikafi dacewa da shi ba ni ba, dasauri Salma tad’ago kanta tare da girgiza kai tace Amina tabbas ke mutunniyar kirki ce kiyafemin domin na cutar da rayuwarki sau dayawa ina abu dan in6ata miki rai ammah ko da sau d’aya baki ta6a damuwa da abinda nake mikiba, wlh yaya fahad dake yadace Amina ba da ni ba domin duk wata matsala ta dalilinsa kika shigesa idan har nace inshiga tsakanin masoya guda biyu toh wlh banyi ma kaina adalciba,
domin sau dayawa ina ganin soyayyarki a cikin k’wayar idon yaya fahad kamar yadda nake ganin tasa a cikin kwayar idonki kinga kenan idan har na amince na auresa banyi ma kaina adalciba saboda gangar jikinsa zan aura duk wani ruhinsa da komai nasa yana wajen Amina kinga ba zanso inyi irin wannan auren marar ‘yanci ba dan haka yaya fahad na Amina ne ita kad’ai
dasauri Amina tarungume Salma cikin kuka tace kidaina cewa haka Salma wlh yaya fahad zai soki kema, itama salma rungumeta tayi tana mail cigaba da kuka tace a’a Amina ba zanso inkasance cikin marassa adalci ba, zan je in auri Wanda yake sona domin nima ahankali zan koya ma kaina sonsa, Ammah yaya fahad nakine ke ka… kukane yaci k’arfinta takasa k’arasa maganar k’ara rungumeta Amina tayi suka cigaba da kukan itama fatima tayasu tashiga yi.
Fahad lumshe idanuwansa yayi yana jin wani iri a zuciyarsa domin baisan yadda zasu k’are da mummy ba a yanzu itace kawai matsalarsa dan a yarda ya lura ta d’auki fushi sosai da shi……………
Aunty khairat dakyar ta lallashesu aka samu su Amina sukayi shuru, duk kukan da suke fahad yana jinsa har cikin ransa musamman ma na Amina ammah ya kasa cemusu komai.
+
Amina tunowa tayi da mummy nan hankalinta ya Ida tashi domin batasan hukuncin da mummy zata yanke ba, k’afafuwanta taji sun gaza d’aukarta daga tsayuwar da take ga wani irin ciwon kai da take kamar kan zai fashe take ji, dakyar tafara takawa zata koma saman sick bed takwanta nan idanuwanta tafara ganin bibbiyu dakyar tadafe kanta tare da furta wash, kawai sai gani sukayi tana shirin zubewa,
Fahad cikin zafin nama yarik’ota ammah ina har ta sume d’aukarta yayi yanufi saman gadon ya kwantar da ita cikin tashin hankali yashiga jijjigata yana kiran sunanta, tuni salma ta ruga domin takira doctor.
Aunty khairat da fatima kanta sukayi suna kiran sunanta suna kuka, daddy ko salati yashiga yi, kallon fahad yayi yaga yadda yake jijjigata sai kace zararre da sauri daddy yajawosa fahad duk ya fita hayyacinsa, daddy yace haba fahad menene haka kakeyi saikace ba namiji ba, fahad cikin tashin hankali yace shikenan fa daddy ta mutu, dasauri daddy yagirgiza kai yace a’a fahad wa yace maka ta mutu? Amina tana nan da ranta kakwantar da hankalinka
Daidai lokacin salma tashigo tare da doctor, dasauri fahad yanufi wajensa yace please kaduba min ita kaga idan tana da rai,
Kallonsa doctor yayi yaga duk ya fita hayyacinsa saikace shima ba doctor bane dasauri yanufi inda Amina take kwance, jin zuciyarta tana harbawa yasa yagane tana da rai,
Kallonsu yayi yace subasa waje domin yayi aikinsa cikin kuka su Aunty khairat suka tashi suka fita, daddy ganin fahad baida niyar fita yasa yajawosa suka ficce,
Ko da suka fita fahad saffa da marwa yashiga yi a wajensa cikin tashin hankali duk tausayin Amina ya kamasa jin dad’insa ma Ameerah ta yi bacci, daddy ne yasamu yashawo hankalin su Aunty khairat domin kukan da suke yi saikace wad’anda aka ce musu ta mutu gudun kar sutada hankalin yan asibitin yasa yamusu fad’a sannan yasamu sukayi shuru.
Wajen fahad yanufa da yaketa zagaye wajen, dafasa daddy yayi dasauri fahad yad’ago kai yakallesa idanuwansa kawai zaka kallah a nan zaka karanto irin tashin hankalin da yake ciki, murmurshi daddy yayi yace haba my son ban sanka da hakaba yakamata kadawo cikin hayyacinka be a man mana saikace ba namiji ba, addu’a yakamata kayi mata insha Allahu zata samu sauk’i,
Dogon numfashi fahad yaja yace toh daddy nagode, daidai lokacin doctor d’in yafito dasauri duk suka nufi wakensa suna tambayarsa jikinta, Kallonsu doctor yayi yace Alhmdllh daman ba wata matsala bace damuwace tasa ta tashiga wannan condition d’in ammah ynz na yi mata Allura ta samu yin bacci, tana buk’atar hutu kar atasheta, dogon numfashi fahad yaja cikin jin dad’i sukayi ma doctor d’in godiya.
Daddy fahad yaja suka wuce masallaci, su ma su Aunty khairat d’akin suka shiga sukayi sallah cike da tausayin Amina da addu’an samun sauk’inta,
STORY CONTINUES BELOW

Ko da su fahad suka dawo Amina yatisa a gaba yana kallo, ko da aka kawo musu abincin dare saida daddy yayi dagaske sannan yad’an ci, Amina har wajen 11 bata farkaba ganin dare ya yi yasa daddy yace sutafi gida abar Aunty khairat takwana a wajenta, fahad ya so yakwana domin yakula da matarsa ammah kuma yana jin kunyar daddy Dan haka kan dole ya hak’ura ba dan yaso ba yad’auki Ameerah suka tafi gida.
Mummy ko da tafito gida tanufa cikin 6acin rai da jimamun abunda fahad ya aikata, ko da ta isa gida kasa zaune da tsaye tayi zagaye room d’inta tashiga yi tace lallai fahad yanzu ace fahad d’ina ne yayi aure batare da sani na ba, abun takaicin wai muna zaune da matarsa a gidanmu batare da ya bayyana manaba har ma da d’iyarsa da wani cikin, cize le6e mummy tayi tare da girgiza kai tace wannan wace kalar *K’addara ce* gaskiya hakan bazai yuwuba. Ahaka mummy ta kwanta yau ko d’akin daddy bata lek’a ba saboda fushin da take ya shafi kowa, dan haka kwanciyarta tayi d’akinta ko da taji dawowarsu bata fito ba.
Fatima ce takar6i Ameerah daga wajen fahad nan babah mairo tashigo da jawahir da take bacci, d’akin fatima suka kwantar da su,
fahad cikin sanyin jiki yanufi d’akin mummy ammah abun mamaki sai yajisa a rufe alamun taciki aka rufe, har ya kai hannu zai k’wank’wasa sai kuma yatuno wani abun yafasa, jingina yayi da k’ofar tare da lumshe idonsa yana jin duk ba dad’i domin babu abinda yafi tsana a rayuwarsa sama da yaga iyayensa suna fushi da shi, saida yayi kusan minti goma sannan yajuya yanufi d’akinsa,
Salma ko d’s tashiga d’akinta saman gado tafad’a, runtse idonta tayi tare da dafe k’irjinta tana jin son fahad yana k’ara ninkuwa a ranta, dasauri tagirgiza kai tace shikenan yaya fahad na rasaka bana jin zan so wani namijin kamar yadda nake sonka saidai kash bamu dace da juna ba Amina ita tadace da kai ba zan iya shiga tsakanin masoya biyu ba domin idan nayi haka banyi ma kaina adalciba, jin zuciyarta tana neman bata gur6atacciyar shawara yasa dasauri tanemi tsarin Allah tare da d’aga hannunnta sama cikin kuka tace ya ubangiji kacire min son wannan bawa naka ya Allah kasamin son faruk a zuciyata domin shine mai sona, kukane yaci k’arfinta saida tayi mai isarta sannan tayi bacci
Cikin dare nurses sukaita zarya d’akin domin suga idan Amina ta farka, sai wajen 2 o’clock sannan tafarka daga baccin da take, Aunty khairat taje takira doctor aka dubata saida aka tabbatar da babu abinda yake damunta.
Tea aka had’a mata tasha, Aunty khairat ce tataimaka mata tayi wanka sannan tad’auro alwallah tagabatar da sallolin da ake binta, bayan ta gama takoma bacci.
Dasafe da doctor yadawo yayi mata injection nan yake sanar da su za’ayi discharging d’insu bayan anmata allura da k’arfe sha biyu.
Wajen k’arfe tara mummy ce tafito tanufi d’akin daddy batare da wata damuwaba a tare da ita lokacin daddy ya fito wanka yana shiryawa zai fita, cikin fara’a mummy ta gaishesa tare da d’aukar perfumes tana feshesa da su, kallonta daddy yayi cikin mamaki domin bai d’auka zata safko daga fushin a yanzu ba, ganin yadda yake kallonta yasa mummy tasakar mashi murmushi tare da furta ya dai maigidana wannan kallon fa? Murmushi shima daddy yayi yace hafsat kenan miye abun 6acin rai da abinda Allah yak’addara mana wlh kin bani kunya ina kika baro hankalinki da iliminki, kiduba fa kiga tarihin rayuwar yarinyar nan idan bamu tausaya mataba ya kikeso muyi, idan d’iyarki ce haka ta kasance da ita zakiji dad’i?
Murmurshi mummy tayi tace shikenan maigida komai ya wuce muje kayi breakfast d’in, daddy dai ya san ba dai hak’ura tayiba daga ma ganin yanayinta kawai dai ta fad’i hakan ne,
Ko da sukaje zasuyi breakfast fatima da salma ne a zaune sunayi salma ce take feeding d’in Ameerah ita kuma fatima tana feeding d’in jawahir, cikin girmamawa suka gaishe da iyayensu, daddy jin shuru da mummy tayi bata tambayi d’anta ba domin ta saba duk lokacin da bai fitoba sai tasa andubo mata Ko lafiya, ganin haka yasa yace fatima je kikira fahad yazo yayi breakfast sai kutafi asibitin ni ba zan samu zuwaba saboda ina da meeting yanzu haka zariya zanje, to fatima tace sannan tatashi tanufi part d’in fahad lokacin ya gama shirinsa yana shirin fitowa daga room d’insa, da sallama tashiga tare da gaishe da d’an uwan nata,
STORY CONTINUES BELOW

Cikin fara’a ya amsa mata tace yaya fahad daman daddy ne yace kazo kayi breakfast kakaimu asibiti, batare da wata damuwa ba fahad yace shikenan mutafi, ko da suka shigo parlour ko inda yake mummy bata kallah ba duk sai yaji ba dad’I domin mummy bata saba yi masa haka ba,
cikin girmama yagaishe da iyayen nasa daddy ne kawai ya amsa masa cikin sakin fuska, mummy gudun kar daddy yakaranto cewa bata huceba yasa ta amsa masa ciki-ciki, wajen shuru yayi kowa yacigaba da cin abincinsa,
Ko da suka gama mummy d’akinta takoma dasauri fahad yabita yana shiga tak’ara d’aure fuska tare da nuna masa k’ofa tace please kafitar min daga d’aki, fahad marairaicewa yayi yace please mummy na san….
Tsawa mummy tadaka masa tace I said get out!!!
Fahad jikinsa ya yi sanyi haka yadaure yaficce daga d’akin, wajen motarsa yanufa a chan yatadda fatima da salma suna jiransa.
Ko da suka isa Asibitin Amina da Aunty khairat zaune suke suna hira sama-sama domin har lokacin Amina ta kasa sakin jikinta, lokacin salma da fatima suka shigo da sallamarsu cikin fara’a suka amsa musu,
Salma tace ah lallai matar yaya kin warke kice sai sallama, kunyace takamata tasunkuyar da kanta, nan suka gaishe da Aunty khairat, Amina cikin jin kunya ta gaishesu, Aunty khairat tace ina kuka baromin d’iyata, dariya fatima tayi tace suna wajen baba mairo muka barosu.
Tea mai kauri fatima tahad’a mata tana cikin sha sai ga fahad ya shigo, kallo d’aya Amina tayi masa tad’auke kai Sanye yake da k’ananun kaya sun kar6esa sosai fuskarsa d’auke da farin space madaidaici ko inda take bai kallah ba nan suka gaisa da Aunty khairat,
Ahankali Amina ta gaishesa batare da ya kalleta ba yace lfy, ya jikin?
Bata ji dad’in yadda yabata amsar ba domin ta lura kamar fushi yake da ita, dasauk’i tace, daga nan bata k’ara maganaba taja bakinta tayi shuru nan sukayita firarsu ita dai bata tsoma masu baki ko da ansakota a maganar daga uhm sai a’a kawai take cewa tana lura da yarda fahad yake k’ara shan k’amshi,
Nan Aunty khairat take sanar da shi discharging d’insu da za’ayi, nan suka kira daddy suka sanar da shi.
K’arfe sha biyu aka sallamesu fargaba da tsoro suka kama Amina domin batasan yadda zasu kwashe da mummy ba nan duk jikinta yayi sanyi, zaune tayi tak’i tashi sutafi Aunty khairat tana ta mata magana ammah bata san me take cewa ba domin ba ta cikin hayyacinta,
Zama Aunty khairat tayi kusa da Amina tare da dafata, firgit Amina tayi tadawo daga duniyar tunanin da take, ganin Aunty khairat ta tsareta da ido yasa Amina tasunkuyar da kana,
Murmushi Aunty khairat tayi tace nasan kina tunanin had’uwarki da mummy ko? Shuru Amina tayi batace komai ba, Aunty khairat bata damu da shurun da tayiba tace kar kidamu mummy tana da sauk’in kai nasan zata safko tafahimceku domin mummy ba ta da rik’o, kikwantar da hankalinki kinji ko?
‘Daga kai Amina tayi alamun eh, Aunty khairat tace yauwa k’anwata taso mutafi.
Ko da suka isa wajen motar fahad har zata shiga baya dariya salma tayi tace Auntynmu ai gaba zaki shiga ku da motarku, mu zamu zauna baya ko my blood? Itama fatima dariya tayi tace eh mana maganarki gaskiyace,
Sharesu Amina tayi kamar ba da ita sukeba tana shirin shiga baya Aunty khairat tace a’a Amina kidai zauna gaba, fahad k”arshen k’ulewa ya k’ule yace idan ba zata shigaba ku kyaleta mana ni kuna 6ata min lokaci, Amina bud’ewa tayi tashiga batare da ta kalli inda yake ba domin tana kula da shi inda za ta biye masa toh da fad’a zasuyi, ko da suka kama hanya gaban Amina fad’uwa kawai yake domin tana gani kamar k’ashen rabuwarsu ce tazo ita da fahad, k’wallace tacika mata ido nan tashiga gogewa, fahad yana kula da ita ammah yashareta domin ya san tatsunniyar gizo ba ta wuce ta k’ok’i, dan shima yana fargabar hukuncin da mummy zata yanke a kansa
STORY CONTINUES BELOW

Ko da suka iso gida dakyar Amina tashiga, hankalinta nan ya ida tashi saida fatima ta rik’eta sannan suka shiga parlour ganin mummy ba ta ciki yasa Amina tafito takoma d’akinta.
Bayan sallar azahar ko wajen cin abinci Amina bata fitoba d’aki baba mairo takai mata nata tare da yi mata ya jiki, itadai Amina duk kunya takamata ganin haka yasa babah mairo tanemi waje tazauna tare da maida hankalinta wajen Amina tace Amina ya akayi hakan ta kasance da ke? Ada ina miki kallon mai hankali da wayau ashe ba haka bane abinda zaki saka ma mutanen nan da shi kenan duk rik’on da sukayi miki? Toh wai ma ina kika samo cikin shege?
Amina da tunda babah mairo tafara maganar kuka take cikin sheshek’ar kuka tace baba mairo cikin nan fa da ubansa kidaina jingina sa da nashege, cikin mamaki bavah mairo tace toh wanene uban nasa? Batare da tsoro ko fargaba ba Amina tace fahad ne ubansa,
Zumbur baba mairo ta mik’e tsaye har tana shirin fad’uwa tace wane fahad d’in ba dai wannan kamilin ba, kasa magana Amina tayi saidai ta d’aga mata kai,
Salati babah mairo tashiga tayi tare da ta6a hannu tace ke ‘yar nan kiji tsoron Allah fahad mutumin kirkine fa, goge hawayenta Amina tayi tace baba mairo saboda na yarda da ke kuma na d’aukeki a matsayin uwa saisa yau kafin nabar gidan nan zan baki labarina domin nasan k’arshen zamana da ku ya zo, bata jira jin komai daga bakin babah mairo ba nan tashiga bata labarinta….
Cikin kuka ta k’arashe ma babah mairo labarinta, mutuwar zaune babah mairo tayi takasa motsin kirki saboda labarin ya rikitata musamman ma aurenta da fahaad da had’uwarsu, dogon numfashi taja tare da jinjina kai tace lallai Amina kinga rayuwa wannan wace kalar matar uba ce marar imani Allah yasaka miki, Kinga ikon Allah ko? Wannan ma ishara ce Allah yanuna mana, tabbas kinyi k’ok’ari da duk k’uncin rayuwar da kika shiga ammah baki mance da cewa *K’addara ce* ba domin Allah yana jarabtar bawansa dan yagwada karfin imaninsa, wad’annan azzaluman bana tunanin zasu cika da imani domin babu tausayi ko tsoron Allah a tare da su fatanmu dai Allah yasa mudace, kar ki damu insha Allahu hajiya zata safko daga fushin da take, cikin kuka Amina toh babah mairo nagode sosai, jin ana kiran sallar la’asar yasa baba mairo tace ma Amina tacire damuwa a ranta taci abinci sai tajetayi sallah, godia Amina tayi mata sannan tafara cin abincin, ganin haka yasa baba mairo tatashi tanufi d’akinta cike da tausayin Amina.
Abincin kad’an Amina taci sannan tatashi tad’auro Alwallah tazo tagabatar da sallar la’asar.
Ko da mummy tafito nan su Aunty khairat suka gaisheta fuskarta ba yabo ba fallasa duk ta amsa musu batare da ta tambayi mai jikiba ganin yadda mummy tad’aure yasa dukkansu suka sha jinin jikinsu.
Bayan sun gama cin abinci Aunty khairat tabi fahad suka je room d’insa, fuskarta d’auke da damuwa tace fahad na lura dukkanmu mummy fushi take da mu, cikin sanyin jiki fahad yace hakane sister wlh nasara yadda zan yi mummy tafahimceni, shuru Aunty khairat tayi chan sai tace yauwa ga shawara, zuba mata ido yayi don jin abinda zata ce.
Murmurshi tayi nan tamatsa tana rad’a mashi magana a kumne _(nima kaina bansan me suke cewa ba😔)_ chan naga fahad shima yana murmushin sannan yace haka ko za’ayi my sister kin kawo gud idea bari muje mugwada muga, dariya Aunty khairat tayi tace insha Allahu zamuyi nasara fatanmu dai tafahimcemu,
Fitowa su fahad sukayi shi yawuce d’akin Amina cikin tafiyarsa ta k’asaita tura k’ofar yayi yashiga kwance ya hangota saman gado kanta yana kallon ceiling da alama tunani take, k’arar rufe k’ofar da yayi ne yadawo da ita daga duniyar tunanin da tashiga,
Kallo d’aya yayi mata yad’auke kansa tare da d’aure fuska yace kitaso muje, gabantane yafad’i a tsorace tace ina zamu? Hawaye suka fara zarya daga idanuwanta tace mummy ta ce ba zata zauna da ni ba ko? Daman nasan sai hakan ta kasance,
cikin tsawa fahad yace nace miki kitaso, Amina a tsorace tatashi tabi bayansa yana gaba tana biye da shi ganin sun nufi hanyar d’akin mummy yasa gabanta yafad’i tsaye tayi takasa shiga saidai hawaye kawai da take,
Ganin haka yasa fahad yarik’o hannunta tare da bud’e d’akin cikin sanyin jiki yayi sallama lokacin mummy tana zaune saman gadonta ta buga tagumi, jin muryarsa yasa tak’ara had’e rai cikin 6acin rai tace me kazo yi min a d’aki? ku fitar min daga d’aki
Amina ta tsorata sosai tana shirin juyawa dasauri fahad yarik’eta tare da girgiza mata kai alamun a’a, janta yayi sukaje gaban mummy suka tsugunna, wani mugun kallo mummy tajefesu da shi dasauri Amina tak’ara sunne kanta a tsorace take kamar ace ket tazunduma aguje,
fahad bai damu da kallon da mummy take yi masaba cikin marairaicewa tare da kwantar da murya yafara magana yace mummyna dan Allah kiyi hak’uri wlh ba a son ranmu haka ta kasance ba *k’addara ce* kawai da tsautsayi kar kimance Allah yana yarabtar bawansa ta kowace hanya domin yagwada k’arfin imaninsa, mummyna hankalina ba zai ta6a kwanciya ba indai kina fushi da ni dan Allah kiyi hak’uri kallon Amina yayi da taketa kuka yace kitaimaka ki kar6i wannan marainiyar wlh itama ba a son ranta hakan ta kasance ba kiduba kiga halin da tashiga duk nine silar gur6acewar farin cikin rayuwarta,
Dasauri mummy ta d’aga mashi hannu tace ya isa banason dogon lafazinka kutashi kuje kubani waje kuje kuyi yadda kuke so da rayuwarku, inkuma farin cikina kakeso toh dole karabu da ita ka auri ‘yar uwarka salma,
Kusan lokaci guda fahad da Amina suka d’ago kai suka kalleta kowa fuskarsa d’auke da mamaki, fahad ya tsorata sosai da jin kalaman mummy domin bai d’auka 6acin ranta ya kai hakaba, dasauri Amina tafad’a jikin fahad tare da fashewa da sabon kuka tabbas tasan fahad rabuwa zai yi da ita, fahad rasa bakin magana yayi kallon mummy kawai yakeyi domin ya rasa meke masa dad’i a ransa, itama mummy kallonsa take domin jin amsar da zai bata, ita kanta Amina da take kuka jira take taji maganar da zata fito daga bakin fahad.
daidai lokacin aka bud’e k’ofar d’akin dasauri duk suka juya suka kalli k’ofar domin suga kowanene, mamakine duk yabayyana a fuskarsu hatta ita kanta mummy………