K’ADDARA CE CHAPTER 14 KARSHE
Bayan sati biyu su Amina suka gama exams d’insu ran asabar gaba d’ayansu harda su Aunty khairat suka kama hanyar katsina a cikin family car d’insu fahad ne yake driving, zuciyar kowa cike da farinciki sai wajen k’arfe d’aya suka shiga garin katsina, wani irin sanyi taji ya ratsata lokacin da tashak’i iskar garinsu, saida suka tsaya sukayi sallah su daddy masallaci sukaje sukuma su mummy suka shiga wani gida sukayi sallah, bayan sun gama takeaway suka biya sukayo saida kowa yaci yak’oshi sannan suka kama hanyar mashi cikin rabin awa suka isa garin mashi, nan gaban Amina yafara fad’uwa nuna masa hanyar da zaibi tashiga yi, koda garin duk ya canza mata saboda sabbin gine-ginen da akayi ammah hakan baisa ta kasa gane hanyar da zata kaita gidansuba, suna zuwa round about tsayawa sukayi arage cunkoso saboda cunkoson hanyar kasancewar ranar suke cin kasuwarsu ‘yan garin.
Gefe guda kuma ‘yan sepa ne suke ta shara , tsaki daddy yaja yace su wad’annan basusan lokacin da ake aikiba ace sai yanzu suke shara abinda akeyi tun asuba, fahad kallonsa yakai ga masu sharar har ya janye idonsa dasauri yak’ara kallonsu saida gabansa yafad’i ba kowa bane yagani face cinnaka dasauri fahad yabud’e motar yafita tare da cema su daddy ina zuwa, wajen cinnaka yanufa da yake tura Barrow cike da shara, fahad cikin murna yace cinnaka da sauri cinnaka yakallosa jin ankirasa da sunan da yarabu da shi kusan shekara biyu da suka wuce, kallon fahad yake fuskarsa cike da mamaki ammah ya kasa gane inda yasan wannan fuskar,
ganin haka yasa fahad yace nine fa fahad, shidai cinnaka bai dai ganeba, ganin haka yasa fahad yayi murmushi yace babban yaro, dasauri cinnaka yawullar da Barrow d’in tare da rungume fahad cikin jin dad’i yace fahad daman kana duniyar? Kaine kakoma haka? Murmushi fahad yayi yace nine, ina su ogah?
Dasauri cinnaka yakai dubansa ga wanda yaketa shara yace zayyana! Wanda aka kira da zayyana d’ago kai yayi yana kallonsu cike da mamaki, yafutosa da hannu cinnaka yayi dasauri ya iso wajen, nunasa cinnaka yayi yace babban yaro ga kwaro nan, kallon wanda aka kira da k’waro yayi fuskarsa cike da mamaki ganin yadda fuskarsa ta cika da k’asumba duk wuya ta kod’ar da shi, nunasa da yatsa kwaro yayi yace babban yaro anya kaine? Kallon cinnaka yayi yace gambo wannan ba babban yaro bane,
cikin murna cinnaka yace wlh babban yarone, rungumesa kwaro yayi tare da fashewa da kuka yace babban yaro kaine kakoma haka? Ashe zamu sake had’uwa kaga yadda rayuwa takoma mana ko? Fahad yace ina su ogah da cha6o? Nan yaga fuskarsu ta canza daga murnar da suke damuwa tabayyana a fuskarsu shuru sukayi basu amsa masaba ganin haka yasa fahad yak’ara tambayarsu,
Kwarone yabud’e baki d’ayar yace babban yaro bayan tafiyarka da sati biyu su ogah da cha6o sukaje yin sata gidan wani Alhaji lokacin bai dad’e da dawowa garinba, sukace yabasu kud’i nan Alhajin yayi musu gardama suka harbesa da bindinga suka kwaso mak’udan kud’i daga baya asirinsu yatonu saboda cha6o wajen kwaso kud’in yamance wayarsa, ta wayar aka ganemu aka kamamu dukanmu watanmu biyar a gidan yari anata shari’a daga k’arshe aka yanke ma ogah da cha6o hukuncin kisa , mu kuma akayi mana d’aurin shekara guda bayan shekara d’aya aka sallamemu shine muka shiryu muka samu wannan aikin sepa d’in muna yi, da ita muke ciyar da kanmu.
STORY CONTINUES BELOW

Fahad mutuwar su ogah ta girgizashi ammah ya yi murna sosai da shiryuwar su kwaro, sai lokacin yatuna da su daddy kallonsa yakai ga motar yaga dukkansu sun zuba masu ido suna kallonsa fuskarsu cike da mamaki ganin mutanen da yake magana da su kamar almajirai, fahad kallonsu kwaro yayi yace kuzo kugaisa da iyayena tare nake da su,
cikin jin dad’i suka biyosa tundaga motar da suka nufa suka san fahad mai kud’ine ammah basuyi mamakin hakan ba saboda tun suna tare da shi sun karanci hakan tun daga kud’in da yake basu da yanayin komai nasa na manyan mutane ne, cikin girmamawa suka gaishe da su daddy, nan fahad yake gabatar dasu, mamakin ganinsu yakama su daddy domin sunji labarinsu wajen fahad, bayan sun gaisa daddy yad’auko 20k yabasu nan sukayita murna suna godia harda kukansu domin rabon da su rik’e ko da 5k ne har sun mance a rayuwarsu,
fahad ne ya lallashesu tare da d’auko card yabasu yace idan kun samu lokaci kuzo kaduna ga address da number d’ina nan, ahaka suka rabu suna ta godia.
Fahad yashiga mota nan yakeba su daddy labarin da yaji wajen su kwaro game da yadda rayuwa ta juya masu, mamaki duk yakamasu Daddy yace fahad kunga ikon Allah ko? _Ita rayuwa idan ka san farkonta toh bakasan k’arshenta ba saisa anason mutum yakasance yana aikata aiki na k’warai, ita zuciya idan kace zaka biye mata sai takaika tabaroka, duk abinda mukeso indai munsan ba alkhairi bane kuma ba na k’warai bane toh kar mubiye ma zuciyarmu duk yadda takwad’aitar da mu yakamata muyi yak’i da ita ita, domin Indai mukace zamu biye ma zuciyarmu toh zata kaimu tabaro ak’arshe kayi nadamar da batada amfani._
Gaba d’ayansu jikinsu ya yi sanyi sosai sukace hakane daddy mungode sosai Allah yasa mudace, daidai lokacin fahad yakawo gaban wani gida Wanda Amina ta nuna masa a matsayin gidansune, tun kafin a ida yin parking tabud’e murfin motar tafita dagudu ganin gidan gwaggo ladi a kulle Amina bataji dad’iba kan dole tashige gidansu ba ko sallama, ja tayi tatsaya ganin wata mata zaune tsakar gida tana wanki gefenta yarane biyu suna wasa, kallon-kallo suke da matar, Amina ce tafara magana tace ummah tana ciki? Cikin mamaki matar tace wacece ummah? Amina da mamaki yabayyana a fuskarta jin ana tambayarta ummah yasa tace mai gidan, matar tace ai nice mai gidan ko dai kina nufin wad’anda suka tashi daga nan, dasauri Amina tace eh, matar tace oh ai mun dad’e da siyan gidan daga wajensu sun koma nan bayan layinmu kad’an.
Mamakine yabayyana a fuskar Amina jin ance ummah ta siyar da gidansu na gado, dakyar tabud’e baki tace dan Allah ko zakisa arakani gidan? Matar d’anta tasa domin yarakata, godia Amina tayi ma matar tana fitowa zaure lokacin su mummy suna shirin shigowa nan take labarta musu abinda yafaru, su ma sunyi mamakin jin haka nan suka d’unguma suka nufi gidan da akace musu, Amina ta yi mamakin ganin gidan da akace ummah tana rayuwa ciki kallon yaron tayi tace ka tabbata nan ne? Yaron yace eh nan ne naira d’ari fatima tabashi nan yaruga yana ta murna,
Da sallama suka shiga gidan, wasu mutane suka gani a zaune gaban wata marar lafiya da take kwance dukkansu idanuwansu sunyi jawur saboda kukan da suka sha, kallonsu Amina takeyi d’aya bayan d’aya daga k’arshe ta safke idonta a fuskar d’aya daga cikinsu da takema kallon sani itama kallon Amina take tace wani kuke nemane? Dakyar Amina tabud’e baki tace ummah muke nema,
Sukace wace ummah? Tace matar marigayi Alh Ahmad, cikin mamaki matar tace wa nake gani kamar Amina kushigo mana, gaba d’ayansu suka shigo aka shinfid’a musu tabarma akayi ma su daddy iso su ma,
Amina tace ina ummah? Matan kuka tafara tare da nuni da wacce take kwance saman tabarma bata iya ko motsi, dasauri Amina tatashi tanufi inda take tatsugunna tabbas ko da matar ta canza ta San ummah ce, fashewa Amina tayi da kuka tace ummana kece kika koma haka? Matar dakyar tabud’e idanuwanta, da ka ganta kasan tana jin jiki murmushin k’arfin hali ummah tayi hawaye nan suka fara zuba daga idonta dakyar tabud’e baki tace Amina kece dagaske a gabana ko dai mafarki nake? Amina cikin kuka tace nice ummah, ummah tace kinga yadda nazama ko? Kinga yadda rayuwa tajuye min mutuwa yau ko gobe dan Allah kiyafe min, Amina cikin kuka tace ummah ba zaki mutuba insha Allahu zaki warke.
STORY CONTINUES BELOW

Ummah cikin kuka tace Amina na cutama rayuwarki dayawa duk wata matsala da kika shiga nice silar faruwarta, kiduba kiga yadda a k’arshe nak’are saidai akwantar atayar, kaichona ina tsoran had’uwata da ubangijina ga-don da yake mallakinkine nacinye gidanmu ma nasiyar, nacutar da mijina da kishiyata da marainiyar Allah tabbas nasan Allah ba zai yafemin ba,
dasauri Amina tatoshe mata baki tare da girgiza kai tace ummah dan Allah kidaina cewa haka ba a fidda k’auna daga rahamar ubangiji, ubangijinmu mai rahamane mai jin k’an bayinsa. Kuma abbah na tun ranar da zai rasu ya fad’amin ya yafe miki duk abinda kikayi masa kuma ya fad’amin mahaifiyata ma saida tace ta yafe miki, itama ce tarok’ar miki arzik’i akan yayafemiki shima, kawai dai sanine bakiyi ba, nima daman wlh tuni na yafe miki ummana cikin jin dad’i ummah tace nagode Amina Allah yasaka da alkhairi Allah yabiyaki,
Yayar ummah itama tana kuka tace Amina kiyafemin nima wlh duk abinda yafaru da sa hannuna a ciki, nan takwashe komai tafad’a musu har mafarin ciwon ummah da rashin kud’in da sukayi yasa tasiyar da gidan ga-donsu suna yi mata magani kuma suna cin abinci aciki. Cikin kuka Amina tace wlh na yafe muku
Su Aunty khairat hatta ita kanta mummy kuka sukeyi.
Daddy da fahad saidai jimamin abun suke suna girgiza kai.
Ummah dakyar tad’aga hannunta mai lafiya tarik’o na Amina tana murmushin k’arfin hali tace Amina bayan tafiyarki dangin mahaifiyarki sun samu labarin rasuwar Alhaji shine sukazo tafiya da ke, dan Allah kije kinemosu kinemaar min gafararsu kije k’auyen…. daga nan kitambayi gidan malam sanusi mai tafsir shine kakanki, dan Allah kiyafe min domin nasan kwanana ya k’are, nan ummah tafara tari daga nan sai aman jini nan da nan tafita hayyacinta, ganin haka yasa duk suka rud’e daddy yace sufito da ita akaita asibiti. Amina tana rik’e da ita tana kuka tace ummah zaki warke insha Allahu bari mukaiki asibiti, cikin kakarin mutuwa ummah ta girgiza kai dakyar ta bud’e baki ta iya cewa a’a kubarni kar ku wahalar da kanku ni kwanana ya k’are nan ummah tafara kalmatush-shahada idanuwanta suka kafe.
Gaba d’aya suka d’au ihu suna kuka, saboda mutuwar ummah ta girgiza kowa hatta su mummy, saida daddy yayi musu nasiha tare da kwad’aitar da su tayata murnar cikawa da imani da tasamu tayi, sannan sukayi shuru suna mata addu’a, d’an uwanta aka kira nan yafad’a ma mutane akazo aka sitirtata aka kaita gidanta na gaskiya, Allahu Akhbar kullunafsin za’ik’atul maut _(jama’a kunji yadda k’arshen ummah yakasance daman ita rayuwa haka take duk abinda kaga mutum yana aikatawa marar kyau kada ka aibatashi domin bakasan yadda k’arshensa zai kasance ba, duk mugun aikin da mutum yake idan Allah yasa yana da rabon shiryuwa toh ko da yana a ga6ar mutuwane sai ya shiryuwa, saisa akeso duk abinda kaga mutum yana aikatawa in baka iya masa nasiha toh kayi masa fatar shiriya ammah kar ka aibatashi, Allah yasa mudace. *TUNATARWACE WANNAN👌*)_
Daddy kud’i yabasu sosai yace asiyo kayan abinci, saida marece sannan suka tashi sukayi musu sallama tare da alk’awalin zasu dawo gobe nan akayi ta musu godiya, kwatancen k’auyen su mamar Amina akayi musu suka bi hanya suna tafiya, cikin minti goma suka isa kasancewar baida nisa sosai, kallon mutanen cikin rugar suke duk fulanine sai kallon motarsu mutanen rugar sukeyi, wani yaro suka tambaya gidan malam sanusi mai tafsir nan yaron yayi musu nuni da wani gida, fahad 200 yazaro yaba yaron, yaron yana ta murna yakar6a tare da yin godia, k’ofar wani babban gida ginin k’asa suka tsaya ko da duk gine-ginen k’auyen na k’asane, fitowa sukayi daga motar daidai lokacin wata mata ta fito daga gidan tana d’auke da k’warya saman kanta ganin Amina yasa tasaki k’waryar a tsorace tace hannatu kaine kadawo daman baka mutuba? Ko fatarwashe kayo mini, dagudu takoma cikin gidan,
Tsaye sukayi cirko cirko daidai lokacin wani tsoho yafito daga gidan yana cewa binto ina kikaga fatarwarshi. wadda aka kira da binto tana bayansa a la6e tace baffa ka ganshinan aradu shine, baffa yace kai banshon..maganarce tamak’ale a bakinsa lokacin da yakai idonsa ga Amina da take ta kuka shima ya firgita da ganinta yace eh ‘yar nan aradu kinyi gashkiya wannan yana kama da hannatuna, Amina cikin kuka tace baffa nice Amina d’iyarta, dasauri baffa yarungumota yace ‘yar nan daman kana duniyar shine baka nememuba? Amina kasa magana tayi saidai kuka, kallonsu daddy yayi yace shannunku da zuwa nan suka gaishesa gaba d’ayansu, ganin mutane sun fara zagayesu suna kallo yasa yace kushigo kdaga ciki mana,
STORY CONTINUES BELOW

Basuyi musuba suka shiga, gidan babbah ne sosai yana d’auke da part part sama da goma da ka gani ka san family house ne, wani part yanufa da su inda wata dattijuya take zaune gaban wani d’aki tana yankan farce, wajen yana da girma sosai ko’ina tsaf, da sallama suka shiga cikin fara’a ta amsa musu suka shigo, ganin Amina yasa tsohuwar itama ta tsorata tafara murza ido tana cewa wa’innahu salaimanu Malam aradu nayi gamo kad’auko ruwan addu’an da kake ajewa kabani insha aradu hannatu she yayi mani fatalwa, yanayin yadda tayi maganar ta basu dariya, Malam yace delu wannan ai d’iyar hannatune wanda yamutu yabari, tsohuwar fashewa tayi da kuka tace d’annan ashe rai kanga rai? Jawo Amina tayi tarungume tana kuka itama Aminar kuka take baffa dakansa yad’auko k’atuwar tabarma mai tsafta yashinfid’a masu daddy suka zauna nan aka shiga gaisawa kan acemi gidan ya cika da dangi saboda binto duk tafad’a musu zuwan d’iyar hannatu, wad’anda sukaje kiwo da gona kuma tuni labari ya kai musu daga mutanen karkarar, nan kowa ya hallara aka fara murna da koke-koke, daddy dakansa yagabatar dasu yafad’a masu matsayinsu a wajen Amina sannan yasa Amina tabasu labarin rayuwarta, nan gida yarikice daga masu koke-koke sai masu salallami,
Baffa yace delu kinga abinda nake gudu ko? Shiyasa naso abamu ita bayan rasuwar hannatu ammah mutanen nan sukak’i aradu wannan matar uban naka bayada kirki shine silar rashin zuwanmu duboki dan Allah kayafe mana domin mun tauye hak’ink’a saboda kina da hak’k’i akanmu na kula da ke, ammah muka watsar aradu ba a son ranmu hakan yakasance ba, cikin kuka tsohuwar tace kayafe mana aradu wannan matar shine silar faruwan haka, taje itada Allah.
Cikin kuka Amina tace na yafe muku wlh ban rik’ekuba daman, saidai dan Allah ina neman alfarma d’aya kuyafe ma ummah….nan takwashe labarin halin da tasamu ummah da mutuwarta tafad’a masu, su ma sun girgiza da jin mutuwar ummah nan sukace su ma sunyafe mata duniya da lahira nan sukayi mata addu’a, su daddy sun jinjina ma hak’uri irin na dangin Amina tabbas sunsan wajensu tagado hak’uri. Godia sukayi ma su daddy akan rik’on da sukayi ma Amina tare da jimamin halin da tashiga, nan suka dinga nan-nan da Ameerah da jawahir tare da yi musu addu’an zaman lafiya acikin aurensu, ahaka akacigaba da gabatar ma Amina da dangin mahaifiyarta maza ukku da mata biyu sai ‘ya’yansu da duk sunyi aure yawancinsu kuma auren zumunci sukayi,
jin Kiran sallah ne yasa kowa yatashi mazan sukayi alwallah sukatafi masallaci matan kuma sukayi sallarsu a gida, bayan sun dawo fura mai kyau damamma wadda taji nono aka kawo musu tare da tuwon dawa miyar ku6ewar da yasha kifi da man shanu, nan su daddy suka ci suka k’oshi cike da mamakin karamcin gidan da iya girkinsu, 6angare d’aya baffa yasa aka gyara musu fes d’akuna biyune a 6angaren sai toilet, tsintsiyar k’amshi aka kunna nan d’akunan suka d’au k”amshi sai aka kunna masu fitilar kwai (aci balbal) , su kuma ‘yan matan d’aki guda a 6angaren kakarsu Amina aka gyara musu, bayan sunyi sallar isha’i baffa yace suje sukwanta saboda gajiya nan daddy da mummy sai fahad sukayi musu bankwana suka nufi 6angaren da aka basu tsarin gidan da tsaftar mutanen gidan ya burgesu,
Su Amina da salma da fatima suka zauna suna hira da ‘yar tsohuwa innah sai wasu ‘yan mata tsararrakinsu su ukku(safara’u jummai da hajara) sai Aunty khairat, cike da jin dad’i sai wajen k’arfe tara sukayi sallama suka nufi makwancinsu.
Bayan sunyi sallar asuba baccinsu suka koma kasancewar duk agajiye suke sai wajen k’arfe tara suka tashi sukayi wanka suka shirya, baffa dakansa yaje kiransu daddy bayan sun gaisa suka d’unguma suka fito domin yin breakfast a tsakar gidan suka tadda manyan tabarmi an shinfid’a mutane duk sun fito nan suka zauna aka aje masu kunun gyad’a da kunun kanwa sai k’osai da fanke nan su daddy suka zuba, kowa cin nasa yake ba ruwan kowa da kowa yanayin tsarin gidan ya burge su fahad, bayan sun gama nan sukayi musu sallama sukace zasuje wajen gaisuwar ummah sai zuwa anjima zasu dawo har bakin mota su baffa suka rakasu sukace suce suna musu gaisuwa insha Allahu da anjima suma zasu shigo.
Su daddy da suka isa suka gaisa tare da k’ara musu gaisuwa nan suka zauna suma suna amsar gaisuwa, su baffa bayan sallar azahar sukazo sukayi gaisuwa sai bayan la’asar suka koma,
Sai gab da magrib sannan suka bar gidan gaisuwar suka koma can k’auyen su baffa, suna isa alwallah sukayi suka wuce masallaci kasancewar magrib ta gabato, su ma su mummy cikin gida suka shiga suka gaisa da su innah sannan suka wuce domin suyi sallah, sai bayan sallar isha’i sannan aka fito domin aci abinci dambune wanda yaji zogale sai fura wacce taji zuma aka kawo musu da kilishi nan suka ci suka k’oshi sannan aka hau hira gwanin sha’awa, sai wajen k’arfe goma sannan akayi bankwana kowa yatafi 6angarensa.
Haka su Amina suka kasance a k’auyen cike da jin dad’in zama tsawon kwana biyar, su safara’u suka shiga dasu gari domin subud’e ido, fahad ma d’an yayan hindatu shi yazama abokinsa tare suka shiga gari yanuna masa wurare, baffa shanuwa d’aya yasa aka yanka masu ana musu pepper kuma ana girki da naman, daren da zasu tafi har wajen k’arfe sha d’aya suna zaune suna hira da mutanen gidan,
Washe gari wajen k’arfe tara nasafe suka gama shirinsu nan suka fito sukayi breakfast nan ‘yan gida suka rakosu wajen motarsu duk basujin dad’in tafiyar da zasuyi, tsarabar nono, fura, zuma, man shanu da lallen gargajiya sai su kuka da ku6ewa da daudawa aka zuba masu a but d’in mota nan sukayi sallama cike da kewar juna suka amshi number d’in masu waya tare da musu alk’awalin idan Amina tahaihu zasuzo, godia sukayi masu sosai daddy 150k yabada nan akayita masa godia,
Saida suka biya gidansu Ummah suka k’ara yi masu gaisuwa dangin ummah suna ta yi masu godia tare da addu’a, sannan suka suka kama hanyar kaduna cike da kewar k’auyen su Amina, Sai wajen k’arfe biyu suka iso kaduna saida suka biya restaurant sukayo takeaway sannan suka wuce gida, nan kowa yanufi room d’insa cike da gajiya sukayi wanka suka gabatar da sallar azuhur…………
Agurguje bayan sati d’aya aka gama ginin gidan fahad, daddy yatsaida magana nan da three weeks Amina zata tare gidanta kuma a lokacin yakeso ayi ma fatima da salma baiko, murna wajen su fatima ba’a magana,+
Daddy kud’i yabayar sosai akayo ma Amina order na furnitures ‘yan Italian masu kyau da tsada duk wanda yagansu sai ya yi santi, mummy ma ba’a barta a bayaba kayan kitchen tayi mata nagani na fad’a.
Fahad shima Aunty khairat yad’auka sukaje aka had’o lefe akwati 6 sets yahad’o mata sannan yayi ma Ameerah itama 2 sets, gaskiya ba k’arya ya kashe kud’i sosai wajen had’a lefen dan bai Zuba k’ananun kayaba duk abinda yasa masu tsada ne kowa ya jinjina ma namijin k’ok’arin da yayi,
Amina rasa bakin yi ma bayin Allahn nan godia tayi saidai kuka tare da yi musu addu’a
Aunty khairat d’auke Amina tayi daga gidan tace ita zatasa ayi mata gyaran jiki a gidanta, duk yadda fahad yaso abar masa matarsa domin buk’ace yake da ita tun kafin suje katsina, ammah Aunty khairat tak’i kan dole yahak’ura yabarta.
Mummy duk ta fad’a ma danginta maganar Auren fahad bata 6oye masu komai ba duk saida suka jinjina ma lamarin tare da masu fatan alkhairi, mummyn salma ma hankalinta ya kwanta ganin yadda d’iyarta bata sa abun a rantaba kuma ta fitar da wanda zata aura nan itama tafara murna, ko da aka fitar da anko ta waya aka tura musu pics nasa, material da atamfa.
Amina gyara take sha sosai wajen mummy zill ‘yar maiduguri ce Aunty khairat tad’auko take mata gyaran jiki ba a d’ura mata komai saboda cikin da ke jikinta had’in kaza ne kawai take ci, kar kuso kuga yadda Amina takoma ta yi gwanin kyau, ta yi jawur, fatarta sai shining take jikinta very smooth kamar na jariri sai kace idan aka latsa jini zai zuba,
Fahad wasa wasa sai da yayi kusan 1 week bai sa Amina a ido ba, gaba d’aya Aunty khairat hanata fitowa take idan yazo shi abun har mamaki yake basa ya yi magiya har ya gaji ya barta, tsakaninsu saidai suyi waya cike da kewar juna, wayarma ba kowane lokaci Amina take d’auka.
Daddy kati yasa aka bugo domin cewa yayi sai ank’ara d’aura aure saboda mutane sushaida da auren su-ma.
Fahad babu wanda yasan maganar aurensa da yayi a abokansa sai yusuf kawai dan haka yasanar da sauran friends d’insa auren da zaiyi very soon sunyi mamaki sosai da jin haka ammah daga baya suka daina damun kansu dan sunsan halin fahad yin hakan k’aramin aikinsa ne, nan suka shirya masa dinner da za’ayi daren d’aurin aure.
Amina k’awarta murja takira tace mata yau tana nan tafe gidansu, murja murna tayi duk ‘yan gidansu saida tafad’a musu zuwan da Amina zatayi kasancewar duk sunajin labarin Amina a wajenta ammah bata ta6a zuwa gidan ba.
Ko da ta iso dagudu Murja ta taryota takaita d’aki tunda suka zauna kallon Amina kawai take cike da mamakin chanjin da tayi, saida Amina tabugota tace kallonfa? Murmushi murja tayi tace bari dai indawo sai muyi magana tashi tayi taje takawo ma Amina kayan ciye-ciye da tand’e-tand’e, ruwa kawai Amina tasha har lokacin murja kallonta take, tace kai friendy kallon bai k’areba har yanzu? Murmushi murja tayi tace wai miye sirrin ‘yanmata nagankine kin koma saikace wata amarya, harararta Amina tayi tace da bakisan amaryar bace?
Murja tace haba ta wasa ba.
Amina bata tanka mataba tajawo hand bag d’inta tad’auko invitation card tamik’a mata,
Batare da ta dubaba tace fatima ce zata aure halan?
Murmushi Amina tayi tace kiduba kigani mana,
Zumbur murja tayi tatashi daga zaunen da take tace friendy dagaske kece zakiyi aure? Shine baki fad’amin ba sai yau?, wlh baki kyauta min ba,
Amina tace dan Allah kiyi hak’uri wlh abun ne yazo too late nima ba a son raina hakan takasance ba,
Dogon numfashi murja taja tace shikenan friendy na fahimceki Allah yasa alkhairi Allah yakaimu lokacin, toh yanzu ya za’ayi da sauran classmate.
STORY CONTINUES BELOW

Amina tace just forget about them, ba sai sun saniba zan dai fad’a musu ta waya tunda kinga bamusan gidajensuba, ni bana ma buk’atar zuwan k’awaye kema dan kin zama dole ne saisa kika sani.
Harararta murja tayi tace wlh da baki fad’a min ba da sai anjimu.
Dariya Amina tayi tace ai daman nasan halin kayana. Yauwa tashi kirakani mugaisa da su mami, tashi murja tayi tace ni kinga ma na shafa’a wlh.
Ko da sukaje d’akin mami cikin fara’a da sakin fuska suka gaisa da Amina tare da tambayarta mutanen gida, nan murja take fad’ama mami Auren da Amina zatayi cikin jin dad’i mami tayi mata Allah yasa alkhairi.
Ko da suka fito murja cewa tayi muje kigaisa da kakus, Dariya Amina tayi tace toh ta wajen kakus muje mugaisa.
‘Dakin kakus suka nufa, murja tad’age labulen tace kakus ga k’awata nakawo miki yau dai kugaisa, cikin fara’a Amina tace Assalamu…. maganarce tamak’ale a bakinta ganin tsohuwar da tafitar da rai da sake ganinta, itama kakus kallon sani take mata, nan suka zuba ma juna ido, nunata da yatsa Amina tayi tace innah ladi kece dagaske? Dagudu taje tafad’a jikinta tare da fashewa da kuka tace innah ladi nice Aminarki, tsohuwar rungumeta tayi itama tafashe da kuka tace Amina daman kina duniyar? Ina kika shiga tsawon wannan lokacin Ina ta nemanki, shine kika gujeni? Ina d’iyarki take?
Lokaci guda innah ladi tajero mata wad’annan tambayoyin,
Murja tsaye tayi sororo tana kallonsu ahankali tatako tazo inda suke tace kakus kar dai kice min wannan ce Aminarki da kike bamu labarinta?
Cikin kuka kakus tace d’iyarnan itace mana wlh itace Aminata.
Murja fashewa tayi da kuka cike da tausayin Amina tare da rungumeta tace k’awata saisa nakejinki har cikin raina ashe kece Aminar da kakus take bamu labari, itama Amina kukan take tana rungume da innah ladi,
Koke-kokensu ne mami tajiyo yasa tafito tazo d’akin, cikin mamaki take kallonsu duk suna kuka tace wai me yake faruwa ne haka? Cikin kuka murja tace mami wannan itace Aminar da kaka take bamu labarinta, mami ma mamaki yakamata tace ikon Allah, lallai daman haka rayuwartake yanzu dai muzauna muji yadda takasance Allah yataimaketa har takawo wannan matsayin.
Dukkansu waje suka samu suka zauna tare da share hawayen fuskarsu kowa ya k’osa yaji labarin Amina,
Nan Amina takwashe labarinta tabasu tun daga lokacin da ummah takoreta har zuwanta gidansu fahad, da labarin zuwanta katsina da nutuwar ummah har ganin danginta da tayi da aurensu da fahad babu abinda ta6oye musu.
Duk saida sukayi mata kuka saboda tausayi, cikin kuka innah ladi tace Allah nasan wannan matar banzar daman ba zata barkiba, ammah bakomai hakan ma Alhmdllh da d’aukakar da Allah yayi miki, ita kuma Allah yajik’anta da rahamarsa, gaba d’ayansu sukace Ameen.
Amina kallon innah ladi tayi tace toh ke innah ya akayi kika dawo nan garin da zama? Innah ladi tace bayan tafiyarki da wata biyu d’ana yazo yad’aukeni yamaidoni nan, murja ai jikatace,
Cikin Jin dad’i Amina tace gaskiya naji dad’i da nak’ara sa ki a ido innata,
Daga nan suka zauna suka sha hira sai bayan sallar magrib da daddyn murja yadawo suka gaisa shima cike da Jin dad’in ganinta tare da jinjina labarinta da yaji sai da taci abinci sannan akasa driver yamaidata gida kyautuka iri-iri tasamu wajen bayin Allahn nan tare da yi mata alk’awali ran juma’a zasuzo sugaisa da su mummy.
Ko da takoma gida nan take ba Aunty khairat labari, itama Aunty khairat ta ji dad’in hakan nan suka kira su mummy suka fad’a musu har zuwan da su innah ladi zasuyi ran juma’a, su mummy ma sunyi murna sosai da jin labarin tare da addu’ar Allah yakaimu jibi lafiya kasancewar yau laraba.
Ran juma’a tun da safe Amina itada Aunty khairat suka shirya sukazo gida nan suka tadda ana ta hidimar tarbar bak’i suma suka taya akayi da su, fahad duk yadda yaso yake6e da Amina ammh Aunty khairat ta hana, ido tasama duk wani motsi nasa kan dole yahak’ura yabarta,
STORY CONTINUES BELOW

Daddy tunda yadawo sallar juma’a bai wuce ko’inaba gida yadawo saboda bak’in da za’ayi,
Bayan sallar la’asar murja takira wayar Amina tace gasunan a k’ofar gidansu,
nan Amina take fad’ama mummy gaba d’ayansu suka fita suka tarosu, Amina innah ladi tarungume cike da jin dad’i,
A sitting room aka kaisu nan da nan aka cikasu da kayan ciye-ciye, bayan sun kammala nan aka hau hira, innah ladi godia tayi ma su mummy sosai akan rik’on da sukayi ma Amina, nan aka kawo mata Ameerah ta yi mamakin ganin girmanta, Kallon fahad innah ladi tayi tace hala wannan shine angon nawa? Dariya fahad yayi yace nine fa uwargidata daga ke ba k’ari, babah ladi tace yauwa mijin ai daman nasan ni kad’aice me zakayi da wannan mummunar bayan kanada ni, gaba d’ayansu sukasa dariya,
Murja tace haba kakus ga sabon gani me za’ayi da wadda tazama chus, daddyn murja dak’uwa yayi mata yace uwartawa ce chus kuma? Dasauri tagirgiza kai tace a’a daddy, dariya akasa gaba d’aya d’akin daganan kuma aka hau hira nan da nan suka shak’u da juna, sai bayan sallar isha’i sannan suka bar gidan, gaba d’aya gidan sukayi masu rakiya tare da cikasu da kayan tsaraba,nan akayi exchanging d’in number tsakaninsu, cike da farin ciki suka rabu da juna.
Aunty khairat ma Amina tad’auka sukabar gidan, fahad ba yarda ya iya dole yahak’ura.
____________________
Awana atashi babu waya a wajen Allah tun saura sati bikki dangin mummy da na daddy sukazo kd, nan aka fara hidimar bikki cike da farin ciki ,
yau kasancewar ranar Alhamis ne kuma ranar aka wa’azi tun da safe su salma sukaje gidan Aunty khairat domin shirye-shiryen kayan da zasu raba ma jama’a, murja ma kayanta tattaro tadawo gidan Aunty khairat tace har sai angama bikkin k’awarta zata koma gida,
Shirye-shirye sukeyi sosai a gidan kasancewar a nan za ayi wa’azin kud’i suka biya akayo musu snacks,
Bayan sallar la’asar Amina shiryawa tayi cikin super wax yellow nd black colour d’inki ya kar6eta, makeup tayi ma kanta sosai kowa saida yayi mamakin kwalliyar da tayi ma kanta ta yi kyau sosai nan kyaunta yak’ara bayyana, bak’ar alkyabba wadda taji kwalliya tasaka daga sama, masha Allah kar kaso kaga had’uwa, nan dangin ango sukayita santin amarya, su ma ‘yan wa’azin ba’a barsu a bayaba anko d’in after drees bak’a sukayi.
Fahad Murja yakira tayi ma amarya pic’s sosai tatura ma,
Malama *Haleema H.@.S* suka kira tayi musu wa’azin aure mai ratsa zuciya, ba amarya ba hatta kansu mutanen da ke wajen wa’azin ya shigesu sosai nan akayita koke-koke, bayan angama wa’azin nan aka rabama mutane ledojin bikkin daga nan aka watse.
Washe gari Ranar Friday around 10:00am su Amina suka shirya da su Aunty khairat suka tafi wajen k’unshi da saloon kasancewar ranar ne za ayi dinner d’inta.
Wani k’ayataccen shago sukaje da’ita wanda babu abinda ba ayi indai 6angaren gyaran jikine wanda *Intelligent writer’s* sukayi had’in gwiwa suka bud’e a k’ark’ashin jagoranci *mummy zill nd hafsat umar*
6angaren *Ummun meenal nd mummyn Fadyl saloon* suka fara zuwa da zuwansu kuwa akafara mata saloon, har kusan 10:30am sannan aka kammala mata saloon d’in, bayan angama saloon sannan suka wuce 6angaren k’unshi inda *Zaynav mtz nd Habiba M* suka fara mata k’unshi na jan lalle da bak’i woww zokugansa afatar Amina kaman dama afatar yake ba zanasa akayiba, bayan angama mata lalle sannan aka wuce da ita 6angarensu *Mummyn Afrah nd meenat* akashiga mata gyara irin namu na mata saboda Aunty khairat tace so take tadawo kaman sabuwar budurwa,
Wankan dilka da kurkur akafara mata sannan akamata halawa bayan nan sannan sukamata wanka da ruwan lalle saboda sunce tinda tanada ciki bazasu mata na tsarki ba sundai mata turaren tsuguno, aranar dai acan suka wuni anafaman gyara Amina cikin awonni kad’an fatar ta tacanja tasulb’e sall takoma tamkar ta jariri sabon haihuwa ga laushi ga santsi gakuma had’adden lallen nan nata dayake kyalli,, saikusan 7:00pm sannan akafara mata make-up namusamman inda *Janaf nd Aufana* suka zauna suna tsantsara mata k’walliya kimanin 1hour da 15minutes akad’auka ana tsantsara mata had’adden make-up hmm zokuganta kuwa tamkar balarabiyar asali, wata had’addiyar wedding gown ce akabata tasaka wacca aka dinka da wani tsadadden material blue and silver colour rigar ta dinku sosai kuma taimata kyau sosai, rigar mai tsayice sosai har k’asa tana ja dak’asa d’ankwalin ta kuma silver colour ne wanda akasakawa stones blue colour anmasa nad’i mai kyan gaske mai step step,, takalmanta da jakarta colour d’aya ne silver mai ratsin blue kad’an asaman, takalman hie hils ne sosai, sarkanta na gold ne wanda Aunty khairat tasiyomata ab’oye batareda tasaniba sai yanzu tagani,.
STORY CONTINUES BELOW

Woww nikaina *Nerja’art* dana kalli Amina saida naji kishi saboda tsananin kyanda tayi kamar ka d’auketa ka gudu tamkar ‘yar tsana djk wanda yasan Amina ashekarun baya idan yaganta yanzu sam bazaitab’a shaidata saboda yanda tasauya kamar a inji akasakata aka canjata,.
Salma da fatima sai murja wayarsu suka kunna sukafara bama Amina pics hakama Aunty khairat pics d’in take d’aukanta saboda tsintsar kyanda tai,
Saikusan 8:00pm sannan suka kammala komai nasu ganin haka yasa Aunty khairat takira su fahad a waya saboda suzo sud’aukesu kasancewar 9:00pm dot za’afara gudanarda dinner d’in,.
Batafi 10minutes dakiransaba kuwa saigashi sun iso sunfaka wasu k’ayatattun motoci dalla dalla bak’ak’e sol guda uku, d’ayar ta tsakiya acikinta fahad yafito daga k’ofar baya,.
Sanye yake dawata dakakkiyar shaddah gizna mai tsadar gaske, silver colour ce wacca tasha aiki blue colour a babbar rigar takalmansa da hularsa ma silver colour, kai yai matuk’ar kyau sosai sai wani kyalli yake yanazuba wani daddad’an k’amshi, cikin wata tafiya mai cike da salo yake takawa har yak’arasa acikin shagon,.
Shima kansa fahad saida yarikice da yaga amina kallonta kawai yake b a k’ek’k’eutawa dariya su Aunty khairat sukeyi masa ammah baisan suna yiba direct wajen da Amina take yanufa itadai sunkuyar da kanta k’asa tayi saboda kunya nema yake ya rungumeta ganin haka yasa Aunty khairat tace kabiya kud’i domin shurun nan da naga ka k’yasa murmushi fahad yayi batare da yace komaiba yakai hannu cikin aljihunsa bandir d’in ‘yan one thousand ya aje ma masu gyaran, jiki yana kyarma suka d’au kud’in suna godia, jerawa sukayi suka fito gaba d’ayansu duk sunsha makeup, fahad motar da yafito suka shiga shida Amina kasancewar yusuf ne yake driving d’inta nan fatima ta bud’e gaban motar tashiga, inda su Aunty khairat suka shiga sauran motocin abokan fahad,
Fahad tunda suka shiga motar rungume yake da Amina ahankali yakai bakinsa saitin kunnenta yarad’a mata kinyi kyau sosai my wife, murmushi Amina tayi tace kaima haka my husby Shima fahad murmushi yayi Wanda yake k’ara bayyana kyawun fuskarsa, bakinsa yakai yana shirin kissing d’in lips d’inta dasauri Amina tajanye fuskarta tare da marairaicewa tace yaya fahad kwalliyata fa Zaka 6ata, fahad baice mata komaiba yakai fuskarsa a wuyanta yana shak’ar turarenta chan kuma sai yafara kissing d’in wuyanta ahankali, Amina kasa motsin kirki tayi bare ta hanasa, yusuf ne yakallesu ta mirror yayi gyaran murya dasauri Amina tajanye fahad daga jikinsa, tsaki fahad yayi tare da d’aure fuska sannan yace uban ‘yan sa ido kawai,bari kagane ma idonka haram,
Dariya yusuf yayi yace ai gudun kar inga haram d’inne natsaida malam dan naga kana nema kazak’e dayawa.
fahad banza yayi yakyalesa, Amina duk’ar da kanta tayi k’asa takasa d’agowa saboda kunya, fatima ko dariya kawai takeyi k’asa-k’asa gudun kar yayanta yajita dan tasan zai iya 6a66allata.
lokacin da suka iso mutane duk sun cika wajen amarya da ango kawai ake jira, wajen k’arshen tsaruwa ya tsaru kid’a sai tashi yake Dj alkon ne yafara magana da loudspeaker yana cewa kowa yagyara yanutsu ga amarya da ango nan sun iso.
su fatima duk fitowa sukayi suka jingina jikin motar, waya salma takira wata sister d’inta nan aka tafo da jawahir da Ameerah da sukasha gown d’insu sunyi kyau sosai.
bud’ema su Amina mota akayi suka fito, jerawa sukayi fahad yana rungume da amaryarsa abokansa suka jera bayansa inda su salma ma suka jera bayan Amina, Ameerah da jawahir ne akasa gaban amarya da ango ajere nan aka fara tafiya ahankali abun gwanin burgewa, mutane kallonsu suke cike da sha’awa, duk sun yaba kyau da dadacewar da ango da amarya sukayi nan camera man suka fara aikinsu, ahaka aka raka amarya da ango mazauninsu inda manyan abokansu suka zauna a gefensu, duk wanda yagansu sai sun burgesa, nan nahango masoyan amarya da ango irinsu……….. kai ba zan iya lissafasu ba sbd yawansu ammah dai ku d’innan dai nake nufi masoya😘, shagali akayi sosai inda abokan amarya da ango suka sha rawarsu sannan aka dakatar dasu inda aka kira ango da amarya domin suyi rawa dukkansu kasa rawar sukayi saida murja tazo tayima Amina rad’a a kunne sannan tafara takawa ahankali gwanin burgewa nan fahad yad’ebo kud’i yafara mata lik’i ahankali Amina tarik’o hannunsa tana d’an takawa nan mutane sukasa ihu abokansu suka fito suka fara musu lik’i nan aka fara ruwan kud’i daman abu ga masu naira,
Fahad gajiya yayi yaja amaryarsa suka koma gefe bayan angama cashewa nan aka kira amarya da ango suka yanka cake suka ciyar da juna nan akasa ta6i, sai wajen 11 sannan aka tashi daga dinner d’in nan akayi rabon jikkuna da calanders da sauran kaya, Amina taso tabi su Aunty khairat ammah fahad yak’i barinta yace shi zai maidata gida da kansa, dole tahak’ura saida suka gama gaisawa da jama’a sannan yad’auketa a motarsa da yakar6a hannun yusuf yamaida ta gida, ko da suka isa hanata fita yayi nan yajawota jikinsa yarungume yalalubo lips d’inta yafara kissing d’inta Amina kasa jurewa tayi nan itama tashiga maida masa nan duk suka fita hayyacinsu, fahad laluben zip d’in rigarta yafara yi yana shirin zage mata ganin haka yasa Amina taturesa tare da marairaicewa kamar zatayi kuka tace please yaya fahad kadaina, dakyar fahad yabud’e idonsa da suke a lumshe ciken dashewar murya yace please kibarni inyi, Amina cikin shagwa6a tace yaya fahad daga gobe fa shikenan sai yadda kayi da ni kaga fa kar… k’arar wayarsace tatsinke mata maganarta daganin Aunty khairat ce yasa yayi picking dasauri ko magana bai farayiba nan Aunty khairat tahau fad’a dan mi zai kai wannan lokacin bai maido Amina ba, murmushi yayi yace babbar yaya ga fa munan mun dawo, dogon numfashi taja sannan tace oya inganta ta shigo gida yanzu, bata jira Jin abinda zaya ceba takashe wayarta,
Murmushi fahad yayi sannan yabud’e ma Amina k’ofa saida sukayi bankwana sannan tafita, har saida tashiga gida sannan yatayar da motarsa yabar gidan cike da kewarta.
Amina tana shiga gida taci sa’a ba kowa parlour dan haka direct bedroom d’inta tanufa nan ta tadda murja har tayi bacci, murmushi Amina tayi sannan tashiga toilet tayi wanka bayan ta fito tayi shirin bacci itama nan takwanta cike da gajiya……
Yau gidajen guda biyu hidima akeyi sosai duk inda kaduba mutane ne,+
Da k’arfe biyu daidai aka d’aura auren Fahad da Amina inda mutane dayawa suka halacci d’aurin auren a chan tsskiyar jama’a nahango Fahad ya sha dakakkiyar shaddarsa fara ya yi kyau sosai sai fara’a yake yana gaisawa da jama’a, abokansa dadama sun hallari d’aurin aurensa.
anan kuma akayi baikon fatima da yusuf sai Salma da faruk daddy cewa yayi baiso asa dayawa dan haka 3 month’s kawai akasa,
Amina tana d’akinta a gidan Aunty khairat ta ci kwalliyarta ta yi kyau sosai su Murja duk suna gefenta su ma sunci kwalliya suna ta hira itakuma tana ta dannar waya.
Aunty khairat ma tana chan d’akinta tare da abokanta duk sunsha gayu anata shige da ficce,
Amina kallon salma tayi da tadage tana ta surutu, cikin tsokana tace k’anwata ba zakuje chan gidaba kukar6o mana kayan baikon muma muci? Harararta salma tayi tace lallaima yarinyar nan wacece k’anwarki kema ai kinsan nan duk mun girmeki, dariya Amina tayi tace yanzu kuma dole kubani girman saboda auren da nayi, kai ko ma bakomai ai ni matar yayankuce dole kugirmama ni, fatima ma harararta tayi tace sannu babba muma ai muna hanyar yin auren zamuji abinda akeji ko my sis? Salma tace barta kawai kuma ba zamu girmama ta d’inba agirme dai mun girmeki, Amina ta6e baki tayi ta d”aurewa fuska tace ohk dat’s gud, let me call him inyaso sai kufad’a masa cewa ba zaku cemin Aunty ba, kamar dagaske tafara dannar waya dasauri fatima tafizge wayar tace dan Allah Aunty kiyi hak’uri mun daina, salma ma cewa tayi haba Aunty Amina daga wasa kuma sai kimaida gaske? Ai ko kaka kikace kinaso zamu cemiki Ammah dan Allah kar kihad’a mu da wannan mijin naki dan wlh tsoransa nake sosai,
Amina batasan sadda dariya takufce mataba takalli murja da itama taketa faman dariya tace u c just for joking fa ammah luk at them yadda duk suka tsorata, fatima kallon salma tayi yadda duk tabi tamarairaice nan itama tabushe da dariya itama salma nan tasa dariya sukayi ta dariya chan da suka lafa Amina tad’aure fuska tace whatever ma dai dole ace min Aunty ko aga aiki da cikawa, dasauri fatima tace ai dolenmu ma muce miki ammah ko irin kunyarnan ta dangin ango ba a ji? Harararta salma tayi tace wace kunya mu da nan da 6 months za a haifo mana baby, Amina dasauri tamik’e zata bisu nan suka ruga aguje saida sukakai bakin k’ofa sannan sukace kibi dai ahankali kar kibama unborn baby d’inmu wahala, sannan suka fita daga d’akin, Amina komawa tayi takwanta hararar Murja tayi da taketa dariya sannan ta jawo wayarta tacigaba da dannawa,
Da marece sai ga classmates d’in Amina wad’anda suke gaisawa da su subiyar sukazo Amina ta yi mamakin zuwansu nan suke shaida mata ai murja ce tagaiyacesu Amina batayi mamakin jin hakanba dan tasan aikin murjane zata aika, sai abokan su fatima da sukazo dayawa su ma, nan aka kawo musu kayan ciye-ciye abinci kala-kala da drinks nan aka zauna akasha fira cike da jin dad’i.
STORY CONTINUES BELOW

Baba ladi da tazo jawo Amina tayi gefe guda tad’auko dafuwar naman kai tace gashi maza kicinye kisha romon Amina batayi gardama ba takar6a saboda cikinta daman maison kwad’ayine nan tazauna tacinyesa saboda baida yawa sosai, cikin jin dad’i innah ladi tace yauwa ko kefa, sanan tad’auko wani ruwan jik’on magani tabata tace amsa kisha wannan shima, Amina tsaye tayi tak’i kar6a tana kallonta itama innah ladi kallon nata takeyi tace kikar6a mana kintsaya kina ta kallona,
Yamutsa fuska Amina tayi tace innah bana iya shansa amai zai sa ni,
Salati innah ladi tayi tace kujimin sakarar yarinya ana so ataimaka miki yadda mijinki zai ji ki daidai ammah kice baki iya sha, to zauna nan wata ai ta kwace mikishi domin mace da gyara aka santa,
Dariya Amina tayi tace innah daga k’in shan magani sai ayimin k’wacen miji?
Kallonta innah take cike da mamaki tace wai Amina dagaske ba zaki sha ba?
Amina sunkuyar da kanta k’asa tayi tace innah ina fa da ciki,
Dafe k’irji innah tayi tace wai dagaske kike ko duk gudun maganin ne?
Cikin jin kunya Amina tace wlh innah dagaske nake;
Innah kasa cemata komai tayi tana ta kallonta sai chan tace toh shikenan Allah yasafkeki lafiya, kiyi hak’urin zaman aure dai, kibi mijinki sau da k’afa, kirik’e masa sirrinsa kikula da danginsa domin suma suna sonki sosai, kiguji abinda zai 6ata mashi da danginsa rai, Amina kirik’e maraicinki…. nan innah ladi tayi ta yi ma Amina nasiha mai ratsa jiki, Amina kuka kawai takeyi.
Bayan Sallar magrib Amina wanka tashiga tayo da ruwan turare mai k’amshi bayan ta fito Aunty khairat material saree tad’auko mata pink colour mai kyau sosai riga da skirt ne sai veil d’in kayan, mummy ce tasiya mata shi, ko da tasa nan kayan suka kar6eta kamar daman an aunata gaban dressing mirror tazauna nan su murja suka tsara mata kwalliya ta yi kyau sosai saikace a shago akayi mata, nan aka yafa mata gyalen a kai masha Allah nan kyaunta yak’ara bayyana ko ni kaina na yaba kyaun da tayi dan saikace ‘yar indiar nan kareena kapoor😜
Su ma su fatima kallonta kawai suke cike da sha’awa suna jinjina ma kyaun da Amina tayi, Aunty khairat ma ta yaba sosai da kwalliyar Amina, nan suka fito gaba d’ayansu suka shiga motochin da daddy ya aiko domin atafi dasu chan gida,
ko da suka isa fuskar Amina a rufe take nan mutane suka fara gud’a duk yadda sukaso abud’e musu fuskar amarya ammah Aunty khairat tak’i direct d’akin mummy ta wuce da ita lokacin mummy tana zaune da abokanta, kallonsu mummy tayi tace kaita d’akin daddynku gani nan zuwa, toh Aunty khairat tace sannan tafito da ita tanufi part d’in daddy da sallama suka shiga, k’asa Aunty khairat tazaunar da Amina itama ta zauna sai ga mummy ta shigo, bedroom d’in daddy tawuce tayo mai magana sai gasu sun fito tare nan suka zauna, Aunty khairat tace daddy mummy ga Amina nan ta zo neman yafiyarku
murmushi mummy tayi tace Allah yayafe mana gaba d’ayanmu ai mu tsakaninmu da Amina saidai addu’a domin ko da sau d’aya bata ta6a 6atamana ba, daddy jinjina kai yayi yace gaskiyarkifa hafsat
Amina hawaye kawai yake zuba daga idonta sai sheshek’ar kuka take,
Daddy yace Amina mu d’iya muka d’aukeki ba sirikaba, wlh da ke da su fahad duk matsayi d’aya muka d’aukeku dan haka nasihar da zanyi ma su fatima kokuma Ince wadda nayima khairat itace zanyi miki kiji tsoron Allah Amina, kibi mijinki sau da k’afa kikula da hak’in mijinki kirik’e sirrinsa banda fad’in sirrin mijinki, idan ya cutar dake ko yatauye miki hak’k’inki kifad’a mana domin mud’au mataki a kai domin ke amanace a garemu a kullum ina fad’a ma fahad haka, ku dai dinga hak’uri da juna, kiyi hak’uri da zaman Aure domin hak’urin ne yake kai mutum ga babban mataki, Aure ba abun wasa bane kina jina, Amina cikin kuka tace toh daddy,
Kallon mummy yayi yace kice wani abu kema, mummy ta bud’e baki zatayi magana kenan sai hawaye suka fara gangarowa daga fuskarta dasauri tasharesu sannan tace Amina kici gaba da hak’uri da tsaftar da nasanki da su, girki ma nasan ba bayaba dan haka kik’ara zage dantse, kiyi biyayyar Aure kizauna da mijinki lafiya domin aljannarki tana k’ark’ashin k’afarsa sai ya d’aga sannan zaki shiga dan haka ladabi da biyayya da hak’k’in miji kar kisakesu kiji tsoron Allah kirik’e ibadarki, idan fahad ya sa6a miki kikiramu kifad’a mana domin mune iyayenki a yanzu inkuma ba zaki iyaba toh ga yayarku nan khairat natabbata ita zata tsaya miki akan komai, Amina Aure ba abun wasa bane dan haka kimaida mijinki yazama abokin sirri da shawararki, Amina kiyafe mana muma mun.. kukan da mummy take 6oyewane yaci k’arfinta kasa k’arasa maganar tayi nan tayi shuru, ganin haka yasa daddy yakalli Aunty khairat itama da taketa share hawaye yace kutashi kutafi khairat Allah yabada zaman lafiya a dai yayyafe Amina, cikin kuka gwanin tausayi Amina tace daddy kuyafemin nagode sosai da karamcinku a gareni Allah yasaka muku da gidan Aljannah, Daddy yace Ameen ya rabb.
Rik’ota Aunty khairat tayi suka mik’e tsaye Amina kuka kawai take nan suka fara tafiya har sun kusan kai k’ofa Amina tafizge daga rik’on da Aunty khairat tayi mata taruga takoma tarungume mummy tana kuka itama mummy kukan kufce mata yayi nan sukayita kuka mai k’unar zuci,
Daddy Kallon Aunty khairat yayi yace janyeta kutafi, Aunty khairat dakyar ta janye Amina daga jikin mummy tanufo k’ofa da ita, Amina kuka takeyi kamar wadda aka aikoma da sak’on mutuwa, lokacin da suka fito mutane har sun fara shiga motoci dan haka motar da aka tanadar ma Amarya suka shiga har lokacin Amina kuka takeyi sosai _(nidai gefe nakoma ina Kallon ikon Allah nace fahad d’in saikace bak’ontane, uhm ba dai ruwana🤭)_
STORY CONTINUES BELOW

Dank’areren gate d’in gidan maigadi yawangame masu nan motocin kawo amarya sukayi ta shiga, masha Allah nace ganin hadad’d’en gida ammah d’an madaidaicine ko da ban shiga cikinsaba tun daga waje na san ya tsaru,
Amina tana kuka aka shiga da ita main parlour ne mai d’auke da d’akuna hud’u gaskiya ba laifi parlourn ya tsaru sosai ko da ba wata k’arya akayiba wajen zuba mata kayan ammah komai order d’insa daddy yasa akayi
‘Daya daga cikin d’akunan aka shiga da ita room nd bed room ne komai na ciki ash nd black colour ne direct bed room aka wuce da ita aka zaunar da ita,
nan mutane sukayita santin gidan da kayan da aka zuba mata itadai Amina tana lullu6e da gyalenta.
tanajin yadda suketa yaba tsarin gidan, saida suka gama ba ido hak’k’insa sannan sukayi mata sallama tare da yi musu addu’an zaman lafiya,
Aunty khairat ma saida tak’ara yi ma Amina nasiha sosai sannan taficce daga gidan,
Nan gida yarage daga Amina sai su murja, salma da fatima bakajin motsin komai sai kukan Amina,
Su fatima k’ara gyara gidan sukayi suka kunna turaren wuta nan da nan gidan yak’ara gaurayewa da turaren wuta sannan suka dawo d’akin Amina har lokacin kuka take nan suka zauna suka lallasheta aka samu tayi shuru,
Sai wajen k’arfe goma sannan fahad yashigo da abokansa nan suka k’ara yi musu nasiha tare da addu’an zaman lafiya daganan suka hau zaulayar Amarya su fatima suna kareta, shidai fahad yana tsaye sai dannar waya yake kamar baima san sunayiba,
Yusuf ne yakallesa yace toh ango mudai zamu wuce sannan yakalli su fatima yace muna jiranku a waje, fahad tafiya yayi yarakasu suna tayi masa shak’iyanci,
Bayan sun fita nan suma su fatima suka tashi suna kimtsawa, Amina marairaicewa tayi kamar zatayi kuka tace dan Allah kar kutafi, shuru sukayi suka kyaleta suma sunajin wani iri acikin zuciyarsu, dasauri tajawo fatima tarungume tare da fashewa da kuka tace dan Allah kar kutafi kubarni, itama fatima kamar jira take nan tarungume Amina tana kuka, su ma su murja kukan suka fara yi dasauri taja salma suka ficce daga d’akin a parlour suka tadda su yaya fahad nan suke fad’a masa Amina tana chan ta rik’e fatima.
Ko da fahad yashiga d’akin taddasu yayi rungume da juna suna ta kuka dakyar yasamu yajanye Amina daga jikin fatima yarungumeta kuka kawai take bilhak’i kamar wacce aka aikoma da sak’on mutuwa, ganin haka yasa fatima taficce daga d’akin tana kuka.
Fahad lallashinta yashiga yi dakyar yasamu tayi shuru sannan yazaunar da ita a saman gado shima yazauna yazuba mata ido yana kallonta, ganin haka yasa Amina tak’ara jawo gyalenta tarufe fuskarta, murmushi fahad yayi sannan yajawota jikinsa yarungumeta tare da d’aura hannunsa saman cikinta yana jin wani sanyi a ransa, itama Amina lumshe idonta tayi tana murmushi, fahad a kunnenta yafara mata rad’a yace meyasa kikeso ki6ata min kyakkyawan fuskarki? Ni fa nakine baidace ace lokacin da zamu kasance da junaba kina kuka ai abun farin cikine,
Shuru Amina tayi bata tanka masaba, fahad bai damu da shurun da tayiba yace kinyi sallar isha’I? Gyad’a masa kai tayi alamun eh
Yace toh masha Allah, kasancewar wanchan daren farkon ya wucemu ya zama tarihi, ammah duk da haka inaso kiyo alwallah muzo mugode ma Allah wannan damar da yabamu na kasancewarmu a tare, da kuma fatan aurenmu yakasance dauwamamme na har abada,
Amina janye jikinta tayi daga nasa tatashi tanufi toilet tad’auro alwallah, lokacin da tafito fahad har ya shinfid’a musu pray mat sannan shima yaje yad’auro alwallah yazo yajasu sallah raka’a biyu, yayi musu addu’a sosai sannan yakama kan Amina yayi mata addu’a,
Ko da yayi mata tambayoyi gme da addininta ga mamakinsa sai yaga tana bashi amsa daidai, Ko kuma baiyi mamakin kasancewar hakan daga garetaba dan yasan ba bayaba daman wajen kula da ibadarta,
Bayan sungama tashi yayi yaje kitchen yad’auko musu plate da cups sannan yadawo yazauna kusa da ita, ledar da yashigo da ita yajanyo bank’ararrun kajine manya guda biyu, d’aya yad’auka yasaka musu cikin plate d’in sannan yatsiyaya musu madarar holandia mai sanyi,
Dakansa yadinga ciyar da Amina saida yatabbatar da tak’oshi sannan shima yaci, bayan ya gama atare suka tattara kayan suka maida kitchen Amina Koda kallon tsoro tayi ma gidan ammah gaskiya ya burgeta,
STORY CONTINUES BELOW

Koda suka dawo d’aki fahad ya-so suyi wanka tare ammah Amina tak’i, kan dole yakyaleta yaje yayo wankansa, saida yafito sannan itama tashiga tayo lokacin da tafito yana sanye da boxer bata kalli inda yakeba tawuce gaban dressing mirrow, mai tafara shafawa bataji tafowarsaba kawai sai ji tayi ya rungumeta ta baya kallonta yake ta mirror itama tana kallonsa nan suka sakar ma juna murmushi, fahad hannu yakai yana shirin cire mata towel d’in da take d’aure da shi, dasauri Amina tarik’e tare da girgiza masa kai alamun a’a, murmushi fahad yayi sannan yazura harshensa a kunnenta yana mata tafiyar tsu-tsa daganan yagangaro a wuyenta nan Amina tafara fita hayyacinta batasan lokacin da fahad yarabata da towel d’in da yake jikintaba, ahankali yajuyo da ita yakai bakinsa cikin nata yafara tsotsa kamar wanda yasamu lollipop, hannuwansa suna a kan k’irjinta yana shafa itakuma ta sargafo hannuwanta a wuyansa nan da nan duk suka fita hayyacinsu ganin tsayuwar ba zatayi musuba yasa fahad yad’auketa yanufi gado da ita yana kwantar da ita, tashi yayi, dasauri Amina tajawosa yafad’o jikinta kallonta fahad yake cikin mamaki yace saikinja na ji ma unborn baby ciwo, Amina dai batace komai ba nan tazura harshenta cikin nasa dasauri fahad yacafke saida sukayi kusan 5 minutes a haka sannan fahad yajanye bakinsa yamaida akan k’irjinta itakuma tana ta faman yamutsa masa gashin kansa…. haka dai sukaita nuna ma juna soyayya daga nan kuma aka zarce, su kansu sunsan sunyi missing d’in juna, fahad sambatu kawai yake ma Amina duk ya fita hayyacinsa har Amina tagaji, abu dama ga mai ciki, ammah yak’i kyaleta tayi ta masa magiya ammah baisan inda hankalinsa yakeba kan dole tahak’ura tabarsa domin itama kanta tasan ya yi missing d’inta da yawa, a k’arshe dai bacci yayi awon gaba da ita saboda a gajiye take, saida yagaji dan kansa sannan yabarta.
Bayan komai ya lafa rungumeta yayi a jikinsa tana ta baccinta yanajin wani irin sanyi yana ratsasa son Amina yana k’ara shigarsa ahaka shima bacci yayi awon gaba dashi,
Kiran sallar asuba ne yatashesa daga baccin da yake janye Amina yayi daga jikinsa tare da gyara mata kwanciyarta sannan yawuce toilet yayo wanka tare da d’auro alwallah, saida yayi shirin tafiya masallaci sannan yatada Amina ammah tak’i tashi, blanket d’in da take cikinsa yajanye dasauri tabud’e idonta tare da jawo blanket d’in tarufe jikinta sannan tamaida idon talumshe, kallonta fahad yake yana murmushi sannan yace please my princesses wakeup it’s tym for prayer now, Amina yamutse fuska tayi tare da yin mik’a, ganin batada niyar tashi kuma gashi ana shirin kabbara sallah a masallaci yasa yajanye blanket d’in yad’auketa yanufi toilet da ita, Amina sai wulla-wullah da k’afa take, cikin shagwa6a tace please yaya fahad kasafkeni, fahad shareta yayi saidai jinta tayi cikin bahon ruwa, dasauri tabud’e idonta cikin shagwa6a kamar zatayi kuka tace please yaya fahad kabarni zanyi dakaina, fahad baice komai ba yaficce yanufi masallaci,
Tana ganin ya fita nan tayi wanka sosai sannan tayi wankan tsarki tare da d’aurd’auro alwallah bayan ta fito tajawo rigar baccinta doguwa tasaka sannan tasa hijab tagabatar da sallar asuba, a daddafe tayi sallar sbd wani irin bacci da takeji dakyar tasamu tayi addu’a sannan takwanta saman darduma d’in dan ji take ba ta ma iya tashi taje tahau gado,
Fahad bai dawo gidanba sai da gari yafara yin haske sannan yadawo, ganin Amina kwance saman darduma yasa yaje yad’auketa yamaidata saman gado shima yahau yakwanta tare da rungumota jikinsa.
Wajen k’arfe goma k’arar wayar Fahad ce ta tashesu, dakyar Fahad yabud’e idonsa yajawo wayar sunan Aunty khairat ne yabayyana a screen d’in wayar dasauri yayi picking, Amina juyawa tayi chan d’an 6angaren, Dakyar yabud’e baki yayi sallama daga chan 6angaren Aunty khairat ta amsa masa tare da cewa k’anena har ynz baku tashiba?
Fahad uhm kawai yace mata
tace ohk ga driver d’ina nan na aiko zai kawo muku breakfast karyazo yayi ta knocking bakujiba dat’s y nakiraka, yanzu ma i think ya kusa isowa tunda tun d’azun yatafo.
Fahad yace toh Aunty mungode, nan sukayi sallama yakashe wayar, duba time yayi yaga har 10 ta yi dan haka janye Amina yayi daga jikinsa tare da gyara mata kwanciyar sannan yabar d’akin.
Amina tana jin fitarsa tamik’e itama dasauri taje ta murza ma k’ofar key gyara bed d’it’a tayi sannan tak’ara kakka6e d’akin tagyara koda ba wani daud’a yayiba sannan takunne turaren wuta nan da nan d’akin yaturare da k’amshi
kayan jikinta tacire tashiga toilet tayi wanka bayan ta fito zama tayi ta tsantsara kwalliya tashafe jikinta da su humrah wajen wardrobe tanufa ko da tabud’e cike take da kaya wata atamfa tajawo sky blue riga da skirt tasaka kayan sunyi daidai da jikinta saidai skirt d’in ya kamata sosai, murza d’aurin kallabi tayi sannan tasaka sarka, feshe jikinta tayi da turaruka masu k’amshi, daidai lokacin taji ana knocking d’in k’ofa, saida tak’ara kallon kanta a mirror taga dai itama ta yaba da kyaun da tayi sannan taje tabud’e k’ofar tana bud’ewa takoma bayan kyaure ta6oye fahad sanye yake da boyel brown yai mashi kyau sosai kansa ba hula k’amshin turarensa kawai yake tashi cikin d’akin yashigo nan yafara waige-waige yana nemanta ganin haka yasa Amina tafito tare da rungumesa ta baya, murmushi fahad yayi sannan yajuyo da ita gabansa kallonta kawai yakeyi ya kasa janye idonsa daga gareta, ganin haka yasa Amina tasunkuyar da kanta k’asa cikin girmamawa ta gaishe, fahad bai amsa ba saima jawota da yayi jikinsa tare da tura hannunsa cikin rigarta yafara shafar cikinta kallonta yake cikin idonta yace my princess ya kika tashi, ya jikin naki dafatan ba ya ciwo? Baby na ma dafatan yana lafiya? Amina turo d’an k’aramin bakinta tayi cikin shagwa6a Tace ni da kawahalar da ni jiya, babynka ma ya wahala, dariya fahad yayi yace sowie ma princess nima ba a son raina na wahalar da ke ba duk kece ai kika ja ai, dariya Amina tayi tace saisa najika kana ta sumbatu jiya me ma kake cewa?, fahad zaro ido yayi yace ke bakida kunya daman? Dasauri Amina tarufe idonta da tafin hannunta taficce daga d’akin tana murmushi, fahad ma murmushi yayi sannan yabi bayanta a parlour yatarar da ita tsaye rik’o hannunta yayi sukanufi dining nan yajawo kujera yazauna tare da zaunar da Amina saman cinyarsa ita tayi serving d’insu nan suka fara ciyar da juna,
Saida suka tabbatar sun k’oshi sannan suka kwashe kwanukan suka kai kitchen dakyar Amina tasamu fahad yabarta ta wanke kwanukan da suka 6ata sannan suka dawo parlour a saman kujera suka baje Amina tana zaune fahad yakwanta saman cinyarta tare da d’age mata riga yana shafar cikinta ita dai Amina shagwa6a take ta zuba masa.
A ranar fahad babu inda yaje inma anga ya fita daga gidan toh masallaci zai je da yadawo kuma zai kasance manne da matarsa ko motsin kirki bai barinta tayi a ranar soyewa kawai suke kowa burinsa yafaranta ma d’an uwansa rai,
Lunch ma daga gidan Aunty khairat aka aiko musu da shi,
Bayan sallar isha’i Amina wanka tashiga tayo tashirya cikin nighty gown fara mai tsantsi har k’asa duk ta kama mata jiki, sannan tadawo parlour tazauba takunna kallo tana yi daidai lokacin fahad yafito daga room d’insa hannunsa rik’e da waya yana yi kusa da ita yazauna zuba masa ido tayi cike da so da k’auna yanayin yadda yake wayar yatabbatar mata da Aunty khairat yake wayar ji tayi ya ce gata toh Aunty, mik’a ma Amina wayar yayi takar6a cikin jin kunya tagaishe da Aunty khairat, daga chan 6angaren Aunty khairat tace k’anwata shine tun yanzu anfara mancewa da mu? Akunyace Amina tace a’a Aunty khairat wlh ban mance da ku ba,
Fahad tunda tafara wayar yake kallonta cike da so da k’auna yanayin yadda take wayar tana burgesa, ahankali yakai hannu bayanta yazage mata zip d’in rigarta, Amina dasauri ta kallesa tare da harararsa sannan tacigaba da magana da Aunty khairat,
Fahad bai damu da kallon da yaga tana masa ba, yasalu6e mata rigarta nan k’irjinta yabayya, bakinsa yakai akai, Amina turesa tashiga yi da hannu d’aya ammah takasa, yanayin yadda yake tsotsarsu saikace yaro yasa Amina tafara fita hayyacinta, Aunty khairat magana take mata ammah Amina batasan me take cemata ba saidai uhm take cema Aunty khairat, ak’arshe dai dakyar sukayi sallama takashe wayar, duka hannuwanta takai tana ture fahad daga jikinsa ammah takasa ganin haka yasa takyalesa yacigaba saida yamurjeta son ransa ko motsin kirki Amina kasawa tayi saida yatabbatar da itama ta zo hannu sannan yad’auketa yanufi bedroom d’insa asaman makeken bed d’insa suka yada zango _ganin haka nima najanyo musu k’ofa nace asuba tagari Mr nd Mrs fahad_
Fahad da Amina soyayyarsu sukesha ba kama hannun yaro, Fahad tuni ya koma bakin aikinsa ammah a kowane lokaci suna manne a waya cike da k’aunar juna, kowa burinsa yaga ya faranta ma d’an uwansa rai.
Amina duk abunda tasan zaisa Fahad farin ciki shitakeyi,
+
Su fatima sau biyu suna zuwa gidan Amina sukawo mata Ameerah taganta susha hira sai dare suke koma, Amina tanaso Ameerah tadawo hannunta da zama ammah ba ta iya magana saboda kunya takeji dan gani take idan ta amsheta bata kyautaba, ganin Fahad bai ta6a mata maganar ba itama taja bakinta tayi shuru.
After 1 month Amina takoma school Fahad dakansa yake kaita sannan yawuce wajen aiki, idan ta taso shi yake Zuwa yad’aukota idan yana da tym inkuma baisamu tym sai driver d’in su fatima yake maidata.
Akwana atashi babu wuya a wajen Allah cikin Amina sai k’ara girma yake fahad yana kula da ita sosai da abinda yake cikin nata, yanzu auren su Fatima saura 3 weeks hidima suke sosai basuda lokacin zama .
Yau kasancewar Asabar ne su fahad suna zaune a parlour Amina ta yi d’ai-d’aya a saman cinyarsa hannunta rik’e da littafi tana karatu, shi kuma fahad yana rik’e da remote yana canza channel, janye littafin tayi ta aje, gaba d’aya tamaida hankalinta wajen fahad cikin shagwa6a tace my hubby wai yaushe zan fara fita? Kaga fa kusan 2 months kenan da zuwana gidannan ammah babu inda nake zuwa sai school ko fa wajen su mummy ban jeba rabona da su tun bikki,
Fahad shuru yayi yakyaleta,
Amina bata damu da shurun da yayi domin ta san indai zata masa maganar fita toh ba ya tankata, tashi tayi zaune suna fuskantar juna tace dan Allah yaya fahad kakaini ingaisa da su mummy kuma fa d’azun da mukayi waya da fatima take cemin gobe za a kawo lefensu, ashema jiya ka je gidan kuma mummy ta fad’a maka shine baka fad’a min ba,
Kallonta fahad shima yake kamar ba zaiyi magana ba sai kuma chan yace eh anfad’a min ammah kiyi hak’uri ba yanzu zaki fara fitaba, su ma fa sunsan kema fama kike da kanki kina buk’atar hutu, kibari kawai sai kin haihu.
STORY CONTINUES BELOW

Amina takaici yacikata fashewa tayi da kuka tare da tashi taruga dagudu tashige bedroom d’inta tafad’a saman gado tacigaba da kuka, dasauri fahad yatashi yabita shima saman gadon yahau yadda take kukan yakejinsa har cikin ransa jawota yayi jikinsa yarungume yace my princess menene kuma na kuka a ciki? Ni fa banso kina wahala ne naga ga zuwa school ga hidimar gida ai kin gaji.
Sharesa Amina tayi tacigaba da kukanta,
Fahad k’ara rungumeta yayi yacigaba da lallashinta ammah Amina ko alamun daina kukan batada niyar yi,
Nan hankalin fahad ya ida tashi cikin damuwa yace dan Allah kidaina kukan hakanan indai batun gidane kishirya gobe sai muje,
Cikin kukan Amina tad’ago takallesa tace dagaske kake?
Murmurshi fahad yayi yace toh ya zanyi kishirya kawai sai muje,
Cikin jin dad’i Amina ta mak’ak’k’alesa tace thanks so much my hubby dat’s y I love you more Allah yabarmin kai duniya da lahira,
Dariya fahad yayi yace Ameen my princess, hannunsa yakai saman cikinta yace kin wahalar min da baby fa, Amina shagwa6e fuska tayi tace shi dai yake wahalar da ni, hancinta fahad yalakuce sannan yace ina fa sonsa da yawa, Amina rik’e hannun fahad tayi da yake saman cikinta tace nima inasonsa sosai saidai nafison mahaifinsu, murmurshi fahad yayi yace kin dai fad’ane kawai,
Itama Amina murmushin tayi tace yaya fahad bakasan yadda sonka yayi d’awainiya da ni ba, a lokacin ga cikin Ameerah ga yawan tunaninka yaya fahad da ace ban samekaba tabbas nasan ba zan rayuba domin tun ranar da naganka Sonka yashiga zuciyata sau dayawa idan nazauna ina tunani abbanah hankalinsa tashi yake sai yad’auka saboda abinda yafaru da ni ne haka zai zauna yana min nasiha nan ko baisan abinda yake cikin zuciyataba, domin a lokacin nasan ko da zaiji damuwata toh baida maganinta saima tada masa hankali da zanyi saisa nabar abun a raina, idanuwan Amina nan suka cika da k’wallah dasauri tajanyesu daga kallon fahad da take dan kar yagane,
Ganin haka yasa fahad yad’ago mata fuska cike da tausayi yace a rayuwata ban san mecece soyayyaba sai a kanki kuma bana fata inso wata bayanki saboda kece *ZA’BINA* da ke kad’ai nakeso inyi rayuwata, zan baki kulawa sannan insha Allahu ba zaki ta6a kuka da ni ba zan zame miki farin cikin rayuwarki.
Amina fashewa tayi da kuka tace nagode sosai yaya fahad,
Gudun kar tacigaba da kuka yasa fahad yazura bakinsa cikin nata yafara tsotsa cike da salon da yake rikita Amina, kan dole Amina tahad’iye kukan da take nan tabiye masa nan da nan suka fara fita hayyacinsu…….
Washe gari tun da wuri Amina tagama ayyukanta cike da d’okin gidan mummy da zasuje, wanka tashiga tayi tashirya cikin shadda gown purple colour wadda tasha aiki da farin zare, ba wata kwalliyar kirki tayiba ammah ta yi kyau sosai, babban veil ne fari tayafa a kafad’arta sannan tad’auko hand bag d’inta tarik’e tare da zura takalmanta high hills, ko da tafito parlour bataga fahad ba dan haka direct d’akinsa tanufa tana shiga tsaye tagansa gaban dressing mirror sanye yake da shaddarsa shima irin ta Amina hannunsa rik’e da perform yana fesawa, kallon juna sukayi tare da yi ma juna tattausan murmushi, ahankali Amina tataka taje wajensa tare da rungumesa shima rungumeta yayi yace kinyi kyau sosai my wife, Amina k’ara shigewa jikinsa tayi tace ai ban kaika yin kyauba my hobby, dariya fahad yayi yace kin ma fini dan ni har na fara tunanin tafiyarnan da zamuyi kar ayita kallemin ke anya ba fasawa zamuyi ba? Dasauri Amina tad’ago kai takallesa, d’aga mata gira yayi
Marairaicewa tayi kamar zatayi kuka tace please yaya fahad kar kayi min haka, kuma kasan nayi missing d’in su mummy sosai dan Allah kakaini ingansu.
Yanayin yadda tayi maganar taso taba fahad dariya, yace toh kar dai kiyi kuka ni wasa nake miki idan kin gama zo mutafi.
Cikin jin dad’i Amina tak’ara rungumarsa tare da sumbatarsa a kumatunsa, dariya tayi tace my hubby kaduba mirror kaga fuskarka
Murmushi fahad yayi yace banyi kyau bane?
Cikin dariya tace kaidai kaduba, yana kallon madubin me zai gani, sai ganin jambakin Amina a fuskarsa yayi, hannu yakai zai jawota dagudu tabar wajen tana dariya, fahad hankacif yad’auko yana gogewa yace zan kamaki yarinya, Amina tana dariya tace kabarsa mana muje haka,
Shuru yayi yakyaleta yacigaba da gogewa yace zamu had’e anjima ai.
Ko da suka shiga mota gaba d’aya glass d’in motar yarufe yace kar mutane suyita kallon min mata
Amina dariya kawai take masa.
Ko da suka isa gidan tun kan fahad ya ida parking tabud’e motar tafito dagudu tashiga gidan tana kwalama mummy kira bata lura da su fatima da suke parlourn ba dagudu tafad’a jikin mummy tana oyoyo mummyna na yi missing d’inki wlh,
Mummy tana dariya tace kuji min d’iya marar kunya sai kinje kin karyani.
Su Aunty khairat dariya suke sukace ai mu bata ma ganmuba.
Amina ma dariya tayi tace kuyi hak’uri Aunty khairat in inaganin mummy mancewa nake da kowa,
Fatima tace eh ai gashinan munga alamar hakan tunda sai yau kika lek’ota tunda yaya fahad yad’auke mana ke,
Amina cikin Jin kunya tasunkuyar da kanta batare da ta ce komai ba.
Daidai lokacin fahad yashigo d’akin gefen Amina yazauna, harararsa Amina tayi ta gefen ido, Ko kallon inda take baiyiba nan aka shiga gaisawa daga nan suka hau hira,
Amina zuwa tayi suka gaisa da baba mairo daganan suka d’an ta6a hira sai tatashi takoma parlour,
Tana shigowa ta tadda su Ameerah da jawahir wajen fahad ya basu chocolate suna sha, suna ganinta dagudu sukayo wajenta Ameerah tana oyoyo mami, d’agasu sama Amina tayi d’aya bayan d’aya cike da sha’awar yaran nata nan tazauna suka haye cinyarta suna mata surutu
Aunty khairat tace oh ni yaran nan dan Allah safkesu kema kina fama da na cikinki kanan suzo suhayeki,
Amina kunya taji tasunkuyar da kanta k’asa, fahad ganin batada niyar janyesu daga jikinta yasa yatashi yad’aukesu yace tunda ke baki iyawa ni ina tsoron suharbe min unborn baby,
Aunty khairat rik’e baki tayi tace fahad gaban mummy kake wannan maganar,
Fahad kallon mummy yayi yace mummy aidai gaskiya nafad’a ko?
Murmurshi mummy tayi tace aikam dai my son ka yi gaskiya.
Dariya sukasa gaba d’ayansu ammah banda Amina da saboda kunya ji take kamar tanitse k’asa.
Aunty khairat tace to Allah yasafke lafiya ai naga gashinan har ya fito,
Fahad yayi karaf yace Ameen
kallonsa Amina tayi yad’aga mata gira dasauri tajanye idonta daga kallonsa tana mamakin rashin kunyar fahad.
A ranar gidan suka wuni har dare sukasha hirarsu gwanin sha’awa,
A ranar aka kawo lefen fatima da salma kowace akwati shidda-shidda, anzuba musu kaya sosai Nan akayita bud’ewa ana tayasu murna tare da yi musu Allah yasa alkhairi.
STORY CONTINUES BELOW

Sai dare sannan fahad yad’auketa sukabar gidan, a mota Amina kallon fahad tayi cikin shagwa6a tace my hubby bacci nakeji, kallonta fahad yayi yana murmushi sannan yamaida hankalinsa go tuk’in da yake yace toh kibari mu isa gida sai kiyi,
Turo baki tayi kamar zatayi kuka tace ni bacci nakeji, fahad bai ankaraba sai gani yayi ta kwanto saman cinyarsa, shareta yayi yacigaba da tuk’insa,
Amina cikin kissa takai hannunta gabansa tata6o joystick d’insa cikin wani irin salo,
Fahad wani irin yanayi yashiga motar kufce masa tayi dasauri yarik’ota yasafka daga saman titi yayi parking,
Tashi Amina tayi daga jikinsa tajingine kanta a jikin k’ofar motar da take zaune tace ni na ma fasa baccin tunda bakaso inyi,
Gani tayi fahad ya tsareta da manyan idanuwansa da suka canza kala, kashe masa ido d’aya Amina tayi tace ya dae my,
Fahad dogon numfashi yaja sannan yakife kansa a jikin steering d’in motar, Amina kallonsa take har yad’ago saida yatada motar sannan yace princess da kinja na yi causing d’in accident Allah ya so ba wata motar bayana,
Amina kamar zatayi kuka tace toh ni yaya fahad me nayi? Ni fa bacci nakeji.
fahad hannunta yarik’o da hannu d’aya yana murzawa, d’an hannun kuma yana driving da shi, nan da nan bai ankaraba Amina tayi bacci,
Ko da suka isa gida fahad bai tashetaba fitowa yayi daga motar sannan yazagaya gefen da take zaune yabud’e d’aukarta yayi kamar jaririya yanufi cikin gida da ita, cikin bacci ta bud’e idonta taganta jikinsa murmushi tasakar masa tare da ratayo hannunta a kafad’ansa tazuba masa ido tana kallonsa,
fahad bed room d’insa yanufa yasafketa saman gado, Amina ruk’o hannunsa tayi ganin ya juya yana shirin fita, juyowa yayi yana kallonta itama kallonsa take yace ya dai? Lumshe ido tayi tace yaya fahad ina zakaje? Murmurshi yayi yace gidan zan rufe sai inzo muyi wanka ko?.
Gyad’a masa kai tayi sannan tasaki hannunsa
________________
Tunda aka fara program d’in bikkinsu fatima dakyar Amina tasamu fahad yana barinta tana zuwa saboda lokacin itama tana jin nauyin jikinta daurewa kawai take tana zuwa bikkin sai dare fahad yake d’aukota, ranar da za ayi dinner duk yadda taso taje ammah fahad hanata yayi ta yi magiyar har ta gaji har da Aunty khairat tahad’asa ammah yak’i yace ba inda zataje masa da baby dan haka suzauna gida,
Ta yi kukan ta yi fushi ammah bai ko kulataba ganin haka yasa takira su Fatima tabasu hak’uri akan ba zata samu damar zuwaba nan take fad’a musu yayansu yahanata basuji dad’in hakanba ammah ba yadda suka iya sukace bakomai sunsan indai yaya fahad ne zai aika,
Fahad ma kashe wayoyinsa yayi gaba d’aya gudun kar su yusuf sudamesa haka suka zauna sukasha love.
Ranar yinin bikki tun da wuri taso tatafi ammah fahad yak’i kaita sai wajen azahar lokacin da zaije d’aurin auren saida ya ajeta sannan yawuce, lokacin gidan ya cika taf da dangi da abokai, ko da su Aunty khairat suka ganta cemata sukayi hala yau ma so yayi yahanaki zuwa? Murmurshi Amina tayi tace a’a daman cewa yayi sai zaije d’aurin aure sannan yakawoni Aunty khairat tace shi dai yasani, nan Amina tacigaba da gaisawa da dangin su fahad, kowa sonta yake, nan-nan suke da ita,
Nan tayita ma amare tsiya haka suka zauna anata hidimar bikki.
Bayan sallar isha’i aka fara shirin kai amare a gidan angwayensu da ke nan government house, anguwarsu Amina saidai Amina ta yi nisa dasu ba laifi.
fahad dakansa yad’auki Amina yakaita saida aka fara kai Fatima gidanta sannan aka wuce da salma nata gidan basuda wani nisa sosai kowa ya yaba da kyaun da gidajen sukayi gaskiya sun tsaru sosai saboda daddyn fatima da daddyn salma sun kashe kud’i sosai wajen ganin sun fiddo ‘ya’yan nasu, musamman ma daddyn fatima da yake gani daga wannan babu wani bikki a gabansa, toh Fatima da salma sai muce Allah yabaku zaman lafiya da mazajenku.
Su kwaro kamar yadda suka d’au ma fahad alk’awalin zuwa basusha wahalaba da sukaso kaduna wajen gano gidan fahad, fahad ya ji dad’in ganinsu sosai gida d’an k’arami yasamu yasiya musu sannan yad’aukesu aiki a hospital d’insa a matsayin attender d’insa, sunyi murna tare da godia har suka rasa bakin gode ma fahad, a k’arshe dai sukabar abun a ransu akan ba zasu ta6a mantawa da shiba acikin addu’o’insu saboda ya taimakesu a lokacin da suke buk’atar taimako.
1
STORY CONTINUES BELOW

*Bayan wata ukku*
Amina zaune take darshen a k’asa saman carpet gabanta plate ne cike da fruits tana Ci, fahad kuma kwance yake saman 3 seater yana kallon films, jitake kamar ana tsikararta daurewa kawai take gudun kar tatada ma fahad hankali.
Da daddarema a daddafe tayi sallar isha’i sannan tashiga wanka bayan ta fito bata tsaya wani shiryawaba rigar bacci kawai tazumbula sannan tahaye saman gado takwanta saboda wani irin ciwon mara da takeyi juyi kawai take saman gadon a k’arshe bacci mai nauyi yad’auketa,
Fahad lokacin da yadawo ya yi mamakin yadda tayi bacci dawuri, bai tadataba yawuce shima yayi shirin baccinsa sannan yadawo yakwanta bayanta,
Wajen k’arfe ukku da rabi na dare farkawa tayi saboda wani irin ciwon mara da taji ya matsa mata, dakyar tatashi tasafko k’asa tazauna dan ji take gadon ma duk ya isheta, ji take ciwon kamar k’aruwa ma yake, duk A.C d’in da take cikin d’akin ammah Amina zufa takeyi, kallon fahad tayi da yaketa baccinsa baisan abinda ake cikiba, dakyar tabud’e baki tafara kiran sunansa, cikin bacci fahad yaji kamar Ana kiransa, yana bud’e ido yaga Amina zaune a k’asa duk ta fita hayyacinta, dasauri yataso yanufi inda take Amina rik’esa tayi sosai tana cije la6enta, cikin tashin hankali fahad yace me yake miki ciwo ko haihuwarce? Dakyar Amina tagyad’a masa kai, dasauri fahad yatashi yad’auko kayansa yasanya sannan yad’auko zane da hijab yasanya ma Amina, jakar da suka tanada ta kayan haihuwa fahad yad’auko, d’aukar Amina yayi yanufi mota da ita tare day kwala ma maigadi kira yazo yabud’e masa gate, dagudu fahad yaficce daga idan baima tsaya magana data maigadinba, direct hospital d’insa yanufa da ita, ko da ya isa special room yanufa da ita, nan yasamu wata k’wararrar nurse, Sister Sainah (ummun meenal love you mum😘) ita tataimaka masa, tsaye sukayi kan Amina da taketa nak’uda addu’a ce kawai taketa yi, fahad dai tausayinta kawai yake ji yake daman akwai dama da yamaida haihuwar a jikinsa,
Ta fi minti ashirin tana nak’uda sannan haihuwar tazo mata gadan-gadan nan kan yaron yafara fitowa fahad ne cikin dabara irin tasu ta likitoci ya ida fitar da jikin yaron batare da ta k’aruba, mik’a ma nurse d’in babyn yayi, Amina ta sha wahala ammah kuma tana haihuwa taji duk ciwon ya tafi, dasauri fahad yazo yarungumeta yana mata sannu, dakyar Amina tad’ago kai takallesa tayi masa murmushi, nurse d’in saida tagyara babyn fes sannan tamik’a ma fahad shi tashiga gyara Amina da wajen da ta6ata,
fahad babyn yazuba ma ido yana fad’in masha Allah itama Amina lek’awa tayi tana murmushi gani tayi yaron ya d’auko kamannin fahad tas har ma ya fi Ameerah kama da shi, nan fahad yayi masa addu’o’i da hud’uba yakira su mummy da su innah ladi yafad’a musu yace ai ta haihu lafiya dasafe ma zasu dawo gida, mik’a ma Amina babyn yayi domin tabashi nono, jin an tayar da sallah yasa yatashi yacanza kayan jikinsa daman na aikine yad’aura daga sama sannan yanufi masallaci.
Amina ko da tagama ba babyn nono kwantar dashi tayi gefenta itama takwanta nan da nan bacci yad’auketa.
Fahad lokacin da yadawo Amina bacci take dan haka bai tashetaba yakoma gefe yacigaba da kiran mutane yana fad’a musu ana tayasu murna, sai wajen 7:30am sannan Amina tafarka nan suka tattara kayansu suka fito nan sauran ma’aikata sukayi ta taya ogan nasu murnar k’aruwar da yasamu.
Lokacin da suka isa gida da mamakinsu innah ladi da su mummy duk suna gidan lokacin har and’aura mata ruwan wanka,
Su murja ma duk sunzo kasancewar yanzu hutun second semester suke, dasauri suka taso suna rige-rigen kar6an babyn kowa ya yaba da kyaun yaron akaita santinsa,
Innah ladi kar6ansa tayi tayimasa wanka fahad ganin yadda akesa masa yaro cikin ruwan zafi yana ta tsala ihu yasa yaji tausayin yaron yace innah ladi dan Allah kibari ruwan yahuce kar ki k’onamin yaro, salati innah ladi tayi tace kujimin yaro marar kunya kaima ai haka akayi maka, su Aunty khairat dariya suketa yi ma fahad, mummy ce tayi masa magana sannan yatashi yabar d’akin.
Amina ruwan wankan aka had’a mata itama tashiga tayo saida tagasa jikinta sosai sannan tafito saboda ita ruwan zafi basu 6ata mata rai indai zata gasa jikinta.
Bayan tafito tashirya kunu aka kawo mata cike da jug nan tad’auka tasha dayawa sannan aka zubo mata tuwon da aka dafa mata tare da yajin daudawa mummy ce ta tisata gaba tazauna taci balaifi, sannan tak’ara ba yaron nono sai takwanta tayita baccinta.
STORY CONTINUES BELOW

Sai wajen la’asar sannan mummy takoma gida, su salma da fatima ma sunzo kowace da k’aramin cikinta.
Bayan sallar isha’i gida ya yi shuru babu kowa sai su Amina da innah ladi saboda ta dawo gidan ta ce itada komawa har sai Amina ta gama wanka,
Amina zaune take bakin gado tana ba babyn nono ita kuma innah ladi tana gefenta suna hira,
Fahad ne yashigo d’akin bai d’auka zai tadda innah ladi a d’akinba, sosai kai yayi cikin jin kunya yagaisheta sannan yazo yakar6i d’ansa da ke hannun Amina,
Innah ladi kallon Amina tayi tace bari inje inyi isha’i kinsan ko sallah banyiba nabiye miki muna ta fira, Amina tace toh innah sai kin dawo.
Fahad kamar jira yake yana ganin ta fita ya kwantar da yaron tare da rungumo Amina itama rungumesa tayi yace my princess yau na yi missing d’inki sosai ban samu ke6ewa da keba, Amina k’ara shigewa jikinsa tayi tace yaya Fahad toh ya zamuyi dole mudinga hak’uri saboda bak’i, numfashi Fahad yaja yace hakane ammah kinsan yau kad’ai har nagaji ji nake daman sudaina zuwa abarmin ke da babyna muyi zamanmu, murmushi Amina tayi tace yaya Fahad ai na lokacine data a anyi suna shikenan ba wanda zai dinga takura mana, Fahad yace hakane yanzu dai kawomin Abinci inci yunwa nakeji, toh tace sannan tatashi takawo masa abinci dakansa tazauna tana bashi a baki har yak’oshi sannan Amina tatattara kayan tamaida kitchen, lokacin da tadawo ta tadda Fahad saman gadon kwance gefen babyn, kallonsa Amina take cike da mamaki tace yaya Fahad ba dai nan zaka kwana ba ko?
Shima kallonta yake yace nan zan kwana mana akwai wani abu?
Turo baki Amina tayi tace gaskiya a’ah kaga kar innah ladi tagani wlh fad’a zatayi.
Dariya Fahad yayi yace sarkin tsoro babu abinda zata ce mana,
Amina kamar zatayi kuka tace wlh nidai ba zamu kwana tare ba.
Fahad hannu yamik’a mata yace toh zo kisallameni sai intafi tunda korata akeyi.
jikinsa Amina tafad’o tace ni ba korarka nakeba ina dai tsoron fad’an innah ne, kuma yanzu kaga babu yadda za’ayi wani abu yashiga tsakaninmu tunda na haihu.
Fahad tunda tafara maganar kallonta yake dogon hancinta yaja yace sarkin sharhi toh nak’i wayon naki.
Amina bud’e baki tayi zatayi magana dasauri Fahad yahad’e bakinsu waje guda yafara kissing d’inta, bud’e k’ofar da akayine yadawo dasu duniyar da suka lula, dasauri suka janye bakinsu tare da kallon k’ofa, salati innah ladi tafara yi tace nashiga ukku yau Allah ya had’ani yara marassa kunya yanzu yarinyarnan tahaihu yau ammah bazaka bartaba? kekuma sakara kizauna nan yad’ura miki wani cikin kinga sai yi gwannai, ki ‘yar dad’i miji kinhaihu ammah dayake bakisan ciwon jikinkiba shine kike biye masa.
Amina kunya takamata dasauri tasafka daga jikin Fahad tare da duk’ar da kanta k’asa,
dariya fahad yayi yace toh sai me innah, inace matatace ba wata matsala,
Hanya innah tanuna masa tace tashi kafita katafi d’akinka tunkan ranka ya6aci, tashi fahad yayi yana dariya yace toh innah, sumbatar kumatun Amina yayi tare da cewa sai dasafe my princess naga innah tanaso tashiga tsakaninmu, innah ta6a hannu tashiga yi tace oh ni Aishatu yau naga ikon Allah yara ba kunya,
Dariya fahad yayi sannan yaficce daga d’akin tare da cewa sai dasafe innah.
Kallon Amina tayi da ta sunyar day kanta tace ashe ke shashasha ce ban saniba kizauna nan ke dad’i miji yad’ura miki wani cikin kina jego.
Amina tace innah ayi hakuri.
innah tace toh taso kirufe d’akinki daman sallama nazo muyi dan bacci nakeji, Amina toh tace sannan tataso takulle d’akinta takoma takwanta.
haka kusan kullum ake chapter tsakanin fahad da innah bata barin Amina taje d’akinsa idan kuma ya shigo gabanta yake rungumar matarsa innah tun tana fad’an har ta gaji ta kyalesa saidai tayi ta masa mita.
ranar suna daddy cewa yayi asa ma yaron sunan marigayi mahaifin Amina, Amina ta ji dad’in ka-rar da akayi mata harda kukanta, yaro yaci suna ahmad ammah suna kiransa da Ameer, fahad akwati d’aya yahad’o mata nakaya tare da bata 500,000 yace ko da tana buk’atar wani abu, Ameer ma akwati biyu yaciko masa da kaya masu tsada Amina ta yi mamakin kud’in da fahad yakashe masu saboda har Ameerah ma saida yasiya mata.
rago d’aya da sa fahad yayanka Shima daddy ba a barsa a bayaba saida yayanka ma yaron rago babbah.
Gidan cika yayi da mutane ‘yan suna, ‘yan katsina tun ana saura kwana biyu suna sukazo suka safka gidansu fahad, Amina ta samu kyaututtuka sosai daga wajen mutane da matan abokan fahad, mummy da daddyma kyautarsu ta musamman suka bata dan shi daddy harda kyautar fili yayi mata, Aunty khairat ma da su fatima kyauta ta musamman suka bata,
Murja ma da iyayenta ba a barsu a bayaba 300,000 suka bata dakayan baby masu kyau set ukku,
A ranar Amina kyaututtaka tasamu sosai,
Fahad kud’i yafitar dasu sosai akayi abincin suna na fita kunya da abinda za’a raba ma bak’i,
Su ma kansu intelligent writer’s dasauran masoyansu fahad saida sukazo akasha sunan da su sukaci suka sha akayi pic’s dasu. Aunty khairat ta so takoma day Ameerah ammah tak’i daman tunda sukazo lik’ema Amina tayi kan dole Aunty khairat tabar musu d’iyarsu.
Nan kowa yawatse cike da murna da farin ciki.
Su murja da su salma ne suka zauna suka gyara mata gidanta fes, sai dare sukatafi
itama murja wanda zata aura ne yazo yamaidata gida.
gida yakoma shuru, Amina kayan da tasamu ta d’ibi turmi biyar tahad’a da dubu d’ari taba innah ladi dakyar innah takar6a tana kuka tace Amina duk ni kad’ai kidai rage, Amina tace a’a innah ai kinma fi k’arfin wannan a wajena a lokacin da kowa yagujeni kekad’aice kika fara jawoni a jikinki, dasauri innah ladi tarufe mata baki tace ya isa haka Amina kidaina tuno abinda yawuce, gyad’a kai Amina tayi tace toh innah nagode,
Amina sauran kud’in tad’auka tanufi d’akin fahad tana rungume da Ameer zaune tahango fahad a bakin gadonsa yana shan coffee Ameerah kuma tana kwance tana bacci, fahad aje cup d’in yayi dasauri yataso yatareta tare da had’ewa yarungumeta ita da babyn, murmurshi Amina tayi tace my hubby ai na d’auka ka yi bacci, amsar Ameer yayi da yaketa bacci sannan yarik’ota suka nufi bakin gado suka zauna yace a’a banyi bacciba my princess ina nan ina ta tunaninki, kwantar da Ameer yayi sannan yajawo Amina jikinsa yarungume, ahankali Amina tad’ago kai tasakar masa murmushi sannan tafiddo kud’in da suke cikin jakarta tamik’a masa tace yaya fahad ga wannan,
Fahad kallonta yake fuskarsa d’auke da mamaki yace wannan kud’infa?
Murmushi Amina tak’ara yi tace wanda nasamune wajen taron suna shine nakawo maka kad’auka nabaka,
Shima fahad murmushi yayi yace toh mezanyi dasu? Hak’k’inkine kiyi amfani da abunki kisaka a account d’inki lokacin da kike buk’ata sai ki d’auko, ammah kuma kid’ibi wani abu daga ciki kiba dangin mahaifiyarki domin sun chanchanci hakan, cikin Jin dad’i Amina tak’ara shigewa jikinsa tace nagode sosai yaya fahad tabbas nasan na yi sa’a da Allah yamallaka min kai a matsayin miji, *K’ADDARA CE* tahad’a mu har mukakai wannan matsayin da muke yaya fahad babu abinda zan iya biyanka da shi sai addu’a domin kulawa babu wacce ban samu a wajenka, narasa iyayena ammah su mummy suka koma min madadinsu, tabbas kai alkhairine a cikin rayuwata,
Fahad shima k’ara rungumeta yayi kamar zai maidata cikin cikinsa saboda wani irin sonta da yake fizgarsa, ahankali yabud’e baki yace Amina a kullum ina k’ara godema Allah da ya mallaka min ake a matsayin mata musamman ma idan naga kyautan ‘ya’yan da yayi mana, tabbas ke kad’aice cikin zuciyata babu wadda zata samu matsugunni a ciki saboda kin riga kin baibaye ko’ina kece za6in zuciyata, kina bani kula yadda yakamata kin haifa min yara wlh Amina kin gamamin komai a nan duniya akullum addu’ana Allah yamallaka min ke a matsayin matata a gidan aljannah, Amina k’ara shigewa tayi jikinsa tace Ameen yaya fahad.
A haka suka kwanta suna rungume da juna cike da so da k’aunar juna kowa a cikin zuciyarsa yana sak’a yadda zai cigaba da kula da d’an uwansa tare da addu’an Allah yaraya masu yaransu sannan aurensu yakasance dauwamamme.
_*Alhamdulillah anan nakawo k’arshen wannan littafin mai suna K’ADDARA CE