K’ADDARA CE CHAPTER 2

  K’ADDARA CE CHAPTER 2

Blanket tajawo talullu6e jikinta.

Daidai lokacin su Abbah suka turo k’ofar d’akin suka shigo dasauri abbah yanufi wajenta hankalinsa a tashe, idanuwanta a lumshe suke hawaye yagani suna gangarowa daga idanuwanta,

Bakin abbah yana kyarma yace Amina kiyi hak’uri laifi na ne ni najamiki wannan mummunar k’addarar.

Bud’e idanuwanta tayi tace a’a abbana kar kace haka K’ADDARA CE kawai kadaina d’aura laifin a kanka domin na san abbah na ba zai ta6a aikata abunda ba daidai bane, kakwantar da hankalinka abbana nasan koma minene yafaru laifin nasune ba na abbana ba.

Dafa kanta yayi yana hawaye yace Allah yayi miki albarkar Amina.

Murmushi tayi tace Ameen Abbana,

Ammah jikinki akwai zazza6i bari asamo miki magani,

Juyowa yayi yakalli ummah da tunda suka shigo tana tsaye batace komai ba yace zainab dan Allah kije d’akina kid’auko mata paracetamol tasha,

Kallon Abbah tayi tace wlh Alhaji ban iya zuwa ni kad’ai tsoro nakeji, jin haka yasa abbah yatafi.

Kusa da Amina tadawo fuskarta a d’aure tace sannu kitashi kid’an watsa ruwa ko kinji dad’in jikinki, kunya Amina taji domin ta gano abinda ummah take nufi,

Dasauri taruntse idonta tace ummah na yi wanka ai, yamutsa fuska ummah tayi tace Allah yasauke,

Daidai lokacin Abbah yashigo d’akin hannunsa rik’e da magani da ruwa tashi kisha maganin kinji mamana,

Ahankali tatashi zaune ba tare da ta bud’e idonta ba, maganin takar6a tasha daidai lokacin aka fara kiran sallah, komawa tayi takwanta ganin haka yasa su abbah suka fita daga d’akin.

Tana jin fitarsu tatashi tana tafiya ahankali tashiga toilet alwallah tayi tazo tasa hijab tayi raka’atan fijir da tagama karatun alk’ur’ani tazauna tayi har aka kabbara sallah sannan tatashi tayi sallar asuba,

Gado takoma takwanta saboda wani irin bacci da takeji bata dad’e da kwanciyaba bacci yad’auketa.

****    ****     ****   ****

Tunda suka dawo suka sauke babban yaro gida suka wuce club danshi cewa yayi ba zai je ba.

A tsaye yake a wajen gidan sai saffa da marwa kawai yakeyi a wajen da ka ganshi ka san hankalinsa a tashe yake akan abinda ya aikata,

Tunaninsa na kullum yafad’o masa a rai, nan danan idanuwansa suka kad’a sukayi jawur.

hawayene suka fara fita daga idonsa, d’aga murya yayi yace innalillahi wa inna’ilaihir raji’un wannan wace kalar KADDARA CE Allah kakawo min mafita.

K’addarace taraboni daga gida, K’addarace tahadani da wad’annan mutanen har nayi wannan aika-aikar Allah kakawomin mafita a cikin K’ADDARA TA (na chubado mhmd) kuka yakeyi sosai kamar k’aramin yaro

WANENE BABBAN YARO

*****    *****    *****  *****

Fahad umar shine cikakken sunansa suna zaune a garin kaduna a tudun wada.

Alh umar shahararren d’an kasuwane yana shigo da kaya daga k’asashe dadama shima wani lokacin yana fita da kayan Nigeria wasu k’asashen da suke buk’atarsu.

Yana da mata d’aya Hajiya Hafsat ‘yar jihar yola ce, da ‘ya’ya ukku khadeeja ce babbah tana da shekara 5 sannan aka haifi fahad dayake bi mata,

Saida fahad yakai shekara goma sannan aka haifi yar autarsu Fatima sun taso cikin gata gasu kyawawa sosai kasancewar mahaifiyarsu bafullatana ce ta usuli mahaifinsu kuma barumayene.

STORY CONTINUES BELOW

Sun taso cikin tarbiya kasancewar iyayensu tsaye suke wajen kula da yaran nasu.

Tunda khadeeja tagama secondary school dinta aka yi mata aure da wani d’an chairman din garin.

Fahad kuma aka fiddashi k’asar U.S.A domin yin karatun doctor,

kasancewar fahad bai da buri a rayuwarsa da yawuce yaga ya zama likita.

Bayan wasu shekaru Alh umar yak’ara aure ya auri wata customer dinsa bazawara mai suna hindatu.

suna zaman lafiya da mummy kasancewar mummy batada hayaniya sosai kuma tana da hak’uri kuma hindatu tana binta sau da k’afa.

hindatu bata ta6a haihuwa ko 6atan  wata ba shekara biyar kenan da aurenta da Alh umar.

Bayan shekara biyar Fahad yakammala karatunsa yadawo gida anyi murna sosai da dawowarsa, lokacin khadeeja ‘ya’yanta biyu.

Lokacin ita kuma fateema tagama secondary school dinta a wata private school.

Tunda hindatu tad’aura ido akansa taji tana sonsa sosai kasancewarta tana bin maza, tunda fahad yaji matsayinta a gidan bai bin takanta domin ba ta gabansa harkarsa kawai yakeyi,

Ahaka har yasamu aiki a wani babban asibiti federal da yake garin kaduna.

Ammah ita sai ta tsiri shishshige masa ko unguwa zataje daddy takeyi ma magana yasa Fahad yakaita,

Insuna tafiya tayi ta jansa da hira ammah ba ya biye mata saidai tayi ta surutunta tagaji tayi shuru.

Daga nan sai ta tsiri zuwa d’akinsa domin suyi hira abinci ma ba ta bari yana cin na ‘yan aiki ita take girka masa,

Mummy tana jin dadi sosai ganin yadda hindatu take ji da yaranta.

Kunsan in akace mutum d’an duniya ne toh sai ahankali ahaka tasamu tajawo hankalin fahad yafara kulata, har d’akinta take jansa domin suyi hira daga nan shak’uwa tashiga tsakaninsu sosai komi yasamo wajenta yake zuwa domin yana ji da Auntyn tashi sosai.

Ranar wata asabar ne kasancewar ba aiki fahad ne zaune d’akinsa yana kallon labarai,

Wayarsace tayi ringing jawota yayi yaduba sunan da yagani ya bayyana jikin screen din yasa yayi murmushi tare da d’aga wayar hello my lovely Aunty,

Daga d’ayan 6angaren akace my son pls kazo d’akina ga wasu takardu nan katayani cikesu wlh tun d’azun nakeyi na gaji.

Shuru yayi batare da ya ce komai ba, hello fahad,

Toh Aunty ganinan zuwa, kashe wayar yayi bai jira jin abinda zata ceba.

Murmushi tayi ta wullar da wayar saman gado tace yau dai burina zai cika akan fahad mafarkina zai zama gaske.

Fridge tabud’e tad’auko jug din kunun ayar da ta had’a kasancewar ta san fahad yanason kunun aya sosai.

Wasu k’wayoyin magani guda biyu tazuba tamotse su tamaida cikin fridge d’in tana murmushin mugunta.

Daidai lokacin akayi knocking din k’ofar.

Dasauri takoma saman gado tazauna,

Yes shigo mana my son.

Turo k’ofar yayi yashigo, bakin gadon tanuna mai inda takardun suke tace pls have a sit mana banason wannan la6e-la6en da kakeyi in kashigo d’akin nan,

Yauwa ka ga takardun nan.

Zama yayi bakin gadon tare da d’aukar takaddun yana dubawa na wasu filayene murmushi yayi yace Aunty fili zaki siya ne,

Eh wlh shiyasa nakeson kaduba min kaga wane zai fi dacewa insiya.

Cigaba yayi daduba takardun daidai lokacin tatashi taje tabud’e fridge din tad’auko jug din da cup.

Gabanshi tazo ta aje mashi tare da d’aukar cup din tacika da kunun aya tace my son ga fa kunun aya d’azu nayi shi,

Kar6a yayi yana murmushi yace thanks my lovely Aunty itama murmushin tayi.

Fara sha yayi yana lumshe ido saboda dad’in da kunun ayar yayi tas yashanye shi sannan ya aje cup d’in.

Hammah yafari tare da lumshe ido yabude ahankali yace Aunty bari inje d’aki bacci nakeji kallonsa tayi tace toh.

mik’ewa yaso yayi ammah ya kasa duk kasala yakeji sai hammah kawai da yakeyi.

Kakwanta nan mana my son.

saman gadon ya ida kwanciya ba ayi minti biyar ba bacci mai nauyi yad’aukesa.

Ganin haka yasa hindatu tafara murna domin burinta ya kusan cika, kayan jikinta tacire tatsaya daga ita sai bra da pant.

Saman gadon tanufa rigar jikin fahad tacire tare da kwanciya saman k’irjinsa wayarta tajawo tadinga yi masu pics .

Har saida tagaji dan kanta sannan tadaina, murmushi tayi tare da gyara kwanciyarta a jikinsa a haka itama bacci yad’auketa.

K’arfe takwas din dare daddy yadawo daga kasuwa yagama shirinsa yana zaune shuru hindatu bata kawo mai abincin sa ba,

Tashi yayi yafito daga d’akinsa part din hindatu yanufa.

Daidai lokacin fahad yafarka daga bacci ahankali yabud’e idonsa,

Jin mutum a jikinsa yasa yamaida kallonsa akanta hankalinsa a tashe dasauri yatureta daga jikinsa yana salati.

Farkawa tayi itama. Mezangani haka meyake faruwa dani ne inji fahad,

Dasauri yasafko daga saman gadon itama safkowa tayi tana murmushi.

Ja yake da baya tana binsa yace Aunty miye haka mi kike shirin aikatawa da haka har yakai jikin bango idanuwansa yaruntse yana ta addu’o’i.

Saida tazo daf dashi har suna jin numfashin juna sannan tace fahad na dad’e ina sonka tun lokacin da nafara ganinka sonka yashiga raina da tunaninka nake kwana dashi nake tashi dan haka yau nakeso kabiya min buk’atata.

Dasauri yabud’e idonsa yace Aunty kinsan hakan baida kyau fa mahaifi na fa kike aure, koma ba hakaba ai haramun ne dan Allah kiyi hak’uri kikyaleni duk abinda kikeso zan baki.

Murmushi tayi tace fahad kai kad’ai nakeso kuma kai kad’ai nake sha’awa idan kayarda kabiya min buk’atata zan baka komi kake buk’ata idan kuma kak’i toh,

Pics din da tad’aukesu tanuna mai tace wlh zan nuna ma Alhaji da mummynka kuma ince ka dad’e kana bibiyata.

Hankalinsa a tashe yake kallonta ya rasa ya zaiyi da rayuwarsa duk tsoro yakamashi,

Ganin haka yasa tayi murmushi tace in ka amince bismillah inko baka aminceba toh kaima ka san sauran.

Kallon tsana yabita dashi yace wlh ba zan aikata ba saida kiyi abinda zakiyi Allah yana tare dani,

Bani waje inwuce rik’esa tayi tace wlh fahad baka isaba sai ka biyamin buk’ata ta Zaka fita daga d’akin nan,

K’ok’ari yake yak’wace daga rik’on da tayi mashi daidai lokacin aka bud’e k’ofa aka shigo.

Dukkansu suka maida kallonsu wajen mai shigowar abbah ne yashigo yana cewa hindatu wai bakisan na..

Maganarce tamak’ale a bakinsa ganin abinda idonsa yagane masa………

Maganarce tamak’ale a bakinsa ganin abinda idonsa yagane masa hankalinsa a tashe, mutuwar tsaye daddy yayi.
cikin sauri hindatu tasaki fahad tafashe da kuka dagudu ta isa wajen daddy tafad’a jikinsa wani kalar kuka takeyi na ban tausayi Alhaji kataimaka min dan Allah kar kabari fahad ya aika abinda yayi shirin aikata min wlh fyad’e zaiyi min,
Rungumeta daddy yayi d’ago kai yayi idanuwansa sunyi jawur yasafkesu akan fahad da yayi mutuwar tsaye yana mamakin maganganun Aunty.
Daidai lokacin mummy taturo k’ofa tashigo tana cewa wai hayaniyar mi nakeji haka innalillahi wa inna’ilaihir raji’un me zan gani haka me yake faruwa Alhaji.
Kallonta daddy yayi yace hafsat kikalli abinda d’an cikina yake aikatawa kuma abun nashi har ya zo kan matata ta sunnah.
Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un fahad yaushe kazama haka ban saniba, mummy wlh ba laifi na bane itace ta… yi min shuru fahad babu abinda zaka ce min baccin ga zahiri nan
Hindatu cikin kuka tace hajiya daman ya dad’e yana bibiyar rayuwata, daman cewa yayi idan har ban amince dashiba toh sai ya kashemin aure, sai ya ja min sharrin da sai na gwammace ban zo duniyaba,
Dan Allah kutaimaka min Alhaji kuka takeyi gwanin tausayi.
Karya kike min Aunty kiji tsoron Allah kifad’i gaskiya miyasa kikeson shiga tsakanina da iyayena wlh k’arya takemin mummy kar ku yarda da maganarta.
Fahad matar tawa take maka k’arya? Karasa wacce zaka nema sai wadda take matsayin uwa a wajenka? Lallai fahad ayau na yi da na sanin kasancewarka a matsayin d’ana.
Hawayen bak’in cikine suka zubo ma fahad yace daddy pls kayarda da maganata wlh ban aikataba
wata muguwar harara daddy yawulla mashi,
wardrobe din hindatu yanufa yad’auko mata doguwar riga yamik’a mata tasanya sannan yamaida kallonsa ga fahad yace zani d’au k’ak’k’auran mataki a kanka kasaurareni,
Hannun hindatu yaja suka bar d’akin.
Kallon mummy fahad yayi da taketa kuka ya bud’e baki zaiyi magana tayi sauri tad’aga mai hannu babu abinda zaka cemin fahad ni ba kalar wannan tarbiyar nabaka ba na yi muku tarbiya mai kyau ammah duba kaga irin abun kunyar da kaja min,
Duk sanyin A.C din da yake d’akin ammah fahad zufa kawai yakeyi innalillahi wa’inna ilaihirraji’un wannan wace kalar K’ADDARA CE,
Mummy wlh nifa, karufemin baki nace idan har kak’ara min wata magana Allah ya isa fahad, fita daga d’akin nan,
ahankali yake tafiya kamar wanda kwai yafashe mawa a ciki yanufo inda mummy take yaduk’a k’asa,
Janye fuskarta tayi gefe d’aya tad’aga murya i said get out!!!
Jiki a sanyaye yatashi dasauri yafita daga d’akin.
‘Dakinsa yakoma hankalinsa a tashe sai zagaye d’akin yake yana nanata innalillahi wa’inna ilaihirraji’un yakeyi wannan wace kalar k’addara ce haka, ya zanyi da rayuwata yanzu babu wanda zai yarda da maganata kowa kallon da yakeyi min kenan,
Ina zansa kaina wane mataki daddy zai d’auka a kaina? Innalillahi wa inna’ilahir raji’un.
Toilet yafad’a yasakar ma kansa shawa, wanka yayi yafito yashirya.
Kwanciya yayi saman bed dinsa ammah ya kasa bacci sai sak’e-sak’e yakeyi a ransa a k’arshe yayanke hukuncin da yaji ya fi kwanta mashi a rai.
Juyi kawai yakeyi a saman gadon har aka fara kiran sallah bai samu yarintsa ba,
Tashi yayi yashiga toilet yayi wanka tare da d’auro Alwallah wardrobe dinsa yabud’e yad’auko kaya kala hud’u yazubasu cikin wata yar k’aramar jaka yazuba ‘yan abubuwan da yasan zai buk’ata,
Shiryawa yayi sannan yad’auki jakarsa yabar gidan ko da yafito mai gadi yana d’aki yana bacci bud’e gidan yayi yafita.
Babu kowa a wajen saida yayi nisa sosai sannan yaji an kabbara sallah a wani masallaci, tsayawa yayi yai sallah sannan yasamu mai acha6a yace yakaishi tashar mota.
Lokacin da suka isa mota d’ayace aka kusan cikawa.
Wajen motar yanufa da yaji anata katsina katsina.
Shiga yayi yazauna ba a dad’eba motor tacika.
Tunda suke tafiya hankalinsa yana wajen taga lumshe idonsa yayi yana tunani,
Idan naje katsina ina zan safka alhali banda kowa a garin wace kalar rayuwa zanyi a garin da banda kowa,
K’arfe 7:00am suka iso katsina a tasha aka safkesu nan aka fara fita daga cikin motar.
Tashar cike take da mutane fitowa yayi yanufi bakin gate din yasamu waje yazauna tunani kawai yake ina zaije.
Ji yayi an dafa kafad’arsa d’agowa yayi yaga wanene wani bak’in  mutum ne k’ato yagani tsaye.
Sannu bawan Allah wai mi yake damunka tun muna cikin mota kake tunani daga gani kana cikin matsala kuma mun iso maimakon kaje gida sai kazonan kazauna  kuma ga garin hadari ke akwai katashi katafi gida nima wucewa zanyi garinmu.
Kallonsa fahad yayi yace ni bansa kowaba a garinnan.
Bakasan kowaba kuma kazo garin,
Eh wlh kawai ji nayi inason zuwa garin domin ban ta6a zuwaba dan Allah ko zaka taimaka kabani masauki?
Kallonsa mutumin yayi ba dan ya yarda da abinda yaceba ya san dai yana 6oye mashi sirrinsane ammah da ka ganshi ka san akwai damuwa a tare dashi.
Ni ba garin nan nakeba a mashi nake idan zaka iya zama dani toh
Eh wlh zan iya zama da kai,
Murmushi mutumin yayi yace toh taso mutafi,
Dasauri yad’auki jakarsa yana mai godiya,
Adaidaita sahu suka samu suka shiga suka nufi tashar motar mashi sukayi sa’a motar mutum biyu ake jira.
Cikin minti talatin suka isa mashi nan suka tari adaidaita sahu mutumin yafad’a mashi inda zai kaisu.
Tafiya sukayi mai nisa har suka fita daga cikin gari wajen wani daji inda ba kowa ko gida babu a wajen nan aka safkesu,
Kud’i mutumin yabiya mai napep din, nan suka haura cikin dajin tafiya kawai sukeyi shidai saurayin duk mamaki ya cikashi binsa kawai yakeyi har suka iso wani gida kusa da wani kongo a tsakiyar dajin….Juyowa mutumin yayi yakalleshi yana murmushi yace nan ne gidan da muke rayuwa ni da abokaina ukku,+
Saidai har yanzu bansan sunankaba,
sunana fahad , murmurshi mutumin yayi yace suna mai dad’i kokuma shima mai sunan ai babban yarone,
Ni kuma sunana zubairu ammah ana cemin bahbah
Kallonsa fahad yayi shima yayi murmushi.
Mushiga daga ciki inji mutumin shiga sukayi,
Gidane d’an madaidaici mai d’auke da d’akuna biyu sai toilet da kitchen k’arami a tsakar gidan.
‘Daya daga cikin d’akunan suka nufa mutumin yak’wank’wasa k’ofar da take rufe,
Daga ciki akace wanene?  Mutumin yace kai kubud’e nine,
Bud’ewa akayi suka shiga d’akin sai hayak’in taba yake tashi, mutum ukkune a zaune a cikinsa hannayensu rik’e da taba ga kayan maye a gabansu,
Jikin fahad duk yayi sanyi ko ba a fad’a mashiba ya san wane kalan mutane ne zaiyi rayuwa cikinsu,
Muryar mutanen ne yajiyo suna cewa ogah sannu da hanya ya kadunar Allah yasa andace?
Yauwa sannunku ai na yi sa’a na samu Alhajin na bashi k’wayoyin shima ya bada kud’in.
Yauwa ashe yau zamusha shagali bahbah,
Murmushi ogah yayi yace ga bak’o na nan fahad babban yaro sai lokacin suka lura da mutumin da yake bayan ogah a tsaye.
kai bahbah ina kasamo wannan mutumin mai kama da larabawa inji d’aya daga cikin samarin.
Murmushi ogah yayi yanuna ma fahad Waje yace yazauna,
Baiyi musuba yazauna shima ogah yazauna kusa da fahad d’in sannan yafad’a masu ainahin had’uwarsa da shi.
Nan sukace muna murna da zuwanka babban yaro,
Murmushi yayi Wanda baikai zuci ba iyakarsa baki sannan yace nagode.
Kallonsa ogah yayi yace ga abokan nawa bari ingabatar maka dasu,
nuna wani bak’in mutum  yayi k’ato idanuwansa jawur yace wannan shine Cha6o,
Wannan kuma k’waro kallon Wanda aka kira da k’waro yayi wani k’atone sosai bak’i ga muni,
Sannan wannan shine Cinnaka,
Wani siririn mutum ne ammah yana da haske babu laifi,
Sai mutumin yace ni kuma nine ogansu sana’armu itace sata da fashi dafatan zaka iya zama damu,
Fahad yad’ago yakallesu jikinsa duk ya mutu yace zan iya zama daku tunda bansan kowa a garin nan ba,
Ammah gaskiya ba zan iya irin sana’arku ba,
Murmushi ogah yayi yace kar kadamu ahankali zaka koya.
Kallon k’waro yayi yace akawo mana abinci,
Angama ogah tashi yayi yaje yad’auko wasu kuloli guda biyu da plate ya aje gabansu, zuba masu yayi tuwon shinkafa da miyar ku6ewa,
Kallon babban yaro ogah yayi yace muje muwanke hannu muci abinci domin na san kaima ka kwaso yunwa,
Baiyi musuba yabashi saboda rabonsa da abinci tun jiya da rana.
Akwana a tashi, Haka rayuwar babban yaro takasance tare dasu ogah ammah bai yarda yana binsu wajen sana’arsu, duk yadda sukaso suja ra’ayinsa yadinga shan kayan maye ammah ina bai sha saidai taba kawai suka ci nasara akansa yake sha,
STORY CONTINUES BELOW
Yana kula da sallolinsa na kowace rana, bai da hayaniya sosai kuma yana da miskilanci bai cika zama cikinsu ayi hira dashi ba,
Idan yana bukatar kud’i yakan d’auki Atm dinsa yashiga cikin gari yaje Atm machine yaciro,
A duk lokacin da suka buk’aci kud’i daga wajensa yana basu bai ta6a hanasu ba, suna mamakin inda yake samun kud’i ammah bai ta6a gaya masu ba,
Abun hannunsa ba ya rufe mashi ido saisa ogah yake sonsa sosai.
   *CIGABAN LABARI*
*****    ****   ****   ****
Tunda yagama sallar asuba yake kwance ammah ya kasa bacci juyi kawai yakeyi,
zuciyarsace take kwad’aita masa da son komawa gida shekara d’aya kenan rabonsa da gida bai nemi kowaba,
Gashi wayoyinsa duk suna gida yabaro, baisan wane hali su mummy sukeba hawayene suka zubo daga idanunsa addu’a yashiga yi Allah yasa gaskiya tabayyana, Allah yasa iyayensa suyafe masa, tunowa yayi da yadda su daddy suka shigo d’akin Aunty suka taddasu,
runtse idonsa yayi afili yace wannan wace kalar k’addarace,
Tabbas dole inkoma gida in nemi gafarar iyayena watakil suyafe min, ko da ba zasu yafeminba na san wata rana dole gaskiya tayi halinta,
Ya yi nisa sosai a tunaninsa bai san shigowarsu ogah ba ji yayi ana girgizashi,
firgit yayi yabud’e idonsa da suke a lumshe hawaye suna zuba,
Dasauri yagoge hawayen,
dukkansu kallonsa sukeyi cike da mamaki ammah basu damuba saboda sun saba ganinsa a wannan yanayin,
Cha6o yace waikai babban yaro tun dazun muka shigo sai magana muke ammah ka share mutane kuma ba bacci kakeba,
Kullum bakada aiki daga tunani sai kuka ance kadinga d’an shan kayan maye ko ka samu sauk’in yawan tunanin da kakeyi ammah ka k’i,
Da kana sha da ba abinda zai dinga damunka arayuwarnan,
Bakaga yadda mu muke rayuwarmu ba hankalinmu a kwance.
Kallon cha6o yayi ransa a 6ace yace ina ruwanka da damuwata inmutu mana, kuma ba zan sha ba, kar kamanta k’addara ce kawai tahad’a ni daku.
Bai jira jin me za suceba yatashi yafita daga d’akin,
Kallonsu suka maida a wajen ogah da yake da zuk’ar tabar sa kamar baisan abinda akeyi ba,
cha6o yace ogah kanajin maganganun da yake fad’a mana,
kabamu izini muyi masa hankali domin na lura har yanzu bai san suwanene mu ba, d’aukar rai a wajenmu ai abune mai sauk’i.
Hannu ogah yad’aga mashi yace ya isa haka cha6o,
Kakyalesa kawai ahankali zai zo hannu, wad’an nan maganganun nasa ai mun saba jinsu daga bakinsa miye abun damuwa,
Kuma ina tunanin abinda ya aikata ne jiya yake damunsa saisa yake fushi ammah kubarni dashi.
Ledar da suka shigo da ita ogah yad’auka yanufi kitchen plate yadauko yazuba waina da miyar da suka siyo,
Waje yafita chan yahango babban yaro zaune a bisa dutsin da yasaba zama ya dafe kansa da hannuwa biyu,
Wajensa yanufa yazauna kusa dashi yace kayi hakuri da abinda yafaru babban yaro,
Kaci abinci na san tun jiya rabonka da abinci kuma da alama kana jin yunwa,
Bud’e baki yayi zaiyi magana ogah yatsaidashi yace ban son gardama,
yanzu dai kaci abinci in ka gama munyi magana,
Baice komai ba yakar6i plate din yafara ci.
*****   *****     *****   ****
K’arfe sha d’aya dai-dai Amina tafarka daga baccin da take zazza6in ya safka, saidai jikinta da taji ba kwari,
abinda yafaru da ita yafad’o mata a rai dasauri takulle idonta tana addu’a Allah yasa duk abinda yafaru a mafarki ne,
Fuskar guy dinne tafad’o mata a rai bud’e idonta tayi hawaye suna zuba,
Tace Shikenan ya lalata min rayuwa, Allah kasaka min wannan wace kalar mummunar k’addara ce,
Kuka tayi sosai har saida ya isheta sannan tatashi tanufi toilet,
Bedsheet din tawanke tashanya shi a toilet din, sannan tayi wanka,
Shiryawa tayi cikin atamfa riga da zane red colour batayi wata kwalliyaba kawai turare tafeshe jikinta dashi koda batayi wata kwalliyaba ammah ta yi kyau,
Yunwace taji tana ji ahankali tabud’e k’ofar d’akin talek’a babu kowa a tsakar gidan angyara ko ina fas,
Dasauri tanufi kitchen domin bataso tahad’u da ummah saboda wata irin kunya da takeji,
Tana shiga tayi sa’a ummah ta had’a breakfast din har ta aje mata nata,
d’auka tayi tadawo d’akinta tazauna taci da tagama magani tad’auko tasha jin kanta har lokacin yana ciwo.
Kitchen takoma tawanke kwanonin da taga an 6ata,
‘Dakin ummah tanufa kanta a k’asa ahankali tayi sallama,
Zaune ummah take saman kujera tana dannah wayarta,
k’asa tazauna tagaishe da ummah,
Kallonta ummah tayi fuska a had’e ta amsa mata ciki-ciki.
Ummah akwai wani aiki da za ayi ne yanzu?
me za a girka ne?
A wulak’ance ummah takalleta tace aikin gidan ne zan bari yakai wannan lokacin ba ayiba?
Dariya ummah tayi tace kirufa min asiri ya za ayi insa amarya aiki itada take cikin amarci kije kawai kihuta,
Abbanki zai siyo mana abinda zamuci domin ni ba abinda zan girka maku,
Tashi tayi tafita jikinta duk ya yi sanyi,
Kallon tsanah ummah tabita dashi munafukar banza taja tsoki tacigaba da danna wayarta.
‘Dakinta takoma takwanta talumshe idonta fuskar mutumin ne take ta yi mata gizo bud’e idonta tayi taja tsaki tace Allah ya isa,
Wayarta tajawo tahau chart daman shine kawai takeyi tana samun sauk’in kad’aicin da takeyi.
Sallah ce kawai take tashi tana yi domin yau abbah shi yayi masu oder din abincin da zasuci har dare.
Duk shigowar da zaiyi gidan sai yashigo d’akin Amina ya duba lafiyarta domin yau baije kasuwa ba.
****    ****    ****    *****
A chan kaduna tunda Fahad yabar gida babu wanda yadamu dan dady cewa yayi ya kyauta ma kansa da yatafi yabar masa gida domin shi ba zai zauna da mazinaci ba,
saidai yayarsa khairat da k’anwarsa sunsha kuka sosai domin suna son d’an uwan nasu,
Mummy ma hankalinta yana tashi ammah da ta tuna abinda ya aikata sai taji duk haushinsa takeji,
Ga kunyar hindatu da takeji har batason had’a ido da ita intatuna abinda d’anta yayi shirin aikatawa.
Bayan wata shidda da faruwar abun daddyne yadawo daga tafiyar da yayi tsawo sati ukku a ghana bai fad’a ma kowa zai dawoba,
Wajen taran dare yadawo mummyce kawai a falo tana kallon labarai,
Batayi mamakin ganinsaba saboda ya saba irin wannan tafiyar.
Da murna tataresa tarakashi dakinsa yashirya takawo mashi abinci yaci,
Da yanutsu yakalleta yayi murmushi yace wai ina ‘yar uwar taki tunda nadawo banji motsintaba,
Itama murmushi tayi tace tana d’akinta mayb ma ta yi bacci domin tun magrib rabon da muhad’u,
ammah kaje kugaisa saboda ba dad’i ace ka dawo yau baku gaisaba har sai safe.
Mik’ewa yayi yace hakane bari intafi mugaisa.
Part din hindatu yanufa yana tura d’akin yaji a bud’e bata kulleba saidai fitila da aka kashe,
Ahankali yashiga d’akin yanufi wajen makunnin fitila yana murmushi domin har ya hango mamakin da zai bayyana a fuskarta idan taganshi ya dawo,
Yana kunna fitilar dasauri yaruntse idonsa domin ba zai iya kallon abinda idanuwansa suka gane masaba innalillahi wa inna’ilahiraji’un kawai yake nanatawa.
Innallillahi wa inna’ilaihiraji’un kawai yake nanatawa.+
Hindatu ce kwance da k’arto a bisa gadon ganin daddy yasa sukayi sauri suka rabu da juna,
k’arton yayi sauri yasaka kayansa yakoma gefe sai zare idanuwa yakeyi.
Hindatu jawo blanket tayi takulle jikinta tafashe da kuka tace na shiga ukku Alhaji dan Allah kayi hak’uri wlh sharrin shed’anne,
Tsaye yake a bakin k’ofar ya kasa motsin kirki hawayene suka zubo daga idanuwansa yace hindatu kin cuceni daman ashe karuwa na auro ban saniba miye kike nema baki samuba a gidan nan?
Wannan wace kalar rayuwace kika d’aukar ma kanki wadda bazata 6ullekiba,
ace kishigo min da k’arto cikin gidana har saman gado?
Alhaji dan Allah kayi hak’uri wlh itace takirani ba laifina bane,
saida nace ba zanzoba tace min ai baka nan.
Kallonsa daddy yamaida wajen mutumin da yake magana duk a tsorace yake kamar ace ket yaruga,
Yace zo kawuce kafitar min daga gida kaje Allah ya isa domin ni ba zan tona muku asiri ba wannan tsakaninku da ubangijinmu ne
Tahowa mutumin yayi yaruga dagudu yaficce daga d’akin,
Juyowa yayi yakalli hindatu da take ta kuka,
Ke kuma hindatu na sakeki kafin safe kitabbata kin bar gidannan kije Allah ya isa tsakanina dake,
wlh na yi da na sanin aurenki k’addara ce kawai ammah bakomai Allah yasaka min.
Dan Allah Alhaji kayi hak’uri,
Nidai na fad’a maki, ba na marmarin k’ara zama dake na tsaneki.
Ficewa yayi daga d’akin,
‘Dakinsa yakoma tafiya yake kamar wanda k’wai yafashe mawa a ciki hawayen takaici suna zuba daga idanuwansa,
Kallonsa mummy tayi cikin mamaki ganin lokaci guda duk ya canza,
Dasauri tatashi tanufi wajen da yake tace,
Alhaji lafiya? Meyake faruwa ne ko hindatu batada lfy ne?
Lokaci guda duk tajera mashi tambayoyin,
Dakyar yabud’e bakinsa yace babu ko d’aya daga ciki hafsat,
Runtse idonsa yayi yace wai matata ta auren sunnah zan kama tana zinah har cikin gidana,
Innalillahi wa inna’ilaihiraji’un Alhaji wannan wace kalar maganace kakeyi hindatun dakanta,
Bud’e idanunsa yayi yace hafsat zan miki k’arya ne?
Da ace fad’amin akayi nima ba zan yarda ba sai gashi na kamata da kaina.
Jikin mummy duk yayi sanyi ta ma rasa me zatace.
Daidai lokacin hindatu tashigo d’akin sanye da doguwar riga da gyale tana kuka,
Share hawayen fuskarta tayi takalli mummy tayi murmushi sannan tamaida kallonta wajen daddy tace,
Alhaji banyi mamakin sakina da kayiba saboda ni da kai daman bamu dace da junaba domin ba halinmu d’ayaba,
Nasan dole irin wannan ranar tana nan tafe.
STORY CONTINUES BELOW
me kuma yakawo ki d’akina kifita kiban waje tun kan ind”au k’ak’k’auran mataki akanki,
Murmushi tayi tace zan fita ammah inaso kusan wani abu d’aya hajiya kiyi hak’uri fahad baida laifi nice na nemeshi a lokacin domin tun lokacin da nafara sa shi a idanuwana naji ina sonsa…….
Nan takwashe duk abunda yafaru tafad’a masu,
Tunda tafara mummy take kuka,
Tace Allah ya isa hindatu kin cuceni kin rabani da d’ana yanzu bansan inda zan ganshiba kije keda Allah.
Kallon tsana Abbah yabita dashi yace lallai hindatu ashe baki da imani d’ana na cikina zaki nema kina auren ubansa kuma,
Pls get out from my room!!!
Na tsaneki hindatu ba na marnarin k’ara ganinki,
Na yi farin ciki da Allah baisa muka samu haihuwa dake ba,
Domin ba na fata d’ana yad’auko irin mugun halinki.
Murmushi tayi tace na san haka Alhaji,
Na barku lafiya gobe za azo a kwashe min kayana, na barku lafiya,
tana gama maganar taficce,
Hankalin daddy duk ya tashi wajen mummy yanufa da taketa kuka rik’ota yayi yazaunar da ita bisa kujera shima yazauna,
Hafsat kiyi hak’uri kidaina kukan hakanan pls.
‘Dago kai tayi takalli daddy tace Alhaji dole inyi kuka bansan ina zanga d’ana ba,
Hakane hafsat munyi kuskure da bamu saurari ta bakin fahad ba muka d’aura duka laifin a kansa,
Ni dai daman nasan ba halin d’ana bane wlh, kawai dai na yarda saboda ganinsa da nayi a cikin d’akinta,
Kinga da ace a d’akinshi muka ganta shine zamuce ita tanemeshi.
Mummy tak’ara fashewa da kuka tace innalillahi wa inna’ilaihiraji’un wannan wace kalar k’addara ce, Allah gareka muka dogara,
Allah kakawo mana mafita.
Dakyar daddy yashawo kanta tayi shuru yace gobe insha Allahu zai sa afara neman fahad.
Tun daga ranar ake nemansa duk inda ake tunanin za a ganshi anje ammah babu shi,
Gidan redio, gidan Tv duk anyi cigiya babu labarinsa, kullum cikin addu’o’i ake.
Mummy da ‘ya’yanta kullum cikin kuka sukeyi Alhaji ne kawai yake danne damuwarsa yana d’an kwantar masu da hankali.
****   ****   ****   ****
Tunda asuba yafarka kasancewar daman baiyi wani baccin kirki ba,
wanka yaje yayi yad’auro Alwallah,
Shiryawa yayi cikin wani yadi fari ammah yadin ya d’an k’ok’e, sallah yagabatar da ita ya dade yana addu’ar neman nasara acikin tafiyar da zaiyi,
Saida gari yafara yin haske sannan yatashi daga saman sallayar,
Duk abinda yake buk’ata nashi yad’auka,
Kasancewar bakowa gidan sai shi kad’ai su ogah suna wajen club,
Takarda da biro yad’auko yayi rubutu kamar haka,
  *Aslm, ya kuke? Kar kuzo kuna nemana hankalinku yatashi na tafi zan koma wajen iyayena innemi gafararsu daman na ce maku k’addara ce kawai tahad’a ni da ku har mukayi wannan zaman*,
*Ku ma ina maku fatan shiryuwa na barku lfy, daga fahad umar*.
     Bissalam*
Sai yadauko dubu hamsin yad’aura saman takardar sannan yad’auki ‘yar jakarsa yafita daga gidan yakulle masu,
Saida yayi tafiya mai nisa yafita daga cikin dajin yana waiwayen dajin da mamakin irin rayuwar da yayi a cikinsa,
sannan yasamu mai acha6a yahau yace yakaishi tashar kaduna,
Tunda suke tafiya gabansa fad’uwa kawai yake tunani yake ya zaije yataradda iyayensa? Zasu kar6esa? Shin har yanzu suna fushin ko sun daina?
Tambayoyin da yake tayi ma kansa kenan ya rasa amsarsu.
Wajen k’arfe sha biyu suka iso garin kaduna,
Wani kalar iska yaji yana ratsashi jin ya shigo mahaifarsa,
Lumshe idanuwansa yayi,
Murmushi yayi wanda bai kai zuci ba.
Mai acha6a yasamu yafad’a mashi inda zai kaishi,
Tunda suka iso gabansa yake fad’uwa baisha wahalaba wajen gane gidan koda anguwar ba laifi ta d’an chanza,
Daidai k’ofar gate din gidan yasafka yabiya mai acha6a kudinsa,
Saida yayi kusan minti goma yana tsaye ya rasa ya zaiyi domin yana cikin fargaba,
Ahankali yafara k’wank’wasa gidan,
Maigadine yafito yana tambayar wanene?
Jin muryar mai gadin yasa yayi d’an murmushi yace malam idi kabud’e nine,
Bud’ewa yayi yakallesa kamar yanaso yatuno fuskar ammah ya kasa, yace yaro kaine wa? kuma wa kake nema?
Murmushi yayi yace malam idi yanzu baka gane niba fahad ne.
Eyyeh fahad fa kace,
kallonsa malam idi yake cikin mamaki yaro d’an kwalisa d’an gayu ga naira ammah shine yakoma haka kamar wani almajiri,
Fashewa da kuka malam idi yayi yace fahad ashe zamu k’ara ganinka ina kashiga muna ta nemanka?
Murmushi fahad yayi yace malam idi ai gani na dawo kukan ya isa haka,
su daddy suna ci?
Eh suna nan kashiga,
Tafiya yake ahankali gabansa sai fad’uwa yake yanufi cikin gidan parking space yakalla yaga motocin duk suna nan alamun daddy yana gida,
Ahankali yabud’e gidan yashiga gefen da d’akinsa yake yakallah yaga a rufe yake,
Tsakar gidan bakowa da alama duk suna d’aki,
K’ofar main palor yanufa gabansa sai fad’uwa yake.
K’arar Tv yaji da alamun suna ciki, saida yadad’e a tsaye wajen tsawon minti biyar sannan yad’aga labulen d’akin……..
 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *