K’ADDARA CE CHAPTER 3
Ahankali yad’aga labulen d’akin daddyne da mummy yagani zaune saman 3 setter sai yaya khairat da Fatima zaune bisa 2 setter,+
Muryarsa tana kyarma yayi sallama,
Dasauri duk suka juyo suka kallosa jin muryar da ba zasu ta6a mantawa da itaba a rayuwarsu,
A firgice mummy tamik’e tsaye tana nunashi da yatsa tace Alhaji kudubu min mafarki nake ko gaske dan Allah kufad’a min fahad dina ne?
Daddy ya yi mutuwar zaune ya kasa motsin kirki kallon fahad kawai yake,
Khairat ce da fatima suka taso dagudu suka nufi wajensa kowa sauri yake yariga d’an uwansa isa.
Rungumesa sukayi su duka biyun suna kuka,
Shima rungume ‘yan uwan nasa yayi yana jin dad’i cikin ransa koda zuciyarsa a tunkushe take da bak’in ciki.
Fatima tace yaya fahad kaine dagaske? Meyasa katafi kabarmu,
Khairat ta amshe tace baka kyauta manaba fahad da har katafi kabarmu ba ka tunanin wane irin hali zamu shiga,
Meyasa ka aikata haka,
Kuka sukeyi sosai, runtse idonsa yayi hawaye suna zubo masa yak’ara matse ‘yan uwan nasa a jikinsa yace,
Kuyi hak’uri wlh ba da son raina hakan tafaruba.
Dai-dai lokacin mummy ta iso inda suke tana kuka tace kumatsa min inji d’umin d’ana,
Janye jikinsu sukayi daga nasa suka bata waje,
Ahankali yabud’e idanuwansa da hawaye suke ta zuba rungumesa mummy tayi tace fahad baka kyauta maniba ashe har zaka iya kai wannan lokacin ba tare da ka nememuba ashe zaka iya fushi da mu haka?
Duk yadda fahad yaso yadaure kar yayi kuka ammah ina ya kasa,
Fashewa yayi da kuka yace mummyna kiyi hak’uri wlh ba da son raina hakan yafaruba dan Allah kuyafe min wlh ba zan k’ara aikata hakan ba,
Bakomai fahad bakayi mana komai ba inma ka yi mana toh wlh mun yafe maka duniya da lahira ammah dan Allah kar kak’ara gudunmu,
Goge hawayen fuskarsa yayi yad’ago mummy daga jikinsa itama yagoge mata hawayen yayi murmushi yace insha Allahu ba zan k’araba mummyna kidaina kuka,
Itama murmushi tayi tace na daina my son.
Kallonsa yamaida a wajen daddy da har yanzu zaune yake saidai ya jingina kansa da kujera ya lumshe idonsa,
Ahankali yarik’o hannun mummy yanufi wajen da daddy yake zaune,
Su khairat suna biye dashi a baya kamar za a k’wace masu shi.
Sakin hannun mummy yayi yamatsa chan kusa da k’afafun daddy yatsugunna hawaye suna zubowa daga idanunsa muryarsa tana rawa yace daddy dan Allah kayafe min abinda yafaru wlh..
STORY CONTINUES BELOW

Bud’e idanuwansa daddy yayi da sukayi jawur ya katse mashi magana yace ya isa haka fahad maganar ta wuce ko a mafarki banson ink’ara tunota,
Nagode ma Allah da gaskiya tabayyana,
Fahad mune yakamata munemi yafiyarka domin mu mukayi maka laifi,
Mun d’aura maka laifin da baka aikataba ba tare da munyi bincikeba.
Fahad yayi murmushi yace bakomai daddy koma minene kuka aikata a gareni daidai ne domin kun isa dani.
Ammah fahad nayi mamaki da kad’auki tsawon wannan lokacin ba tare da ka nememuba duk inda mukasan zamu sameka mun nemeka ammah babu kai babu labarinka,
Hawayen fuskarsa fahad yagoge yace kugafarce ni daddy nima ba a son raina nayi nesa daku ba ammah insha Allahu hakan ba zai k’ara faruwa ba.
Haka suka sha koke-kokensu na murnar dawowarsa,
Ko masallaci daddy yana rik’e dashi sukaje kamar za a k’wace masa shi.
Ma’aikatan gidan duk sunyi muryar dawowarsa,
Abinci mai rai da lafiya mummy tasa aka shirya masa,
Aranar saida akayi ‘yar k’aramar walima a gidan,
Nan yakejin labarin rabuwar daddy da hindatu wajen ‘yan uwan nasa,
Fatima dakanta tashiga tagyara ma yayan nata d’akinsa ko da kasancewar d’akin daman fes yake ana gyarasa.
Sai k’arfe taran dare daddy yasa driver yamaida khairat gidan mijinta ba yadda ta iya dole tatafi tana mai kewar d’an uwan nata.
Abokansa ma sunyi murnar dawowarsa.
**** **** **** ****
A chan 6angaren Amina ko da taga dare ya yi hankalinta yatashi domin tana tsoron dawowar wad’annan ‘yan fashin,
Kwance take a saman gadonta juyi kawai take ta kasa bacci ko kad’an tad’anji motsi sai ta tsorata,
Ga shi ba ta minti talatin sai fuskar guy din ta fad’o mata a rai saidai taja tsaki saboda haushinsa da takeji.
Ahaka har bacci 6arawo yasaceta.
Tun da asuba datayi sallah takoma bacci ba ita ta farkaba sai wajen 8:30am dasauri tafito daga d’akinta tanufi kitchen domin tahad’a masu breakfast kafin ummah tafito tarufeta da masifa,
Sannan tagyara gidan tayi wanke-wanke .
Sai wajen k’arfe goma tagama ayyukanta,
‘Dakin ummah tashiga tagyara mata shi fes kasancewar ta san ummah tana d’akin Abbah.
Fitowa tayi takoma d’akinta tagyara takunna turaren wuta Sannan tafad’a toilet tayo wanka,
Mai da powder kawai tashafa sannan tashirya cikin material riga da skirt pink nd black colour sunyi mata kyau sosai sannan tafeshe jikinta da turare.
Fitowa tayi tanufi d’akin abbanta da sallama tashiga tataddashi yana shirin tafiya kasuwa,
Tsugunnawa tayi har k’asa tagaisheshi kanta yana kallon k’asa saboda kunyar abbah da takeji,
Murmushi yayi yace lfy lou mamana,
Dafatan kema kin tashi lfy,
K’ara sunne kanta tayi tace lafiya lou Abbah
Toh Alhmdllh daman akwai maganar da nakeso muyi in na dawo daga kasuwa ammah bari muyi ta yanzu,
Murmushi tayi tace toh Abbah,
Yauwa ga kud’in wannan bawan Allan da yabada na sadakinki ya..
Bata jira jin abinda abbah zai ida fad’a ba tace,
STORY CONTINUES BELOW

Abbah kawai in angansu amaida masu kud’insu ni wlh ba zan auri d’an fashi ba tafashe da kuka.
Kallonta Abbah yayi yace nima hukuncin da na yanke kenan mamana,
Ko da na yaba da hankalinsa a cikinsu kwata-kwata shi baiyi kama da d’an fashi ba domin yana da tausayi sosai,
Nima ba zanso ad’aura ma d’iyata aure da kud’in sata ba zan aje kud’in.
Kikwantar da hankalinki kidaina kukan haka,
Share hawayenta tayi tace toh Abbah.
Yauwa Allah yayi miki albarka,
Ameen Abbah,
Tashi yayi zai tafi kasuwa rakoshi tayi bakin k’ofar gida tace Allah yakiyaye Abbah sai ka dawo.
Ameen mamana.
Saida taga ya tada mota sannan tadawo gida,
‘Dakin abbah takoma tagyara fes sannan tatafi kitchen tad’auko breakfast d’inta takoma d’akinta tayi.
Da tagama taje tawanke kwanonin da ta 6ata sannan tanufi d’akin ummah da sallama tashiga,
Tsugunnawa tayi k’asa tana gaishe da ummah,
Ummah da take kwance a saman 3 setter tana danna waya ba tare da ta juyo ta kalleta ba ta amsa mata ciki-ciki kamar yadda ta saba,
Ummah yau me za a girka?
Ba tare da ta juyo ta kalleta ba tace amarya har angama amarcin kenan,
Tuwon shinkafa da miyar ku6ewa nakeson ci akwai kifi a cikin fridge ai ko,
Eh akwai,
Ohk, sannan ga wanki na nan na had’a za kiyi min,
Tace Toh ummah, tashi tayi tafita daga d’akin
Tsaki ummah taja tace munafukar banza kullum kaganta sumi-sumi kamar duka kenan.
Kitchen tashiga tad’aura girkin sannan tad’auko wankin ummah tafara,
Ahaka har tagama girkin, sai wajen k’arfe ukku tagama wankin,
‘Dakinta takoma tayi wanka tashirya sannan tad’auko abincinta taci ko da tagama littafin islamiyyarta tad’auko tayi tilawar karatu,
Tana sallar la’asar tayi shirin islamiyya,
Jakar islamiyyar ta tad’auko tanufi d’akin ummah,
Dasallama tashiga tace ummah zan tafi islamiyyah.
Harararta ummah tayi tace kin gama min wanki na?
Eh ummah na gama,
Ta6e baki ummah tayi tace bawani islamiyyar da zakije na san yawon karuwancin da kika saba zakije mudai fatanmu kar akwaso mana cikin shege cikin gida.
‘Dago kai tayi takalli ummah tuni idanuwanta sun cika da k’wallah tace wlh ummah babu inda nike zuwa islamiyyah kawai nake zuwa kiyarda dani.
Ta6e baki ummah tayi tace daman kullum dasunan islamiyyah kike fakewa,
Ni wuce kibani wuri kuma kidawo dawuri tunda yau ba za ayi abincin dareba kiyi min guga,
Goge hawayen fuskarta tayi tace toh ummah sannan tafice tatafi,
A chan gaba da gidansu kad’an tahango k’awarta sumayya a tsaye tana danna waya da alama ita zata kira tafito sutafi islamiyyah domin ba ta shiga gidan saboda tana tsoron masifar ummah da bak’ak’en maganganun da take yada masu.
Daidai lokacin Amina ta iso tayi sallama tace yau ba sai kin kiraniba gani na fito dawuri,
Murmushi sumayya tayi suka gaisa sannan suka kama hanyar islamiyyah.
**** **** **** ****
Bayan wata biyu fahad ya murje ya k’ara kyau ya koma fahad d’insa na ainahi d’an gayu,
Zaune yake d’akinsa yana latsa laptop dinsa Fatima ce tashigo d’akin da sallama.
Amsa mata yayi ba tare da ya juyoba.
Shigowa tayi tanufi inda yake tana murmushi tace yayana nakaina sannu da aiki,
Daina abinda yakeyi yayi yajuyo yakalleta shima yayi murmushi yace yauwa k’anwata takaina,
Yayana kataso muje muyi lunch su mummy suna chan kan dining suna jiranmu,
Murmushi yayi yace toh,
kashe laptop din yayi yatashi suka fito tana mashi shagwa6a yana biye mata har suka isa wajensu mummy,
Wuri suka samu suka zauna suka gaishe da iyayen nasu sannan suka fara cin abinci.
Bayan sun gama zaune suke a parlor suna hira fahad yace daddy dan Allah inaso asamomin admission a india inaso inje inyi masters d’ina a chan,
Kallonsa daddy yayi yace toh insha Allahu za a samo maka nima burina kazama babban likita,
itama Fatima ina neman mata admission ne a university ta nan kaduna domin tacigaba da karatunta,
Murmushi yayi yace toh daddy na gode,
Kallon Fatima yayi da taketa murna yace k’anwata angirma za a shiga university toh wane course zaki yi choosing,
Murmushi tayi tace biochemistry,
Wow gud gurl kin iya za6ar course
Allah yabada sa’a,
Ameen suka ce dukansu,
Tun daga ranar fahad yafara shirye-shiryen tafiya india,
Bayan sati biyu jirginsu yad’aga.
**** **** **** ****
tunda ta tashi yau takejin jikinta ba dad’i daurewa takeyi kawai tana aiki domin ta san ko ta fad’a ma ummah ba ta lafiya ba yarda za tayiba,
duk ta bi ta rame lokaci guda domin ko abinci a ranar ta kasa ci,
Kitchen take tana soya kifin da abbah yadawo dashi daga kasuwa zuciyarta taketa tashi daurewa kawai take,
Amai ne taji yana shirin kufce mata dagudu tafito daga kitchen d’in tanufi chan bakin famfo tafara kwarara amai kamar zata amaye ‘yan cikinta………..