K’ADDARA CE CHAPTER 4

 K’ADDARA CE CHAPTER 4

Dasauri abbah yanufi wajensu domin jin halin da d’iyar tasa take ciki.+

Kallonsa likita yayi yace Alhamdulillah tun kan muyi aikin Allah yataimake mu kan d’iyar yalek’o  tahaihu dakanta batare da mun yanka ta ba, saidai ta jigata dayawa yanzu ana gyarata ne za a kaita d’akin hutu ita da babyn nata anyi mata allurar bacci yanzu bacci take ammah muna sa ran nan da awa d”aya zata iya farkawa, ammah gaskiya ba yanzu za a sallameku ba saboda tana jin jiki sosai sai munga ta warware sannan zamu sallameku.

Muje office inbaka takardar magunguna da injection da za a siyo mata,

Abbah saboda murna ya ma mance bai tambayi abinda aka samuba.

Bayan nursing d’in sun gama gyarata da babyn nata waje suka fito rik’e da babbyn ita kuma mai jego aka turata zuwa d’akin hutu domin za asa mata drip.

Dasauri gwaggo tataso takar6i babbyn

Masha Allah take ta cewa ganin baby gurl fara sosai maikyau kwata-kwata ba ta kama da mamantata duk kyan Amina babyn nata tafi ta.

Dai-dai lokacin abbah yadawo daga wajen siyan maganin.

Wajen gwaggo yanufa yana murmushi mik’o mashi babyn tayi tace Alhaji ga fa jikar taka,

Kar6a yayi yace masha Allah, Allah yarayata sannan yai mata addu’a

Gwaggo tace Alhaji bari inje gida kafin tafarka indafa mata abincin da yafi dacewa taci.

Toh gwaggo muje in aje ki.

A’a kazauna bari inje inhau adaidaita.

Kud’i abbah yazaro yabata dakyar ta amsa.

A 6angaren Amina ba ita tafarka ba saida tayi kusan awa biyu tana bacci,

Nurses d’inne suke zagayowa duk bayan 30 minutes,

Ahankali tabud’e idonta babu kowa d’akin daidai lokacin nurses d’in suka shigo d’akin dubata suka k’ara yi ganin babu matsala yasa suka fito suka fad’a ma abbah tashinta domin ahad’a mata tea mai kauri tasha.

Dasauri Abbah yashiga d’akin rik’e da babyn dasallama yashiga.

Wajen gadon yanufa yana mata sannu kasa bud’e idonta tayi saboda kunyar abbah da takeji,

Amina kibud’e idonki kiyi ma babyn addu’a mana.

Bud’e idanuwanta tayi tasafkesu akan babyn da abbah yamik’o mata masha Allah tace a cikin zuciyarta sannan tamik’a hannu takar6eta, murmushi yasu6uce mata ganin yadda babbyn take kama da ubanta ko da sau d’aya tata6a ganinsa ammah ba zata ta6a mance fuskarsa ba domin kullum dashi take kwana take tashi a ranta.

Addu’a tayi mata sannan abbah yakar6eta.

Kallon abbah tayi tace Abbah Allah tana kama da d’an fashin nan.

Murmushi abbah yayi yace masha Allah ashe babyn babanta tabiyo.

Abbah dakansa yahad’a mata tea mai kauri tasha,

Wajen sha biyun rana lokacin gwaggo tadawo d’auke da kayan abinci.

Sallama abbah yayi masu yace zai tafi ammah zai dawo da anjima.

STORY CONTINUES BELOW

Dakyar Gwaggo talalla6ata taci abinci sai da sukayi dirama sosai da gwaggo sannan Amina tayadda tashayar da yarinyar.

Haka Amina taci gaba da zaman asibiti tana samun kulawa daga wajen mahaifinta da gwaggo ladi har tsawon kwana goma,

Gwaggo ladi ita take mata wankan jego duk wani gata da mai jego take samu itama tana samun daidai gwargwado.

Tunda ummah tazo bayan kwana ukku da haihuwar bata k’ara lek’owa ba shima saida sukayi kaca-kaca da abbah sannan tazo.

Ranar suna da Abbah yatambayeta sunan da takeso asa ma d’iyar duk’ar da kai tayi tace abbah duk sunan da kaga ya dace kasanya mata domin ni da ita duk a k’ark’ashinka muke,

Murmushi abbah yayi yace Allah yayi maki albarka toh na za6a mata sunan gwaggo ladi saboda mutunci da alkhairin da takeyi mana nima zan mata ka-ra dan haka na sanya mata Aisha ammah idan ya yi miki?

Murmurshi itama tayi tace abbah nima ya yimin na ji dad’in hakan.

Yarinya ta ci suna Aisha ammah ana ce mata Ameerah,

Gwaggo ladi saboda murna kuka tafashe dashi tana godiyar ka-rar da akayi mata.

Abbah rago yayanka mata gwaggo ladi takira ‘yan uwanta a gidanta suka soya.

Ba’ayi wani taron suna ba kasancewar suna asibiti kuma ba kowa yasan da cikin ba.

Bayan kwana goma aka sallamesu suka dawo gida nan k’ananun maganganu suka fara tashi a anguwar cewa Amina ta yi cikin shege ta haihu mutane har shigowa suke ganin k’wam.

Abbah bai damuwa da surutansu harkar gabansa kawai yakeyi.

Hankalin Amina a tashe yake jin maganganun da ake ta yadawa a kanta hatta ita kanta ummah yada mata maganganun take,

Gashi ummah ta bud’e wuta cewar ba zasu zauna da d’an shegeba saidai akaishi gidan marayu saida sukayi rigima sosai da abbah ganin igiyar aurenta ta fara rawa yasa tahak’ura domin tasan zai iya sakinta akan d’iyarsa.

Amina bata samun sauk’i sai wajen abbanta da gwaggo ladi, tana kula da d’iyartata saboda tana sonta sosai.

Tsakaninta da ummah kuma saidai hange daga nesa domin harara da bak’ak’en maganganu kawai take shiga tsakaninta da ummah,

Abbah dakansa yasamo mai aikin gida saboda d’iyarsa tahuta itama dan yasan halin ummah batada imani k’aramin aikinta ne tasa Amina aiki tana jego.

Bayan wata biyu Ameerah sai k’ara wayau take ta yi 6ul6ul kamar ‘yar wata ukku ga kulawa tana samu daga 6angarensu abbah.

kasancewar yau Alhamis kwance take d’akinta ta lalla6a Ameerah da tasha riga ta yi bacci,

Chart kawai takeyi domin shi yake d’ebe mata Kewa,

Abbah ne yashigo da sallamarsa, tashi tayi daga kwancen da take ta amsa mashi tare da gaisheshi.

Kallonta yayi cikin fara’a yace sarkin rigima har tayi bacci knan,

Murmushi tayi tace eh abbah bata dad’e da yi ba.

Wuri yasamu yazauna daga gefen gadon sannan yace Amina magana nakeso inyi dake,

Duk’ar da kanta tayi tana wasa da yatsunta tace toh abbah,

Ledar da yashigo da ita yabud’e kud’i yad’auko wad’anda adadinsu zai kai dubu hamsin yamik’a mata yace ga wannan,

Kar6a tayi tana kallon abbah cikin mamaki domin jin ko kud’in minene.

Murmushi yayi yace wannan kud’in gadonki ne da ummanki ta rasu,

Sannan yamik’o mata dubu ishirin yace wannan kuma kud’in sadakin kine halak d’inki ne.

Kwallace tacika mata ido tace abbah ammah ai da ka aje wajenka,

A’a mamana nafison ki aje wajenki domin bamusan halin rayuwa ba, idan nafad’i namutu ai bakowa yasan kud’in naki bane.

Kasa magana Amina tayi jikinta duk ya yi sanyi.

Tashi yayi yamatsa kusa da Ameerah yashafa kanta yana murmushi,

Kallon Ameena yayi yace mamana Allah yayi maki albarka dake da zuriyarki baki d’aya.

Ameen abbah.

Murmushi yayi mata akaro na k’arshe yace toh ni zanje kankia dubo wani abokina da baida lafiya,

Toh Abbah Allah yabashi lafiya, Allah yamaido mana da kai lafiya.

Ameen mamana Allah yayi maki albarka.

Fita yayi daga d’akin yanufi d’akin ummah dake zaune tana tsifar kitso,

Yace zainab nidai na wuce zanje kankia gano Alh sani da nafad’a maki baida lafiya kusan sau biyu yana kwanciya asibiti ammah banjeba.

Ta6e baki tayi tace toh adawo lafiya

Allah yasa, zainab kikula da Amina da yarinyarta dan Allah.

Haba Alhaji wai mi kamaidani ne cutarsu nake ne koko wani abu ita Aminar tace ina mata?

Ita ai ba yarinya bace zata iya kula dakanta.

Murmushi yayi yace nasan da haka zainab ammah ke matsayin uwa kike a wajenta idan tayi ba daidai ba ai kina da ikon kwatanta mata adai ci gaba da hak’uri.

Ummah saboda k’ulewar da tayi kasa magana tayi tacigaba da abinda takeyi.

Baidamu da shirun da tayi ba yafita daga d’akin yayi tafiyarsa

A ranar Amina bata lek’o tsakar gida ba d’akinta tayi zamanta jikinta duk ya yi sanyi gabanta sai fad’uwa yake.

Jin fad’uwar gaban ya tsananta yasa tatashi tad’auro alwallah tafara karatun alk’ur’ani har saida Ameerah tafarka daga bacci sannan ta aje.

Bayan sallar isha’i zaune take tana lalla6a Ameerah domin tayi bacci,

Salati da kuka taji ummah tanayi cikin tashin hankali dasauri tad’auki Ameerah tanufi d’akin ummah,

Waya taji ummah tanayi tace wane asibiti ne?

Toh gamunan zuwa k’ara fashewa da kuka tayi tafad’a saman kujera tace nashiga ukku ni zainab yau asirina ya tonu hijabi tajawo zata saka,

Dasauri Ameena ta iso wajen ummah tace lafiya ummah mi yake faruwane?

Kuka ummah takeyi sosai tace Amina nashiga ukku bansan ya zanyi da rayuwata ba idan narasa shi.

Ummah dan Allah me yake faruwa kifad’a mani  wanene baida lafiya inji Amina itama kukan take tana rungume da Ameerah da take bacci.Cikin kuka ummah tad’ago kai takalleta tace Amina abbanki ne yayi accident baisan inda kansa yakeba duk ya yi karaya yanzu haka ance yana asibiti.

Amina tak’ara fashewa da kuka tace Innalillahi wa’inna ilaihiraji’un nashiga ukku abbah shine gatana shine rufin asirina ya ubangiji katashi kafad’ar abbanah.

Ummah bari ind’auko hijab mutafi asibitin,

Dasauri tanufi d’akinta tagoya Ameerah sannan tad’auko hijabinta saboda rud’ewa a baibai tasanyata bata luraba kuka kawai takeyi.

Fitowa tayi tatadda ummah har ta kai zaure dasauri tabi bayanta dakyar tasamu takulle gidan sannan suka samu mai adaidaita sahu.

Ko a cikin napep kuka kawai sukeyi babu mai lallasar wani har suka iya comprehensive da take mashi.

Ummah ce tabiya mai adaidaita sannan suka nufi cikin asibitin direct Accident & Emergency unit suka nufa,

Likitane sukaga ya fito daga wani room dasauri suka nufi inda yake ummah ce tayi k’arfin halin yi mashi bayanin wanda aka kawo d’azu,

kallon ummah doctor d’in yayi yace na gane ammah gaskiya saidai kuyi hak’uri Allah ya yi mashi rasuwa nan ne d’akin da nafito yanzu haka ma xuwa zanyi inkira azo akaishi matuary kafin dasafe akira iyalansa ammah tunda gaku kunzo ai shikenan.

Ummah kallonsa take kamar bata fahimci abinda yake cewaba.

Amina ce tayi k’arfin hali tace doctor ko dai baka fahimci wanda muka ce ba, ba abbanah kake nufiba domin shi bai rasuba,

Ummah taho muje mutambayi wasu,

Kallonsu doctor yayi yace kushigo kuga idan ba shi bane sai kutafi ammah wannan gaskiya shikad’ai aka kawo mana bayan sallan magrib.

‘Dakin suka nufa jikinsu duk ya yi sanyi Amina kuka kawai take,

wajen gawar da take lullu6e doctor d’in yanufa zanen da aka lullu6eta duk jini.

Runtse idonta Amina tayi gabanta sai k’ara fad’uwa yake addu’a takeyi a zuciyarta Allah yasa ba abbanta bane.

Zanen da aka rufe gawar doctor yajanye yace ga mutumin,

Dasauri ummah ta ida isa talek’a k’ara tasaki tafad’i k’asa tace na shiga ukku wlh asirina ya tonu yau na bani na lalace ni zainab wlh shine dagaske ya mutu ko suma yayi doctor?

alhaji dan Allah katashi kar kamutu kaine farin cikina,

Dasauri Amina ta6ud’e idonta ba tare da ta iso wajenba tace ummah ko dai kin rud’ene saisa kikaga kamar abbah ne?

Hawaye sha6e-sha6e a fuskar ummah tad’ago kai tawulla mata hara tace dan ubanki a cikin hankalina nake kizo kigani mana,

Amina tak’ara rikicewa tace a’a ummah kar kice abbah ya mutu, bari kigani yana da rai dakyar Amina taja k’afarta ta isa wajen gawar talek’a dagudu tafad’a saman gawar tana kuka tace abbah dan Allah katashi wlh nasan ba mutuwa kayiba bacci kake likita yake jawo maka mutuwa dan Allah katashi abbanah kai kad’ai nakedashi a rayuwata kaine rufin asirina kaine kad’ai nake gani inji dad’i dan Allah kar katafi kabarni abbah na,

Kuka take gwanin ban tausayi ga Ameerah ta farka itama tana kuka ammah Amina bata damuba ta abbanta kawai take.

STORY CONTINUES BELOW

Likitan ne yafita yakira wasu nurses dakyar suka janye Amina daga saman gawar,

Goyon suka kwance jin jaririya tana ta kuka,

Sumbatu kawai Amina takeyi kamar mahaukaciya dakyar suka samu tazauna suka taimaka mata tashayar da d’iyar.

Nurses d’inne suka dinga masu nasiha kan sudaina kukan mutuwa babu kyau addu’ansu kawai suke buk’ata

,

Dakyar sukayi shuru nan Amina tatashi tana rungume da babynta tanufi wajen gawar Abbah tafara mashi addu’a hawaye suna zuba a idonta.

Ummah ta kasa motsin kirki tunda tazauna wajen itama addu’an tacigaba dayi mashi.

Wayar abbah aka mik’o masu akace susan yadda za a yi da gawar,

Dasauri ummah talalubo number d’in Alhaji sani abokin abbah bugu d’aya yad’auka nan take fad’a mashi halin da suke ciki.

Alhaji sani ya firgita da jin mutuwar abbah salati kawai yakeyi cewa yayi gashinan zuwa asibitin

Ba a yi minti goma ba sai gashi ya isa nan hankalinsa yak’ara tashi idanuwansa suka kad’a sukayi jawur addu’a yayi ma abbah,

Sannan aka d’auki gawar suka nufi gida,

Amina da ummah hawaye kawai suke suna mashi addu’a,

‘Dakin abbah aka aje gawar ganin har k’arfe sha d’ayan dare ya yi.

Wasu daga cikin mak’otansu gidan sukazo suka zauna a lokacin.

Alhaji sani yayi ta basu baki sai wajen d’aya yakoma gidansa.

Su ummah ko kad’an basu runtsaba duk sun canzs sunzama gwanin tausayi mak’otansu suma a gidan suka kwana dakyar suka lalla6a su Amina suka d’anci abinci,

A daren akayi ta kiran waya ana fad’a ma mutane.

Washe gari k’arfe goma angama shirya gawar mutane dayawa suka sallaci gawar aka tafi kaita Allahu akhbar kullunafsin za’ik’atul maut.

Sai a lokacin Amina tak’ara tabbatarwa da ta rasa abbanta ya tafi inda ba zai k’ara dawowa gareta ba,  tayi kuka har tagode ma Allah,

Ameerah kuma saidai hannun ‘yan zuwa gaisuwa tawuni saidai idan ta ji yunwa ake kawota wajen Amina.

Abokan abbah su suka d’auki nauyin duk abinda ake buk’ata azaman gaisuwar har tsawon kwana bakwai.

Bayan sadakar bakwai kowa ya watse gida ya koma daga ummah sai Amina,

Kowa rayuwarsa yake.

Tun dasafe mai aikinsu take zuwa gidan tayi shara tahad’a masu breakfast sai tayi girki tatafi, tsakanin Amina da ummah gaisuwa ne kawai take had’asu.

____________________

Bayan sati biyu Amina ce a toilet tana wanka daidai lokacin Ameerah tafarka tafara kuka dasauri ta d’auraye jikinta tafito tad’auketa,

Ummah ce tashigo d’akin kamar an jefota ranta a 6ace takalli Amina tace ke ya zaki aje wannan shegiyar d’iyar taki tayi ta mana kuka bacci nake ammah kukanta yatasheni,

Jikin Amina yana kyarma tace ummah dan Allah kiyi hak’uri wlh wanka nashiga bansan za ta farka a lokacinba.

Harararta ummah tayi tace toh wlh anyi nafarko kuma anyi na k’arshe ba zata sa6uba ni da gidana wannan shegiyar d’iyar tahana ni hutawa dan haka ki kiyaye in ba hakaba zan d’auki mataki,

Toh ummah insha Allahu hakan ba zata k’ara faruwaba,

Ta6e baki ummah tayi tace ya rage naki har ta juya zata tafi sai kuma tajuyo tace yauwa na mance ban fad’a makiba daga yau mairo mai aiki za ta aje aiki saboda babu yadda za’ayi wannan d’an aikin gidan da baida wani yawa ace har sai ansamo ‘yar aiki toh wlh ban iya almubazzaranci ba, ba da kud’ina ba dan haka na sallameta sai ki tsara yadda zaki tafiyar da aikin gidan kuma banson k’azanta kisan yadda zaki dinga renon wannan shegiyar.

Bata jira abinda zata ce ba kawai tafice fuuu daga d’akin.

Hawayen fuskarta tashare domin ta tsani taji ankira d’iyarta da shegiya babu yadda zatayi tagardama saboda k’addara ce da rabo kawai yashiga tsakani.

Tun daga ranar aikin gidan yadawo hannun Amina duk ta bi ta rame,

Kud’in da abbah yabata ranar da zai rasu dasu take siyan duk abinda take buk’ata na amfaninta da d’iyarta,

Ko kad’an batason Ameerah tayi kuka saboda fad’an ummah.

Ga ummah ta sa ta a gaba komai ita takeyi mata ga fad’a ga cin mutunci na yau daban na gobe daban.

Bayan sati biyu Amina ce kitchen take girki ummah batanan ta je anguwa, jin kukan Ameerah yasa taje dasauri tad’aukota tadawo kitchen d’in tacigaba da juya miyar da take dan kar ta k’one.

Daidai lokacin ummah tadawo daga gidan k’awarta da taje, kitchen d’in tanufa cikin masifa tace wai ke Amina wane kalar kunne gareki ban hanaki ta6a wannan shegiyar ba idan kina min aiki?

Ke wlh na ma gaji da surutan mutane har kunyar fita nake saboda wannan shegiyar da kika haifar mana a cikin gida.

Toh wlh saidai kiza6a ko dai kikaita gidan marayu kidawo kizauna dani ko kuma kibi d’iyar taki kutafi kubarmin gida.

Dasauri Amina tad’ago idanuwanta da suka cika da kwallah tace ummah dan Allah kirufa min asiri wlh ba shegiya bace da ubanta k’addara ce kawai tasa nahaifeta idan nakaita wani waje wlh sai Allah ya kamani saboda ba ta da hak’in kowa,

Kuka Amina tashiga yi tace wlh banda kowa inba ke ba ummah kar ki min haka……Kallonta ummah tayi a wulak’ance tace ya rage naki nidai za6i nabaki kuma dole kid’au d’aya domin ba zan zauna da shegiya ba acikin gidana.+

Kije kiyi tunani na baki awa d’aya kacal duk wanda kikaga ya fi dacewa gareki toh.

Amina cikin kuka tatsugunna k’asa tace ummah kar kiyi min haka kituna ni marainiya ce banda kowa dan Allah kirufa min asiri wlh ummah ban ta6a zina ba KIYARDA DANI(na chubado mhmd),

Amina magiya take tayi ma ummah ammah ina ummah ta kafe akan maganarta saidai cikin biyu ayi d’aya,

Da taga ta dameta sai tace wlh Amina idan kika cigaba  da zama gidan nan tare da wannan shegiyar d’iyar toh zaki nemeta kirasa domin zan iya badata inda ba zaki k’ara ganinta ba,

Ni ai taimaka maki nayi idan kina zaune da ita ai ba wanda zai so aurenki kina da d’iya shege kowa ai burinsa yasamu mace tagari,

Kallon ummah tayi cikin mamaki tace ummah Allah ya san ni ban ta6a zina ba kuma komai yafaru ga bawa daga Allah ne k’addara ce da rabo kawai suka ratsa, ummah dan Allah kiyi hak’uri kar kibi ta maganganun mutane ita rayuwa anaso mutum yakasance mawadaci ammah ba zai kasance hakaba har sai yazama MAHAK’URCI (na Sainah ummun meenal).

Keh dakata kar kice zakiyi min wa’azi tunkan ahaifeki aka haifeni dan haka za6i ya rage naki,

Murmushin takaici Amina tayi tace shikenan ummah na za6i zama da d’iyata domin ba zan iya zaluntar ta ba alhali batada hak’in kowa a tare da ita.

Na yi ma abbah alkawali tun yana da rai cewa zan kula da yarinyar nan kinga idan ban kula da itaba ai na zalunci kaina kuma KYAN ALKAWALI acikasa (na jameesha) dan haka na ji zan barmiki gidan zanje inyi rayuwata inda banda kowa Allah yana tare da ni.

Murmushin samun nasara ummah tayi tace za dai kije yawon karuwanci toh tunda haka kika za6a ya yi miki kyau,

Na baki minti goma kifita kibar min gida,

Tashi Amina tayi tana kuka tanufi d’akinta ta aje Ameerah saman gado sannan tad’auko jaka tazuba kayanta kala takwas sai ta d’ibi na Ameerah tad’auki abubuwan da tasan zata buk’ata sauran kud’in da suka rage mata tad’auka sannan tagoya Ameerah tafito.

Kallon ummah tayi tana shirin yi mata magana dasauri ummah tad’aga mata hannu tace na yafe zancenki bani buk’atar jin komai daga gareki kedai kije kawai tunda kika za6i shegiya akaina.

Amina tana kuka takalli d’akin abbanta tace Allah yajik’anka abbana da kana da rai da duk wannan abun bai faru dani ba kuka takeyi sosai kamar ba zata tafi ba.

Tsawa ummah tadaka mata kifita kiban waje nace maki tun kan ranki ya6ace.

Wucewa Amina tayi tafita daga gidan gidan gwaggo ladi tanufa har zata shiga sai kuma tafasa  tace nan bai dace daniba domin zan dinga ganin gida k’ara intafi inda bansan kowaba inyi rayuwata.

Mai adaidaita sahu tasamu tace yakaita tashar katsina,

Har suka iso bata saniba tunani kawai take muryarsa taji yana cewa mun iso,

Kud’insa tabashi sannan tanufi wajen motar tashiga ba a d’au wani lokaci ba motor ta cika.

STORY CONTINUES BELOW

Cikin minti talatin sai gasu sun iso katsina,

Tafiya take ta rasa inda zataje domin batada kowa a garin duk hanyar da taga ta yi mata bi kawai take ga yunwa tana ji ga kuma Ameerah tana ta kuka.

Idan kaganta sai kace mai ta6in hankali duk tabi ta canza.

Ta rasa ina zataje tasayi abinci taci wajen wani mutum da tagani a zaune saman machine d’insa tanufa.

Sallama tayi mashi ya amsa mata sannan tace dan Allah bawan Allah ina ake saida abinci a nan,

Kallonta yayi yace ammah ke bak’uwa ce ko?

Eh tace mashi.

Ohk, kishiga kwanar haggunki kimik’e kad’an zakiga wani gidan abinci a nan da symbol a gabansa ansa meenat restaurant ammah fa suna da tsadar abinci bansan ko zaki iya siya ba,

Murmushi tayi tace nagode, hanyar da yace mata tabi nan takebi har tazo restaurant d’in gidane mai had’e da wajen cin abinci ba laifi ya had’u.

Shiga tayi tare da sallama tanufi chan inda tahango masu saida abincin sukace me za a zuba miki tace komi kuka zubamin.

Kallonta sukayi sukace ai ke xaki za6i kalan abincin da kikeso.

Toh kuzuba min jalop rice tace

Toh ammah plate 500 naira, nan suka zuba mata, kallon wajen tayi taga duk mazane zaune a saman chairs d’in, mata basuda yawa,

Sai ta amshi abinci takoma chan sauran gidan taci.

Saida taci tak’oshi sannan talalla6a Ameerah tayi bacci, alwallah tayi tashimfid’a kallabinta tayi sallar la’asar addu’a tadinga yi na Allah yakawo mata mafita Allah yakareta daga sharrin dukkan halitta.

Datagama sai tashiga gidan da sallama mutane tagani suna ta hidima daga ganinsu ‘yan aikin mai gidanne.

Amsa mata sukayi taduk’a har k’asa tagaishesu tace dan Allah hajiyar tana ciki.

Wata dattijuwa daga cikinsu tace aikam batanan ta je anguwa sai zuwa dare za ta dawo.

Jim Amina tayi tarasa ya zatayi kamar tace abata waje taxauna tajirata toh kuma sai taga kamar basu yarda da itaba saboda irin kallon da suke mata.

Sallama tayi masu tafita tasamu chan saman dakalin gidan tazauna kayanta suna gefenta, tunani kawai take komai ya yi mata zafi,

Hawaye suka shiga kwarara daga idonta gogewa tayi tace innalillahi wa’innah ilaihiraji’un wannan wace kalar k’addara ce ina zansa kaina ya ubangiji ka fi kowa sanin halin da nake ya Allah kakawo min d’auki,

Tana zaune wajen tana kallon masu wucewa da masu shiga siyan abinci har aka fara kiran sallar magrib,

Pure water tasiyo tazo tayi alwallah tagabatar da sallah,

Bata tashiba har saida tayi sallar isha’i.

Goye take da Ameerah saidai intayi kuka tasafkota tabata tasha ahaka har gari yafara duhu nan hankalin Amina yak’ara tashi,

Tunanin mafita tashiga yi ammah ta rasa yarda zatayi.

Tana nan zaune tana sak’e-sak’e a ranta har goman dare tayi gari duk ya yi shuru mutane d’ai-d’ayane suke wucewa lokacin har ankulle restaurant gidan ne kawai a bud’e.

Cikin kayanta tad’auko zane tashimfid’a sannan tasafke Ameerah da take ta bacci takwantar da ita, itama kwanciya tayi tayi matashin kai da jakar kayansu sannan tarungume d’iyarta tsoro da fargaba duk suka taru cikin ranta,

Chan wajen k’arfe sha d’aya hasken motar da tatsaya k’ofar gidanne yatada ta daga baccin da tafara,

Wata matace ta sha adonta tafito daga acikin motar, gidan tanufa zata shiga daga gani itace mai gidan har ta wuce tagaban Amina zata shige sai kuma tadawo tace baiwar Allah ya zakizo nan kikwanta a matsayinki na mace ai hakan bai daceba maimakon kitafi gida ga kuma jinjira a tare dake.

Tashi Amina tayi cikin ladabi tagaida matar sannan tace hajia wlh bansan inda zanje ba banida kowa dan Allah kitaimaka min ko wanke-wanke indinga yi maki.

Kallon tuhuma matar tayi mata tace toh ya akayi kike rayuwa a haka?

Cikin kuka Amina tace wlh mijina ne yarasu toh shine gidan da muke haya suka koreni saboda banda kud’in da zan biyasu gashi ni ba ‘yar garin nan bace aure yakawoni garin.. ita kanta Amina mamakin k’aryar nan da tazo mata lokaci guda tayi ma matar tayi.

Cikin tausayi matar takalleta tace Allah sarki Allah yajikansa wlh wasu mutanen basuda kirki maimakon kishiga ciki sai kizauna nan.

Hajiya nashiga akace bakinan saisa nafito saboda baidace inshiga inzauna ba da izininki ba.

Maganar Amina ta burge matar tace hakane kina da hankali taso mushiga daga ciki,

Ameerah tad’auko tasa6i jakkar kayanta tabi bayan hajiyar suka shiga gidan dasallama nan ma’aikatan gidan dasuka rage su ukku sukai ta mik’o gaisuwa wajen hajiya suna mata sannu da dawowa.

Kallon Wata dattijuwa tayi tace babah salame ga bak’uwa nan kibata abinci kitafi da ita d’akinki takwana

Toh hajiya angama.

Kallon Amina tayi tace kije kici abinci kikwanta gobe munyi magana.

Duk’awa Amina tayi har k’asa tana yi ma hajiyar godiya sannan suka wuce.

‘Daki babah salame takaita dakanta ta amshi Ameerah takwantar da ita sannan takawo mata abinci kad’an taci kallon babah salame tayi tace babah dan Allah inaso in d’an watsa ruwa idan babu damuwa.

Toilet babah salame tagwada mata Wanda yake cikin d’akin, wanka tayi tashirya sannan takwanta.

___________________

Tun da asuba da sukayi sallah basu koma bacciba Amina kama masu tayi akayi aikin da ita sunyi-sunyi tabarshi ammah tak’i saida Ameerah tafarka sannan taje tad’auketa.

Wajen k’arfe goma suka gama komai suka fitar da abincin a restaurant d’in sannan sukayi wanka da breakfast.

Hajiya maimuna ce ta aika aka kira mata Amina.

Cikin wani had’add’en falo suka shiga dasallama hajiya maimuna tana kishingid’e bisa kujera tana kallo a makekiyar TV d’in da take mak’ale a bango, cikin sakin fuska ta amsa mata…..

Tsugunnawa Amina tayi tagaisheta,

da fara’a ta amsa mata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *