K’ADDARA CE CHAPTER 5
Kallonta Hajiya maimuna tayi tace ni sunana Hajiya maimuna ni nakeda wannan resturent d’in na meenat resturent,
Na sa mashi suna meenat saboda sunan d’iyata ne ita kad’ai gareni mace sauran biyun duk mazane ina sonta sosai,+
Murmushi Amina tayi tace Allah sarki Allah yaraya su.
Ameen am kince kinason yin aiki a gidannan ko?
Eh hajiya in zan samu wlh inaso.
Eh zan d’aukeki aiki saboda ina tausayin rayuwarki dan haka girki ne sai serving d’in customers idan sunzo, salary zan dinga biyanki 3k per month tunda a nan gidan zaki zauna, ina bada 5k ga wad’anda suke zaune gidan mazajensu indai zaki zauna lafiya damu toh masha Allah muna maraba da ke banson tashin hankali ko da daga ganinki kamar ba zakiyi rigima ba,
Murmushin jin dad’i Amina tayi tace insha Allahu hajiya ba zaku sameni da matsala ba zan zauna daku tsakani ga Allah.
Toh shikenan kin kyauta saidai har ynz ban san sunanki ba,
Sunana Amini d’iyata kuma Ameerah
Woww nice name ashe namesake d’in daughter d’ina ce inji hajiya Amina tana murmushi.
Eh Hajiya.
Toh kije ga d’aki chan kusa da na babah salame zansa agyara maki sai kizauna ke da d’iyarki saboda zaki fi jin dad’in zama ke kad’ai.
Sannan sauran ayyukan zansa sukoya maki yadda suke tafiyar dashi
Toh Hajiya nagode sosai Allah yasaka da alkhairi, Allah yak’ara girma.
Ameen zaki iya tafiya.
Godia tak’ara yi ma hajiya sannan tafito tanufi resturent wajensu inna salame suna gwada mata yadda suke tafiyar da komai daga nan suka cigaba da serving d’in customers, tana goye da Ameerah Sallah ce kawai take tadasu daga wajen sai kuma cin abinci,
Tana jin dad’i sosai domin hakan yana d’ebe mata kewa,
Sai wajen taran dare sannan aka rufe resturent d’in sauran matan da ba kwana suke gidanba suka tafi gidan mazajensu, su kuma suka shiga gida,
‘Dakin da aka gyara mata d’an k’arami kusa da d’akin baba salame shi tanufa ledace a shimfid’e a d’akin sai ‘yar k’aramar katifa sai toilet daga ciki,
Kwantar da Ameerah tayi tashiga tayi wanka sannan tashirya takwanta.
Tunda sukayi sallar asuba suka fara gudanar da aikin girki kowa da abinda yake yi ba su suka gamaba sai wajen k’arfe goma,
Wanka tayi tashirya, tashirya d’iyarta tayi breakfast suka gaisa da hajiya sannan suka nufi restaurant domin gudanar da aiki.
Haka rayuwar Amina tacigaba da tafiya a gidan hajiya maimuna tana jin dad’in zama dasu, su ma suna jin dad’inta domin bata da k’yuyar aiki kuma tana ba kowa girmansa a matsayinta na k’aramarsu duk abinda taga ya dace shi takeyi ba ta shiga harkar kowa rayuwarta kawai take,
STORY CONTINUES BELOW

Duk abinda take buk’ata tana siye da kud’in da suka rage a wajenta, tana kula da d’iyarta sosai.
Ta samu kwanciyar hankali sosai a gidan domin batada matsala da kowa, saidai a kullum tunanin mutumin da yasa ta a cikin matsalar nan da burin sake ganinsa take domin ko kad’an ba ta jin haushinsa saboda yadda takejinsa a ranta, sau dayawa ta sha ta6oye a d’akinta tasha kukanta domin tasamu sauk’i a zuciyarta, wani lokacin har addu’ar shiriya take mashi da fatan dawowa gareta, itama kanta tana mamakin yadda yashiga ranta lokaci guda koda ta san k’addara ce tahad’a ta dashi ya mata nisa ammah ya zamo wata tsoka a cikin jinin jikinta.
***** ***** ***** ******
A chan 6angaren fahad karatunsa yake hankali kwance saidai wani lokacin idan yazauna tunanin abinda ya aikata yana damunsa musamman fuskar yarinyar da take kuka a lokacin da yai mata aika-aikar tayi ta mashi gizo duk sai yaji yana jin haushin rayuwar da yayi a lokacin da abinda ya aikata,
Gashi gidansu bai fad’a ma kowa kalar rayuwar da yayiba saboda kar hankalinsu yatashi.
Yauma kamar kullum bayan sun fito daga lecture direct gidan da suka kama haya suka nufa shi da abokansa biyu, kowa room d’insa yanufa,
Wanka yayi yagabatar da sallah sannan yajawo wayarsa yakira mummynsa,
Fatima ce da salma zaune a main parlor suna kallo k’arar wayar mummy ce dake kusa da ita takatse mata kallo, hannu takai tad’auko wayar ganin wanda yake kira yasa tasaki murmushi dasauri tayi picking d’in call d’in tare da yin sallama,
A chan 6angaren aka amsa mata,
Cikin girmama tagaishe da yayan nata,
Murmushi yayi ya amsa tare da cewa my little sis ya kk?
Hmm yaya fahad kenan kaida ka mance da ni ko irin kace bari kakira k’anwarka ammah shuru ni fushi ma nake,
Ayyah am sowie my little sis wlh kina a raina a kowane lokaci kawai dai ina busy ne dat’s y kwana biyu baki jina.
Allah sarki yayana nima na yi tunanin hakan, toh y study,
Alhmdllh my little sis, ya naku dafatan dai kina maida hankali sosai baki wasa ko.
Eh wlh yaya ina maida hankali.
Fira suke sosai itada yayan nata
Kallonta takai wajen salma da tunda tafara wayar tatsareta da ido,
Murmushi tayi tace yaya fahad ga salma kugaisa,
Jim yayi sannan yace wacece salma kuma?
Cikin shagwa6a tace haba yaya har ka manceta salma fa d’iyar Aunty maijidda da take yola.
Ta6e baki yayi sannan yace oh ynz nagane zuwa tayi ne?
Ka mance na fad’amaka itama ta samu admission a school d’inmu shine take zaune a nan gida,
Oh god i forgot wlh am so sowie.
Dariya tayi tace yayana ko dai ka fara tsufane duka yaushe mukayi maganar ammah har ka mance.
Murmushi yayi yace ai da alamar hakan my dear sis.
Toh yaya gata kugaisa, wayar tamik’a ma salma a tsorace ta amshi wayar a hankali tayi sallama,
Amsa mata yayi ciki-ciki shima,
Gaisawa sukayi sama-sama sannan yai mata nasiha akan tadage tayi karatun da yakawota banda wasa,
Godiya tayi masa, sannan sukayi sallama.
Mik’awa fatima wayar tayi yace My little sis mummy ba ta kusa ne?
Ayya yaya tana room d’inta a nan parlor ta mance wayar, i think ma yanzu haka ta yi bacci sbd tun d’azu naji tana cewa bacci zatayi.
Ohk badamuwa my little sis i will call her letter, gud bye
Nan sukayi sallama suka aje wayar,
Kallon salma tayi da har yanzu bata daina kallonta ba, murmushi tasakar mata tace ya dai sister?
Itama murmushin tayi tace kawai dai kuna burgeni nima sai inji daman ni ke da bro kamar ke.
Hmm toh kema ai kinada Aunty mariya,
Ai ita macece duka fa mu biyune, ni inason inga ina da yaya namiji.
Ammah irinsu yaya fahad sai ahankali ni wlh wani lokacin har tsoro yake bani yanayin yadda yake d’aurewa kwata-kwata shi ba ya son wasa bai sakin fuska kuma bai shiga harkar kowa.
Kai my sis yanzu duk yayan nawa yake haka?
Eh mana kema ai kinsan halinsa.
Dariya sukayi sannan suka cigaba da kallonsu.
Fahad tunda suka gama wayar da little sis d’insa kiran friends d’insa yayi yace nifa yunwa nakeji kuzo muje musamo abinda zamuci daga chan sai muwuce library domin inason yin research kan wani abu da ban ganeba.
Had’ad’d’an restaurant suka tafi shi da abokansa biyu ‘yan nigeria sukayi order d’in abinci sukaci sannan suka wuce library,
Bayan sungama gida suka dawo kasancewar magrib ta gabata alwallah sukayi sukai sallah sannan suka zauna hira sai bayan sallar isha’i sannan kowa yakama gabansa domin suyi karatu.
Wajen k’arfe goman dare yagama karatun wanka yayi yashirya sannan yakwanta bacci.
Tunanin da yasaba yi yafad’o mashi a rai nan hankalinsa yafara tashi hawayene suka zuba daga idonsa yace innalillahi wa’inna ilaihiraji’un ya zanyi da wannan k’addarar dole inje insamu mutanen nen inbasu hak’uri ko nasamu sauk’in abinda nakeji a raina,
Shi dai a tunaninsa ya san tausayin yarinyar yakeji saboda bai kyauta mataba.
Zumbur yatashi zaune daga kwancen da yake yace innalillahi wa’inna’ilaihiraji’un auren da aka d’aura mana fa tabbas na san ban saketaba a lokacin ya akai hakan tafaru,
Dafe kansa yayi yace Wannan wace kalar k’addara ce tasameni me yake faruwa dani gaskiya dole inkoma innemi afuwarta da ta iyayenta sannan insauwak’e mata aurena da yake a kanta saboda hakan shine kawai mafita kusan shekara da wata hud’u kenan,
To kuma yaushe hakan za ta faru ni da ban Nigeria oh god,
Ammah dole insamo mafita domin very soon nakeson zuwa Nigeria ko dan saboda wad’annan bayin Allahn.
Allah gani gareka.
Kwanciya yayi yana ta tunanin yadda zai 6ullo ma lamarin daga k’arshe saida yaga ya samo mafita sannan yayi bacci.