K’ADDARA CE CHAPTER 6 BY MAMAN NUSAIBA
_KADA KU MANTA WANNAN LITTAFIN NA KUD’I NE KI GARZAYO KI BIYA NAKI KUD’IN DOMIN AYI TAFIYAR NAN DAKE SISTER_
_NOMAL N300_
_VIP N500_
_Ku tuntubeni ta WhatsApp number na+966599791573_
_Mai buk’atar HAFSAT BOOK 2 ya zama document complete zaki biya N400 ki samu wannan labarin, duk mai son HAFSAT BOOK 2 ku tuntubeni ta WhatsApp number na +966599791574_
_بسم الله الرحمن الرحيم_
_17/ 18_
Zaman dirshan Hanan Tayi, tana tunano maganar da Baba ya fad’awa Yaya Faris. Ta gumi Tayi tana fad’in shikenan ni Hanan zanyi Auren cin amana! Waiyo Allah Baba dan Allah karki amince da maganar shi! Nifa ko mutuwa zanyi ba Mijin aure bazan auri Yaya Faris ba, haba! ai d’an halak baya manta halacci, bazan iya ba Baba na! Ka taimake ni Baba! karka ce ka yarda. Da sauri ta share hawayen ta jin Baba na kiran ta, tashi Tayi ta shiga toilet ta wanke fuskar ta,duk dan kar Baba ya gane Tayi kuka, tana isowa wajan Baba Ta ce.” Baba gani naji kana kirana ko?
Baba Ya ce.” Eh Hanan na kira ki, ina fatan dai kinsan da zuwa Faris Gidan nan ko?
Danna kukan daya tafo mata Tayi Ta ce.” Eh Baba na sani zaizo yau..
Baba Ya ce.” To Masha Allah, to dama yazo min da wata magana ne wadda yasa nace mishi saina tambayeki naji ra’ayin ki akai..
K’ara sunkuyar dakai Hanan Tayi Ta ce.” To Baba wata magana ce haka? Tayi maganar kamar bata san komai ba…
Baba Ya ce.” Faris Yace” min yana son na aura mishi ke, saboda ya yaba da hankalin ki, kuma Matar ma ta yaba da hankalin ki, Yace” baya so a dauki lokaci wajan bikin naku, dan yana son zuwa Ummura Saudiya, Yace” zaiyi wata d’aya acen, daga nan zai wuce K’asar China saboda kasuwancin shi, shine nace saina tambaye ki naji ra’ayin ki akan maganar, Yan zu ke Ya kike ganine Hanan?
Tin da Baba ya soma magana, Hanan ta kasa rike hawayen ta , sosai take jin zuciyar ta na zafi da k’una, taya ma zata fahimtar da Baba? Ko ta mishi bayani kila ba tabbas ya fahimci mai take nufi,. D’ago da idon ta Tayi ta zuba su akan Baba, wanda suka ji jajur saboda kukan data ci Ta ce.” Baba ka fahimceni dan Allah!
Jikin Baba ne Yayi sanyi ganin yadda Hanan take kuka, jikin ta har rawa yake da kuma muryar ta, a hankali ya rike hannun ta Ya ce.” Hanan ki kwantar da hankalin ki nasan me kikeson fad’a min, amma bamu da mafita ne,kuma kinga mutanen nan sun magana halacci a rayuwar mu! To taya kike gani idan suka rok’i alfarma a wajan kuma muka ki amincewa da buk’atar su? Kin san ai baza suji dad’i ba idan har muka zama masu manta alkhairi a garesu! Kiyi Hak’uri nasan kika tunanin in kika auri Faris kinci amanar Ilham ko? To ki dena ita ce ma ta bada kwarin gwiwar haka kinji Ya’ta!
Share hawaye Hanan Tayi Ta ce.” Shikenan Baba naji zan aure shi, kuma Insha Allah zan zama mai biyayya a gareka, bazan tab’a b’ata wa Anty Ilham rai ba da sunan kishi, duk da shi dan Adam ajazi ne. Tana fad’in haka ta daura kanta à kafad’ar Baba taci gaba da kukan ta gwanin ban tausayi…
_*************************_
_B’AN GARAN SU IMAN_
Sultana ce zau ne tayi tagumi ana ta mata magana bata ma san ana yiba, tunanin Aminiyar ta take, Yan zu da suka tare da suna ta hirar su ,gashi sai ita d’aya take siyar da Abinci.. ji Tayi an dafa kafad’ar ta, da sauri ta d’ago da kanta dan ganin meye ya tab’a ta..
Abdul Malik ne t’a gani cikin k’ananan kaya masu tsadar gaske, kayan sun amshi farar fatar shi, gashin kanshi yasha gyara, ga wani tsadaddan agogo dake manne à hannun shi, takalmin shi kalar wandon shi da rigar shi, kyakyawar fuskar shi dauke da k’ayataccen Murmishi ,duk à cikin minti da bai fi daya ba Sultana Ta k’arewa Abdul Malik kallon.. Kamar wata sakarya ta saki baki da hanci tana kallon shi da mamaki, Al’ajabi tama rasa me zata fad’a. A zuciyar ta take nanatawa wai dama Abdul Malik yana da cikakken hankali ashe? Kai gaskiya nasha mamaki ko dama , shaye-shayen ne da yake yasashi zama mahaukaci?
Ajiyar zuciya ta sauke Ta ce.” Abdul Malik kaine ko dai wani mai kamar ka ne nake gani? In kuwa kaine to ya naga ka canja kamar ba kai ba?
Dariya Abdul Malik Yayi yana zama a gefen Sultana wajan da Iman take zama Ya ce.” Eh nine dai Sultana ba wani bane. Wai Sultana ina Mutumiyar ne? Kinsan bana Gari ne shiyasa banzo mun gaisa daku ba…
Ita dai Sultana bata dena Mamaki ba na ganin yadda Abdul Malik Ya canja Ta ce “ai Iman ba lafiya, wani ne ya tada mata Aljannun ta , to tin ranar bata sake zuwa talla ba, Yanzu haka tana Gida kwance na ba
ro ta amma da sauk’i sosai kila wani satin ta soma zuwa tallar…..
ro ta amma da sauk’i sosai kila wani satin ta soma zuwa tallar…..
Da sauri Abdul Malik Ya kalli Sultana kamar zaiyi kuka, dan ba k’aramin so yake yiwa Iman ba, so na gaskiya yake mata wanda babu Algus a cikin shi, wannan tafiyar ma da Yayi kasa jure rashin ganin Iman ne yasa shi dawowa daga inda yaje ya dawo.. Ya ce.” Haba Sultana Yanzu Iman d’ina ba lafiya shine ko ki sanar dani ta waya! Ai koda baki da number ta saiki shiga wannan Babban shagon na Baba nane, da kince wa Masu siyar da kayan wajan kina son magana dani zasu kirani muyi magana, amma shine kika k’i fad’a min Sultana why?
Sultana k’ara shiga duhu tayi jin Yace” wai wannan fakeken shagon wanda babu mai girman shi a kaf cikin Kasuwar _MARSHÈ DANTOKPA_ Yace” na Mahaifin shi ne? K’ifce- k’ifce ta ringa yi da ido kamar tayiwa Sarki k’arya an kama ta, tagumi Tayi ta zubawa Abdul Malik ido saboda Al’ajabi da rad’anin data shiga……
Dariya sosai Abdul Malik keyi ganin yadda Sultana Ta kafeshi da ido ko K’iftawa babu, yasan kuma dole zatayi mamaki, saboda bai taba nuna musu shi waye ba shiyasa duk take ganin abun ban barakwai wai Namiji da suna Hajara. Ya ce.” Nasan dama zakuyi mamaki inna fad’a muku cewa _Alhaji Aliyu mai atamfa shine Mahaifina_ saboda baku san waye Babana ba, kuna dai ganina kamar mai tab’in hankali, yanzu na dawo hayyacina Alhamdulillah…
Nannauyar ajiyar zuciya Sultana Ta sauke tana dauke kallon ta daga kan Abdul Malik Ta ce.” Kai Wallahi badan kai bane ka fad’i haka ba, da wani gaskiya zance Yayi k’arya, ni sai Yanzu ma nake ganin kamannin ku dashi, duk da ba koda yaushe yake zuwa kasuwar nan ba, yana zuwa ne kamar duk bayan wata d’aya ko sati biyu, gaskiya ba wanda zai dauka kai D’anshi ne, amma kuma yanzu ka fito a asalin D’anshi…
Murmishi Yayi Ya ce ” please tashi muje Gidan su Iman na duba jikin nata! Saboda fa da kasa jure rashin ganin ta na baro Abuja na dawo Kwatano, ina zuwa ko zama banyi ba na garzayo kasuwar nan, dan Allah muje ki kaini na ganta ko zanji sanyi a zuciya ta!
Sultana Ta ce.” To Abincin nawa fa?
Ya ce.” Ba ki gani. Wayar shi Babba ya ciro a aljihun shi kirar IPhone 12 ya danna ya kara a kunnen shi, Ya ce.” Zashali kazo nan gefen shago ina jiran ka, zaka ganni da wata Yarinya muna zaune. Yana fad’in haka ya kashe kiran, bai k’ara magana ba saima murtuke fuska da Yayi ,yana danna wayar shi….
Ita dai Sultana tana ganin kayan Al’ajabi da mamaki, a Ranta Ta ce”. Hmm lallema dama haka Abdul Malik yake da shan kunu haka?, duk wai Dan kar a renashi….
Shazali na zuwa ya rusuna Ya ce.” Ranka ya dad’e gani nazo.
Abdul Malik Ya ce.” Ka dauki Abincin nan ka kai ciki kuci kaida Y’an Uwan ka, nasan ba’a kawo muku Abincin rana ba, to kuje kuci..
Shazali dan murna yama rasa mai zaice saboda yunwa sukeji ba’a kawo musu Abincin rana ba, sai gashi Mai Gidan basu ya siya musu. Sake rusunawa Yayi Ya ce”. Godiya muke Oga Allah ya k’ara girma…
Abdul Malik bai d’ago ba Ya ce.” Emeen ya Allah..
Shazali daukar Abincin Yayi ya shige shagon su, su kuma su Sultana suka nufi bakin hanya.. har zasu fita a kasuwar Abdul Malik Yace” wa Sutlana muje ga motata cen nazo da ita sai muje a ciki..
To kawai Tace” tana binshi a baya kamar rakumi da akala. Suna zuwa ya bud’e mata ta shiga shima ya shiga suka nufi Unguwar su Iman..
Suna isa k’ofar Gidan su Iman Sultana Ta fita Ta ce.” Bari naje na kira ta sai tazo. To kawai Yace” ya koma jikin kujerar motar ya lumshe idon shi kamar mai jin bacci….
Sultana n’a shiga ta shiga ta gaishe da Mama tukun tayi ciki, tana shiga ta samu Iman na daura dan kwali alamar bata jima da fitowa daga wa ka ba, k’arasowa Tayi kusan gadon yana murmishi Ta ce.” Ta Abdul Malik bada kanki a sare kije gida kice ya fad’i….
Wurga Mata Harara Tayi Ta ce.” Ke nifa ki karki dameni daga zuwab ki! Iman Ta k’arashe maganar tana turo baki gaba…
Dariya Sultana Tayi Ta ce” to wannan turo baki fa? Ki tashi yau zan baki mamaki muje waje, Abdul Malik ne yazo ganin ki….
Iman Ta ce.” To shikenan muje tana saka hijabin ta. Suna fitowa tacewa Mama zata fita wani ne yazo dubata da jiki.. Murmishin Manya Mama Tayi Tace” musu su dawo lafiya. .. suna fita Iman taga wata hadaddiyar mota mai masifar kyau, sosai motar ta tafi da ita sai da Sultana Ta tab’a ta tukun ta saita nutsuwar ta….
Abdul Malik na ciki yana bin Iman da kallon k’auna mai narkar da zuciyar masoya, ji yake kamar ya fita ya rumgume ta saboda ba k’aramin cutuwa Yayi ba na rashin ganin ta. Ajiyar zuciya ya sauke Ya ce.” My Iman kin tafi dayawa, bazan iy
a jure rashin ki a kusa dani ba, ai dole ma inna koma Gida na cewa da Abba yazo ya nema min auren ki, bazan so ganin wani Namiji a tare dake ba inba ni ba, ke tawace ni kad’ai da yardar Allah.. bud’e motar Yayi ya fito yana zuba k’amshi ,, idon shi akan Iman yana mata kallon Yayi kewar ta da kuma tausayin ta….
a jure rashin ki a kusa dani ba, ai dole ma inna koma Gida na cewa da Abba yazo ya nema min auren ki, bazan so ganin wani Namiji a tare dake ba inba ni ba, ke tawace ni kad’ai da yardar Allah.. bud’e motar Yayi ya fito yana zuba k’amshi ,, idon shi akan Iman yana mata kallon Yayi kewar ta da kuma tausayin ta….
Iman baki da hanci ta saki tana kallon wanda yake mata murmishi mai saka zuciyar masoyi cikin shauk’in k’auna, badan tasan fuskar shiba da baza tace” shi bane, sosai take kallon shi har ya k’araso inda suke bata sani ba, sai da taji zazzak’ar muryar shi Ya ce .” Assalam alaikum Ya Masoyiya abar kaunar ta……
Murgud’a baki Tayi tana juya mishi baya, tana magana k’asa².
Ita dai Sultana ganin ta had’a su saita koma ciki tana dariya, dan yau tasan sai Iman tayi halin nata..
Ganin Sultana Ta tafi Iman Ta juyo tana aikowa da Abdul Malik sak’on harara.. Dariya Yayi Ya ce.” Kai Masoyiyar k’auna bako sannu da zuwa? Sai sak’on harara..
Iman Ta ce.” Yo naga ka wani zama Babba kamar wanda ake busa ka, kuma a ina kaje ka dauko motar aro da kayan aro, hadda wani askin Y’an Gayu, to baka burgeni ba ma da kayi haka. Tana maganar tana mishi gatsine….
Abdul Malik murmishi Yayi jin Abun da Iman Ta fad’a, wai yayo kayan aro? Koda yake ai bata san shi waye bane shiyasa Ya ce.” Ayya My d’ina kiyi Hak’uri da ban sanar dake ko ni dan wanene bane! Na san dai kinsan _Alhaji Aliyu mai atamfa_ ko? To shine Maihaifina, ganina da kike a kasuwar _MARSHÈ DANTOKPA_ To ina zuwa shagon Daddy na ne…
Warm ido Iman Tayi jin bayanin Abdul Malik, nan da nan ta had’e rai jin sunan Baban shi, Tace.” Wato da munafurta na kaso yi ko? Shine ka fito min a Talaka, sai da na kamu da sonka ka bayyana min asalin ka ko? To sai dai ka sani ni bazan iya aurar Mai kud’i ba, a tsarin Rayuwa ta babu auren mai kud’i, saboda shi mai kud’i inka aure zai dauka dan kud’in shi kake tare dashi, ni kuma bazan yarda da renin hankali irin na masu kud’in zamani ba, to ka fice min a nan ! Iman Ta k’arashe maganar tana had’e rai babu alamar wasa a fuskar ta, kana ganin zaka gane maganar daga cikin zuciyar ta take ba daga bakin taba……
Abdul Malik kamar zaiyi kuka jin Abun da Iman Ta fad’a wai bazata iya auren shiba, wanda hakan barazana ne ga Rayuwar shi inhar ya rasa Iman, zuciyar shi bazata juri haka ba. Sunkuyawa Yayi a gaban ta ya had’e hannun shi biyu alamar rok’o Ya ce.”
Haba Iman wannan wani irin ra’ayi ne gareki , dan Allah karki sa zuciya ta ta buga! Bazan iya jure rashin kiba, please Iman kice bugun munfashi na karki min haka! Ni bana cikin mutanen da kike magana akai, kiyi Hak’uri kinji! bana son rasaki a rayuwa ta, kin zama jini da b’argo na jikina, kar muyi haka dake Iman dan Allah please mana!
Iman Ta ce.” Ka gama bayanin nake ne koda saura?
Mik’ewa Yayi Ya ce.” Na gama ki duba magana ta Iman, kiji tausayi na karki gujeni a lokacin da nake buk’atar ki a kusa dani!
Numfashi taja tukun ta kalle shi , Allah yana gani ta kamu da k’aunar Abdul Malik , amma tinda ya kasance d’an masu kud’i dole ta Hak’ura dashi, dan bazata iya auren wulak’anci ba. Ta ce.” Kayi hak’uri! bazan auren mai kud’i ba sai anjima. Tana fad’in haka ta shige Gidan su….
Abdul Malik dafe kanshi Yayi Ya ce” a a Iman ! No! No!! No!!! Karki min haka Iman ki dawo gareni bana son rasaki a wannan lokacin! Ganin ta shige ciki bata ko waiwage shiba , saiya Hak’ura ya koma motar shi. Saida ya kwashi minti goma tukun yaja motar shi a hankali yabar Unguwar. …
Idan kin karanta ki daure kiyi comment sister 🤝🏻
_Maman Nusaiba ce. ✍🏻Alk’alami yafi takobi_