La asar sakaliya garin Kano ya yi sanyi, ga yanayi irin
na farkon shigowar damuna. Iska mai sanyi ta na kad’ awa tana fifta duk wani mai rai da ke cikin wannan garin. Babu abinda za ka dinga hangowa sai korayen ganyen dake kadawa, tufafin jamaa yana kadawa, don haka jama’ar da ke giftawa su na tafe cikin nishadi ba tare da gajiya ko wahalar tafiya ba.
.
Alhaji Bakura matashin mutum ne dan kimanin shekaru arba’in cif-cif. Wanda ke tafe cikin tsaliliyar motarsa qirar INFINITI EX 32 SUV. Mai launin ruwan toka (silver), kasancewar sanyin iskar da ke kadawa tafi sayin A.C motarsa dadi sai ya kashe ya bude gilasan wunduna, ya na tafe iska na kada shi. Nan da nan ya tsinci kansa cikin nishadi, kallo daya za ka yi’ masa annurin fuskarsa ya tabbatar maka da hakan. Dadin dadawa ma kid’a da wakar D’an kwairon da ke tashi a hankali daga cikin rediyon motarsa ya k’ara masa nishadi.
Mace duk kawaicinta da kunyarta idan ta kalli Bakura
sai ta sake kallonsa saboda mutum ne kyakykyawan gaske mai kyawun fasali, Allah Ya tsara halittarsa a jikin Bakura. Dogo ne sosai mai bakar fata lallausa mai shek’in kyau, gashi da dogon hanci gami da dara-daran idanuwa, bakinsa madaidaici mai k’unshe da was kyawawan hak’ora masu matukar haske har da was siraran wushiryoyi a sama da k’asan hakoran, yana da bak’in dadashi wanda ya kara fito da tsananin farin hakoran.
Duk da kyawun da Rabbul samawati Yayi masa sai Ya
yi shi mutum mai tsananin tsafta da son kwalliya hakan ya sake fitar masa da kyawawan suffarsa a fili. Kwalliya ba ta tafiya daidai Idan babu kudin da za’a sayi kayan kwalliyar, amma Bakura yayi sa’a Allah Ya hada masa dukka. Ya bashi arziki mai yawa don a yanzu haka shahararran dan kasurwa ne a cikin K’asar nan har ma da kasashen k’etare baya ga dinbin ilimin qur’ani da na boko da Allah Ya bashi. Domin mahaddacin kur’ ani ne, a bangaren boko kuwa Masters gare shi a bangaren Engineering.
Kallo daya za ka yiwa yadin dake jikin Bakura ka tabbatar da tsadarsa saboda kwanciyar da yayi luf a jikinsa don laushi, yadin mai launin ruwan madara(cream) sai ya saka bakar hula da bakin takalmi tsadaddu.
Kamshin turaren jikinsa kuwa duk ta inda ya gifta fiye
da minti talatin kamshin baya barin wajen. Bakura dan mutanen Maiduguri kana gaminsa ka ga Kanuri kasancewar anyi masa tsage irin na barebari fashin goshi da tsage bibbiyu a kuncinsa, amma sai idan ka k’ura masa ido sosai sannan za ka iya tantancewa akwai tsaga a fuskarsa domin zanen bai fito rangadadai ba.
Mutum ne mai yawan fara’a da son zolaya idan ya ga
dama, amma fa wasu lokutan akwai tsare gida, idan ya b’ata rai babu mai iya sa shi dariya. Dokoki ya gindayawa iyalansa da duk wasu da suke zaune a garqashinsa kala-kala a, kuma dole su bi idan su na son su zauna da shi lafiya. Mutum ne wanda baya son raini, baya son rashin tarbiyya da rashin kamun kai. Baya son sakaci da addini.
Hatta yadda ake yin magana ya koyawa yaransa da
matarsa, yadda za su dinga fitar da sautin maganarsu a nutse ba’a baragada ba. Idan ka shiga gidansa za ka tabbatar akwai tarbiyya domin karami ya na girmama na gaba da shi duk kangantar shekarun da ke tsakaninsu. Gashi d’an boko komai a tsare yake an. rubuta a time table kamar lokacin tashi daga barci, lokacin sallah, lokacin cin abinci, lokacin makarantar boko da islamiyya, lokacin kallon talabijin ko hira, lokacin da yara za su dinga fita farfajiyar gidan da kekuna su zazzagaya. Haka lokacin fita wuraran shagatawa ma an ware kamar Zoo, shopping a super markets, cinema da dai sauransu. Idan aka yi dogon hutu kuma an rubuta qasar da za’ ayi visa su dunguma su tafi har da wasu daga cikin masu aiki.
“Tsanani irin na Bakura ba akan iyalinsa kad’ai ya tsaya ba, abun ya shafi ‘ya’yan makwabtansa ma. Zaka ga yaran makwabta sun ga mahaifinsu ba-su razana sun daina fitinar da suke yiba,- amma su na ganin Bakura za su nutsu dan tsoro da kwarjini hade da girmamawa da suke yi masa. Domin shi halinsa ko wucewa ya zo yi ya ga yara su na rashin da’a zai dawo baya ya kira yaron yayi masa fada, idan ta kama da murde kunne ya murde, idan kuma ya ga ya san mahaifin yaron ko yarinyar lallai kuwa zai yi sallama a gidan ya fad’awa mahaifinsa cewar ga fitinar da d’anka yake yi a waje don haka a kula a saka ido.
Duk da wadannan tsauraran matakai da ra’ayi nasa bai sa jama’ ar unguwa da iyalansa sun tsane shi ba saboda Allah Ya gani tsakani da Shi ya ke duk abinda ya yake yi ba dan ganin ido ba ne, dan haka Allah Ya zamar masa jagora, Ya bashi farin jini a wajen iyayen yara da kwarjini a idon yaran gari.
Haka kuma a zamani irin wanna da wuya ka sami
mutum mai arzikin da yake taimakon jama’ar gari da daukar nauyin iyalinsa irin Bakura. Mutum ne mai matukar kyauta da kyautatawa. A kullum kuma a koda yaushe bayarwa yake dare da rana mikawa yake, saboda haka ubangiji Ya ke sake buda masa.
***
Akan Titin Lamido cresent ya ke tafiya da zummar zai tafi masallacin Sheik Aminuddin don daukar karatun yamma da na bayan magruba kamar yadda ya saba zuwa duk ranar jumaa da ranar asabar. Tafiya yake yana bin waga wacce baitocinta ke burge shi
saboda an zuba hikima da habaici da zambo. Kamar, daga sama ya ga wata budurwa ta tsallako ba tare da ta duba titi kafin ta tsallako ba. Saura qiris ya buge ta sai da ya yi da gaske sannan ya iya taka burki gami da yin sauri ya dauke kan motar, saura kadan ya afka cikin kwalbatin da ke gefen hanyar. Irin garan da burkin ya yi, hayaqi da warin taya kai ka ce gagarumin hadari aka yi Allah Ya sa babu mota a bayansa.
•Ya jima a zaune a cikin mota zuciyarsa na bugawa ba tare daya san abinda zaiyi ba kuma amma yaji dadi matuqa da ya ga yarinyar a tsaye ba ta fadi ba dan haka ya tabbatar bai taba ta ba. Ya ci gaba da yiwa Allah godiya a bayyane.
Abin mamaki yarinyar ba ta firgita ba ko kadan ta juyo
ta dube shi a fusace ta harare shi ta yi tsaki ta ce ” kaje a koya maka tuqi, banza kawai.” Ta tsallaka da sauri ta ci gaba da tafiya har tuntube take yi, kallo daya za ka yi ma ta ka tabbatar a gigice take. Daga nan ya tabbatar abinda ya biyo ta ya fi kadewar mota firgici.Ya ji kalamanta tamkar a mafarki yadda yarina
Karama ‘yar cikinsa ta tsaya ta zage shi bayan laifinta ne ma. Ya ji zafin zagin nan sosai, ya tabbatar ba ta da tarbiyya. Amma bai gama yanke hukunci gaba daya ba don ta burge shi kasancewar sanye take da dogon hijabi tun daga kanta har idon sawun kafarta, ya na yi mata kyakykywan zaton ba rashin tarbiyya bane firgicine
• kawai ya sa ta zage shi. Ya bi ta da kallo ya na mamakin irin sauri da ta ke yi. Tana tafe fana ta waiwaye-waiwaye kamar marar gaskiya har. Ya ji a jikinsa in bai bi bayan yarinyar nan ya bincike ta ba bai yiwa kansa adalci ba. Ya juya kan motarsa da sauri ya fara bin ta a hankali. Wani lungu ta shige, tun kafin ta shiga ya hango ta yaye burgujejen hijabin nan da yake burge shi ta cusa a
Hmmmm