KAI KAFI CHAN CHANTA CHAPTER 12 BY JAMILA UMAR TANKO

Bakura ya yi shiru yayin da tsananin rudanin da yake*

ciki ya sake linkuwa a zuciyarsa. Ya dade ya na tunani a ransa. Ya na kuma tambayar kansa da kansa, “Shin ya ya aka yi haka? Ta ina Sajida ta samo kamanninta;, tunda ba ta yi kama da mahaifinta ko mahaifiyarta ko qanninta Yahuza ba? Ita kadai kamarta daban, kuma. sak kamar Zuhuriyata. Qalu innalillahi wa’inna ilaihir raju’un.”

Kamar daga sama ya ji Zahra ta ba shi amsar duk

wadannan tambayoyin da ya jero a cikin zuciyarsa.

Ta ce “Abba, ikon Allah ya wuce haka. Allah Ya na

tsara halittarsa yadda ya nufa. Zai iya halittar d’a bai yi kama da uwa ko uba ba, a can cikin dangi sai ya yi kama da wani d’orin d’osano. Ko kuma ma sai su yi kama babu danganta ko daya.”

Ya gyada kai ya ce ” zai iya faruwa kadan daga cikin

-ikon Allah.”

Zahra ta gyara zama ta ce ” bana son Saidar nan don bata da tarbiyya bata jin maganar iyayenta kuma mamarta ke taya ta.”

Wannan Karon kallonta ya yi da sauri cike da mamaki har da bude baki.

Cikin rawar murya ya tambaya'” me ta yi?!..

Zahra ta tabe baki ta ce ” da alama Babanta ya hanata yin waya da samari sai ta taka turmi ta lege maqwabta ta ari waya ta yi masa.”

A tsakiyar titi ya taka burki ya tsaya Allah Ya sa babu mota a daf da shi da an buga masa. Zahra ta firgita matuga ganin yadda ya razana abin har ya bata tsoro.

Da kyar ya dawo hayyacinsa sannan ya gangara géfen

hanya ya tsaya. Zahra tana jero masa tambayoyin da ya gagara bata amsa mata. ” Abba me ya faru? Me ya saka taka burki? Me* yasa muka tsaya?”

Ya dade a kishingide a jikin kujera ya rufe ido ya dago ya gyara zama muryarsa na rawa ya ce ” bani labarin abinda ya faru dalla dalla.”

Zahra ta bashi labarin komai amma bata ce an karbi

aron wayarta ba, dan kada ya huce akanta yadda taga ya hasala yana cije baki.

•Ya daki sitiyarin motar da garfi yana magana cikin kakkausar murya da fusata.

” daga yau babu ke babu Sajida, kada ki sake cewa in kai ki ki ga me kama da Zuhuriyya. Na yi kuskure, nayi nadama, damar ban kawo ki ba.”

Haka yake fada yana nanatawa kamar karatu. Ya tashi

mota ya fisga kamar zasu tashi sama.

Zahra ma ta yi nadamar zuwanta gidan su Sajida da

kuma bawa mahaifinta labarin abinda ya faru. A lokacin fadan yin samari a boye ya taso har suka isa gida gargadi ya ke yi mata akan kada ta biyewa gawaye masu yin samari kada itama ta ce za ta yi saurayi ko a makaranta kada ya ji ko ya gani. Duk ranar da ya kamata da maganar saurayi sai na lahira ya fi ta jin dadi.

Da alama Bakura ya kwana bai yi baccin kirki ba,

walwalarsa ta ragu kowa ya kasa gane kansa. Zahra ce kadai ta sani ita kuwa ba zaa ji mutuwar sarki a bakinta ba.

Aiki ya shawa Bakura kai bai samu ya je wajen Malam

Yakubu daukar karatu ba sai bayan kwanaki hudu. Ranar da ya je kuwa ko karatun bai tsaya ya dauka ba sai da ya fayyacewa Malam komai akan halinda Sajida take aikatawa a cikin gida. Ya fada ne dan tausayin Malam Yakubu ya na kogarin yin tarbiyya amma ana ruguza masa. Yadda ya ga hankalin Malam ya tashi sai Bakura ya shiga lallashi akan ya kwantar da hankalinsa ya bi abin a hankali. Ya

Kara saka ido kuma yayi mata nasiha da addua.

Malam ya amsawa Bakura da “insha Allah ba zai

aikata wani abu marar dadi cikin fushi ba, zai bi abin a hankali.”Anan suka yi sallama Bakura ya juya ya tafi gida.

*******

Malam ya shigo cikin gida ya iske Umma Furera da yaranta

su ma zaune a tsakar gida. Bayan ya yi sallama bai ce komai ba, sai

kawai su ka ga ya tunkari Sajida ya zakulo wata katuwar bulala

dorina mai baki biyu daga cikin aljihunsa ya fara shadada mata a doron bayanta.

Ta na ihu saboda azaba, amma ta kasa gudu a

sanadiyar cukuikuye kanta da ya yi a cikin burgujejen hijabin data zunbula.

Umma Furera ta zaburo da gudu za ta kwace ta sai ta

ga alamunsa ya na niyyar zambada ma ta, idan ta kuskure ta qaraso inda yake.

“Sai ta daka tsalle gefe ta na kwakwazo ta na cewa

“Malam me ta yi maka? Kar ka kashe ta fa.”

Malam ya daki Sajida har ya gaji ligis yayin da ya

tabbatar ya farfasa ma ta baya, sannan ya rabu da ita.

• Tun muryar Sajida na fitowa ta na ihu har sai da ta dishashe kamar mai mura. Ta fadi a qasa ta yi shame-shame ta na nishi mai hade da kuka.

Yahuza kuwa tuni ya arta waje da gudu a tunaninsa

dukan kan mai uwa da wabi ake yi duk wanda aka samu zaa daka. Malam ya dubi Umma Furera ya juya ya dubi Sajida ya ce “‘Wannan somun tabi ne, kadan ku ka gani. Ni da ku mu zuba a cikin gidan man. Ni da Abdulmajid zan ga wa za ku zaba, idan na jinyata ki ko ma tsiyaye miki ido ai kun ga Abdulmajid zai guje Ki don daman ba son Allah ya ke yi miki ba.

“Umma; Furera ta zabura ta ce, “Wanne rin

.. ..Abdulmajid kuma? Tsohon zance, yaushe rabon Sajida da maganar wani Abdulmajid? Ai tunda ka kwace wayarta zance ya wuce.”

Malam ya daka mata tsawa ya ce “rufe min baki maci

amana, ba a gabanki take hawa katanga ta ke karbar aron waya ta na yi wa dan iskan yaron nan

Abdulmajid waya ba. To zamanku ku dukka ya kusa garewa a gidan nan, don wallahi idan na sake jin wata magana game da Abdulmajid saina kore ku daga gidana, sai dai ku koma gidan

Abdulmajid din. Ya fice kofar gida a fusace ya na huci.

Umma Furera ta garaso wajen Sajida a guje, ta tashe ta zaune gami da yaye hijabin da ke jikinta ta wurgar gefe. Ta kwaye rigar don ta ga irin raunin da ya ji mata a bayanta, sai ga shatin bulala sharba-sharba fatar duk ta farfashe ga jini.

Umma Furera ta dau kukan mutuwa ta na cewa

“na shiga uku, wannan wacce irin kiyayya Malam ya ke yi wa Abdulmajid haka ne. Akan Abdulmajid ya na kokarin ya kashe

‘yarsa ta cikinsa. Wannan wanne munafukin ne ya ke bibiyarmu, duk abin da mu ka yi akan idonsa ya kwashe ya fadawa Malam?”Cikin sheshshegar kuka Sajida ta ce, “na san Yahuza ne, gashi nan ya ruga da gudu daga gani an fara dukana.”

Umma Furera ta ce, wallahi kuwa shine zai fada masa.

Idan ba shi ba to waye a cikin gidan nan? Lallai yau Yahuza sai ya yabawa aya zaginta, sai ya gwammace bai barka ni ya fito daga cikin cikina ba, domin ni ba zan haifi dan da zai jawo a tozarta ni a duniya ba.

Tozartawa mana idan muka sake Malam ya kore mu daga-gidan nan, sai dai mu koma ruga mu yi tallar nono mu da muka saba zama a birni. Mu sha lafiyayyan kunu, ga dan wake har da albasa da salad, tuwan masara da na dawa sai wanda muka zaba.

A sati mu ci shinkafa sau biyu. Naira biyar dinka ta isa ka sha pure * water mai sanyi. A ruga a ina za mu ga firiji?”

Wani qululun bakin ciki ne ya tokare wuyan Sajida

game da maganganun mahaifiyarta.

Ta fada a fusace: “Umma ke ta ruwan sanyi da shinkafa kike, ni ta Abdulmajid nake. Yanzu duk motsin da na yi tare da Abdulmajid:

  •   sai an fadawa Baba ya dake ni. Ba ni da wata hanya da zan ji muryar Abdulmajid kuma a rayuwata bayan haramta min ganinsa da aka yi kwata-kwata. Wallahi ba zai yiwu ba, sai dai Baba ya kore mu ai gara mu koma rugar kin ga Abdulmajid zai dinga zuwa ya na ganina, idan aka daura mana aure sai in tafi da ku gidana shi kenan mu rabu da Baba.”
  • Umma Furera ta daka tsalle ta dafe kirji da hannu biyu ta zazzare ido ta ce, “rufa ni ki saya ni ‘yar nan, kar ki min sakiyar da babu ruwa. Yaushe za a yi wannan danyen aikin da ni?

Ai kuwa in baki rabu da Abdulmajid ba za mu raba hanya. Yaron mayaudari. Aka ce miki aurenki zai yi? Aini tunda na rabu da- rugar fulani insha Allah ko gawata anan birni za a binne ni.

Wannan wasiya ce na bar miki. Haka idan Malam ya shigo zan bar ma sa wanna wasiyyar. Kuma Zan shiga makwabtan idan Malam baya nan, sai na ja kunnen lyayye da take migo miki aron

Hmmmm