KAI KAFI CHAN CHANTA CHAPTER 14 BY JAMILA UMAR TANKO

Yahuza ya fice da sauri ya na kuka sharkab. Sajida da

Umma Furera suka bi shi su na kwalla kiran sunansa, amma abu ya ci tura. Tuni Yahuza ya keta zaure, ya wuce dandamalin kofar gida, ya tsallake kwata, ya bi ta kan bola ya tunkarí masallaci. Bai dire a ko’ina ba sai a lungun liman a gaban mahaifinsa. Yahuza. magana yake amma baa fahimtar abin da yake fada wani tsatstsaman kuka da yake tasowa daga can cikin zuciyarsa a inda jiyiyoyin idanuwansa suke zugo wani ruwa mai dumin gaske suna fesarwa saboda tafarfasar da zuciyarsa ke yi da tsananin quna da

soyuwa.

Malam ya dade ya na tambayarsa haka Yahuza ya

dade ya na bada amsa, amma baganewa ta ci tura, saboda hayaqinda bakinsa yake na takaici. Malam ya kamo hannun: dansa, abin kaunarsa Yahuza ya nufo gida don jin ba’asi.

Sajida tsaye take a tsakar gida ta na kai kawo cikin

zulumi da fargabar abin da zai je ya zo.

Fada take, “Umma, kar fa yaron nan ya je ya hada min

tuggu, Baba ya zo ya sake yi min duka irin na jiya.”

Ta na rufe bakin sai ta ji sallamar mahaifinta ya danno

kai cikin gida riqe da hannun Yahuza. Ta zabura ta daka tsalle sai ga ta a bayan Umma Furera ta buya.”

Malam ya fada cikin sanyayyiyar murya,

“Tsaya daina gudu, ba dukanki zan yi ba. Don me zan dinga dukanki kamar jaka?

Ai bambancin dabba da mutum shine hankali shine tunani da jin magana. Me yake faruwa ne Yahuza ya je min da kuka?”

Da Yahuza ya ga sun fara hanya-hanya su na gogarin

baudewa su gyara magana, sai ya yi goqarin kashe gobarar da take cin makogaransa, don ya ceto muryarsa ta fito radau dan ta cece shi. Ya rangada bayani tas yadda aka yi tun daga farko har karshe.

Kan ka ce kwabo idanuwan Malam sun ciko da hawaye, ya dubi Yahuza duba irin na tausayi. Ya sa hannu ya share masa hawaye.

Ya ce, ” Allah sarki, sun dauki alhakinka, sun

zarge ka da laifin da ba ka aikata ba. Sun yi kuskure wajen yanke maka hukunci. Idan ba yafe musu ka yi ba, Allah sai ya Kama su da hakkin zalumci. Ka je ka saka kayan makarantarka,. ka karbi koko kasha ka zo in raka ka makaranta, saboda sun sa ka makara.”

Yahuza ya nufi dakinsa ya na goge hawaye yayin da

zafin da ke kona zuciyarsa ya fara hucewa a sanadiyyar haqurin da mahaifinsa ya ba shi.

Malam ya juya ya dubi Sajida da mahaifiyarta

wadanda kowannensu ya yi wuqi-wuqi da ido a lungu su na jiran hukunci a game da taaddancin da su ka aikata da sanyin safiyar nan.

Ya ce, “Kun dauki alhakin yaron nan, ku nemi

gafararsa wallahi Yahuza bai taba fada min wata magana game da Abdulmajid ba, sai dai ma ya dinga boye min abin da ke wakana don kada in doke ki. Kin manta irin tashin hanklin da yake shiga tun ya na yaro idan ina dukanki? Kin san dai ba na tsoronki kuma bana mahaifiyarki, da har zan yi muku rantsuwa dan kar ku gara dukan Yahuza. Ina da ikon da zan saka dokar kada a gara dukan Yahuza har ya girma, kuma dole a bi maganata. Dan haka kar in sake ji ko in gani an bakantawa yaro a bisa laifin da bai ji ba kuma•bai gani ba. Ko yau kika kula Abdulmajid a fili ko a waya labari zai ruske ni, zan dauki mataki mafi tsaurin gaske akan ku, ku dukka.”

Daidai lokacin Yahuza ya gama shan koko ya dauko

jakar makarantarsa, Malam ya kama hannunsa suka fice ya raka shi har cikin Giginyu Primary.

Sajida ta sulale ta zaune gami da jan wata doguwar ajiyar zuciya mai dauke da jimami hade da rudani.

Haka Umma Furera ta shiga irin wanna hali ba shiri ta lalubo

‘Yar kujerarta ta zauna ta doka tagumi.

Lokaci mai tsawo aka dauka aka rasa wanda zai fara magana a junansu. Ba tare da Sajida tayi miyar furtawa ba bakinta ya. yi caraf ya fitar da tambayoyin da suka addabi zuciyarta.

“Wannan wanne munafikin ne yake bibiyata akan

– Abdulmajid? Wallahi sai na gano munafukin nan da yake so ya raba ni da Abdulmajid, ko waye ko kuma ko wacece, duk tsufanta ko kuma duk tsufansa ko da

gemunsa yana ja da gasa, sai na ci mutucinsa na tozarta su ko da yin haka zai jawo a raba ni da numfashina a duniya.”

Umma Furera ta ce, “hakika na yarda ba Yahuza ba ne

ya fada, don da Malam ba zai boye ba. Kuma duk abin da Malam ya yi rantsuwa gaskiyar ta kai gaskiya. Daman Yahuza ban san shi da gulma ba, shi dai a bar shi da kwadayi da roko. Kash na dau alhakin d’ana.

****

Da daddare misalin garfe goma, bayan Zahra ta yi sallama da mahaifanta ta shiga kwanciyar barci. Ta cikin falonta ta wuce kai tsaye zuwa dakin da gadonta yake. Shigarta ke da wuya sai ta zarce bandaki don ta watsa ruwa. Ta fito ta wuce kai tsaye durowar da ta jera rigunan bacci kawai kala-kala wanda a kalla sun fi kala hamsin. Riga da wando, riga da siket, doguwar riga ba masu santsi da masu laushi (cotton). Ta zabi wata ‘Yar yaloluwar riga iya gwiwa ta saka, ta zo ta shiga bargo. Bayan ta gama addu’o’in kwanciva barci ta shafe jikinta tun daga kanta har kafafunta. Ta lumshe ido yayin da sayin split A.C da ke kunne a dakin yake bi sanka-sanka yana ratsa hudojin jikinta. Ba ta ankara ba sai ta ji wata muguwar girgiza a garqashin filonta, a tunaninta garin ne gaba daya yake girgiza. Ta tashi zaune gami da daga filon da sauri ta son ta ga abin da ke ciki ashe wayarta ce ta manta ba ta kashe ba, ashe wayar tasata a vibration take. Ta yi wata ajiyar zuciya domin tuni numfashinta ya quracewa huhunta, saboda tsorata. Ta miga hannu ta dauki wayar ta duba sunan Hassana Ummi Sulaiman ne ya fito dara-dara. Ta yi mumushi gami da farin cikin jin kira daga kawarta, aminiyarta, makarantarsu ta boko wato PRIME COLLAGE, haka Islamiyyarsu daya Hassan Gwarzo islamiyya dake Sulaimanu Cresent. Ta fada cikin tsokana. Ummi ‘yar autar Mama ya kike? Ya gari? Ya aka yi kika kai goma da rabi baki kwanta ba, don na ji hayaniyar Nura, Sulaima da Faruk?”

Ummi ta yi dariya ta ce, “albishir na kira in miki. Ashe

gobe mid-term break ne babu makaranta har muke damun kanmu da karatun test mun manta, sai yanzu Khadija Rabiu Gumel ta kira ta tuna min.”

Zahra ta Kama kai ta tsuke fuska ta ce, “Oh God! na

manta, amma ban ji dadi ba wallahi na karantu sosai. Don dazu bayan na dawo gida daga makaranta da yake babu Islamiyya, Na kira Abbana a waya ya zo ya kaini Kano State Library mu ka yi ta karatu da shi. Ya sake koya min Physics sosai sai garfe shida muka dawo gida. Shi ma ya manta gobe ba makaranta yanzu ya: gama cewa in zo in kwanta, saboda gobe in tashi da wuri. To- bari in bar wayana a kunne idan Mama ta tashe ni da Asuba, in ce mata ta-yi kwanciyarta gobe hutu ne. Thank you very much Hassana Ummi kin taimaka da kika tuna min. Ki gaida gaida su Mama dan

Allah.” Hassana Ummi ta ce “Za su ji insha Allah. Good night partiner.”

Su ka kashe waya a lokaci guda, Zahra ta mayar da waya karkashin filo ta kwanta tana tunano hirar da sukayi da kawarta wacce koda yaushe Su na tare a wani Gangaren kuma rashi yin makarantar taimaka mata akayi da aka fasa yin test din. saboda yau ta karantu idanuwanta har ja suke yi saboda barci. Ai ko ba komai ta san za ta bar

kwakwalwarta ta huta, kafin ranar-jarabawar.

Sai ta ji wayarta ta sake daukar qara wanna karon

mamaki ne ya rufe Zahra. Sai ta ce a ranta, “Na san Sadiya Idris ce ko Bilkisu Hamisu za sa fada min gobe ba makaranta, basu san Hassana Ummi ta riga su ba.”

Tana duba wayar, sai ta ga lamba ce ba suna, don

haka ba su ba ne, amma zai yiwu su din ne ko wayarsu ba kudi suka yi amfani da ta ‘yan gidansu. Kamar yadda a da kafin a hada mata waya take amfani da wayar Mamarta wajen kiransu. Ta danna wayar cikin farin ciki gami da cewa. To Hassana Ummi ta riga ku, na sani gobe mid-term break babu makaranta, don haka babu test.!

Sai taji wani lallausan murmushi an ce, “Hello,

dan Allah. Zahra ce akan layi?”Gabanta ya yanke ya fadi ragagagasss!!!! Domin muryar namiji ce. Tunanin da ya fado mata shine, to tunda ba Babanta ba ne yake kira tabbas Baban daya daga cikin kawayenta ne. Abin da ta dauka wata kawarta ce marar waya ta roki Babanta a kira mata gawarta shine ta ji muryar namiji. Nan da nan Zahra, ta gyara zama ta duka ta gaishe shi cikin ladabi. Ta cigaba da sauraron abin da zai fada mata. Ya na magana cikin sanyayyar murya, nutsatstsiya. Ko wanene wannan mai maganar hakika ya 

Hmmm