san darajar bil’adama. Tunanin Zahra sai ya fara babanta da manufar wannan mai wayar, ma’ana ba ta ji ya ce ma ta ga kawarta ba wance. Bayani kawai yake yi mata akan ya yi matukar farin ciki da jin muryarta.
Ta gigice yayin da hankalinta gaba daya ya tashi. Ta
tambaya cikin wata hardaddiyar murya mai rawar disko, saboda gigicewa.Ta ce, “Malam ko ka yi kuskure ne ka bugo ba ni Zahrar ka ke nema ba?”
Ya yi murmushi mai fitar da sigar muradi ya ce, “Ban
yi kuskure ba, ke Zahra nake nema, domin lambarki ko daga barci aka tashe ni zan kawo ta.”
Saboda tsabar firgicewa sai tasa hannu ta katse wayar
jikinta ya dau karkarwa tamkar mai jin sanyi.Matukar mamaki ya rufe ta. Ta ina wannan mutumin ya sami lambarta? Me yasa ya kira ta’? Me yake nema a wajen ta’? Babu amsar wadannan tambayoyi na ta. Tana cikin wanna hali sai kuwa ta ji wayarta na girgiza ta sura da sauri ta duba lambar dazu ce, don haka sai ta ki dauka yayin da kuka ya fara rufto mata, tsoro ya addabi zuciyarta ta rasa abin da yake yi mata dadi. A zaune take akan gado ta yi quri, domin
kwanciya ta gagari hakarkarinta. Mutumin nan dai bai hakura ba, kira yake sake yi tsakaminsa da Allah. Ta miga hannu ta danna kai ka ce kashi ne a jikin wayar yadda take kyamar wayar. Ba tare da ta bari ya yi magana ba ta fada cikin kuka da rawar murya.
“Malam waye kai? Me kake nema a wajena?”
Ya yi murmushi ya fada cikin lallausar murya ya ce
“Zahra cool do down my dear, Za ki ji ko ni waye, kuma da kuma dalilin da yasa na bugo miki. Ya yi ajiyar zuciya mai hade da murmushi ya ce “Na san baki sanni ba, kuma za ki yi mamaki da na kira ki, actullaly my name Is Abdulmajid EI-Museh ina kira daga Bampai quaters.”
-Zahra ta maimaita sunan, “Abdulmajid El-Musch ban sanka ba, ban taba jin sunan nan ba.”
Yayi dariya, “Allah sarki daman na san ba za ki sanni
ba. Sai dai ina fatan ki san ni nan gaba,”
Zahra ta fada cikin fushi, gami da daga murya, “Me
yasa ka kira ni, me kake nema?”
Ya sake lanqwasa murya ya ce, “Haba baby me yasa kike tayar da hankalinki, ko ban ganki ba daga ji muryarki na san kina da kyau. Ba’a son mace me kyau ta dinga wahala cool down.**
; Zahra ta ji wani dacin takaici yana kokarin shage mata wuya, sai wani hawaye mai dumi ne ya ke zubo mata. Hankalinta gaba daya ya tashi, abin da take ji wai-wai-wai a gari ya iso gare ta.
Ya katse mata tunaninta ya ci gaba da cewa, Zahra
gaskiya abin da ke tafe da ni alkhairi ne, babu komai a ciki sai tsananin so da kauna. Kin fahimce ni ko? I love u so much Zahra.”
Yayin da Zahra ta dafe qirji, domin ta ji wani abu daga
cikin kirjinta ya na zillo zai fado qasa, don a fargaba. Ba tare da ta iya cewa komai ba, ta katse wayar. Daga nan ta tabbata lallai
• wannan bawan Allah ya dauko hanyar da zai rugurguza Zaman lafiya a gidan nan. Ba ita kadai ba har mahaifiyarta kashinta ya bushe daga lokacin da mahaifinta ya san abin da yake faruwa.
Kuma nan da nan Bakura Zai Iya ganewa saboda duk sanda. za ta tafi makaranta ya kan karbi wayar ya riqe har sai ta dawo sannan zai ba ta. Haka
kuma duk bayan wata yana Karbar wayarta data mahaifiyarta ya fita da ita ya sako musu credit. Ya na yawan bincike wayar har wani lokaci ya yi game. Bakura yana yawan ja mata kunne cewar ta kiyaye kada ta sake ta kira saurayi ko wani ya kirata. Ya hada mata waya dón ya dinga tashinta da Asuba ko idan ta fita unguwa a kira aji in ta isa lafiya, sai kuma don ta dinga hira da kawayenta mata.
Kuka mai yawa ya karu. Ta fito falonta ta zauna a kan kujera yayin da ta dora kafafunta biyu akan kujera tasa hannayenta biyu ta matse kafafuwanta tana mai karanto Inna illlahi wa’inna ilaihir raji’un.
Wayarta ce a gefenta ta sake daukar ruri, ma’ana waya na shigowa. Ta juya fuskarta a hankali tana duban wayar, saboda tsabar tashin hankali, lambar Abdul majid ce ke shigowa don haka sai ta qi amsawa.
Matukar mamaki ya rufe zuciyarta, ta na; tunanowa a duniya a ina ma ta taba jin mai su Abdulmajid. Don ità ba ta taba hulda ko a danginta na wajen uwa da ba kacokan babu mai irin wannan suna Abdulmajid, sai kira yake tun karfi. Ya kira ta yi ringing har ta gama Zahra ta qi ta amsa. Sai ta ji massage ya shigo. Cikin rawar hannu ta dauki wayar ta bude sakon, ta ga dai har yanzu Abdul majid ne abin da ya rubuta kuwa shine kamar haka:
Hi sweety, answer my calls. I will explain pls. Ma’ana ya abar zazzagar kauna ki amsa wayata zan yi miki bayani. Firgita kan firgicewa yayin da ta kwatanto a zuciyarta ace mahaifinta ne ya bude sakon nan wayar na hannunsa, ya ya za tayi ai na lahira sai ya fita jin dadi in ji Bahaushe. Abdulmajid ya cigaba da kira, Zahra ta yanke hukunci mafi sauki akanta gara ta dinga amsa wayarsa akan ta qi amsawa idan ya ci gaba da turo® mata irin wadannan sakonnin matsala ne. Amma in waya ce a gaban iyayenta ta iya dauka ta ce wrong number ta katse, amma idan a rubuce ne babu mai fitar da ita sai Allah. Zahra tasa hannu ta danna ma’ana wajen amsa waya, ta fada cikin dakakkiyar zuciya, domin tsananin tsoron da take ji ya fita yanzu, fatanta ta kwaci kanta.
Ta ce, “What do you want from me?”
A wannan karon shi kuma tasa muryar ce take
karkarwa.
金
Ya ce, “Zahra ki saurare ni mana ina sonki ne, na yi miki alkawari zan canja miki rayuwarki. I will do anything for you.”
Ta fada cikin fushi, “Kamar ya ya?”
Ya ce, ‘Waya mai tsada, in zuba miki kudi a ciki account babu adadi, English wears kala-kala. Ke zan iya siya miki mota
-saboda ina sonki, ki rabu da sauran samarinki…
Ta daka tsawa ta katse shi ta ce, ” enough is enough, ka sanni kuwa? Ka san yaya nake? l’am a small girl, I am just 15yrs ya za ka dinga kirawo min sunan samari? Ya za ka ce za ka siya min mota? Me ye Abbana ba shi da shi da kake so ka nuna min kudi? Abdulmajid please I beg you ka rabu da ni kana so ka jawo min matsala infact ka jawo abin da Abbana zai aikata kisan gilla a kaina ko a kanka. Akwai manyan yan mata a gari ka je ka tsara su ka rabu da ni please. Yaushe ka san ni? A ina ka sami number na for God sake, za ka jawo min problem.” Sai ta fashe da kuka. Abdul majid ya fada cikin nadama da tausayawa “Oh God baby don’t cry. Ni mai sonki ne zan kawo miki farin ciki ba zan jawo miki problem ba. Na sami number a dalilin wata sister ta Sajida.”Zahra ta dakata da kukan ta maimaita sunan “Sajida, Sajida, Sajida.” Har sau uku a inda kwakwalwarta take kai kawo tana so ta tuma inda ta taba jin mai suna Sajida ta na ta kokarin tuna a duniyar da ta taba haduwa da mai suna Sajida a rayuwarta.
Abdul majid ya ci gaba da cewa, “Ba kawarki ba ce
Sajida? Ai ta taba kirana da wanna lambar anan na sami lambarki, ta fada min sunanki Zahra.”
Zahra ta sake maimaitawa, “Kawata Sajida, a ina-nake da kawa Sajida? Ni gidan wacce kawa ake barina inje?”Abdul majid ya ce,Common baby, ki tuna mana a
cikin satin nan Sajida ta kira ni da wanna lambar da yamma. Baki tuno Sajida Yakub Kawo ba?”
Sai a lokacin computer kwakwalwarta ta fito mata da
Sajida muraran ta gane wacce yake mufi, sai ta ji wani sanyi a ranta, ta fada cike da murna.
“Okay na gane Sajida a Kawo ka kira ne a bata waya, ai bama tare. Ko ba SajiAbdulmajid ba budurwarka. Ai Sajida aminiyata ce duk sanda mu ka hadu zan kira ka in ba ta waya saboda haka ba sai ka gara kira ba.”
Abdulmajid ya yi dariya ya ce, “Kina da wayo da yawa
Zahra. Tunda kin fahimci Sajida budurwata ce, no need in boye miki harma kin rige sunan da ta had Sajimajid. Abdulmaid so yake yanzu in zama na an hada mana
SAJI-ZAH-MAJID Abdulmajid.” ma’ana Zahran
Zahra ta tsuke fuska yayin da wani mummunan sabon
tashin hankali ya far mata. Ta mike tsaye a fusace.
Ta ce “Kai ba zai yiwu ba, ba zan iya ba, ba zai yuwuwa ba. Gara ka rabu da ni tunda wuri kafin mahaifina ya sani. Kar ka kara kirana. Ka zama mai bata tarbiyyar da iyaye suka yi wa ya’yansu.
Hmmmm