Mace kwarya ce me kyau wacce iyayenta suka adana ta suka sagale ta a ragaya, don karta fito tsakar gida a yi amfani da ita ta yi datti. Amma kai ka zuga kwaryar nan mai kyau take ballowa daga ragaya take fita titi tana tunbele kana garari da ita, har sai da ta baci, sannan ta zagayo ta haye ragaya kamar ba ta yi datti ba a tunanin Iyayenta, kwaryar nan ta su tana nan da kyawunta,”
Ta ci gaba da cewa “Abdulmajid, Abbana ya ce ni
kwaryarsa ce mai kyau, ya sagale ni a ragaya don kada in yi datti ya ce min yana fatan wanna kwaryar tasa ba ta fakon idonsa tana ballowa tana fita ta yi yawan garari ta yi baki ta zo ta d’ane a ragaya, kamar wata kwarya ta gari kamar yadda Sajida ke yi.”
Zahra tana gama fada sai ta murtsike wayar gaba
daya ta kashe. Yayin da take murza idanuwanta ko mafarki take a cikin barci. Ta ga daram ba mafarki bane, ido biyu ne.
Babu abin da take hangowa a cikin idanuwanta sai lokacin da suke tafe da mahaifinta a mota bayan sun taho daga gidan su Sajida sanda ta yi masa zancen Sajida ta na lekawa katanga ta ari waya su yi magana da saurayi. Hankalinsa ya yi matukar tashi kamar zai jawo ya dake ta ita mai ba shi labarin. Ina ga idan ya ji ita ce take zance da saurayi a waya?
Jikinta na karkarwa ta koma kan doguwar kujera ta takure yayin da wannan dare ya zame mata shine daren farkon da ta taba haduwa da irin wannan gagarumin tashin hankali a rayuwarta ta duniya, tun da Allah ya halicce ta. Dan haka yau ne dare na farko da barci ya karacewa fatar idonta. Yadda ta ga rana, haka ta ga dare tana zaune tana tunani. Ba tare da tasan Asubah tayi ba, Abbanta ya gwada kiran wayarta ya ji a kashe, don haka sai ya zo da kansa har kofar dakinta yana bugawa. Saboda tsabar ba ‘a cikin
hayyacinta take ba, haka ta zurawa kofar ido tana kallo ta manta idan ka ji ana buga kofa budewa ake a ga ko wanene. Wanne irin bacci kikeyi haka ne?”
Muryar mahaifinta ta ji ya ce “Yagana, bude kofa mana. Sai ta yi firgigit ta tashi zaune daga kishingiden da take
ta amsa cikin rawar murya. “Na’am.”
Ta yi duru-duru ta fisgo wani ‘dogon hijab ta magala ta bude kofar falon da sauri. Nan, aka hau kallon-kallo tsakanin Zahra da mahaifinta. Shi ya na kallonta saboda yadda yaga tana kallonsa galala tana zare ido kamar wata sabuwar tababbiya da alama idanuwanta su na tattare da barci mai yawa don sun yi luhu-luhu. Ita kuma tana ganin mahaifinta sai tsoro ya kamata don ta kwatanto irin tashin hankalin da za a yi duk lokacin da ya kama ta da Abdulmajid ya bugo mata waya ko ya turo mata sako ta waya.
Bakura ya fada cike da mamaki, “Mamana, lafiyarki
kalau kuwa? Kin yi bacci yau ko karatun test din kike yi tun dare?”
Zahra ta ji dan sanyi a ranta da ta ji ya fadi haka, ta
amsa da sauri. “Eh karatu na kwana ina yi.”
Bakura ya yi shiru na wani dan lokaci, sai ya girgiza kai. Ya ce “Ba kya jin magana, maimakon ki yi bacci yau ki tashi a nutse meye amfanin kin kwanciya ba ki yi barci ba, ki shiga dakin jarabawa kina gyangyadi? Ki shiga ki shirya ki je makaranta da wuri.”
Tana rawar jiki ta rufe kofar falonta, ta shiga ciki da
gudu tà lalubo wayarta a karkashin filon kujera, hannunta na karkarwa ta kunna wayar cikin ‘yan dakikai sai ga waya radau ta kunnu, yayin da kunnuwanta suke jiyo mata wani sauti daamm, daamm sakon text message yana shigowa, har guda uku. Wannan karon ma firgita ta sake yi tun kafin ta bude taga me aka rubuta babu tantama ta ji a jikinta Abdulmajid ne mai wannan danyen aikin.
Ta bude sakon farko, sako ne daga Abdulmajid yana
bayyana mata tsantsar kaunar da yakè yi mata. Sai take kwallar
takaici. Ta bude sako a biyu, sako ne daga Abdulmajid yana bayyana mata tsamanin begen da yake yi mata. Sai ta ji hawayen qunar rai. Ta bude sako na uku, sako ne daga Abdulmajid ya na bayyana mata tsagwaron halin da ya shiga a sanadiyar kin ba shi hadin kan datayi, ya baza hajarsa bai siyar ba ma’ana bata karbi soyayyarsa ba. Sai ta ji wuyanta ya hau makakin tashin hankali.
Wannan ne karo na farko da Zahra ta ji ta fara tsanar rayuwarta.
Bugun da ta ji ana yiwa kofar falonta ne ya zaburar da
ita, ta cillar da wayar gefe ta mike tsaye tana muzurai, sai ta ji muryar mahaifinta yana kwalla kiran sunanta. Ta na karkarwa ta je ta bude sai ga mahaifinta da kaninta Abubakar a tsaye carko-carko sai zare ido take, ta kalli wannan ta juya ta kalli wancan.
Bakura ya ce “Da gaske ne yau babu makaranta kun
fara mid-term break?”
ta fara gwagwarmaya da makoshinta. “Eh, eh, ashe haka ne na manta.
Bakura ya tsuke fuska ya ce “Me yasa kika kashe* wayarki? Na san kawayenki su Khadija Rabi’u za su kira su fada miki tunda ke kin manta. Ki na ‘yar yarinyarki karama kina mantuwa, kamar wata tsohuwa? Ki je ki dauko wayar ki kunna ki kawo min in yi magana da principal. Ya za a yi a ce ana hutun midterm ba’a ba ku a rubuce ba.”
Zahra ta na karkarwar jiki ta koma cikin falonta da
sauri yayin da fargaba da tashin hankali suka garu akan na da.
Abubakar ya dubi mahaifinsa ya ce “Abba an bamu
takarda a rubuce a cikin mota muka bar su, bari in je in duba.” Ya nufi wajen mota kafin Bakura ya bude baki Zahra ta fito cikin muzurai da rawar jiki ta mikawa mahaifinta waya. Ya karba ya juya ya nufi dakinsa da wayar. Juyawarsa ke da wuya sai wayar ta yi kara alamar sako aka turo (Test massage). Bakura ya yi sauri ya tsaya Cak ya duba wayar bai yi wata-wata ba sai ya bude sakon ya karanta ya juyo da sauri ya dubi Zahra. Tuni
• numfashin Zahra ya fara tafiya kamar mai shirin tafiya barzahu.
Ya dube ta, ta dube shi, sai taga ya gyada kai ya juya ya tafi. Ta sulale ta tsugunna don tsananin tashin hankali, ta san tabbas Abdulmajid ne, sakonnin kuma soyayya duk da ta goge wadancan na jiya kafin ta mika masa wayar. Ta irin matakin da mahaifinta zai dauka akanta, yanzu ta sake tsanar kanta, takaicin da dana sanin dama bata nace ta ce mahaifinta ya kai ta ta ga Sajida mai kama da Zuhuriyya. Ba dan ta je gidan ba, da tsautsayi bai’sa ta bada aron wayarta ba. Da a ina Abdulmajid zai sami number wayarta?
Hawaye ya dinga surnano mata babu tunanin da baizo
mata ba a rai ba, ta ji kamar ta hada kayanta ta gudu wajen dangin mahaifinta a Maiduguri a neme ta a rasa, saboda ta san yau hukuncin da zai dauka akanta ba kadan ba ne.
“Muryar mahaifinta da mahaifiyarta taji su’na fitowa
daga dakinsa, Zahra ta zabura ta miqe tsaye gami da goge hawayen da ya yi mata faca-faca a Idanuwanta. Ta yi zuruf tana kokarin shigewa cikin daki da gudu sai ta ji muryar mahaifinta ya kwalla kiran sunanta. Ta waiwayo a firgice cikin rawar murya ta amsa. Ya karaso kofar falonta a inda take tsaye ya mika mata wayarta. Ba tare da ya sake duban inda take ko ya yi wata magana ba, ya zarce zuwa babban falo.
Mahaifiyarta ce ke biye da shi ita ce ta tsaya tana kallon
Zahra kallo irin na lafiyarki qalau Kuwa? Zahra ta gaishe da mahaifiyarta cikin firgici. Samira ta amsa gami da jero mata tambayoyi har guda uku a jere.
“Lafiyarki kalau kuwa? Me ke damunki duk kika
susuce? Me yasa kika kashe wayarki?”
Amsar wadannan dogayen tambayoyi su ne,
“Ba komai.” In ji Zahra.
Ba tare da Maman Zahra ta sake cewa komai ba ta
juya ta nufi falo. Zahra ta yi wuf ta afka cikin falonta gami da* datse kofar da mukulli, ta dade a jikin kofar a jingine, ta yi ajiyar zuciya mai fitar da tsantsar tashin hankali. Sannan zuciyarta ta tuno mata da addu’ar da ake karantawa idan ka gamu da wata masita.
“Inna lil laahi wa innaa ilaihi raju’un, Allahumma ajirni fi musiibatii wa aq-likini khairan minhaa.”
Ta fada ta maimaita ta sake ta maimaita har sau uku,
sannan ta ji numfashinta ya fara dira daidai. Ta wuce bandaki domin dauro alwala. Rabon Zahra da ta rasa sallar Asuba har ta manta, amma yau saboda tsananin tashin hankalin da Abdulmajid ya jawo mata ya sa ta rasa sallah akan lokaci, sai da gari ya waye tangararai.
Sallamar sallarta ke da wuya. sai wayarta ta dau ruri:
Ta yi ta maza ta suri wayar gami da dubawa, sai Ta ga lambar Abdulmajid ce, a take ta ji wani takaici da daci a ranta. Ta danna a fusace ba tare da ta ce masa komai ba ta kasa kunne tana sauraronsa. Ya yi ta magana tamkar da itace yake waya.
Ya yi gyaran murya ya ce, “Ko ba Zahmajid ba ce, shin kin ga sakonnina na jiya da na yau da safe kuwa ?
Tun daga nan Zahra ta sake susucewa tabbas shine ya
turo wanna sakon mahaifinta ya karanta. Babbar matsalar Zahra
Hmmm