Shine ita ba ta iya tsiya ba, ba ta san yadda za ta cashewa Abdulmajid ba. Muryarta na karkarwa cikin kuka take masa magiya ta ce “Abdulmajid me yasa kake son jawo min masifa da bala’i a rayuwata? Ba ka sanni ba, ban sanka ba, na fada maka ni yarinya ce qarama yar makaranta. Abbana ya hana ni kula samari, wani lokacin wayata a hannunsa take, sai ya kusan kashe ni a duk lokacin da ya kama text massages dinka ko kiran wayarka. Ka rabu da ni ba na soyayya, ba na sonka.”
Ya yi wata shamilalliyar dariya mai kara takaici ga
wanda ake yiwa.
Ya ce, “Zahrah wallahi ba zan rabu dake ba, ko da za a kashe ki, nima a kashe ni. Ban taba hanuwa ba idan ina son yarinya ko da iyayen yarinya za su hadiyi zuciya su mutu.”
Zahra ta razana ta dora hannu aka ta fasa kuka tana
cewa, “Wa iyazubillah, Allah ya yi min tsari da kai.”
Ta murtsike waya ta katse. Hannunta na karkarwa ta
bude inbox don ta karanta sakon dazu, don taga me mahaifinta ya karanta. Sakon Hassana Ummi Sulaiman ne ta rubuto mata akan maganar yau ba makaranta anjima zata zo ta koya mata lissafi.
Zahra ta yi ajiyar zuciyar jin dadi. Amma sai ta tuna cewa
“Abdulmajid da bakinsa” ya* ce ya turo da sako da sassafen nan.
• “Anya kuwa ba sakon Abdulmajid Abba ya karanta ba kuwa da gama ya goge? Kai sakon Hassana ne ya shigo dazu da na Abdulmajid ne a take zai yi magana ba zai yi shiru ba ya kyale ta ya gyada kai ya wuce ba. Zahra ta shiga wani matsanancin kokonto da wasi-wasi. Abdulmajid ne yake ta tutturo mata sakonni a jere a jere wannan na bin wanna wancan a bayan wancan. Yana kara jaddada mata shi fa yana sonta, kuma ba zái rabu da ita ba. Kuma ko a ina take sai ya nemo ta. Tun tana karantawa ma har ta daina _sai dai tayi ta gogewa, daga ya shigo sai ta goge. Sallamar kaninta Usman ce ta tunasar da ita a duniyar
da take, don tuni ta zurfafa a fagen tunanin yadda za ta yi da rayuwarta. Ya shigo ya durkusa a gabanta ya gaishe ta. Zahra na zaune akan sallayar da tayi sallah a tsakar dakinta, ta zubawa
Usman ido tana kallo sai can ta bude baki dakyar ta amsa gaisuwar, saboda ba ta kaunar yin magana, ba ta so a kusance ta yau.
Ya ce “Sister Zahra, Mama ta ce ki fito mu yi break fast
•ke ake jira tun dazu.”
Ta yi kamar ta ce ta koshi, sai ta tuna ashe bata Isa ba
lafiyarta kalau ta ce ta koshi mahaifinta na raye a doron kasa tabbas zai hukunta ta.Ta fada cikin siririyar murya. “Ina zuwa.”Fitarsa ke da wuya ta mike da sauri ta fada bandaki bayan ta yi brush sai tasa sabulu ta wanke fuskarta tas, ta zo ta rangada kwalliya a kodadden idanuwanta. Ta saka doguwar jallabiya mai hade da hula ta fito, Kai tsaye ta wuce babban falo kan dining table. Ta iske su su dukka a zazzaune ba wanda ya fara ci ita ake jira. Ta yi musu sallama, gaba daya suka amsa mata. Ta jawo kujera ta zauna ba tare da ta yarda sun hada ido da daya daga.. cikin’ mahaifanta ko qannenta ba. Kowa ya zuba nasa a plate bayan* sun yi. Bismillah da addu’0’i, kamar yadda Bakura ya koyar da. Iyalinsa tun su na kanana. Dole idan sun zo cin abinci suyi addu’a su ce, “Ya Allah ka kara bamu lafiya, ka raba mu da yunwa, kishirwa, talauci, da fatara. Allah ka raba mu da rowa da hassada da bakin ciki. Allah Ka bamu ikon taimakon mabuqata. Allah Ka taimaki mai nemowa duk sanda ya fita nema kada ya rasa.”Ire-iren wadannan addu’o’i Bakura da iyalansa suke yi, duk sanda suka zo cin abinci sun haddace tsaf kamar karatu. Bayan sun shafa addu’ar a fuskokinsu, sai kowannensu ya farwa plate din dake gabansa ga kofin shayi a gefe. Soyayyen dankali ne da soyayyen kwai, ga farfesun talo-talo a gefe. Sannan ga ferarrun yankakkun kayan marmari kamar gwanda, ayaba, lemo a cikin katon faranti a tsakiyar teburin kowa da cokali mai yatsu (folk) a gabansa wanda zai nutsa ya danko ya kai bakinsa.
Duk wannan rashanar ba dadinta Zahra ke ji ba, tamkar dusa take cusawa a cikinta. Kallon karillar da mahaifinta ke.yawan yi mata shi yake sake tayar mata da hankali, sai ta ji abincin ya tokare makoshinta ta kasa hadiya. Ta yankewa kanta shawata gara ta fita da gudu ta kelaya aman karya ko ta sami sukuni, ta fake da rashin lafiya dan kar a gane ta na cikin matsala.
Hankalin Maman Zahra ya yi matugar tashi haka ma
Qannenta a lokaci guda su dukka suka zabura za su bita bakin gofa inda ta fita ta durqúsa tana kakarin amai, Bakura ya daka tsawa ya ce duk su koma su zauna, su ci gaba da cin abincinsu su gyale ta.
Wannan al’amari ya yi matugar ba su mamaki musamman Zahra.
Hankalinta ya tashi matuga a yanzu bata tantama ta san dalilin da yasa ya yi mata haka, tabbas yaga sakon da Abdulmajid ya turo mata. Ta shigo tana layi yayin da ta nufi hanyar dakinta.
Bakura ya fada cikin bata fuska. “Zo ki dauki plate din
“abincinki da kofin shayinki ki shiga da shi dakinki ki ci a can.”
• Hannuwanta na karkarwa ta zo ta kwasa, kallo daya za ka yi wa mahaifiyarta da qannenta kaga alamar tausayinta a fuskokinsu.
Sai kalmar “Sannu, sannu, sannu.” ce ke fita daga bakunansu.
Zahra na amsawa dakyar ta wuce zuwa dakinta. Ta na shiga sai ta bude wani shafin kuka, na musamman da ta jawo wayarta taga missed calls din Abdulmajid da text massages guda biyu, sakonnin dai na soyayya ne har yanzu. Samira ta dubi maigidanta Bakura ta ajiye cokalin da
yake hannunta ta yi ajiyar zuciya.
Ta ce, “Abban Yagana, ko dai tsananin son karatu da naci ne ya jawowa yarinvar nan ciwon ulcer saboda rashin maida kai ta ci abincin kirki?”
Shiru yayi bai ba ta amsa ba. Samira ta kasa:
daurewa ta dube shi ta ce “Oga baka ganin rashin baccin da yarinyar nan ke yi shi ya jawo mata kasala da jan ido? Ya kamata a kaita asibiti tun dazu na lura da ita kamar tana fama da zazzabin cikin kashi. tana zazzabin dare ne?”
Wannan karon ma danna abinci yake a cikinsa ko
kallonta bai yi ba.
Samira ta fusata ta mige tayi wuf ta fada dakin ‘yarta
Zahra, a rigingine ta iske ta ta na kallon silin da fankar da ke jujjuyawa a hankali. Daga dukkan alamu tunani ke damunta.
Zahra ta yi firgigit ta mige zaune da ta hango mahaifiyarta na shigowa. Kafin Samira ta ce wani abu wayar Zahra ce ta dau ruri.
Ta na dubawa sai taga lambar Abdulmajid ce.
Tashin hankali marar misaltuwa ne ya rufto mata, ta kalli wayar ta daga kai ta kalli mahaifiyarta.
‘Sai Samira ta ce, “Ki amsa wayar mana.
Zahra ta ce “Mama ban san lambar ba.” Samira ta ce
“Sai an san lamba ake amsawa, ko ke ma mulkin ne irin na Abbanki maganarsa ma sai an siya wataran?”
Zahra ba ta daga wayar ba har ta katse. Samira ta zauna a gefen gado ta dubi plate din abinci da kofin shayin, dankar yake da abinci ko dandanawa bata yi ba. Ta juya ta dubi Zahra ta ce, “Yagana me yake damunki ne yau?” Zahra ta lumshe ido ta yi murmushin karfin ta ce, “Mama bani da lafiya.”
“Ciwon mai yake damunki?” Samira ta tambaya.
Kafin ta ba ta amsa shigowar Bakura ce ta katse su, Samira ta mige a fusace ta fice daga dakin dan ta ji haushin share ta da yayi dazu tana yi masa magana.
Zahra ta firgita ta daga kai ta dube shi-ta zabura ta gyara zama. Ta ce, “Abba sannu da gida,” Ya ce “Yauwa, Mamana ya jikinki? Wai me yake damunki ne.”
Ta sosa weya ta ce “Abba, ciwon kai ne.”
Ya ce “Ba wani ciwon kai rashin barci dai. Ki ci abinci ki
sha maganin ciwon kai ki kwanta ki yi barci, rashin bacci ne yake damunki.
Kafin Bakura ya rufe bakinsa wayar Zahra ta dau ruri.
Yayin da zuciyarta ta fara dukan uku-uku, musamman data duba ta ga lambar da ake kiranta, Abdulmajid ne. Saboda gudun zargi ta yi sauri ta danna yayin da hannunta ya dauki rawa, cikin karkarwar murya ta yi sallama.
Ya amsa mata da cewa “Wa’alaikis salam ya abar
Kaunata. Zahra, me yasa kike azabtar da ni, kike wulakanta ni a dalilin tsantsar son da nake yi miki?”
Ta yi caraf ta ce “Wrong number.” Ta katse wayar. Kafin ta ce wani abu tuni Bakura ya juya ya fice ba tare da ya yi mata salama ba.
Zahra ta shiga halin laila hau ilahi da matsananciyar damuwa. Zuciyarta ta shiga zullumi.
Ta ce a ranta” Anya kuwa Abban bai jiyo abin da Abdul majid ke fada ba? Tabbas rayuwata tana cikin garari, hakika za mu raba gari da Abbana.”
Hmmm