‘yarsa ta fasawa ‘yata kai, sharia ni da shi babu mai saka ni na janye.”
Malam Yakubu ya ce “tabbas kar ka bar maganar nan nima ban goyi da bayan ka bar maganar nan ba,zan tambayi Yagana da kaina ta fada min gidan su Yarinyar sai mu je har da ni maji dalilin da yasa ‘yarsa ta fasawa Yagana kai. Idan ya nuna
‘yarsa bata yi laifi ba ko-tayi daidai to ya cancanci a kai maganar kotu suyi musu tsakani.”
•Bakura ya gyada kai ya ce “Allah ya kai mu
Kano lafiya.” Malam ya ce “amin Allah ya kai mu lafiya.”Washegarin ranar ne ranar walima, taro yayi taro sai dai shagalin ya raunana saboda da goshin Yagana ya kunbura suntum duk wanda ya dube ta sai gabansa ya fadi, kowa yana tambaya me ya sami Yagana a goshi?
“faduwa ta yi.” Amsar da Samira take basu kenan.
Itama Yagana amsar da take bawa kawayenta kenan.
Tun ranar da abin ya faru, safe da rana da yamma da
dare Bakura sai ya bugo waya yana tambayar Zahra me ya hada ta da yarinyar, kuma wacece yarinyar? Sai Zahra ta hau nuku-nuku tana kame-kame da alama bata da niyyar fada masa,
Malam Yakubu ma ya sha karbar wayar yana
lallashinta yana lallaba ta akan ta fadi sunan yarinyar don ayi musu tsakani amma Zahra ta qi fada idan aka takura mata da tambaya sai ta fashe da kuka duk da Zahra bata san da wanda take magana ba ma’ana bata san mahaifin Sajida ba ne.
Idan ran Bakura yayi dubu ya gama baci a yanzu ya fi
jin haushin Zahra akan yarinyar da ta fasa mata kai. Allah- Allah yake kwanakin su cika ya dawo Kano ayi wacce za ayi. Ranar da su Bakura suka cika kwanaki goma sha biyu, a ranar suka dungumo suka dawo Kano, daga filin jirgi ba’a wuce da su Malam gidansu ba sai suka zarto gidan Bakura kai tsaye sai suka kutsa farfajiyar gidan. Malam da almajiransa sun ga aljannar duniya, sai kallon gidan suke zuciyarsu cike da sha’awa, suka wace cikin katafaren falon inda suka iske an shinfida katuwar darduma an jera abinci kala-kala da abubuwan sha iri-iri. Bayan sun zazzauna Samira da Zahra sanye da dogayen hijabai tare da kannen Zahra gaba daya suka biyo layi sukazo gaban su Malam suka zube suka kwashi gaisuwa. Zahra na ganin Malam Yakubu ta tuno da fuskar cewa Mahaifin Sajida ne, sai taji gabanta ya fadi.
Daman ita Samira bata san shi ba bata san ma daga inda Bakura ya samo su ba, ita dai ya bata umarni a dafa abincin mutane goma sha biyu zai zo da su, kuma ta dafa shikenan abinda ta sani bata damu ta tambaye shi su waye ko daga ina suke ba.
Bayan sun gaisa sai Samira ta ce da yaranta “to mu
shiga ciki mu barsu su ci abinci. Har sun juya baya zasu tafi Bakura ya kwallawa Zahra kira, gabanta ya yanke ya fadi ras,Jikinta ya dau karkarwa* kan ka ce kwabo” sai hawaye ya dinga kwararowa daga idanuwanta.Ta zo ta durkusa a gabansu. Bakura ya harare ta, ya juya ya dubi Malam ya ce “dubi goshin yarinyar nan ka gani. Yau wajen sati kenan amma har yanzu da sauran kunburin a goshinta.
Wa yasan yadda gurin yayi a lokacin da akayi abin?
Wallahi Yagana ban taba dukanki ba amma idan ki kayi min taurin kai sai na bubbugeki.”
Zahra ta fashe da kuka yayin da jikinta ya dau rawa.
Malam yasa hannu ya dakatar da Bakura. Ya ce ka ”’kyale ta a hankali zan tambaye ta za ta fada cikin lumana.da kwanciyar hankali.
Malam ya shiga jawowa Zahra ayoyin Kur’ani da
” nasihai kala-kala masu ratsa jiki, ita dai kuka shaf-shaf-shaf take.Ta na tunanin yadda zata dubi kwayar idon Malam ta fada masa
‘Yarsa ce ta fasa mata kai. Ta kudiri niyyar yau ko mahaifinta zai kashe ta ba zata iya fada masa wacce ta fasa mata kai ba.Bakura ya ce “Malam ka ci abincinka ka rabu da ita har ta gama kukan, ko kukan jini zata yi yau sai na saka ta a gaba ta nuna mana gidan su yarinyar. Ta yaya za’ayi ma tace bata san yarinyar ba, kuma ta qi fadar abinda ya hada su?”
-Ya dakawa Zahra tsawa ya ce “koma can gefe ki zauna ki gama kukan, ko ki fada ko karki fada muna gama cin abincin nan zamu saka ki a gaba ki nuna mana gidan, idan kika qi za ki ga abinda zan yi miki a yau. Me za’ayi da irin shiru-shirun nan naki? zurfin cikinki yayi yawa.”
Zahra ta koma gefe tana ta rusar kuka ta rasa abunda
yake yi mata dadi, tunda take a rayuwarta bata taba shiga irin wannan tashin hankali ba. Tayi nadamar zuwa gidan su Sajida da tayi.
Sautin kukanta ne ya ke tayarwa da Samira hankali ta
kasa zaune ta kasa tsaye sai safa da Marwa take a tsakanin gofar falo zuwa cikin gida. Ta san Zahra da zurfin ciki, Bakura kuma da zuciya. Idan ya hasala zai iya mangare ta a sake yin rauni na biyu.
Ta ji kawai ba zata iya ba gara kawai ta matso daga kusa tana ganin abinda zai faru. Ta yi sallama ta shigo falon bata damu da hararar da Bakura ke yi mata ba •Ta sami kujera ta zauna a kusa da Zahra, magana take yi mata cikin rada, shawara take bata kawai ta fadi sunan yarinyar da adireahinta babu abinda zai faru hakkinta zaa kwato mata. Su Bakura su ka gama cin abinci tas, Zahra ta san kanta
zai dawo. Zahra ta dubi malam Yakubu ta juya ta dubi mahaifinta sai ta ji gabanta ya sake faduwa.
Tsoro mai firgitarwa Bakura ya daka mata tsawa daga ita har Mahaifiyarta sosai da suka razana ya ce “wannan shine tambayar da-zan yi miki ta karshe ki fada min wacece yarinyar?
Kuma waye ubanta a Kano? Kuma da wa take taqama a kasar nan?”.Bakin Zahra yana karkarwa, haka hannunta yana rawa sai ta nuna malam Yakubu cikin rikikitacciyar murya ta ce “Malam ne mahaifinta, Sajida ce.Malam ya kalli Bakura, Bakura ya dubi Malam gada daya suka juyo suka dubi Zahra. Su ka hada baki a tare su ka tambaya”Sajida? ”
Samira ma ta tambaya “Wacece Sajida?”
•Wannan amsar ta gagari bakin Zahra, ba ta san amsar da za ta bata ba.
TAMBAYA???
- Shin wacece Zuhuriyar nan da Bakura yake mutukar kauna fiye da iyalansa, fiye da kan kansa?
- Meye dangartakar Zuhuriya da Bakura da yake tsananin begenta?
- Shin ina Zuhuriyar take ne, ko ina ta tafi? Shin Bakura zai yarda ya auri Sajida? musamman yadda tsantsar rashin tarbiyyarta ya bayyan a fili?
- Shin yaya za’ayi a raba soyayyar Abdulmajid da Sajida?
- yadda Sajida take tsananin kaunarsa haka?
- *Shin yaya soyayyar Zahra da Abdulmajid zata kasance?
- Musamman daya ganta a zahiri kuma tayi masa?
- *Shin wanne mataki Bakura zai dauka akan mahaifin Sajida da ita Sajidar kanta? Tunda yayi rantsuwa sai ya dau fansa ba zai gyale wacce ta aikatawa ‘yarsa Jalli daya kwal wannan ta’asar ba,
- *Shin wanne mataki malam Yakubu zai dauka akan Sajida da mahaifiyarta musamman idan ya ji ance da Abdulmajid suka fita?
Hmmmm