KAI KAFI CHAN CHANTA CHAPTER 23 BY JAMILA UMAR TANKO

Bakura ya ji gabansa ya yanko ya fadi kamar

• yadda irin wannan fargaba ta ruftowa Malam.

Bakura ya juya ya dubi Malam, yayin da shi ma Malam ya juyo ya dube shi, duba mai cike da dimaucewa, gami da gigicewa, lokaci guda suka Juyo suka dubi Zahra. Bakura ya ji ga66ansa sunyi sanyi, har ba shi da kuzarin da zai iya ci gaba da rike katon faskaren da yake hannunsa. Cikin sanyin jiki ya tsugunna ya ajiye faskaren a kasa, yayin da’ Malam ya sulale ya durkushe a kasa yana karkarwa.

Yana fadin. “Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un, Sajida, Sajida kin cuce ni,bazan barki ba har sai an fitarwa. Zahra hakkinta kamar yadda muka Kudira, saboda kada muyi kaffara ni da kai gaba daya.

Sajida ta cancanci a hukunta ta, saboda yarinya. ce marar jin magana, mai tsiwa. Ka haifi mutum ba ka haifi halinsa ba. Ya ya zan yi da rayuwata? Ina zan saka raina? A ce ni a rayuwata ba zan matsa nan da nan ba, sai dai in zauna in yi gadin Sajida da Abdul Majid. Yanzu Sajidar da na hana zuwa makaranta, itace aka hadu da ita har a Super market.

Kafin Malam ya rufe bakinsa, kuka ya kece masa saboda takaici. Hankalin Bakura ya tashi, tausayin Malam ya lullude shi, yayin da ya ji kwalla ta cika masa ido. Yayi sauri ya mayar da ita.

Tsananin, fushin da tafasar da zuciyar ke ciki ya lafa,

zuciyarse tayi sanyi. Yayi Salati, hade da sanyin jiki ya girgiza kai• Ya ce da Malam *Na yafe, na bar zancen nan duniya da lahira, tunda Sajida ce. Sai dai nayi mamakin abin da zai hada ta da Zahra har ya kai su ga haka. A iya sanina, sanda Zahra ta ziyarce ta sun rabu lafiya, ba tare da sun yi fada ba. To, me yake faruwa?”

Malam ya rike kai yana jujjuyawa, don takaici yana magana cikin zubar da hawaye.

Ya ce, “Mugunta ce kawai tsagoranta, amma me Zahra za ta yi mata har ya kai su ga yin fada. Ai ko baka sa an kulle Sajida ba, yanzun nan zan biyo ta police station, in tafi da ‘yan sanda su kulle ta.”

Bakura ya zabura, gami da daga hannu biyu yana yi wa Malam magiya akan ya yi wa Allah ya bar zancen nan. Yasa hannu ya tashi Malam tsaye, gami da ci gaba da lallashinsa, yana mai ba shi baki ya kwantar da hanakalinsa ya bi abun a hankali, kada ya biyewa sharrin zuciya ya lahanta ‘yarsa. Ita ma

• Zahrar ba kyalle ba ce, watakila wani abu ta yi wa Sajidar har ta kai su ga haka. Da kyar Malam ya jefa kafarsa ya karasa wajen mota, Bakura na gefensa ya yi sauri ya bude masa kofa ya shiga gidan gaba ya zauna, yayin da sauran gardawan almaiiran suka shiga baya.Har Bakura zai rufe masa Kofa, Malam ya rike Kofar, gami da juyowa ya dubi Zahra ya kwalla kiran

sunanta. Ta yi firgigit ta karaso gabansa ta durkusa, yayin da bugun zuciyarta ya sake karuwa. Malam ya dubi zahra cike da tausayi da nadama. Ya ce,

“Zahra kiyi wa Allah ki fada min duk abin da ya faru tsakaninki da Sajida?”

Zahra ta dago da sauri ta dubi mahaifinta, yayin. da ta ci karo da galleliyar hararar da yake gallo mata, ta durkusar da kai kasa, yayin da muryarta ta hau rawar disco tana sama tana qasa don fargaba.

Babban tashin hankalinta kada zancen saurayi ya fito a cikin maganar, saboda yadda mahaifinta yake Kyamar abun. Ita kuma ta san saboda Abdulmajid yana yi mata waya, Sajida ta kullace ta. Zahra ta yi narai-narai da ido. Ta ce Babu abin da na yi mata ta jawo gwangwani ta fasa min kai.”

Tsawa tsawa firgitarwa Bakuta ya daka mata, ta ji har tsakar kanta na karkarwa, Ya ce, “Ki fada mana gaskiya, ko mahaukaci ka ga ya bi yara tsokanarsa sukayi.” Cikin kuka Zahra ta ce,

“Abba, wallahi na rantse da wanda numfashina yake hannunsa, tun ranar da muka je da kai ban sake ganin Sajida ba, kuma babu abin da ya hada ni da ita sai ranar da muka hadu a Super market dinmu. Kalmar da na ji ta ambata da ta ce da kawarta Hajiyayye ga munafukar da take hada min tuggu. Kafin in tambaye ta, ta wawuro gwangwani ta kwada min.”

Kuka ya sake kece mata, Malam ya gyada kai ya ce, “Ita da Hajiyayye suka fita Super market siyayya. Ina suka sami kudi?’ Wannan ma abun tuhuma ne, tabbas kwarya ta gari tana ragaya, Sajida ba tayi sa’ar uwa mai tarbiyya ba. Zahra goge hawayenki zan bi miki hakkinki. Tashi ki tafi ki yi hakuri, ki yafe mana, ki yi mana afuwa ba za a sake ba.

Zahra ta ce, “Na yafe mata Malam.” Ta yunkura ta tashi ta nufi inda mahaifiyarta da kannenta ke tsaye carko-carko, suna kallo suna sauraron wannan al’amari mai kama da al’mara.

Bakura ya ce da Malam, “Kamar yadda kake ba ni shawara nake dauka, ka yi min alfarma guda daya nima a yau. Dan Allah idan ka je gida kada ka daki Sajida, balle ka ce za ka dauki itace ko wani makami ka fasa mata kai, ko ka ce za ka hada ta da ‘yan sanda da dai sauransu. Ka lallaba ta ka tambaye ta dalla-dalla abun da ya faru tsakaninta da Zahra, kamar yadda ka tambayi Zahra cikin sanyin rai. Ka mata nasiha, kada takurar ta yi mata yawa har ta falle fiye da yadda take a yanzu.”

Malam ya gyada kai ya ce, “Na yi maka alkawari ba zan dake ta ba. Sai dai ina gudun kada wannan abu ya jawo silar tabarbarewar zumuncin da ke tsakanina da kai.”Bakura ya zabura ya ce, “Haba, haba Malam me zai sa ka yi wannan tunanin, babu abin da zai sa in canja. Jibi ma zan zo daukar karatu insha Allah.

Sajida yata ce, ko in ce kanwata ce. Ita da Zahra duk daya ne.”

Malam yaji dadin kalaman Bakura, ya yi murmushi ya ja kofar motar ya rufe.

Ya ce “Allah ya saka da alkhairi, na gode ina sauraron zuwanka jibin.” Direba ya ja mota suka tafi, kallo daya Bakura ya yi wa dandazon ‘yan aikin da suka taru don bada hakuri, sai kowa ya warwatse sum-sum-sum, ya kama gabansa. Yayin da ya sake wurga idonsa ya dubi iyalinsa suma suka dibi ‘yan kafafuwansu zuwa cikin gida. Bakura ya sami kujera a gindin wata bishiya mai sanyi dake farfajiyar gidan ya zauna yana mai tsananin tunani, yana jujjuya kalmar da Sajida ta fadawa Zahra.

“Ga munafukar da take hada min

tiggu.” Wanne munafunci Zahra ta yi mata a karon farko da ta fara saninta? Wannan al’amari ya dimauta zuciyar Bakura matuka.

A cikin gida kuwa, Zahra ce da Mamarta ake fafatawa, domin ran Samira ya baci matuka. Ta saka Zahra a lungu ta ritsa ta, ta ce sai ta fada mata.

Wacece Sajida? A ina take? Yaya aka yi har suka je gidansu, amma ba su tada fada mata ba? Zahra ta zayyanawa mahaifiyarta duk yadda aka yi da dalilin da yasa suka je ta ganta. Samira ta ji hankalinta ya tashi, duk da ta san labarin yarinya mai kama da Zuhuriyya, amma ba ta ga dalilin da Bakura zai dauki Zahra ya kai ta gidansu ba.Lallai akwai wani boyayyen al’amari, akwai wata hujja mai karfi a cikin wannan magana, musamman ga wanda ya san tsatstsauran ra’ayin Bakura.” Samira take tattaunawa a zuciyarta, yayin da take kai-kawo a tsakiyar falo. Zahra ta takure akan kujera ita da kannenta gaba daya sun rasa abin da yake yi Wa rayuwarsu dadi a yau, domin su ba su saba haduwa da irin wannan tashin hankalin gidansu ba. A koda yaushe iyayensu a cikin nishadi suke, amma yau komai ya hautsine.

Samira ta juyo a fusace ta dubi Zahra. Ta ce

“Mahaifinki ne abokin shawararki, mahaifinki ne abokin hirarki, shine ki ke fadawa damuwarki, ban da ni.”

Zahra ta bude baki za ta yi magana, Samira ta dakatar da ita da hannu, gami da daka mata tsawa mai Kara. Samira sai bambamin fada take har da kumfar baki, ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, domin ranta ya baci matuka. Zahra ta yi shiru, yayin da kuka ya addabi idanuwanta tayi nadama, ta yi dana-sanin zuwa gidan su Sajida a rayuwarta.

Hmmmm