KAI KAFI CHAN CHANTA CHAPTER 4 BY JAMILA UMAR TANKO

Magaji ya sake zazzare ido’ ya fad’a cikin rawar murya

“daga makaranta ba inda na taba kaita wallahi.”

Bakura ya gyada kai ya yi shiru can ya ce “wallahi,

Allah kenan fa. Na yarda amma ka tabbatar abinda ka fada min gaskiya ne, zanci gaba da bincike, daga lokacin da na gane ka yi min garya daga sanda ná lahira zai fi ka jin dadi. Domin ka fi kowa

•sanin halina a duk cikin ma’aikatan nan. Shekararmu goma sha daya kenan tare.”

Bakura ya wuce cikin gida ya-bar Magaji a nan ya na muzurai gami da mamakin wannan tambaya.

Kofar wani katafaran falo ya nufa wanda aka yi shi a. cikin wata kayatacciyar baranda mai dauke da tukwanen fulawoyi

An jejjere kana shiga dosar kofar falon za ka ji sanyin na’ urar sanyaya daki (AC) ta daki hancinka gami da qamshi mai dadi. Ka na shafa labulen da ke zagaye da falon za ka tabbatar bada gujari-gujarin auduga gama gari aka halicci yadin labulen ba, saboda laushinsa. Zanen fulawar jikin labulen zai tabbatar mu ku da cewa ba dagigan mutane ne suka qera labulen ba. Haka yanayin dinkin da yadda aka liga labulen kansa sai wanda ya yi masters akan dinki, wanda ya karanci design and decoration ne. Labule ma kenan ina ga kayan alatun dake cikin falon nan? kallo daya za ka yiwa kujerun, center table, flower bases din falon ka gasgata cewa an gera su ne da ruwan gwal, anyi musu design da azurfa. Komai na falon anyi masa kalar kore da ruwan goro (green and orange) kama daga fentin jikin bango har centre •kafet, dake tsakiyar kujerun har su kan su kujerun da dining table da yake dining area a falon. Hatta fitulun falon abun kallo ne domin su ma hasken da suke bayarwa kore ne da ruwan goro.

Katuwar talabijin woto LCD ce a maqale a jikin bangon

falon kai ka ce mutum ne a jikin bangon ba hoto ba. Akwai gofa wacce za ta kai ka cikin gida, ka ma fita tsakar gida za ka gani.

Wanda aka gawata shi da tiles tsakiyar kuma anyi masa dan zagayyen tudu an dora flower veses da wata gatuwar bishiyar (umbrellar) wacce take hana rana shigowa. Wäsu kawatattun kujeru na kaba aka jejjera domin shan iska. Qofofi ne guda shida a zagaye da tsakar gidan, idan ka bude na farko wani gaton kicin ne mai girman gaske wanda babu abunda za ka hango illa kayatattun kitchen cabinet kalar ruwan dorawa (yellow) sai Gas cooker da-electronics kala-kala. Hakika kallo daya za ka yiwa kitchen din nan ka tabbatar wadanda su ka hada kicin din karanta su ka yi ba kai tsaye suka tari aradu da ka ba. A takaice dai duk abunda ya ke

-cikin kicin din nan fari da ruwan dorawa ne. Sauran kofofin kuwa™ guda biyar kowannensu gaton falo ne, da kuna bibbiyu; da kayataccen bandakai guda biyu.

D’aya na Zahra ne, d’aya na ‘ya’ya maza ne, daya na

matar gidan ne, d’aya na mai gidan, d’aya kuma a rufe ya ke ba kowa na saukar bagi ne.

Sai dai dakin Bakura (master bed room) ya fi sauran

girma sosai da qawatuwa domin girman falonsa ya kai girman wani garamin gidan kacokan.

• Falon hade yake da dining area, da kicin sai ka shiga bed room maimakon dakuna bibbiyu irin na sauran d’akunan shi guda d’aya ne aka yi shi makeke, ya yi dukka biyun girma in abun a fashe su ne.

Biro na da takarda baza su iya zaiyana haduwar

bangaren maigida ba sai dai na kan iya fadar kalar da aka hada a ciki. komai na ciki kalar nan madara ne aka dan sirka da fari.

Kama daga fenti, kujeru, dining table, kayan kicin, set din gadon da kayan toilet shima ko ba’a fada maka ba ka san turawa ne su kazo Nigeria su ka baje fasahar da Allah ya ba su, suk a shiryawa

Bakura gidan nan. Haka ma dakin matarsa aka gawata mata falonta, dakuna biyu da bandakanta, ita kuma kalar jan duhu (maroun) ne komai.

Dakin Zahra babbar ‘yarsu kuma ita ce ‘yar su mace kadai itama na ta bangaren falo da dakuna biyu da bandaki a kowanne daki. Itama an zuba mata funiture da su ka dace da budurwa, duk ko ina tayi like-liken hotunanta dana iyayenta, qannenta da gawayenta. Komai kalar pink ce a dakin.

Dakin ‘yaya maza kuwa su uku ne, na biyun sunansa

Abubakar shekararsa goma sha uku, shi ya dauki daki daya. Mai bin sa Umar shekarunsa bakwai da d’an autansu Usman shekarunsa hudu su bigu a dayan d’akin. Kowannensu da d’an garamin gadonsa da lokar kayansa da mudubi da kujera da teburin karatu da rabutu. Falo kuwa durowar litattafai ce iri-iri da set din kujeru, sai Talabijin da settelite game da tashoshin cartoons da karatun qur’ani kadai aka jona musu. Duk abinda ke cikin dakin kama daga fenti har furniture da bandaki kalar Blue ne aka sirka da pupple.

Dakin dake rufe ma ba’a bar shi a baya ba wajen kyau

da tsari duk da ba kowa a ciki amma akan yi baqi mata daga wani gari su ake saukewa, shi ma duk abunda ya ke ciki kalar brown ne.

Bakura na shiga katafaren: falon nan ya iske matarsa

abar qaunarsa Samira, ta caba ado ta na jiran mai gidanta ya dawo.

Ya na shigowa ta daga ido ta dube shi, sai ta yi masa fari da fararen idanuwan nan na ta dara-dara. Irin farfarin da ta gane yana kwantar masa dá hankali. Yayi murmushin garfin hali gami da yi mata sallama. Samira ta amsa cikin jin dadi tare da miqewa da sauri ta na rangwada ta nufo shi sanye da wata atamfa koriya super Holland wacce tayi mata hadadden dinki na matsatstsiyar riga da siket mai daukar hankalin maigida. Tana garasowa inda ya ke sai hancinsa ya daki qamshin turaren jikinta designers, hade da na hadaddiyar humra

da turaran wuta.

Ta fada cikin sanyayyiyar murya mai kama da rada

“sannu da zuwa Sweety.”

*Kafin ya bude baki ya amsa ta sumbaci gefen kumatunsa, ya sa hannu ya dakatar da ita gami da zare jikinsa daga gare ta ya wuce abinsa. Ya shiga cikin gida Samira ta tabbatar yau hankalin Sweety ba’a kwance ya ke ba, sai ta fara jerowa kanta tambayoyi ta na tuhumar kanta da kanta ko ta yi ma sa laifi ne kafin ya fita. Ta tuno ai lafiya kalau su ka rabu har ta raka shi mota su na wasa da; dariya da yamman nan ya fita ya na nishadi.

Samira ta fada a bayyane “waya tsokano min

maigidana? Ya b’ata ma sa rai mutumin da idan ransa ya b’aci ya kan yi fushin kwana uku bai huce ba.”

Fushin Bakura shi ne babban tashin hankalin Samira

domin ba zai kula ta ba, ba zai ci abincinta ba, babu wasa balle hira, ga mummunar harara da daka tsawa. Dan haka yadda take lallaba jaririn da ta haifa sabuwar haihuwa haka take lallaba maigidanta don kada ya yi fushi. Allah ya jarrabi Samira da tsamanin kaunar Bakura, tana ji a jikinta da a raba ta da Bakura gara a rabata da rayuwarta.

A sangare a tsaye Bakura ya bar Samira ta ma tunani

hade da fargaba da karanto addu’o’i a zuci. Addu’ar Allah Ya yayyafawa zuciyarsa ruwan sanyi koma me aka yi masa a waje. Shigarsa dakinsa ba dadewa ya fito jikinsa da ruwa da alama dai alwala ya dauro.

Tayi sauri ta saki fuskarta, ta dube shi ta yi murmushi ta ce “alwala kayi, za ka jè masallaci?”.

Ya amsa a ciki-ciki “eh:” Har ya kai gofar fita ya juyo ya dubeta ya ce “ina Yagana?”

Ta amsa cikin jin dadin maganar da ta samu ya yi mata. Ta ce “ta na daki ta na karatu, saboda sun kusa fara jarabawa.

•Ya sake cewa “ina Abubakar, Umar da Usman?

Ta ce su na nan a masallacin gofar gida tunda yamma, Malam Hashim ya zo su na daukar karatu.”

Ya juya ya fice ba tare daya ce komai ba.

Mamaki ya sake lullude zuciyar Samira ta kasa gane halin da yake ciki yau, kamar ya na farin ciki kamar ya na bagin ciki. Ta shiga dakinta ta yi alwala ta yi sallar magrib. Tayi ta lazumi tana addu’a kamar yadda ta saba kullum akan Allah ya sassauta zuciyar

Bakura, ya so ta d’ari bisa d’ari kamar yadda take son sa, ya dinga sakar mata fuska, ya rage wannan muzuran da kwarjinin da ya ke yi mata don haka kawai ta ji ta na tsoransa. Kada Allah ya hada shi da wacce zai ji ya na so a rayuwarsa balle ya yi mata kishiya, duk da ta san tsautsauran ra’ayinsa ba shi da niyyar yin mata biyu a rayuwarsa. Mata basu cika burge shi ba amma ta san lallai idan ya hadu da yarinya mai tarbiyya wacce take da ladabi da biyayya za ta iya burge shi ya aure ta, ita kuma tsantsar sonsa ne ya dasa mata tsananin kishinsa. Addu’ar Samira kenan, dan duk wanda ya santa ya san ta ya san ra’ayinta.

Aka kira sallar sha’i a masallacin gofar gida, su Bakura suka bi jam’i aka tayar da sallah. Samira ma daga dakinta ta

Hmmm