na cire Sajida daga makarantar boko ta na aji biyar na sakandire.
Saboda a hanyar makarantar bokon ne ya ke tare ta su dinga zance.
Ni dai na fada duk lokacin da ta yarda Abdul majid ya lalata mata rayuwa, ma ana ta bari ya yaudare ta, ya san ta ya mace ya cuce ta kuma daga lokacin da na aurar da ita na yi bincike aka tabbatar min ba cikekkiyar budurwa ba ce sai na yanka ta.”
Bakura ya yi shiru na wani dan lokaci kansa a sunkuye a kasa kamar mai tunani. Can ya dago da kansa ya yi ajiyar zuciya.
Ya ce “Allah ya kyauta.” Malam-yakubu ya dubi Bakura ya ce “wai daman ka san Sajida da Abdul majid ne ko ka na da labarinmu?
Ko ka na da masaniya akan tagardamar da ke
tsakanina da shi?”
Bakura ya ce “ko daya ban san su ba, na hadu da su ne akan hanya zan wuce, na kalli Sajida na dubi Abdul majeed na tabbatar ba abokin huldarta ba ne. Na bata shawara ba ta saurare ni ba, sai na ga ya dace in biyo ta don in hadu da mahaifanta in fada mu su don su san halinda ‘yarsu ta ke ciki. ka san mu barebari akwai mu da tsawatarwa Baba.” Su dukka suka bushe da dariya.
Malam Yakubu ya ce “ai mu Fulani mu aka sani da kara, kunya da kawaici, ai Sajida ba ta biyo Fulatancinmu ba, na rasa yadda zan yi da ita. Amma yanzu na saka ma ta takunkumin da ko ita ce uwar dubara da wayo ba ta isa su hadu da wannan dan iskan yaron ba, marar tarbiyya.”
Bakura ya ji kansa ya yi masa nauyi ya fada a ransa “su Saida Fulani né kenan ashe babu hadi Saida da
Zuhuriyya.” Hikimar Bakura daman ita ce ya ambaci Barebari ne don ya ji ko su Sajida su na da alaga da Barbari idan da alaka to. ta ina, waye da waye ko kuma ta ina alakar ta hada zuhuriyya da
ita. Amma babu wata alaka kwata-kwata.
Bakura ya nisa ya ce “Malam ku fulanin ina ne?”
;Malam yayi murmushi yace “fulanin Shanono ne amma mazauna Kano, tun-ina yaro na zo Kano yawan almajiranci, daga
nan ban koma ba.” Bakura ya sakejin ya kidime yayin da yake jinjina da yabo ga Rabbul samawati wanda Shine ya halicci Sajida tayi kama
da Zuhuriyyarsa sak. Bakura ya dubi malam Yakubu yayi murmushin nan nasa mai faranta zuciyar wanda ya yiwa. Ya ce Malam ina son in zama daya daga cikin almajiranka domin nima
asalina almajiri ne yawon almajiranci ne ya rabo ni da garinmu Maiduguri zuwa Kano.”
“Almajiranci fa kace?” malam ya tambaya cike da
mamaki. Bakura ya gyada kai ya ce “kwarai kuwa malam.” Malam ya nisa ya gyada kai ya na shafa dogon gemunsa ya ce
“‘Allahu Akbar!!! Yanzu yaro kai almajiri ne ada? Allah ya rufa maka asiri ya maka arziki? Haka Allah’ Ya ke ikonsa. Yaya sunanka?” Bakura yayi murmushi ya ce
“Sunana Bakura, sunan mahaifiyata
Yagana, mahaifina kuwa sunansa Bahna. Ina da mace daya mai suna Samira. Yarana hudu babbar sa’ar Sajida ce shekarunta goma sha shida sunanta Zahra, ina kiranta da Yaganá don sunan
mahaifiyata ne. Na biyun Abubakar sai Umar da
Usman. Ina zaune a unguwar Amadu Bello Way.” Malam Yakubu ya dubi Bakura cike da sha’awar dama
nine na sami irin wannan ni’ imar taka.
Ya ce “yanzu yaro ka haifi yarinya budurwa kamar
Sajida ‘yar shekara goma sha shida? Amma a haka-kamar baka yi auren fari ba ma.”
Bakura ya yi dariya ya ce “haka ne, nayi aure da wuri ina dan shekara-ashirin da uku, yanzu shekaruna arba’in kenan.” Qaunar Bakura ta sake shiga zuciyar malam. Ya ce ”’yaro ka zo duniya a sa’a, Allah ya yi maka baiwa wacce ba kowa ya samu haka ba, ka godewa Allah.
Bakura ya ce “Alhamdulillahi Ala kulli halin.”
Malam Yakubu ya ce “Allah Ya sanya albarka a cikin dukiyarka da iyalinka, Allah ya gara budi. Yaro Allah ne Ya hada mu, Allah ya dad’a mana dankon zumunci.”
Bakura ya ji dadin addu’ar malam Yakubu ya na
amsawa da “amin summa amin malam.
Bakura ya sake gyara tsayuwa ya ce “Sajida da Yahuza ne gananan yaranka kenan?”
Malam ya gyada kai ya ce “na’ am, su ne kanana kuma
su ne manya.”Bakura ya tsurawa malam ido ya na kallonsa duba irin na rashin fahimta.
Sai Malam yavi murmushi ya ce “ni da matata Furera
mun yi aure tun quruciya amma Allah bai ba mu haihuwa ba sái da muka manyanta, Su biyunan da ka gani su ne kadai ya’yanmu.”
Bakura ya yatsune fuska kamar mai ciwon kai wanda
har hakan ya ja hankalin Malam Yakubu ya tambaye shi “Bakura lafiya ko kwaro ne ya fada ma ka ido?” Bakura ya ce “a’a Malam na dai ji dadi da Allah ya ba
ku haihuwar kafin ku tsufa yadda ba za ku iya haihuwar ba ma kwata-kwata.”
Nan kuwa tsabar firgita ce, ya ji gabansa ya fadi
kasancewar babu sauran wani tunani ko bincike akan alakar Sajida da Zuhuriyyarsa kuma da zai sake yi.
Ya fada a ransa “yanzu babu dangin Zuhuriyya guda
daya da zan kalla in ji dadi a doron duniya? kan ka ce kwabo jikinsa ya yi sanyi idanuwansa sun kada sun yi jajawur, muryarsa ta yi qasa sanyi kalau. Amma sai ya daure ya na hira da Malam don kada ya gane.
Hira su’ke ta yi tamkar d’a da uba, ko kaka da jikansa kai ka ce sun yi shekara da shekaru da sabawa. Daga karshe su ka yi sallama su ka tsayar da shawara akan Bakura zai dinga zuwa daukar karatu da daddare tsakanin sallar magaruba da isha’i sau uku a sati wato ranakun Juma’a, asabar da lahadi. Ba tare da
Bakura ya bawa malam komai ba ya shiga mota ya tafi.Hikimar hakan kuwa shine Bakura mutum ne mai
yawan kyauta amma mai yawan gwada mutane don ya gane masoyansa na zahiri.
Ya na sane sai yaqi yin kyauta don ya ga shin mai zuwa gaishe shi zai ci gaba ko zai daina daman ba don Allah ba ne. Bakura kenan!!!
Bayan tafiyarsa Bakura ya tsinci kansa cikin farin ciki
da tsanamin kaunar Sajida da mahaifinta. Kauna ta saboda Allah ma’ana ya na son su so na tsakani da Allah saboda albarkacin kamar da tayi da Zuhuriyya, ya sa a ransa cewa Allah ne Ya hada shi da mai kama da wacce ya fi so don su yi zumunci.
Kullum Zuhuriyya ce a ransa Allah ya dubi halin da ya
ke ciki Ya kuma amsa addu’ar da yake ta yi shekara da shekaru ya aiko masa da Sajida dan ya dinga ganinta ya na jin sanyi. Allah ne kadai Ya san boyayyan sirrin daya shirya. Irin koyar da tarbiyya da jajircewar da mahaifin Sajida ke da ita shine ya sa ya kwantawa Bakura a cikin zuciyarda, uwa uba” yadda ya ke koyarwa da al’ummar Annabi karatun kur’ani mai girma. Allahu Akbar!!! ;
Ranar juma’a kafin sallar magaruba Bakura ya dira- a kofar gidan malam Yakubu, tare da shi aka yi Jam’in sallar magriba aka idar sai aka firfito da fitilar kwayaye guda uku daga cikin gida.
Manyan maza da dattijai ne suka zagaye malam su na
daukar karatu, kowanne da qur’aminsa. Abin ya yi matukar burge Bakura bai taba zaton haka maza ke ;cika su na daukar karatu ba, a kalla sun yi su ashirin duk da haka ma mutane da yawa ba su sami damar zuwa ba.
A lokacin da malam ya fara dora musu karatu sai ya
fuskanci Bakura ya riga ya haddace duk inda aka bude, sai bayan da aka gama daukar karatu aka yi sallar isha’ i kowa ya watse sai Bakura da Malam ne kadai su ka rage.
Malam ya ke tambayi Bakura shin saukarsa nawa?
Bakura ya ce “ba adadi, amma haddata sau bakwai, na haddace kur’ani, na sake maimaitawa har sau bakwai.”
Malam ya gyada kai alamar ya jinjina masa ya ce “sai dai ka zama mataimakina ka dinga taya ni koyarwa amma kai ba dalibi ba ne, malami ne:”
Su dukka suka yi dariya. Bakura ya ce “Malam anya
ayi haka kuwa?”
Malam ya ce “haka za’ayi Bakura. “
Bakura ya ce “to malam ai kai uba ne ba zan yi ma ka
musu ba. A can gidana ma akwai masallaci a qofar gidan, mazan
Hmmmm